Showing 129001 words to 132000 words out of 150681 words
fara cin karo Yana shiga hancinsu da sauri Dad ya dago cikin ransa yana fatar LIMBA dinne da gaske sbd Jannah ta samu ganinsa ko zata samu farin cikinta data rasa amma a fili Dan kame fuska yayi yana satar kallan gefen Ummah da tsananin farin cikin ganin AZIZ din daya sako Kai ya cikata tana miqewa da sauri ta isa gurinsa ya rungumeta cikin jikinsa yana samun nutsuwan ganinta cikin farin ciki.
Cikin farin ciki ta tambayesa hanya da Kuma su Mama
Kafin ya amsa sakinsa tayi Jin palon tsit kaman ba kowa ta juyo,
Tana kallan Dad ba shiri ya washe Baki baisan ma ya furta
"Wow Masha Allah barka da zuwa"
Murmushi tayi tana kallan AZIZ din wanda yanda Dad din ya washe Baki gabaki daya ba shiri ya sakasa murmushi me nutsuwa yana Dan boye dariyansa ya gaida Dad din Wanda ya amsa dole yana washe Baki sbd ummah dayake neman shiri da ita.
Maheer ma ganin Umman ta kallesa da yanda Dad ma ya washe Shima dole ya Dan sake din suka gaisa yana zaunawa Saleem na yar dariyar mamakinsu su dukan.
Ammar ne kadai ya miqe tsaye da zuciya daya ya miqa AZIZ din hannu yana Masa barka da zuwa Shima a natse ya miqa masa suka gaisa yana cewa "thank you"
Fatma ce ta fito a sake cikin girmamawa ta gaidasa tana Masa barka da zuwa taje da Kanta ta kawo Masa ruwan sanyi da coffee din data San yana Sha.
Dad ne ya fara silalewa yabar palon kafin Maheer ma ya zame aka bar Ummah da Ammar sai Saleem da muhammd suka sake abinsu sukai fira sosai.
Jannah dince ta sauko tana shigowa palon sanye da doguwan riga mara nauyi da hula akanta qamshinta me sanyi yana shiga hancinsa direct Dan haka ya dago fararen idanuwansa ya Kafeta dasu tin Bata qaraso ba tareda mantawa ba shi kadai bane a palon.
Tana isowa ko zama batai ba Ummah tabar musu gurin sbd ganin yanda AZIZ din yake kallanta.
Ammar ma da Muhammad sallama sukai Masa suka bar palon.
Hannu ya miqa mata ta kallesa tana murmushi ta kama zata zauna gefensa ya miqe yana cewa
"Tafiya zamuyi"
Da sauri ta kallesa tana fasa zaunawa kafin ta Kalli Saleem Wanda baice komaiba ta dawo da kallanta kan AZIZ din zatai magana ya Dora hannunsa kan bakinta yana cewa
"Shihhhhhhh zamuga Dr ne"
Ajiyan xuciya ta sauke tana Jin hankalinta na dawowa daidai daga tashin da yai.
Hannunta ya kama suka fice bayan Fatma ta kawo mata mayafi qarami ta yafa suna fita.
Akan idon Maheer motar AZIZ din tafice da Jannah yana Kallo baida abin cewa zuciyarsa na nauyi da tinani kala kala.
Kai tsaye gida suka nufa suna isa ta kallesa da mamaki zatai magana yace
"Welcome home Mrs LIMBA"
Magana zatai idanuwanta suka sauka akan Doctors biyu da suka fito daga motar datake harabar gida suna yin ciki dan haka ta sauke ajiyan xuciya sbd ta dauka ya daukota kenan.
Suna shigowa palon farko na gidan daidai Nicky na fitowa da nata cikin Wanda yafi na Jannah din girma da wani irin shock Jannah ta zubawa cikin Ido Kanta na Sarawa kirjinta na nauyin da numfashinta yafara toshewa ta Kalli Falaq da Mama da suka fito da Nicky din cikeda kulawan data saka take shedan ya saka mata mummunan tinanin daya saka kafafunta kasa daukanta tana kokarin zubewa qasa Nicky data ga halinda take neman shiga da sauri cikin karfin murya tace
"Ba na AZIZ bane na Garba ne......
Da Mama da Falaq da fiddausi da Sayd dashi kansa AZIZ din cikin mummunan firgicin da basu taba shigaba suka juyowa da karfi suna kallanta a rikice Jin sunan Garba.
Jannah Kuwa qarasa kaiwa qasa tayi cikin sabon tashin hankalin daya juye mata Jin sunan Garba.
