Showing 18001 words to 21000 words out of 149705 words

Chapter 7 - Jalilah Book One Complete Hausa.doc

Ayusher   

28 Oct 2025

608

aika aka kira mata Jalila, tare dukansu suka hadu a kitchen sukai ta aiki, Safeena kuwa tana gidan Kanin Inna a cikin gari, suna gamawa Mumy tace ma Jalila tace tai wanka a toilet din Safeena.

Wani had'ad'en material ta dauko mata ta saka, Jalila kam yau tayi mamakin kyan da tai, dan tayi kyau sosai, Mumy da kanta ta daura mata dankwali sannan ta sa mata turare.

? Wajen azahar motar Taura tai parking a gida.
Ummy ce ta fara futowa sannan shikuma ya kashe motar ya fito.
Kallo d'aya zakama Ummy kasan macece mai class ba wani shigar karya tai ba sai dai kana ganinta kasan matar manya ce.
Taura ya matso sannan ya nuna mata hanyar.

? Dady ne ya fito ya shigar dasu falon baki, sai wani washe baki yakeyi, Inna ta sauko suka gaisa, nan suka dan tattaba magana akan harkar business, Mumy ta mike ta shigo dakin Safeena inda Jalila take a zaune,tace "Jalila zo ki kai musu abinsha."
Jalila ta mike tana cewa "Mumy kunya nake."
Mumy ta yafa mata mayafi tana cewa "abokana Dadynki ne gaisawa kawai zakuyi."

Haka ta fito ta amshi tiren ta nufi falon, ta rasa me yasa gabanta ke faduwa, yaye labulen tai ta shiga da sallama.

? Ummy tana shigowa ta kura mata ido, haka kawai taji yarinyar ta shiga ranta, yanayin nutsuwarta ne ya kara burgeta, Jalila ta ajiye tiren kanta na kasa dan ji take kamar kallanta akeyi.

Kanta na kasa ta gaishesu, Ummy ta fara amsawa sannan Taura ya amsa ya daura da cewa " Ya karatu?"
Tace "Alhamdulila."

Yace "ance kun kusa fara jarabawa sai a dage ko?"
Tace "insha Allah."

Ganin yanda take tsugunne a gun yasa Ummy tace "tashi kije."
Nan Jalila ta mike ta fita.

Inna ta kalli Ummy tace "kun ganta?"

Ummy tace " Mun ganta sai fatan Allah ya kaimu lokacin, sannan muna fatan bazaku mata maganar auren ba har sai ta gama karatunta kamar yanda aka tsara."

Inna tace "dama hakan shine daidai."

Ummy tai shiru kafin can tace "sai dai ni banasan auren dole, a matsayina na mace banasan tauye hakkin mace yar uwata, kar muje akwai wanda takeso."


? Mumy tace "in dai wannan ne ba matsala dan Jalila ba ruwanta da kula kowa, ita kunya ma bazata barta ta kula saurayi ba."

Ummy ta jinjina kai na gamsuwa, haka suka sa hannu a takarda na yarjejeniya.......

Sannan sukai sallama.


Nace uhm hmm..........
[07/10, 21:28] * +234 803 222 1758, : =??? *JALILAH* =???

Written By : *AYUSHER MUHD*
Wattpad: *Ayusher Muhd*


*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*

? (_D home of expert and perfect writer's_=ء?)

*NO 11*


? Ummy har ta sa hannu zata kwankwasa kofar Hassan sai kuma naga ta sauke hannunta sannan ta bi kofar da kallo, juyawa tai jiki a sanyaye tana neman sauka.
Sagir ne ya fito daga dakinsa, kallan Ummy yai sannan ya matso gunta, yace "Ummy menene?"
? Tace " Sagir ashe kana ciki?"
Ya kalli shima kofar Hassan sannan yace "Ummy in koma dakin yaya ta karfi?"
Harararsa tai na wasa tace "kana tunanin zai barka ne?"
Yace "sai in zauna ta karfi ince bazan fita ba."
Ummy tai murmushi tace "karka damu insha Allah na kusa samun mai tayashi kwana."
Cikin zumudi yace "haba?wanene?"
Ummy ta fara sauka daga matatakalar tana cewa " watace."
Sagir cikin mamaki yace " Aure?"
Nan ta shiga bashi labarin abinda ke faruwa sannan ta daura da cewa " Sagir ni na rasa me yasa tunda na ga yarinyar nan nakeji kamar akwai alamun tauye hakki acikin wannan lamarin."

