Showing 39001 words to 42000 words out of 149705 words

Chapter 14 - Jalilah Book One Complete Hausa.doc

Ayusher   

28 Oct 2025

653

ni kanwar yaya......"

Da sauri Jalila tace "kawatace Goggo, biyoni tai dan ta gaisheki."
Mamaki ne ya kama Ameera wacece wannan da har batasan asan matsayin ta? Sai dai ba shakka suna tsananin kama, dan kamar ma harta baci.

Jalila ta kalli Ameera, Goggo ta kara kallanta tace "Allah sarki na gode sosai."
Ameera tace "bakomai."
Kallan Jalila tai tace "bari inje gun Ya Sagir."
Ta juya ta fita, tana rufe kofar ta kara bin kofar da kallo, tabbas dabadan ance yar Mumy bace da tace wannan ce mahaifiyarta.

? Kwanciya Jalila tai a gefen Goggo dan tana jin jiki, Goggo ta shafi kanta tace " ki koma can ki kwanta dda kyau mana."
Jalila ta girgiza kai tace "barni anan."

Goggo ta kalleta tace " naji yarinyar nn tace Yaya Sagir? Ko Sagir din da ake bani labari?"
Jalila tai shiru dan batasan me zata ce ba.

Goggo tai murmushi, Jalila kam idanunfa ta rufe kawai, tana san sanar da mahaifiyarta sai dai tana tsoron kar jinjnta ya sake hawa, dan kuwa sanda aka kwantar da ita sai da akace a kiyaye sata a damuwa, wanda ta tabbatar in Goggo taji, ba magana kawai.....


? Acan gidansu kuwa Hassan ya shigo cikin gida, Ummy na zaune afalo tai shiru.
Tsayawa yai yanasan mata magana kuma baisan ta inda zai fara ba.

? Ganin bata da niyyar kallansa yasa ya juya jiki a sanyaye zai hau sama, jiyai tace "yanzu Hassan abinda kai ka kyauta min?"
Juyowa yai sannan ya matso kusa da ita, yace Ummy ni ban gane me na aikata ba.

Tace "kafi kowa sanin yanda matsala da lalurar cikin dare ke faruwa, taya zaka bar yarinya ita kadai a daki, yanzu inda ciwon ya gama cinta cikin dare fa?"
Yace "Ummy kinfi kowa sanin bana iya kwana da wani kusa dani....."
Tace " Hassan kanaso kace bakasan dalilin dayasa muka nemarma aure ba? Ko kuwa san kanka ne ya maka yawa da baka duba halin da nake ciki?"

Kallanta yai jiki a sanyaye, tace " akoda yaushe hankalina baya kwanciya da barin ka kai kadai a daki, saboda ina tsoron abinda zai iya faruwa, sannan yanzu an maka aure nan ma kace kai kadai zaka dinga kwana? Fad'amin Hassan menene marabarka da kafin kai auran?"

Kallanta yai sai dai baice komai ba.

Tace "In har na isa dakai na kuma isa in fadama kaji to daga yau inganku a d'aki daya, ban damu da duk abinda zai biyo baya ba sai dai jiya ya zama rana ta karshe da zaku kwana tare, sannan ko kunya ka barsu suka tafi asibiti kai ka shigo."

Yace "Ummy kinsan bana san asibiti."
Kallansa tai kamar zatai magana sai ta fasa, dolene subi komai a sannu tunda gaggawa ma aikin shedan ne.


? ****
Sagir ne ya kalli Ameera yace "ina kuma kuka je?"
Nan ta fadamai abinda ya faru, cikin mamaki yace "yanzu tana can?"
Tace "eh."
Sagir ya haura saman.

Jalila na kwance kusa da Goggo suka bude kofar tare da sallama.

? Jalila na jinsa ya shigo, kallab Goggo yai sannan ya gaisheta.
Ta amsa fuska a sake tace "Malam Sagir ashe da rabon zan ganka?"
Dasauri Jalila ta d'ago ta mike tsaye tace "Goggo sai mun dawo."

Mamaki ne ya kama Sagir, ya mike yana cewa "ki zauna...."
Tace "muje kawai."

? Sai da suka kai kofa sannan ta ma Goggo salama suka fita, suna sauka ta kan beni mai kula da Goggo tana hawa.

Gaisawa kawai sukai suka sauka.

An mata gwaje gwaje sannan aka bata magunguna, akace su jira a gama test, Ameera tace "Ya Sagir ka maidamu gida, kai ka dawo ka amsa."


