Showing 123001 words to 126000 words out of 150681 words

Chapter 42 - Kalbim Book 2 Complete Hausa Novel

Mamuhgee   

23 Sep 2025

9116

baya suka zauna a palon sunayi har sallah tayi sukayo suka sake zaunawa har magrib tukuna kowa ya watse.

Daga masallaci acan su Dad suka sake zaunawa da saleem sukai Masa bayanin komai da ake ciki na cikin dayake jikin Jannah da hukuncin da suka yanke na riqeta tayi renan cikin har haihuwa.

Da mamaki Saleem ya kallesu Banda Ammar da bai saka bakinsa ba sbd yanzu ya iya tsayawa iya limits dinsa duk maganar AZIZ da Jannah ya dena shiga kwata kwata.

Cikin mamaki da damuwa Saleem yace

"Dad meyasa haryanzu Kun kasa yadda ku karbi AZIZ ne?
Idan har da gaske ne Kun cire komai a ranku Kun zubar babu sauran kowace irin tsana ko gaba to meyasa bazaku barsa da Jannah ba tinda gashinan clearly Kun gani tana sonsa haryanzu tinda ta iya Daukan cikinsa,

Dad kunsan wata ko satikan Jannah anan tareda mijinta?"

Da sauri suka kallesa da tsananin mamaki hadda Ammar Wanda koyaushe sabon mamaki yake samu gameda lamarin Jannah da AZIZ LIMBA.

Numfashi saleem ya sauke ahankali yana ajiye wannan zancen yace

"Dad ku Kalli ummah Dan Allah,
Ku Kalli yanda ta bar Dan data Haifa a cikinta sbd kawai tazo a cikinku tayi rayuwa kada ku shiga damuwa ko wani gararin sbd rashin uwa ko mace babba a familyn Nan,

Tanasonsa fiyeda kowa a duniya amma ta zabe ku akansa kunsan Yaya yake ji a xuciyansa amma ya danne ya hadiye ya yafe ta zo din sbd kawai yana tsananin son Jannah da girmama familynta duk da abinda ya faru a baya,

Dad pls Dan Allah ku barsu su samu farin cikin daya kamata sbd har abada Jannah bazata taba farin ciki da kowa ba idan ba AZIZ LIMBA ba haka ni kaina har abada AZIZ LIMBA bazai taba sauka ko raguwa daga zuciyata ba."

Yana gama fadan Hakan ya juya yabar gurin yana Jin gabaki daya familyn nasa sun sauya takaici da zaman gidan yari da garari duk ya yamutse kwakwalwansu.

Ammar ne yafara sauke ajiyan xuciya Shima cikin nutsuwa da sanyi yace

"Dad idan har sbd ni ne bazaku karban AZIZ ba wlh tallahi na Dade da cire Jannah a zuciyata sbd na riga na gani na tabbatarda har abada bazata iya son wani ba bayan AZIZ LIMBA,

Mune muka saka mata zuciyan datake bugawa a kirjinta Dan haka dole zamu hakura mu rungumi abinda zuciyar tazo dashi sbd zuciyar Ummitah bazata taba qin AZIZ LIMBA ba,Jannah da Ummitah ne suke tsananin sonsa a lokaci daya dan haka nidai na yafe na hakura na bar Jannah da Wanda takeso idan zaku yadda da Hakan mu taru mu rungumi abinda kaddara tazo dashi zamu Fi samun nutsuwa,

AZIZ LIMBA a zuciya yanzu ba maqiyina bane sbd har abada yanzu bazan iya qin jinin Ummah ba musamman da a gabansa ta zabe mu tabarsa babu amfanin dagewa akan aurenda masu auren suke son abinsu hakama bare Kuma AZIZ ya riga ya gama damu tinda ya dasa jininsa a cikinmu gwara mu rungumi kaddara mu rungumi abinda zaa Haifa shikenan"

Yana gama fadan Hakan Shima yabi bayan Saleem yabar gurin.

Muhammad ma bayan Ammar yabi sbd shine nasa aka bar Dad da Maheer tsaye a gurin babu me iya motsi ko cewa komai jikinsu a tsananin sanyaye sbd su kansu duk sun gaji da wannan masifar daga wannan sai wannan barema fada sukeyi a Baki sbd bacin Rai amma tsananin son da sukewa Jannah ko cikin shege ne a jikinta bazasu iya cirewa ba sbd kada wani abin ya sameta.

Da daddare Jannah Bata sauko cin abinci ba a daki fatma takai mata taci kadan Shima sbd zata Sha magani ne.

