Showing 18001 words to 21000 words out of 150681 words

Chapter 7 - Kalbim Book 2 Complete Hausa Novel

Mamuhgee   

23 Sep 2025

9092

ta sauke ahankali jiki a sanyaye ta miqe tsaye ta nufi kofar palon ta miqa hannu ta bude ahankali ya shiga.

Kai tsaye bedroom dinsa zata nufa sai gashi ya bude kofar dakin a natse ya fito sanyeda jallabiya black me kyau ta kalli fuskansa ta sauke ajiyan zuciya bata ce komaiba ta kama hannunsa suka zauna a kujera ta kwantar da kanta gefen kafadansa tana bude baki ahankali ta furta

"I love you Daddy"

Lumshe idanuwansa yayi ahankali tareda bude baki daqyar yace

"Thank you for being here Falaq"

Haka ta zauna gurinsa ta tayasa zaman harya qarasa dawowa normal dinsa tukuna ta fice ta basa damar sallar magrib itama taje tayi tata.

Bai fito cin abincin dare ba dan haka babu Wanda ya gansa sai washe gari karfe goma da mintina ya fito a kame cikin navy blue Armani suit da Prada shades black a fuskansa.

A duk lokacinda Mama ta kalli AZIZ alfahari takeyi kai tsaye tareda godiyan Allah data kasance itace uwarsa sbd babu uwar da zata haifi da kamarsa bataiwa Allah godia Tai kuma alfahari da abinta ba dan haka a kowace sallarta bata dena yiwa FATIMA adduar hasken kabari ba idan kuma tana raye Allah ya bayyanar musu da ita sbd kaunarta da Fatima a jikinsu take tana fatan Allah ya hadasu a duniyar nan kafin Allah ya dauki ranta.

Falaq ma cikeda tsananin son mahaifinta tace

"Good morning Besty"

Kallanta yayi cikeda kauna yace

"Morning my precious"

Sayd hannu ya bata suka gaisa tana cewa

"Barka da fitowa our ranka ya dade"

Dariya yayi Yana matse hannunta har saida tayi Yar kara AZIZ yayi masa wani kallan daya sakasa sakinta Yana Yar dariya yace

"Dan duba maka lafiyanta nayi Sir"

Mama ce ta amsa gaisuwarsu a tare fuskanta a sake itama cikeda kaunarsu.

Fara breakfast din sukai AZIZ black lemon tea yasha da shawarma bread da akai toasting da egg.

Yana gamawa tissue ya dauka ya goge bakinsa ya dago ya kalli Mama a natse cikeda girmamawa yace

"Next week ne tafiyanku Nigeria kowa ya shirya komai zai kammala na tafiyan nan da 5days me inshallah
Idan akwai buqtaan da kowa keso Sayd zai kawo raw cash gida"

Ajiye tissue din hannunsa yayi zai miqe Mama ta ajiye spoon din hannunta fuskanta na sauyawa gabaki daya ta kira sunansa kai tsaye wanda hakan ya sakasa fasa miqewa Yana dagowa ya kalleta a natse kafin ya dauke idanuwansa cikin girmamawa.

Tsit table din yayi gashi Allah yasa Nicky bata gidan ta fita tinda safe sbd ita yaune jirginta da daddare zai daga zuwa Nigeria sbd zata rigasu isa.

Kallan Falaq Maman tayi kai tsaye tace

"Ki tashi zanyi magana da daddynki"

Dagowa Falaq tayi zata miqe tabar gurin mama ta kallesa fuskanta babu walwala ko kadan tace

"Idan harka gama yadda da amincewa akan buqatan Falaq na son komawa a duk inda tace tanaso to ka Sani ni kuma uwa a gareka wlh tallahi bazan taba binku ba zan koma kauye ne nayi zamana sbd bazai yiyu muna maida hannun agogo baya ba...

Dagowa yayi ahankali ya kalli Maman da idanuwansa da sukai ja take
ya bude baki zaiyi magana Maman ta daga masa hannu tana rage bayyanar fushinta da yanda ranta yake sake mummunan baci tace

"Har so nawa zaka biyewa duk abinda Falaq takeso?
Baka San ta girma bane tinda ta zama budurwa,
Ka yadda ka zubar da dukkanin tarin ayyuka da huldodinka tareda companies naka ka koma Nigeria sbd kawai Falaq ta fada hakan?