Sagir yace "ba wani tauye hakki Ummy, na farko Yaya ba mahaukaci bane, ba kuma nakasashe bane, sannan a zamanin da ai mace ma ance ba sanin wanda zata aura take ba har sai anyi mata auren."

Kallansa tai tace " hakane nima dan Abbanku sai da aka gama komai na ganshi."
Tana fada tana dariya.
Yace "kinji ma ko? Wow Ummy harna kosa naga yarinyar, tunda ta kwanta miki ma tabbatar yarinyar ta gaske ce."
Ummy tace "kai sai yaushe zaka nunamin taka budurwar?"
Yace "nan gaba kadan nafisan ne sai mun rabu ta gama makaranta sai na fara zuwa gidansu a matsayin saurayinta ba malami ba, kinga sai na kawo miki ita kiganta."

? Ummy tai murmushi tace "babban burina a duniyarnan bai wuce abubuwa uku ba Sagir, na farko naga yayanka ya warke ya dawo kamar da, na biyu naga ya samu macen da zata kula dashi na uku kuma na ganka kaima da matar da kakeso kuna rayuwar farin ciki."

? Sagir yai murmushin jin dadi yace "insha Allah Ummy duka burikan nan naki zasu cika ba da dadewa ba."

? Haka suka sauko kasa suna hira.
*****

? Kansa yaji yamai gingirin gim, gaba daya dakin yamai zafi, mikewa yai ya fito daga d'akin ya sauko kasa.

Yana jin muryar Ummy dasu Ameera a kitchen, waje yai ya fada motarsa yai waje...........

Wani irin farinciki kwanan nan takeji, ga gida yanzu ana santa sosai, ga tsananin soyayya dake kara shiga tsakaninta da Sagir, jiya suka gama waec zasu fara neco, shine yau ta fita da kanta ta hau mota tace gidansu Zarah ta amso aran wasu litattafanta.

Tana zaune cikin adaidaita tana murmushi suka dan tsaya saboda dan karamin go slow dake gun, gefenta ta kalla motarsa ce a gun, kallan motar tai sannan tai dan tsaki tace " irin motar wannan dan iskan."
Kallan motar ta sakeyi sannan, da yake motar mai tint ce sannan bata ganshi ba a wancan ranar shiyasa bazata iya ganewa ba.

Sa'a akai ya juyo da fuskarsa inda take,? kawai ya hangota tana murguda baki da hararar motar, mamaki ya kamashi dan ya tabbatar bata ganinsa bare tace wani abin ya mata.
Har ya dauke idanunsa sai ya kara juyawa, baki ta kara tabewa sannan ta juya kanta tana yan guna guni, kai ya girgiza sannan ya juya fuskarsa.

? Jalila tana dan masifa tana cewa ai indai na kama mutumin nan ko ban mai komai ba sai na harareshi irin taimakon nan ma bai iya ba, ba kunya ranar ya mata rashin mutunci.

Hassan kam gaba yai ya tafi can inda ya saba zama, ya kashe motar sannan ya kwantar da kansa a jikin kujera tare da kunna karatun al-qur'ani, kira'ar Malam Abdullahi Abba ne ya zagaye cikin motar.


?? Jalila an samu jin dadi, yanzu kayanta kala kala, sannan haka zata zauna wani sa'in a falo itafa Yasmeen suyi ta kallansu, duk sanda suke kallan india in ana soyayya itada Sagir dinta kawai take hangowa, ba shakka bata san sanda san Sagir yai nisa a zuciyarta ba.

Goggo najin dadin yanda Jalila yanzu ta murmure duk da ba kiba tai ba amma inka ganta zakaga ba wahala a jikinta.

? A kasan zuciyar Goggo har yau hankalinta ya kasa kwanciya da yanda su Mumy da Dady ke jan Jalila a jiki, sai dai duk sanda Goggo ta nemi Jalila data rage zuwa gunsu Jalila sai tace "Goggo Allah ba abinda sukemin sai mutunci."

