Showing 138001 words to 141000 words out of 149705 words

Chapter 47 - Jalilah Book One Complete Hausa.doc

Ayusher   

28 Oct 2025

635

da sauri zatai magana ya saki shower gaba daya ta jike, kallansa tai sannan ta kalli hannun daya riketa dashi tace "Yaya?" Ta fada tana kallan hannunsa.

Zata sake magana ya jawota tare da kai bakinshi cikin nata.........



^**********


Ganin magrib ta kawo kai yasa Mumy ta kalli wayarta sannan ta kira Safeena.

Da sauri Safeena ta daga tace "Mumy ina hanyya"

Ahankali Mumy tace "kin dauko takardun?"

Tace "eh Mumy sa'a nai Dady bayanan."

Mumy ta kashe wayar tare da jinginar dakanta jikin kujera.

Matar kawunta ce ta kalleta tace "Fatima ki taimaka kisa abinci abakinki."

Mumy ta girgiza kai alamar a'a sannan tace "karki damu dani, ko nasa abincin ma banaji zan iya taunawa."


#OneLuv=ؕ?=??? *JALILAH* =???


Written By : *AYUSHER MUHD*
Wattpad: *Ayusher Muhd*


*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*

*76*


Safeena na shigowa ta shige daki, Mumy ta mike ta bita.

Hijab dinta ta cire sannan ta mikama Mumy katuwar enveloped din dake boye a hijab dinta, Mumy ta amsa sannan ta bude, kamar yanda Inna ta fada takardar gida ne da kuma fili, sai kuma takardar bankinta wanda ke dauke da kudi da dan dama, sannan sai takardun shares dinta na company dinta.

Kurama takardun ido tai wasu zafaffan hawaye na zubo mata, kuka ne ya kwace mata tanayi tanA cewa Inna ki yafemin...

Safeena ce ta rungumeta Itama tana kuka, sun dade a haka kafin Mumy tace  in anyi uku ma sanar ma Sultan abinda ake ciki.

Safeena tace  ai Mumy inaji ma yasan abinda ke faruwa, nasan dai bai san duka ba amma na tabbatar yasan rabi daga ciki, dan ko tambaya ta dady baiyi ba.

Mumy tai shiru kafin ta share hawayenta tace  Rayuwa ce, nasan mun cuci su Jalila amma ko da wasa banida hakkin mahainfinku, dda zuciya daya nake zaune dashi....

Safeena ta share nata kwallar tace  Mumy dan Allah ki daina kuka hakanan, sannan kisa tawakalli a ranki.

Mumy tai shiru tana kallanta, kafin tace  Safeena ban taba tunanin wannan abin bazai shafeki haka ba, ban taba tunanin kece zaki zama mai lalashina ba.

Safeena tace  Mumy baki san halin dana shiga ba bayan tafiyata, da yanda gaba daya rayuwata ta nemi hargitsewa a lokaci daya, na tabbatar addu arki ce ta kareni, tun a lokacin na shiga hankalina ganin irin abubuwan dake neman faruwa dani.

Mumy ta jawota jikinta tace  Safeena nagode sosai, Allah shine ke shiryar da bawansa na tabbatar da irin tarbiya da nuna komai dole ne ki samu da muka nuna miki shi kikai amfani dashi, da yanzu bansan abinda zai faru ba, Allah mungode ma.

Haka suka kwana cikin wani irin yanayi da su kadai sukasan irinshi, dan Mumy kam bata ko rintsa ba, dan tana matukar san Abakar, ta kuma yarda dashi dari bisa dari...


***********


Yau kwana goma sha hudu kenan da mutuwar Inna, zuwan Jalila uku gidan gaisuwa, a duk sanda zata je kuma sai Hassan ya hada kayan abinci sun kai, sau biyu sukaje da Goggo dayan kuwa ita kadai taje, wanda shine yau ranar bakwai, su Mumy sun shirya dan yau zasu koma can gidan, dan dama itace tadanyi rashin lafiya shiyasa basu koma da wuri ba, jiya tasa Sultan yaje ya ga gidan shida Driver dinsu wanda sun san yanzu suna tattarawa zasu sallameshi, ga gidan da nisa sosai ga kuma jarabawar Sultan ta matso, jarabawar karshe waec, Mumy tai shiru tana tunani, Jalila ta kalli Sultan tace  yakai minti nawa daga can zuwa makarantar taku?