#MAMUH
07019691719*_KALBIM_*
Mamuhgee
Book 2
Chapter 74
Mama data rikice Kanta na juyewa batasan lokacinda tace
"Wane garban Kuma?
Garba na zaadens kokuwa Gabriel kike nufi Ayshatu??
AZIZ da kansa yayi wani irin nauyi har zuwa kirjinsa Jin yayi tashin hankali biyu na rufesa na Jin wai cikin Garba ne a jikin Nicky da Kuma Jannah datai tinanin cikinsa ne take neman illata Masa Kanta,
Amma duka kafin wannan Shima kallan Nicky din yayi idanuwansa na yin ja yana dawowa da hankalinsa da Tinaninsa daidai ya bude baki yace
"Waye Garba Kuma?
A ina yake?
A Nigeria ko Greece?"
Shiru tayi kowama Shirun yayi suna sake dauke wutar jikinsu sbd tsananin rikicewa da tashin hankali suna jiran amsarta.
Zufa ne yake gangarowa Nicky din yana jiqata Bata San Yaya ake Jin kunya ba sai yau datake Jin wata irin kunya me tsananin gaske tana rufeta sbd ambatar Garba da zatai a matsayin uban danta Kuma tasan itace ta Kai Kanta Kuma ta jawa Kanta komai,
Tayaya zata bude Baki tace itace ta fara jansa a lamarin Wanda ta tabbatarda kaman itace tai Masa dole duk da basa hayyacinsu amma babu abinda suka manta.
From fiddausi ce jiki a matiqar sanyaye zuciya cikeda firgici har lokacin ta qaraso gurin Jannah datake sake Jin rikicewan tinani ta kamata suka nufi kujera ta zaunar da ita a natse
Falaq ma gurin Jannah din ta qaraso ta zauna gabanta na tsananta faduwa itama da abinda suke kokarin ji me rikitarwa wai garba ne yayiwa Nicky din ciki.
Mama Nicky din ta kama suka qarasa suma suka zauna sbd kowa kafafunsa kokarin kasa riqesa sukeyi Dan haka kowama zaunawa yayi Banda sayd dayake kokarin tina ko yasan wani garban bana zaadens ba.
Shiru AZIZ yayi yana sake juya sunan Garba din a kansa yana kokarin tina Wanda ya sani me sunan bayan Muhammad na zaadens amma babu Dan haka ya sake Dora idanuwansa akanta tayi Shiru idanuwanta a qasa sunyi jajir hawaye cike dasu amma sun kasa saukowa sbd damuwa da quncin datake Jin ya cike kirjinta.
Cikin nutsuwa a kame yace
"Aysha,da naso barin ki huta daga zaman asibitin da kikayo kafin miyi wannan maganar ta waye me cikin jikinki amma Hakan bazata iya samuwa ba yanzu ina son sanin gaskiyan waye ne me shi?
Maana waye babansa sbd ina buqatan ganinsa Kai tsaye batareda batawa Kai lokaciba."
Shiru ta sake yi Saida Mama dake zufa ta tabata tana cewa
"Kaddarar samunsa ta riga tafaru a yanzu mafita ake nema ta yanda zaa fuskanci lamarin Dan haka kiyi magana,
Kin ambaci sunan Garba ne ko Gabriel bamu fahimta ba ki bude Baki kiyi bayani dallah dallah asan matakin dauka akansa idan ma wani abin ya Miki"
Ahankali hawayenta suka gangaro ta sauke numfashi me dumi da ciwo ta dago tana kasa kallan kowa ta bude Baki cikin sanyi da tsananin Dana sani sosai a muryanta tace
"Garban Zaadens ne Daddyn cikin......"
Wani salati me karfi Mama ta sake tana kallan bakin Nicky din tinaninta na kasa daukan zancen.
Fiddausi Kuwa cikin sanyi da mutuwan jiki taja Falaq suka bar gurin sbd zancen yayi nauyi da mamakin da kan Falaq ma ganin take bazai dauka.
Sayd guri ya nema ya zauna a natse sbd dai garban Zaadens din take nufi kenan ba wani garban ba.
Jannah Kafe Nicky tayi da idanuwanta da sukai jajir tana kokarin karantar idan ba sharri zataiwa garban ba sbd Kanta da zuciyarta bazasu taba dauka wai Muhammad dinsu ne zai zama uban cikin Nicky wanda kwata kwata ma basu San juna ba a ganinta bare Kuma tayaya ma wani abin me kama da wannan zai shiga tsakaninsu,
A ina? Ta Yaya?
