Showing 63001 words to 66000 words out of 149705 words

Chapter 22 - Jalilah Book One Complete Hausa.doc

Ayusher   

28 Oct 2025

638

in kara mata damuwa.......
Da sauri tai shiru tare da juya kai, takowa yai a hankali zuwa inda take, yasa hannu ya juyo da fuskarta yace  Damuwarta?

Yawo ta hadiya sannan ta mike da sauri ta matsa daga inda yake.
Hannu yasa a gefen cikinta ya jawota yana kallanta da idanunsa wanda suka canza.
Gabanta ne ya shiga faduwa, tana kallansa.

Dayan hannun yasa ya juyo da fuskarta saitinsa yace  tambayarki nake.

Jalila idanuna suka firfito tace  hmm.
Saketa yai yana neman fita, da sauri tasha gabansa tace  Yaya Please!

Kallanta yai yace  in bakyasan in tambayeta ki fadamin meke faruwa?

Jalila ta kalleshi tace  wlh bansani ba nima, ranan nan ne na fita naji Abba nadan fada.

Yace  yace me?

Jalila tace  Yaya dan Allah.....

Cikin zafi yace  bani hanya

Jikinta ne yai sanyi ta kalleshi sannan ta sanar dashi abinda ya faru, ta daura da cewa  Yaya dan Allah karka nuna ka sani, dan Allah.

Gani tai a hankali idanunsa sun rikede, a hankali tadan matsa baya kadan, tana tsoron kar ya mazge ta.
Gani tai ya dau key din mota a zuciye yayi waje.

Biyoshi tai da sauri, sai taga ya fita waje.

Komawa tai kitchen gun Ummy tana cewa  Ummy yahkuri na dade.

Ummy tai murmushi tace  bakomai, dama kinyi zamanki, Hassan ne ya fita?

Tace Umm kawai dan batasan me zata ce ba daga nan......



#OneLuv=ؕ?

=??? *JALILAH* =???

Written By : *AYUSHER MUHD*
'ote me on Wattpad : *Ayusher Mohd*


*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*
(_D home of expert and perfect writer's_=ء?)

" *Sending you smiles for every moment of your special day...Have a wonderful time and a very happy birthday!*" .......Phertyn Uwani=?? (El-Mustapha)

*37*


Haryasa key ya ta da motar sai ya kashe motar ya kwantar da kansa jikin kujera tare da rufe idanunsa.

Idanunsa ya bude wanda yanzu ya kara kadawa yai jaa sosai, wayarsa ya dauko ya kira number Abba.

Bayan sun gama yawo shi da ita yai parking din motarsa a gaban gidansu.
Zaliha ta kira number yayarta a waya tace "Aunty mun dawo."

Tace "to bari in fadamai ya fito."
Hafiz ta kalla wanda ke faman hada takardu tace mai "Taura yana waje."
Wasu takardun ya dauka ya fita, Taura na ganinshi ya kalleta yace "ki shiga ciki bari muyi magana."
Tace "a'a ku gama magana ni ina jiranka anan, banasan rabuwa dakai yanzu."

Taura yai murmushi sannan ya fita, tsayawa sukai da Hafiz suna tattauna wani abun.

Ringing din waya ne yasa ta kalli inda ya ajiye wayarsa, Eldest Son abinda taga an rubuta kenan.

Eldest? Tuno hoton maza biyun nan tai, ta tabbatar wanda ya maze din nan shine babban, murmushi naga tayi sliding ta daga wayar, a kunnenta ta kara.

? Hassan shiru yai kafin can yace "Abba?"

Zaliha tadan sake murmushi tace "Bayanan."

? Gani nai Hassan ya bude kofar motar ya fita yace "waye"

Gaban Zaliha ne ya fadi dan batasan ya akai ta tanka mai ba.
Cikin tsawa yace "waye nace?"

Bakinta ta shiga motsawa dan ta kasa magana, raban dataji tsawa ace ita akema har ta manta.
Hassan cikin tsawa da karfin gaske yace " kin fadamin ke wacece ko sai nazo nan na fasa miki baki."

Zaliha ta kalli inda Taura yake a rikice tace "Bari ba........"

Yace "ina mai wayar?"
Da sauri ta bude motar ta taho inda Taura yake jiki na rawa ta mika mai wayar.

