Showing 66001 words to 69000 words out of 150681 words

Chapter 23 - Kalbim Book 2 Complete Hausa Novel

Mamuhgee   

23 Sep 2025

9077

idanuwanta suka kusa rufewa akan idonta Dad ya sako kai yana nufota da sauri Ammar kuwa daukanta yayi gabaki dayanta suna kokarin fitowa garba ya fado ya dauki fatma Shima.

Suna fitowa Maheer ya kwace da karfe Yana nufosu ya karbi Umman sbd Ammar da dad din dake neman xubewa a qasa.

Yana karbanta Jannah dake ihun Kiran sunanta ya nufa ta fizgo da gudu itama tana zubewa gaban Ummar da Maheer ya kwantar a qasa gaban ABDULAZIZ AY LIMBA Wanda yayi mutuwar tsaye idanuwansa kafe akan fuskar dake gabansa kwance.
#MAMUH
07019691719*_KALBIM_*
Mamuhgee

Book 2
Chapter 38

*_SHOP WITH ME BY RANO_*
08030811300
Kina neman in da zaki samun kayan yara classy kaya na yan gayu at a very affordable price? Ko kina son fara kasuwancin kayan yara amma baki da jarin da zaki saro kayan? Nesa ta zo kusa, kiyi joining community din nan muna saka kaya masu kyau available da inganci a farashi me sauki da zaki dauka ki tallata har ki samu naki kema.
Burinmu shine kowacce mace ta samu sanaar da zata dogara da kanta.

*************
Wani irin haske idanuwansa suka cike dashi jinsa na daukewa daga sautin komai saina ihun Kiran sunan da Jannah da ahalinta ke yi,

Dumm kansa yayi Yana kasa motsa ko yatsa daya daga jikinsa ya bude bakinsa ahankali cikin wani irin sauti da slow yace

"UMMAH"

Falaq ce datake isowa gurinsa da gudu tana kokarin riqesa cikeda tsoron wutar ya tureta da karfi Yana ficewa hayyacinsa gabaki daya komai na jikinsa na tsananin daukan rawa ya isa gabanta da karfin gaske yana ture Maheer tareda kowannensu ya cakumota da karfi yana kallan fuskanta cikin karfin gaske yace

"UMMAH, UMMAH FATIMA.....

Mama da gabaki daya imaninta yake akan wutar batareda tasan nafito da Umman ba jin saukar muryansa a kunnuwanta ya amabaci Fatiman ya sakata juyowa da karfin gaske a rikice gabanta na mummunan faduwan data saka jikinta daukan rawa idanuwanta na sauyawa gabaki daya.

Ture Nicky da Madam Sisi tayi da karfi daga gabanta tana nufar inda AZIZ din yake kafafunta na hardewa ta kife qasa da karfi,

Da rarrafe jikinta na rawa ta iso gurin tana zubawa fuskanta Fatima idanuwanta dake cikowa da tsananin hawaye zuciyarta na cewa

"Fatima sai da kikai nasara akaina,
Fatima saida kika bayyana gaban AZIZ,
Fatima kin kasa tafiya ki barni da AZIZ sbd nice na cancanci zama uwarsa Ni danake da cikakken hankali,
Fatima bazaki iya rabani da AZIZ ba sbd na riga na zama uwar da bazai taba iya sauyawaba...
Fatima kin lalata komai."

Nicky ce ta iso da sauri gurin Maman ta kamota Zata tayar Maman da babu karfin komai a jikinta tanajin kaman taje da gudu ta fada wutar ta kone ta huta akan yanda zata iya fuskantar AZIZ akan bayyanar Fatima gidan.

AZIZ kuwa sake dago Umman yayi gabaki dayanta da karfi yana sake ture duk Wanda ya kusantota ya sake ambatar sunanta da karfin gasken daya saka idanuwanta budewa a wahalce suka koma suka rufe tana qarasa somewa gabaki daya.