Karfe goma kowa ya shige jiki duk a sanyaye sbd yanda saleem ya sake nuna musu matsayin AZIZ LIMBA a rayuwansa ya wuce komai a yanzu Wanda Hakan yake musu nuni da ba riqon azaba ko wulaqantawa AZIZ yayiwa saleem din ba Dan haka sai sukaji kaman jikinsu na neman yin sanyi.

Washe gari dukkanin sauran abinda babu a Villa din na buqatan kowa Saida aka kawosa tareda wani irin sabon shopping din abinci da abubuwan buqata.

Haka suka sake wuni suna hutawa da sanin sauran abubuwan gidan Dana waje da anguwan Dan sanin inda zasu fara sabuwan rayuwa.


Kwanaki suka Dan fara dauka da dawowansu kowa ya fara kama harka gabansa,

Ammar fita yakeyi da mota shi da Muhammad sbd baida matsalar komai a ransa da damuwan Komai ya kwallafa ransa akan addua da yawaita karatun al'Quran da ummah ta tsaya tsaf akansa da Hakan Dan haka komai yaye Masa yakeyi kaman ba shiba.

Ummah ma hankalinta a kwance Jannah kawai take lallabawa sbd ganin ta kasa cire damuwa a ranta.

Shi kansa Saleem harkokinsa yakeyi hankali kwance sbd business dinsu gabaki daya dazai koma hannun Maheer sbd daman shine shigaban dayake gudanar dakomai da Zaadens,

Fatma ma hankalinta ya kwanta kwance batada damuwa ko matsalar komai itace take kulawa da komai na harka gidan duka masu aikin itace me fadan yanda zaayi sai Ummah wadda itace kaman shigaba kwata kwata.

Tsakanin Dad da ummah bayan gaisuwa babu abinda yake hadasu sbd Bata taba zuwa ko hanyar dakinsa ba tana sama ta tattarasa ta ajiye Da 'yayanta kawai take raharta da firarta sai Kuma AZIZ da kullum sai sunyi waya hankali kwance.

Dan haka hankalin Dad duk ya sake kasuwa Kashi Kashi sbd ya rasa ta ina zai fara kamawa,

Lamarin Jannah da AZIZ zai fara kamawa kokuwa na Umman wadda ko fuskan magana babu yanason Kuma magana da ita ya sanar mata cikin AZIZ ne a jikin Jannah.

Jannah Bata gama tsinkewa da shiga tashin hankali ba Saida taga suna maganar cike wata da dawowa Lagos amma ko so daya Bata taba Jin AZIZ LIMBA ba,

Bai taba nemanta ba,bai taba Kiran Fatma ya buqaci magana da itaba,
Koyaushe yana waya da Ummah tana jinsu amma bai taba tambaya ko yiwa ummah maganartaba,

Tsananin kewansa da damuwan abinda tai Masa ne suka fara nukurkusanta ta fara rama gashi anan gida ma kowa ya kasa cewa komai akanta kawai harkokin gabansu sukeyi har Umman taki ce mata komai akan AZIZ ko shiryasu kawai kulawa da ita akeyi da cikinta.
#MAMUH
07019691719*_KALBIM_*
Mamuhgee

Book 2
Chapter 71

Maheer daya fara zama busy hakama Ammar duk da Ammar bai shiga aikin sosai ba sbd yanayin lafiyansa dayake healing Amma dai da Muhammad suke zuwa ana koya Masa abubuwa da dama wainda zai iya duk da karatu Ammar din yake kokarin nema Masa ya fara.

Dad kuwa hutawa kawai yakeyi a gida Dan haka lokuta da dama shine da Ummah suke Kai Jannah din asibiti ganin doctor sbd yanzu baida zabin daya wuce Bata kulawa itada da cikin dayake jikinta.

*******Sai da suka cike wata biyu cif da dawowa Lagos bata taba Jin koda muryansa ba hakama duk Kiran da zataiwa Falaq ko Fi bada taba yi Mata maganarsa Dan haka hakurinta ya qare ta da daddare bayan ta kwanta taji babyn cikinta na juyawa ahankali batasan lokacinda ta fasa kuka ba tana dafe cikin tana Jin kaman ta janyo AZIZ din zuwa garesu duk inda yake sbd suna tsakanin sonsa da kewansa,
Fushin dayake yi da ita kasheta yakeyi bazata iya jurewa ba yanzu Kam.

Kwana tayi tana kuka sosai Wanda ya a sakata tashi da zazzabi me karfin gaske.

Fatma ce ta fito daga dakinta ta shigo Dakin sanye da kayan baccinta riga da wando masu santsi.