Yana ganin sunan Hassan gabansa ya fadi, kallanta yai cikin takaici yace "Meyasa kika dagamin waya?"
Tace "bansani ba nima...."

Matsawa yai daga gun sannan ya kara wayar a kunnensa yace "Hassan!"

"Hassan? How can u call my name as if ba abinda ke faruwa"

Abba yace "Ya akai? Ina wani meeting ne Secretary gun ce ta dauka."

Hassan fuskarsa ta kara hadewa yace " Wacece wannan? Abba me kakeyi a garin Abuja? Ba dai......"

Kasa karasawa yai saboda kansa da yaji yamai nauyi, Abba a rikice yace "Hassan? Hassan jikin ne?"

? Idanunsa ya runtse cikin takaici yace " Abba ko ka manta wacece Ummy a gareka? Ta yaya zaka yi mata haka?"
Abba a rikice yace "Hassan ba haka bane ka tsaya kaji."
Cikin takaici yace " Wallahi Wallahi Abba in dai ina numfashi a doron kasa bazan taba bari ka tozarta Ummy ba, sannan kayi gaggawar gayawa wannan yarinyar dan na tabbatar muryar yarinya naji, wallahi in har bata shiga hankalinta ba har cikin gidan ubanta zanzo in lahantata, in yaso a kamani."

Ya kashe wayar cikin takaici sannan ya saki wayar kasa cikin wani irin bakin ciki ya saki wani irin kara tare da tsugunnawa.

Jalila da Ummy dake kitchen suka fito da gudu saboda karar da sukaji, da sauri Ummy ta karasa kusa dashi tace "Hassan! Menene?"

? Idanunsa na runtse bashi koma da alamar dagawa, Ummy ta kalli Jalila a rikice wacce itama gaba daya hankalinta ya tashi, tace "Jalila kira Sageer a daki."

Da gudu a juya, bata kwankwasa kofar ba saboda rikicewar da tai itama ta bude kofar.

Yana kwance daga shi sai singlet da gajerar wando, yana ganinta ya mike zaune da sauri, juyawa baya tai da sauri tace "Uncle kazo, yaya....."
Ai yanajin tace yaya ya sauko da sauri ya zari goduwar riga ta fito, shima ya fito bai ma karasa sa kaya ba sai a falon.

? Yasan nanan a tsugunne duk yanda Ummy tai ta dagashi yaki, Sageer na zuwa ya dagashi da kyar, kallan Ummy Hassan yai idanun sa jawur kai kace garwashi.

? Ummy batasan hawaye na zubo mata ba tace "Hassan lafiya?"

? Idanunya rufe kawai dan takaici, wato ita tana nan ta dauka mijinta na aiki ashe mata yake bi? Tun yaushe ya fara? Badai zina yake ba?


? Sageer ya kalleta yace "Ummy akaishi daki."
Ta matsa tana share hawayenta, hannunsa ya zare daga jikin Sageer sannan yace "take care of Ummy zan karasa da kaina."

Sageer ya kalleshi har yai gaba, Jalila tabi bayansa da sauri.

Ummy kam jingina tai da motarsa tana share hawaye, Sageer yace "Ummy muje ciki."

Kallansa tai tace "Sageer kaji karar da ya saki? Bai tabayin irin haka ba, ina murna ya fara samun sauki, Sageer meke shirin faruwa?"

Sageer yai shiru tausayin Yaya da Ummy ya hanashi cewa komai, ta share hawayenta sannan tace " Sageer kaje gun Dr kajii ko da matsala."

Sageer yace "To Ummy, amma muje ciki ki zauna tukun na."

Hassan na shiga ya zauna a kasa jikin gado ya jinginar da kansa a jikin gado.

Jalila ta tsaya a bayansa ta rasa ta ina zata fara mai magana, ta dade a tsaye dan tayi wajen minti ashirin kafin ta juya jiki a sanyaye, hannu yasa ya riko hannu ya riko hannunta ta baya.

Juyowa tai da sauri tana kallansa, haka suka tsaya hannunsa na rike da nata ba kuma wanda yana wani magana, har na tsawon minti goma sha biyar, kafin ta tsugunna jin kafarta na dan zafi, ji tai ya saki hannunta.

Kallansa ta sakeyi sannan tace "Yaya jikin ne ko wani abun ne ya faru?"
Bai kalleta ba, sai dai yanzu ya mike daga kasan da yake ya zauna akan gado.

