Showing 111001 words to 114000 words out of 149705 words

Chapter 38 - Jalilah Book One Complete Hausa.doc

Ayusher   

28 Oct 2025

627

mata a ba zata, sannan bata taba tunanin zai mata irinta ba.

? Kallan kofar tai wacce ya rufota, saukowa kasa yai Ummy na kokarin yimai magana taga ya fita da sauri, ina zaije da magrib din nan?

? Jalila kam tafi minti goma sha biyar a tsaye ta kasa motsawa daga gun, kafin haushin kanta ya kamata. Me yasa batace mai komai ba? To me zatace? Da munyi soyayya amma aka kwaceni daga gunshi akamin auran dole?

? To me zata ce? Hanyar kofa ta nufa da sauri ta fito daga dakin, saukowa kasa tai da sauri, sai dai baya kasa.

Fitowa waje tai nan ma bataga motarsa ba, jiki a sanyaye ta kalli inda yake ajiye mota, sannan ta juyo ciki.

Ameera ce wace ke rike da cup da spoon tana juya cornflakes din data hado ta kalleta tace "Matar Yaya daga ina?"

? Jalila ta kalleta tare da yimata yake kawai ta nemi hanyar sama, Ummy ce tace "Jalila?"

Juyowa tai ta kalli Ummy wace itama take fitowa daga kitchen tace "ashe Mahaifinki ya tafi?ai bansani ba."

Jalila tace "nima bansan ya tafiba Ummy."

Kallan mamaki ta mata "wani abun ya faru ne? Naga Hassan ma ya fita."

Jalila tace "bakomai Ummy."

Ummy ta kalli Ameera tace "in zakici abu ki zauna banasan cin abincin nan naki a tsaye."

Ameera ta koma ta zauna, Jalila kuwa tahau sama.

? Ummy ta bita da kallo tare da fatan Allah yasa ba wani abun bane.

Jalila kuwa tana komawa ta zauna a falo tana jiransa, ganin ta kasa zaman yasa ta dauko wayarta ta sauko da sauri, dakin Ameera ta shiga.

Ameera wacce shigowarta kenan tana kokarin yin alwala ta kalleta tace "Yaya Jalila lafiya?"

Jalila ta matso ta dau wayar Ameera ta mika mata, Ameera cikin mamaki take kallanta, Jalila tace dan kira Yayanki.

Cikin mamaki Ameera tace "ni? In kirashi ince mai me?"

? Jalila tace "ki dai ki kirashi."
Ameera ta amsa tana cewa "yaji yayi ne?"

? Jalila tace "abinda yafi yaji ne. Tunda kin taba gani namiji da gidansa yayi yaji."

Ameera tai dariya tana dialing tace "kece dai baki taba gani ba amma yanzu maza ma yi suke."
Jalila ta harareta tace "wallahi Ameera nikam kina ban mamaki, bansan a ina kika san komai haka ba, yarinya kafin ki tafasa kina neman konewa."

? Ameera tai dariya tace "nasan komai wlh, pratical ne......."
Jin alamun kamar an dauka yasa tai gum tare da cewa "hello!" Ta fada tana kallan Jalila.

Jin ba magana yasa ta kalleta, sannan ta kalli wayar.

Cikin mamaki tace "banaji."

Jalila tai shiru kafin ta amshi wayar tasa a kunnenta, tace "Hello!"
Tana magana aka kashe wayar, kallan Ameera tai ta amshi wayar ta sa number ta juya ta fita.

Ameera na san magana amma ba dama, saboda ta fahimci sabani suka dan samu.
Jalila na fitowa ta koma sama ta zauna a bakin gado rike da waya a hannu.

Ta zarfafa cikin tunani taji wayarta na kara, da sauri ta dauka ko kallan mai number batai ba tai sallama.

Goggo tace "Jalila!"

Cikin mamaki ta kalli number sannan tace "Goggo? Number wanene?"

Goggo tace "tawa ce, yanzun nan aka aikon da ita."

Tace "wane?"
Tace "ai ke zan tambaya,tunda haka akacemin gashi daga Jalilah, na dauka ma number ce baki sani ba."

Jalila tace "bansani ba wlh,amma nasan bai wuce inji Ummy."

Tace "kila to, ya gidan naku?"
Tace "lafiya kalau inatasan nima nazo."

Goggo tace "a'a banasan yawon zuwan nan ba dadi, ke dai ki zauna a gidanki cikin iyalanki, ni muna zaune da Lantana lafiya anan, komai muna dashi, a koda yaushe sai dai in muku addu'a dake da mutanen nan na arziki."

