Showing 135001 words to 138000 words out of 149705 words

Chapter 46 - Jalilah Book One Complete Hausa.doc

Ayusher   

28 Oct 2025

617

ta kara.

Ganin sabuwar number yasa "ta daga jiki a sanyaye."
Jalilah? Cikin mamaki tace "Safeenah"

Safeena tana abin kuka tace "Jalila Allah yayima Inna rasuwa."

Gaban Jalila ne ya fadi, ta mike tsaye daga jikinshi jikinta duk ya fara rawa tace "Inalilahi wa Ina Ilaihi Raji'un, yaushe?"

Safeena tana kuka tace "dazun nan, yanzu muna hanyar kaita gida ne za'a mata wanka."

Jalila hawaye ne ya zubo mata tace "bari nima ganinan zuwa."

Safeena tace "Gidan kawu zamu kaita, acan za'ayi zaman makoki, dan Dady ya koremu."


Jalila jitai kanta yayi dum kafin tace "ya koreku kamar ya?"

Safeena tana kuka tace " sai kinzo."
Dan batasan me zatace ba acikin wannan yanayin, gaba daya Jalila ta juyo tace "Yaya? Inna ta rasu."

Hassan wanda tundayaji yanda take magana jikinshi ya bashi Inna ce ya matso ya rike hannunta wanda keta rawa yace " Jalilah?"

Kallansa tai tana zare ido tace "yaya ina Dady yake?"
Yace "wallahi bansani ba, menene?"

Tace "Yaya meke damun Dady? Taya zai kori mutane daga gidansu?"

Hassan yace " bangane kora ba?"

Tace "nima bansani ba amma kome ya faru wannan abinda dan adam ya kamata ya aikata ne? Gidansu ne fa?"


Ta fada a rikice, Hassan yace "yanzu kizo muje in kaiki gidan gaisuwa komai ya biyo daga baya, sannan mutanen nan sumafa sun cutar dake."

Hawaye ya sake zubo mata tace "sun cutar dani amma ba kamar shi wanda ya haifeni ba, ya banzatar dani da mahaifiyata duk abinda ya faru damu ba ruwansa........."

Rungumentan dayai ne yasa tai shiru, yace "ya isa haka nan, ki kira Goggo ki sanar mata sai mu biyo mu dauketa."

? Ta daga kai alamat to.


Nan ta kira ta sanar mata, Hankalin Goggo ya tsahi tsantsa dan gaba daya ma kasa magana tai, Jalila ta koma ta shirya suka fito suka shiga mota, gaba daya haryanzu hankalinta ya kasa kwanciya dajin abubuwan nan biyu.


Gidan Goggo suka wuce suka daukota suka fito, Hassan yace "kamar ya kamata asai wani abun ko?"

Jalila tace "abu kamar me?"

Yace "bari na tambayi Abba."

? Shiru tai ya kira Abba sukai magana, itakam sai cewa take "Goggo nikam dama Inna batada lfy ne? Ni gaba daya na kasa gane abinda ke........"

Tabota da Hassan yai ne yasa ta kalleshi, magana yai mara sauti yace "Karki kauce hanya."

Shiru tai itakam gaba daya....
Goggo kam dama tundaga gaisuwa batasake magana ba, gaba daya mutuwar tazo mata a ba zata.



**********

? Kallan kansa yai a madubi "me ya kawoshi nan?"

Hannu yasa yana shafa kirjinsa yace "Sageer da alama ziyara zaka gidan Aunty Nana."

? Wata zuciyar tace "kaine kake zuwa gidan haka kawai?"

Can yai sauri ya kara cewa "ai yanzu haka na koma."

? Kallan layin da yake yai yace "ai dubata zanyi a musulunci kuma ziyarar mara lafiya akwai lada mai yawan gaske."

? Kara tada motar yai yana dan hango gidan shikam yaje yace me?
Inaa bada shi ba, gaba yai kadan ya juya kan motar, yana neman yin gaba mai adaidaiti na parking, fitowa tai daga ciki sanye da kayan makaranta na health school, kudi ta mikamai ta juya, hartayi gaba sai kuma ta tsaya ta juyo ta kalli motar, girman idanta ta rage dan ganin mutumin dake ciki.


Kunya ta kara kama Sageer ya daure ya fito tare da dan daga mata hannu kadan, yana yake.

Maimuna ta dan fara takowa shima yana takowa, sai da suka matso kusa da juna sannan tace "Ina yini?"