Sannan ya kalleta, idanunta na kansa ta kara cewa "yaya!"


Kallanta yai sannan yace " are u worried about me? Or are u scared?"

Ta kalleshi tace "Yaya dan Allah kadaina min tambayar nan, dan bansan me zance ba."

Yace "okay, jeki to."
Tace "naam?"
Yace "ba fita zakiyi ba na tsayar dake?"

Kallansa ta sakeyi tace " Yaya."

Kallan daya mata ne yasa ta mike tai waje jiki a sanyaye.

Zama tai a falon tana tunanin abinda ya faru yanzun nan, ya riketa sannan yace jeki, mekenan? Itakam tana kasa ganeshi wani sa'in.


**********

A Abuja kuwa Abba na gama waya ko kallan Hafiz baiyiba ya fada motarsa yai gaba hankali a tashe, kayansa kawai ya dauko a dakinsa sannan yai check out ya fito tare da ajiye motar.

Airport ya nufa dan hankalin sa a tashe yake, yana zuwa yai sa'a akwai jirgin da zai tashi karfe 3:00pm zama yai yana jira sai dai zuciyarsa ta kasa nutsuwa.

Lokaci nayi kuwa ya mike da sauri, ba nisa daga Abuja zuwa kano a jirgi kan kace me sai gasu sun sauka.

Bai tsaya neman Mamman ba kawai ya hau taxi zuwa gida.


Ummy na kwance a falo, tayi shiru tana tunanin Hassan, tana jiran dawowar Sageer daga gun Dr.
Jin an taba kofa ne yasa ta mike da sauri dan ta dauka Sageer ne.

Da sauri ta bude kofar tana cewa  Sageer me Dr din ya.......

Ganin Abba yasa ta tsaya da maganar tana kallansa, kafin tace  Sannu da zuwa.

Kallanta yai jiki a sanyaye yace  Yauwa, sannan ya fara kokarin shiga ciki.
Hannu tasa ta amshi jakarsa tai gaba fuskarta ba walwala.

Kallan falon yai sannan ya kalli hanyar sama, kafin yace  ina mutanen gidan?
Tace  Ameera tace sai jibi zata dawo, Sageer ya fita.

Yace  Jalila fa?
Tace  Tana sama.

Yace  Hassan fa? Ya jikin nashi?

Kallansa tadanyi kamar zata fadamai sai tace  da sauki. Sannan tai gaba.


Ba abinda yakesan ji ba kenan, so yake yaji ko wani abun ya faru dashi, sai dai baisan ta ina zai fara ba shiyasa yai shiru.

Ummy tana ajiye mai jaka ta juya zata fita, har takai kofa yai sauri yace  kinje taron kuwa?
Kallansa tai tace  banje ba.

Yace  Naga kamar bakya farinciki da dawowata.

Wani murmushin takaici tai kafin tace  banasan musu ko fada dakai daga dawowarka, mu bar maganarnan, kai wanka kafin ma shiryama abinci.

Kallanta yai hartabar dakin, zama yai a bakin gadon sannan ya sa hannayensa ya rufe fuskarsa.


Jalila kam ganin hankalinta ya kasa kwanciya yasa ta mike ta kara turo dakin a hankali.
Yana zaune yasa farcensa yana karzar bayan hannunsa, idanunsa nakan bango yana tunani, idanunsa da fuskarsa a hade suke.

Jalila ta shigo ciki, har taje kusa dashi bai san tazo ba, hannunsa ta kalla taga yana ta karza har yaji ciwo ga jini nan.

Kallan tsoro tamai sannan tasa hannunta agun dayake karza, tana kallansa.

Dagowa yai ya kalleta sannan ya kalli Hannunta sannan ya kalli nasa hannun, sake kallanta yai sai dai yanzu idanunsa sun canza.

Idanunta ne suka ciciko tace  Yaya wani abun ne yafaru ko? Menene dan Allah? Ko akan abinda na fadama ne?

Hannunsa ya janye sannan ya mike daga kan gadon zai nufi toilet.

Tace  kayi hakuri dan Allah, laifinane dana sani ban tsaya naji abinda suke cewa ba, sannan dana sani ban fadama abinda ke faruwa ba, kayi hakuri dan Allah, it s all my fault.

