Showing 69001 words to 72000 words out of 150681 words
ta kama wadda ta gama lalata mata komaiba itama a yanzu ta kanta takeyi.
Fitowan doctors ce ta saka kowa miqewa tsaye suna kallansu da dukkanin hankalinsu da nutsuwarsu,
"Bata cikin kowane irin mummunan hali yanzu zata farfado kowane lokaci inshallah so sai ta farfado zamu iya qarasa dubata da wasu aune aunen"
Shiru dukkaninsu sukai kafin Dad cikin damuwa yace
"Hope dai ba konuwa a jikinta koina"
Numfashi Dr ya sauke Yana kallan Dad din yace
"Eh babu a iya dai inda muka duba so banajin akwai konuwa koina inshallah"
Ajiyan zuciya suka sauke dukkaninsu palon Banda Mama data bar palon idanuwanta na cikowa da hawayen tsananin baqin ciki.
Dad ne da Jannah kai tsaye suka nufi dakin da Umman take sedai kafin su isa AZIZ ne yafara isa cikin dakin Yana zubawa fuskanta idanuwansa da har lokacin suke kasa gasgata itace a gabansa har cikin gidansa.
Zaunawa yayi gefenta tareda Dora hannunsa ahankali kan nata zaiyi magana su Ammar da Maheer suka shigo Dad kuma ahankali ya janye hannunta daga na AZIZ din Yana riqewa cikeda kulawa ya riqe cikin nasa Yana qin dagowa ya kalli AZIZ din sbd ko fuskansa baya son kalla kaman yanda su Maheer ma babu wanda ya kallesa.
Jannah ce ta saci kallansa cikeda fargaba taga ya dago jajayen idanuwansa ya zubawa Dad cikeda mamaki da wani irin dacin daya taso masa ya maida kallansa kan su Ammar yaga sun dauke kai suna sake tsananta hade fuska cikeda baqin cikin kasancewansu guri daya dashi suna shaqar iskan daki daya.
Hadiye radadi da bacin ransa yayi Yana kokarin kallansu da fuskan rahama ya miqe tsaye kai tsaye y zare hannun mahaifiyarsa daga cikin na dad din ya kallesa cikin ajiye komai yace
"Bansan tayaya mahaifiyar AZIZ LIMBA ta zama Ummah a zuriar Zaadens ba,
Bansan meyake faruwa ba anan Amma dai nasan duk duniya mahaifiyar data haifeni daya ce kuma itace Nan a gabana Wanda babu Wanda zai iya sauya hakan kaman yanda duk duniya babu Wanda ya isa ya sake rabani da ita idan ba Allah ba dan haka inaga abinda kaima kakeyi din haramun ne ga mahaifiyata sbd.......
Ammar ne cikin tsananin quncin dake cin zuciyarsa y katsesa da cewa
"Kana tinanin kai tsaye zamu yadda da ka Santa ne kafin ma a yadda da ita din mahaifiya ce a gareka??
Ba kaine ka fara ikirarin ka santa ba mahaifiyarka ce ta fara yi mana barazana da dukiya harma da rayuwar dan uwanmu akan mu bata ita tasan Yan uwant, ohh nama manta kudi tace mu fada zata siye mana Umman ta rabamu da qaya hkaa ta fada,
Kai kuma yanzu sai ka fada mana nawa ne naka farashin da zaka bayar akan siyanta kokuma kaima rayuwar Saleem din zaka dauka sbd ka qarasa gamawa damu??
AZIZ da idanuwansa sukai mummunan ja yana sanqarewa a tsaye da jin mummunan abinda Kansa yake kasa dauka bare fahimta.
Maheer ne ya karbe zancen da cewa
"Koma menene abu daya ne da zaka fara Sani anan shine Ummah tamu ce halak malak sbd matar mahaifinmu ce kuma uwa a Zaadens dan haka kasan abinda zai fito bakinka....
Cikin wata irin mahaukaciyar Muryan da baitaba Sanin Yana da ita ba ya daga hannu dukkanin jikinsa na rawa zai saukewa Maheer wani lafiyayyan Mari Dad ya riqe hannunsa tareda tsayawa gabansa ya kallesa yace
"AZIZ LIMBA ka koyi riqe fushinka sbd kada mu bayyana maka namu fushin abin zeyi muni dan haka gwara mu tsya a iya qiyayyar datake cikin kowannenmu a yanzu.....
