Showing 132001 words to 135000 words out of 149705 words

Chapter 45 - Jalilah Book One Complete Hausa.doc

Ayusher   

28 Oct 2025

629

da za a biyamu kudin mu.


Nan fa guri ya kachame da kananan maganganu.


Hassan kam abin ya birgeshi wani irin dadi yakeji a ransa, lalai ilimi rahama ne.

Hannu ya daga ya yima Sageer jinjina.

Dady kam ji yai gaba daya wata muguwar zufa na ketomai ta ko ina.

Wani daga cikinsu ne yace  ta ina zamu yarda da abinda ke faruwa?

Sageer yace  da farko ga signing din Chairwoman din nan sannan ga yartanan zatai duba, dan tana nan akai komai, sannan zan miko muku ku gani kuma.

Mumy wacce gaba daya dana sani ya gama kamata, jikinta duk ya gama yin sanyi, meke faruwa? Itakam ai ba haka sukai ba, ta dauka ko ita zasu barikon kwarya kafin ta samu Dady ya dawo hankalinsa, ya kamar take ganin anyi amfani dasu?


Haka tace ai komai daya fada daidai ne sannan aka mikama kowa ma ya gani, nan fa ba yanda suka iya aka ba Sageer kujerar shigabanci ya zauna akai.


Dady kam gaba daya ya koma mutum mara amfani dan jiyai ma dakin kamar ba kowa a ciki ba kuma abinda ake cewa a ciki.

Sai zafi da kirjinsa yakeyi......


Mumy kallansa kawai takeyi......


Sageer ya kalli Hassan sukai murmushi, Sageer ne ya tuno kalaman Abba dayace akwai tsuhuwar contract din da suka farayi dama time din da akasa kenan, to shi bai yaga ta ba shine yasa Sageer ya nemo, Abba yace da Jalila tayi nisa a karatu da ita zai sa aba wannan matsayin ko dan mahaifinta ya hankalta.



#OneLuv=ؕ?
[12/30/2018, 10:08 PM] El-hajj: =??? *JALILAH* =???


Written By : *AYUSHER MUHD*
Wattpad: *Ayusher Muhd*


*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*


*72*


? Gaba daya haka kowa ya fito daga dakin taron zuciyarsa a cunkushe da wannan al'amari.
Ya rage daga Hassan, Sageer, Mumy, Dady sai Sani ne kadai a ciki.

? Mumy ta kalli Hassan tace "amma nikam ai ba haka mukai daku ba."

Hassan ya mata wani kallo yace "ke wacece da zaki tsara mana abinda kikeso muyi? Na dauka farincikinki kawai a kwace company din ne daga gun wannan, ba kuma naji kinada wani iko na samu ko hanamu."


Dady zuciyarsa takai makura dan dama daurewa kawai yakeyi, jin kalaman Hassann ya kara tunzuro shi, matsowa kawai yai naga ya daga hannu kamar zai gaurawa Mumy mari, sai kuma ya sauke hannunsa yana hucci, kamar wani kumurci sannan ya bugawa Hassan wani banzan kallo.

Hassan kam ganin yanda yake kallansa yake muzurai yasa shi yin wata dariya tare da cewa "bani na kar zomon ba, sannan ni na taba ganin wannan karfin halin?"

Cikin tsananin fada yace "karfin hali? Karfin hali fa kace, ka san wace irin rayuwa nai har na kawo wannan ranar?" Yadanyi kara cikin karaji yace "who are u? Da har ka isa ka wargazamin abinda nake shiri shekara da shekaru?"

Baa mumy taja saboda tsoron da Dady yake bata, Hassan ya hade fuska yace "rayuwar dakai? Wani ne ya saka? Kai fa ka sa kanka, sannan kai tambayar who am i? Nine wanda har karshen rayuwata indai har inada dama bazan taba barinka ka saci abinda ba naka ba."

? "Sata? Sata nai? Uban waye yacce haka ake sata?"

Yace "To sanar dani in ba sata ba menene? Tsabar san zuciya ka wulakanta iyayenka, matarka, yarka, sannan yanzu kake neman ka sace abinda dayan matar da 'ya'yanka ke da shi."

Cikin tsananin zafin rai ya matso ya sa hannu da karfi ya hankade Hassan, baya yai saura kadan ya fadi ya rike teburin dake gun.

Dady yayo kanshi cikin fada yace "uban waye ya baka damar shiga rayuwata? Uban waye?"