AZIZ ma kasa kwantar da zancen yayi cikin kansa ya sake Kallanta ganin tana kuka cikin tausayi da kokarin dawo mata da hankalinta jikinta ya ambaci sunanta tareda nuna mata kusa dashi yace ta dawo Nan ta zauna.
Miqewa tayi jiki a sanyaye idanuwanta jajir ta dawo gefen nasa ta zauna ya juyo ya fuskanceta da Kyau yana sake daidaita nutsuwarsa akanta ya bude Baki yace
"Aysha kikace Garba ne??
Gyada kai tayi hawaye masu dumi na gangaro mata.
"Garban Zaadens???
Sake gyada Masa Kai tayi tana kallansa da idanuwanta masu ja da hawaye.
Handkerchief dinsa ya ciro me tsananin kamshinsa ya miqa mata cikin kulawa kafin ya sauke numfashi me zafi yana kokarin controlling tsananin fushinsa da bacin ran dake tafaso Masa sbd kada ya firgita Nicky din da babyn cikinta ya Dan dauke idanuwansa daga Kanta yana sake danne kansa kafin ya sake Kallanta yana bude Baki yace
"Raping naki yayi k.....
Cikin tsananin quncin dake tafasa a kirjinta Jannah dake kallan yanda yakewa Nicky din ta katsesa da cewa
"AZIZZ"
Bai juyoba yayi Shiru yana qara hadiye nasa bacin ran shima
Nicky data bude Baki zatai magana Jannah ta miqe tana kallanta tace
"Karki batawa Garba suna pls Nicky ki fada gaskiyan waye me cikin nan sbd garba bazai taba aikata wannan abin da kike kokarin maqala Masa ba"
Dawo da kallanta kan AZIZ din tayi Wanda yake kallanta da mamaki tace
"Tayaya zaka kira Kalman raping ga Garba??
Nicky cikin wani irin kuka Mai tsima xuciya tace
"Wallahi tallahi na Garba ne,
Cikinsa ne na rantse da Allah Shima aka tambayesa zai fada"
AZIZ da maganar take sake caza kwakwalwansa kallan Mama yayi yace
"Mama a shiga da ita dakinta ta huta gobe zanga garban dama duk Wanda ya tsaya Masa"
Yana fadar Hakan ko juyowa baiyiba ya kama hannun Jannah wadda ta fizge da karfi tana kallansa masifa na cinta zuciyarsa na mata radadi.
Wucewa tayi tabar gurin kirjinta na sake daukan zafi Kai tsaye Palonsa ta nufa tana isa ta tsaya kirjinta kaman zai tsaga da tsananin bacin ran kalamansa da abinda yayi din tana Jin shigowansa ya juyo a fusace zata fara magana ya rungumeta jikinsa gabaki dayanta yana neman nutsuwa da kwantar da nasa bacin ran dayake tafasa a kirjinsa Dan ita kadai ce zata basa wannan sassaucin.
Turesa ta fara yi da karfi tana dukan kirjinsa tana hawaye cikin fushi tana cewa
"I hate you for real AZIZ LIMBA,I hate you......
Sake qanqameta yayi jikinsa kalamanta na ratsashi suna tsananta radadin dayake zuciyarsa ya rufe idanuwansa yana sake rungumeta tsamtsam a kirjinsa yana nemo kansa dayake neman gushewa.
Kuka ta fasa Masa tana ci gaba da turesa tana jin gidansu kawai take son komawa gurin familynta taci gaba da turesa tana kuka tana cewa
"I hate you AZIZ LIMBA"
Cika kunnuwansa maganganun nata sukai suna yanka xuciyansa Dan haka ya saketa a hankali take ta nufi kofa da gudu zata fice tabar gida gabaki daya sai Kuma ya kasa barin Hakan Dan haka ya sake riqeta yana rungumeta ta baya a jikin kofar daya kasa barinta budewa ya saka kansa wuyanta yana rufe idanuwansa yana sake Jin kukanta na ratsasa.
Karewa karfinta ya fara yi sbd yanda take turesa da kukan duk sun fara cinye karfinta da kuzarinta ta fara sanyi tana cewa
"Ya barta tafiyarta zatayi ita ta dena sonsa gaba daya"
Juyo da ita yayi yana zubawa fuskanta data lalace da hawaye sosai har lokacin kuka takeyi na wani irin kishin dayake neman kasheta da Kuma kalamansa akan garba.
Lura da Hakan tareda karantar Hakan sosai ne ya sakasa sauke numfashi me dumi yana gano fushinta cikin wani irin sanyi ya ambaci sunanta zaiyi magana ta sake kokarin turesa Wanda Hakan ya sakasa dafeta jikin kofar yana Kai fuskansa Kai tsaye ya hade bakinsa da nata yana hanata fadan maganganun datake fada Masa masu soya zuciyarsa.