To idanma baka San dalilinta na son komawarba ni na sani bare kaima nasan ka Sani din dan haka tinda duka Kun gama yadda da komawar inason ka Sani daga ranar da muka sauka Nigeria wallahi tallahi duk wanda ya sake tada maganar Zaadens bare neman inda suke wlh ABDULAZIZ AYOUB LIMBA sedai ka sauya wata uwar bani ba dan har abada na cireka daga 'dana,
Ka Sani idan har zaka nema JANNAH ZAD da kanka ko saka wani nemanta ko dan kanka ko dan sbd Falaq na yafeka Ni sakina...."

Ahankali ya rufe idanuwansa da sukai wani irin jajir Yana hadiye wani irin abu daya danne kirjinsa me tsananin nauyi yana saka hannuwansa wata irin rawa me Muni Amma ya kanne ya jima shiru kafin ya bude idanuwansa Jan su na qaruwa ya bude baki ahankali cikin kamewa batareda yanayinsa ko daya ya bayyana ba anatse yace

"Allah ya huci zuciyarki Mama har abada babu Wanda zai iya taka umarninki a nan gidan"

Falaq dake tsaye bata qarasa fita ba tana jin hakan wasu zafafan hawaye masu tsananin zafi da ciwo suka gangaro mata tana dafe kirjinta sbd take wani radadi taji Yana gauraye kirjinta ta daddafa tabar gurin zuwa dakinta tana son fasa kuka Amma radadin wannan danyan hukuncin na mama data daure Daddy dashi yafi karfin kuka sbd zai yadda ya mutu da radadin rashin abinda zuciyarsa ke tsananin haukar so akan ya take umarnin Mam dan haka taji ciwon kirjinta na qaruwa ta rufe dakinta dan itama ta xabi ta mutun ma da ciwon ta huta da ganin halinda Daddynta zai shiga sbd girman wannan alkawarin.


Sayd ma wani irin zufa ne me tsananin gaske ya feso masa sbd tsananin tashin hankali da shock din maganar Maman Wadda ta gama kashe AZIZ dinne da kanta dan har abada kuma ta rasasa sbd bazai taba komawa AZIZ LIMBA dinta ba.

Miqewa AZIZ din yayi yai mata sai anjima ya fice Sayd na miqewa zufa na sake jiqasa yabi bayansa.

Kai tsaye mota ya nufa Sayd yayi saurin bude masa ya shiga ya rufe masa ya zagaya ya bude motar ya shiga ya tayar suka bar gidan.

Sanin waye AZIZ din har suka kai office baice komaiba motar tsit take.

Parking yayi ahankali ya bude ya fice yabarsa a motar ya tsaya daga waje tsawon mintina masu dan tsayi kafin AZIZ din ya bude ya fito bayan ya hadiye dukkanin emotions nasa.

Kai tsaye ciki suka nufa maaikata tako ina suna fitowa gaidasa yana amsawa da kai ko hannu kawai sbd fuskansa dake a kame ba fuska ko kadan.
#MAMUH
#BEST LOVE STORY
#HOT ROMANCE
#JANNAH ZAD LIMBA
#AZIZ LIMBA
#ZAADENS
#LIMBAS


ZAFAFA BIYAR

KALBIM 500
Mamuhgee

KIRJIN ME HANKALI 500
Miss Xoxo

ADUNIYATA 500
Huguma

AJIYA A DUHU 500
Billyn Abdul

09033181070
09032345899

*_KALBIM_*
Mamuhgee

Book 2
Chapter 11

A lokacinda Mama tariga da tasan AZIZ zai iya komai Amma bazai taba iya take umarninta ba dan haka ayau ta samu nutsuwa da kwanciyar hankalin data rasa na tsawon shekaru akan dawowan Zaadens rayuwarsu sbd tana jin shakka da tsoron girman abinda take gani a idanuwan AZIZ gameda Jannah Zad wadda babu alkhairi shigowanta rayuwarsu hakama sbd itane akaiwa tata 'yar kisan gillar da har abada bazata iya mantawa ba.

A yanzu data daure AZIZ da kalamanta, daurin da har abada tasan bazai taba kuncewaba koda Fatima zata dawo duniya kuwa bazata iya warwaresa ba sbd yanda tasan girmanta a zuciya da rayuwarsa.

Hankalinta ya kwanta zuciyarta ta samu nutsuwa da rashin fargaban sauka Nigeria ta zauna dan tasan maganar Zaadens kuma ta rufu kenan har abada tinda Allah ma ya raba duniyarsu ta tasu sbd a yanzu duk inda suke akwai nisan da babu cikewa har abada tsakaninsu.