Yanda yake yi ne yasa Hassan ya kura mai ido yana kallan ikon Allah, gaba daya ma mutanen dake gun ma kowa kallan mamaki yake mai, Mumy kam hawaye ne kawai ke zubo mata, cikin masifa yake kallan Hassan yace "Uban waye nace? Duk duniya duk wanda ya kuskura yace zai hanani abinda nasa gaba wallahi zan iya mai abinda ni kaina ban san zan iya ba."

Mamaki ne ya kara kama Hassan yace "ya zamuyi?"

"Dame?" Dady ya fada a harzuke, Hassan yace "dan banaji zan dakata daga nan, har kasa na fara zakuwa naga mai zaka iya aikatawa."

? Cikin tsananin zafin rai da bakin ciki, Dady yakai hannu ya naushi Hassan, wanda sai da ya fasa mai gefen bakinsa, ya daga hannu zai kara Sageer ya rikeshi, Dady ya juyo cikin tsananin masifa yace "menene hakan?"

Hassan ya mike ya goge bakinsa, yace "ya zamuyi yanzu kuma?"

Dady ya mai wani kallo, Hassan yace "Sageer baka tunanin ya kamata a koreshi daga aiki?"

Sageer yace "ai ba sai ka bata bakinka ba Yaya, Zakai resigning ne ka fita da martabar ka ko kuma kafisan mu koreka?"

? Dady yace "mene?"

Sageer yace "ba dai kana tunanin duk wannan bugun dakai a banza kayi shi ba? Sai dai fa kayi hakuri dan duk na dau video ina jiran naji uzurinka dayasa ka naushi investors din ku."

? Dady ya zaro ido ya kalli Hassan gani yai Hassan ya mai wani murmushi sannan ya matso ya danyi ajiyar zuciya yace "in zaka saida shares dinka na company in gari yama zafi ka kawo Jalila zata siya."


? Hassan yai gaba ya barshi a gun, cikin takaicin hali irin nasa, Sageer yace "sai naga resignation letter gobe a sabon office dina." Ya juya ya fita.

Dady ya saki wani irin ihu wanda ya kara razana Mumy.

Sani ma juyawa yai ya fita dan shikam hankalinsa ya kasa jawomai cikaken abinda ke faruwa.

? Dady ya matso kusa da Mumy ya daga hannu ya sharara mata mari, ya kara daga hannu ya sake mata wani sannan ya nunata da yatsa yace "ke har kin isa ki sa wannan dan iskan yaran yacimin mutunci?"

? Kallansa tai tana hawaye tace "Dear."e

Da yatsa ya kara nunata yace "don't you dare call my name like that."
Ya matso kusa da ita sosai yace "ni kika ci amana saboda bakyasan na zama wani abun ko? Na miki saki daya."

Kawai taga ya juya ya fita, gaba daya jitai kanta na wani irin juyawa dan ta kasa tantance takamaimai meke faruwa.
Batasan yawan mintinan da ta kwashe a tsaye ba kamar mara numfashi.
Yanda wayarta ke ta zuba kara ne yasa ta farga, daga wayar tai ba tare data dubama wanda ya kira ta ba.
"Mumy ki zo gida yanzu." Muryar Sultan taji a rikice yana fadar haka.

Da sauri ta fito ta fada mota sukai gida, wasu gardawa ta gani a cikin harabar gidan, gefe kuma Sultan ne a tsaye.

Tana zuwa ta karasa gunsu tace "lafiya?"

Turo mu akai akan ku tattara kayanku ku bar gidan nan.

Cikin mamaki tace "mu bar gidan kamar ya kenan?"

? Yace "ko ku bar gidan gaba daya ko kuma yace ku koma boys quaters."

? Yanzu kam ta gane wanene ya turo su, waya ta daga ta kirashi.

Kamar bazai daga ba sai taji ya daga, cikin mamaki tace "Abakar me kake nufi akan munar gidan da mahaifina ya gina?"

Yace "kema kiji in aka kwacema abinda yake naka ya kakeji."

Tace "ni menene naka dana kwata?"

? Tambaya kike?
Tace "badai company dinmu kakeso kace ba?"

Yace "ko ma menene magana ta kare, ke kika bani gidan nan da kanki sai kisan inda dare ya miki."

Tace "zan san inda dare yamin amma 'ya'yanka fa?"

