Showing 45001 words to 48000 words out of 149705 words

Chapter 16 - Jalilah Book One Complete Hausa.doc

Ayusher   

28 Oct 2025

654

 ganin daki kamar ya?
Inna tace  au a aurar da yarki guda? Sannan babbar jika a gareni ina tunanin ya zama dole muje bayan an kaita muga muhallinta.
Mumy tai yar dariya tace  Lalai Inna, jikarki? Ni dai a kara za a iya cewa  yatace amma Inna ke ai......

Kallanta tai fuska a d aure tace  me kike nufi?
Mumy tace  Inna ai kece bangane me kike nufi ba.
Inna ta ajiye wayarta sannan ta mike tace  na rasa sai yaushe ne kwakwalwarki zata fara aiki yanda ya kamata.
Mumy ta mata kallan rashin fahimta, Inna tace  nikam wacece babbar  yarki?
Tace  Safeena mana.

Inna ta kalleta cikin takaici tace  wacece babbar yarki?
Mumy tace  ni Inna rudani kikeyi.
Inna ta harareta sannan ta girgiza kai cikin takaici tace  ni wuce muje ki shirya mu tafi, ni in munje gidan na miki bayani.

Mumy ta mike ta fita tana tunanin kalaman Inna, batagane wacece babbar  yarta ba, yo ai kowa yasan Safeena Qta fara haifa.
Hart takai matattakala uku sai ta tsaya cak tace  ba dai......?
Komawa tai da gudu saman ta bude dakin Inna, tace  Inna badai so kike ki cema mutane nice mahaifiyar Jalila ba?
Inna bata kalleta ba sai shafa man zafin da takeyi a kafarta da takeyi, Mumy cikin mamaki ta karaso kusa da ita tace  Inna?
Inna ta kalleta tace  me? Kina tunanin is in possible?
Mumy cikin tsoro tace  Inna me kike tunani? Taya zaki canzama yarinya mahaifiyarta? Bayan mahaifiyarta nanan da rai?

Inna ta kalleta tace  kina tunanin in Taura yasan gaskiyar al amari akan ba yarinyarki bace zai yarda? Bakya tunanin zai ga yaudararsa mukai? In ya kwace kudin dayai investing a company dinmu fa saboda munyi betraying dinsa?

Mumy tace  to ai bai fito filli yace  yata yakeso ba, shidai babbar yarinyar gidan nan yace, sannan in ta sanar dasu fa kafin kije? Ni Inna wannan karan ban amince da abinda kika tsara ba.

Inna ta kalleta tace  shiyasa akoda yaushe nake ganin hankalinki da wayan ki na banza ne, ke wai haryanzu kina tunanin Abakar sanki yake?
Tace  Inna zaki fara ko?

Tufe maganin zafin tai tace  kiyi gaggawar tashi daga baccin da kikeyi, kada ki kuskura kiyi relying akan kowa inba ni ba, sannan kada kiyi trusting din kowa inba ni ba.

Mumy ta kalleta sannan ta mike kawai batace komai ba ta mike ta fito, itakam duk abinda Inna tace mata tana bi sai dai wannan karan hankalinta bai kwanta da hakan ba.

**********

Jalila kam da sutai sallar asuba falonsu na sama ta fito ta kwanta dan taga alamar baida niyyar mikewa daga gun.

Wajen karfe tara ta farka, jitai jikinta ya ware, saukowa tai daga kan kujerar data ke kwance sannan ta karaso jikin kofar, hannu tasa a hankali ta murda kofar, kanta ta zuro a hankali tana lekawa, bata ganshi akan gadon ba hakan yasa tai tunanin baya dakin, tura kofar tai shiga, tana shiga ta hangoshi a kwance akan sallaya inda yai sallah, baki tadan tabe tace  kamar gaske.

Wucewa tai zata shiga toilet, gani tai ya fara wani abu harta je bakin toilet din, juyowa tai da sauri ta kalleshi, gani tai yana zufa sannan sai wani murkusus yake, idanunsa a rufe gam.

Kallansa ta sakeyi tace  mafarki yake?
Kusa dashi taje tadan sa hannu tadan tabashi, hannunta ya rike da karfe yana wani irin numfashi, sankamewa taga yanayi, tsoro ne ya fara kamata, ga hannunta ya kankame da karfi wanda zafinshi ya isheta.