#Oneluv=ؕ?
[08/10, 02:16] * +234 803 222 1758, : =??? *JALILAH* =???

Written By : *AYUSHER MUHD*
Wattpad: *Ayusher Muhd*


*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*

? (_D home of expert and perfect writer's_=ء?)

*I am really Proud of you! Can't believe Kainuwa has reach more than 300k views on wattpad, Heart U* =ؕ?=ؕ?=ؕ?=ؕ?=ؕ?=ؕ?=ؕ?

*No 24*



?? Shiga d'aki yai ya tsaya yai shiru, tunani yake mai yai? Shi dai a iya saninsa baiga laifin da yai ba.
? Bandaki ya shiga yai wanka, zama yai shiru, ga wunya da ta fara cinsa, yau Ummy mantawa dashi tai? Ko laifin daya mata ne yasa tai fishi dashi?

? Kwanciya yai ya d'au jornal din da yake karantawa.
Jiyai yau karatun sam ba dadi, shi yace amai aure? Mikewa yai zaune sannan ya shafi fuskarsa, makullinsa ya d'auka da wayarsa ya fito, ba kowa a falon hakan yasa yai waje.
Yana kokarin shiga mota, su kuma suna shigowa.
Sai daya jira sukai parking sannan ya shiga mota ya tada ta.
? Sagir ya fito da sauri yanasan mai magana, kafin ya karaso Hassan yaja motarsa yai gaba.
Sagir yabi motar da kallo, a ransa yace "anya nama Jalila adalci kuwa?"
Ameera ce ta bi motar sa da kallo sannan ta kalli Jalila ta mika mata hannu, Jalila tai murmushin yake sannan ta fito.
? Ameera ta kamata suka shiga ciki.
Ummi najin motsin mota ta fito, tana kallan sanda Hassan yai waje, ga Abba tun safe yau ya tafi Abuja.
? Suna isowa falon Ummy ta rike Jalila ta shigar da ita dakin Ameera tunda a kasa yake.
Ummy ta kalli Ameera tace "Ameera dauko abinci."
Nan Ameera ta fita, Jalila ta fara kokarin mikewa tana cewa "Ina kwana?"
Ummy tai saurin riketa tace "Karki damu, ma gaisa inkin ware."
Sagir na tsaye a jikin kofa yana murmushi, yasan halin Ummy ya tabbatar Jalila bazata taba wulakanta ba indai har Ummy na nan, kaf a duniya shi agunsa bai taba ganin mace kamar Ummy ba.

? Ameera ce ta shigo da tiren abincin, Ummy tace "zubo mata dankalin kadan"
Ameera ta zuba mata ta mika ma Ummy, da kanta ta gyara mata zama sannan ta mika mata abinci, kallan mamaki Jalila take mata, bata taba tunanin zata samu kulawa haka ba, balle daga zuwanta ko sanin ta ba'ai ba.

Haka ta dinga dan ci dan samon kanta tai da kasa yima Ummy musu, sai data gama Ummy ta miko mata magani da ruwa.
Sai data sha, sannan Ummy tace karki kwanta kidan jira abincin ya tsirga miki kadan sai ki kwanta.

Jalila ta d'aga kai, sannan ta maida idanta kasa.
Ummy tai murmushi ta fita.
Ameera ta mike ta biyota.

Sagir na zaune a falon suka fito, yace "Ummy na!"
Tace " Sagir sannu da kokari."
Yai murmushi sannan yace "Ina Yaya yaje? Naga ya fita yanzu."
Yanayin fuskarta ne ya canza, tace "yaushe rabon da insan inda Hassan zaije?"
Sagir yai shiru dan ya fahimci yayi laifin tambayarta, Ameera ya kalla yace "Ashe kawarki ta koma gida?"
Ta dan turo baki tace "sai yanzu ma ka kula?"
Yace "kinsan dazu muna kan Jalila sam ban kula ba."
Ya mike yai kitchen.
Ameera ta kalli Ummy tace "Ummy nikam dazu a asibiti, na rasa wa taje dubawa."
Ummy tace wa kenan?

Ameera tace "matar yaya."
Ummy tace "ya sunanta ita matar yayan?"
Ameera ta kalleta tace "Ja....."
Kallan da Ummy ta mata ne yasa tai saurin cewa "Yaya Jalila."
Ummy tace "me ya faru?"
Sagir ne yai saurin katseta yace "to uwar gulma, ki bari ita Ummyn ta tambayeta da kanta mana."