"'Ya'ya? Ki tabbatar kin kwashesu."

? Hawayenta dake zubowa ne ya karo, tace "nikam Abakar tunda nake dakai ka taba min so na tsakani da Allah kuwa?"

? "So? Wasan yara kika koma yi kuma?"

Mumy ta toshe bakinta saboda kuka na neman cin karfinta, kawai kashe wayar tai ta kalli Sultan tace "wuce kaje gidan Kawu, ni zan koma asibiti."

Yace "wai mumy meke faruwa ne?"

Tace "jeka in na dawo mayi magana."

Shiru yai kamar ya sake magana sai kuma yace "to."


Tana ganin ya fita kawai ta tsuguna tasa kuka, ba kowa a wajen sai ita dan mutanen ma sun tafi, itakam me tayi? Laifin me tayi da rana daya rayuwa ta juya mata haka? Hakkin bayin Allah da kukaitaci.
Kuka ta sake sawa, ta dade tana kuka kafin ta mike ta tafi asibiti.


? Safeena na ganinta ta taso tace "Mumy menene?"

Mumy hawaye ne yazubo mata tace "Safeena ya zamuyi?"

Hankalin Safeena ne ya tashi tace "menene?"

? Nan mumy ta kwashe komai ta fada mata tana kuka, sam basu san kafin su fara labarin Inna ta farfado ba.


? Kuka sosai sukeyi itada Safeena, Safeena tana kuka tana cewa "yanzu Mumy haka Dady ya mana? Kema Mumy kamar baki da wayau kina ganin yanda ya banzatar da abinda ya haifa duk rashin mutuncin mutun ko duk mutuncinsa indai har bai daraja abinda Allah ya bashi ba banaji zuciyarshi a tsarkake take, kina ganin duk abinda za'ama Jalila bai taba sa baki ba, bai kuma taba nuna damuwa ba, tunda kikaga haka ai kema kinsan Dady ba mutumin kwarai bane."

Mumy tana kuka tace "duk laifinane Safeena, Inna tasha nunamin gaskiya amma banaji, yanzu gashinan ai."

Yanda Inna ke yi ne yasa suka juya inda take da sauri, hankalin Mumy ya tashi tace "Safeena kira likita."

Da gudu ta fita, Mumy ta kamo hannunta kawai ta sa kuka.

? Inna ta fizge abin hancinta cikin wani irin murya tace "Fatima!"

Mumy ta dago da sauri tana kuka, Inna tace "ki daina kuka, ni nasan tawa tazo karshe, ke nakeji Fatima bansan wace rayuwa zakiyi ba."

Mumy tana kuka tana girgiza kai tana cewa "Inna ki daina fadar haka."

Inna ta girgiza kai cikin tsananin ban tausayi tace " ki duba kasan katifa ta akwai key na safe dina akwai takardun gida dana siya kwanaki can da suka wuce, kisa Sani ya kaiku gidan.

Fatima kiyi hakuri duk nice na cuceki, duk nice na dauraki akan rayuwar da kikeyi, san kaina da sanki yasa bana tunanin komai, Fatima bansan ya zakuyi ba, shares dina basuda yawa sai dai nasan zasu rage muku na cin abinci.

Yanda numfashinta ke kara sama ne yasa hankalin Mumy ya kara tashi, Inna tace "karkima Abakar magana, kar kuma ki nemi kwatar gidan, ki barshi rayuwa ce,? gashinan nima na gani dayawa sun gani shima kuma zai gani, sai dai ki taimakeni da abu daya.

Mumy ta kara runtse ido hawaye na kara zubo mata "Jalila! Da Mamanta!"

? Idanunta ne suka shiga lumshewa tace "Fatima ki nemarmin ????? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ?  yafiyar........."

? Yanda ta kara birkicewa ne abu na ta zubowa daga bakinta ne yasa ta kasa magana, Dr ne ta shigo da sauri ta matso kusa da Inna.

?? Kafin ta yi wani abu har rai yayi halinsa.
Wani irin kuka Mumy ta saka, Safeena ma ta sa kuka abin tausayi.


***********


? Abubakar kam yana zaune a dakin hotel din daya kama, idanunsa sunyi jaa in ya tuna abinda aka mai sai yajii zuciyarsa na kara tafasa, Fatima? Sai kaga ya naushi gefen da yake zaune, can ma sai gani nai ya mike a zuciye ya nude window kawai yana kallan waje.

