Showing 27001 words to 30000 words out of 149705 words

Chapter 10 - Jalilah Book One Complete Hausa.doc

Ayusher   

28 Oct 2025

607

tsautsayi yazo da mutuwa fa?"

? Inna tace "kin min shiru ke kuma ko kuwa?"
Mumy tai shiru, Inna ta kalli Abubakar tace "zanyima tambaya ta farko kuma ta karshe akan harkar Jalila, da ita da company dinmu wanne kake ganin yafi cancanta a ceta?"
Dady ya kalleta jiki a sanyaye, tace "ina jinka."
Yace " ba dogon nazari Inna kinsan company yafi, sai dai......."
Tace "magana ta kare, daga yanzu kuma? daga kai har Fatima sai ku bar komai a hanuna, yarinyar nan dai ba gidan yankan kai zamu kaita ba, ba gidan yan shaye shaye ko talakawa zata ba, mezaisa kudinga haka?"


? Dady da Mumy sukai shiru, can tace "ina takardar asibitin?"
Dady ya zaro a aljihu ya mika mata, nan suka fito.

Dady na shiga daki ya zauna a bakin gado ya shafi fuskarsa sannan yai wani irin ajiyar zuciya.
Kusa dashi Mumy taje kusa dashi ta zauna, tasa hannunta a kafarsa.
Hannunsa ya sa ya zare hannunta daga jikinsa yace "Fatima duk yanda naso nai tunani akan abin nan i think this is not right."
Hannunsa ta kamo tace " let us save the company first, in komai ya daidaita sai musan ya zamuyi da Jalila, karka damu."

? Kai ya daga alamar gamsuwa, sannan ta jawoshi jikinta ta rungume.
Shiru yai yana tunani, tabbas company dinsu shine darajarsu sai dai idanun Jalila sun tsaya mai a rai.

*********


? Yau duk yanda taso tai bacci ta kasa, juyi kawai take tana kara karanto rayuwar mahaifiyarta, tabbas dolene yanzu ta dau damarar taimakon mahaifiyarta, insha Allahu yau ne rana ta karshe da Mahaifiyarta zata zubar da hawaye, tunda a tsawon rayuwarta ta kula rabi na bakinciki da zubar da kwalla ne, sai dai ta yaya zata temaki mahaifiyarta?

? Hawayenta ta share, kalaman Inna ne suka sake dawo mata, haka tai ta juyi har batasan sanda bacci yai gaba da ita ba.

******

Washegari Ummy bayan anyi sallar azahar ta fito da lefe dan kara dubawa ita da yan uwanta, Ameera na ta zungurin Aina'u dan tasan Aina'u na san Hassan.
Aina'u tai murmushi kawai ta mike tai ciki.
Hassan kam dama tunda ya fara jin hayaniyar mutane ya bar gidan, da Sagir akai ta hidimomin.

Bayan la'asar aka kawo lefe gidansu Jalila, yan uwan Mumy me suka karbi lefen, ganin uban kayan da aka kawo, dan akwati set biyu aka kawo masu dan karen kyau da tsada, sannan kayan dake ciki, ba'a magana, yan uwan Mumy sukai ta mata fada akan ta bark dan masu kudi yaso yar da ke zaune a gidansu a maimakon yarta, in taji haka murmushi kawai take sai tace wai ai so ba ayi masa dole.

? Haka yan kawo lefe suka tafi bayan an tsaida biki sati biyu.
Ameera ce ta sanar ma Mumy cewa Ummy tace angon zai zo gobe dan yaga Amarya.
Ana watsewa Mumy ta hau sama da sauri ta sanarma Inna.
Ganin abin bai damu Inna ba tace "Inna kina tunanin Jalilan zata yarda taje?
Inna tace " ki tura mota a daukomin Jalila zanyi magana da ita."
Mumy tace "me zakice mata?"
Inna tace "ba ruwanki, ke dai ki yi abinda nace."