Da wani irin tsananin fushin maganganun Ammar na farko dake kashesa yake jin saukan maganganunsu da bama yanda ko daya zai yiyu sbd Mama bazata taba gani ko sanin fatima na kusa dashi ba ta kasa fada dan abune da har abada bazai yiyuba,
Sai kuma maganar aure da akeyi na cewan Ummansa Matar wani ce ba waninma Dzad Wanda a tasa zuciyan be San matsayinsu ba a nasu Bangaren kuma ya San tsana ce zallah mara sirki,
Wayene ma ya isa yace masa ya auri mahaifiyarsa a cikin yanayi na ciwon rashin hankali?
Me suke nufi da wai Ummansa Matar Zaadens ce?
Tayaya ma hakan zata faru?
Bama abu ne me yiyuwaba dan kuwa yasan ba saukowa zasuyiba kaman yanda shima a yanzu baima karba aurenba bare se yaji Wanda ya bada ikon yin hakan.
#MAMUH
#LIMZADS
07019691719*_KALBIM_*
Mamuhgee
Book 2
Chapter 40
*_SHOP WITH ME BY RANO_*
08030811300
Kina neman in da zaki samun kayan yara classy kaya na yan gayu at a very affordable price? Ko kina son fara kasuwancin kayan yara amma baki da jarin da zaki saro kayan? Nesa ta zo kusa, kiyi joining community din nan muna saka kaya masu kyau available da inganci a farashi me sauki da zaki dauka ki tallata har ki samu naki kema.
Burinmu shine kowacce mace ta samu sanaar da zata dogara da kanta.
************
Jajayen idanuwansa ya dago ya saukesu akan Dzad Yana masa wani irin kallan fushi Yana kasa riqe dukkanin abinda yake ransa dayake riqewa sbd Jannah akansu Amma sun wuce limit na yanda zai iya riqe kansa sbd Ummah Fatima ta kere kowace irin darajar rayuwarsa ya bude baki Yana kallansu daya bayan daya da tsananin fushi kafin ya tsaida idonsa akan Dzad da yake ganin shine ma kadai yakai ya iya magana dashi yace
"Anan,a gabana, a cikin gidana a cikin kunnuwana da gaban idanuwana Mahaifiyar LIMBA ce ko Fatima sbd maganar Aure da tarkacen da yake cikinsa babu Wanda ya isa duk duniya ya tsaya gaban idanuwana yace mun kai tsaye shi mijin mahaifiyata ne Wadda batada lafiya hankali batareda na masa mummunan daurin da seya rasa nasa hankalin ba sbd girman laifin hakan,
Kallan Maheer yayi yace
"Kuna tinanin kunada mahaukata ne?
Mahaukacin ku yanada license na zama cikakken mahaukacin gasken?
Idan akwai cikakken daya isa ya rabani da mahaifiyata zan gansa ko shi waye"
Shan gabansa Maheer yayi Shima cikin tsananin fushin da bacin rai a bayyane yace
"Wannan kuma ba kaine zakai deciding ba Umman ce da kanta idan ta farka zata tabbatarda ita waye a gurin kowa daga Nan ne zakasan kai din ba kowa bane face AZIZ LIMBA dan kuwa ba Umman kadai ba ko Jannah ka saka kalla wlh nayi maka alkawarin ganin cikakkiyar haukar da kake ambatar Zaadens din nada sbd har abada Jannah ta gama dakai babu abinda zata sake yi da Wanda yayi sanadin rasuwar mahaifiyarta da baqin cikin ahalinta tareda salwantar da dan uwanta.."
Lumshe idanuwa AZIZ yayi ahankali Yana controlling da hadiye tsananin fushi da masifar dake quna cikin jininsa ya bude idanuwansa akan Jannah ahankali Wadda idanuwanta sukai jajir wani irin daci da ciwo ke cin kirjinta akan tashin hankalin AZIZ LIMBA da familynta da batasan yaya zataiwa kowannensu ba.
Magana yaso fada musu wadda har abada bazasu dena jin zafinta ba sbd idan ana maganar wani yayi sanadin rasuwar wani sunkai karshen marasa kunya da har bakinsu yake iya furta hakan sbd abu daya dashi kansa daya Sani shine bai dauki fansar daya kamata akansu ba sbd Mummunan son 'yarsu daya shiga gabansa ya dakatar da komai ya hanasa ganin sun karbi hukuncin daya kamata Wanda shine hukuncin kisa dan koda kowa bai karba hukuncin kisa ba Wanda shine asalin hukuncinsu to Ammar da Dzad zasu karba Amma ya hana barin hakan ta hanyar zabar musu hukuncin dayafi kowane sauki dan kawai kada ya dawwamar mata da baqin cikin rashinsu a rayuwarta,
A yanda sukaiwa Ummitah kisan gilla ko me gadin gidansu akaiwa wannan kisan ya tabbatarda wani labarin ne daban bare ace daya daga cikinsu ne Amma sunada bakin fada masa magana.