Ameera ta turo baki, Ummy tace "Sagir ya akai?"
Hannunsa rike da plate din da ya zubo abinci ya zauna akan dinning yana cewa "Wlh nima bansan wacece a asibitin ba Ummy, sai dai yanda hankalinta ya tashi da alama mai mahimmancice a gareta....."


Ummy tace " shikenan, zan tambayeta."

Sagir shiru yai ya kasa ko kai loma d'aya bakinsa, tunawa yai sanda suna zance da Jalila a makaranta yawanci in zatai abu zai ji tace ai Goggo kaza, ai Goggo kaza.

Kallan Ummy yai da sauri yace "Ummy wannan matar data kawo Jalila itace "Mahaifiyarta?"
Ummy tace "eh mana."
Sagir yai shiru can yace "me suke ce mata?"
Ummy tai murmushi tace "ina fa na sani? Dan jarida?"
A tare sukai dariya

^********^


Jalila tayi bacci sosai dan sai azahar ta tashi, Ameera na dakin tana sa kaya sanda Jalila ta farka.
Kallan Agoggo tai sannann ta mike da kyar ta kalli Ameera tace "Dan Allah zanyi alwala."
Ameera tace "ki shiga ga toilet."

Jalila ta mike tai alwala, Tana idar da sallah Ameera tace mata ga abinci nan kici, Jalila tace "banajin yunwa.
Bata sake mata magana ba, ta karasa kwalliyarta dan fita zatai ta fito daga d'akin.

D'akin Ummy ta shiga tana zaune tana ta kiran number Abba, tun safe take ta ringing amma no answer.
Ameera ta shigo tace "Ummy dawa zan kai sakon gidan Aunty Nanan?"
Ummy tace " dama abin gara ne, gashi ba driver a gidan, ki duba ko Sagir nanan."
Har ta juya Ummy tace " yayar taki ta tashi ne?"

Tace "eh tayi sallah ma."

Ummy ta mike ta fito tare da ajiye wayar.
Sama ta hau dan taji alamar dawowar Hassan dazu, dakin ta kwankwasa.
Yana kan sallaya rike da littafin Riyadul Salihin, ajiyewa yai ya bude kofar.
Kallansa tai tace "Hassan ya jikin matar taka?"
Kallanta yai yace "Ummy ni ai banganta ba?"
Tace " baka ganta ba? Tana ina kenan?"
Yace "ina na sani ni ai tun da suka fita ban kara ganinta ba."

Tace "ko?"
Baice komai ba sai kallan mamaki da yake mata, Ummy me take mai haka? A iya saninsa batasan abinda zai bata mai rai, sannan ko magana zatamai a cikin sanyi take mai.
Kallanta yai yace "Ummy na kasa gane me ke faruwa, kince na amince da auran nan na amince ba tare da na musa ba, yanzu kuma gaba daya kin canza."

Kallansa tai, yanayin fuskarta ya canza, abinda bataso dan ta kula in tama Hassan lago lago tabbas yarinyar nan zata kuntata a gunsa.
Tace "Hassan ko kare ne aka baka shi akace ma gashi an baka shi, baka tunanin ya zama hakkinka ka kula dashi? In har kasa hannu ka amsa a iya tunani na dolene ka bashi hakkinsa, Hassan dabba ma kenan, balle dan adam, dan adam din ma mace mai rauni, yarinya karama."

? Kallanta yai baice komai ba, tace " yanzu da ace gidanku daban kenan haka zaka barta har ciwo ya mata illa?"

Hassan ya kalleta yace "ba gaku nan ba,Ummy? Na tabbatar abinda zaku mata ni bazan mata ba."
Tace "Hassan zuciyarka ma ta fara rikidewa?"

Kallanta yai sannan ya kauda kai gefe, tace " a iya sanina yarona mutum ne mai tausayi da kula da abinda yake nasa da wanda ba nashi ba, Hassan yaushe zuciyarka ta fara rikidewa zuwa rashin tausayi?"

?? Shiru yai jikinsa yai sanyi bai ce komai ba, tace " na haramta mata kwana a d'akinta, daga ranar jiya Hassan ko me zai faru in ganta a d'akin nan.

Yace "Ummy...."
Tace "zan kulle d'akinta ne ma in tafi da makullin, zan sa Ameera ta dawo da kayan sawarta nan dakin."

