Showing 36001 words to 39000 words out of 150681 words

Chapter 13 - Kalbim Book 2 Complete Hausa Novel

Mamuhgee   

23 Sep 2025

9072

din ta mutu ne.

Kiran AZIZ ne ya sake shigowa ba kakkautawa a wayan na Mama data kasa dagawa har lokacin,

Wayar fiddausi ma dake dakinta Sayd na can na mata Kiran da babu adadinsa Amma baa dauka.

Fatma dake gyaran dakin fiddausin ne dataji Kiran yayi yawa ta fito da wayar ta iso dakin tai sallama kanta a qasa tace

"Anata Kiran wayar ne"

Tasowa fiddausi tayi ko ganin gabanta batayi ta riga Maman karban wayar tareda dagawa a take bama tareda ta duba waye ba Amma tasan bazai wuce Kiran Daddyn Falaq din ba ko Sayd..

Muryan AZIZ ce kai tsaye ta bayyana babu rahama ko kadan a cikinta cikeda kamewan da hatta Mama saida cikinta ya juya yace

"Meya samu Falaq din?

Kuka fiddausi ta fasa mara sauti sosai sedai cike yake da tsananin tashin hankali tace

"Ta yanke jiki tana tsaye stairs sai ta fado amma ankir....dif taji ya kashe wayar yana dago idanuwansa da suka sauya take yace

"Siyamun ticket na tafiya yau dinnan idan akwai"

Sayd da tin dazun yafara kokarin siyan tickets din yace

"Already on it"

Miqewa yayi daga zaunen dayake yana barin office din cikin gidansa da suke suna wani aikin ya wuce ciki Yana kallan agogon hannunsa sbd ya kwatanta time din isarsa idan ansamu ticket din yanzu.


Acan kuwa wayar na mutuwa fiddausi dagowa tayi ta kalli Mama wadda tariga ta shiga mummunan yanayi me girman gaske sbd tasan mutuwa kawai zata hana AZIZ LIMBA isowa Nigeria zuwa dare ko asuban yau,

Fiddausi take kalla da wata irin mummunan yanayi zatai magana fiddausi ta girgiza kai tana cewa

"Bani bace kawai Kiran na samu a yanzu gabanki aka kawon wayar Mama"

Juyawa Mama tayi kan Nicky dake kokarin isa gurin Falaq ta riqota ta dawo da ita gabanta idanuwanta jajir tace

"Waye ya kira AZIZ ya fada masa?
Kece kikai hakan?

Damuwa Nicky din ta bayyanar sosai a fuskanta dan nuna kulawanta akan Falaq tace

"Na shiga tsoro da tashin hankali ne shiyasa na sanar masa sbd kada yaji daga baya yaga laifinmu da muka boye masa amma ai bai daga wayanba Sayd na kira....."

Zamewa Mama tayi ta zauna kan sofa dake dakin tana rintse idanuwanta cikeda wani irin tsananin baqin ciki da takaicin Nicky din ta kalleta kaman zatai mata duka tace

"Kin kirawa kanki balai da masifar da bazaki iya ba garin neman sunanki,
Kin kira mana ruwan da baya taruwa,
Meya kaiki?
Wa ya aikeki.
Innalillahi wainna ilayhi rajiun"
Tinda kikai hakan saiki shirya ganin abinda baki tsammata ba kala kala sbd.........

Kasa qarasawa tayi tana dafe goshinta sbd yanda kanta ma yake sarawa,

Babu daqiqiya irin Nicky sbd ta wargaza mata komai da wannan Kiran dataiwa AZIZ,

Itadai haduwansa da Jannah tasan bazata taba iya hanawa ba indai ya iso din sedai tasan bazai taba komawa Jannah dinba tinda tai rantsuwa dan haka wannan Nicky ce a ruwa tsundum ita tata matsalar shine cigaba da hana Ummah fitowa duk rintsi bazata fito inda AZIZ zai ganta ba ko Sayd sbd Sayd na ganinta a take zaiga kamannin Ummitah a tattare da ita kuma ma tana shakkar idan kila bai taba ganinta koda a photo bane dan akwai sketches dinta da a baya AZIZ ya ringa sakawa anayi masa na nemanta suna nan daki guda a yanzu batasan inda AZIZ yakaisu ya boye ba da ko ita ta dena ganinsu tinda Falaq t fara wayo y boye su sbd kada ya raba mata hankali tinda haryau bata san cewa ba Mama bace ta haifesa ba.