Babu wani abu daya rage mata a rayuwar AZIZ dinta bayan aurensa da Nicky ta nunawa duniya tayi sirikar da babu gurbataccen jini a jikinta,

Zatayiwa AZIZ auren da a duk inda Zaadens suke zasu gani a labarai Susan sun jima da rufe babinsu na shafe tahirin auren yarsu a LIMBAs a yanzu 'yar da aka kashe mata tata Yar sbd gata da nuna karfin ikon dukiya ba kowa bace face bazawara a gabansu yanzu.

Gidan a ranar tsit babu wani farin ciki ko walwala damuwa ce me girman gaske a zukatansu Musamman Falaq da gabaki daya duniyarta take ganin ta juye a lokaci daya dan badan Mama itace mahaifiyar data haifi Daddynta ba data gama tsanarta ayau Amma dayake tana girmama duk abinda mahaifinta keso dan haka take hana zuciyarta tsanarta sbd daddy na kaunar mahaifiyarsa.

Mama kadai ce a gidan take farin ciki tana zuciyarta kalau sbd matsalarta da tsoronta ya kau dan haka batada sauran fargaba hankalinta kwance saima hidimarta takeyi itada Nicky da zata wuce hakama acan Nigeria tariga ta kira Sayd ta basa umarni ayau din kafin isar Nicky tini aka tanadar mata driver lafiyayye me xamanta tareda sabuwar mota fitinanniyar sabuwar mota daidai raayinta aka kuma sanar da securities da maaikatan gidan isowanta kafin su.

Saida ya sanar da AZIZ umarnin Maman Wanda ko sauraron duka zancen baya buqatan yi yace yayi duk abinda Maman tace kawai baya buqatan ji.

Karfe 7 na dare Mama da kanta ta fito ta saka Falaq binsu dole suka raka Nicky airport tareda Dr Nico Wanda yake rungume da Nicky din kwata kwata bayason rabuwa da ita sbd yasan zata saka kanta ne a motar da zata fito da dana Sani kila da damuwa sbd baisan gaba ba Amma bayajin akwai filin da kowace irin mace zata samu a zuciyar AZIZ LIMBA dan yasan komai na LIMBA ciki da waje tinda shine likitansa.

Dagewan Nicky din ya saka yabarta ta gwada koda akwai damar samun soyayyar AZIZ din tinda zai iya kaunarta ya bata dama ko dan sbd shi.

Mama ma kamar baby haka ta ringa tarairayan Nicky din tana mata fatan sauka Lfy da fadan ta kula da kanta sosai akwai isasun masu aiki da aka zuba kome takeso zasu mata.

Lafewa jikin Maman Nicky tayi tana sake nuna mata irin kewanta da zatai sbd jinta takeyi kaman mahaifiyar data haifeta sbd tsananin son datakewa 'danta ya shafeta.

Falaq Nicky din ta rungume itama tareda sakar mata kiss a tsakiyar kai tana cewa

"I will be waiting for you guys"

Numfashi Falaq ta sake tareda gyada Kai ahankali tana furta "safe landing" a taqaice.

"Thanks my LIMBAs precious" inji Nicky tana sake rungume brothernta tana jin tsananin sonsa da kaunarsa na saka idanuwanta cikowa da hawaye kafin ta sakesa it sake rungume Mama kafin ta juya ta wuce suna mata bye bye.

Suna barin airport din ba jimawa jirginsu Nicky din ya tashi suma zuwa Nigeria.


****Adaidai wannan lokacin kuma Jannah ce kwance jikin Ummanta idanuwanta rufe jikinta a sanyaye tana jin kewan Umman na ciko mata da kwalla a ido sbd ta dauki lokaci me tsayi bata kwanta jikin Ummanta b sbd yanayin jikinta sai yau din Umman da kanta taxo ta janyota ta kwantar da ita jikinta tana Shafa mata kai cikeda wata irin kauna da babu sirki itama tayi tsananin kewan Jannah din dan haka yau ta janyota da kanta.

Hawaye ne masu dumi suka gangaro idanuwan Jannah ahankali sbd kewan mutum da har abada bazata taba denawa ba bakuma zata taba dena jin radadi da ciwon rashinsu ba wato Miminta da Wanda bai mutu ba Amma a gurinta a zuciya da rayuwarta ya mutu.

Ganin hawayen dake gangarowa idanuwan Jannah ya saka Ummah ma idanuwanta cikowa da hawaye kawai suna gangarowa batareda tasan daliliba Amma dai tasan a rayuwarta idan har zataga hawaye idanuwan Jannah to itama nata idanuwan basu kasa zubo da hawayen ba hakama duk duniya batasan tsana ba amma da zataga abinda yake saka Jannah dinta kuka to zata tsanesa da dukkanin zuciya da ruhinta.