? Jalila tai murmushi sanda ta tuno Hassan a ranta tace Goggo ina cikin wani hali.

Amma a fili tace "to Goggona."


Nan sukai yar fira kadan kafin suyi sallama, Kara kallan wayar tai tana tunani, idanunta ta rufe sannan ta mike tai alwalar magrib tai sallah ta kara dauko wayarta, yanzu kam kiranshi tai sai dai bai dauka ba harta katse.

? Shi kuwa Hassan tunda ya fita yake tafiya a mota, yayi tafiya mai tsawo kafin ya ja gefen titi yai parking? Kansa ya kwantar akan kujera ya rufe idanunsa, da wani irin zama zasuyi? Ya tabbatar akan wata alaka a tsakaninsu mai karfi, yanda ta razana, idanunta ta ya tuno da yanayin da ta shiga a lokacin, kenan har yanzu tanasan Sageer?


Idanunsa ya runtse cikin wani irin hali, yana ganin kiranta bai dauka ba har ta gaji ta daina.

Ummy daga kasa taga ba Jalila gashi har lokacin cin abincin dare yayi, Ameera ta aiko akan ta kirata, lokacin tana kwance akan sallaya, Ameera ta turo kofa tana lekowa tare dayin sallama a hankali, Jalila ta kalleta tana ganin ita kadaice ta shigo.

Ameera tace "ki sauko muci abinci, yaya fa?"

Jalila tace "nakoshi, sai dai bari sauko na daukomai nashi."

Ameera tace "kinsan sai dana bude kofar na shiga tunanin in yaya na nan fa?"
Hmm kawai Jalilah tace batace komai ba, ta mike suka sauko w AUmmy tace "bai dawo ba?"
Tace "eh Ummy inaji ya tsaya a wani gun ne bari na daukar mai."

Ummy ta dauka su biyun take nufi, shiyasa batace komai ba.

Kitchen ta shiga ta zuba mai sannan ta dau tiren ta fito, tana shigowa falon Sageer da Ameera na fitowa daga daki, da alama kiransa taje yi.

? Gaisheshi kawai tai ta wuce sama tareda yima Ummy sai da safe.

Ta hau sama, abincin kawai ta ajiye tai sallar isha'i sannan ta dauko qur'ani inda ya koya mata jiya ta biya sannan ta dawo farko, ta dade tanayi kafin ta rufe qur'anin tadan kishingida tai akan sallaya, bacci ne ya dauketa.

Sai can wajen karfe 11 ya dawo, yana shiga ya shiga toilet ya fito ya kwanta.

Juyi ya shiga yi, hankalinsa bai kwanta da kwanciyar datai a kasa ba, gashi ba bargo, duk yanda yaso yai bacci ya kasa.

Mikewa kawai yai yadau bargo ya rufa mata ya koma ya kwanta.

Da asuba yana sallah yau ko karatun bai koya mata ba taga ya juya ya kwanta.

Dama tashin ma sai data farka taganshi kawai yana sallah.

Tace "Yaya ba....."
Yanda ya kwanta yasata yin shiru dan bashida alamar sauraranta.
Tama rasa me zatace, haka ta gaji ta kwanta.
Tana tashi taga baya dakin.

Gaba daya hankalinta ya kara tashi, ta fito falo ta zauna idanunta suka ciciko, batasan ta damu da Hassan ba kamar yanzu, gaba daya kin kulatan dayai na kwana dayan nan jitake kamar tayi hauka, me yasa Yaya bazai bari tayi magana ba?

? Shikam gaba daya bayasan yaji wani abu daga gunta, tsoro yake kar tacemai Sageer takeso ba shiba, dan bayaji zuciyarsa zata dauki wannan hukuncin, a yanzu bayaji zai iya rayuwa ba Jalilah, to in itama bazata iya rayuwa ba Sageer bafa? Ko shi yace bazai iya rayuwa ba ita fa? Wannan dalili yasa yake tsoron jin abinda zai fito daga bakinta.

? Wajen karfe 8 ta farka, da sauri ta bude dakin sai dai ba shi ba alamarsa, abincin daren ta kalla, ta bude kulolin, gaba daya ba alamar ma ya bude shi.

? Kawai zama tai a kasa tasa kanta a cikin cinyoyinta, samun kanta kawai da sa kuka, yanzu inyace yabarma Sageer ita fa? Dan ta kula gaba daya ba wanda yake damuwa da ra'ayinta dukansu tunanin junansu kawai sukeyi.

