Showing 42001 words to 45000 words out of 149705 words

Chapter 15 - Jalilah Book One Complete Hausa.doc

Ayusher   

28 Oct 2025

642

ya fita.


Tana zaune tana kuka Ameera ta turo kofar, da sauri ta goge hawayenta, Ameera ta kalleta tace "jikin ne?"
Kai ta daga alamar a'a sannan tace "Sunanki Ameera ko?"
Tace eh, Jalila tace "ni sunana Jalila."
Ameera tace "na sani."
Jalila tai murmushi tace "Oh, yahkuri."
Ameera ta kalleta tace "Ummy ce ta fadamin, sannan na gani a katin daurin aure."

Jalila ta jinjina kai, Ameera ta mika mata ledar tace "gashi inji Ya Sagir, ah bakisanshi ba ko?"
Jalila ta kalleta batace komai ba, Ameera tace "shine kanin Yaya, daga shi sai ni, mu uku ne."
Jalila tace "Yaya?"

Ameera tace "Ya Hassan fa nake nufi mijinki."

Jalila batasan sanda tai wata dariya ba wace ni kaina bansan irinta ba, miji? Mijin da sai yanzu ma tasan sunansa?

? Kallanta tai a ranta tace Husainin fa? Tace Hassan sannan tace Sagir.
Kamar Ameera tasan me take tunani tace "ya rasu, dan uwan nasa."
Jalila ta kalleta tace "Ayya Allah ya jikansa."
Ameera ta ajiye ledar tana cewa Ameen.

Jalila ta dau maganin tasha.
? Jalila can tace "wanka nakesan yi kayana fa dan Allah?"

Ameera tace "muje sama."
Jalila ta mike ba tare da ta musa ba, Ummy na saukowa suna fitowa, Ummy ta kallesu murmushi tai sannan tace "Jalila kin mike?"
Kai ta daga tare da sunkuyawa, tsugunawa sukaga tayi tace "Ina wuni."

Ummy tasa hannu ta dagata sannan tace "ke da bakida lafiya?"

Jalila kanta na kasa, Ummy tai murmushi sannan ta kamo hannunta, maimakon su hau sama sai ta riketa zuwa falo.

Ameera ta kalla tace "Ameera asa mana abincin dare."
Ameera tace "Ummy yau ma nice?"
Ummy tace "ai na fada miki dama, daga kin shiga aji shida shikenan girki ya kamaki, yanzu kuwa kunyi hutun canjin aji kinga kuwa a matsayin yar aji 6 kike."

Ameera ta shagwabe fuska ta nufi kitchen ranta ba dadi, ita kam tana ganin ya kamata a samarmusu mai aikin yin abinci amma taki, mai musu aiki ma suna gama gyara gidan suke tafiya sai kuma gobe.

? Ummy ta maido da hankalinta kan Jalila ta zauna sannan ta zaunar fa ita a gefen ta.
Jalila ta zauna a darare, Ummy ta riko hannunta tace "Jalila!"
Jalila ta kalleta kadan sannan ta maida kanta kasa tana kallan yanda Ummy take rike da hannunta, Ummy tace " ya jikin naki?"
Jalila tace Da sauki.
Ummy tai shiru kafin tace "da rokonki nake san yi."
Jalila ta kalleta da sauri tana san jin menene, sai dai bazata iya dadewa tana kallanta ba, da sauri ta maida idanunta kasa.

Ummy tace "rokonki zanyi akan ki saki jikinki da mu, ki maida gidan nan kamar gidan ku koma sama da gidanku, nasan zama da iyayen miji ba abune dayake da dadi ba,? abu ne mai wahala tun balle ga yarinya, sai dai mu lalurace tasa muke sanki anan gidan, sannan bawai dan mu cutar dake bane sai dan muna ganin in kina kusa damu hankalinki da namu sai yafi kwanciya."

Lalura? Abinda yazo mata a ranta kenan sai dai batace komai ba har Ummy tace "Jalila mun miki laifi wanda nikaina nasan bamu kyauta miki ba."
Jalila ta kalleta tace "Laifin me?"
Ummy ta saki hannunta sannan jiki a sanyaye tace "mun miki laifi gun b'oyemiki larurar Hassan."