? Mumy ta mike ta fita.
Jalila na zaune duba dan karatun da Goggo ta d'ora mata na islamiya, dan itama Goggon ba wani nisa karatun nata yai ba.
Goggo na kwance tana bacci, dan da safe sai da aka tsaga kafarta akai mata aiki, aka daye fatar gun aka wanke.
? Amsa sallama tai sannan ta kalli kofar, Sultan ne ya shigo ya ajiye kular abinci sannan ya kalleta yace "ya mai jikin?"
Tace da sauki Sultan.
Yace "Inna na san ganinki."
Tace "akan me?"
Ta fada tana kallan Goggo, ganin tana motsi yasa ta mike da sauri ta kamo Sultan suka fito, tace "akan me?"
Yace "ban sani ba wlh, amma jiya dai naga mata sunzo da akwatuna, naji kuma ana cewa naki ne."
? Tace "Mene?"
Shiru yai ganin yanda tai, yace " menene? Baki sani ba?"
Idanunta ne ya ciciko tace "Sultan zaka iya zama agun Goggo naje na dawo?"
Yace " ba matsala."
Tace"nagode Sultan, dan Allah ko ta tambaya kace mata naje gida dauko kaya ne."

Ya daga ai.
Mota ta shiga drivern ya ja, tunda ta shiga jikinta ke rawa har suka isa.
Haka ta fito da kyar ta shiga cikin gidan.
Yasmeen na falo ita da Mumy, gaishesu kawai tai ta wuce.

? Inna na zaune ta shiga, sai da ta zauna sannan ta gaisheta.
Bata amsa ba ta ajiye mata farar takarda a gabanta.
Jalilata kalleta tace "Na menene?"
Inna tace " duba ki gani."

Jalila ta sa hannu ta dauka, receipt ne da aka bada a cashier, ga kuma tambarin asibitin Standard a jiki.
Kallan Inna ta sake yi, Inna tace " Bakiyi makaranta bane?"
Jalila ta kara kallan takardar, kudi ne zunzurutu wanda aka biya, na daki da kuma na aikin da aka mata da na treatment, sa dai bataji su a gunsu kudi ne mai yawa.

Kallan Inna ta sakeyi dan bata fahimci me takesan nuna mata ba.
Inna tace takardar kudin da muka kashema Mahaifiyarki ne.
Jalila tace "na gani angode Allah ya saka....."
Inna tace " Biya zakiyi."
Jalila cikin rashin fahimta tace "bangane ba."

Inna tace "kina tunanin kina zaune a gidan mu, mun saki a makaranta, mun kula dake da mahaifiyarki, mun biya mata wannan kudin, sannan kice ba zakibi umarnin mu ba?"

? Jalila tace "Inna......."
Inna ta katseta tace "yaya? Kina da kudin da zaki biya mu dai ko?"

Idanunta ne suka kara firfitowa ta fara zubarda hawaye, Inna tace " in har kinfi karfin bin umarninmu sai mu zare hannunmu daga rayuwarku sai inga yanda zakuyi, ina fatan kinada inda zaku zauna da kuma kudin da zaki cigaba da kula da mahaifiyarki harta warke."


? Jalila tasa kuka tace "Inna dan Allah kiyi hakuri, Goggo tana neman kulawarku dan Allah ki yafemin."
Inna ta mike tace " tashi ki fita, na baki daga yau zuwa gobe da safe inhar baki bi umarnin mu ba, zansa a koreta daga asibitin, sannan kubar gidan mu bayan kin biya kudin."

? Jalila ta zauna tana wani irin kuka mai ban tausayi, Inna tace "tashi ki fita."
Mikewa tai tana hawaye ta sauko.
Yasmeen na mata magana ko kallanta batai ba ta fito tana hawaye.
Bangarensu ta nufa kawai ta zube akasa tana kuka, ya zatai? Uncle ne ya fado mata, da sauri ta janyo jakarta ta zaro wayar nan.
Ganin irin kiran da yai mata yasa ta saurin danna kira, ringing take ta yi ba'a daga ba.

Shikuwa a lokacin Ummy ta nemi ya rakata store, sai daya shiga mota ya tuna yabar wayarsa a gida.
Sai dai ganin ba wani dadewa zasuyi ba yasa ya fita kawai.

?? Kuka ta shiga yi sosai da taga bai daga ba, kira take tayi ba kakkautawa.
Ganin ba dama ta cila wayar kan gado ta fito rike da jakarta.

Tana tafe tana kuka, drivern na mata magana ko bi takansa batai ba tai waje.
Tana tafe tana wani irin kuka.

? Sai da ta mike layinsu sosai, taje tsalakawa ta titi shi kuma ya taho saura kiris ya bugeta, wani irin burki yaja da karfi sannan ya kifa kansa da sitiyari.