? Haka ta sauko da abincin, tai sa'a Ummy ma sun fita da Abba, tana fitowa Sageer ya sanar da ita, Ummy ta riga hartayi abincin safe, komawa tai sama kawai ta kwanta dan bazata ma iya cin abincin ba, tai wanka tasa atamfa riga da skirt kawai ta murza mai da turare ta kwanta.

? Wayarta na hannunta jefi jefi tana kokarin kiran Hassan.

Sai wajen rana ta sauko tai abinci kawai tasa a kula ta koma sama.
Yauma bai dawo ba sai data kwanta barci, ya dade a tsaye yana kallanta, sannan ya kalli abincinsa data ajiye masa, zuciyarsa na tsoron jin labarin nan, jiyake bazata iya daukan abinda zata ji ba.

? Bargo ya dauka kamar jiya ya luluba mata, sannan ya kashe wutar dakin ya taho kamar zai wuceta sai kuma ya dauko pillow yazo yadagata ya sa mata sannan ya mike zai tashi.

Hannu tasa da sauri dan taji alamunsa ta rikoshi, idanu ta bude da sauri.

Kallanta yai sannan yace "ba bacci kike ba?"

? Tace "bacci nake yanzu na farka."

Hannunta ya dan zare zai mike, da sauri ta kara rikoshi, bai kalleta ba sai dai ba damar tashi.

Cikin sanyin murya tace " Yaya haka zamu zauna? Kafin na farka ka fita sannan kafin ka dawo nayi bacci?"

Kallanta yai kamar zaiyi magana sai ya fasa, tace "Yaya ka tambayeni dan Allah duk wani abu da kake sanji, ni kuma na baka amsa, wannan abin ba shine mafita ba."

Hannunsa ya zare yamike tsaye, Jalila ta mike tsaye da sauri tare da rungumeshi ta baya.

Tsayawa yai sai dai zuciyarsa na harbawa da sauri da sauri, tace "yaya dan Allah."

Kasa daurewa yai kawai ya juyo ya rungumeta tsam ajikinsa, can yace "Jalila zuciyata ta kasa daukar abinda take zargi, na kasa samun nutsuwa, ina tunanin kamar na tauyekine da abinda kikeso....."

Kai ta shiga girgizawa da sauri da sauri, kafin tace " ko kadan Yaya, bazan musa ma akan da ba amma banda yanzu."

? Dagowa yai ya kalleta, yace "Inke hakan ne shi......."
Daga kafarta tai ta kara rungumeshi tace "Yaya......."

Bakinta taji a cikin nashi, wani yanayi ya shiga mata wanda ita kanta batasan sanda ta shiga maidamai ba, jitai kafafuwanta sun kasa daukarta, hannu yasa ya dagata gaba daya ya kaita kan gado, sun dade suna sumbatar juna kafin ya saketa kadan, yana wani irin numfashi yace "Jalilah banaso na zama mai tauye miki hakki........"

A hankali ta lumshe ido hawaye suka taru mata ta sumbaci bakinsa, sannan tace "yaya da ne, shikansa yaya Sageer din ya hakura, sannan duk cikin rashin sani ne, please ka........"

? Kara hade bakinsa yai da nata, yanzu kam ya kasa controlling din kansa, a hankali ya shiga zare mata rigar jikinta.

? Idanunta kawai ta rufe tana tunanin yaushe ta zama haka? Wai ita ke kara mikama namiji kanta?
Kafin ta gama lissafi ya gama zare kayan jikinta a hankali ya kara maida bakinsa cikin nata..........

(Ban kula ba najini a kasa timmmm wai ashe dadin soyayya ne yasa Hassan ya hankadoni waje da kafarsa sai ji nai ansa lock a kofar.


? Nace hmm asha love kafiya)



#OneLuv=ؕ?
[12/7, 10:12 PM] El-hajj: =??? *JALILAH* =???


Written By : *AYUSHER MUHD*
Wattpad: *Ayusher Muhd*


*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*


? (_D home of expert and perfect writer's_=ء?)


? _Ga kyautar shafi kyauta gareku 'yan Zauren Biebie, Word of Hausa Novel, Haske Fans, Kundin Haske, Pherty Novel godiya gareku mai dumbin yawa >?p?Luv u=ؕ?



? *62*


Dagota yai ya kara rungumeta a jikinshi wani sanyi na ratsashi, kanta nakan kirjinsa idanunta a lumshe suke, a hankali yace "Jalilah!"