Nicky shiru tayi tana nazarin maganganun Mama Amma bata wani damu dasu ba sbd ita dai a saninta kaf duniya Falaq zata nunawa kulawa da so ta samu AZIZ sbd Falaq ce abinda zakaso ka Samu isa zuciyarsa kuma indai hakan zaisa y dawo Nigeria batada baqin ciki tinda dawowan nasa shine aurenta dashi dan haka koma me zai biyo bayan ya biyo bai dameta ba indai zai diro qasar buqatanta ta biya.

Isowan Dr ne ya saka dukkaninsu fitowa sai fiddausi aka bari suka dawo palo suka zauna ran Mama babu dadi kwata kwata.

Nicky kuwa breakfast dinta ta saka Jannah ta kawo mata har saman ta ajiye mata ta fara ci a natse hankalinta kwance.

Kallan takaici da baqin ciki kawai Mama ke binta dashi tana rasa abin fada mta amma dai tasan idanuwanta da zuciyarta zasu fada mata nan ba da jimawaba indai AZIZ LIMBA da JANNAH ZAD suka hadu.

Jannah da wani irin nauyi ne yake danne da zuciyarta a natse ta gama ayyukanta tana kokarin saukowa fiddausi ta bude dakin Falaq ta fito tareda Dr da zai wuce ta sauke idanuwanta da sukai jajir akan Jannah dake kokarin sauka ta bude baki kai tsaye tace

"JAN"

cak Jannah ta tsaya idanuwanta tana lumshe idanuwanta ahankali sbd Falaq dinta ce kadai me kiranta da sunan fiyeda kowa.

Kasa juyowa tayi saida fiddausin ta tako a natse ta tsaya bayanta tace

"Tana buqatan black tea zata Sha magani dashi"

Ajiyan zuciya ahankali Jannah din ta sauke sbd tasan fiddausin na kokarin fada mata Falaq din taji sauki.

Gyada Kai tayi batareda ta juyoba ta fara sauka tana sauke ajiyan zuciya a jere sbd ayau bayan shekaru zata hadu da Falaq ta kalleta da kyau taga lafiyan data samu zata hadu da Falaq ayau a matsayin 'yar da zuciyan dake kirjinta ta Haifa.

Tana isa kitchen din kai tsaye tea da pancake ta fara kokarin hada mata da lafiyayyan zuma da chocolate mix.

Acan saman kuwa Jannah din na sauka miqewa mama tayi ta isa dakin Falaq ta sameta zaune tana kokarin saukowa gadon ta fito jikinta har wata irin rawa yakeyi idanuwanta suna tara ruwan hawayen farin cikin datake jin kaman uwar data haifeta ce ta dawo duniya,

Kuka takeson fasawa tana son furta JAN Amma bakinta sbd rawan dayake ya kasa furtawa ta nufi kofa da sauri zata fita Mama ta shigo dakin.

Rufe kofar dakin Mama tayi tareda juyowa ta kalli Falaq da idanuwanta fes tace

"Jannah ce da gaske kaman yanda kika gani amma a matsayin me aikin 4&4,
Bazaki taba komawa yanda kike da ita a baya ba zaki mu'amalanceta ne only as Yar aikin gidan nan idan kikai abinda ya wuce hakan nayi Miki alkawarin korarsu aiki su tafi inda har abada bazaki taba sake ganinta ba,
Dan haka indai kinason ganinta zaki kulata ne kadai a matsayin me aikin gidan nan,

Duk kaunar da mahaifinki ke Miki karki manta baya taba saba umarnina dan haka korarsu ba wani big deal bane a gurinsa idan nace hakan,
If kinason Jannah ta zauna lafiya a 4&4 ba azabar aiki ba wulaqantawa kibi yanda nace,
Zabi ya rage naki"

Juyawa tayi ta bude kofar dakin zata fice Jannah ta buga kofar dakin ta fiddausi n gefenta.