? Bai taba tunanin wani abu zai kawo mai cikas ba a wannan lokacin, ihu ya saka tare da cizar lebe.


************

Goggo kam hankalinta ya kwanta dan yanzu kam taje taga yan uwanta data dade tana kewa, sun dan dade suna waya da yayanta wanda ta amshi numbersa sukai ta gaisawa da yan uwa suka mata ban gajiya sannan ta kashe, wai yanzu itace yan uwanta ke nuna mata kauna haka? Lalai duniya juye juye.


***********


? Suna shiga mota Sageer yace "Yaya wannan mutumin kansa daya kuwa?"

? Hassan yace "kansa daya kawai tsabar greediness ne ke damunsa."

? Sageer yai tsaki yace "ji fa abinda ya maka?"

Murmushi yai yace "kar ka damu ba komai, sannan dan Allah mu bar abin nan mu biyu."

? Sageer yai dan tsaki sannan ya cigaba da tukinsa.

Suna isa gida ya kalleshi ya mai alamar zip da bakinsa.

Sageer ya bishi da kallo, shikam da sauri ya shiga ciki, Sageer kam juya kan mota yai ya fita dan dama akwai abinda zaiyi.

Hassan na shiga ya wuce kitchen da sauri, ba kowa a ciki, da alama harta kammala yanda yaga har kitchen din ta gama gyarawa, juyowa yai ya wuce sama.

Kallan kanta tai a madubi tace "kai inaa.... bazan iya sa kayan nan da Ameera ta ban ba."

Rigace iya gwiwa, ba dogon wando, tace dama taban wando ne kila dana saka.

Ta juya jikin wardrobe tana neman cirewa ya turo kofar dakin.

? Ta manta kayan dake jikinta, gani tai ya taho inda take da sauri, yana karasowa ya rungumeta tsam a jikinsa.
? Shiru tai a hankali yace "Baby wannan shigar fa?"

? Tunowa tai, ta kasa cewa komai, dagota yai ya kalleta daga sama har kasa, kunya tasa ta juya baya da sauri, kara juyo da ita ya rungumeta yace "saura kadan fa na fadi."

Kallansa tai tace "kai Yaya."

Sumbatarta yai zaiyi magana sai ya fasa yanda yaga ta kura mai ido.

Yace "menene?"

A hankali takai hannunta gefen bakinsa tace "me ya faru?"

? Hannunta yadan ture yace "ba wani abun bane ina sauri ne ban kula ba na danji."

? Idanunsa ta kalla sai dai ta rasa me yasa bata yarda ba.


Kamar zatai magana sai kuma ta fasa, gani yai idanunta sun fara cicikowa yace "Menene kuma?"

? Ta fara kokarin shanye kwallar tace "ba saboda fitar dakai bane wani yama haka? Ko dad......"
Kara jawota yai ya rungume yace "ki bani abinci, yunwa nake ji."

? Shiru tai cikin rada? yace "mu biyu ne a gidan, na dauka Sageer zai shigo sai naga ya juya, kinga yau sai mu....."

Sai ya kara matsowa kusa da kunneta yace "sai a biyani bashina duka."

Dagowa tai ta kalleshi, kamar zatai magana kuma sai yaga tayi murmushi tace "ka dainajin yunwar ne?"

Cikin shagwaba yace "ina fa? Ai ni yau a nan ma za'a bani indai anaso inci." Ya fada yana nuna bakinsa.

Dariya tai, ya ja hannunta suka nufi kasa.


#OneLuv=ؕ?=??? *JALILAH* =???


Written By : *AYUSHER MUHD*
Wattpad: *Ayusher Muhd*


*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*


*74*


Haka ya jawo hannunta har kasa, dinning ya nufa ya zauna akan kujera yace "anan."

Kai ta daga alamar to sannan ta nufi kitchen, tana zuba abinci tana tunanin abinda ya faru har aka bigemai baki dan kana gani kasan ba faduwa bane.

? Haka ta zuba ta nufi dinning, tana ajiye wa ya dagata ya daurata akan saman dinning din inda yake, kallansa tai tana dariya tace "karfa nai barna, inya fashe fa yaji nauyi."

Baki ya bude alamar mamaki yace "kuma fa haka ne, kar muje muji abu ya fashe ba shiri."

Fuska ta hade tace "yanzu ni har katuwa ce dazan fasa wannan table din?" Ta fada tana bubuga table din."