? Kallanta tai sannan ta tuno sanda ya fadi akan titin nan, aljanu? Hauka? Abinda ya fado mata arai kenan, Ummy tace "Hassan nada larura wanda mu kanmu iyayensa bamu sani ba, haka kawai tundaga mutuwar dan uwansa da dan kanin mijina Hassan ya koma haka, duk yanda mukaso musan matsalarsa mun kasa, munje asibitoci kala kala sai dai maganar daya ce, ba abinda ke damun kwakwalwarsa sai dai bamu san meke damunsa ba."

Ummy ta juyo tare da goge kwallarta tace "Jalila ki yafe mana wannan laifin da muka aikata."

? Ganin Matar da ta sani a rana d'aya tana share kwalla sai taji gaba daya hankalinta ya tashi, batasan sanda tace "Bakomai na yafe muku."

Ummy ta kalleta cikin jin dade sannan ta kara riko hannunta tace " jikina yana bani ke alhere ce a gareshi da mu kanmu, daga sanda naganki hankalina ya kwanta dake, Jalila ki daukeni a matsayin mahaifiyarki, ni kuma zan yi miki duk wani abu da uwa takema danta."

Jalila tai murmushin jin dadi, dan haka kawai taji tanasan matar, dazu kukanta kadai yasa hankalinta tashi.

Ummy ta kalleta tace "wa aka kwantar a asibiti?"

Jalila ta kalleta idanunta suka ciciko, a hankali hawaye ya fara zubo mata.
Ummy hankalinta ya tashi tace "ya isa haka nan Jalila, bazan kara tambayarki ba harsai sanda hankalinki ya kwanta da ki sanarmin."

Jalila share hawaye kawai take, Ummy ta mike tace "tashi kije dakin nasan abu zakiyi na tsayar dake."
Jalila ta dago sannan ta mike, sama ta fara hawa, Ummy taji tace "dakin kusa da wanda aka kaiki jiya zaki shiga.
Jalila tace to, nan ta tura kofar dakin, sanyin Ac dake kadawa a dakin da wani sansanyan turare ne suka bugeta, idanu ta lumshe a hankali sannan ta kalli dakin, yanayin kan madubin kadai yasa tasan dakin hade yake da namiji.
Da sauri ta fito ta nufi dakin data shiga jiya, jin dakin tai a kulle, komawa tai dakin ta bude wardrobe gefe daya kayanta ne kaf, dayan kuma na namiji.

Daki daya zasu zauna kenan?

? Inners dinta ta ciro sannan ta shiga wanka, kamar ba dakin namiji ba dan komai nashi a tsars suke, haka ta fito ta saka wata doguwar riga sannan ta kwanta agefen gadon, tana tunanin rayuwa, tabbas itakam zata fadama Ummy matsalar Goggo dan bazata iya kwana biyu ba bata ganta ba.
Ta tabbatar Ummy zata fahimceta.


? Batasan bacci yayi gaba da ita ba, dan dama in tana zazzabi ta dinga bacci kenan, tsabar bacci ya mata dadi har da kara kwanciya, sanyin Ac din yasa ta jawo bargo.
Bacci take hankalinta a kwance.


? Kofar dakin ya turo, gaba daya shi gidan ma baya san zama, tunda ya fita yana cikin mota a zaune.
Sai yanzu daya gangaro gida, ganin magrib tayi, ya tabbatar Ummy yanzu zata shiga nemansa.


Cak ya tsaya a kofar dakin yana kallan ikon Allah, tunda yake yau ne rana ta farko da wani ya taba bajemai akan gado haka, harda jan bargo?

Ransa ne ya turnuko dan shi sam bayasan yaga wani a dakinsa, kusa da ita ya matso ya sa hannu ya fizgi bargon da karfi.

? Jan bargon da yai yasa ya hado da kasan doguwar rigarta yadan kwaye ta.
Da sauri ta bude idanu, kallansa tai a zabure, shima idanunsa ne suka kai kasanta daya kwaye, da sauri ya dauke kansa, ita kuma ta mike zaune da sauri tana gyara rigarta tace "Malam me kenan?"

Kallanta yai yace "Malam? Malam me kenan?"
Bakinta na rawa tace " Umm."
Ya hade rai yace "will you get up?"
Kallansa tai cikin rashin fahimta, yace " bakyajin yaren?"
Nan ma tai shiru, yace "banasan magana please tashimin daga kan gado."

Jalila ta kalleshi tace " dan zaka ce in tashi sai ka min haka?"

Wani kallo ya buga mata wanda batasan sanda ta mike ba, yace "a haka kika gadon?"

A ranta tace "ahh yau ga wani irin mutum."