Bude dakin Mama ta qarasa yi ta kallesu kafin ta juyo ta kalli Falaq wadda idanuwanta sukai jajir tanajin kaman zuciyarta zata buga sbd tsananin baqin ciki da radadi me zafi...

Mama tasha gabanta anan sbd bazata taba yadda a rabata d Jannah ba ayanzu,
Bazata taba yadda a wulaqanta Jannah ba hakama bazata taba iya kallo a wahalar da ita ba.,

To amma indai Mama tace hakan zata yadda ba komai bane indai Jannah na mansion din Daddy dinta ma yananan hakan ya isheta zata nunawa Mama umarninta daban abinda zai faru daban sbd indai hakanne ma Jannah a matsayin me aiki shine abu mafi kyau a yanzu gareta dan hakan na nufin zata bawa Jannah umarni tabi kowane irin ne kuma zata sakata aiki kowane irin ne tayi ba gardama.

Ajiyan zuciya ta sauke tareda dagowa ta kalli Mama tana share hawayenta da suka gangaro ta juya batareda ta kalli Jannah dinba ta zauna bakin gadon data tashi.

Shigowa Jannah tayi a natse ta ajiye tray din hannunta tareda dagowa ta saukar da idanuwanta akan Falaq tanajin duk wani tsananin kaunar Falaq din data danne tana tasowa cikeda kewa.

Qin kallo Jannah Falaq tayi ta dago a hankali ta kalli fiddausi ta bude baki tace

"Bani maganin"

Fiddausi data gama cika da mamaki sanyin jiki na shigarta ta kalli Falaq din ta juya ta kalli Jannah da jikinta ya fara sanyi sbd da alama Falaq ma ta tsaneta kenan kaman duka LIMBAs.

Numfashi ta sauke a boye tana juyawa ahankali ta nufi kofa ta fice tana hadiye duk abinda ya taso mata a kirji sedai hawaye ne ke kokarin saukowa daga idanuwanta tana kasa riqesu sbd Falaq idan ta qita zuciyarta zata iya kasa dauka.

Tana isa kitchen bata iya riqe kanta ba durkusawa tayi tsakiyar kitchen din tana rufe fuskanta da tufukan hannuwanta hawaye na gangaro mata.

Falaq ma Jannah na ficewa daga dakin hawayen ta gangaro tana dagowa ta kalli Mama data fice hankalinta kwance.

Fiddausi data fahimci abinda ya faru zamewa tayi ta zauna tana kasa cewa komai.


Shiru gidan yayi a wunin babu motsi me yawa bayan na Nicky daketa kai da kawo cikin farin cikin dawowan rabin ranta dan haka karshe ma fita tayi taje spa sai dare ta dawo a lokacin suna dinner gabaki dayansu a dining,

Zaunawa tayi aka qarasa da ita ana gamawa kowa ya haye sama da tinanin ko yaya maigidan sbd kowa ya kasa samunsa bare Sayd a waya dan haka basuda Sani ko tabbacin zuwansa da haka har dare yayi sosai suka kwanta.
#MAMUH
#LIMBAS
#ZAADENS
#BEST LOVE
#HOT ROMANCE