Dad ne da babu karfi sosai a jikinsa sbd zafi da hayaqin wutar daya dakesu,

Ganin irin girgiza da riqon da AZIZ yayi mata Yana tare kowa da isa gareta ya sakasa tahowa ya ture AZIZ din da karfi dan ya saketa sedai ko gezau sbd ba qaramin riqo yayi mata ba gabaki daya ya fice hayyacinsa.

Ammar ma turesa ya hau yi jin Yana kiranta da Umman da suke kiranta Wanda duk a tininsu sbd Jannah ne yake kiranta hakan,

Maheer ma banbareta daga hannunsa suka hau kokarin yi suna kasawa,

Su uku suka tarar masa suna kokarin cireta Amma hakan ya gagara,

Wasu hawaye masu tsananin zafi da gudu ne suka fara gangarowa daga idanuwansa ya dagota da karfi ya rungumeta a kirjinsa qamqam Yana fasa kuka a gaban kowa me karfi da tsananin tsima zuciya sbd kukane da duk duniya babu Wanda ya taba ji yayi,

Cikin kukan ya sake ambatar sunanta da "FATIMAN ABDULAZIZ DA UMMITAH......
UMMAH FATIMA...

Cak Jannah da duka Zaadens suka tsaya daga kokuwar da sukeyi dashi dan basu hakura ba sai ya saketa,

Fatiman daya ambata ne ta AZIZ da Ummitah ya sakasu kallan Umman da wani irin sauri da tashin hankali me tsananin gaske wadda sukasan sunanta Fatima a bakin Mama,

Dad ne da Ammar a lokaci daya suka juya gurin Mama suka kalleta wadda ta rintse idanuwanta da sukai jajir hawaye na cikowa a cikinsu.

Maheer kuwa kai tsaye fuskan Umman tasu ya zubawa idanuwa jikinsa na daukan tsananin rawa sai kawai a take kamannin AZIZ LIMBA suka ringa bayyanar masa akan fuskan Umman da basu taba tsayawa suka lura da hakan ba sbd abune da ko a mafarkin sun haukace basu taba kawosa ba.

Jannah kuwa qanqancewa idanuwanta sukai cikeda yanayin da batasan ma ya zata fassaraba ta rarrafa gurinsa da sauri ta kamo fuskansa dake cikin wuyan Umman Yana kuka sosai..

Qwace fuskansa yayi da karfi yana sake maidawa wuyan mahaifiyarsa yana jin kaman yana motsi ba daidaiba zata bace daga gabansa.

Sake riqo fuskansa Jannah tayi da sauri hawaye na bin fuskanta muryanta na rawar tashin hankali tace

"Ummanah ce....

Girgiza kai yayi da karfin gaske kaman qaramin yaro jikinsa na sake daukan rawa yanayinsa na tsananta ya sake qanqame Umman yace

"Umman AZIZ ce,
Umman data haifi ABDULAZIZ ce,
Umman data haifawa AZIZ Ummitah ce,
Ummanah ce,
Rayuwata ce ita ba Umman kowa bace bazata....

Rungume Kansa Jannah tayi tana fasa kukan ganin yanda haukansa gabaki daya ta bayyana a gaban kowa hakama Umman na tsananin buqtaan taimakon gaggawa tace

"Umman AZIZ ce,Fatiman AZIZ ce,
Ummanka ce babu Wanda zai sauya hakan amma tana buqatan taimakon gaggawa ka bari a tafi da ita AZIZ"

Yana jin hakan ya dago da sauri Yana sakin Umman daga jikinsa ya miqe jikinsa na rawa ya dauketa sukutum gabaki dayanta yana barin gurin da ita da gudun gaske Yana qwala Kiran Sayd Wanda tini ya kira likitoci kusan uku duk suna hanya gashi basuda nisa.

