Showing 30001 words to 33000 words out of 149705 words

Chapter 11 - Jalilah Book One Complete Hausa.doc

Ayusher   

28 Oct 2025

659

matsala bane, Jalila ta kalleta a ranta tace me zata samu da take bin ta kowace hanya dan ganin ta min auran nan?"
Dagowa tai da sauri datai tunanin wani abu tace "Inna tsoho ne?"

Inna tace "a'a saurayi ne"
Jalila cikin tsoro take kallanta, anya? Me suke tunani? In har ba wata matsalar mai zaisa su bar yarsu su zabeta?

? Inna tace " ki tashi ki sauka kasa, bayan kinyi aanka kinci abinci ki shirya, ance bayan la'asar zaizo."

Jalila ta mike ta fito zuciyarta fal da tunani kala kala.
Bangarensu kawai ta nufa ta kwanta, karar wayarta taji.
Da sauri ta jawota, ta daga.
Muryar Uncle ne ya daki kunnenta, ji tai wasu zafaffan hawaye sun zubo mata.
Sagir yace "Jalila ina kika shiga haka? Ba dai wani abin bane ya faru ko?"

Kasa magana tai, hankalinsa ne ya tashi.
Ya shiga tambayarta, can ta daure tace "Uncle yaushe zamu hadu? Akwai maganar da zamuyi dakai."
Yace " ko yanzu ma in kinaso."
Tace "a'a banda yau."
Yace "nima na manta yau zan raka yayana wani gun, gobe fa?"
Tace " to, Allah ya kaimu, zan kiraka goben."
Haka kawai tace ta kashe wayar saboda yanda taji zuciyarta ta karye.
Tana kashewa kuwa tasa kuka.
Shikenan Uncle, soyayyar da muke ma juna ashe anan zata tsaya.........

Sagir na kashe wayar shima yai shiru, tabbas akwai abinda ke damunta......


#Oneluv=ؕ?
[08/10, 02:09] * +234 803 222 1758, : =??? *JALILAH* =???

Written By : *AYUSHER MUHD*
Wattpad: *Ayusher Muhd*


*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*

? (_D home of expert and perfect writer's_=ء?)

*No 18*


?? Sake kwanciya tai, ta kwantar da kanta akan katifa, itada take burin auren soyayya? Yanzu me kenan?
Idanunta ta bude a hankali, tana kallan dakinsu, rayuwarsu da mahaifiyarta ne ta shiga dawo mata, rayuwace wacce sukai ta talauci da tsana, sai dai a tsakaninsu rayuwace mai cike da dinbin kewar juna da shakuwa, zata iya rayuwa ba tare da Goggonta ba?
Haka tai ta saka da warwara har bacci yai gaba da ita.

? Sai wajen karfe uku ta farka, shima mafarki ne ya tasheta wanda ya sata razana da sauri, sai dai me? Duk yanda taso ta tuno wani mafarkin tai ta kasa sam, wayarta ta dauka da sauri ta yima Sagir text.
Uncle please mu hadu a makaranta ko na minti goma ne, i really want to talk to you.
Ajiye wayar tai ta mike, gaskiya dole ta sanar ma Uncle abinda ke faruwa taji me zaice.

? Mikewa tai ta kalli kayan da aka kawo mata ta saka, nan tai wanka ta saka ta fito sidif sidif tai waje.
*****

A can gidansu Hassan kuwa, Sai da Ummy ta mai magana ya kimtsa, da kananan kaya ya saka tasashi ya koma ya sako manya kaya.
Fitowa yai daga dakinsa sanye da dakakiyar shad, cyan color wanda mukafi sani da bluegreen, shadar ta mai kyau sosai, dan shi dama bai fiya sa manyan kaya ba, daga kanana sai jallabiya, Abba ne baya gajiya da dinkamai.
Ameera da kanta ta d'aukomai hula ta mikamai.
Hassan kallansu kawai yake dan bayasan magana ya amsa.
Takalmi ya saka sannan ya sauko kasan, Sagir sai janshi yake da tsokana wai kai Yaya gaskiya wannan kyan kamar ranar auranka.

Hassan ko kallansa baiyi ba bare ya tankamai, shima Sagir din manyan kaya ya saka.
Ummy ta jawo Sagir tace "Sagir ka taimaka kar a samu matsala, kasan halin yayan naka."
Sagir ya daga kai yace "Karki damu Ummyna, ki bar komai a wuyana."