Tana shigowa ganin Jannah a rife cikin bargo har lokacin ya sakata kallanta tana cewa

"Yaya dai?
Lafiya dai ko?

Qarasowa tai tana Dan zaunawa bakin gadon ta miqa Hannu tana Dan yaye mata bargon.

Wani zafi ne ya daki fuskanta da sauri ta Kalli Jannah din tana miqa Hannu a wuyanta ta taba taji zafin gaske.

Miqewa tai tana qarasa yaye mata rufar Jannah datake cikin tsananin azabar ciwon mara kuka ta fasa tana Jin kaman zata mutu jikinta na tsananin tsananin rawa ta qanqame cikinta.

A rikice Fatma ta fita ta nufi dakin Ummah taga Bata nan Dan haka ta sauko qasa da sauri tin a palo kafin ta isa hanyar kitchen take kwalawa Ummah kira.

Ba hayaniya a gidan Dan Hakan ne duk akai hayaniya a gidan koman kankantar ta saita damu kowa dan haka Muhammad ne ya fara fitowa sai Maheer Wanda yake Shirin ficewa sbd yanada baqin da zai gani a yau din.

Ummah dake kitchen daman lokuta da dama tana shiga kitchen ayi aiki da ita sbd motsa jiki,
Fitowa tayi tana goge hannunta da qaramin kitchen towel tana cewa

"Lafiya me yake faruwa ne kike wannan ihun Kiran"

Qarasowa Fatman tayi tana cewa

"Ummah ciwon mara sosai Jannah ke yi ko magana Bata iyawa ko haihuwa ce?

"Wace haihuwa ana zaune kalau ciki wata hudu cikin na Biyar"

Hanyar tafiya saman suka nufa hadda Maheer daya mara musu baya hankalinsa na Dan tashi.

Ummah na zuwa da saurin gaske ta isa gurin Jannah din wadda har ta fara Dan bleeding hankali tashe Ummah tace

"Maza asibiti zamu babba ne lamarin"

Maheer na Jin haka ya sauko yana cewa Muhammad ya fito da mota.

Kowa fitowa yayi take gabaki daya hankalinsu ya tashi Ammar ma fito da tasa motar yay hakama Saleem Dan haka Maheer ne ya koma ya daukota cak ya sauko da ita a motar Ammar ya sakata su Ummah suka shiga itada Fatma shi Kuma ya shiga ta Saleem suka bi bayansu zuwa asibiti zuciyoyinsu na sake tsinkewa.

Dad da Muhammad sai daga baya suka biyosu Muhammad yana tuqa motan Dad na kusa dashi.

Suna isa akai gaggawan karbanta zuwa ciki sbd zuwa lokacin tayi laushi sosai karfinta ya kare.


Tinda aka shige da ita kowannensu ya kasa zama zuciyar kowannensu na wani irin tsallen fargaba da damuwa,

Damuwansu da tsananin halinda suke shiga a baya ne a duk lokacinda aka kawo Jannah asibiti da tana ciwonta na baya ne ya sake dawo musu yana mamayesu sbd a yanzu dai gasu a tsaye ba zuciyar take buqataba halinda take ciki ko Rai dari nawa zasu kashe babu abinda zasu iya Bata ko mata a yanzu sbd magana ce ta wani Rai dayake motsi a cikinta Dan haka addua kawai da safa da marwa sukeyi zuciyoyinsu ba dadi.

A daidai wannan lokacin ne Kiran AZIZ ya shigo Wayan ummah ta Kalli wayar tana kasa dauka sbd batasan ya sani.

Har wayar ta tsinke Bata daga ba Dan haka yana sake wani kiran Bata daga ba ya dakata bai sake kira ba Dan daman iyayensa kawai yakewa kira biyu a rayuwansa,

ajiye wayan yayi kan table din abinci da suke Kai zasu fara breakfast daga gefe yana dagowa ya gaida Mama data ke isowa dining din.

Amsawa tayi tana zaunawa tace

"Kayi waya da Fatima kuwa sbd inata Kiran wayarta Bata dagawa tin daxu gashi Bata cika nesa da wayarta ba"

Cikin nutsuwa da kamewansa yace

"Inaga tana wani abin Bata daukan Wayan kwata kwata"

Jin Hakan Falaq tace

"Bara na kira Jan muji ko Umman na wani abin ne to"

Wayan Jannah din ta saka kira da wayarta dake gefenta itama.

Harta yanke baa dauka Dan haka tana fada ko rife bakinta bataiba AZIZ ya dago tin kafin ya Kalli Sayd sayd din ya ciro wayarsa yana saka Kiran Saleem Zad sbd Jin lafiyan mutane biyu dayake dasu a zaadens babynsa da mahaifiyarsa.