Gabaki daya duk Wanda yake gurin mutuwar tsaye ce ta kamasu Musamman Nicky datake jijjiga sbd a gban idonta ko yanzu aikinta ya lalace lalacewan da kila dama irin wannan zatai wuyan samu,

Bata yadda da AZIZ nada wata uwar ba bayan Mama sbd tasan dai koma wacece wannan din Mama dai itace ta haifesa dan haka kallan Maman tayi jikinta na sake rawa da jijjiga ta bude baki zatai magana Mama datake jin jininta na qonewa batasan lokacinda ta daga hannu ta sauke mata wani lafiyayyan mari ba tana mata kallan tsananin baqin cikin shigowanta rayuwarta ma gabaki daya.

A rikice Nicky da rabin hayyacinta yabar jikinta sbd kanta daya motsa ta kalli Maman zatai magana Maman ta katseta cikin mugun yanayin na tafarfasa da cewa

"D farko bansan wace kaddarar takaini karbanki ba Sedai a yanzu na San mummunan kaddara ce sbd babu alkhairi ko daya a tattare dake,
Duk abinda kika sakawa hannu saiya lalace ya zama mugun Abu,

Kinsan ayau me kikayi?
Kinsan me kika janyo da wannan aikin da kika lalata mana?
A tinaninki zaki kashe matsalolinki ne a cikin wutar da kika Cinna?
To ki Sani dukkanin manyan matsalolin da suke kwance ne kika tayar mana Wanda wutar zata cinyemu,
Babbar matsalar dataci uwar tasu Zaadens ce kika tado mana wadda a yanzu sedai kowa yayi ta Kansa dan kuwa a yanzu babu sauki ko kalilan a lamarinmu sai kuka da baqin ciki."

Nicky data kasa yadda da faduwa cikin tafasar zuciya tace

"Mama bazan taba yadda da faduwa ba akan Zaadens,
Bazan taba barin.....

A tsananin fusace da tashin hankali Mama tace

"Kin San waye Fatima?
Kinsan waye mahaukaciyar Zaadens da kike fada koyaushe?
Kina ganin yanda suke tsananin sonta take sonsu??
To itace Asalin mahaifiyar data dauki cikin AZIZ LIMBA ta kawosa duniya,
Itace macen datafi kowace mace a duniyarsa da babu kamarta kuka babu Wanda zai iya cika gurinta a ransa har abada,
Akan Fatima AZIZ zai iya fito na fito da kowa,
Akanta ne idan ba mafita muka samo ba AZIZ LIMBA ya gama zama bawan Zaadens har abada sbd Fatiman da kanta ta zama Zaadens sbd auren Dzad ne a kanta....

Baya Nicky tayi tana faduwa qasa jikinta na tsananin rawa da shiga mummunan tashin hankalin da bata saka masa rana ba.

Mama ma datake jin tana neman haukacewa juyawa tayi ko gabanta bata gani tabi bayan AZIZ da Zaadens da sukai ciki tin dazu acikin tashin hankali.

Palo AZIZ ya nufa da Umman ko gabansa baya gani kaman zai kife suna biye dashi dukkansu suma kaman zasu kife din sbd basuda wata niya ko qarama ta daga masa kafa akan Fatiman dan haka wutarsu a riqe take.

Jannah ce take kwashe pillows din kujera Ammar da baida hakuri ya fizgosu gabaki daya ya watsar dasu qasa AZIZ ya kwantar da ita Yana kasa dauke idanuwansa akanta har lokacin jikinsa rawa yakeyi sosai kansa kaman zai buga hakama ya hana kowa tabata a cikin rashin hayyacinsa dayake ciki sbd gabaki daya duk Wanda yake gurin yasan ba AZIZ LIMBA bane a gurin wani AZIZ LIMBA dinne da basu sani ba dan haka Sayd daya san meyake faruwa yace subi komai a sannu idan ba hakan ba komai zai lalace dan AZIZ din yanzu baya Kansa.