07019691719*_KALBIM_*
Mamuhgee

Book 2
Chapter 21

*_ZUZEAM VENTURES_*
08144015291
Best Aphrodisiac/kayan mata
ASLM barkanmu da wannan lokaci
Ina Mai farin cikin sanar daku cewa Zuzeam ventures takawo maku ingantattun magunguna masu inganci cikin Aminci Muna da kaya kamar haka
Mallaka Maganin sanyi
Maganin cire tumbiMaganin farin jini
Maganin matsiMaganin mata
Maganin sa ni’ima da dandano
Dulka Amare Set na gyran jiki
Set na amarya
Tabaje tsumin Gomba
Xuma kiba ta hips and Brest
Magungunan gyran Brest
Magungunan Karin hips
Maganin sliming
Turaruka kala kala Na jiki da kaya da daki turarukan amare
Turaren kabbasa
Muna da kaya masu inganci  cikin sauki da rahusa
Ina wadda keneman mallaka sahihiya quaranty wlh hajiya kixo ga zuzeam ventures xakiji ddin mallaka duk fadin ran ogah duk fadansa wlh sai yyi sanyi 08144015291
Idan maganin mata kikeso akwai
Idan gyran jiki kikeso gyran fata gyran Brest magungunan sa kiba da hips
DOMIN samunta Kai tsaye kira wannan no 08144015291 DOMIN mgn da ita whatapp 08144015291muna tura kayanmu ko ina cikin iKon allah 🥰👌🏻
Bononza Bononza Tsimin mallaka 2k Tsimin dabino 1k Gumba madara 1500 Gumba aya da nonon rakumi  1500 Garin kafi ciccibi 1k
Garin bata gaban kishiya 1k
Matsin mallaka tada zaune tsaye 2500
Turaren mallaka ba aba mai kishiya 2500 Total kayan 13k
Za a bakisu akan 5500
Kuma mutun goman farko nadakyautar Abun 2k
🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️ ASSALAMU ALAIKUM ALHAMDULILLAH YAN UWA  NEW PROMO YA KAMMALA💃🏽💃🏽💃🏽😁😁😁 da 8k dinki ki kwashi kayan 16k hajiyata 💃🏽💃🏽💃🏽😃🙃Kazar gadali ta mallaka sashe 3500 Tsimin gam gam 1500 Ruwan kara zunzurutun dadı😋 1k Garin 7in1 2k Gumba 3 balai 1500 Gumba kwakwa da dabino 1500 Na Infection  1500 Garin zunzurutun dadi 1500Matsin ba a fira d wando 500 Matsin infection mai matse mace gam 500 18k All at 8k koda kudinki saida Rabonki.

******************
Karfe 7 na safe Jannah ta iso bangaren ta hau sama kai tsaye tafara aikinta a natse itada Fatma da itace me gyaran dakin Falaq.

Jannah na gamawa ta sauka ta koma kitchen suka fara aikin breakfast da Amina wadda keta bata labarin Madam Sisi tinda safe tana dakin Mss Nicky haryanxu bata fito.

Shiru kawai tayi batareda tace komaiba sbd batasan me zatace din ba,

Karfe 9 suka gama jere komai a dining suka dawo kitchen,

Jannah kai tsaye bangarensu ta koma dan Ummah ta tashi yau bata jin dadi jikin nata ya dan motsa..

Ko data isa su Dad ta tarar zaune dukkaninsu a guri daya da alama magana suke suna ganinta suka zuba mata idanuwa dukansu kowa yanayinsa ba dadi.

Dauke kallanta tayi daga kansu tana zaunawa gefen Ummah dake shan ruwa ahankali tace

"Dad,wani abin ya faru ne na ganku hakan?

Shiru sukai Banda Ammar da idanuwansa sukai jajir kaman zai kashe Kansa yakeji ya kalleta ya bude baki ba zato yace

"Dad dan Allah a daura mun aure na Jan kafin na mutu,
Dan Allah a cikamun wannan burin kafin Allah ya dauki Raina"

Kallansa dukansu sukai batareda mamaki ba sbd a yanzu da AZIZ LIMBA ya sauka a qasar Yana kuma cikin gidan Ammar bazai taba samun nutsuwa ba,
Suma bazasu taba samun nutsuwanba matiqar ba daurawa Jannah aure sukai ba da Ammar din.