Saukan hawayen Umman akan gefen fuskanta ya sakata bude idanuwanta ahankali ta zubawa Ummah idanuwanta tanajin kaunar da batasan ta inda take fitowa ba ga Umman,

Ta rasa wace irin kauna me tsananin tsafta da girma takewa Ummah wadda bata jinin komai da itaba Amma tanajin kaunarta har jininta kamar yanda ta rasa wace irin kauna Ummah ke mata.

Sharewa Umman hawaye tayi tana komawa ta kwanta a kafafunta tareda lumshe ido wannan karon baccin me dadi da nutsuwa tayi a jikin nata.


Se dare sosai ta farka taga Umman na dakin nasu har lokacin wato bata tafi gurin Dad ba Wanda gabaki daya yake cikin damuwar ko ta samu tayi baccin.

Rufa tai mata tareda addua kafin ita kuma ta miqe ta fada toilet tayo fitsari tayi alwala ta fito tafara nafilolin dare ta jima tana adduoi kafin ta miqe taje ta kwanta take bacci me nutsuwa ya dauketa.


Washe gari tinda asuba aka tada Ammar akai masa sauyin aiki aka basa key din lafiyayyar sabuwar motar BMW iX tareda suna da hoton Nicky Managern kamfanin 4&4 ya kawo masa yace yaje airport ya dauko matar gidan.

Baiji komaiba ya amshi sauyin aikin cikeda girmamawa ya fice daga gidan ya kama hanyar airport Yana kallan gari cikin sanyi da nutsuwa.


Yana isa babu bata lokaci ko wahala ya samu damar ganinta ya zuba mata ido kafin ta iso gurinsa Yana kallan halfcast din macen da kana ganinta bazakai mata tinanin musulma kai tsaye ba duk da doguwar Arabian gown ce jikinta dark brown Amma yanayin yanda ta Dora gyaralen ne fiyeda rabin gashinta a fili.

Dauke idanuwansa yayi daga kanta Yana qarasowa gurinta cikin nutsuwa yace

"Welcome"

Kallansa tayi kafin tace komai ganin sunan 4&4 baro baro dake jikin shirt dinsa me kyau da jeans ya sakata kai tsaye sanin drivernta ne ya iso.

Fasa amsa gaisuwarsa tayi ta miqa masa kayanta wanda ya karba ya tura har mota ya saka bayan ya bude mata motar ta shiga ya zagaya ya shiga ya tayar batareda ya sake furta komaiba har suka isa gida.

Kallo daya tayiwa gaban 4&4 mansion din ta tsayar da idanuwanta akan sunan sbd bata dauka har gidan da AZIZ LIMBA zai zauna ba a qasarsa bazai saka masa sunansa ba sedai numbers da haryanzu basuda maanar komai.

Cikeda girmamawa dukkanin securities din gidan suka taso suka mata barka sauka aka bude gate din suka shige da motar.

Maheer ne da Dad suka bude gate din na biyu a tare Wanda ya saka zuciyar Ammar dake kallansu wani irin ciwo da radadin ganinsu suna bude kofar gidan wani.

Shigowa yayi yai parking ya fito ya zagayo ya bude mata kofar suma su Dad din cikeda sosuwan zuciya suka sauke idanuwansu daga kallansa.

Fitowa tayi su madam Sisi na fitowa tarbanta cikeda girmamawa aka fara mata barka da zuwa duka cikin turanci sbd ba hausarta bata irin karfin nan ba dik da tanaji sbd tsawon shekara biyun datai dasu mama ta koya sosai.

Ciki akai da kayanta tana tafe bayansu kafin ta dakata ta kalli Ammar ta ciro 100 dollar ta miqa masa tace ya nemo mata layin Nigeria me kyau.

Karba yayi Yana cewa ok.

Lafiyayyan sitting room din farko data fara sako kafarta ta sake sauke ajiyan zuciya akusan Karo na biyar sbd ta tabbatarda taxo inda zatai rayuwa irin Wadda takeso sbd duka luxuries na rayuwar duniya babu Wanda babu a 4&4 mansion dan haka AZIZ LIMBA kawai ya rage mata ta mallaka Wanda a cikin gidan nan takeson tafara Haifa masa yayan da zasu sauya rayuwarsa gabaki daya su bata lasisin zamowa rayuwarsa har abada.

