Showing 117001 words to 120000 words out of 149705 words

Chapter 40 - Jalilah Book One Complete Hausa.doc

Ayusher   

28 Oct 2025

626

barma saman."

Dukansu sun gane me yake nufi, Sageer yace "ayi haka kuwa?? Ba gwara ni in fita ba ko kusa ne sai na nema?"

Da sauri Hassan yace "a'a kaga kaine karami kana......."

Dariyar da suka samai ne yasa yai shiru tare da cewa "ya akai?"

Abba yace "wato kafisan kaganku ku biyu?"

Hassan yai gum tare da cigaba da tukinsa, Abba ya mai nuni da fruit suka tsaya suka siya.

A cikin gida yai parking, suka fito.


**********


Jalila kuwa bayan ta fito Ummy ta kaida ita daki ta sata ta shafa janbaki da kuma kwalli, tana sawa kusa ta fito das, Ummy tace "ko ke fa? Ki dinga yin wannan simple makeup din amma ba daga mai sai powder ba."

Jalila tace to a kunyace, Ummy ta fito tana cewa "Jalila fito ki tayani mu karasa, nan Jalila ta fito da sauri dankwalin na saman kanta, haka suka karasa girki dan dama Ummy tayi kusan rabi, suna jerawa a dinning Ameera ta dawo, tsalle tai tana kallan Jalila tace "gaskiya ne Matar Yaya irin wannan kashe kala?"

Jalila ta maka mata harara tace "to hajiyar sa ido."

Ameera ta ajiye jaka da hijab ta matso kusa da Ummy ta gaisheta da gida sannan ta gaida Jalila da gida tace "amma an samu matsala da daurin dankwali."

Jalila ta matso kusa da ita tace "ai anan matsalar take."

Ameera ta sa hannu ta rikota tace "Ummy muna zuwa."

Jalila ta tirje tace "bari mu karasa jerawa, ko?"

Ameera ta saketa sannan itama ta fara neman tayasu, Ummy tace "dama kin barshi dan ana gama ci zakiyi wanke wanke, sannan kiyi abincin dare."

Kallan Ummy tai da sauri tace "duk ni kadai?"
Ummy tace "ko dani za'ayi?"

Ameera tace "a'a!"

Jalila tasa dariya dan yanda tace a'a abin dariya.

Suna gamawa taja hannun Jalila sukai daki, zata fara yi mata Jalila tace "tsaya ayi a hankali dan na koya."

Ameera tace to, nan ta fara mata a hankali tana gani, suka gama aka sake warewa aka sakeyi, Ameera tace "yauwa Matar Yaya yanzu kinfi kyau."

Jalila tai murmushi tace "Allah yasa na iya daurin da kaina."

Ameera tace "ai ba wuya zaki iya."

Nan ta kara sa dan sosan hoda ta gyara fuskarta, jin magana a falo yasa ta kalli Ameera da sauri.

Ameera tace "Mai Sanyinki ya dawo."

Jalila ta mintsineta tace "wallahi zan fadamai sunan da kike cemai."

Ameera tace "na tuba ayi hakuri."

Nan Jalila tai dariya, Ameera ce ta cire kaya ta sa wasu tana cewa "ba wanka dan wallahi sanyi nakeji."

Jalila tace "ni dai sa mu fita tare dan kunya nake."

? Ameera ta sa riga yar kanti doguwa zuwa gwiwa sannan tasa wando pencil tasa mayafi, ta kalli Jalila tace "ya kamata muje kema mu samo miki kayan....."

Ta wani kanne ido, Jalila ta zuba mata ido can tace "wai ni Ameera a gidan wa kika san komai haka? Gaba daya nikam mamaki kike bani."

Ameera tai dariya tana sa turare tace "lalai Aunty Jalila ai mu nan.... a dai bar maganar kawai kar aji kunya amma idanun nan sun san komai."

Jalila tace "to kuwa na kusa fadawa Ummy ko in fadama Yaya."

? Ameera tace "rufamin asiri wallahi wata kawa nai a islamiya ita ke fadamin komai, har littatafai take karanta mana."

Jalila tace "ba karatu kuke ba kenan?"

Ameera tai shiru kafin tace "munayi."
Jalila tace "Hmm..."

Da sauri Ameera tazo kusa da ita tace "Ni kaina nasan abinda muke bai daceba, kafin ma ki fada Allah na daina, dan na tabbatar Ummy inta sani zataji ba dadi dan ta yarda dani."