Jannah kuwa kallansu ta sake yi tana cewa

"Ammar wani abin ya faru ne??

Girgiza kai yayi idanuwansa na cikowa da hawayen da baisan ya zaiyi da abinda yakeji a zuciyarsa gameda Jannah din ba yace

"Jannah aurenki shine burin Dana jima dashi tin kina ciki dan Allah ki cikamun wannan burin na aurenki sbd zuciyata takasa samun nutsuwa,
Wlh akanki ban daddara ba zan iya sake zama makashin duk wanda zai rabani dake sbd rasa tinani na nakeyi lokuta da dam.....

Dad ne ya hanasa qarasawa Yana kama hannunsa yace

"Ammar na maka alkawarin muna barin 4&4 dinnan a ranar zan daura maka aure da Jannah Ni nayi maka wannan alkawarin insha Allah."

Da sauri Ammar ya rungume dad din hawaye na gangaro masa.

Jannah ma ajiyan zuciya ta sauke batareda tace komaiba sbd batajin zata iya cewa komai sbd indai aurenta da Ammar zai qarasa wanke abinda yake zuciyarta ta shirya hakan sbd ta samu ta wanke idan hakan zai yiyu.

Shiru sukai babu wanda ya fada mata AZIZ LIMBA ya iso da asubar yau din Wanda Garba ne ya bude second gate din dukkaninsu tinda suka ga shine suka kasa bayyanar da kansu sbd abubuwan baya da suka ringa dawo musu na baqin ciki me girma.

Wanka tayi sbd yau tayi lattin tashi batai wanka ba ta tafi tayi aikin safen,

Tana fitowa cikin sauri ta sake shiryawa ta koma kitchen din suka hau aikin lunch ta tadda hadda madam Sisi ake aikin.

Kallan renin hankali madam din tai mata tana cewa

"Kada ki sake barin kitchen batareda angama aikin masu gidan ba daga yau sbd naga kina wasa da aikinki sbd ganin Mama ta daure muku gindin zama a gidan bayan muguwar taasar da me hankalinku tayi"

Shiru jannah tayi batareda tace komaiba tana ci gaba da aikin yanka carrot data tarar.

Maganganu Sisi tahau yi wanda babu Wanda yace komai sukai shiru suna jinta banda Jannah data hana kanta jinta ta hanyar dauke hankalinta akan maganganun.

Karfe goma da mintina mutan gidan suka fito suka halarta a dining dan breakfast dinsu suna zaune banda fiddausi dake tsaye dan serving nasu.

Kokarin fara cin abincin sukeyi Sayd ya bayyana a dining room din cikin sallama da kwanciyar hankali idanuwansa akan Falaq da itama mamaki ya gama kasheta sbd ga dukkanin alama ba yanzu yanzu ne suka iso ba hakama bata taba saka ran ganinsu a yanzu ba dan ta dauka bazasu dawo din ba...

Mama take taji yunwar cikinta ta bace bat ta zubawa Sayd ido tana jiran bullowanu uban gidan nasa.

Fiddausi kuwa tinda take a cikin LIMBAs tsawon shekaru bata taba farin cikin dawowansu irin yau ba hamdala tayi tana sauke ajiyan zuciya daidai nan qamshin Grand soir ya fara bayyana a gurin Wanda ya saka Falaq ajiye cup din hannunta tana miqewa tsaye daidai nan ya sako kai a natse sanyeda fararen kayan Brioni na zaman gidan fuskansa fresh da wani irin kwarjini da nutsuwa,

Idanuwansa akan 'yarsa suka fara sauka Wadda tin a Daren jiyan yaje dakinta tana bacci dan haka bai tashetaba y fice ya kyaleta...