? Cikin sanyin murya tace "Naam"
Yace "Nagode kwaraia da gaske da kika shigo rayuwata, a koda yaushe yanzu ina godema Allah daya kawomin ke, kin canzamin komai na rayuwata wanda ban taba tunanin zai canzu ba."

? Kanta tadan gyara sannan tace "Yaya kaine kake tunanin nice na canzaka amma a zahirin gaskiya ba haka bane." Yace "menene to."

? Ta dago ta kalleshi sannan ta nunashi da yatsa tace "kaine ka canza kanka da kanka, ni dai na taimaka maka ne."

? Jitai ya sumbaci bakinta, da sauri tasa kanta akan kafadarsa saboda kunya, yace "ya zafin gun? Ya ragu?"

? Bata kalleshi ba tace "kadan."

Yace "ansha raki."
Cikin shagwaba tace "haka ne raki? Wallahi nayi dauriya......"

"Wayyo yaya......."
hannu tasa da sauri ta toshe mai baku dan ta fahimci abinda tai dazu yakesan ya maimaita, kallanta yai yana dariya.

Ta saki bakin nasa tace "yaya nidai ka daina."
Yace "zan daina amma mai za'a bani?"
Tace "me za'a baka kamar ya?"

"Yanzu bakisan ba'a aikin banza ba? Indai kinaso na daina sai......." ya nuna kuncinsa wai saita sumbata.

Tace "ni fa kunya nakeji."
Yace "ansha kunyar karya, dazu wanene ya fara rungume......."
Da sauri ta sumbaci kuncin nasa dan tasan yanzu zai fara.

Tana sumbata ta kule cikin jikinsa, yace "da alama dai wannan jikin ana sanshi dayawa, naga kamar baza'a iya sakeshi ba."

Sa hannu tai ta dan ture jikin nasa, ya jawota ya maida ita yana dariya, tace "wlh yaya kaima...."

Yace "zaki iya tashi kiyi wanka ko ni na zo muyi tare?"
Da sauri ta kalleshi tace "muyi tare? A'a zan iya."

Ya kalleta yace "fara to dan na tabbatar zaki iya."

? Kallansa tai sannan ta fara neman mikewa, guntae dariyarsa yai dayaga yanda take dan dingisawa, sai data kusa zuwa toilet sannan ta juyo, ya mata alama da ya taso? Da sauri ta girgiza kai alamar a'a
Ta shige tare da rufe kofa.

? Wanka tai da ruwan zafi sannan tai wankan tsari ta fito.
Yana ganin ta fito ya taso yazo kusa da ita, tambayarta yai ya jikin? Batace komai ba sai shagwabe fuska datai, kallan kan gadon tai har ya canza bedsheets din, dan dama Hassan bashida wannan girman kan, ko sanda bashida lafiya.

Hannunta ya rike tace "zan iya fa."
Ya saketa sannan ya shiga toilet shima, sai daya fito ya kalleta tana kan kujera a zaune, yau ma towel dinshi a kasa ya daura, yau kam sai taga ta rage kunyar kallansa, sannan ko ita datai wanka towel ta fito dashi sai dai ta yafa wani a samanta.

? Kallanta yai yaga tana kallansa yace "ya ya? Yanzun ma so ake akwanta?"
Yanda yai maganar ta gane me yake nufi da sauri ta dauke idanunta, sai daya sa riga jalabiya sannan ya matso yace "let's pray."
Tace "nayi isha'i ai."
Yace "na godiya ga Allah."
Bata musa ba ta mike da kyar, hannunsa ya miko mata ta rikeshi suka karasa, sallah sukai raka'a biyu, ya danyi addu'oi sannan ya kalleta, mikewa yai kawai yazo kusa da ita, tana neman yimai magana sai jitai ya dagata, kan gado ya ajiyeta sannan ya zubo musu abinci a plate, yasa spoon daya.

? Kusa da ita yazo ya zauna ya fara ci, kallansa tai tace "yaya nimafa yunwa nakeji."
Yace "au ai ma dauka ke bakyajin yunwa."

Hade fuska tadanyi, ganitai ya debo a cokali ya miko mata, baki tadan turo tana neman yin magana.
Sumbatar bakinta yai ta kalleshi da sauri, yace "bude"
Bakin ta bude tana kallansa, haka ya dinga ci yana bata, bayan sun gama ne ya zauna kusa da ita tare da kwantar da ita kan kafadarsa, ya rufe musu kafa da bargo sannan ya sa hannunsa cikin naga, shiru sukai na wasu mintina kafin taji yace " bacci?"