Cikin tsananin tsoro ta fara cewa  Yaya! Dan abinda taji suna cemai kenan, Yaya! Yaya! A tsorace take kiran sunan nasa.

Ganin zufa tana keto mai ta ko ina ga sai kara kamewa yakeyi, yanzu kam hannunta ya saki yasa hannunsa a wuyansa yana kokarin jawo numfashinsa da yake mai wahalar shaka.

Jikinta ne ya fara rawa, ganin yanda yake sa hannu a wuyansa yasa tai saurin sa hannu ta rike nasa da karfi, a tsorace take cewa  Yaya! Yaya! Menene?

Ganin abin karuwa yake yasa ta fara tofamai kulhuwallahu, falaqi da nasi, dan bata iya addo oi ba.

Hannunta data rike nashi ya jawo hakan yasa ta fada jikinsa, da sauri ta mike, sannan ta shiga kiransa tana tabashi.

Ahankali yai wani dogon numfashi, sannan ya bude idanunsa wanda sukai jaa.
Idanunsa ne suka sauka a kanta tayi tsuru tsuru kamar kace mata kyaa ta ruga a guje....

Kallanta yai cikin rashin jin dadi, dan shikam yasan abinda yake tsoro kenan, bayasan wani ya ganshi cikin wannan halin.
Jalila kam tana nan a zaune kamar abu mara motsi har ya mike zaune, ganin yanda ta kame yasa ya mike tsaye ya zaune a bakin gado sannan yasa hannu ya shafi fuskarsa cikin takaici.
Jalila a hankali ta juyo ta kalleshi bakinta na rawa tace  hmm ka ka......
Kallanta yai fuskarsa a hade ga idanunsa sunyi jaa, wani irin tsoronsa ne ya kamata, gabanta ya shiga faduwa.
Idanunsa na kanta yace  ka me?
Kai ta girgiza da sauri tace  hm ba komai.
Ta juya da sauri gaban wardrobe taje ta bude ta rasama me zatayi a kai sannan ta matso gaban madubi shima ta tsaya, sannan ta bude bandaki da sauri ta shiga ciki.

Duk abinda takeyi idanunsa na kanta, idanunsa ya sake runstewa cikin takaici, gani nai ya bude idanunsa ya mike da sauri ya dau waya da key din motarsa.

Yana kokarin fita itakuma tana fitowa, kallan juna sukai da sauri ya dauke kansa sannan yai waje.

Kallan kofar daya rufo tai sannan ta zauna a bakin gado tana maida numfashi kai kace gudu tai, me ke nan? Me ya faru dazu? Aljanu ne dashi? Kansa kalau kuwa? Badai wannan bace matsalar da Ummy tai magana?

Ta dade a zaune sannan ta mike tai wanka, haka ta sa kaya jiki a sanyeye sam hankalinta ya kasa kwanciya.

Ameera ce ta kwankwasa kofa, Jalila ta bude mata.
Tiren abinci ta miko mata tace  ga abincin yaya, ke kuma ki sako muje kasa.

Jalila ta kalleta cikin sanyin jiki tace  Bayanan, sannan ni banajin yunwa.
Ameera ta kalleta tace  yaza ai kice bakyajin yunwa?

Jalila ta kalleta sannan ta koma ciki, gaba daya itakam abin duniya ya dameta, Ameera ta ajiye tiren sannan ta kalleta tace  ga na yaya nan sai kici anan, shi nasan ba yanzu zai dawo ba.
Ajiye abincin tai ta fita.

Jalila kam a zaune kawai take akan gado tama rasa ta ina zata fara tunanin abinda ke faruwa.

Ganin ta rasa amsa kawai ta dauko hijab dinta ta sauko, su Ummy na cin abinci ta sauko kasa, kusa da Ummy taje ta gaisheta sannan ta gaida Sagir, Ummy tace  zauna muci abinci.

Jalila wacce ta fito dan sanar da ita tana san zuwa gun Goggo tai shiru tana wasa a hannunta.
Ummy ta kalleta tace  Ya akai Jalila? Wani abin kikesan fadamin?
Dagowa tai ta kalli Uncle sannan ta kalli Ummy.