Yadan sosa keya kadan yace "lafiya, nazo wucewa ne sai na hango gidanku, naji kamar ya kamata na tambayi jikinki."

? Kallansa tai dan taga sanda ake juya motar tana hanya, tace "na gane shine kake neman juyawa?"

Yace "hmm daga bayane nai tunani kamar kuma na tafi, kar kiji abin banbarakwai."

Murmushi tai tace "yanzu fa?"

"Yanzu kam tunda naga kingani naga kuma kamar dai kamar dai."

? Tace "to yanzu nagode zance?"

"Ba nagode kadai ba kinga saboda kar asani tunani dawowa inaji number kawai za'a bani yanda zan kira."

? Batai mamaki ba, dan yanda fuskarsa take da idanunsa yasa ta fahimceshi, tadai gane ta baya yakesan biyo mata.

? Murmushi tai kafin ta mikamai hannunta, wayarsa yamika mata yana murmushi.

? Amsa tai ta saka mai, nan suka danyi hira kadan kafin ta shiga ciki.

Tana shiga ya washe baki yace "ahhh Malam Sageer da alama kaima......"

*************


? Kayan abincin da ake ta shigowa dashi ne yasa mutanen dake zaune suka mike suna cewa "daga ina??"

? Jalila ce ta shigo itada Goggo bayan masu ajiye abincin sun ajiye, Safeena na hango Jalila ta mike da gudu tazo ta rungumeta tare da fashewa da kuka....

Itama Jalila hawaye ne ya zubo mata, Yasmeen dake kwance jikin Mumy ce itama ta mike da gudu ta taho gun Jalila.

Hawaye ne ya kara zuboma Mumy aranta tsantsar nadama ce fal, Goggo Safeena ta kalla tana kuka tace "Goggo sannu da zuwa." Dan da bata ganeta ba saboda canzawar datai.

Mumy ta mike tacema "Goggo tazo ta zauna."

Mutanen gun kuwa mamakin kayan da aka shigo dashi da kuma sunan Jalilah da suka jine yasa kuwa ya kunshe gulmar dake ransa, dan tabbas sunsan sunan wasu kuma sunsanta.

? (Balle dama a wannan lokacin da gidan mutuwa ya zama gidan gulma, gidan sa ido, gidan hira da gidan cika ciki, mutuwa kuma anbarma wanda akayima)


********

Tsaki yai tare da cillar da wayar kan gado dayaga sakon Safeena akan cewa Inna ta rasu, a fili yace "Ankarama kasa nauyi."


? Ya kwanta kawai tare da neman yin bacci.

Sai dai duk yanda yaso yai baccin nan ya kasa, daga ya kwanta sai ya farka a razane, mikewa yai ya dara bankan ruwa, tare da komawa kan kujera ya zauna......



#OneLuv=ؕ?=??? *JALILAH* =???


Written By : *AYUSHER MUHD*
Wattpad: *Ayusher Muhd*


_Gaisuwa tare da sakon godiya gareku Mom Farhan, Haske da Meela Adeel wanna shafin naku ne >?p?>?p?>?p?>?p?Much Luv

*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*

Tuba nake jiyaan jini dif kamar wutar nepa=?H?
*75*


? Tana shiga daki ta jingina da jikin kofa tana maida ajiyar zuciya, itakam Hassan nema yake ya maidata mara kunya.

? Jin an murda kofar yasa ta kalli jikin kofar inda take a jingine, yace "wallahi ko a bude ko kuma in na shigo in wahalar da mutum."

Jalila tace "menene wahalar?"

Yace "Ayya wallahi in na irga uku ba'a budemin ba? Hmm ban masan ta ina zan fara ba."

Guntse dariyar ta tai tace "nima sai na kira Ummy."

Yace "wacce Ummyn? Ai kema kinsan Ummy tawa ce, ko kwace akesan min ne dama ban sani ba."

"Zan faea irgawa fa, kuma ko wacce number na kira tana dauke da babban bashi wanda kiss kadai bazai biyashi ba."

? Daga kofar tai ta shige can cikin dakin, yana shigowa ya bita da inda tai, da sauri ta haye gado tare da saukowa daya bangaren, tana kokarin nufa kofar yai gudu ya rufe kofar sannan ya fizgota suka fadi kan carpet.

Wani irin dan kara yai tare da cewa "shikenan an karyani."