Jalila tace "to dan Allah adaina."

Nan suka fito tare.


*******

A falo kuwa Hassan suna shigowa ya wuce sama dan ya dauka tana can, yana shiga yaga bata ciki, juyowa yai ya fito sai daya fito falo ya tsaya yace "yanzu in na sauka bazasu fahimci abinda nazo nema ba?"

Nan ya zauna a falo na wasu yan mintina kafin ya sauko, Ummy na ganinsa ya sauko tace "Hassan ka sauko?"

Ya matso yana cewa "eh Ummy nadan shiga toilet ne."

Tace "ya kaji yau? Dakaje masallaci?"

Kusa da ita ya zauna yace "Ummy dadi, sosai."

? Tai murmushi tace Alhamdulila, muje muci abinci."

Nan suka nufi dinning.
Abba da Sageer na zaune suna magana, suka karasa, Abba yace "ah mama boy an karaso?"

Hassan yace "Ummy kinji Abba abinda yake cewa"

Ummy ta kalli Abba tace " gaskiya adaina tsokanarmin yaro, haka kawai mutum da matarsa muna sa ran baby kusa amma........."

Kallan da Hassan ya mata ne yasa tace "Hmm me ma nake cewa?"

Dariya sukasa dukansu banda Hassan wanda yama rasa me zaiyi, Ummy tace "zauna kaji Hassan dina."

Hassan ya zauna yana cewa "Ummy na kula kema."

Tace "a'a ni ai wasa kawai nake ma.

Fitowar dasu Jalila sukai ne yasa ya kalli gun, dan yanajin motsi yasa tasa ce ta fito, baimayi tunanin Ameera ba dan ya dauka bata dawo ba, sannan yama manta dasu Ummy agun.

Zuba mata ido yai, wanda itama ta kalleshi, ganin yanda yake kallanta yasa kunya ta kamata, ta sauke idanunta kasa.

Sageer ne ya tabashi yace "Yaya ka manta muna falon ne?"

Juyowa yai ya kallesu yace "waccan yarinyar nake kallo, badai yau bataje makaranta ba?"

Sageer yace "taje mana sun dai tashi ne."
Fcd
Ya kalli Sageer kamar gaske yace "da wuri haka?"

Yace "ka manta friday ne? Ai da wuri suke tashi."

Yace "oh! Lalai."

Yaja baki yai shiru.



Su Jalila ne suka karaso Ummy tace "Jalila zauna kusa da mijinki, Ameera ke dawo kusa da Sageer."

Jalila ta dan kalleshi sannan taja kujera a kunyace ta zauna, itakam da kyar gaskiya ta iyacin abinci a haka? Dan ma ta yafa mayafi a kasan kafadarta.


Ameera ta karaso ta gaida kowa, ita ma Jalila ta gaishesu, Hassan kam kallanta kawai yai bai ce komai ba.

Abba ne ya fara zuba abinci kafin kowa ya zuba, Hassan bai kara kallanta ba sai dai gaba daya so yake a dan tashi su hau sama kawai ya dan jawota jikinsa ya rungume.

? Haka kowa ya zuba itakam dan kadan ta zuba a plate dinta, Hassan dayazo zubawa ya jawo plate dinta ya kara mata, a hankali cikin maganar rada yace "ko kinfisan ci da ni?"

Kallansa tai sannan tai kasa dakai, tura mata plate dinta yai sannan ya zuba nashi ya ajiye.

? Duk abinda sukeyi kowa na kallansu amma ba wanda ya bari aka? gane, a hankali take cin abinci, har ya kusa cinye nashi bata wanici dayawa ba, Hassan ya karkato kadan yace "in ba so kike na baki a gun nan ba kiyi gaggawar ci."

Tace "inafa ci?"
Yace "to ko na taimaka miki kici sosai?"

Da sauri tace "zanci."

Murmushi yai sannan ya juyo, Sageer? Abinda ya fado mai kenan da sauri ya kalleshi, gani yai hankalinsa ma baya kansu, magana suke da Ameera.

Gaskiya shikam yana tunanin barin gidan nan, ko saboda Sageer kamar bai mai adalci ba, gwara ace suna dan nesa ko yaya ne.


Abba ne bayan sun gama suna shan fruit din da suka kawo a falo, Jalila da Ameera na zaune a gefe, ya kalli Hassan sannan ya kalli Ummy yace " jiya inata wani tunani."

Tace name kenan?