Turesa take kokarin yi daga bakinta amma yanda ya mata kyakkyawan riqo da jikinsa a jikin kofar ya saka ta kasa kwacewa sai hawaye masu dumi dake gangaro mata tana sake Jin zuciyarta Bata dena zafi ba.
Kissing dinta yakeyi sbd samar musu sassaucin zuciyoyinsu dake wani halin ya dauketa cak yana barin kofar da ita ya isa bedroom dinsa da ita yana wucewa bathroom Kai tsaye yana shiga bai tsaya koinaba sai a cikin bathtub dayake cike da ruwan sanyi masu qamshin Sweetest desire bathperf.
Wata ajiyan xuciya me karfi ta sake sbd yanda sanyin ruwan ya ratsata har cikin Kanta ta bude idanuwanta da suka fara kumbura ta kallesa tana son sake dukansa amma sanyin na ratsata yana kashe jikinta Dan haka zuba Masa idanuwa tayi hawaye na gudu akan fuskar.
Kamo fuskan yayi Shima sanyin na shigarsa ahankali yana ratsasa yana Jin yana samun nutsuwa ya janyota jikinsa ya dorata a sama yana daga qasa suna cikin ruwan ya bude Baki cikin sanyi da rashin iya hayaniya yace
"Bazan taba iya hating naki ba ko a Baki Jannah Zad.......
Wani sabon kuka ta fasa mara sauti sosai Jin abinda ya fada ta tana kokarin barin jikinsa ya sake dawo da ita yana sake hade bakinsu ahankali yana fara kissing nata cikin wata Sonta data gama Masa illa.
A jikinsa ya shigar da ita yana sake samun daman kissing nata cikin ruwan sanyi Wanda ya saka ta fara rage Jin sanyin ruwan tana sake gangaro hawayenta a fuskansu dake hade Dana juna.
Sbd cikinta da bayason sanyi ya kama ya sakasa fitowa dasu ruwan yana zare mata kayan jikinta ya dumamata da ruwa zafi tukuna suka fito da kansa ya saka mata kayan bacci masu kauri suka kwanta babu me magana har lokacin.
Bacci gagarar kowannensu yayi Dan haka ya dago fuskanta ya zuba mata idanuwa yana Dora hannunsa daya akan cikinta.
Irin kallan dayake mata ne ya sakata sauke fuskanta qasa tana dauke idanuwanta daga kansa tareda bude Baki cikin tsananin sanyi da muryanta data Dan toshe sbd rigimar datai Masa a sanyaye tace
"AZIZZ" alaman ya dena mata kallan.
Tana rufe bakinta ya daga yanda take ambatar sunansa koyaushe da wani irin sauti dayake tada gashin jikinsa ya Dora bakinsa akan nata yana zira harshensa ya tsotso cikin bakinta da yai missing taste nasa yana lumshe idanuwansa ya Dorota saman jikinsa gabaki daya yana kwance ya sake hade bakinsu suna kissing juna ahankali yana Jin cikakkiyar nutsuwarsa na dawowa jikinsa.
Zaune ya tashi da ita a jikin nasa yana zare rigar jikinta ahankali yana bin fatar wuyanta da kirjinta da wasu kisses masu sanyi hannuwansa na yawo a kan cikinta zuwa cinyiyinta da suke zagaye dashi ya saka harshensa ya lashi kirjinta da Saida tsigar jikinta ta miqe gabaki daya tayi baya ya tarota yana sake hade bakinsu a zafafe da tsananin shauqin junansu suna fidda numfashi me sanyi da kewan juna.
Sbd cikinta ya saka ya ringa binta ahankali yana rikitata har Saida suka gama lalacewa a gadon tas sun watsar da komai nasu kafin yaiwa kafafunta wata kyakkyawar warewa akansa yana sake hade bakinsu yana kissing nata sosai cikin wata irin salon da Bata saniba kawai tajisa yana bi da ita Kuma har lokacin bakinsa na hade Dan haka idanuwanta suka rife wani numfashi me karfi suke sakewa yana Jin motsi tako ina a kansa.
#MAMUH
07019691719*_KALBIM_*
Mamuhgee
Book 2
Chapter 75
Baccin nutsuwa sukai sbd tsawon lokacinda suka dauka ba tareba ba qaramin kewan juna sukai ba dan haka washe gari late suka tashi bayan sunyi Asuba kenan sun koma.