Numfashi ya sauke me zafin gaske kafin ya juya ya fice daga dakin dan zai iya kasa riqe zafi da tsanarsu shima daya danne yana kokarin gogewa tsawon shekarun nan da kuma bayyanar mahaifiyarsa a hannunsu Wadda zai iya musu komai akan hakan sbd sun basa sabuwar rayuwar da bai taba tsammani ba Amma kuma yaga alamar bama zasu taba samun fuskantar juna bada wannan fushin da qiyayyar ba sbd Shima a nasa bangaren abinda suke kokarin zuwa dashi bazai taba yadda ba dan Yama fisu jin duk abinda suke ji dannewa yakeyi Amma akan mahaifiyarsa gwara suyi fito na fiton.
Yana ficewa daga dakin Dzad ma ya fito haka dukkaninsu aka bar Jannah kawai Wadda ta rasa tinanin yi sbd kanta dayake toshewa.
Yana fitowa kai tsaye palon su Mama ya nufa Falaq da fiddausi na bayansa koda ya isa Nicky na tsaye tana bubbuga kanta dake neman bugawa,
Mama dake zaune idanuwanta jajir tana ganinsa ta miqe tsaye ahankali zuciyarta na neman fadowa sbd bugawa ta zubawa fuskansa da babu rahama ko kadan tana kallansa lokacin Sayd y shigo palon shima fuskansa jajir sbd tashin hankalin dayake qin qarewa a gidan.
Wani mugun 'daci da zafi tamkar na wuta AZIZ ya hadiye a maqoshinsa daya bushe ahankali kafin ya bude idanuwansa yaqi kallan Mama sbd maganganun Ammar Zad akan Maman dake yawo cikin Kansa suna neman haukatasa da bakinta yakeson ji ta fada.
Rawa hannuwansa ke yi ya bude baki a Karan farko daya hadesu gabaki daya gidan har Mama dayake banbanta girmanta akan kowa,
"Waye da waye ya San da Ummah Fatima na gidan nan?
Waye da waye ya taba ganinta?
Waye kuma ya taba magana da ita?
Shiru dukkaninsu sukai tsit kowa jikinsa na daukar rawan fargaba sbd yanda yake din d yanda yayi tambayar kai tsaye kowannensu yasan ba AZIZ LIMBA din bane wannan tsananin fushi da bacin ransa a bayyane yake da zai iya aikata komai akan duk wani me laifi lokacin.
Falaq ce da duk take cikin tsananin rudanin kasa gane gaskiar waye Mama waye Fatima a gurin Daddynta da Ummitah ta matso gaba ahankali tana kallansa tace
"Daddy ina ganinta duk naje gurin Jan Amma kafin na fara zuwa gurin Jan ban taba ganinta ba kuma haryanxu bantaba jin maganarta ba ni"
Fiddausi ma cikin sanyi daga inda take tsaye bayan Sayd ta bude baki tace
"Ina ganinta idan naje gurin Jan Amma na fara ganinta ne a lokacinda ta fara bugawa Mama kai.....
Qafewa yawu da numfashin Mama yayi ta rintse idanuwanta tana jin jikinta na mutuwa gefe daya tana kallan AZIZ da sauri wanda rufe idanuwansa ahankali ya budesu akan Nicky.
Nicky da gabaki daya ta rude da tashin hankali sbd bata taba ganin AZIZ a cikin wannan yanayin nasa ba a rikice tace
"Mama ce tafara zuwa gurinta acan nasan Ummansu Jannah ce"
Bai juyo ya kalli Maman ba saida ya tattare duka fushinsa ya saka a maqoshi kafin ya ambaceta Yana qin kallanta har lokacin sbd gudun yanda zuciyarsa zata karbi zancen da zai fito bakinta akan idanuwansa sbd zuciyarsa ta kasa yadda da har abada Mama zata ga fatimanta ta kasa bayyana masa bayan yasan yanda suke kaunar junansu.
Shiru Mama tayi tana kasa magana idanuwanta sunyi jajir sun kafe da tashin hankalin da bata taba saka ran zai risketa ba sbd tin a yanzu tana hango wata irin zazzafar tsanar da AZIZ zai mata Wanda bazata taba iya daukan hakan ba sbd ta San bazai taba iya cigaba da zama da ita ba zai raba kansa da ita ne a lokacinda take ganin babu wanda ya isa yaci amfaninsa idan ba ita ba sbd itace tai dawainiya dashi ta shanye baqin cikin da duk ya shiga da qunci.
