Showing 9001 words to 12000 words out of 149705 words

Chapter 4 - Jalilah Book One Complete Hausa.doc

Ayusher   

28 Oct 2025

605

da Mumy da mijinta ta kalla, sannan ta zauna tare da bude littafin da take karantawa, wanda jin matsalar nan ya sa ta ajiye.



? Su Jalila an shiga tarkon kauna tunda Sagir ya bayyana mata zuciyarsa, yau komai take in ta tuna kalamansa sai dai kaga tana murmushi ita kadai, yau aikin gidan ko wahala bai bata ba dan yau zuciyarta a cikin shauki take.
Nace Hmmmmm


#Oneluv=ؕ?
[08/10, 19:18] * +234 816 365 0557, : =??? *JALILAH* =???

Written By : *AYUSHER MUHD*
Wattpad: *AyusherMohd*

*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*
(_D home of expert and perfect writer's_=ء?)


*No 6*


? Kamar hadin baki yau Sagir da Jalila wani irin bacci sukai mai cike da mafarkin junansu, Jalila bayan tayi sallar asuba ta kalli Goggo dake jan carbi sannan ta gaisheta.
Goggo ta amsa sannan tace "Jiya na kula a farinciki kike Allah ya kara kawo farinciki mai d'orewa a rayuwarki."

? Jalila tace "Ameen Goggo."
Sannan ta d'ora da cewa "Goggo kidinga min addu'a inkin yi sallah Allah yasa na auri wanda yake sona nima nake sanshi wanda zai kularmin da ke."
Goggo ta daga carbi alamar zata zula mata,da sauri ta matsa tana dariya.
Goggo tace "wato gaba d'aya yanzu kinci idon akuya ko? Na kula kwanan nan fitsara kike ji sannan aure kikeso."
Tace "Goggo daga cewa amin addu'ar miji sai kice aure nake so?"
Goggo tace "bazakuwa ki daina cewa Miji ba kuwa ko?"
Jalila tace "Goggo kice komai na a rayuwa, ni ba kawa ba in ba a boko ba, ni ba kowa ba, kedin dai kece komai na, kinga kuwa dole komai na nasanar dake."
Goggo tadan murmusa sannan tace " kashe fitilar nan ga haske nan ya fara shigowa, kinga kar battery dinmu yai sanyi."
Jalila ta kashe sannan ta mike tace "Na tafi bauta."
"Bauta? Kai Jalila bakida dama."
Har takai kofa ta juyo tace " Allah ya taimakemu an daina bauta amma wasu karfi da yaji nema suke su mai dani baiwa." Ta fada tare da bude kofa, Goggo tai murmushi tare da bin bayanta da kallo, tace "a koda yaushe addu'ar miji na gari zan miki Habiba."

? Jalila na fita ta zagaya ta baya inda kofar kitchen take dan tanan take shiga wai dan kar ta tashesu daga bacci, kwanukan da akaci abincin dare ta hade guri d'aya sannan ta zauna ta soma fere dankali, tana d'aura mai ta shiga yin wanke wanke, tana zubawa tana gyaran kitchen, tana gamawa tasa tafashen naman kaza sannan ta fito falo ta fara shara, haka ta gama shara tai goge goge, tana gama abinci lokacin suke fitowa daga daki alamar tashi daga bacci, nan ta shiga dakuna ta gyara ta wanke toilet sannan ta fito ta dafa ruwan tea, ta dau bread din da aka ajiye domin su, nan ta fita.

Tana zuwa ta fada wanka tana fitowa ta zura kaya sannan ta shafa mai, duk abinda takeyi tanayi tana duba agoggo, tana fitowa falo Goggo ta miko mata tea a kofi tace "zauna."
Jalila ta kalli agoggo taga bakwai da ashirin, da sauri tadan kurbi shayin tadan gutsiri bread kadan tadan ci, tana jin alamar tada mota ta suri jakarta da hijab dinta.
Goggo tace " kidan kara ci mana ai naga motar sai tayi zafi"
Jalila tace "Goggo ai yanzu ba late a rayuwata."
Tai waje da gudu a ranta tana cewa "ina san bari Uncle Ya ganni a cikin late comers?"