Sai karfe 10 na safe ya tashi daga baccin datakeyi me nutsuwa a cikin jikinsa Wanda shi ya jima da tashi amma bai sauka ba sbd a cikin jikinsa take da haka wayarsa kawai yake Dan dubawa yana Dan kallan fuskanta akai Akai har Saida ta farka Dan Kanta.
Tana bude idanuwanta akan fuskansa ta saukesu tana zuba Masa su tana kallansa tanajin hannunsa daya yana shafa cikinta ahankali.
Hannunta daya ta Dora akan nasa dayake kan cikin ta lumshe ido ta bude Baki a sanyaye tace
"Good morning"
Idanuwanta ya kalla cikin kasala kafin ya Kalli bakinta dayayi maganar ya kai bakinsa yayi kissing hancinta tukuna yace
"Barka da tashi Mrs LIMBA,ohh na manta kaman jiya kince kin dena auren kin sakeni ko??
Turesa tayi tana Bata fuska tareda tashi daga jikinsa tana Harararsa ta sauka gadon tana nufar bathroom.
Saukowa yayi ya bita yana murmushi daga shi sai short din bvlgari daya manne Masa a jiki.
Ko daya shiga tana kokarin fara brush Dan haka qarasowa yayi ta bayanta yana saka kafarsa cikin towel dinta ta qasa yana ziro kansa wuyanta ya dauki bush yana farawa sunayi tare yana sake shafa cinyoyinta ahankali da kafansa.
Sun Bata lokaci kafin suka gama shiriritan sukai wanka suka fito.
Itace ta fara fitowa ta shirya cikin doguwan riga sbd sune kayanta yanzu.
Shima shiryawa yayi cikin milk kaftan da hula tareda gold Rolex watche qamshinsa na tashi kaman koyaushe yana gauraye hanyar dayake bi.
Fitowa sukai Kai tsaye Jannah na zare hannunta daga nasa ta nufi hanyar dakin mama.
A hanya suka hade da Falaq Dan haka tare suka qarasa Falaq na maqale gefenta tana Jin farin cikin dawowan Jannah cikinsu da baby limba dinsu.
Suna isa dakin Mama na zaune tana waya da Ummah tana sanar da ita masifar da suka kwana suka wayi gari a cikinta.
Ummah Mummunan tashin hankali ta shiga tana kasa ta inda ma zata fara fadar wannan masifar a zaadens da haka zatai Shiru sai AZIZ din yazo kaman yanda suka San sai ya iso din sbd fuskantar yanayin.
Kashe wayar mama tayi tana kallansu fuskanta a Dan sake da suma cikin nutsawa da girnamwa Jannah ta qaraso tana gaidata.
Amsawa Maman tayi tana sake Dan rarrashinta akan kada tayi fushi da AZIZ akan abinda yanzu dukkaninsu sukeji daga Nicky din Kuma idan har tace garba ne shi dinne idanma ba shi bane ai bazaa yanke hukunci ba sai anji daga garesa Shima garban koda nasa ne ma yace ba nasa bane ai babu abinda zasu Masa sbd Nicky da babynta sai sun riga sun zama amanarsu duka Dan haka zasu kula da ita su taru su Rena abinda zata haifa.
Shiru Jannah tayi kafin ta sauke ajiyan xuciya tana cewa Allah ya kawo mafita a lamarin to.
Shigowan AZIZ dinne ya saka Mama kallansa tana sake fuskanta sosai da kulawa
Falaq ma tashi tayi tana isa gurinsa ta Dan kama hannunta daya tana tsayuwa gefensa tace
"Ina kwana besty"
Amsawa yay yana qarasowa ya zauna yana gaida Mama wadda itama take amsawa tana cewa Falaq Sam ta kasa sanin ta girma a gurinsa.
Jannah miqewa tayi ta fice daga dakin tana neman fiddausi wadda sai a lokacin itama ta fito sanye da riga da wandon Rissap palazzo da qaramar hula a Kanta tana kamshi me sanyi.
Kitchen suka nufa sbd yunwar gaske Jannah din takeji.
A kitchen din ta hada tea da biscuit Tasha suka fito lokacin kowa ya fito breakfast suka zauna aka fara cin abincin hadda Nicky dake zaune gefen Mama tana rarrashinta akan taci abincin sbd damuwan data sakawa Kanta.
Suna gama breakfast Jannah ta matsu yace ta tashi su tafi amma Shiru babu zancen komai haka ya fice gidan ya barta ta ringa Kiransa a waya bata samu har se yamma ya dawo yashige.
Tana sane da dawowansa taqi baro dakin fiddausi