Kallanta yai sannan ya kalli gadan, Jalila ta fara gyara gadan da karfi kana gani kasan na mugunta takeyi, tana yi tana dan murguda baki.
Kallanta yai a ransa yace wannan kana gani kasan batada kunya wannan bakin sai ba fasashi wata rana.

Jalila kuwa tana gyara wa tana cewa yo matsala ma ai basai an tambaya ba, mutum ba mutunci ai babbar matsalace.


#OneLuv=ؕ?


=??? *JALILAH* =???

Written By : *AYUSHER MUHD*
Wattpad: *Ayusher Muhd*


*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*

(_D home of expert and perfect writer's_=ء?)


*26*



Toilet ya shiga ya d'auro alwala, yana fitowa ya kalleta, tana tsaye tsuru dan itama jiransa take ya fito, ga fitsari ya matseta.
Tana gani ya fito ta shiga ciki, kallan kofar data rufo yai ransa ya kara baci dan bakin cikinsa ya ganta a dakin nan.
Tada sallah yai, bayan ya idar ya zauna ya fara addu'oinsa, itakam daga gefe ta dan rakube tai sallah, tana idarsa ta zauna agun tana yima Goggonta addu'a.

Ameera ce ta buga musu kofa tana cewa "Yaya Jalila ki fito kici abinci"

Juyowa yai ya kalleta ransa a bace, mikewa tai da sauri zata bude kofar.
Batasan ya mike ba sai gani tai ya rigata sa hannu ajikin kofar.
Kallansa tai yanda taga idanunsa sunyi yasa taji tsoro.
Da karfi ya bude kofar sannan ya kalli Ameera.

A tsorace Ameera tace "Yaya kana nan?"

Kallanta ya sakeyi,ba sai ya mata magana ba tasan me yake nufi.
Da sauri tace "Yahkuri yaya bansan kana nan ba."

Jalila ya kalla, itama kallansa tai sannan ta kalli Ameera, bata fahimceshi ba sai cewa tai "me zanyi?"

Hannu yasa ya turata waje sannan ya rufe kofarsa, Ameera ta kalla sannan ta kalli kofar tace "menai?"
Ameera tasa hannu ta jawota tana mata alamar tai shiru.

Suna sauka kan steps din tace "bayasan magana da hayaniya."
Jalila ta kalleta batace komai ba, haka suka sauka kasa.

Ummy nakan dinning tana rike da waya, kara neman number Abba takeyi amma shiru sai taita ringing harta katse ba'a dauka ba.

Sagir ne ya ajiye kular daya dauko daga kitchen yana cewa "Ummy haryanzu Abban bai dauka ba?"
Ta kalleshi tace "haryanzu, baka tunanin ko wani abun ya faru?"
Zama yai a kusa da ita yace "bakomai insha Allahu, maybe ko aikin dayaje yi ne ya rikeshi."

Su Ameera ne suka sauko, Ummy ta kalli Jalila tace "Jalila ban yarda da kici abinci ke kadai ba dan ba lalai kice dayawa ba."
Jalila tai murmushi sannan ta zauna kusa da inda Ameera ta zauna.
Bata kula da Sagir ne a saitinta ba, sai da Ummy ta mika mata serving spoon.
Jalila ta amsa sannan ta kalli Sagir, idanunsu ne suka hadu da sauri ta maida kanta kasa, tana kallan plate din, ta ina zata ci abinci a nan?"

Ta dan zuba abincin kadan, Ummy ta kalleta tace "Jalila wannan dan abincin fa?"
Jalila ta kalleta tace "Ummy wlh haka cin abinci na yake."
Ameera tai dariya tace "irin cin abincin Yaya kenan, hmm kunyi anko."
Idanunta ta dago kadan ta kalli Sagir wanda yake ta juya abincin.
Shiru ne ya biyo bayan falon sai dan karar cokula da suke tashi, Ummy ta rasa me yasa gabanta ke ta faduwa.

Mikewa tai dan abincin da kyar take danci, ta kalli Ameera tace "ki dauko mata magungunanta tasha." Ta karasa maganar tana wucewa d'aki.
Ameera ta mike tai daki, ya rage daga shi sai ita agun, Sagir ya kalleta yace "Ya jikin naki?"
Bata kalleshi ba tace "na warke."

Shiru suka karayi yace "Jalilah....."
Ajiye cokalin tai da sauri sannan ta mike, dan batasan jin kalma daya daga gareshi, ina zata?
Nufar dakin Ameera kawai tai, Ameera na fitowa ta kalleta tace "ina zaki?"