Falaq da gabaki daya hankalinta yayi mummunan tashin da tsoro ya ciketa sbd ayau Daddynta ya tureta sa karfi har sai dataji rauni,
Kuka takeyi sosai a jikin fiddausi da itama ta dade da Sanin Mama ba itace asalin mahaifiyar AZIZ LIMBA ba to Amma shock dinta shine babu Wanda ya santa daga AZIZ din sai Mama kuma Mama ta dade da Sanin Umman na gidan duka lokacin nan tayi shiru Harma suke kiranta mahaukciya
To kadai Maman bata gane Umman bane??

Jannah ma daya hanata motsowa kusa dashi Sam jikin Dad dinta ta lafe tana tsiyayar hawaye zuciyarta cike fal da tsoron sabuwar kaddarar data bullo musu a yanzu na kasancewan Ummansu mahaifiyar AZIZ LIMBA Wanda tasan wlh komai AZIZ zai iya basu Amma bazai taba barinsu da mahaifiyarsa ba,

Zai durkusawa Zaadens qasa ya basu damar takasa Amma bazai taba basu Ummansa ba kaman yanda tasan Dad dinta zai rasa ransa da shi kadai ne ya rage masa Amma bazai rabu da Umman ba.

Hawaye masu tsananin zafi ne suka gangaro mata tanajin tsananin tausayin AZIZ din ganin yanda yake cikin rashin nutsuwansa da hankalinsa kwata kwata sbd ganin macen daya rasa tin Yana qanqaninsa,

Ya rasa kaunarta,ya rasa duminta,ya rasa kulawanta,ya rasa nutsuwar mahaifiyar,ya rasa walwala duk sbd rashin uwa mahaifiya,

Mama sunan uwa kawai take amsawa a garesa Amma babu shaquwa da kauna me zurfi da kusancin dayake tsananin buqata daga uwa shiyasa rayuwarsa take gabaki daya a baibai.

Maida idanuwanta tayi akan fuskan Umman ta kafeta da ido kaman bata taba ganinta ba kamanninta na bayyanar mata tanajin zuciyarta na narkewa sbd kaunar datake jin tanawa ummah me tsananin da babu sirki ta zuciyar Ummitah ce dake kirjinta da kuma kasancewarta uwar data haifi love of her life,
Uwar data haifi AZIZ LIMBA mutumin da bazata taba iya dena so ha har qarshen numfashinta.

Isowan likitoci ne ya saka AZIZ din miqewa tsaye Yana basu guri yana cewa kada su bari komai ya sameta zai basu komai na rayuwarsa.

Lafiyayyan bedroom din a cikin na palon aka maidata doctors din suka shiga.

Ana rufe dakin ya juyo idanuwansa jajir hannuwansa na rawa ya dago idanuwansa ya fara kallan Zaadens din daya bayan daya hawaye na ciko idanuwansa kafin ya tsayar da idanuwansa akan Jannah wadda take kallansa cikeda tsananin kauna tanajin kaman ta rage masa abinda yake ji a zuciyarsa na tsananin halinda baimasan yaya yakeji ba.

Shima kallanta yakeyi da dukkanin tsananin sonta da buqatanta hawayen idanuwansa na saukowa kan fuskansa...

Kasa riqe Kansa yayi ya iso inda take idanuwansa na rufewa ya janyota jikinsa ya rungume yana fasa kuka mara sauti Yana cewa

"Ummanah ta dawo gareni"

Hawayenta ne suka gangaro tana Manta kowa da komai ta rungumesa tana kokarin basa sassauci.

Dad da Maheer mutuwar tsaye sukai suna kallansu zuciyoyinsu na rawa da jijjiga,

Ammar da daman baya cikakken hayyacinsa bin bango yayi Yana fita waje sbd numfashinsa dayake sarkewa Yana neman rasa ransa yana fita waje y zube qasa wani irin kuka na zuwar masa Amma kirjinsa ya kasa dauka dan haka ya zube qasa yana dafe kirjinsa.