Jikinsa ne ya shiga karkarwa, Jalila kuwa ta dauka karshen rayuwarta yazo har ta tsugunna, ganin bai kade ta ba kawai sai taji wani irin kuka yazo mata.

? Tsananin tsoro yasa zufa ta shiga keto mai, da kyar ya iya fitowa daga motar, kusa da ita yazo yanda yaji tana kuka yasa yaji kansa na wani irin juyawa, dan tabbas ya dauka ya mata illa, dan uwansa ya hango alokacin da matsalar da bazai taba mantawa ba ta faru, numfashinsa ne ya shiga sarkewa, hannunsa yasa a wuyansa yana wani irin abu.

Jalila ta dago, ganin mutum na neman zubewa yasa hankalinta ya tashi.
Da sauri ta shiga yin ihun neman taimako.
Mikewa tai zata nemo mutane, hannu yasa ya riko siket dinta.
Juyowa tai da sauri tare da tsorata.
Da kyar yace " ba bige nai ba?"

? Gaba daya ta tsorata dan ta dauka shi aka bige.

Siket dinta ta fizge ta tsaya tana kallan sa.
Mikewa yai sannan ya matso kusa da ita, matsawa ta dan yi.
Ya kara matsowa fuskarsa a hade, kara matsawa tai cikin tsoro.
Yace " meye dalilinki na tsugunnawa akasan motata da sa mun kuka?"
Jalila ta kalleshi tace " motarka ce?"
Yace "tambayarki nake?"
Ta kara kallan motar sannan ta tuno abinda ya faru da irin mai motar, da alama duk masu irin motar nan basuda mutunci.
Tace " na dauka ma hakuri zaka bani, tunda kasan na tsorata."

Baya san magana amma yanda tai maganar yasa ransa ya baci yace " me? Hakuri?"
Ta daga kai, kallanta yai, harzai sake magana sai kuma naga ya fasa, motarsa ya koma ya shiga ya fizgeta da gudu.

? Jalila ta harari motar, ta cigaba da tafiyarta tana matsar kwallarta.
Da alama yau gaba daya ranar bakin ciki ce a gareta.



#ONELUV=ؕ?
[08/10, 02:08] * +234 803 222 1758, : =??? *JALILAH* =???

Written By : *AYUSHER MUHD*
Wattpad: *Ayusher Muhd*


*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*

(_D home of expert and perfect writer's_=ء?)

*No 17*


A hankali ta tura kofar dakin, Tana kokarin shiga nurse din na kokarin fita, jiranta tai ta fito maimakon ta shiga sai tabi nurse din.
Tana gaisheta, Nurse din ta tsaya ta amsa, Jalila ta matso tace " Aunty ya jikin Goggo?"
Tace "da sauki, ya akai? Kina tsoro ne?"
Jalila ta goge kwallarta tace " Aunty kina ganin kamar kwanaki nawa zamuyi kafin kafar Goggo ta samu sauki?"
Tace "maybe 3 to 4weeks"
Jalila ta zaro ido tace "da tsayi haka?"
Tace "Umm."

Jalila tai shiru, Nurse din tace " ba wata tambayar?"
Jalila tace "in tabar asibitin fa?"
Nurse din cikin mamaki tace " ta ya za'ai tabar asibitin tana cikin wannan state din? Ko asibitin kuke san canzawa?"

Jalila ta runtse ido can tace " Aunty kudin ne......."
Muryar Sultan taji yace "me kike anan?"

Idanunta ta bude da sauri, Nurse din ta wuce ganin kamar bazata iya magana ba.
Sultan ya karaso yana kallanta.
Ya kara cewa "me kike anan?"

Jalila bakinta ne ya shiga rawa ta kasa magana, Hannunta ya rike yace "meye hakan?"
Kamar ya tabota kawai tasa kuka, mamaki ya kamashi can yace " Mumy ce?"
Kai ta girgiza, yace "Dady ne?"
Nan ma kai ta girgiza, sam bai kawo Inna ba saboda ba kasafai take shiga harkar rayuwar gidan ba, yace "Jikin Goggo?"

Hawayenta ta share tace "Sultan ya zanyi?"
Yace "name?"
Tace "tsakanin rayuwata data mahaifiyata."
Yace "wace irin tambaya ce wannan, sannan in amsa
kike so ai ke yarinya ce mai kuma lafiya, ita kuwa Goggo ba lafiya ne da ita ba."
Jalila ta shiga daga kai tana cewa "haka ne, Goggo itace gaba da komai."
Kallan mamaki ya kara mata, ta kakaro murmushin takaici tace "nagode Sultan."
Leda ya miko mata yace "gashi, Ni bari na wuce."