Dagowa tai da sauri gabanta na faduwa, ta lleahi idanunta sun firfito.
Cikin tsananin tsoro tace " Yaya? Ina ne? Nashiga ukuna."

Hannunsa ya langwabar yace "nan ne, nikam kamar kashin gun ma ya karye."

? Gabanta ne ya kara faduwa a tsorace ta kalleshi sannan ta shiga taba hannnun, tsabar tsoro sai ma taji kamar ya karye din, tana tabawa yana cewa "wash Allah na...."

Jalila ta kar rikicewa tace "Yaya tashi muje asibiti, nashiga ukuna."

Idanunta duk sun canza, yadan karkace kai irin abin zafin nan yace "Jalila kaini na kwanta kawai ba sai naje asibiti ba."

"Yaya kargun yai tsami gobe azo kasha wahala."

Yadan kara raunane fuska yace "yanzu insu Ummy sukaji kin karya musu d'a mai zasu ce? Ki bari gobe sai mu fita ba tare da kowa ya sani ba."

Jalila tai shiru tana tunani, yace " kinsan dai in Ummy taji kin karya mata d'a akwai karamin matsala ko?"

Jalila tai shiru tana tunanin yanda Ummy ke san Hassan, yawo ta hadiya sannan ta kalleshi.

Yace "kaini na kwanta bakomai insha Allah."

Jalila idanunta sukai raurau gaba daya itakam batasan ma ya zatai ba, yace "ni nace ki kaini na kwanta ba wani abun."

Jalila ta dagashi yanata wani wash, ta kwantar dashi.

Yace "dan bani ruwa nasha."

Da sauri ta juya ta dauko mai ruwa a fridge ta matso ta bashi, yace "bazan iya mikewa ba."

Da sauri ta ajiye ruwan ta shiga kokarin dan jinginar da shi, sannan ta miko mai ruwan ya amsa da dayan hannun ya fara kokarin yanda zaiyi ya bude, da sauri ta amsa ta bude mai sannan ta mikamai, amsa yai da hagu yasha.

Yana gamawa ya mika mata jarkar ta amsa, yace "bari na kwanta dan buguwar tasamin ciwon kai, idanunta suka kara raunana tace "yaya Allah muje asibiti naba su Ummy hakuri."

Yace "karki damu Baby, Kinga Ummy tanada hakuri tana kuma da sanyi sai dai bata kyale wanda ya tabani ko kadan, kinga mubar maganarnan."

Jalila ta kalleshi sannan tace "to."

Gyaramai kwanciya tai sannan ta zauna a gefenshi, tare da rike mai dayan hannun.

Yace " banfa ci abinci ba tun na safen nan ga yanzu har an kusa magrib."
Tace "bari naje kasa na zuboma nasan tunda Ameera ta dawo tayi girki."

Ya daga kai kamar wanda baya magana, tace "sannu." Sannan ta mike ta fita, tana fita yai dariya yace "ahh baby nah." Ya jawo pillow ya rungume.


**********

Kallansa yai kafin yace "kana nufin bazaka bani kudina ba kenan ko me? Ni na kasa fahimtar inda ka dosa ne."
Wani mugun murmushi yai yace "wai kai da a haukarka kana tunani ni zan bi wadanda muka rabama kudi ince su dawo dashi ne ko me?"

Cikin zafin rai Dady yace "dama ba sun amshi kudin bane dan su bani mukami? To tunda bai samu ba basai su dawo dashi ba?"

Wata dariya yasa mai wanda ya kara kular da Dady yace "stop dreaming Abakar, dama nine na damu mu baka wannan mukamin ko saboda nima na samu abinda nake so, ko da dan haukarka da karamin tunani ka dauka 'yan board din ne suka amince a kawo ka a baka matsayin nan?"

Kallan mamaki Dady yakemai kafin yace "ba hakan bane?"

Director din yasa dariyar mugunta yace "ah haba? Abinda ka dauka kenan? Saboda na basu kudinka na lalabasu ne yasa kaga suna daga wuya akan a baka mulkin nan, kudin daka raba musu ne yasa suka bi bayanka bba wani abun ba."

Dady ya matso a zuciye ya cakumeshi yace "ni zaka wulakanta? Kasan ko ni wanene?"