Kiran Sayd na shiga wayar Saleem aka daga cikin sanyi da damuwan dayake kokarin daidaitawa saleem din ya sanar da Sayd suna asibiti da Jannah ba lafiya sosai she's bleeding.

Kallan LIMBA sayd yayi yana sallama da Saleem din ya kama nutsuwansa tsaf ya riqe kafin ya fara yiwa AZIZ din bayanin Jannah ce ba lafiya suna asibiti gabaki daya familyn.

A hankali cikin sanyi da nutsuwa AZIZ din ya sauke cup din dake bakinsa yana sipping lemon herbal tea ya buda baki yace

"Kasan meya kamata kayi"

"Already on it Sire" Sayd ya fada yana qarasa booking tickets din zuwa Lagos din.

Mama ce ta katse sayd din da cewa

"Am going too ka siya ticket Dani"

Cikin damuwa da neman fara kuka Falaq tace

"Allah yasa babu abinda zai samu baby limba da Jan,
Pls daddy nima zan tafi bazan iya zamaba,

Sayd na jin Hakan ya fara kokarin siyan tickets din dukansu kawai.

Nicky da kusan fiyeda kwanaki babu Wanda ya sakata a ido sbd kwata kwata Bata iya shiga mutane ce ta qaraso kunnuwanta na ji mata "BABY LIMBA" da Falaq ta ambata Wanda ya sakata tsayuwa daidai cikinta datake boyo yana bayyana a jikin hijabin da yanzu sune kayan datake sakawa Dan boye cikin batareda ta sani ba shock ya sakata tsayuwa daidai cikin na bayyana akan idanuwan kowa muryanta ma rawa tace

"Cikin Jannah na AZIZ LIMBA ne ko me???

Mutuwan da kowa yayi zaune idanuwansu akan cikinta ya saka babu Wanda ya iya Bata amsa saima salati me karfi da Mama ta sake a rikice tana cewa

"Aysha Ciki ne a jikinki ko me??

Sai a lokacin AZIZ ya dago yana kallan Nicky din da mamakin maganar Maman sai gashi Kuwa idanuwansa suka ganar Masa ciki a jikin Nicky din.

Fiddausi data San da cikin Nicky Bata taba fada bane sbd rufa asirin da batasan Yaya yake ba amma tin kwanaki da dadewa taga cikin amma Bata fadawa kowa ba sunkuyar da Kanta tayi cikeda tausayin Nicky din wadda kowa ya kalli yanda take rayuwa yanzu yasan tana cikin tsananin qunci da kadaicin rayuwa da rashin kowa.

Falaq Kuwa cikin mamaki da tsananin tsoron daga ina ita Kuma Nicky ciki yake bayyana a jikinta?
Tsoro taji yana shigarta Dan haka miqewa tayi tana komawa bayan Daddynta cikeda mamaki me hade da tashin hankali.

AZIZ Jin yayi kansa yayi wani masifaffen nauyi hankalinsa na mummunan tashi ya Kafe cikin da idanuwa yana kasa yadda da ciki ne a jikinta sbd ba yanda zaayi tana amanarsa daya karba ta amininsa,likitansa daya zama shaqiqinsa wannan mummunan abin ya faru bai saniba sai dai yaga ciki kawai a jikinta,
To daga ina ma wai?

Bude Baki yayi idanuwansa na sauyawa zuwa Jan tsananin tashin hankali da bacin Rai zai ambaci sunanta ta yanke jiki a gurin tana faduwa sbd tsananin tashin hankali da tsoron cikinta daya bayyana a gaban AZIZ da damuwan data Dade tana cin zuciya da lafiyanta da rayuwanta ma gabaki daya batada inda take samun sanyi ko kadan.

AZIZ dinne ya tareta a jikinsa sbd faduwan da zatai a kife Da cikin a jikinta sai a lokacin hankalin kowama ya tashi da tsananin tausayinta sbd wata irin mummunan Rama ce ta bayyana a jikinta me muni da aka cire hijabinta.

Da sauri sayd ya fita yana janyo mota har kofar fitowa Palo
AZIZ dinne da kansa ya dauketa a jikinsa ya fito da ita idanuwansa na sake tsananta ja sbd wannan sabon tashin hankalin daya bayyana a ahalinsa Shima yanzu rana tsaka.

Asibiti suka isa da ita da gaggawa inda aka karbeta itama da gaggawa ana shigewa da ita.

Sai a lokacin ya zauna yana rintse idanuwa kansa na sake daukan nauyi yana shiga sabon damuwa da tashin hankali amma very calm yake a zaune bazaka ce yana cikin matsanancin damuwa da tashin hankali a cikin zuciyarsa ba.