Ran Hassan ya baci sai dai bai iya cewa komai ba, yana ji ta juya ta sauka, da kallo ya bitaa sannan yai ajiyar zuciya, dama ba auran ba, azomai da wasu sababbin al'amura shi ya tsana, sanda sukesan yai auran ba acemai komai ba, sai yanzu da yai auran ake san a canza mai rayuwarsa, me yasa basa duba yanayin lalurarsa tana bukatar sirri da kadaicewa?


? Ameera bata samu Sagir ba, tazo ta sanar ma Ummy, ba tare da damuwa ba Ummy tace "a kai gobe, yanzu muje sama."
Tace "Sama kuma?"

Haka suka shiga d'akin Jalila tasa a kwaso kayanta, tayi mamaki sosai dataga duk an d'auke kayan lefen da suka sa mata masu tsadar ciki, sai dai bata nuna ma Ameera wani abu ba, Hassan na jin alamunsu yasan me suke shirinyi.
Fitowa yai ya sauko kasa ransa a bace zai fita.

Jalila ta fito dan neman yarinyar da batasan sunanta ba, tanaso tace mata ta nuna mata inda kayanta suke tanaso ta dauko abu (wanka take sanyi ga batasan inda inners dinta suke ba.)

? Tana fitowa ta nufo falo tana tunanin inda zata ganta, tangamemen falon ta shiga kallo, dan dazu da yake kunya take sannan ba lafiya ce da ita ba ko kai bata daga ba, haka gidan yake? Kallan gidan ta shiga yi shi kuma ya sauko daga sama, san bata kuka dashi ba, shi kuma ransa a bace yake yana san fita.

? Tana tafe shi kuma ya taho da karfinsa ya bigeta, tsoron faduwa yasa ta riko rigarsa suka fadi a tare.

? Zafin faduwar ne yasa tai dan kara kadan, dagowa yai ya kalleta, itama kallansa tai.
Idanunta ne suka fito dan ta ganeshi shine na jiya, wato shine angon nata kenan, kura mata ido yai sosai wanda yasa ta tsarguwa.

A ina ya santa? Kallanta ya sakeyi, sannan ya mike tsaye.
? Haushi ya kamata duk da batajin dadi ai yaci ace ya mata sannu dan ta tabbatar yasan ta bige sosai.
Hararsa tai wanda shi kuma daidai lokacin ya juyo da fuskarsa, hada ido sukai tana harararsa da sauri ta wayance tace "yaji ne ya shigarmin ido?" Wai ita adole bata ma kula dashi ba, magana take da kanta.

? Hassan kallanta yai sannan ya tuno harararnan an masa ita sau biyu, har ya juya sai kuma ya kara juyowa yai ya kalleta dan ya fahimceta sosai, itace takan hanyarnan da wacce ta harareshi a adaidaita.
Oh, a ransa yace mai kuka?

Jalila ma shiru tai tana tunanin faduwarnan, bashakka ta tuno, da sauri ta d'ago ta kalleshi.
Mikewa tai tsaye, tana kokarin mai magana shikuma yai waje.

Da sauri tace " ba kai bane?"
Bai tsaya ba balle tasa ran tanka mata, kara kankance ido tai tana tunani, tabbas shine, wanda ya fadi akan titin nan.
Zata kara magana taga harya fita, da kallo ta bishi sannan ta dan tabe baki tace "ba dai sanda ya kusa kadeni ya sanni ba?"

? Ganin batada amsar tambayarta yasa ta juya tana neman Ameera tare da rike bayanta, dan ta bugu sosai.

? Ummy tasa aka matsar da kayansa bangare guda, sannan aka jerama Jalila nata, hatta kan madubi sai da aka matsar da kayansa akasa nata.

Ameera ta kalleta tace "Ummy kina tunanin Yaya zai? barta kuwa?"

Ummy tai shiru, meye amfanin yi masa auran in basa tare?

Haka suka gama sannan suka sauko.

Jalila kam ganin ba alamar kowa yasa ta koma dakin ta zauna.


**********

? A can gidansu Mumy kuwa, Dady na kwance yayi shiru, Mumy ta shigo dakin, kusa dashi ta zauna ta sakalo hannu ta gefen cikinsa ta rungumeshi tace "Dadyn Yasmeen tunanin me kake?"

? Fuskarta ya shafa yace " Tunanin ki?"
Tace "ban yarda ba, tunanin Jalila kake?"