Sagir ya kalli Ummy yace  ko jikin ne?
Ummy ta kalleta tace  Jikin ne?

Jalila da sauri tace  bashi bane.
Ummy tace  to menene?

Jalila ta kalleta sannan ta sake yin shiru, Sagir ya yace  asibitin zaki koma?

Kallansa tai sannan ta kalli Ummy, Ummy tace  wai haka?

Jalila ta daga kai, Ummy tai murmushi tace  menene to da kika kasa fada? Ki zauna kici abinci sai kuje da Sagir.

Kallan Sagir tai da sauri, sai dai batace komai ba.
Ummy tace  in bakya san ci anan ki hau sama kici kafin ya gama.
Jalila tace  nagode Ummy. Sannan tajuya tai ta hau sama.

Zama tai a falon tai shiru Hassan take hangowa abinda yai dazu.

Kanta ta kwantar akan kujera, Muryar Ameera taji tana kiranta, nan ta mike ta sauko ko dakin bata koma ba.

Da zata fita Ummy ta kirata, Jalila ta juya taje gunta, Ummy ta miko mata leda sannan tace ki gaisheta, dan gwarama da kika tuna min yau kije, dan Abban Ameera inya dawo ba lalai ya barki ki fita ba, bayasan fita.
Jalila ta amshi ledar tana godiya.

A bakin mota ta hangoshi a tsaye, nan ta karasa kusa dashi, gani tai ya bude mata bayan motar sannan ya juya ya shiga gun zaman driver tare da kunna motar.

Rufe kofar motar tai yaja suka fara tafiya, Motar tayi shiru sai karar redio dake tashi a cikin motar.

Sunyi tafiya mai dan tsayi kafin can yace  Jalila.
Idanunta na jikin window tace  naam.
Yace  Jalila nasan na miki laifi sai dai nan gaba zaki fahimci dalili na nayin hakka sannan na tabbatar a lokacin zaki san abinda nake nufi da kalamai na.

Kallansa tai sannan ta daure tace  magana ta wuce, sai dai meke damun Yayan naka?
Shiru yai kafin yace  Ni kaina ban sani ba, dukanmu yan gidan ba wanda yasan meke damunshi, shikadai yasan abinda ya faru a lokacin.
Lokacin?
Yace  eh lokacin da su Husain da Nazir dan kanin Abba.

Jalila tai shiru batace komai ba, Sagir ya kalleta ta madubin gaban motar, yana tsananin san yarinyar nan haka kuma yana tsananin tausayinta sai dai duk yanda yaso da so da kaunar ta bai isa ba.....bai isa ba.

Dagowa tai ta kalli madubin suka hada ido, kanta ta kawar sannan a hankali tace  Uncle!
Yace  naam.
Har zata cemai Goggo mahaifiyarta ce sai ta fasa, tace  shikenan ma.
Yace  menene? Dan Allah ki fadamin.

Shiru tai kafin can tace  Goggo nace a asibitin.

Yace  nayi tunanin Goggon da kike maganar ta ne amma ya kuke?ni da nadauka ai Goggon mahaifiyarki ce.

Zatai magana ya taka burki da karfi, juyowa yai ya kalleta yace  Jalila are u okay?
Tace  eh menene?
Yaran da suka tsallaka titin ya kalla yace  yara ne wlh saura kiris su ja mana.

Shiru tai batace komai ba, gangarawa asibitin yai, parking yai sannan yace  Jalila ki yi hakuri dan Allah.

Kallansa tai tace  zancen hakuri da rashinsa ai ya kare, kafin ai abu ne ake neman canzashi ba bayan anyi ba.
Ta bude motar sannan tace  nagode.

So yake ya shiga amma bayasan ya kara bata mata rai.

Bata dade da shiga ba sai gatanan hankali a tashe tace  Uncle na rasa Goggo na.
Sagir yace  ban gane ba?

Kuka ta saka hankalinta a tashe take cewa sunce an mata transfer zuwa wani asibitin kuma basusan sunan asibitin.
Yace  ban gane ba?

Tana kuka tace  wai basu sani ba......