Murmushi tai tace "godiya nake dan lele na."
Haka suka fito kowa yana farinciki, Ummy ta mikama Sagir gift din da zasu kai mata.

Aina'u na jikin dakin Ameera tana kallansu, komawa tai cikin dakin ta kwanta ranta ba dadi.

? Motar Hassan suka nufa, Hassan na shiga ya rufo kofa, Sagir ya zagawa ta bangaren kusa da driver yana cew "Yaya na dauka da Mamman zamuje saboda shi yasan gidan.

Jiyai kofar a rufe, cikin mamaki yace "Yaya me kenan?"
Hassan ya zuge glass dinsa yace " ka shiga motar ka Mamman ya jaka, ni daga can wani guri zanje."
Sagir ba tare da tunanin komai ba ya juya ya shiga motar sa shida Mamman.

?? Haka suka fita da motoci biyu, su Sagir na baya shi yana gaba.
Suna tafe suna hira sam hankalinsa baikai kan wayarsa ba domin yanzu harkar yayansa ce a gabansa baya tunanin akwai wani abu da zai ratsa wanda zaiyi distracting dinsa.

? A kofar gidan Mamman yasa signal sannan aka bude mai gate ya shiga, maimakon Hassan ya shiga kawai sai yai gaba.

? suna parking Sagir ya juya baiga motar Hassan ba, mamaki ya kamashi da sauri ya fito wajen gidan yana lekawa, sai dai ba shi ba labarinsa.

Haka suma mutanen gidan, dan tun lokacin da Mumy ta aika Jalila tazo ta karasa shiryata, taki zuwa hankalinsu ya tashi, ta fito ta duba bangarensu bata ganta ba.

Hankalinsu yayi tsananin tashi dan sun duba ko ina basu ganta ba, Mumy kam kamar tai ya ya.
Nan Dady ya fito nemanta.

? Can ita kuwa tana tsaye a inda suke haduwa, tana duba agoggo, taji ance bayan la'asar zaizo shiyasa take sauri Uncle yazo suyi magana ta koma kafin hudu da rabi.

? Agoggon hannunta ta kalla, karfe 4:30jiki a sanyaye ta juya, lalai yanzu wata zuciya tana sanar da ita Uncle bai damu da ita sosai ba, wata zuciyar kuma neman yi masa uzuri takeyi.

Haka ta tako jiki a sanyaye ta tsaya akan titi dan neman adaidaita.

Tana tsaye mota tai parkin ta bayanta kadan, kallan motar tai dan ta dauka uncle ne, batai ma tunanin motar waye ba kawai ta nufi motar.
Shikuwa yanda tazo saitinsa ne yasa cikin mamaki yake kallanta.

? Sai dataje jikin kofar sannan tai tunanin ba shi bane, lalai zuciyarta a matse take da san ganin Uncle, baki ta turo sannan ta juya jiki a sanyaye.
Yana zaune a ciki yana kallanta, da yake motar tint ce itakam bata ganshi ba.


Haka ta tsaya a titi zuciyarta duk ba dadi, sai kara leka hanya take ko zata ganshi.

Yana kallanta harta samu mota ta shiga, kai ya girgiza sannan ya kashe motar, yasa kansa akan kujera yana tunani, shikam ta ina zai fara kallan mace da sunan zance? Sannan in tsautsayi yasa matsalarsa ta tashi fa?
shikam hankalinsa ya kasa kwanciya, ya san kuma Sagir zaisan me zaice mata.

? Haka ta samu adaidaita ta hau jiki a sanyaye, ajiyar zuciya taitayi a cikin adaidaitar har suka isa, tana kokarin biyan kudin adaidaitar su kuma suka fito daga cikin gidan.

Motar tabi da kallo, taga mutane biyu a zaune sai dai hankalinta ba'a kansu yake ba.

Haka ta taho a hankali ta tura gate din gidan.

? Mumy ta ganina waje itada Dady suna magana, suna ganinta suka juyo suka zuba mata idanu.

Dady a zuciye ya fara takowa, ganin haka yasata ta tsorata.
Hannu ya daga zai shara mata mari, da sauri ta runtse idanunta, tsayawa yai sannan ya kalleta rai a bace, yatsa ya nuna mata yace "ni zaki cima mutumci?"

Mumy ta matso ta sauke mai hannu tace "Dadyn Yasmeen meye hakan?"
Kallanta yai yace "yanzu da badan shima dalili ya hanashi zuwa ba fa?sannan da kanin nasa bai fahimcemu ba fa?"