Yace " akan karatun Hassan, kinsan yanda kasarmu take, yanzu in Hassan zai nemi level 1 duk abin baxai mai dadi ba saboda shekarunsa, shiyasa nake tunanin mu nemarmusu kasar arab haka suje can shi da matarsa suyi karatunsu a tare."

? Hassan ne ya kalli Abba yace"Abba wata kasar?"
Yace "Eh mana ai gwara a nema tun yanzu kafin karfina ya tafi, yanzu ga Sageer kaga inka dawo kuka hadu ku biyu hankalina zaifi kwanciya nima sai na ajiye aikina na huta."

Ummy tace "kace jiya bakai bacci ba kanata tsare tsare?"

Yai dariya yace "kudaije kuyi shawara ku gani dakai da matar taka."

Hassan yace to, yanasan barin gida amma ba wata kasar ba.


Mikewa yai ya hau sama, Jalila ta bishi da kallo, Ummy ce tace "La Jalila kinga baisha abarbarnan ba, dauka ki kaimai."

Tace to sannan ta mike tazo ta dauka tahau sama.

A hankali tasa hannu ta murda kofar tare da sallama, Hassan na zaune a bakin gado ta shigo, drawer dake gefen gadon da yake ta ajiye sannan ta zauna kusa dashi tace "Ummy tace na kawo......"

Jawota yai ya rungumeta tare da sakin numfashi, a hankali yace "ya jikin?"

Tace "da sauki."

? Saketa yai sannan yasa hannu ya jawota kan cinyarsa tare da sakala hannunsa ta cikinta, kansa ya zuro ta kafadarta ya dan kwantar kadan yace "Jalila me kike tunani akan maganar Abba?"

Tace "Kaine zakai tunanin abinda kaga ya dace, ni ko me ka yanke yayi a guna."

Hannu yasa ya juyo da fuskarta saitinsa a hankali ya sumbaci bakinta yace "kinyi kyau wanda har ji nai kamar na jawoki jikina."

Idanunta ta dago ta kalleshi tace " ya bakai ba?"

Yace " oh kumafa haka ne, ya akai banyi ba?"

Tace "ah haba nima ai wasa nake."

Yace "wasa? Nikam ba wasa nake ba, next time ki bini bashi."

Idanu ta zaro tace "da gaske sai kayi?"
Yace "ah ba matata bace?"

Kallan mamaki tamai tace "agaban su Ummyn? Su Abba?"

Yace "Uhm Hmm....."
Baki ta saki tana kallansa, nashi bakin yakai ya sumbaceta kallansa tai.
Yace "me? In kara ne?"

Tace "kai yaya."

Fuska ya hade yace "wai ne menene hadinki da sunan nan?"

Tace "wai to meyasa bakaso?"
Yace "ah ni yayanki ne? A yaushe na zama yayanki?"

Tace "to ba duk haka aka cema ba?"
Yace "inji wa?Ummy Hassan take cemin haka ma Abba, Sageer da Ameera ne ke cemin haka."

Tace "to ni me zance ma inba haka ba?"

Yace "oho amma nidai banasann sunan."

Kallansa tai ta sakarmai wani murmushi tace "to ya...."
Sai kuma tai gum...


(Nace samun gu su Hassan>??)

#OneLuv=ؕ?
[1/12, 9:39 AM] Maryam: =??? *JALILAH* =???


Written By : *AYUSHER MUHD*
Wattpad: *Ayusher Muhd*


*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*


? (_D home of expert and perfect writer's_=ء?)


*65*


? Idanu ya kafeta dashi, tace "to ni wlh...."
Katseta yai yace "shikenan fadi abinda ya miki nima zan fadi abinda yamin."

Ya dagata daga jikinsa ya mike, da sauri ta sa hannu ta rikoshi, kallanta yai fuskarsa a sake yace "menene?"
Tace "haushi kaji?"
Yace "ko kadan, banasan ne na takura miki akan abinda bakyaso."
Tace "baka fahimceni bane yaya bawai banaso bane."
Sai kuka tai shiru tana kunyar tace batasan me zatace mai ba.

? Kallanta yai yace " mubi komai a hankali, gaba dayanmu a new to this, kar muyi rushing, let's take it slowly.
Kinji?"
Yai tambayar yana kallanta, kafin yace "it look like kamar ni nake rushing dinmu."

A hankali tana kallansa tace "a'a yaya, ko kadan ba haka bane."