Tace " hmm bandaki zan shiga."
Ameera ta mika mata maganin, amsa tai ta shiga ciki.
Tunda ta mike yake kallanta harta shiga, idanunsa ya rufe yana neman tsari daga sharrin zuciya, shikam ya san ya hakura sai dai yana san ya warware misunderstanding dake tsakaninsu.

*********

Acan Abuja kuwa Abba ne ya kalli abokin nasa yace "wai kai da mukazo yin signing contract me ya kawomu nan?"
Ya fada yana kallan wani gidan da abokin nasa yai parking.
Abokin nasa mai suna Hafiz ya kalleshi yace " abu zan amsa gun wani, yanzun nan zan fito.
Fitowa yai daga motar yabar Taura a ciki, tsaki taura yai shi ya kosa su gama ya koma masaukinsa dan ya manta da wayarsa garin sauri.

? Sam bai kula ba sai jiyai ana kwankwasa glass din motarsa.
Zuge glass din yai tare da kallan windown, wani irin kamshi ne ya shiga ratsa cikin motar, kallanta yai yarinyace wacce batafi shekara 28 ba, fara ce wanda har farin nata ma yasa zakasan ba cikakiyar bahaushiya bace, kana ganinta zaka san irin matan nan ne shuwa.

Tasha kwalliya irin na zamani, kamshin da takeyi kuwa ba'a magana.
Ya rasa dalilin dayasa ya kasa dauke idanunsa daga kanta.
Murmushi tamai sannan tace "Yaya yace ka shigo kaci abinci."
Yace "Yaya?"
Tace "Eh ai mijin yayatane."

? Yace "oh gidanshi ne kenan?"
Tace "eh."
Gani yai tasa hannu ta bude lock din cikin motar sannan ta bude kofar.
Kallanta yai, kayan da ke jikinta irin material ne mai kyalkyali, mace ce mai suna mace dan shape din ta ma abin kallo ne.
Kai ya girgiza da sauri dan shikam mace baiga kyan da zaisa ta rinjaye shi ba.
Kauda kansa yai daga kanta, matsowa tai saitin kunnensa tace "Please."
Baisan sanda ya mike ba yace "muje."
Gaba tai tana wani murmushi, dan dama wannan shirin sunfi wata biyar sunayinshi, tundaga sanda taganshi a Abuja yazo shida matarsa wani taro, kayan jikin matar kadai ta kalla tasan kudi ya zauna musu, data tambayi mijin yayarta shine ta karajin irin kudin da yake dashi.
Tun daga lokacin suka fara shirin jawoshi inda suke.

? Haryasa kafa zai shiga sai ya tsaya, juyowa yai ya kalleta yace "kicemai yai hakuri inada abinyi."
Ya fada tare da juyowa tana mai magana bai tanka mata ba.
Motarsa ya shiga ya jata da sauri.

? Ita kuwa Zaliha tana shiga cikin gida ta hade fuska, yayarta ta kalleta tace "ya ya?"
Kai ta girgiza mata kawai sannan ta wuce daki cikin takaici.
Yayarta ce ta kalli mijinta tace "Hafiz ya haka?"
Yace " Taura namiji ne da bai kallan matan waje kuna tunanin daga haduwa daya zai amince?"
Harararsa tai sannan tai gun kanwarta.


***********

? Abba na koma wa dakinsa ya dau wayarsa, kiran Ummy ya sau goma, sannan yaga kiran Sagir sau biya, sai sauran wanda abune na aikinsa.
Yana shirin kiran Ummy wayar Hafiz ta shigo, dagawa yai cikin takaici yace "Hafiz bakada hankali ne?"
Hafiz yace "kayi hakuri dan Allah wlh dana shigo ciki ne matata ta dage akan sai na kiraka kaci abinci shiyasa nace Zaliha ta kiraka."
Yace "meyasa to baka fadamin gidanka bane?"
Yace "banasan ne kaji ba dadi, haba Taura dan Allah kayi hakuri."

Kashe wayar yai sannan yai cilli da ita kan gado, ya rasa me yasa yarinyar ta tsayamai a ransa......


***********

? A can gidansu Hassan Kuwa jalila tana zaune a dakinsu Ameera, har wajen karfe 10, Ameera ta kalleta tace "ki tashi kije ki kwanta kafin Ummy tai magana."
Jalila tai ajiyar zuciya sannan tace "bazan iya kwana anan ba ko?"
Ameera da sauri tace "a ina? Ba ruwana wlh."
Jalila ta kara yin ajiyar zuciya sannan ta mike, ta fito.

