Showing 33001 words to 36000 words out of 149705 words

Chapter 12 - Jalilah Book One Complete Hausa.doc

Ayusher   

28 Oct 2025

610

kusa da Goggo ta rike hannunnta idanunta suna neman canzawa tace "Goggo sai na dawo."

Goggo ta jinjina kai tace "ki bari sai gobe ko jibi."
Tace to.

Haka suka fito ta shiga mota.

Suna fara tafiya ta kalli Sultan tace "Sultan wani abin ya faru ne?"
Yace "ban sani ba sai dai na tabbatar an kusa auranki tunda yanzu ma gidan da mutane, sannan naji Mumy na cewa an turo wai yau kanin Ango zaizo dan kuyi magana, tun jiya yaso zuwa to sai sukai tafiya, bandai san maganar da zakuyi ba."

? Gaban Jalila ne ya shiga faduwa, a hankali hawaye suka fara zubo mata, kanin ango? Zancen me? Ankusa bikinta? Da wa? Wad'an nan sune suka sake ingizata ta shiga zubar da hawaye.





#Oneluv=ؕ?
[08/10, 02:12] * +234 803 222 1758, : =??? *JALILAH* =???

Written By : *AYUSHER MUHD*
Wattpad: *Ayusher Muhd*


*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*

? (_D home of expert and perfect writer's_=ء?)

*No 20*


?? Suna isa gidan ta fara gaida bakin dake gidan, duk yan uwan Mumy ne dan dama a iya tsayin rayuwarta bata taba ganin dangin mahaifiyarta ba, dan duk yawansu ba mai nemansu, sannan shima Dadyn baya kuma san su nemeshin.
Shikuwa danginsa dama Mahaifinsa ya dade da rasuwa, sai mahaifiyarsa wacce dama ita kam bata san auransa da Goggo sai Mumy, takanzo lokaci zuwa lokaci, abinda zai baka mamaki shine, ita kadai take zuwa sai kanwarsa wacce dama ita fitsarariyace.
Ko sau d'aya Mahaifiyarsa bata taba cewa Innan Goggo tazo suje muhalin yarta ba, Jalila na shekara 10 Allah ya d'auki ran mahaifiyar Dadyn.
Shikadai yaje, dan sai daya dawo daga gaisuwa ya aiko mata da tsintsiya, kuka da gyada wai inji babarta sannan tasan yaje, sai Jalila data jiyo gun Safeena akan mahaifiyar Dady ta rasu.

? Kaf gidan yan uwan Mumy ne, sai ita kanwar Dadyn ita kadai.
Abin mamaki shine taya akai tasan ana taro? Kuma me yasa itama in zata zo sai dai ta taho ita kadai? Kana ganin hakan kasan Dady ne ke sanar da ita.

Jalila itakam gaishesu kawai takeyi, tana gamawa ta mike zatai gun Mumy wacce ta leko tana mata alama da hannu akan tazo.

Jalila ta mike zata wuce taji an tawo mata hijab saura kadan ta fadi, kallanta tai zatai magana sai kuma ta fasa tace "Aunty?"
Kanwar Dady wato Aunty Adama tace "Ke dama bakida tarbiya, in ba haka ba ki gaida kowa baki ko kalleni ba?"
Jalila ta tsuguna tace "Aunty kema kinsan ban ganki bane."
Tace "eh ni da nake a kauye ai bazaki ganni ba, tunda kaf falon nan akaina idan naki ya makance."
Jalila zatai magana, Mumy tace "Jalila!"

Kallan Mumy tai sannan ta amsa, ta kalli Adama kafin tai magana ma tace "tashi kije ana kiranki."
Jalila ta mike ta wuce.
Tana shiga d'akin Mumy ta rufe kofa sannan ta riko hannunta.
Gefen gado ta zaunar da ita ta rike hannunta duka biyun tace "Jalila? Kinji abu kwatsam ko?"
Jalila ta kalleta idanunta sun canza kala tace "Mumy ban fahimci abinda ke faruwa ba."
Mumy ta rungumeta cikin murya mai rauni tace "Jalila nikaina abin nan na rasa ta ina zan fara sanar miki, dangin mijin ne suka ce suna san auran cikin gaggawa, yanzu nan da kwana uku za'a........."
Yanda ta ture Mumyn daga jikinta ne yasa Mumyn yin shiru, Jalila bakinta na rawa tace "kwana uku?"
Mumy tace "kiyi hakuri Jalila, sadaukarwa ce kikayi don ceto mahaifiyarki, kinfi kowa sanin Inna inhar bakiyi abinda tace ba, tabbas zata daina biya ma Goggo kudin asibiti ne, sannan zata iya korarku daga gidan nan, kinsan dai ba lafiya ne da ita ba, kar kuje garin wahala ciwon ya cita har azo ana dana sani...."