Su Ummah ne suka iso asibitin itada Fi Banda Falaq da duk ta firgice sbd Bata taba ganin ciki da babu aure ba a zahiri duk Kuwa zamanta a turai da tashin ta acan.

Zaman jiran tsammani da damuwa sukeyi a gurin Fi nata kaida kawo tana Jin tausayin Nicky din na neman narka zuciyarta idanuwanta sai cikowa da hawaye sukeyi tana hadiyewa.

Ruwa Sayd yaje ya kawo mata ya kama hannunta ya zaunar da ita tareda miqa mata ruwan bayan ya bude mata cikeda kulawa da sanyin kalami yace

"Ki kwantar da hankalinki pls,
Babu abinda zai sameta zata tashi lafy kalau harma da babyn"

Zuba Masa idanuwanta tai tana Dan sake Jin kaman zatai Masa kuka ya lumshe Mata fararen idanuwansa yana gyada mata Kai alaman komai zai daidaita.

Ajiyan xuciya ta sauke tana Kai ruwan bakinta Tasha kadan ahankali tana miqa masa ya karba yana rufewa ya ajiye gefensa yana ciro handkerchief dinsa dayake fidda qamshinsa me sanyi da tsada ya Bata ta karba tana goge bakinta a hankali ta miqa masa ya karba yana maidawa aljihunsa yana sake kwantar mata da hankali sbd sanin abu kadan yake daga mata hankali.

Jikin Nicky din sosai ya rikice yana zama serious sbd ta jima bp dinta yahau sosai sbd tsananin qunci da damuwa da rashin kulawa Dan haka kwata kwata likitoci basu ga yanda suke so a tattare da ita ba Dan haka sukaita nuna rashin Jin dadin yanda aka kasa kulawa da ita sbd cikin aka bari damuwa da quncin sukai mata yawa.

Shiru AZIZ yayi damuwansa na tsananta sbd yanda yayi watsi da ita bai taba nema ko Jin lafiyanta ba ko Bata ko kallan rahama ne ko Dan sbd Dan uwanta da Kuma soyayyar datake Masa wadda ta sakata baro Dan uwanta da gatanta ta biyosu.

Hankalinsa rabuwa biyu yayi cikeda damuwa da dacin zuciya sbd nasa cikin na can cikin hadari hakama Nicky da Bata da kowa bayansu tana cikin hadari da nata babyn Wanda kafin komai ya biyo baya suna buqatan Bata kulawa da kokarin ganin ta tashi itama da nata babyn.

Sayd ne yayi duk wasu formalities daya kamata ayi na tafiyansu da Nicky din zuwa Lagos sbd hadewa a can gabaki daya Dan nema mata lafiya idanma waje ya kamata a fita da ita AZIZ din ya shirya Hakan sbd zai tsaya ya nema mata lafya da Jin damuwanta Dan debe mata kadaicin dake cin rayuwanta da Bata tarbiyan a Bata samu ba tin farko daman Hakan ya kamata yayi tin farkon zuwanta cikin iyalinsa bawai watsar da itaba da yanzu zuciyarta Bata lalace irin hakanba.

Cikin tattali da kulawan gaske ga mara lafiya jirginsu gabaki daya LIMBAS yabar Abuja zuwa Lagos.

A daidai wannan lokacin suma su modibbo dasu kawu motarsu ta sauka a Lagos Allah yayi sun taho ganin gida da hutu zuciyoyinsu fal farin ciki da tsananin murnan wannan arzikin daya tabbata dai anyi ana tareda su.
#MAMUH
07019691719*_KALBIM_*
Mamuhgee

Book 2
Chapter 72

Muhammad ne yaje park daukansu da lafiyayyar motarsa datake daukan idanuwansu suna ganinsa da farko basu ganesa ba sbd sauyawansa gabaki daya kwata kwata,

Ganin basu ganesa ba ya sakasa fitowa motar ya qaraso har gabansu cikeda farin cikin ganinsu da kulawa yace

"Modibbo barkanku da sauka"

Da sauri dukkaninsu suka sake Kafesa da idanuwa bakinsu na wata irin washewa da tsananin farin ciki da mamaki kawu isiya yace

"Garba,Garba Kaine kika koma haka kaman baturiya,
Garba ina Fatma itama ta sauya haka kenan??"

Murmushin nutsuwa garban ya sauke yana bude bayan mota ya saka kayansu yana cewa

"Kawu Fatmanku ai ta koma macen birni"

Wani sabon dadine

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login