? Jalila an dage sosai ana ta karatun Neco saboda Sagir yace tai karatu sosai dan yanasan yaga matarsa ta cigaba da karatu.
Duk sanda yai wannan maganar sai Jalila ta sunkuyar da kai wai ita kunya, sai dai a kasan ranta wani dadi take ji.

? Goggo har ta gaji da labarin Sagir dan kusan kullum sai ta mata tadin shi.


? Su kuwa a bangaren su Inner company ya kara habaka saboda sun samu kudi sosai a gun Taura, yanzu company din ma yafi da karfi.
? Su uku suke tsara abin biki dan har kayan daki sun fara siya, Safeena kuma suna ta shirye shiryen kaita Egypt wai ta cigaba da karatunta.
Sai dai ni nasan suna kokarin fita da ita ne dan karma a san da zamanta har sai anyi auren.

? A can gidan su Ummy kuwa, suma ita da Ameera da Aina'u suna zuwa siyayyar kayan lefe, sanda Aunty nana taji zancen nan har gida tazo tacema Ummy wai tayi dabara ai gwara da suka nemarmai mata ta kudi wai sai yafi daraja.
Sanda tai maganar nan Ummy bata tanka ba dan haryau kalaman Aunty Nana na mata ciwo.

??
? Yau suke zane paper karshe ta neco, suna fitowa suka hau ihon gama makaranta.
Jalila ma zaune itada Zarah a can gefe, Zarah tace "Jalila ni tun jiya nakesan fada miki wani abu."
Jalila tace "menene? Fada kukai da Nasir?"

? Zarah ta juyo saitin Jalila sosai tace "Jalila tsoron abinda na aikata nakeyi."

Jalila ta mata kallan tuhuma.

Zarah tace "Jalila jiya Nasir ya sani yin abinda na ke ta tsoro."

? Jalila tace " me ya saki yi?"
Idanun Zarah ne suka canza suka ciciko da kwalla tace "Jalila jiya muna tare da Nasir kinsan in zaizo kasan layinmu yake tsayawa sai ni kuma naje saboda tsoron kar yayana ya ganmu, jiya sai na ganshi a mota sai yake cemin motar babansa ce aka aikeshi, bayan mun gama hirarmu a cikin mota zai tafi sai cemin yai wai sai na mai kiss."

? Jalila cikin tsantsar mamaki tace "kiss?"

Zarah ta runtse ido cikin dana sani tace "Jalila kinsan yanda? nake tsananin san Nasir ganin ransa ya baci dana tsaya ina tunani yasa na matso kusa dashi na sumbaceshi a kunci, shine yace shi sai na mai a baki, nan na kai bakina saitin bakinsa shine ya rikoni ya dinga tsotsar leb'ena bansan sanda na bude mai cikin bakina ba, Jalila bansan ya akai ba na kasa kwacewa sai bashi hadin kai danai, dakyar na kwavi zuciyata na fizge jikina da sauri na fito daga motar nai gida da gudu........."

? Kuka ne ya zo mata wanda yasa ta kasa karasa abinda takesan fada, Jalila kam sam tama kasa magana sai inalilahi kawai da take cewa........

? Ganin yanda Zarah ke kuka yasa Jalila ta riko hannunta tace "Zarah it's okay! Kinyi laifi babba ma kuwa sai dai tunda harkin fahimci kinyi laifi sai ki nemi yafiya a gun Allah ki kuma kiyayi aikata makamancin abinda kika aikata."

? Zarah ta rungume Jalila tana kuka, Jalila tace "Sai dai magana daya zan fada miki gaskiya ki bincike san da Nasir yake miki, so ne ko sha'awa, in so ne sai ku tuba ga Allah ku nemi kariya daga shedan in kusa sha'awa ne sai kisan zaman da zakiyi dashi."


? (_Gareku 'yan mata da samari masu irin wannan soyayyar, sai kaga saurayi yazo gun budurwa in zai tafi sai yace sai ta mai kiss ko sai ya rungumeta, ko kuma ya nemi tamai abinda bai kamata ba, wanda ke da kike aikatawa kinsan haramun ne, sannan shi da yake saki shima yasan haramun ne._

_Dan Allah mu guji fadawa halaka saboda wani buri na zuciyar mu, Allah ya mana tsari ya kare mu daga sharrin zuciya_Ameen suma Ameen)

? Jalila na zaune itada Zarah tana kara mata fada aka aiko tazo inji Uncle Sagir.
Kallan Zarah tai tace "Zarah ina zuwa."
Zarah tace " Ba sai kin dawo ba dan na san ba ganinki zanyi yanzu ba."