? Wasu zafaffan hawaye ne suka zuboma Jalila, ta kara maimaitawa kwana uku?
Mumy tace " karki damu, mahaifinki ya yanke hukunci inhar akai auran kikaga ana cutar dake to ki sanar dashi shidakansa zai sa a raba auran."
? Wayyo yarinta da rashin tunani mai zurfi yasa Jalila tace "Haka yace ?"

Mumy tace "sosai, kina tunanin zai bari a cutar dake ne?"
Shiru tai tana kallan Mumy, Mumy ta mike ta bude drawer ta d'auko mata wani dankararen material mai duwatsu, tace " ki tashi ki shirya, kaninsa zaizo yanzu, insha Allah Jalila ba abinda zai faru dake, kidinga sa mahaifiyarki agaban komai."

? Jalila bakinta ma rawa tama kasa magana, Mumy ta mikar da ita tace "kiyi hakuri ki saka Jalila, dan tundazu akace ya taho."

Haka ta hau saka kaya tana kuka, tana gamawa Mumy ta mata kwalliya da kanta, ta fesa mata turare sannan ta d'aura mata d'ankwali.

Jalila tana zaune agaban madubi akai knocking, mai aikinsu ce tace mata wai yana falon baki.
Mumy ta kalleta tace "Jalila!"
Kallanta tai sannan tace "Mumy?"
Mumy ta kara rungumeta tace "Jalila ki yafemin wahalar da na baki a da, ni kaina ina dana sanin yin hakan, kishi ne yasani yin komai."

? Da yake yarinyace mai kishiriwar nuna mata kulawa, jitai gaba daya jikinta yayi sanyi balle dataga Mumy na matse kwalla.
Haka Jalila ta fito daga d'akin fa nufi falon bakin.


********

? Sagir na zaune yana waya da Abba, yace "Abba nifa kasan bansan me ake cewa ba?"
Abba yace "kai dai Sagir sai a hankali, to inkungaisa sai kai introducing din kanka, inkundan yi hira kadan sai ka bata kudin kace na kwalliya ne da wasu hidindimo, dama ai laifinkune da baku bata ba da wuri, sannan laifin yayanka ne da bashida aboki ko d'aya a duniyar nan."

Sagir yai murmushi yace "Abba bye na fara jiyo kamshin Amaryar mu."
Dariya sukai a tare ya juyo yana cewa "Abba sai.........."
Kallan da yake mata ne yasa ya kasa karasawa, Abba ya kashe waya yana murmushi.
A hankali ta shigo falon kanta a kasa, kusa dashi taje ta ajiye tiren dake hannunta.
Sannan ta dago dan gaidashi.

Sagir cikin mamaki yace "Jalila?"
Da sauri ta karasa dago da fuskarta tace "Uncle?"
Kallan juna sukai kawai sai sukai dariya a tare, yace "Jalila ta!"
Kanta ta sunkuyar sannan ta kalleshi tana murmushi tace "Uncle kaine dama? Ya akai kasan gidanmu?"

Yace "woah da alama we are made for each other, kinsan ban taba tunanin ganinki ba?"
? Samun kanta tai da zama a kasan gun, fuskarta dauke da tsantsar farinciki tace "Uncle ni kaina nayi mamakin ganinka."

Yace "wai ina kika shiga ne? Ko fishin ne yasa aka kashemin waya?"

Tace "Uncle wata matsala ce ta hanani magana dakai."
Shiru yai yana kallanta, yanayin fuskarsa ne ya canza, ido ya kura mata wanda haryasata tsarguwa, tace " ka ganni kamar bani ba ko?"
Idanunsa na kanta sai yanayin fuskarsa dake kara canzawa, a hankali yace "Jalila nan ina ne?"
Tace "Gidanmu ne mana."

Wani mugun faduwa gabansa yai ya kara kallanta, itama yanzu jikinta yayi wani irin sanyi a hankali tace "bakasani ba?"
Bakinsa na rawa yace " ina Amar Amaryar?"

Jalila gabanta ne yai wani faduwa hannu tasa tadan tura jikinta tai baya kadan sannan ta kalleshi idanunta sun ciciko.