Ya dan canza fuska yace "kuma fa haka ne, taya ma za'ace babyna guda zata karya wannan katan abin? Wai waye ma ya fada?"

Ido ta kafeshi dashi, waige waige ya shiga yi yace "ni wai waye ya fara maganar nan?"


? Serving spoon ta mikamai tace "zubama da kanka."

? Kwanciya yai a kan cinyarta yace "ni kam in ba'a ban abinci ba nan da minti biyar Allah inaji za'a samu matsala."

? Dayake rigar karama ce daya kwanta sai ya zama kasansa kadan rigar ta tsaya, hannu yasa ta cikin cinyoyinta da sauri tace "zan zuba wallahi, ni wallahi tsoron zama anan nake, in wani ya shigo fa?

Dauke kansa yai daga cinyarta yana dariya yace "in suka ganmu kinga sai suyi gaggawar bamu namu muhallin."

Jalila ta kalleshi cikin mamaki tace "lalai yaya." Ta karasa da dariya tare da fara zubamai abincin.

Shiru yai yana tunanin mahaifinta, Jalila ta kalleshi tace "Yayah!"
Kallanta yai yace "yah?"

Tace "me kake tunani?"
"Me kika gani?"

Tace "bakomai."

Fork ta mikamai, ya kalleta sannan ya dan shagwabe yace "ni faduwar danai dazu ma kamar na bige hannuna."

Murmushi tai sannan tace "ba sai kayi pretending ba." Ta karasa tana debo abincin.

Murmushi yai sannan ya shiga karba, yaci sosai sannan yasha tea, kwantar da kansa ya sake yi a cinyarta tace "yaya....."

Jitai cikin sanyin murya yace "Jalilah?"

A hankali tace "Naam."
"Ki dinga ma mahaifinki addu'a yayi nisan da sai dai a kwatoshi da addu'a, da fatan nemar masa shiriya agurin mahalicci."

? Jalila tai shiru tana kallansa, dago da kansa yai amma kan na kan cinyarta yace "bawai wani abun bane, kawai dai ina tunani addu'arku ita yafi bukata. Ya karasa da murmushi wai dan ya nuna mata bakomai.

? Yanda take kallansa ne yasa yace "ba wani abun bane kawai dai........"

Katseshi tai tace "shi yama haka ko?" Ta fada tana taba gefen bakinsa."

"Oh wai akan me babban mutum zai daki kamar ni? Ni ba dan yaro ba nima?"

Jalila tace "abinda Mumy ta fada hakan ne ko?"
"Name kenan?"
Na Dady zai kwace musu company dinsu da gidansu?"

Kai kawai ya juyar ya kara kwanciya yace "bansani ba."

? Hannu tasa ta dagoshi tace "Yayah?"

Yanda ya kalleta yasa ta sakeshi tana murmushi tace "hakan ne , yanzu ya kukai?"

Yace "mun samu an kwace company din daga gunsa yana gunmu yanzu sai dai bansan maganar gidansu ba."


? Jalila ta fara neman hadiye kwallarta tace "Yaya ta ina dan Adam zaiyi haka? Taya mutum zaiyi haka? Kuma mutum din ma wanda yake mahaifi? Miji?........"
Hawayenta ne suka nemi fitowa yasa ta shiga motsa baki tana neman hadiye kukanta.

? Hassan ya jawota kan cinyarsa yana kallanta, kallansa tai sannan ta sunkuyar da kanta hawaye suka fara zubo mata.

Yace "to ke yanzu kukan me kike a takaice? Ke kikai? Shifa yai sannan a yanda mahaifinki ya nuna kamar ba wanda ya isa ya....."
Sai kuma yai shiru, hawayenta ta shiga sharewa suna sake zubowa tace "ni da wani ido zan kalli mutanen gidan nan? Da wani ido zan kalli wadanda suke jinina?"
Hassan ya jawota jikinsa yana lalashi, yace "mubar kasar nan a dan kwanakin nan, naga alama in ba barin kasar nan mukai ba bazan daina ganin kina kuka akai akai haka ba."

? Dagowa tai ta kalleshi, yace "ni kila zan dan saki kuka amma kadan, dan haka." Ya fada yana nuna tsagun karamar dan yatsansa.

Jalila tace "ashedai zaka sani kaima."
Yace "kardai inyi karya ne ai.


Murmushi tai sannan ta kalli gefenta da wayarta ke

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login