Tafada tare da share kwalla.

Juyowa yai ya kalleta kanta na kasa, tana share hawaye, ya dade yana kallanta kafin yace  ba akanshi bane, sannan in ma shine ba laifinki bane laifinane tunda ni na matsa miki sai kin fadamin.

Kallansa tai sannan tace  akansa ne ko?

Kai ya girgiza mata alamar a a sannan ya shiga toilet.

Kallansa tai sannan tai ajiyar zuciya tace  Goggo ya zanyi? Inaji nayi laifi ga wanda zai taimakeki, na tambatar da ban fadamai ba kila yau zai dauke ki daga asibitin sai dai da alama wannan bakin nawa ya ja min........




**************

Inna ce ta kalli Dady tace  Abakar!

Kallanta yai sannan ya amsa, tace  sai yaushe zaka gidan Jalila?
Yace  so nake sai Taura ya dawo, naji ance yayi tafiya.

Tace  meye damuwa ta da haduwarka da Taura?

Dady yai kasa dakai yana cewa  ai kinga ya kamata mu sake mai godiya da taimakon daya mana.

Inna tace  wace godiya bayan abinda muka aikata yana neman wargajewa saboda shirmanka.

Dady yace  Inna ni......
 Dalla rufemin baki, so kake kace ba laifinka bane? Ka tabbatar ka lalabata da mijin nata, dan kafi kowa sanin dayan plan dinmu da mukesan sake bude wani branch dinmu, ka kuma tabbatar inba da taimakon Taura ba abin nan bazai yiwu ba, ya kamata kasan abinyi, kafin ni insa hannu, kasan in nasa bazata ma kyau ba.

Dady yace  To inna.

Ta kalleshi sannan tace  tashi kaje, ka kuma tabbatar kaje gun Jalila, dan a yanda na ganta da yaran nan ina tsoro karta fadamai komai, wannan yaran idanunsa kadai zaka kalla zaka fahimci ba kara a idanunsa balle ya mana.

Yace  to sannan yai waje.

Shiru tai tana sake wani tunanin, yanzu me ya dace tayi??????

(Nace  kya tambaye ni=?? )

*********
Sageer ne ya kalli Dr yace  kana nufin hakan alamu ne na samun nasara?

Dr ya kalli Sageer sannan ya jinjina kai yace  Sageer kasan Hassan yana dauke da trauma ne wanda shikadai yasan abin da kuma faruwar abin, tunda abin ya faru ka taba gani yayi ihu ko fada da karaji?

Sageer yace  a a sai dai zafin rai, rashin magana da kadaicewa, sai kuma rashin nuna emotion na farin ciki ko na tsantsan bakin ciki a fuskarsa, a koda yaushe fuskarsa a hade take wanda yake nuna alama ta bakin ciki ba alama na canji.

Dr yace  Good, yau kuma fa?

Sageer yace  yau yayi kara sannan kana kallansa kasan ransa a bace yake wanda bacin ran ne da alama yasashi yin karan.

Yace  Very Good, ka gano improvement?

Sageer yace  na fahimta Doctor, a da yana fada sai dai bawai da jikinsa yakeyi ba, ko zuciyarsa yanayi ne da fuskarsa da bakinsa.

Yace  Very Good ka fahimceni yanzu?

Sageer ya daga kai cikin gamsuwa da jin dadi yace  nagane Dr, na kuma gode sosai.


#OneLuv=ؕ?


=??? *JALILAH* =???

Written By : *AYUSHER MUHD*
'ote me on Wattpad : *Ayusher Mohd*


? ?? *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*
? (_D home of expert and perfect writer's_=ء?)



*38*


? Saukowa kasa tai, tana matatakalar karshe, taha an bude kofar dakin Ummy, tsayawa tai tana jira Ummyn ta fito sai ta karaso.
Ganin Abba tai ya fito daga dak??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????in, mamaki ne ya kamata da sauri ta karaso dan yana fitowa suka hada ido, tsugunawa tai ta gaisheshi.

Kallanta yai bayan ya amsa yace " Jalila Hassan yana sama ne?"
Tace "eh."

Da sauri ya wuce ta ya nufi sama, bata kawo komai a ranta ba kawai ta wuce falo.
A kitchen taji Ummy nan ta nufi gunta, tanashiga tace "Ummy ashe Abba ya dawo?"