Shirun mama ya saka jikinsa tsananta rawar daya saka kowa ja da baya suna sauke kai ya juyo ya kalli Maman da idanuwansa da babu kyan gani ya bude baki yana kokarin riqe girmanta dake idonsa har lokacin da da'a yace
"Mama kinsan da Fatima na Nan gidan tareda Zaadens?
Kinsan da Ummanah na 4&4 tin lokacinda kika dawo tsawon watannnin Nan?
Kinje gurinta?
Kinyi magana da ita?
Kinyi magana da Zaadens akanta?
Mama ban yadda da maganarsu data kowa ba taki kawai nakeson ji sbd kece kika San girma da mahimmacin Umma Fatima a rayuwata,
Kece kadai kikasan waye Fatima a duka fadin duniyar AZIZ LIMBA"
Bakinta na wata irin rawa hakama hannuwanta da kafafunta ta bude baki tana kallansa idanuwanta jajir tana kasa musawa sbd tsanarta da zata wuce misali da gyara a zuciyarsa tace
"Eh AZIZ nasan tana Nan Amma wallahi inason......
Wata dafar data saka console mirror din dake gefensa yayi Wanda ta sakasa fashewa da karfin gaske Yana yanka hannunsa sosai yayiwa mirron jikinsa na wata irin jijjigar data saka Sayd da Falaq matsowa da sauri zasu riqesa ya daga musu hannu jikinsa na tsananta rawa koina.
Mama na ganin hakan ta matsosa kafafunta na sake rawa idanuwanta n sake rinewa da rikicewa tace
"AZIZ walh da farko bangane ba inason tabbatarwa ne kafin na sanar maka sai ga....
Sarewa kafafunsa sukai Yana zubewa cikin glass din gurin da gwiwansu idanuwansa na rintsewa hawaye masu tsananin zafi na cikowa idanuwansa sbd bayan mahaifiyarsa data haifesa Mama itace uwarsa daya san haihuwansa ne kadai bataiba Amma zata iya bda ranta dan nemo masa duk abinda tasan shine rayuwarsa wato mahaifiyarsa,
Amma a Karan farko Mama ta basa shock din dayafi na Zaadens sbd su daman yasan zasu iya komai akan son kai da zuciya... itace ta farko data fara boye masa ganin Fatima....
Dafe kirjinsa yayi sbd wani irin azabar dayake jin Yana kasa dauka ya rintse idanuwansa Yana kasa magana sbd bazai iya yanke hukuncin Mama cikin fushi ba.
Falaq da sauri ta qarasa gurinsa tana fadawa jikinsa tana fasa kuka tana kokarin tadasa sbd hannunsa dake jini sosai tana Kiran sunansa da karfi.
Nicky ma gabaki daya tsoro ya rufeta jikinta wani irin rawa yakeyi tayi baya ta kasa matsowa sbd tsoron AZIZ din.
Maman ma hawayen baqin ciki da dacin zuciya ne suka fara gangaro mata tana son matsawa Amma fushin dake tattaredashi ya hanata hakan sbd kada ta tinzirasa aikata abinda baiyi niya ba akanta.
Sayd ne ya isa garesa Shima zai kamasa AZIZ din ya miqe Yana sake dafe kirjinsa yabar gurin baya ganin gabansa ya nufi stairs yana dakatar da kowa daga binsa.
Kallansa sukeyi cikeda kulawa da faduwan gaban kada ya fado sbd yanda baya gani harya haye saman ya shige palonsa ya rufe kofar.
Yana shiga suka fara jin qarar fashewan kaya da karfin gaske tareda glasses.
Da sauri Falaq ta yunqura zata bisa saman Sayd ya riqeta yana rungumeta ta fasa kuka tana cewa
"Daddy na zai sake illata Kansa,
Yana cikin qunci da damuwa,
Banason inga Daddyna a cikin irin wannan yanayin Ya Allah ka basa lafiya ka kawo nutsuwa da kwanciyar hankali a rayuwarsa"
Mama zubewa tayi qasa tana dafe kanta cikin hawaye da baqin ciki halin data saka AZIZ din da kuma tsananin tsanar Zaadens da Nicky dama duk Wanda yake rayuwar AZIZ din bayan ita.