Sagir ya fara girgiza kai yana cewa "U are not the one ko? Na tabbatar ba ke bace ba ko?"

Hawaye ne suka fara zubo mata, idanunta na kansa, gaba d'aya jiyai wani irin zufa na keto mai yace "will you please tell me?"
Jalila ta runtse ido wasu hawaye suka zubo mata tace "Uncle i am sorry."

Sauko wa yai ya zauna a kasa sannan ya sa hannayensa ya shafi fuskarsa, kallanta yai cikin wani yanayi mai wuyar fassarawa yace "Jalila kinsan waye Angon?"

Kai ta girgiza tana hawaye tace "bansashi ba kuma bana sha'awar saninsa Uncle, kai nake so kai kadai nakeso Uncle na rasa yanda zanyi, rayuwar........."
Tana kokarin sanar dashi rayuwar Goggonta, sai jitai yace "Yayana ne fa."

A firgice ta bude idanunta, tace "me kace?"
Idanunsa ya rufe sannan ya bude yace "Jalila he is my brother."

Mikewa tai tana kallansa tace "brother? Ha kana nufin yayanka ne gidanku d'aya? Kenan zuwanka gidan nan a matsayin kaninsa kazo?"

Sagir ya rufe idanunsa cikin takaicin abinda ke faruwa?
Meke faruwa?
Yau me takeji haka?

Mikewa tai da sauri zata fita.

Jitai yace "He is someone whom i love alot."
Tsayawa tai cak ba tare da ta juyo ba, idanunsa ne suka zubo da wasu kwalla yace "He is someone whom I respect alot."

Yacigaba "He is someone whom I can't compare to anyone, i can sacrifice everything for his happiness."

Jalila ta juyo da sauri tace "me kake so kace?"
Idanu ya rufe wasu hawaye suka zubomai yace "Jalila bazan iya fad'a miko komai ba ayanzu, sai dai a hankali zaki fahimci abinda nake nufi ba sai dai bazan taba zama dalilin da zai zama silar bakincikin zuri'ar mu ba."

Kallan mamaki Jalila takemai, sai hawaye dake ta gudu a idanunta tace " Kana san kaima kace inyi hakuri da auran kenan?"

Sagir ya taso a hankali yazo inda take, kallanta ya shiga yi hakan yasa ta rufe idanunta tana hawaye.

Jin batajin motsinsa ne yasa ta bude idanunta a hankali, me zata gani? Sagir ta gani gwiwowinsa a kasa.

Da sauri ta ja baya tace "Uncle me kenan?"

Sagir yace "That is how much he means to me."

Jalila kallan tsoro ta fara mai, tama kasa magana sam, sai kai da take girgizawa a ranta tana cewa "banda kai Uncle, Please banda kai, ko kowa zai fada Please banda kai, Please ku tasheni daga baccin da nakeyi."

Sagir a ransa yana hango abinda zai faru inhar ya nemi bin zuciyarsa, yanzu ma da ya ya yayan nasa ya yarda? Sannan inya tuno da tashin hankalin da iyayensa ke ciki da abinda Hassan yamai a rayuwa bayaji akwai wani abu a cikin duniyar nan da zai kasa barmai, inya tuno da rashin lafiyarsa kuwa tabbas mace kamar Jalila itace best choice, sai dai kai fa?"

Abinda zuciyarsa ke fadamai kenan, muryar Jalila yaji tace "Uncle have you ever love me?"

Kallanta yai yana murmushin takaici, tace " me yasa kowa baya tunani na? Me yasa kowa yake san tsaramin rayuwata? Me yasa kowa yakesan ya zama nice mai sadaukarwa? Me yasa kowa yakesan yin amfani da ni?"

Tsugunawa tai a gun kawai tasa kuka.

Gana daya ya rasa yanda zaiyi, harcikin zuciyarsa yakejin kukanta.

Baice mata komai ba sai tafasa da tasa zuciyar takeyi.

D'agowa tai ta share hawayenta kawai ta meke zata fita.
Sagir har ya kai hannu zai riko mayafinta sai ya fasa.
Cewa yai "Jalila!"
Kallansa tai sannan tace "zan shiga ciki."
Yace " bamu gama magana ba."
Tace " na fahimci me kakeso kacemin."

Yace "Akwai sakon dana kawo miki."