? Ta riga su Safeena ma fitowa, a cikin mota ta sa safa sannan tadan karkade sandal dinta.
Safeena ta tabe baki tace "Jalila nikam dan Allah ki daina karkadomin disease."
Jalila ko kallanta batai ba ta kalli madubin gaban mota ta shiga dan duba fuskarta, Safeena ta kara jan tsaki tace "Mutum sai kace wanda zaije tallar kai, sai wani iyayi akemana, ni wlh na tsani iskancin banza."

Jalila ta kalleta tace "ke da wa?"
Tace " tambaya kike?"
Jalila ta tabe baki tace " ba tambaya nake ba dan na kula ke kullum cikin neman masifa kike."
Safeena ta bita da harara.

? Fuskarta ta maida jikin window tana kallan titi tare da tunanin yau da wani ido zata kalli Sagir?
Ita duk kunya takeji.

Yana tsayawa ta sako daga motar sannan tama Yasmeen bye bye.

Tana kokarin shiga makaranta taga mota tayi parking a gaban makarantar.
Jalila ta juya tare da kallan motar, kamar tasan motar nan, kara kallan motar tai sannan ta juya tare da cewa "in ma na san motar meye nawa a ciki?"

? Jitai ance Jalila!
Tsayawa tai dan ta gane muryar mai maganna.
Sagir yasa kanshi a cikin motar bayan ya fito, yace "Yaya godiya, zakaxo d'aukana?"
Kallansa Hassan yai sannan yamai alama da hannu akan ya cira kansa daga cikin motar.

Sagir ya fita tare da daga mai hannu, juyawa yai ya kalli kofar, gani yai bata gun.
Murmushi yai a ransa yace " naji dadin ganinki."
Shiga cikin makarantar yai fuskarsa dauke da fara'a.

Kasancewar yau friday karamar rana ce sannan Sagir shine last period dinsu.

? Kafin ya shigo Jalila ta kalli Zarah tace "Zarah yau bakizo da sosan hoda bane?"
Zarah ta mata kallan mamaki sannan tai dariya tace "yau kece da kanki?"
Jalila ta dan canza fuska tace " in an tashi ba gida zani bane, ba kuma nasan inje fuskata na maiko."
Zarah tace "sai ki bari sai an tashi sai ki nema bawai tun yanzu ba."
Jalila tace "ana tashi nake san tafiya b........"
Gaisuwar dataji anayi ne yasa tasan Uncle ya shigo.
Harara ta makama Zarah sannan ta sunkuyar da kanta kasa.
Uncle kuwa ko kallan ida take baiyi ba har ya fara lesson dinshi.
Ganin baya kallanta ne yasa tadanji ba dadi a ranta sannan ta dago tare da kallan abinda yake koya musu.

? Har ya gama sannan ta fita, yana fita Zarah fa miko mata sosan powder da madubi.
Jalila ta ture hannunta tace "banaso."
Sannan ta maida kanta kan desk ta kwanta, Zarah tace "tashi mu tafi."
Jalila tace " jeki ni sai anjima zan fita."
Zarah ta fita tai gaba, tana kwance har aka wa watse, idanu ma ta rufe kamar mai yin bacci, batasan sanda ya shigo class din ba.
Ya nemeta a waje bai ganta ba shiyasa yai tunanin ajin, kallanta ya tsaya yi yana murmushi, a hankali ta bude idanunta dan jin kamar ana kallanta.
Idanunta ne suka sauka akan fuskarsa shagwabe fuska tai dan ta tabbatar kila tunaninsa da takeyi ne yasa take ganin kamar shine.
Maida idanun tai zata rufe yace " fushi ake da ni ne?"
Da sauri ta bude idanunta tana kiftasu, sannan tai saurin komawa ta zauna, Sagir yace " me kike a class ke kadai?"
Batasan me ya sameta ba kawai ganintai ta wani hade rai wai ita a dole an mata laifi.
Sagir yace "Da alama wannan Malamin yayi laifi kenan?"
Kallansa tai fuska a hade tace " ba kai bane dazu ko kallan inda nake bakai ba?"
Tayi mamakin canzawar ta da kuma yanda take magana, a ranta tace "Lalai Jalila wato kin zama kwarariya."