Zaadens da duk abinda yake faruwa suna ji shiru sukai suma zuciyoyinsu a tafashe sbd tana sake tabbata dai Umma Fatima mahaifiyar AZIZ LIMBA ce,
Babu Wanda yayi farin ciki ko misqala zarratin da hakan,
Basa kaunar abinda duk zai sake hadasu da LIMBA,
Basa kaunarsa basa kaunar zuriarsa basa kaunar duk wani ma me kaunarsa tayaya yanzu kwatsam zaa ce Ummah itace uwar data haifesa?
Babu ruwansu da hakan tinda dai watsi yayi da ita suka samu suka tattala suka kaunata suka bata sunansu dan haka ba gudu ba ja da baya bazasu taba basa ita ba karshenta ma tana tashi tattarawa zasuyi su tafiyarsu da ita idan ma Yana ikirarin mahaifiyarsa ce to ai mijinta a yanzu yafisa iko da ita zasu nuna masa power da igiyoyin aure yake dashi ya gani ganin idonsa.
#MAMUH
#ZAADENS
#LIMBAS
07019691719*_KALBIM_*
Mamuhgee
Book 2
Chapter 41
Jannah da sautin komai itama yake sauka a kunnenta rufe idanuwanta tayi tana jin zuciyarta kaman zata dena bugawa sbd tausayin AZIZ da jin ciwonsa cikin ranta,
Yana tsananin buqatanta ayanzu dayake cikin mummunan halin ciwonsa da duk saiya raunana Kansa rauni me Muni ma kila batareda kowa ya rungumesa ba ya basa sassauci.
Kofa ta kalla da idanuwanta da sukai ja itama tana Sanin acikin familynta kowannensu a yanzu qiyayyar AZIZ ta kere sonta a zukatansu ta yanda zasu iya illatata idan ta zabi zuwa garesa dan basa kulawa da sassaucin dayake nema.
Har karfe 10 na safe gidan babu motsin kowa bare ayi maganar breakfast sbd kowa na cikin damuwa ga Umma har lokacin bata tashi ba.
Me gidan kuwa kwata kwata duk zaman jiran da kowa keyi na saukowansa babu Wanda ya sake jin ko motsinsa.
Fatma da Amina ne a kitchen da Sisi sukai aikin abincin rana ga na safen ma baa ci ba,
Karfe 2 na rana duka Zaadens suka fice sallah tareda Sayd Wanda yake tareda su jiran tashin Umman wadda daga qarshe bayan sun kira doctor ya sanar musu tashinta suna sakaran ba kusa ba sbd hayaqin ya shiga lungs nata sosai ga kuma shock da suke tinanin ta shiga dan hakanne ma kowa ya samu damar matsawa zuwa fita.
Sayd ne cikin mutuntawa ya gabatar musu da lafiyayyun bedrooms dake palon qasa na bangaren kofar gaba bana qasan su Mama ba,
4 bedrooms ne a qasan Wanda Dad daya Jannah da fatma daya sai Maheer daya Ammar da Garba daya sbd Ammar din ya saba da yanda Garba ke kulawa dashi.
Basuda niya ko raayin cigaba da zama a 4&4 kwata kwata a yanzu ko me zai faru tafiya zasuyi Amma zasu jira tashi Umma dole Wanda hakan ne kadai ya sakasu karban dakunan.
Shigewa sukai dan wanka daga qaurin wutar da suke ta yi.
Lafiyayyun bedrooms ne masu komai da komai da hutu yake buqata ko beddings din da decos din are all classy dan haka ba bata lokaci sukai wanka suka fita sallah.
Suna dawowa anan palon Fatma da Amina suka kawo abincinsu suka jera musu a dining da duk abin buqata.
Jannah kuwa anan dakin Fatma ta kawo mata abinci ta tirsasa taci daqyar ta Sha maganin kanta dake tsananin ciwo tai sallah.
A inda tayi wanka anan wahalallen bacci ya dauketa se yamma ta farka da sauri ta nufi toilet tayo wanka ta fito daure da sabbin towels da Amina ta kawo daga store ta jere a dakin Umman Harma da dakinsu sbd Umarni da sabuwar doka da odar da Sayd ya bawa duka maaikatan gidan akan Zaadens Musamman Ummah da Jannah Wadda a yanzu babu abinda ya hada suna bare matsayinta da kowa a gidan.
Hijab ta saka dogo har qasa ta tayarda sallah a natse jikinta a sanyaye.
Tana idarwa ta miqe tana zare hijab din jikinta tana tinanin inda zata Samu kayan sakawa sbd kayansu gabaki daya sun kone.
Kofar dakin aka bude kai tsaye cikin nutsuwa da kamewa.
Juyowa tayi da sauri tana nufar hijabinta taji an rufe dakin ahankali cikin nutsuwa da sanyi.
Qamshinsa