Yace "A'a why should i?"
Tace "karka boyemin komai plx, sannan kaima kaga gidan Taura ai, kasan daidai mata ne zasu samu zama a irin wannan gidan."

Yai murmushi, tace "yaushe za'a fadawa Goggonta?"

Yace "karki damu, ko ta sani yanzu ba abinda zata iyayi, macece mai hakuri, indai taga yarta cikin farinciki bazata iya cewa komai ba."

Mumy ta jinjina kai, yace "ya gun Safeena?"
Tace "suna Abujan, wai sai gobe zasuje ayi visa din."

Yace "okay."


#OneLuv=ؕ?
[08/10, 04:14] * +234 803 380 9216, : =??? *J??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????ALILAH* =???

Written By : *AYUSHER MUHD*
Wattpad: *Ayusher Muhd*


*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*

(_D home of expert and perfect writer's_=ء?)


*25*


Tana zama bata dade ba taji anyi knocking din kofar sannan taji ance "Ameera!"
Gabanta ne ya fadi jin muryar Uncle, wai nan fa gidansu ne ko? Sunanta Ameera dama?
A hankali tace "batanan."
Shiru yai shima kafin yace "Jalila dan bude."

Mikewa tai ta bude kofar ba tare da ta bari idanunsu sun hadu ba.
Sagir ya miko mata ledar dake hannunsa, kallansa tai bata amsa ba sannan batace komai ba.
Kallanta shima yake sannan yace " test din ya fito, shine sukaban magunguna, dama kinada typoid ne?"


Bata amsa mai ba ta amshi ledar ta bude, bayan magani taga yoghurt da exotic a kasa, zare ledar maganin tai sannan ta mikamai ledar kasan wanda ke dauke da yoghurt din.
Kallanta ya sake yi sannan yace "kinsan wasu basa san shan magani da ruwa shiyasa....."

Kallansa tai kamar zatai magana sai ta fasa, tace " Ameeran bansan inda tai ba."

? Juyawa tai tana neman rufe kofar, hannu yasa da sauri ya rike kofar, juyowa tai ta kalleshi idanunta sun canza suna neman yin kuka.
Yace "Jalila wacece dazu a asibiti?"
Tace " me kake so ka sani?"
Yace "Kina nufin haka zamu zauna ko magana bakyasan ta hadamu?"
Kallansa tai zuciyarta na kuna, sannan ta juya da sauri ta banko kofar.
Hannu tasa ta rufe fuskarta saboda bakin ciki, wasu hawaye ne suka gangaro mata, ba santa yake ba, ta tabbatar yanzu kila kawai tausayin halin da ya ganta yakeyi.

? Sagir tsayawa yai ajikin kofar tare da kurama kofar ido kamar tana gun, sannan ya juya jiki a sanyaye.
Yana neman fita yaji Ameera nacewa "Ya Sagir!"

Juyowa yai ya kalleta, yana tsaye harta karasa gangarowa daga saman benan, ta matso gunsa tace "ina zaka?"
Leda ya mika mata yace "Gashi kiba matar Yaya."
Amsa tai tana cewa "menene ya Sagir? Sam ka canza? gaba daya yanzu bakasan magana sosai."
Murmushi yai na dole yace "Ummy fa?"
Ta nuna sama da hannu tace "tana sama" sannan ta matso kusa dashi sosai alamar rada tace "Ummy fa ta dage sai yaya ya amince da matarsa."

Sagir ya kalleta yace "bangane ba...."
Tace "tana sama tana hada musu daki daya."

Wani abu ne yaji ya harba kirjinsa me kake tunani Sagir? Abinda wata zuciyar ta tambayeshi kenan?.
kallanta yai yace "haba."
Dakyar yai maganar, tace "Ai Ummy ta dage wannan karan."
Harararta har sannan ya ture kanta yace "yaushe kika zama mara kunya? Wato harkin fassara zamansu a daki daya kena?"

Tace " ko yaro dan shekara sha biyar ai yasan me ake nufi a wannan lokacin."
Buge kafadarta yazoyi ta zille da sauri yace "Ameera? Kece kuwa?"

Dariya tasa tace "ni ba ruwana Ya Sagir."

Da kallo ya bita yana murmushi harta shige daki, tana shiga yanayin fuskarsa ya canza, daki daya? Wata zuciyarce ta kara cewa me kake tunani ne wai? Daga lokacin da aka daura aure ai kaima kasan abinda ya kamata.
Juyawa yai jiki a sanyaye

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login