Lafiyayyan bedroom din dayake hade da wani nutsatsen palo aka kai kayanta Wanda tini aka gyaresa aka kunna ac da qamshi da komai hatta su towels da toiletries an siyo an jeresu tas.

Wanka kai tsaye ta fara shiga tana fitowa ta saka riga da wandon bacci sallarma da kyar tayi ta haye gado tareda kashe hasken dakin t shige duvet bacci me nauyi ya dauketa.

Fatma ce taxo ta duba tana bacci dan haka baa sake zuwa ba sbd kada a dameta saida ta tashi dan kanta karfe biyun rana kafin ta sake wanka ta fito sanyeda doguwar riga mara hannu da qaramar scarf na Versace akanta tana fidda qamshi ahankali.

Madam Sisi ce da kanta tayi serving dinta abinci lafiyayye varieties taci tana gamawa ta koma palo daidai nan Jannah ta sako kai a natse cikin rashin hayaniya sanye da Doguwar riga boubou daidai jikinta da hula hannunta riqe da jakar MTN da Ammar ya bata ta kawo mata.

Muryan Jannah dince data gaidata cikin fluent English dinta dayake bayyanarda kai tsaye su din a turai aka haifesu kuma suka taso...

Hakanne ya saka Nicky dago idanuwanta da sauri ta sauke akan Jannah din tareda zubawa fuskanta ido tana kallanta batareda ta iya dauke idanuwanta akantaba.

Jannah dinma dago idanuwanta tayi jin shiru ta sake magana a natse tana miqo jakar tareda tarin canjin kudin dake cikin jakar da layin yake ciki.

Hannu Nicky ta miqa ta karba Jannah din ta juya zata fice ta bude baki tace ta dawo ta saka mata layin sbd bazata iyaba.

Dawowa Jannah tayi ta karba tareda karban wayar ta saka mata ta juya t fice zuwa aikinta.

Da daddare Jannah ce tayi serving dinta abinci tanaci tana waya da mama hankali kwance batareda jin kadaici ko wani abin ba.



Washe gari kai tsaye tace aikin Jannah takeso a komai sbd tafi iliminda zata ringa fahimtar abinda takeso dan haka Jannah ce ta koma me aikinta komai bata iyayi sai anyi mata.

Nicky haka kawai ilimi da kyan Jannah tareda wani irin class datake dashi Wanda a jininta yake sai take ganin kamar girman kai Jannah din ke nunawa ita kuma ta tsani Wanda yake qasanta yafita kowane irin abu dan haka tanason raba Jannah da wannan nutsuwar datake dashi dan haka duka ayyukanta n wahala ne Jannah keyi gashi Jannah din bata wani cika magana ba komai tace tayi zatace ok shikenan.

Ammar ma ta nasa bangaren aikin yawon wahala ne sukeyi sosai dan kullum sai anfuta da ita gashi batasan koina b shine me kaita harta gama shigarda report na zuwanta zatai hutun satika kafin ta fara zuwa aikin.

A hakan sati ya zagayo gabaki daya Nicky ta rikita gidan da murnan zuwan sauran familyn gidan da zasu iso a Daren ranar amma banda mai gidan a yanda suka ji.

Sabbin motoci aka kawo da wasu drivers din daga kamfani na mahaifiyarsa da 'yarsa dan haka karfe 1 jirginsu zai suka na dare dan haka duka motocin suna airport tin 11 na dare dan daukansu zuwa gida.
#MAMUH
#JANNAH ZAD
#AYSHNICKY
#ZAADENS
#LIMBAS

ZAFAFA BIYAR

KALBIM 500
Mamuhgee

KIRJIN ME HANKALI 500
Miss Xoxo

ADUNIYATA 500
Huguma

AJIYA A DUHU 500
Billyn Abdul

09033181070
09032345899*_KALBIM_*
Mamuhgee

Book 2
Chapter 12

Sai dare sosai motocin da suka dauko su Mama daga airport suka iso bakin main gate na 4&4 mansion aka bude musu cikeda girmamawa da farin cikin zuwansu motocin suka shige tin kafin su iso second gate Maheer da Dad suka wangale gate din suna rabewa gefensa suna musu hannu alaman barka da isowa Wanda babu Wanda ma ya lura dasu a cikin motocin harsuka wuce kurya sukai parking.

Madam Sisi da Nicky ne suka fito suka tarbesu suna musu barka da zuwa kafin sukai ciki dasu kowannensu a tsananin gajiye dan haka babu abinda suka tsaya sukai ciki.

Suna wucewa ciki su Maheer na gama rufe gate

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login