Cikin karfi ya fincikeshi hakan yasa dady ya fadi kasa, board director din ya nunashi da yatsa yace "kai wanene? Mtsw ni zaka maida karamin mutum? Ko ni nace ma ka kwaso kudi dayawa? Ni dai nasan cema nai kawai ka kawo kudi a basu, ko nace ma ga yawon kudin da zaka ciro? Shashashan banza kawai, har kai ka isa ka maidani karamin mutum? Ashe da babban kuskure na kusa tafkawa.

Yai tsaki sannan ya koma cikin gida, Dady ya mike da kyar ya shiga mota yai shiru, can ya dauko wayarsa ya duba dan yaga balance dinshi.

Dubu dari shida ya gani kwata kwata, dan dama miliyan bakwai ne dashi a ciki, wai saboda ya birgesu sai yabada miliyan shida wai a raba musu dan su zabeshi, sannan ya kama katan hotel inda yake ciki, tsaki yai kafin ya sa hannunsa a saman kansa, yanzu gashi ance dole ya kawo takardar ajiye aikinsa gobe, nausan sityarin motar yai kafin yai wata ajiyar zuciya, tun farko ya riga ya bata kansa agaban mijin Jalila yazu gashinan hanyar daya bi bata billemai ba.

Kwafa yai kafin yaja mota yai gaba, hotel dinsa ya shiga ya wuce ya kwanta yana lissafi, can ya dau waya ya kira Jalila, dolene ya kira ta ya lallabata ta samu tasa mijinta ko aikinsa ne a barshi dashi in har baza'a bashi matsayinsa ba.

Hassan na kwance yana jiranta ta kawo mai abinci yaji wayarta na kara, ganin number ne yasa ya ko daukan wayar, kiran bai dade da katsewa ba ta turo kofar, da sauri ya gyara kwanciyarsa.

Ta shigo ta ajiye abincin ta matso inda yake, tace "yaya tashi kaci abincin."
Kallanta yai tare da kara ragwancewa yace "Jalila hannuna kamar zai cire."

A tsorace tace "nikam yaya ka taimakamin muje asibiti zanba Ummy hakuri."

Yace "dagani naci abinci."

Dagashi tai sannan ta kalleshi rike da spoon din, dan a hannun dama ne ta ina zaici?
Kallanta yai sannan ya bude bakinsa, haka ta debo zata samai wayarta tai kara, kallan wayar tai sannan tasamai sannan ta matso gefensa tasa hannu ta dauko wayar, dauka tai tare da yin sallama.

Jalila! Sunanta da aka kirane yasa gabanta faduwa dan ta gane mai muryar, dady yace "Jalila magana zamuyi in kina kusa da mijinki dan Allah kidan matsa."

Jalila ta kalli Hassan wanda shima kallanta yakeyi, tace "me zakacemin da har sai na matsa?"

Dady yace "Jalila wai yaushe kika zama mai musu ne? Nine mahaifinki wanda fa duk duniya baki da kamarshi."


Shiru tai sannan ta ajiye abincin a side bed sannan tamike, Hassan kam bai mata magana ba yana kallo ta fita falo ta rufo kofar.

Jalila tace "inajinka yanzu ba kowa, Dady yadan ja numfashi yace "Jalila tunani nakeyi, mai zai hana in
dawo da mahaifiyarki? Na tabbatar ke kanki babban burinki ne hakan, yanzu tunda nasamu gurin zamazan kula da ita yandaya dace, ke kanki kinsan bawai santa bane banayi, ba dai yanda zanyi ne."


Jalila tai Shiru tanajin wannan sabon salon wulakancin, cikin takaici taji Yana cewa "Jalila kinsan abinda mijinki yamin kuwa? Kinsan wulakancin da sukamin shida kaninsa? Amatsayina na mahaifinki ai banaji ko mai nai ya kamata yaran nan yaci mutuncina, sai dai bayansa zanyi nima nasan ban kyauta ba dana nausheshi, dan Allag Jalila ki bashi hakuri kinji? Ni mahaifinkine ya kamata yasan darajata kinji?"


Bakin Hassan ta tuno a ranar dama jikinta ya bata Dady ne sai dai batasan zargi shiyasa.

Dady zaiyi magana tace "kaje gaisuwar Inna?"

Yace "wani gaisuwa bayan na rabu da matar sannan ko kin manta ne? Yanzu nake miki zancen komo da mamanki."