Jalila ta kalleta tace " har kin dago?"
Zarah ta harareta tace " yanda kike nunawa ta ya ya zan kasa ganewa? Ba ni ba na tabbatar yawancin mutane sun sani."

? Jalila ta matso tace "da gaske? Ina nunawa a fili?"
Zarah tai dariya tace gashi nan kin rubuta a goshinki da jan biro."

Jalila ta dan daket tace "bansan iskanci."
Zarah tace "daga ke har shi ai kun gama sanar ma mutane dan ni a bakin mutane ma na fara ji."

Jalila ta dan shagwabe fuska tace " kice kowa kallona kawai yakeyi?"

Zarah tace "ah to mu ai yan kallo ne."

Jalila ta rufe fuskarta tace "bari in rufe fuska ta inje a haka."
Zarah tai dariya tana cewa " u are so Naive."

Jalila tana ta wani nuku nuku a haka har ta fita dan dama jiya ma a waje suka hadu gaban makarantarsu kadan, wani dan lungu.

Sai data dan laleka kafin ta gangara wai ita a dole batasan a ganta.

? Sagir na kallanta yana murmushi har ta karaso, yace " me kike ta lekawa?"
Tace "Uncle ya zamuyi? Duk fa ansan menene tsakanin mu."

Yace "to sai akai ya?"
Tace "qx
Yace "nace sai akai ya?"
Tace "hmm hmm"
Murmushi yai yace " kin manta kin gama skul? Sannan ba yaudara ko wasa muke ba balle muce bamasan a sani, ya zakiyi in sukazo auranmu? Ko gidan mu?"

? Idanu ta zaro sai kuma ta rufe idanta da sauri, yace "oh? ni wai sai yaushe ne za'a daina min kunyar nan?"
Sauke hannu tai tace "ni in kai wata maganar ne sai naji kunya ta kamani."
Yace "to da alama zan tattara maganganun dake cina sai munyi aure."

Murmushi tai, sun dade tare kafin tace zata tafi, dan yau ita kadai za'azo dauka tunda Safeena tana gidan kanin Inner tun last week tacan take zuwa makaranta.


? ********

? Abba ne ya kalli Ummy yace " ya kamata yau na sanar ma Hassan abinda ke faruwa."

Ummy tace " ni kam tsoro nake kar abin nashi ya dawo."

Abba yace " sai yaushe ne zaki bari a fadamai? Tun wancan satin kike sani nake jan lokaci ko so kike sai abin ya zo zai sani?"
Tace"shikenan ka fadamai yau."
Abba ya mike yai sama...........

#ONELUV=ؕ?
[07/10, 21:30] * +234 803 222 1758, : =??? *JALILAH* =???

Written By : *AYUSHER MUHD*
Wattpad: *Ayusher Muhd*


*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*

(_D home of expert and perfect writer's_=ء?)

*NO 12*


? Hassan na sa kaya yaji Abba na knocking, da sauri ya karasa sa rigarsa sannan ya murda makullin ya bude dakin.
Abba ya matsawa ya shiga cikin dakin, kallan dakin Abba ya shiga yi yana jinjina kai, gashi dau duk lalurar dake damun Hassan amma bazaka taba ganin dakinsa da datti ba, yadan murmusa dan tabbas bai manta lokacin yana yaro ba kafin abin nan ya sameshi Hassan mutum ne mai tsafta da tsantsani, sai dai dakin bai musu karami ba? Ko sagir zai maida kasa? Dan dama saboda Hassan ne ya dawo nan kusa da dakinsa.

? Ganin Abba na ta dubs dube yasa hassan ya koma kan sofa ya zauna.
Abba ya kalleshi sannan ya koma kusa dashi shima ya zauna.,
Matsawa kadan Hassan yai dan Abba ya zauna daf dashi.
Abba yai murmushi yace " Hassan yada matsawa?"
Bai tanka ba dan dama Abban yasan ba tankawar zaiyi ba.