Ya daga kai alamar fahimta, kafin ya dan rungumeta na wasu sakan ni sannan ya saketa ya nufi toilet.

? Zama tai tare da yin ajiyar zuciya, ta sa hannu akanta tare da cewa "duhun kai baiyi ba wlh, ni yanzu sunan ma dazan cemai kadai bansani ba?"

? Kwanciya tai rigingine tare da sa hannunta a saman goshinta tace "Goggo na!"

Hassan kuwa yana fitowa ya shafa mai a hannunsa ya sa turare, kallanta yai itama ta kalleshi sannan ta mike zaune, yace "kin gaji ko? Naga kunsha girki."

Tace "a'a bayan duk Ummy ce tai sama da rabi."

Ya matso tare da daukan agoggonsa daya cire daya shigo yana sawa yace "Ki sha abarbar."

Tace "Ummy ce tace na kawo ma fa?"
Yace "itama Ummy wasa takeyi tasan abarba bata dameni ba inasha amma ba sosai ba tun ina yaro."

Cikin mamaki take tunanin to meyasa Ummy tace ta kawo mai?
Kallanta yai yace "nasa a dauko mun motata inaji yanzu ta iso, ko zamu ki gaida goggo?"

Da sauri tace "da gaske?"
Yace "eh, naji zatai tafiya gwara kije kafin ta tafi."

Tace "bayan ko fadamin batai ba."

Wayarsa ya dauka yace "to tunda bazaki ba bari ni naje."

Da sauri ta mike tace "zani zani."

Murmushi yai tare da yin gaba.

? ***************


A zabure Inna tace "me kace?"

Dady yai murmushi tare da ajiye mata takarda yace "Yanzun nan muka dawo daga gun lawyer 'yarki tamin transfer na shares dinta, shine nace bari na sanar dake karkiji a gari kiji ba dadi."

Hannunta ne ya shiga rawa ta na kokarin daukan takardar, Dady yasa hannu ya dago mata tare da mika mata saitinta yace "gashi! Shiyasa yanzu nake tunanin kamar zan iya kwatar matsayin da aka hanani, dan yanzu na fiki shares a company din balle in na hada dana Safeena da Sultan, tunda jininane su, ni an hanani saboda ni ba jininki bane yanzu fa?"

? Inna kam takardar kawai take kallo ga kalamansa na ratsata, kanta ne yadau wani irin zafi sai gani nai tayi baya luuu.....
? Dady ya mike tsaye a tsorace tare da kwallawa Mumy kira, ya boye takardar a aljihu, gabansa na wani faduwa saboda tsoro karyaje ya zama ajalinta.

Mumy wacce ke kwance akan kujera tunda suka dawo ta mike da sauri a zabure ta hawo sama.

Ganin Inna a kwance yasa ta kwalla kara tare da kallansa tace "mu kaita asibiti, in wani abu ya samu Inna banaji zan iya rayuwa...Nashiga ukuna."

Da sauri ya kinkimeta sukai kasa, a rikice suke dukansu, a mota ya sata suka ja sukai gaba.

A cikin asibitin Standard suka tsaya, Mumy rungume da Inna sai kuka take kamar ranta zai fita.

Suna shiga aka amsheta, nan likitae dake aiki a lokacin ta shiga duba halin da Inna ke ciki.

Sai da suka dade dan har Mumy tayi kuka harta gaji kafin su fito.

? Kallan Mumy wacce tana ganin likitan ta fito ta taso da sauri, tace "Doctor menene ya faru da Innata?"

Murmushi ta mata tare da dafa kafadarta tace "ki shiga tana ciki, in kin gama ki sameni a office zanga wasu patient ne."

Da sauri ta shiga ciki, Dady ya bi bayanta.

Inna na kwance tana bacci, ansa mata abu a hancinta, Mumy ta zauna tare da rike hannunta tana hawaye.

Wayarta da tun suna mota taketa kara ta kalla, zaro ta tai a jaka tare da duba mai kiran.
Number Safeena ce a hankali ta daga tare da cewa "Safeena!"

Kuka kawai taji ansa mata, hankali a tashe tace "Safeena? Menene hakan?"

Safeena cikin kuka take cewa "Mumy ki taimakeni, dan Allah ki zo ki daukeni daga garin nan ko kice in taho."

Hankali tashe tace "Safeena menene hakan? Ke da kika tafi karatu?"