Cikin mamaki ta kalleshi, tana kallansa ya mike yaje inda yake a zaune dazu ya d'auko wata yar karamai jaka ta kwali sannan ya mika mata.
Hannu tasa ta amsa sannan ta kalleshi, bai saki jakar ba yace "Jalila Please."
Kallansa tai bakinta na rawa tace " zan shiga ciki."
Sakin jakar tai, hakan yasa yai saurin mika mata yace "Yaya yace inkawo miki na hidindimo sannan yace kiyi hakuri bai samu zuwa ba rannan, da kuma yau."
Jalila ta kalleshi kawai dan tama kasa magana.
Juyawa yai da sauri, kallan bayansa tai sannan ta fita.




#OneLuv=ؕ?
[08/10, 02:13] * +234 803 222 1758, : =??? *JALILAH* =???

Written By : *AYUSHER MUHD*
Wattpad: *Ayusher Muhd*


*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*

(_D home of expert and perfect writer's_=ء?)

*No 21*

?? Tana tsaye har ya fita daga falon, jitai kanta yayi wani irin sarawa kawai ta zube agun ta zauna, yanzu kam hawayen ma sun kame, sam ta kasa yinkukan, batasan sanda Mumy ta shigo falon ba.
Sai jinta tai tana cewa "Dubu d'ari da Hamsin!"
Lalai mutanen nan.
Kallanta tai sannan ta kalli kudin hannunta, jakar da Uncle ya mika mata ne, har yaushe Mumy ta shigo ta amshi jakar?
Mikewa tai dakyar sannan ta fita itama ta baya tana layi, Mumy ko ta kanta batai ba ta fita falo, ta haura sama.

Bangarensu ta nufa kawai ta zube a kasa ta kwanta, me ke faruwa da ita? Uncle? Dady? Mumy? Inna? Me yasa kowa yake san tsara mata abinda yaga dama? Me yas ba wanda yake tunanin farincikin ta?"


Wasu zafaffan kwalla ne suka gangaro mata, tana nan azaune sam batasan sanda bacci yai gaba da ita ba.

**********

? Sagir kam tana fita daya shiga mota ya ja ta da gudu, gaba daya ya rasa tunanin me ya kamata yai, ta ina zai fara iya zama gida d'aya da Jalila? Sannan amatsayin matar yayansa?

Wani irin burki yaja, ya gangara gefen titi sannan ya kashe motar.
Kansa ya kifa akan sityarin motar yana tunano kalaman Jalila, idanunsa ya runtse cikin tsananin damuwa, yace a fili "Am sorry, i am really sorry Jalilah."

? Kiran Ummy ne yasa ya d'ago, sannan ya daga wayar, Ummy daga can bangaren tace "My son ya kukai?"
Ya kakaro murmushi yace "komai ya tafi daidai Ummy, sannan na tabbatar yarinyar nan zata kula da Yaya sosai."

Tai dariya cikin jin dadi tace "kai ma ka gano hakan ko?"
Yace "sosai Ummy, she is really kind, innocent and honest, yaya zaiji dadin zama da ita."
Ummy tace "Na gode sosai Sagir, sai mumai fatan amincewa da ita."
Sagir ya daure yace "sosai ma kuwa Ummy."
Tace "Ka taho ne?"
"Ina hanya zan dan tsaya wani gun ne."

Yace "ba matsala, ka gama abinda kakeyi, sai na ganka."


? Nan ta kashe wayar tana murmushin jin dadi.
Aunty Nana ta kalla wacce ke ce mata, wai da gaske a birni take?

Tace "wai ke haryanzu baki yarda ba? Kindauka a kauye take?"
Aunty Nana tace "ba wai haka bane."
"Ko kina tunanin ba mai bawa Hassan yarsa ne ya aura?"

Aunty Nana tace "ni ba haka nake nufi ba, inadai mamaki ne."

Ummy ta kalleta cikin mamaki tace "indai har ke yar uwata kika fadi haka ai banaji akwai wanda zai fadi haka naji haushi."

Ta mike ta fito daga dakin tanajinta tana cewa "ke dai bakya san gaskiya......"

Ummy ta janyo kofar ta fito dan kara duba sama, dan sunce gobe zasuzo jere, ba wani taro zasuyi ba saboda halin da ake ciki, dan sunsan ko sunce zasuyi Hassan bazai taba zuwa ba, aure kawai za'a daura a kawota da daddare.

?? Bangaren ya gyaru sosai, tura kofar Hassan tai dan tasan yana ciki.
Jin kofar a rufe yasa ta dan yi knocking, Hassan ya mike ya bude kofar.