Tace "kai kadai?"
Yace " inada kudi a jikina, nan ya zaro dubu biyu yan dari biyar biyar, mika mata dubu daya da dari biyar yai ya maida dari biyar aljihunsa yace " gashi ko zaki sai wani abin."

Ta amsa tamai godiya, juyawa yai ya fita, da kallo ta bishi sannan ta goge fuskarta ya tura kofar dakin.

Goggo na zaune shiru ta shiga, Jalila ta karasa tana cewa "Goggo a zaune kike?"
Goggo ta kalleta tace "kin dawo?"
Tace "eh."
Jakar hannunta ta kalla tace " baki daukon kaya ba?"
Jalila ta bude baki tace "wayyo, wlh na sha'afa sam, ni fa dama jakar nan kawai naje daukowa."
Goggo ta kalleta cikin zargi tace " me ya samu idanunki? Abubakar ya miki wata magana ne?"

Ta zauna kusa da ita tace "Kai Goggo, ni ko ganinsa ma banyi ba."
Goggo tai ajiyar zuciya tace " sai yaushe zamu bar asibitin nan?"
Jalila tace "tab aima ki gyara zama goggo, dan wlh yanzu Nurse take cewa sati uku zuwa hudu."
Goggo cikin mamaki tace "Wannan asibitin mai tsada? Kina tunanin zasu biya mana kudin?"
Jalila tai murmushin takaici tace " karki damu da wannan, ke dai ki kwantar da hankalinki, kinji dai mai likita yace jiya."

Goggo tai murmushi, Jalila ta bude ledar da Sultan ya miko mata, ruwa ne mai sanyi faru tace "ruwa kika aikeshi?"
Tace "Allah sarki Sultan cewa nai ya bani ruwa in akwai, ashe wai babu shine naga ya fita."
Jalila a ranta tace "dama sai a dinga kawo abinci ba ruwa."

Haka tai ta kokarin boyema Goggo damuwarta.

*********


Sagir na komawa gida ya hau sama dan dauko wayarsa, ganin irin kiran da Jalila tamai yasa hankalinsa ya tashi, nan ya shiga buga mata waya shima, sai dai duk yanda ya kira No Answer kawai ake rubutamai,

Fitowa yai ya shiga mota ya tafi makarantar su, ba ta nan, ya akai baiyi tunanin amsar address din ta ba? Wai shi yana ganin yasai mata waya, kwatancen gidansu bazai zamarmai wahala ba.
Kai ya shafa cikin takaici, ina ne gidansu? Haka ya dawo gida jiki a sanyaye.

Abba ne bayan Magrib ya shiga d'akin Hassan, yana zaune rike da littafi a hannunsa yana karantawa, Jornal ne.

Yana ganin Abba ya rufe littafin sai dai baiyi motsi ba daga inda yake bai kuma yi magana ba.
Abba ya shiga ya zauna kusa dashi, Shiru ne yadan ratsa dakin, can Abba yace " Me zakayi gobe?"
Hassan ya mai kallan mamaki, me zaiyi? Shi daka rayuwarsa ai kullum iri daya ce, Abba ya kalleshi yace "Gobe da yamma ko bayan magrib kuje kai da Sagir ku ga yarinyar."

Kallan Mahaifinsa yai cikin mamaki yace " inje ince mata me?"
Abba yace "kaje ku gaisa ta ganka, ka ganta."
Hassan yai shiru can yace " Ai wannan tun a farko ya kamata kuce naje, Abba abinda ya kamata kuyi tun farko kenan, ta ya zaku sa rana ba tare da yarinya ta ganni ba?"
Abba yace "Hassan bakasan me nai ba akan samar maka abokiyar zama."
Hassan ya kalleshi yace " me kake nufi?"

? Abba ya mike yace "Ka taimaka gobe kuje kai da Sagir, wannan rokone uba yake ma dansa."

Hassan yai shiru baice komai ba, fita Abba yai tare da rufe mai kofa, shiru Hassan yai yana tunanin wannan abun, shi gaba daya ya kasa hasko rayuwarshi da wata mace, macen ma wacce bai sani ba.