Ummy ta juyo tace "eh, ya jikin Hassan din?"

Jalila tace "da sauki." Ta fada tare da karasawa gunta tana neman taimaka mata gun rufe kullar da ta gama zuba ma abinci."

Ummy tace "dauki abincinku la'asar har tayi ba wanda yai lunch."

Ta amsa da to.

Abba kam dakin ya karasa yai knocking din kofar, Hassan daga ciki ya fito daga toilet kenan daure da alwala ya bude kofar.

? Tsayawa sukai yana kallansa hannunsa rike da kofar, fuskarsa kuwa ya kara hadeta tamau, Abba ya kalleshi yace " Hassan baka ganni bane?"

Hassan ya saki hannun kofar baice komai ba ya wuce ciki.

? Abba ya shiga dakin sannan ya maida kofar ya rufe, yace "Kayi mamakin ganina ko? Bayan dazu mukai waya."

Hassan bai kalleshi ba balle yai magana, Abba ya zauna akan sofa sannan yace "Hassan!"

Hassan ya juyo ya kalleshi da jajayen idanunsa, yace "How can u? Of all people?"

Abba ya runtse idanunsa cikin takaici sannan ya mike ya kamo hannun Hassan suka zauna akan kujerar.

Hannayensa na cikin na Abba yake kallansa, Abba yai shiru kafin yace "Hassan."

Hassan ya kalleshi cikin takaici sannan ya zare hannunsa daga nashi yace "Zina kake?"

Abba cikin mamaki ya kalleshi yace "Hassan wani irin magana kakeyi haka? Taya zaka cemin ni mahaifinka? Ka kalleni kace zina nake?"

Hassan ya mike tsaye tare da dan matsawa daga inda yake yace " Ni kaina ina fatan hakan ya zama laifi ne na aikata."

? Abba yai shiru yana kallan Hassan, gaba daya ma ya rasa ma mai zaice.

Muryar Hassan yaji yace "wacece?"

Abba yai shiru tare da shafar fuskarsa, Hassan ya juyo ya kalleshi cikin bakin ciki yace "Budurwarka ce?"

Abba yace "Hassan ni kaina ina mamakin kaina, wai nine nakesan........"

So? Hassan ya kalleshi ya sake cewa, so? Abba so kace?"

Abba yace " Hassan wai me yasa kake kokarin juya kalamai na zuwa abinda ranka ya raya maka?"

Hassan cikin dan daga murya yace "ta ya bazan fassara ba? Ta yaya Abba zaka kalleni kacemin wai so? Ta yaya zaka furtamin kalmar so, sannan kalmar san bawai akan Ummy kake yinta ba, ta ya........"

Kasa karasawa yai saboda numfashinsa dayaji yana seizing.
Abba ya mike da sauri yazo kusa da shi yace "Hassan menene?"

? Hassan ya zare jikinsa daga rikon da Abba yamai ya dan ja baya cikin takaici yace "ni danka ne, banida ikon hanaka abinda kai niyya, sai dai wlh Abba kamar yanda na fada in dai had ina numfashi bazan taba bari ka tozarta Ummy ba."

? Kofar dakin aka bude, Abba ya kalli kofar shikam Hassan kai ya juya cikin takaici dan yayi tunanin Jalila ce.

? Muryar Ummy yaji tace "Hassan!"

Juyowa yai da sauri ya kalleta, Ummy ta share kwallarta data zubo mata sannan ta matso kusa dashi dariya yaga tanayi tana share hawayenta, tace " Hassan yanzu Sageer ya kirani, Dr yace sauki ne ke samuwa a gareka,? ya gama min bayani naga bazan iya hakuri ba sai na ganka."

Ta kara share hawayenta tace "Hassan bansan yanda zan kwatanta maka dadin da nakeji ba."

? Cikin takaici ya kalli Abba sannan ya kalli Jalila wacce ta juya ta fita, Hassan ya kalleta yace " Ummy?"

Tace " fadanku da Abbanka a kaina?"

Ya kalleta cikin tausayawa, tai murmushi tace "karka damu Hassan bakomai, ko ka manta ba mace daya aka halarta ma namiji ha aura ba? Ta yaya zaka nemi mahaifinka ya zauna da mahaifiyarka ita kadai? In mukai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login