Haka ta haura sama jiki a sanyaye, hannu tasa a hankali ta murda kofar dakin, yana kwance akan gado yana karatu.
Kamar munafuka haka ta shiga cikin dakin, ko kallanta baiyi ba ya cigaba da karatunsa.

? Jalila tana tsaye har kusan minti ashirin, jitai kafafunta sun gaji nan ta matso kusa da gadon kadan, ta karasa kan kujerar dake dakin ta zauna tana dan matsar da littatafan dake jere agun.
Jitai ance "karki kuskura ki hargitsamin abu, komai da kika gani agun a jere yake."

Baki tadan tabe sannan ta daina taba litattafan, dama haushi yakeji dalilinta duk an canzamai tsarin dakinsa.

Shiru ne ya kara ratsa dakin sai sanyin Ac dake kara sanyaya dakin.
Bacci ne ya fara kamata dan har 11 ta wuce, tana zaune tana tunanin Goggonta.

Ganin bashida niyyar fadamata inda zata kwanta yasa ta mike ta dau pillow din dake gefensa sannan tazo tana san daukan bargon dake kan gadon.
Kafafunsa ne akai ta kalleshi tace "zan dan dauka."

Kallanta yai yace "banaji naki ne."
Tace "a ina zan kwanta?"
Alama ya mata da kasa da hannunsa ba tare da ya dauke kafarsa ba.

Jalila haushi ya kamata, harararsa tai cikin takaici, sannan ta sa pillow ta kwanta a kasa, ai bayau ta saba kwanan kasa ba, dama saboda sanyi takesan luluba.
Shikuwa bai kalleta ba sai dai ya tabbatar ta harareshi dan ya kula idanunta sun kware da harara sannan bakinta ya kware da murguda a bayan fage.

Kwanciya tai ta lulube kafarta da zani, bacci ne yai gaba da ita.......

Kallanta yai sannan shima ya juya ya kwanta, abinda zai baka haushi bafa luluba zaiyi da bargon ba haka kawai.........

Wajen asuba ya farka, yai hamdaka da samun bacci mai kyau dayai, dan dama ba kullum abin tashi ba.
Dome light din dakin ya kunna sannan ya mike.

Alwala yai sannan ya dauko sallaya zai shimfida, kallan Jalila yai tana kwance a inda yake shimfida sallayarsa, bacci take sosai kafa yasa ya zunguri kafarta.

Kara gyara kwanciya tai, ya kara sa kafa ya dan kara zungurar kafar tata, a hankali ta bude idanunta.
Ganin namiji tai a kanta da doguwar riga fara, tsorata tai, da sauri tai baya tare da yin ihu, tace wayyo Allah......
Da sauri ya rufota ya rufe mata baki, yace meye hakan?
Sai alokacin ta tuna ashe fa wai a wani gidan take, sannan daki daya da namiji.
Shiru tai sannan ta kalleshi, shima kallanta yai sannan ya mike yace " bakiji kiran sallah ba?"

Tai shiru, dan batasan me zatace ba.
Mikewa tai ta nufi ban toilet.

********

Inna ce ta kalli Dady tace "bazaka iya ba?"
Yace "ba wai bazan iya bane sai dai banga dalilin dazaisa a dauketa daga asibitin da take ba zuwa wani ba."

Ranta a bace tace "kayi abinda na saka kawai, ko kana tunanin zan cuceta ne?"
Kallanta yai yace "ba haka nake nufi ba."
Tace " kamaida ita Premier m, sannan kasa a gyara mata bangarenta, asa mata duk wani abu da ya kamata."

Mamaki ya kamashi, a canza mata asibiti sannan a gyara mata bangarenta? Ya tabbatar wani abun take shiryawa na cigabanta ko na cigaban yarta.
Bai musa ba yace to sannan ya mike ya fita.

Shiru tai tana tunani........

#OneLuv=ؕ?

**********

=??? *JALILAH* =???

Written By : *AYUSHER MUHD*
Wattpad: *Ayusher Muhd*


*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*

(_D home of expert and perfect writer's_=ء?)


*27*


Dady na fita daga dakin ta dau waya ta kira Mumy.
Mumy na shigowa ta kalleta tace  ki shirya muje ganin daki.

Mumy tace

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login