********

Abba kam dakyar ya samu bacci jiya, ya rasa meyasa gaba daya tunanin yarinyar da bata fi sa an dansa ba ya dameshi.
Ai kuwa da sassafe ya fada mota da driver dinsa suka nufo kano, ko kara bi ta contracts din baiyi ba.

Me ya sameshi? Me ke faruwa dashi?

*?**********

Mumy ce ta kalli Sultan tace  Sultan bari muje gidan Jalila, ko zakaje?
Inna ce tai kakari wanda yake nuna mata ta daina, Mumy ta kalleshi tace  bari muje.


Nan suka fito daga gidan suka shiga mota.

#OneLuv=ؕ?


=??? *JALILAH* =???

Written By : *AYUSHER MUHD*
Wattpad: *Ayusher Muhd*


*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*

(_D home of expert and perfect writer's_=ء?)


*28*

Kasa tsayuwa tai kawai ta tsugunna agun tasa kuka, Sagir ya koma cikin asibitin ya tambayesu, yanda suka fadamai haka suka fada mai, fitowa yai gunta yace ta shiga mota tunda ai sunce wanda ya kawota shine ya dauketa.
Tanaji tace "Dady ne."
Nan suka shiga yaja motar da gudu suka nufi gidansu, basuyi nisa da fara tafiya ba wayar Sagir ta shiga kara, Sagir ya daga tare da cewa "Ummy!"

Ummy tace "Sagir kuyi sauri ku dawo iyayen Jalila da kakarta sunzo."
Yace "gamunan."
Ya juya kan motar yana cewa "jalila iyayenki suna gida."
Hawayenta ta share tace "an fadama wa nene yazo?"
Yace "kawai dai cemin tai iyayenki da ko kakarki ne?"

Jalila tai shiru sai fatan Allah yasa ba wani abin bane ya faru, suna isa gidan ta fita da sauri ko motar bata rufe ba ta nufi cikin gidan.
Da gudu ta shiga, a falo ta taradda Ameera rike da waya tana latsawa.
Jalila ta matso tace "Ameera ina Mumy?"
Kallan ta tai tace "suna sama."

Jalila tai sama da gudu, a falon sana ta taradda Inna, tsayawa tai sannan ta karaso a hankali, tsugunnawa tai ta gaida Inna kafin ta gaida Mumy.
An ajiye musu kayan ciye ciye a gaban su.

Ameera ce ta hawo saman sannan ta mika mata makullin dakinta, Jalila ta mike ta bude dakin sannan tace ku shigo.

Mumy ce ta fara mikewa, Inna kuwa sai data karema falon kallo sannan ta shiga dakin, zama tai tana kallan dakin kafin tace "ina mijin naki?"
Jalila tace "ya fita."
Inna ta kalleta tace "rufe kofar."

Jalila ta mike jiki a sanyaye ta rufe kofar, Inna ta kalleta ta mata alama data matso kusa da ita.
Jalila gabanta sai faduwa yake ta matsa a hankali, ta tsugunna.

Mumy ta kalleta tace "Jalila gun Goggo kika je?"
Ta kalleta sannan tace "eh amma bata asibitin, ance Dady ya dauketa."
Mumy ta kalli inna, Inma ta kalli Jalila tace "ni nasa ya dauketa daga asibitin."
Jalila ta kalleta tace "Inna kikace in na amince da auran nan zaki kula da Goggo?"
Inna ta kalleta tace "hakane."
Jalila tace "kuma....."

Inna tai murmushi tace " ba dai kina tunanin wani abin muka mata ba?"
Jalila a tsorace ta kalleta, Inna tace " kinsanar ma wani a gidan nan Goggo ce ta haifeki?"

Jalila jiki a sanyeye tace "a'a amma......."
Inna tace "Jalila wacece ta haifeki?"
Kallan mamaki ta mata tace "ban gane ba Inna?"

Har yaje zai shiga dakinsa yaji kamar ana magana a dakin Jalila bayan yasan Ummy ta rufe dakin, kuma yaga Ummy da Ameera a kasa.
Hannu yasa kamar zai bude kofar yaji ance "tambayarki nake sannan amsarki nake so naji."
Jalila tace "to ai Inna tambayarki gaba d???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?aya na kasa fahimtarta, bangane wanene ya haifeni ba?"
Har ya juya zai tafi dan shi mutum ne da bai damuwa da abinda bai dameshi ba.