Mumy ta kalleshi tace "tunda dai komai yazo da sauki ba shikenan ba?"
Yace "in Inna taji fa? Me kike tunanin za'ace?"
Mumy tace "sai muce mata ta ganshi sun gaisa harya tafi."

Dady ya kalleta cikin jin dadi, wanda baisan? a ranta ba wai damuwa da Jalilan tai ba balle tace batasan a mata fada ne, tayi hakan ne dan abin ya kara karfafa.
Jalila ta kalla sannan tace "Hassan din wani uzuri mai karfi ya tasomai a hanya bayan sun fito, dole ne yasashi kin zuwa, shiyasa ya turo kaninsa.

Jalila ta dan tabe baki kadan, dan itakam ba damuwarta bane.
Mumy ta rike hannunta tace "muje ciki ko?"

Jalila tace "A'a Mumy asibiti zan koma."
Mumy ta jinjina kai tace "bari mu kaiki."

Jalila fuskarta dama a daure take tai bangarensu.
Kayan da Goggo tace ta dauko mata ta dauko sannan ta fito.

Suna tsaye suna ta wani abu wai su a dole mata da miji, ita Mumy sai wani shagwabewa take, haushi ya kara kama Jalila a ranta tace "mutum ya girma amma jinsa yake kamar yaro."
Ta gabansu tazo ta wuce, Mumt ta riko hannunta tace "Jalila tare zamu tafi."
Jalila tai shiru tana kallan Dady.
Mumy ta bude mata baya sannan ta shiga, ita kuma ta shiga kusa da Dady.
A hanya tayi shiru tana kallan waje, wayarta ce ta fara ringing, da sauri ta zarota.

Uncle? Da sauri ta daga tace "Uncle!"

? Jalila i am............
Bata gama jin mai zai fada ba, Dady yai wani irin parking, wanda ya tsoratata, sam ta mantada mutane a motar.

Mumy ta fizgi wayar tana cewa "Jalila me kenan?"

Jalila a tsorace ta kalleta, sunan da ke jiki ta kalla MINE? Nunawa Dady tai ya kashe wayar yace "uban wa ya sai miki waya?"
Idanunta ne suka firfito tai shiru.
Mumy tace "Jalila zance kike a bayan idanun mu?"
Jalila ta kallesu sai dai ta kasa magana, cikin salo Mumy tace "shiyasa take neman bijerawa maganarka kenan? Lalai samarin zamani sun iya siyan zuciya, da har zasusa 'da ya bijirema mahaifinsa."

Dady cikin takaici yace "Uncle? Malamin ku ne kenan? Dama abinda kike a makarantar kenan?"

Jalila da hawaye suka fara zubo mata tai shiru tana kallan ikon Allah.
Dady yace "wato ina miki magana ma kinfi karfin amsawa ko?"
Jalila tace "ba haka bane Dady."
Mumy tace " Jalila yaushe kika zama haka?"?

Jalila jitai hawaye suna gudu a idanunta, wannan shine a dakeka a kuma hanaka kuka.

Haka tana kallo Dady ya zare sim din ya karyashi sannan ya cilar waje, sannan ya ajiye wayar cikin motar sa.

? Jalila tana kuka tana cewa "dan Allah dady ka barni ko magana daya muyi."
Dady ko kallanta baiyi ba ya ja motar sukai gaba.
Mumy tana cewa "lalai Jalila wato ya baki kima saurayinki magana?"

Juyawa tai tana kallan window tana wani irin kukan takaici.


#ONELUV=ؕ?
[08/10, 02:11] * +234 803 222 1758, : =??? *JALILAH* =???

Written By : *AYUSHER MUHD*
Wattpad: *Ayusher Muhd*


*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*

(_D home of expert and perfect writer's_=ء?)

*No 19*


? A kofar asibitin Dady yai parking sannan sukai shiru a cikin motar, Jalila tasa hannu. zata bude kofar Dady yace "Jalilah!"
komawa tai ta zauna tana kallansa tare da amsawa.
Dady ya juyo yace "Fatima dan bamu guri."
kallansa tai kamar zatai magana sai naga ta fasa, kofar ta bude ta fita sannan ta nufi cikin asibitin.