? Sunyi shiru sai karar fanka dake kadawa a cikin dakin, sai sanyin A.C, Abba ya rasa ta ina zai fara, can ya daure ya maida hankalinsa kan Hassan yace "Hassan!"
Kallansa yadanyi baice komai ba.
Sai daya dan kara yin shiru kafin yace "Hassan ke kake tunani game da aure?"

? "Aure? Aure kamar ya?"
Abba yace "baka tunanin aure?"

? Cikin rashin fahimta yace "ban fahimci aure ga mara lafiya?"
Abba ya danyi shiru kafin yace " Hassan mubar zancen lafiya da rashinsa, kafi kowa sanin halin da mahaifiyarka take ciki a kanka, ka kuma san yanda tasha wahala akan rashin dan uwan............"

? Kallan sa Hassan yai idanunsa har sun kada, bakinsa ne ya fara rawa, hannunsa ya sa a wuyansa yana dan kakari, cikin lokaci kankani Hassan ya rikede, hankalin Abba ya tashi sosai rungumeshi kawai yai dan ya rasa ma mai zai mai.

? Da kyar numfashinsa ya daidaita sai dai zufa da ta keto masa, Abba jikinsa ya kara yin sanyi tsananin tausayi dan nasa ya kara kamashi.

? Ya dade sosai kafin ya dawo daidai, Abba ya mike zai fita, Har yakai kofa Hassan yace "Wani abu ya samu Ummy ne?"

? Abba ya juyo daga inda yake a tsaye cikin raraunar murya yace " Hassan in har ka damu da halin da muke ciki ka amince ka auri yarinyar da mukesanka da ita."

Mamaki me ya kara kamashi yace" tambayar abinda ya samu Ummy......."
Yanzu Abba ya canza muryarsa daga alamar tausasawa zuwa dan bacin rai, yace " akwai wani abu dake damunta ne a duniya daya wuce matsalar da kake ciki? In har kanasan hankalinta da nawa ya kwanta ka yarda da auren da muke kokarin yi maka."

? Hassan shima cikin dan zafi abinda rabon da yai magana mai tsayi haka harya manta yace " Taya zaku nemi min aure bayan kunsan halin da nake ciki? Sannan ni a rayuwata kunfi kowa sanin banasan zama inba ni kadai ba, ya zakuyi kuyi tunanin hadani da wata? Bayan kunsan daga ita har ni hakkin mu zaku shiga?"

? Abba ya dan matso yace "wannan halin da kake ciki shine yasa muke tunanin ma auren kota wani hali, halin zama kai kadai, halin kin fadar in baka da lafiya, halin nunkufarci da rashin fadar matsalar ka, halin kin yima kowa magana, halin rashin kula da kanka, wannan kadan ne daga cikin dalilan dayasa mukesan ma aure."

? Hassan har zaiyi magana yaji kansa yayi gingirin gim dan gaba daya dama baya iya magana mai tsayi, mikewa yai ya shige cikin toilet ya rufo kofar.

? Abba ya juya ya fita, Ummy na tsaye a falo a kasa sai zagaye takeyi tana ganinsa ta matso tace ya kukai?
Yace "kema kinsan bazai yarda ba daga bugu daya ba."
Tace haka ne, yace "ke zaki mai magana gobe, dan inyaga kin damu kema kinsan zai yarda."
Tace "amfani dani da tsauyi da kaunar da yakemin zamuyi?"
Abba yace "ba haka nake nufina, hakan dai shi kadai ne haya."
Shiru tai batace komai ba.



? Jalila kuwa tana zaune kusa da goggo suna dan cin abinci duk ta dameta da labarin film din India data kalla mai suna Vivah tana ta fada mata yanda saurayin ciki da budurwar ke san juna can tace "Goggo kinsan abin mamaki? Matarfa ranar auransu ta kone a jikinta amma saurayin nan dan tsabar san da yake mata ya nuna shi wannan ba komai bane, Goggo a asibitin fa ya aureta......"

? Goggo tace " nikan Jalila sai yaushe ne zaki kyalemu muci abinci shiru? Bafa asan mutum na cin abinci na magana, sannan ni na rasa me yasa baki da aiki sai zancen soyayya, wani irin so kikema Sagir din nan dayasa kika koma haka?"

? Jalila tai dariya tace "Goggo karki damu yanzu tunda muka gama makaranta zaki ganshi tunda kinga gobe za'ai taron yaye mu,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login