Jiyai ance " abinda zamsanar dake inaso ya zama amsarki a duk lokacin da aka tambayeki, daga yau ko waye ya tambayeki mahaifiyarki ki tabbatar kince Mumy ce ta haifeki."

Da sauri Jalila ta kalli kofar, shima da sauri ya kalli kofar, meke faruwa? Shidai a iya saninsa bai taba ji inda ake sanar da d'a mahaifiyarsa ba.

? Jalila tace "Bangane Mumy ce ta haifeni ba? Goggon tawa rasuwa tai ko me? Ina kuka boyeta? Ta fada cikin wani yanayi mai ban tausayi wanda yasa Hassan din jingina da bangon jikin kofar.
Inna tace "ko daya, ina dai sanar dake ne hakan shine kadai zaisa mu taimaki mahaifiyarki mu kuma bata rayuwa na gari."

Jalila jitai ta sa wata dariya mai tattare da bakin ciki da kuka, tana hawaye tace " A lokacin da za'amin auran nan kunce in na amince zaku kula da Goggona, sannan bayan na amince yanzu kunce kuma gaba daya ma in canza mahaifiyar datai wahala akai........"
Marin da aka kifa mata ne yasa tai shiru, Inna tace " dan kinyi aure a gidan nan ne yasa kika fara tunanin yin jayayya dani? Ina magana kina magana?"

Haryasa hannu zai bude kofar saboda ransa ya baci sai kuma naga ya tsaya, hannunsa naga ya dunkule sannan a ja baya daga jikin kofar, cikin takaici.
Saboda nine kenan? Saboda iyayena sun nemi auranta yasa har ake neman sata yin haka.

Labansa ya ciza sannan ya bude dakinsa ya shiga, ya rufo kofar da karfinsa na gaske.
Wanda yasa sukaji kara, Inna ta kalli Jalila tace "mijin naki ne?"
Jalila tana hawaye ta daga kai, Inna ta tabe baki a ranta tace hauka yake muraran irin wannan buga kofa haka? Ai kanaji kasan na marasa hankaline.

Maida kallanta tai kan Jalila tace "shawara ya rage naki, inhar kinasan kiga mahaifiyarki kiyi abinda na saki, in kuma bakyaso ki hakura da ganinta ne wannan ya rage naki."

Ta kalli Mumy tace "tashi mu tafi dan ba'a dadewa gidan surukai."

Jalila tana kallansu suka mike gaba daya inbanda hawaye ba abinda takeyi, Inna ta fita daga dakin ta juyo tace "bazaki rakamu ba?"

Jalila ta kallesu, yanda Inna take kallanta ne yasa ta mike ta fito falon.
Tana fitowa shima yana fitowa daga dakin, rufo kofa, fuskarnan tasa a daure kallo daya ya musu ya dauke kansa, yi yai kamar bai ga mutane a gun ba ya wucesu ya sauka.

Inna ta kalleshi sannan ta kalli Jalila bayan ya sauka tace "shine?"
Jalila ta daga kai, Mumy tace "amma yana ganinmi kamar yaga kashi?"
Inna tace "ki mai uzuri......"
Sai kuma tai shiru, kallanta Jalila tai badai sunsan matsalarshi ba? Ai a take tai tunani, haba itadai ta tabbatar da wani abun daga sanda ta iso gidan nan, ta tabbatar Bazasu taba ajiye Safeena su dauketa ba.
Yanda take kallan Mumy ne yasa Inna tace" me kikeyi? Na dauka cewa nai muje ki rakamu."

? Zubewa akan gwiwowinta tai tana hawaye tace "Inna dan Allah na rokeki kiyi hakuri, zanyi komai amma dan Allah banda gurbin mahaifiyata."
Inna ta kalli hanyar sama tace" me kike yi hakan? Salan wani ya ganki yace cutar dake mukeyi?"

Jalila ta mike tana matse kwalla, Inna tace "muje."

Haka suka sauko kasa tana bayansu.

Ummy ta fito daga daki tace "har zaku tafi?"
Mumy tace "eh wlh."

Ummy ta kalli Jalila tace "Jalila ana kukan rabuwa ne?"
Jalila

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login