Ummy ce ta kalleshi sannan ta shiga.
Hassan ya maida kofar ya rufe sannan ya tako ya zauna abakin gado.
Kallan d'akin tai tace "Hassan baka tunanin ya kamata mu canza gado?"

Kallanta yai baice komai ba, tacigaba " wannan sofar ma ta tsufa ya kamata mu sa wani, sannan carpet din nan shima ya kamata mu canza shi, Hassan mai kake gani?"

Hassan bai kalleta ba yace "Ummy Please ki bari."
Tace "me? Bakaso a canza?"
Yace "na rasa me yasa kike zumudin auran nan, Ummy bakya tsoron abinda zaije ya dawo?"

Kallansa tai cikin mamaki tace "me kake nufi?"

Yace "Ummy kinfi kowa sanin me nake nufi."

Ummy yanayin fuskarta ya canza tace "Hassan please ka dingama kanka fatan alkairi, sannan ka dinga sa salama a cikin zuciyarka."

Kallanta yai kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa, ya rasa me yasa duk basa gane abinda shi yake nufi.

? Ummy tai shiru, jiki a sanyaye ta fita daga d'akin, kallan kofar yai sannan ya runtse idanunsa dan jiya ma sam baiyi bacci sosai ba saboda matsalarsa data tashi, ta ina zai iya zama da mace a haka? Ya tabbatar daga randa ta ganshi cikin wannan halin zata gudu.


*********

? Jalila haka ta kwana a bangarensu ita kadai, abinda zai baka mamaki ba wanda yabi ta kanta sai abi???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?ncin dare da aka kawo mata, sannan taje fita da safe mai gadinsu yace ai ance karta sake fita.
Haka tanaji tana gani ta dawo ciki.

Wanka kawai tai Mumy tazo ta d'auketa sukaje gun salon, a can ne ma ta daure ta tambayeta inda Safeena take.
Nan Mumy tace mata tana gidan kanin Inna har yanzu, bayan alokacin ma tana Abuja gidan babban d'an Alhaji Sanusin wato kanin Inna.

Jalila bata ce komai ba, haka aka fara mata gyaran jiki, Mumy ta barta agun suka tafi gidan Taura yin jere.
Shikam Hassan da sassafe ya garkame dakinsa ya bar musu gidan, Sagir ma yaso gudu sai dai Ummy ce ta hanashi tace "ya kamata ace da namiji agun.

? Haka ya zauna cikin tsananin damuwa, yana bin masu jeren da kallo.

? Sai yamma aka turo aka dauketa, Mumyy ta kama hannunta sukai bangaren Safeena.
Jalila tace "Mumy gun Goggo nake san zuwa."
Mumy tace "kiyi hakuri Jalila sai dai ki je gunta da mijinki, dan umarnin Inna da Dadynki ne."

Tasha kuka ranar sai a lokacin tai dana sanin guduwa da batai ba daga gun salon.

? Haka ta kwana tana kuka, bacci ma sai zarar ta yai.
Abinci kuwa dama turawa kawai takeyi.

Ba wanda ya damu da ita bare ya fahimci ranmar da tai a dan kankanin lokacin nan.

? Yau take asabar, Goggo na zaune akan gado tayi shiru tana tunani, me yasa tun jiya take tunanin Jalila? Ta tabbatar inhar lafiya bazata taba yin kwana uku bata zo ta ganta ba.

Shiru tai ta shiga yin addu'a akan Allah yasa lafiya, sannan Allah yasa Sultan yazo ta tambayeshi.

? Jalila kam yau rufe kofar d'akin Safeena tai dan wani irin zazzabi mai zafi ne ya rufeta sam bata san hayaniya.

? Gudar da taji ne cikin bacci yasa ta bude idanunta a hankali, ba kowa a d'akin sai ita, sai dai daga falo tana jin ana guda.
Mikewa taj da kyar ta sa saitin kunnenta a jikin kufar, duk lab'an bakinta sun bushe.
Jitai wata ta sakeyin gudar, sai jitai ance "dalla malama yi mana shiru, sai wani guda kike kamar auran yar gata, da auran Safeena akeyi sai mu jure jin gudar nan amma kinzo kin cikamana kunne."

? Jalila tai murmushin takaici, har zata juya sai taji ance "Wai ke Fatima kin taba ganin mijin ma kuwa?"
Tanajin muryar Mumy tace "inafa na ganshi?"
Wacce tai magana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login