Tace "a'a kawai tunanin rayuwa nakeyi."

Shiru sukadanyi kafin yace "mene daga ciki kike tunani?"
"Hmmm yanda kawai rayuwa ta juyamin."

Ya dan kwantar da kansa a saman nata yace "yaushe kika san Sageer kanina ne?"

? Ta dago ta kalleshi tace " sanda yazo gidanmu kawo sako."
Yace "ya kukai?"

Tace "kawai fa kasan me? Na fito inata yan kunkunina wai ina zuwa falo naga Uncle? Mamaki ya kamani, shima yana ganina..........."
Yanda Hassan ke kallanta ne yasa tai shiru, sannan tai dariya tace "bacci nakeji."
Da sauri ta kwanta ta lulube kanta da bargo.


Shiru yai kafin yace Sageer am really sorry.

Ya dade a zaune hartai bacci kafin shima ya kalli agoggo karfe 2 saura, yaye bargon yai yana kallanta tanata baccinta kafin ya sunkuyo ya sumbaci goshinta, sannan ya kwanta ya jawota jikinsa.

? Yau kam zai iya cewa bai tabayin bacci mai dadi kamar nayau ba, dan sallar asuba ma makara sukai.
Sai karfe bakwai na safe ta farka, tana kwance a daga gefe da alama garin dadin bacci ne har ta matsa daga kusa dashi, juyowa tai ta kalleshi, batasan sanda murmushi ya bayyana a fuskarta ba, juyowa tai ta kalli agoggo, karfe bakwai? Badai yaya ganin tanata bacci bane yasa bai tashe ta ba?

Mikewa tai sam ta manta da jikinta, tana mikewa da karfi taji azaba, da sauri ta koma ta zauna, sannan ta sauka a hankali, tana bude toilet ya bude idanunsa, yana ganin yanayin gari ya kalli agoggo da sauri.

Istigfari ya hau yi kafin ya mike, tana fitowa ya shiga, mamaki ne ya kamata, yau yaya ne ya makara? Daren jiya ta tuno, kunya ya kamata, da sauri ta shimfida sallaya tana neman tada sallah.

Gani tai har ya fito, ya mata alama data matso nan ta matsa bayansa kadan ya tada sallah sukai, sai daya mata dori sannan suka kwanta, bacci ne ya kwashesu tana kwance akan jikinsa.........


? ************

? Ummy ce ta kalli agoggo karfe 11? Lafiya? Gashi sai ita kadai, yau juma'a Ameera na skul, Sageer da Abba sun fita tare, tana san ta dubasu amma tana ganin rashin dacewar hakan, a zaune take tsuru ta zubama sama ido tana addu'a akan Allah yasa lafiya, taji wayarta na kara.

Jawota tai tare da dagawa tace "Aunty Nana in kwana?"

"Wato tunda Ameera ta dawo bakida niyyar kira ko?"

Ummy tace "kiyi hakuri wlh inata san kira abubuwane duk suka chabe min."
"Hmm akwai abinda zai chabe miki banda damuwar yaran can, gaba daya komai na rayuwarki kin dorashi akansa, sam bama kya damuwa da wanda ya dace ki damu dashi."

Tace "zaki fara ko? Wai meyasa kike haka ne? Da Sageer da Hassan ai duk 'ya'yanane kuma 'ya'yanki?? me yasa kike haka ne?"
Aunty Nana tace " hmm haka zaki bar Sageer din ba aure?"

"Wai yaushe ma Sageer ya girma ne? Duka duka yaushe ya gama service? A bari ya zauna mana?"

Aunty Nana cikin dan zafi tace "sai ki bari inya taufa sai kimai....."

"Allah ya baki hakuri, ni narasa me yasa kike haka wlh."

Aunty Nana tai karamin tsaki, Ummy tace " Ina Hajiya Aina'u ta gujemu."

"Aina'u nanan, dazun nan ma taje skul dubo result."

Ummy tace "to Allah ya taimak ya kuma bada sa'a."

? Tace "Ameen."
Sun danyi hira kadan kafin suyi sallama.


*********

A sama kuwa sai karfe 11 da rabi Jalila ta bude ido, tsananin mamaki yasa ta kara murza idanunta tare da kallan agoggo.
Inda Hassan ke kwance ta kalla, a zaune ta ganshi rike da littafi, cikin mamaki tace "yaya ya zaka barni nai ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login