FSagir samun kansa yai da darawa sannan yace " Nayi laifi, sai dai kin manta dazu Uncle Sagir ne? malamin student a ajin?"
Tace "Yanzu fa?"
Yace "Yanzu kuwa Urs Sagir ne."
Da sauri ta sa hannu ta rufe fuskarta.
Kallanta ya sakeyi yace " ba haka bane?"
A hankali tace "Hakane."
Murmushin jin dadi yai sannan yace " tunda na ganki hankalina ya kwanta dan dama Abbana zan raka wani guri, nace bari nazo na ganki."

Kallansa tai tace "Okay, sai Monday kenan."
Yace "Kai! Har sai monday fa ko?"
Tace "ka manta yau friday?"
Fuska taga ya canza yace "gashi naga alama ke ko yar wayarnan baki dashi, anya zan iya jure missing dinki har sai monday?"

? Kanta ta sunkuyar kasa tana murmushi, ajiyar zuciya yai sannan ya matso daf da ita yace "bari nai full charge yanda zan cancana battery dinA."

? Kallansa tai sannan ta maida idanunta kasa tana murmushi.
Ido ya kura mata sosai sannan ya ce "Na tafi."
Sai dayaje kusa da kofa sannan tace "sai anjima."
Juyowa yai sannan ya juya ya tafi.

Ta window ta bishi da kallo, wani zazzafan so na ratsata.

Sam ta shagala da tunani kafin ta farga ta fito da sauri,
Tafi minti goma a tsaye taga dai ba alamar su Safeena, sannan ba alamar? ma d'alibai suna wucewa, lalai ta tsaya soyayya antafi an barta, yau tana cikin wani hali dan tasan masifa kam ba'a magana.

? Tana tafe tana dan mitocinta ita kadai..........


************

?? Inna ce ta kalli Sani sannan ta kalli takardar daya kawo mata dauke da sunan Taura da number sa.
Tace " da ka sake bincike ba wani abu game da rayuwarsa da ta kyalansa bayan matsalar yaran?"
Sani yace "eh gaskiya ba wani abu special, sai...."
sai kuma ye " ba ma dai komai."
Tace "da ke zaka fada?"
Yace dama kamar yaransa maza biyu ne, 'yan biyu babban Hassan sai kaninsa Husaini, sai dai jiya sai aka cemin wai Hassan ne da Sagir sai macen.
Inna tace " ko dai kaine ka manta ba?"
Yace "zai ita yiwuwa inaji Husainin tun yana karami ya rasu."

Tace " Dama ai maza biyu mace d'aya kacemin."
Yace "hakan na sani amma nadauka 'yan biyun ne ashe wa da kani ne."
Inna ta jinjina kai cikin rashin damuwa tace " ba wani abu bayan nan?"
Yace "babu."
Nan ta saka number a wayarta sannan ta anna dialing.
? Sai atai ringing hudu sannan ya d'aga.
A banngarensa yana zaune a bayan mota shi da Ummy, sai Sagir dake zaune a mazaunin driver shi kuma hassan na gefe, suna hanyar zuwa asibiti.
Yana daga wa Inna tai sallama,Abba ya amsa sannan yace "ban gane ba."
Inna tace " Taura nice Hajiyar grain."
Sai daya danyi nazari na wasu dakiku kadan sannan yace "Hajiya ina wuni?" Yai magana tare da canza yanayin maganarsa zuwa girmamawa."
Inna ta amsa sannan tace " Taura ganinka nake san yi ina fatan zaka bani lokaci."
Yace " Haba Hajiya, kina wani gari ne?"
Tace ina kano, ina neman alfarma ganinka sanda kake da lokaci.
Yace " yau dai inada abinyi, sai dai banaji gobe akwai abinda zanyi, a ina zamu hadu?"
Ya fada yana kallan Ummy, tace " gida na zakazo ko nice zanzo ko kuwa a wani gurin zamu hadu?"
Yace " a'a ba matsala ni zan zo."
Tace "Nagode Taura zan turoma da address din gidan."
Ya amsa da to sannan ya kashe wayar, Hassan ya kalla wanda idanunsa ke rufe kamar me bacci sai dai kowa na cikin motar yasan ba bacci yake ba, Ummy ya kalla ya shiga fada mata wacce ta kira.

Gate din wani katon asibiti naga an bude musu, Sagir ya shiga da motar.