Mama dake tsaye itama mutuwar tsayen tayi sbd ganin sabon tashin hankali a gabanta AZIZ a jikin Jannah Yana kuka.
#MAMUH
#JAZIZ 2025
#LIMZAD 2025

07019691719*_KALBIM_*
Mamuhgee

Book 2
Chapter 39

*_SHOP WITH ME BY RANO_*
08030811300
Kina neman in da zaki samun kayan yara classy kaya na yan gayu at a very affordable price? Ko kina son fara kasuwancin kayan yara amma baki da jarin da zaki saro kayan? Nesa ta zo kusa, kiyi joining community din nan muna saka kaya masu kyau available da inganci a farashi me sauki da zaki dauka ki tallata har ki samu naki kema.
Burinmu shine kowacce mace ta samu sanaar da zata dogara da kanta.

***********
Qanqameta yakeyi kaman zai shige jikinta tamkar yaro qanqanin da baisan abinda zeyiba da neman sassauci a jikin wanda yake samun nutsuwa,

Sassaucin take kokarin basa ta hanyar sake basa daman rungumeta da kyau tana shafa bayansa duk da yafita tsayi sosai tana kokarin hana nata tashin hankalin kere nasa sbd duk yanda suke cikin tsananin shock da tashin hankalin me yake shirin tabbatar musu na cewan Ummansu itace Umman AZIZ LIMBA amma tasan nasa tashin hankalin da mummunan shock din ganin Matar daya shafe shekaru tin Yana yaro yana nema dole ya kere nasu.

Dad da tashin hankalin dayake ciki da kuma abinda idanuwansa ke gane masa zuciyarsa ta kasa dauka yana kokarin isa gurin Jannah ya fizgota Maheer da tasa zuciyan take radadi da bacin rai ya rigasa isa tareda kamo hannun Jannah ya janyota daga jikin AZIZ din da karfi Yana jefata gaban Dad dinsu daya dago ya kalleta da idanuwansa jajir zuciyarsa na sake shiga wani halin tsananin tsoro akan tashin hankalin d suke ciki.

Me AZIZ yake kokarin yi masa akan 'ya?
Shin bai gaji da wasa da zuciya da rayuwarta bane bayan duk abinda yayi mata ya kuma dankara mata saki?
Menene kuma sukai masa yanzu da zai sake lalata rayuwar Jannah ta hanyar kokarin dawo mata da sonsa,

Numfashi ya sauke me zafin gaske Yana kallan Jannah da fuskanta ke kallan qasa cikin tsananin tsoro da baqin cikin kasa riqe zuciyarta datai ta bari ta sakawa ahalinta shakku akan zuciyarta da zata iya sake jefasu wani masifar kaman farko data jefasu masifa akan son datake wa AZIZ LIMBA Wanda shine ya lalata komai.

Cikin sanyin jiki sbd damuwar dataci karfinsa Dad yace

"Kinsan me kikeyi Jannah?
Kinsan haramcin abinda kikeyi kuwa?
Karki manta ba aure tsakaninku a yanzu kuma babushi har abada sbd ba abu ne me yiyuwaba ba dan tamkar ma ya haramta ne dan mun haramta so yafi Miki kiyi gaggawar dawowa hayyacinki kafin ki saka raina mummunan baci"

Shiru tayi tana qasa da kanta tareda hadiye hawayenta da suka ciko idanuwanta tana janyewa gefe inda Maheer ke mata kallan mamaki dan kuwa kaman yanda Dad ya fada menene zai sake sakasu barin tabi raayinta akan duk Wanda takeso bayanma maganar aurenta da Ammar ta riga ta gama tsayuwa ba fashi har abada.

AZIZ da baya hayyacinsa cikakke baisan me suke yi ba bare fada sbd ya zube zaune a kujera dafe da kansa.