? **********

? Wajen karfe d'ayan dare ta mike daga kwanciyar datai dan dama ba bacci take ba, fitowa tai daga dakin ta zauna a kasan matatakalar benin, shiru tai tana tunani, ya zatai? Gaba daya duk yanda taso ta canza shawarar dake zuciyarta in ta auna lafiyar mahaifiyarta wacce ta rayu cikin bakin cikin da namiji bataji zata iya canza wata shawarar, rayuwar mahaifiyarta itace gaba da komai a rayuwarta.

? Kanta ta kwantar akan gwiwowinta tana tunano rayuwar da sukai da Sagir da irin rayuwar da tai fa mafarkin yi dashi.
Wasu zafafan hawaye ne suke zubo mata, a wannan rana bacci baiga idanunta ba.

Wajen karfe 1o aka kawo musu abinci sannan drivern yace mata "Inna na jiranki."

? Ta fahimci me yake nufi, kallan Goggo tai tace "Goggo zanje na kwaso kayan, akwai abinda kikeso?"
Nan ta fada mata abubuwan da takeso ta taho mata dashi, har zata fita sai ta dawo da sauri ta rungume Goggo idanunta na neman kawo kwalla.
Goggo tace "Jalila menene? Badai jiya karya kikamin ba? Ance miki wani abun a gidan ko?"
Dagowa tai tana dariya tace "Goggo kenan, kema kinsan bana iya boye miki komai a dunia, me zaisa in ki sanar dake? Inaji fa ganin kin kwanta yasa jikinsu yayi sanyi da zancen."
Goggo tai tsaki tace " duk yanda naso in zauna dasu lafiya in har suka sake suka miki zancen hadin aure wlh sai sunsha mamaki."

Jalila tace "ni inada ke a duniya me zaisa inji tsoro Goggona?"

Murmushi sukai a tare, Jalila ta juya ta fara takawa a hankali, daga sanda tasa kafa tabar dakin nan ta shiga motar ta tabbatar rayuwarta shikenan ta canza, bazatai dana sanin fita daga dakin nan ba kuwa?
Ai dana sani tun kafin ta fita tasan rayuwarta lalai tana cike da danasani, domin kuwa batasan wani irin zama zatai ba.

? Sai data kai kofa ta juyo tama Goggo murmushi sannan ta fita.
Mota ta shiga tai shiru tana kallan waje, mutane take ta kallo kowa yana nasa rayuwar, haka har suka isa gidan.
Sai dayai kusan minti biyar da parking sannan ta bude kofar ta fito.

Inna ta kalli Mumy dake leken window ta dakinta, Mumy da sauri ta juyo tace "ta iso kuwa Inna."

Inna ta kalli Dady tace " sai ka kyautata mata kai kuma, ka tabbatar bata nunama mijin nata tsana ba."
Dady yace "to."??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????
Mumy ta matso tace "Dadyn Yasmeen let us try our best."
Murmushi yai mata na dole sannan ya mike.
Inna tace " in zaku siyo ragowar kayan gida kudinga daukanta a asibiti."
Yace to, sannan yai waje.

Yana isa falon tana shigowa, tsayawa tai tana kallansa, wai mahaifinta? Wanda hakkinta ke rataye a wuyansa?
Dady ne ya matso kusa da ita, ya sa hannu a aljihunsa yace "Jalila ya mai jikin?"
Kallansa kawai take batace komai ba, sai idanunta da sukai ja, bata amsa mai ba.
Yace "me kike tunani?"
Kai ta girgiza alamar bakomai tace " kawai ina tunanin yanda Allah ya rataya wa uba hakkin dansa a wuyansa ne."
Dady yai shiru, zaiyi magana Mumy ta karaso tace "Jalila, yanzu muke shirin zuwa asibiti."
Jalila tai shiru a ranta tace "tunda kunsamu abinda kukeso ai dole."

? Nan ta haura sama batare da tace komai ba.

Inna na zaune sai data zauna sannan tace "YA YA? Kin yanke shawarar?"

? Jalila ta kalleta dan tana tsananin shakkarta ta daure tace "Amma kimin alkawari biyu."
Inna tace "inajinki."
Jalila tai shiru kafin tace " da farko zaku kula da Goggo, zaku samo mata wacce zata dinga taimaka mata, sannan na biyu karku fada mata komai har sai ta samu lafiya."

Inna tace "duk ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login