Jalila cikin takaici tace "Dan Allah dady kai wani irin mutum ne? Wanda zuciyarsa da kansa kawai ya sani? Taya mutum magidanci mai iyalai kamarka za'ace bakasan komai ba sai kanka? Baka tausayin mu? Baka tunanin yanda muke kallanka?
In har ni da Goggo bazaka faranta mana ba taya za'ace wadanda ka moresu a iya tsawon rayuwarkasuma bazakaji tausayinsu ka faranta musu ba? Wannan wani irin tsabar san kai ne?
Sannan maganar Goggo ma ka dainata dan alama ce ta kaidinba mutumin da zai iya rike wani bane, kanka kawai zaka iya rikewa, sai ka cigaba da zama kai kadai har karshen rayuwarka dauke da alhakin 'ya'yanka wadanda Allah ya daura maka hakkinsu, sannan magana ta karshe, Karkayi tunanin Goggo har yanzu a wacce ka sani ne, yanzu tanada gatan da ya wuce tunaninka, dan tanada gidan zama sannan bata rasa komai na duniya ba, insha Allahu kuma Allah zai bata wani mijin ta aura, hakan yasa dama nake neman taimako a gurinka akan in da auranka a kanta ka taimaka ka sauwake mata, ko dan........."

"Jalila ni Abubakar kike fadawa haka? Har yaushe aka haifeki da zaki nemi yimin wa'azi?"

Jalila ta maida numfashi tace "ba wa'azi nake ma ba rokonka nake."

Roko? A banza? Inhar kinasan na saki mahaifiyarki sai kin sa mijinki ya barmin aikina ya kuma barmin company din dana sha wahala gun kula dashi."


Mamaki ya kara kama Jalila idanunta suka ciciko cikin takaici tace "Dady yaushe ka zama haka? Nasan dama can kanada san kanka sai dai bansan abin naka yakai haka ba? Dady wace irin rayuwa ka daura kanka a ciki?"

Dady yai shiru, Jalila tana kuka tace "ka manta wahalar dakaba baiwar Allahn nan? Kasa ta rabu da iyayenta, ta rabu da 'yan uwanta, sannan kai baka bata farin ciki ba sai kunzuga mata dakai, yar data haifa baka taba tausaya mata ba, baka taba nuna mata ko kula da ita kamar yanda Uba ya kamata ya kula da dansa ba, dan Allah dady a tsawon rayuwarka mai ka taba yima baiwar Allahn nan? Wannan wani irin san.........."

Kukan daya kubce mata ne yasa ta kasa magana, dady yai shiru shikansa yanzu jikinsa yayi sanyi dajin kalamanta, da sauri ya kashe wayar sannan ya kwanta rigingine a kan gado.

Hassan na jin kukanta, sai dai baisan me zai ce mata ba, bakin cikin mahaifi ne wanda ba wanda ya isa cire mata shi.

Idanu kawai ya runtse yanajin kukan har ransa, mikewa tai ta bude kofar tana share hawayenta, kusa dashi tazo kawai ta rungumeshi tsam, shafa mata baya ya shiga yi, ta dago ta kalleshi tace "bari nasa abincin a microwave nasan yanzu duk ya huce."

Kai kawai ya daga mata ta dau abincin ta fita dan dama a plate kawai ta zubo mai.


Tana sauka su Ummy na shigowa ta musu sannu da zuwa sannan tai kitchen, Ummy ta kalli Abba tace "Jalila akwai sansanyan hali, yanzu kaga wai matar data mutu fa tayima kuka haka idanta ya canza haka?!

Abba yace "matar data wahalar da ita, gaskiya mu gode Allah."

Nan sukai ciki suna hirarta, komawa tai sama ta taraddashi a zaune yanda tabarshi, kusa dashi taje ta zauna tace "tunanin me kake?"

Yace "ba komai." Amma a ransa yace a satin nan zamu muyi visa.

Haka ta zauna ta bashi abincin har ya koshi, ta bashi ruwa yasha, zata mike ya riko rigarta, kallansa tai yace "wanka nake sanyi."

Cikin mamaki tace "yanzun? Ya zamuyi?"

Yace " ya zakiyi kuwa tunda ke kika jimin ciwo kika karyani, haka nan zaki zo kimin."
Idanunta taxaro tace " ni?"

Yace "sosai."

Haka ta taimaka mai ya cire kaya yasa towel itakam duk kunya ta isheta, sai rokonshi take ya bari yayi wankan gobe amma yaki, haka ta jashi sukai toilet.

Bayata juya saboda kunya shikam ya sa hannu ya jawota cikin bath hub din, kallansa tai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login