*************

? Jalila kam taci uwar tafiya kafin ta isa gida, duk ta gaji tayi ligib.
Tana shiga ta tadda Mumy a bangarensu, gabanta ne ya fadi sannan ta kalli Goggo wanda kuka ne kawai batai ba amma da alama daurewa kawai takeyi.

? Mumy na ganinta tace "kin dawo daga yawon iskancin?"
Jalila fuska ta canza sannan ta kalli Goggo wacce ta tabbatar an kare mata cin mutunci ne, tace " Mumy ban gane b....."
Marin data kifa mata ne yasa ta kasa karasawa sannan ta rike kuncinta, Mumy tace " ce miki akai nan gidan karuwai ne? Ko me?"
Mamaki ya kama Jalila tace " Mumy ban ga........."
Wani marin ta kara kifa mata tace "a gidan ubanwa kika tsaya? Kungurmar munafuka? Dama kwanakin nan na kula bakyasan dawowa tare dasu Safeena saboda kina yawon bin maza."

? Cikin wata irin kakkausar murya Goggo tace " RAMLATU!"

? Kallan Goggo sukai a tare, dan Jalila bata taba ganin ran Mumy ya baci ba haka.



#ONELUV=ؕ?
[08/10, 19:18] * +234 816 365 0557, : =??? *JALILAH* =???

Written By : *AYUSHER MUHD*
Wattpad: *AyusherMohd*

*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*
? (_D home of expert and perfect writer's_=ء?)

*NO 7*

Goggo cikin jin zafin kalaman Mumy tace "Ta ya zaki kira yarinya ta da haka? Kina tunanin 'ya'yanki sunfi na wa ne? A koda yaushe ina jure komai ne badan banajin zafin abinda akema Jalila ba sai dan ina tunanin kila hakan shine zai kawo salama a zuciyarta, komai da kika gani inayi inayinsa ne domin ta, taya ma zaki kalli 'ya a gaban uwarta ki kirata da wadan nan munanan kalaman?"

Mumy ba shakka ta dan tsorata, ta daure tace " ni kike yima fada? Kijira ni."
Tafada tare dayin waje da sauri, tana fita Goggo ta rike kirjinta wanda ya mata wani irin nauyi, ga wani irin dum na tsananin ciwon kai daya fara sara mata, Jalila ta karasa kusa da ita tare da rungumeta tace "Goggo na."
Cikin shagwaba tai maganar, Goggo ta daure dan batasan Jalila ta gane batada lafiya tace " Karki damu, ko me za'amin indai har akanki ne zan ita jure komai."

Jalila ta kwantar da kanta akan kafad'ar Goggo cikin tausayama kansu.
Banko kofar da akai ne yasa ta d'ago da sauri cikin tsoro, Dady ta gani bayansa Mumy ce.
Jalila da sauri ta mike ta tsaya a gaban mahaifiyarta alamar kareta tace "Dady kome ya faru laifi......."
Wani wawan mari daya kifa mata sai data fadi kasa, Goggo ta d'agota da sauri tana tambayarta.
Dady cikin tsananin bacin rai ya kalli Goggo yace "uban wa ya baki dama ki cima matata mutumci?"
Goggo ta kalleshi tace " ni duk mutuncin data cimin bai zama laifi ba kenan?"
Yace " Me yasa bakya abu da tunani? Ko kuwa kwakwalwarki ce bata aiki? Gidan da kike zaune,abincin da kike ci, kayan da kike sakawa, karatun 'yarki duk a cikin arzikin wa kike ci?"
Goggo tai shiru tare da maida kanta kasa, sannan tace " duk da haka banaji tanada damar cima 'yata mutunci...."
"Yanzu yarinya tayi laifi kina nufin tafi karfin a hukuntata ne ko me?"
Jalila ta mike da sauri ta rike kafafun Dady tace "Dady na tuba, dan Allah kayi hakuri laifinane."
Kafa yasa ya hankadata yace " gayyar tsiya."
Sannan ya juya ya kalli Mumy ya dafa kafadarta yace "muje ciki ko?"
Yi tai kamar me share kuka tace "Ba sai danace kayi hakuri ba?"
Juyowa yai ya bugama Jalila wani kallo na takaici daga ita har Goggon sannan ya juya shida Mumy, har sun kai kofa Jalila tace " Dady me kake nufi da gayyar tsiya?"
Wani banzan kallo ya buga mata sannan yace " idan kika sake min magana da wannan vibe din wlh sai jikinki ya gaya miki, sannan kiyi gagawar tasowa kiyi aikin daya kamata kiyi."
Ya juya shida Mumy sukai gaba, Jalila da kallo kawai ta bisu idanunta na zubar da hawaye, kallan Goggo tai kamar zatai magana sai ta fasa, hawayenta ta share sannan ta mike ta daukoma Goggo maganinta ta mika mata tace "Goggo share kinsan halin Dady akwai saurin hawa kamar farashi, amma na tabbatar ba duk abinda ya fada yake nufi na, ai uba ubane ko?"