Da wani irin gudun tsananin kaunarsa da kewansa datai ta nufesa dole ya zaro hannuwansa daga aljihunsa yana budewa dan tarbanta ta fada masa ya rungumeta gabaki dayanta yana sauke ajiyan zuciyan da saida ya bayyana a fili na ganinta fit and fine sbd kafin isowansa bugawane kawai zuciyarsa bataiba da tinani kala kala.

Sake qanqamesa tayi a natse tana cewa

"I love you Daddy,i love you"

Dagota yayi ahankali Yana kallan fuskanta cikin sake samun nutsuwa yace

"Ok ok karki gajiyar d kanki da yawa kin riga kinsan kene zuciyan Bestynki"

Murmushi ta sake farin cikinta yana qara tsananta sbd ganinsa a gabanta a gida daya da Jannah batareda ya Sani ba.

Mama ya kalla Wadda ciwon zuciya ma taji kaman Yana neman kamata cikeda girmamawa yace

"Barka da safiya Mama,
Mun sameku Lfy?

Ajiyan zuciya ta sauke tana sake fuskanta tareda bayyanarda farin cikin ganinsa tana amsawa tareda kallan Sayd dayake gaidata ta amsa shima tana cewa

"Ashe gida daya muka kwana daku shine baku sanar mana da isowanku ba tin cikin Daren"

Zama AZIZ yayi har lokacin Falaq na riqe da hannunsa cikin nata ya dago yayiwa Nicky dake gaidasa kallo daya da idanuwansa da suka kusan sumar da ita daga zaune ya amsa mata kai tsaye ba damuwan komai kafin ya amsa gaisuwan fiddausi itama.

Zaunawa kowa yayi fiddausi zatai serving nasu Mama ta kalli Nicky take ta miqe ta karbi aikin tafara zubawa AZIZ din komai daidai yanda zai ishesa tukuna ta bawa fiddausi tayi serving kowa.

Da mamaki Sayd yake kallan hakan hakama fiddausi ganin sabon salon batai wani dogon mamaki ba.

Mama kuwa sai yabawa Nickyn takeyi shikuwa Wanda akeyi akansa baice komaiba abincin yafara ci a natse Falaq ma murmushi tayi tana saka spoon cikin nasa tana diba tana hadawa na nata tanaci.

Dagowa Falaq tayi ta kalli fiddausi tace

"Fi pls wani daga kitchen ya kawo mun honey banason Nutella mix dinnan"

"Ok" fiddausi tace da sauri tana juyawa zuwa kitchen din sbd saka Jannah kawowa.

"Fiddausi ki kawo mata da kanki bama buqatan Yan aiki anan yanzu Musamman ga AZIZ Yana zaune koba yau ba kada a gwada hakan"

Shiru kowa yayi banda AZIZ da hakan bai damesa ba sbd bai taba damuwa da harkan masu aiki ba bare tin can iya fiddausi ce ke iya xuwa gurin cin abincinsu idan yana gari ita kadai ce me wannan matsayin sbd ta zama Yar gida.

"Barshi kawai" Falaq tace tana kallan Dad dinta kafin ta kalli Mama Wanda itama AZIZ din ta kalla.

Fiddausi ficewa tayi batareda ta dawoba har suka gama tukuna ta dawo ta tattara gurin.

Daga dining kai tsaye samansa ya wuce tareda Falaq da Sayd zuwa palonsa suka zauna Nan aka sake Kiran Dr yazo yayi masa bayanin ba matsalar komai.

Fira suka hau yi har yana mamakin irin farin cikin dayake gani tareda ita ya bude baki a natse ya dan kallanta ya maida hankali kan wayarsa dayake dubawa yace

"Ya dai?
Akwai wani abin da kika samu ne??

Murmushi tayi tana kallansa tace

"Ina tsananin murna da farin cikin ganin Daddyna ne kawai"

Sayd dayake tura sakon da basu samu nutsuwar turawaba suka taho yace

"Anya?
Bara dai na gama mu saka labule"

"Da waye ne zan saka labule?
Da kai?
Ina gama fada maka Daddy zai maka kallo daya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login