Tana kuka tace "gaba daya ni banajin dadin komai a garin nan, ban iya komai ba, dan komai yi min ake anan, ni ba kawaye ba kowa baya sona, gaba daya komai yamin zafi, wallahi ni karatun ma ba gane shi nake ba, Mumy ki taimaka ki ce na taho inba haka ba Allah zakuyi dana sani."

Cikin tsananin tashin hankali ta mike tsaye tace "Safeena! Karkiyi komai na rokeki da Allah, naji koma menene ni zan dauki laifin ki shirya ki sai ticket ki taho, koma menene ayi daga baya."

Safeena tasa kuka tace "nagode Mumy!"

Kafin Mumy ta sake magana harta kashe, Dady ne yasa hannu ya rikota yace "menene ke faruwa? Me makwan ki lalasheta sai kice ta taho?"

Tace "to ya zanyi? Cewa tai wallahi zamuyi dana sani, intai abinda bai kamata ba fa?"

Yace "ke bakisan birgar yara ba? Bakisan halinsu ba kenan? Tayi ne dan dama ki tsorata."

Tace "Dadyn Yasmeen in kuma ba hakan bane ba fa?"

Yace " amma yarinya akaita wata kasar ki sa ta dawo? Kudin da aka kashe fa?"

Mamaki ya kamata tace "kudi? Mu daina musu anan, Inna na kwance, amma nikam ya akai Inna ma ta shiga wannan halin?"

Shiru yai kafin ya jawota jikinsa ya rungume yace "ina lekawa na ganta a haka, bakisan tashin hankalin dana shiga ba."

Hawaye ne ya zuba mata tace "nagode ma Allah ma dayasa ka shiga da bansan ya zamuyi ba."

Dady ya kalli Inna tare da runtse ido.....


************

Yana gaba tana binshi a baya suka fara sauko wa, harya kai steps na hudu tace "yaya? Me zakacema su Ummy?"
Yace "ke zakiyi musu bayani ai."

Ta saki baki zatai magana taga har ya yi nisa, da sauri ta sauko.

Suna falo a zaune anata hira, Ameera ta zake sai labari take basu.

Sageer sai dariya yakeyi.

Suka sauko, Ummy ta kallesu tace "za'a fita ne?"

Yace "eh Ummy dama...."

Bata jira ya cigaba ba tace "a dawo lafiya."

Yace "sai mum dawo."

Sageer yace "Yaya ba neman Ameera tai rakiya?"

Harararsa yai yace "yau ba islamiya ne?"

Tace "yau fa friday yaya..."

Yace "oh ba'azuwa yau?"

Tace "eh!"
Ya juya ya fita, Jalila kanta a kasa tace "Ummy!"

Ummy tace "a dawo lafiya Jalila"


Ameera tai dariya, fitowa tai ta taddashi a gun Mamman da alama makullin ya ansa sannan suna magana.

Yana ganin ta karaso ya bude motar da key din hannunsa sannan suka cigaba da magana.

Itakam shiga tai ta zauna tare da kallansa yana magana, ta tabbatar da dane gaisuwa ma dakyar zata hadasu.

Can ya taho itakam ta saki jiki tana kallansa, sai dataga yazo jikin motar ta sauke idanunta da sauri.

? Bude motar yai ya shiga tare da kallanta ya kunna motar suka fita.

Sun danyi shiru kadan kafin yace "Kinsan wata rana da kika taho cikin ruwa, kina kuka?"

Tace "ni? Yaushe?"
Yace "ranan dana fara ganinki amma ke baki ganni ba."

Kallansa tai da sauri tace "kaine dama wannan dan......"
Sai kuma tai gum, sai kuma tasa dariya tace "dama kaine?"

Ya kalleta sannan yace "kinsan nasan kin zageni a lokacin?"

? Tace "ni?"
Yace "sosai dan na ganki a adaidaita ma kina harare harare, da yan maganganu."

? Kallansa tai tace "inalilahi..."
Ya kalleta kawai tare da mai dakai kan titi yace "ban taba tunanin mara kunyar nan itace wacce ake nemamin ba."

Tace "Allah inada kunya."

Yace "ai da nake nufi, dan haka na daukeki, sai dai in aka duba abin nine na miki ba daidai ba, ta ya ina ganinki cikin wannan halin amma nai ignoring dinki sannan naji haushi dan kin hararen?"

Ta kalleshi tace "nima ai ban kyauta ba, menene nawa nasan wanda ban sani ba ya taimaka min?"

Yace "kuma fa haka ne."

Dariya tai tace

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login