Goggo ta tabbatar tannayi dan hankalinta ya kwanta ne shiyasa itama ta daure ta daga kai tace "haka ne."
Jalila ta cire kayan makarantarta sannan ta fita.

Yau kam tana aiki tana zubar da kwalla, itakam dole me gaskiya tana gama makaranta tace Sagir ya fito suyi aure ta d'auke Goggonfa subar wannan dan iskan gidan.


************

A asibiti kuwa bayan sun shiga cikin office din wanda a saman kofar naga an rubuta Neurologist, suna shiga ya mike daga zaman da yake sannan ya saki fuskarsa yana cewa Welcome Taura.

Abba ya karasa kusa dashi ya mika mai hannu suka gaisa, sannan suka gaisa da Sagir, Ummy tace "Dr Ahmad mun sameka lafiya."
Yace "Lafiya kalau Hajiya ya mai jikin?"
Kallan Hassan tai sannan tai murmushi kawai.

Guri suka samu suka zauna ita da Sagir, shi kuma ya shiga wani dan d'aki shida Hassan da Abba.

Hassan ne ya kwanta akan wani abu, sai naga an tura abun cikin wani inji, da alama dai scanning din brain dinsa ake san yi, mutumin yana daga zaune yana duduba yanayin kwakwalwar Hassan.
Bayan ya gama d'aukan hoto sai ya dana wani abu sai Hassan ya fito, Nan Abba yaje ya taimakamai ya sauko.
Guri ya bashi ya zauna sannan shima ya zauna kusa da Dr Ahmad ya kalli Hassan yace " Hassan!"
D'agowa yai ya kalleshi baice komai ba, Dr yace " kana experiencing din wasu sababbin symptoms ne?"
Hassan ya girgizakai alamar a'a sannan ya dan hadiyi miyau yace " Sai dai kwanan nan bana baccin awa d'aya nake farkawa."
Dr yace "da mafarkin kake farkawa?"
Yace eh
Bayan su fa?
Yace " bakomai sai yanda dama na saba."
Yace "Haryanzu kanajin numfashinka na rikewa?"
Kai ya daga, alamar eh, yace " kirjinka fa?
Kai ya sake d'agawa, yace ras???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?hin san hayaniya fa?
Nan ma ya daga kai, Dr yace "duk ba abinda ya ragu daga abinda kake ji da?"
Hassan ya d'aga kai.
Dr yace " tashi kaje."

Hassan ya mike ya fito daga d'akin, Dr Ahmad yai gyaran murya sannan yace "Taura abin ne sai mun dage da addu'a sannan mun bulo mai ta yanda ya kamata, da farko dai kamar yanda ka sani har yanzu ba matsala dan gane da kwakwalwarsa, matsalar tana tare ne da zuciyarsa dolene sai mun dage inhar munasan ganin ci gaba."
Abba yace "Ni Ahmad na rasa yanda zanyi, abin nan ko ina muka je za'ace matsalar bata kwakwalwa bace, kuma nima na yarda da hakan, tunda yana tuka mota da kansa ba tare da matsala ba sannan bai taba yimana abu na mahaukata ba, sai dai na rasa yan......."
"Abinda ya faru dashi a baya, na tabbatar shine ya rike mai zuciya, yana zargin kansa ne akan duk abinda ya faru a wannan lokacin laifinsa ne."

? Abba ya kalleshi cikin nazari kafin yace "amma bayan abin nan ya faru yafi shekara d'aya a asibiti ba'a hayyacinsa ba, sannan bayan ya farka akace mana ya manta da abinda ya faru dashi a wannan lokacin."

? Ahmad yace "That's what we think, sai dai ina tsoron kar dai abin na nan a ransa, kawai dai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login