Tsit palon ya sake dauka kowa a tsaye da fargaba da tashin hankalin dake tsananta sbd farfadowan Ummah dake tattare da tabbatarda abubuwa da dama wanda zasu kawo sabon rikicewa a rayuwar kowa,

Shin da gaske mahaifiyar AZIZ LIMBA ce Ummansu shine tashin hankalin da Zaadens suke ciki Wanda idan hakan ta tabbata basajin zasu sake nasu matsayin a kanta tinda ta riga ta zama  mata kuma a uwa a Zaadens tsawon lokaci dan haka ba abu ne me yiyiwa ba kai tsaye su sake barin AZIZ LIMBA ya rabasu da abu me mahimmaci dan haka suke tsaye cikin rikici da tinani suna fatar ba hakan bane ya zamto sabanin tinani kawai aka samu da kamanni.

AZIZ LIMBA kuwa babban buri da tsananin buqatansa daya a yanzu kada wani abin ya samu Umman tukuna ta farfado ta kallesa ya samu kallan rahama daga idanuwan da sukafi kowane daraja a rayuwarsa,

Ummansa ko ya girma zata ganesa sbd kamanninsa da basu sauya ba,
Zata gane 'danta,jininta kuma hamma AbdulAziz dinta itada Ummitah koda kuwa tana cikin yanayi na gushewan hankali haryanxu.

Falaq ce data kasa isowa garesa tin dazu sbd tsoro ta daure ta iso ta zaune gefensa ahankali tareda kama hannunsa daya da duka hannuwanta biyu ta qanqame tana kwantawa jikinsa tace

"Daddy Ummansu Jan zata ji sauki ka kwantar da hankalinka dan Allah kaji"

Lumshe idanuwansa yayi ahankali Yana zagaye Falaq din da hannunsa daya ya rungumeta Yana sauke ajiyan zuciya ahankali batareda ya iya cewa komaiba.

Mama da kiris zuciyarta ke jira ta buga hakama jikinta gabaki daya kaman zai kama da wuta sbd zafin tashin hankalin daya gama kameta,

Tsoro da tashin hankalinta daya ne tak wato AZIZ,
AZIZ ne iya tashin hankalin datake tsoron rasawa ko shakkar fita a ransa datake fiyeda kowa,

Zaadens takejin sabuwar tsanarsu na cike koinanta sbd abinda tai gudun shine suka hadasa mata tareda qarin zasu iya fadawa AZIZ komai akan Fatima data kasa fda musu gaskiar wace ita,

Idan har suka bude baki suka fadawa AZIZ ko kalma daya akan yanda komai yake tsakaninta dasu sun gama lalata mata rayuwa sbd AZIZ zai cireta ne daga ransa Wanda tafi kaunar kowa ya mutu kafin a samu maganar fahimta a tsakaninsu harma a fada abinda tayi,

Bare bazata taba iya gani ko barin AZIZ ya samu shiri da Zaadens ba kaman yanda tasan zafin tsana da fushinsu na Nan fil a ransu saita dawowa da AZIZ tasa akansu ta yanda bama aure tsakaninsa da Jannah zai dawo ba dan kuwa irin son da Fatima kewa Jannah AZIZ zai qare ne gabaki daya akan Jannah da Fatima,

Duka batama fatan hakan ta faru adduarta da fatanta Fatiman ma kada ta tashi kwata kwata idanma ta tashi bata fatar ta dawo hankalinta shine lamarin zaiyi saukin sauki.

Nicky kuwa tana dayan palon t kasa qarasa shigowa sbd yanda kanta ke rawan rashin lafiyanta tana jin kaman ta Dora hannu akai ta kurma ihu kokuma ta sakawa 4&4 din wuta kowama ya mutu ta huta da wutar datake jin tana cin kirjinta tana tafasa jininta sbd batajin zata iya daukan ace mahaifiyar data AZIZ LIMBA itace a hannun Jannah tana riqo tamkar uwar data haifeta,

Kenan ko anan Jannah ta sake shan gabanta sbd zata sake samun AZIZ ko akan hakan ne,
Ita kuma fa?
Wa ta kama? Uwar da bata haifesaba Ashe

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login