Jalila ta kalleshi sai dai gani take kamar shiryawa sukai, Dady ya kalleta sannan yace "Habiba, na tabbatar kina ganin kamar ban damu dake ba wanda a gaskiyar magana ba haka bane, a duk inda uba yake to lalai tabbas ne yaso abinda ya haifa, kallan mamaki tamai dan tabbas da ace Goggo ba ta bata labarin yanda tai rayuwa dashi ba tabbas zata yarda yana santa sannan zata iya tunanin wani abun akamai daya hanashi nuna mata so.

Dady ya kara kallanta yace " kinajin haushi na ko?"
kanta na kasa batace komai ba, yace " Jalila wannan auran da za'a miki ba wai rayuwar mahaifiyarki kadai zai taimaka ba, ni kaina kin ceci ni sannan kin taimaki rayuwar yan uwanki."

Dagowa tai ta kalleshi cikin rashin fahimta tace " Dady ba aure ne tsakaninku da Goggo?"
kallanta yai yace "me kike tunani?"
Tace " amsar da zaka bani ita zata bani ikon ajiye komai dake raina."
Shiru yai yana kallanta yace "Jalila yanzu ba zancen wani aure da rashinsa bane a gabanmu, inhar kinason Inna ta taimaki mahaifiyarki dolene sai kin amince da auran nan, sannan in fada miki gaskiya ko ki yarda ko karki yarda Inna sai ta aura miki yaran nan."

Idanunta ne suka fara zubar da kwalla tace "Dady kaine mahaifina ko Inna?"
Cikin fada yace "Wai meke damunki ne?yaushe kika fara gardama haka? kina tunanin lalabakin da nakeyi zai baki damar bijirema abinda mukesanki dashi ne? inhar kinasan farincikin uwar data sha wahalarki, kina neman lafiyarta to kibi abinda muka ce miki sannan karki kuskura ki fada mata zancen nan."

Kallansa kawai take tana zubarda hawaye, faduwar da Goggo tai kenan su riba suka samu da rashin lafiyarta? tunda batasan dame zasuyi threatening dinta ba.

Dady ne yace "muje."
A hankali ta tura kofar ta fito, jitai kafafunta na rawa hakan yasa ta rike kofar motar.
Haka suka shiga cikin asibitin yana gaba tana baya.

********
A cikin asibitin kuwa Goggo ce tana kwance tana tunanin Jalila da bata dawo ba,Mumy ta turo kofar dakin.
Goggo ta kalleta sannan ta gaidata, dan dama tunda sukazo gidan haka suka saba, Goggo ce ke gaidata.
Mumy ta zauna a kan kujera sannan ta kalleta tace "Ya jikin?"
Goggo tace "Da sauki, tare kuke da Jalila ne?"
Mumy tace "eh suna tare da mahaifinta ne yanzu zata shigo."

Da sauri Goggo ta canza fuska tace "me yake ce mata? ba dai zance........."
Mumy ce ta katseta tana murmushi tace "Kai maman Jalila, ba wannan zancen bane, ai wannan maganar an ajiyeta sai kin samu lafiya, mun isa mu yanke hukunci ne mahaifiyar yarinya na asibiti?"

Goggo ta mata kallan zargi, Mumy tace "duk rashin kirkirnmu ai bamu isa yi mata aure dai kina asibiti ba, sannan mahaifinta ma har fada mukai akan zancen nan, ya hana a kara tada shi."

Jin hakan ne yasa Goggo tadan saki jiki har tace "mun gode kuna ta dawainiya."
Mumy a ranta tace "Yarki dai nayi.
Amma a fili tace " Karki damu, ke dai ki kwantar da hankalinki ki samu lafiya, kinga dai irin kudin da ake narkarwa a asibitin nan."

Turo kofar da Dady yai ne yasa ta dan canza fuska wai ita a dole fishi takeyi.

Jalila ta shigo ta tafi kusa da Goggo ta zauna.
Dady fuskarnan a hade yace "Ya jiki?"
Tace "Alhamdulila."

Kusa da ita ya matso ya ajiye mata kudi sannan ya juya.
Mumy ce ta mike tace "Sai an kawo abincin dare."

Goggo tace "Angode."

Haka suka fita, Jalila ta kwanta a kafadarta.
Goggo tace "Menene?"
Jalila ta kara gyarawa tace " Kawai dumin Goggona nakesan ji."

Goggo tai murmushi tace "wani abun ya faru ne?"
Tace " me zai faru? Ni fa bangarenmu naje na kwanta, hardasu barci."
Goggo tace "kin kyauta, ki dinga zuwa kema kina hutawa, zaman asibiti ba dadi sannan na kula bakya samun barci sosai."
Jalila ta daga kai tana murmushi.
Goggo ta miko mata duka kudin da Dady ya ajiye tace "irga."
Jalila ta irga tace "ni Goggo dubu ashirinn nake gani."
Goggo cikin mamaki tace "dubu ashirin? Me zamuyi da kudi haka? Sannan ni tunda nake a rayuwata ban taba rike kudi mai yawa haka ba."
Jalila a ranta tace " gashi kin rike yau tunda suna san saida farincikin yarki."

Goggo tai shiru aranta tana mamaki........



***********

? A can gidansu Hassan kuwa, Sagir sai karya yai akan sunje sannan shima yayan ya ganta.
Ummy duk ta matso dasan jin labari tace "Sagir kana tunanin ta mai?"
Yace "kinsan halin yaya baice komai ba amma ga dukan alamu ta kwantamai."
Ummy tai murmushi tace "ni kaina nasan zata kwantamai dan wannan inaji a jikina alheri ne atattare da ita."

Abba yai dariya yace "Ah Alhamdulila lalai yau hankalinmu ya kwanta."

? Hassan sai wajen magrib ya dawo, yana shigowa Ummy ta fito cikin farinciki tace "Hassan ka dawo?"
Kai ya daga kawai ya nufi sama.
Yana shiga daki, kafin kofar ta rufo Sagir ya shigo, yace "Yaya dan Allah me ka aikata dazu? Ta ya zaka tafi ka barmu a gidan yarinya?"
Hassan bai tanka mai ba sai rigarsa da ya cire dan dama ya gaji da ita.
Sagir yace "Amma Yaya wlh ba dadi, bakaji yanda na ji kunya ba, gashi an hada maka abinci kala kala.

Hassan ya juyo ya kalleshi, Sagir yace "Ya Hassan."
Hassan ya matso kusa dashi yace " Sry." Ya juya yaja towel ya shiga toilet.

Sagir ya bishi da kallo sannan yai ajiyar zuciya.
Juyawa yai ya koma d'aki, dan shi yau abin duniya shima ya dameshi.

Baiga Jalila a makaranta ba daya koma sannan duk yanda ya sake kiranta a waya sai acemai a kashe take.

*?*?*???**

Ta kowani bangare shirin aure sukeyi, Sagir ya dawo kasa an kara gyara musu saman, sai dai duk yanda ake shirin auren nan Amarya da Ango ko a tsikar jikinsu, dan ita tana asibiti gun mahaifiyarta, yanzu ko gidan ma bata zuwa, kayanta kala uku data taho dasu shi take ta sawa.
Sam batasan auran sati biyu aka saba itadai kawai tasan batasan zuwa gidan ne ma bare a mata zancen.

Kudin da Dady ya basu shi suke dan kwalam dinsu, sai abinci da ake aiko musu, kaf gidan ba wanda ya sake zuwa duba Goggo sai Sultan da yake zuwa duk bayan kwana biyu, sannan ita ko lefen ma da aka kawo basu nuna mata ba, ita kuwa dama ba wannan bane a gabanta, bakincikinta inda zataga Ya Sagir.
Zuwanta makarantarsu uku amma ba ta taba dakar sa'ar ganinsa ba, har ta hakura.

A yau da yazone wanda kwananta 10 kenan da zuwa gida wanda yai daidai da kwana 11 da kawo lefe.
Yau saura kwana uku kenan bikin ta amma bata sani ba.
Tana zaune bayan sunci abincin safe Sultan yazo shi da wata yarinya wacce batakai Jalila ba, gaida Goggo yai.
Jalila ta kalleshi tace "Sultan wannan fa?"
Yace "itace zata dinga tayaki zama, mai kula da Goggo."
Gabanta ne ya fadi dan tabbas ta fahimci me hakan yake nufi, yace "sannan Dady yanasan ganinki yanzu."

Jalila tai yake tana kallan Goggo, Goggo cikin mamaki tace "Allah sarki angode, kinga yanzu sai ki taimaka inkinje gida ki huta ki bari sai gobe ko jibi kya dawo tunda kinga jikin nawa ai da sauki sosai, ni da zasu sallamemu ma da naji dadi."

Jalila ta mike jiki a sanyaye, yarinyar ta gaida Goggo, Goggo ta amsa fuska a sake tace "ya sunanki?"
Zulai yarinyar ta fada.
Jalila ta matso

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login