Sultan yace  tab gidan fa a can wajen gaba da gida dubu yake, wasu sababbin gidaje agun.

Cikin mamaki Jalila tace  kai!

Safeena ta kalleta tace  da nisa sosai ko?

Jalila tace  nima bansan gun ba nadai taba wucewa sai dai gaskiya da nisa sosai.

Sultan yai ajiyar zuciya yana cijen lebensa yanda ya saba in ransa ya baci.

Mumy tace  sai dai ka hakura da jarabawar, dan kaga kawunka tafiya zasuyi, dan dama mutuwar goggo ce ta tsayar dasu, ga kuma itama datai rashin lafiya, sannan a yanda suke nuna mana suma yanzu kamar sun gaji da zamanmu ne, kaga ban isa in kara daura musu wani nauyin ba.


Jalila ta kalli Yasmeen dake jikinta a kishingede sannan ta kalli Mumy, tace  ko zai zauna a gidan Goggo?

Gaba daya kallanta sukai, Jalila tai murmushi tace  ban tambayeta ba sai dai nasan Goggo bazata taba hanashi ba, mai zai hana ya zauna a can inyaso sai mu nemarmai keken hawa kawai ya dinga zuwa?

Idanun Mumy ne suka ciciko, tai shiru tana kallan Jalila, Sultan ma kallanta yake kafin yace  Akan me zaki taimakamin Jalila?

Tace  ban gane ba?

Muryarsa ta fara rawa yace  kin manta cin kashin da aka miki a gidan mu? Kin manta wahalar da Mumy, Inna, Dady da wannan Safeenar suka miki? Taya zaki........

Kunnenta ta toshe tace  ya isheni haka nan, oh ni Sultan yaushe ka fara magana haka? Sannan kome ya faru ai dane, sannan ka manta kai wanene a gareni?

Mumy batasan hawaye sun zubo mata ba sai da Safeena ta kamo hannunta, Mumy ta share kwallarta tace  Jalila nagode, ko ince Mun gode, kin nuna mana yanda ake saka sharri da alkairi, butulci da hallaci, mungode.....

Jalila tai murmushi tace  bari na kira Goggo na sanar mata inyaso sai mu fara kaishi kafin kuwuce.

Mumy tace  Jalila dan Allah wata alfarma.

Kallanta tai tace  tame?

Mumy tace  ki taimaka kima mahaifinki magana munaso mu kwashi kayan sawar mu.

Tace  Safeena ta kirashi ta fadamai ko ke mana, ai kayanku ne dole ya baku.

Mumy tai murmushin takaici tace  tun shekaran jiya muke kiranshi bai dauka ba.

Jalila ta mike tare da yin sallama saboda muryar Goggo dataji, tace  Goggona!

Ta fada tare dayin ciki, bayan ta gaisheta ne ta sanar da ita abinda ke faruwa, Goggo ta tausaya musu kafin tace menene a ciki, yazo ya zauna ai duk daya ne.

Jalila tace  Lanta ga?

Goggo tace  dama tare muke kwana da ita, shimfida takeyi a kasa, nace ta hau kan gado mu kwanta taki wai ita tafi san kwanciyar kasa, dama dakin a rufe kawai yake.

Jalila tace  shikenan ma.
Sun danyi hira kadan kafin suyi sallama, harzata fita daga dakin sai ta kira wayar Dady, yana ganin numberta ne ya dauka da sauri yace  Jalila.

Tace  Dady kana ina?

Yace  ba gaisuwa bakomai haba Jalila?

Ta daure tace  Ina wuni?

Yace  lafiya ina gida, ya akai?

Tace  zamuzo dasu Mumy su debi kayansu ne dama shine nake so naji inda kake.

Yai tsaki yace  sabodasu kika kirani? Wai Jalila baki da wayau ne? Kin manta mai mutanen nan suka miki?

Tace  sai munzo, kawai ta kashe, tare da zama akan gado tana rike da wayar.

Mikewa tai sannan tace musu ta fadamai, sannan Goggo ta amince, murna agun Mumy kamar me, Sultan kam shiru kawai yai yana kallanta, duniya kenan.

Text tama Hassan tace  Yayana ka dawo?

Da yake dama ajiye tayai akan zai leka gun Abba ya dawo, ganin reply tai akan saura 2mins ya iso.

Murmushi tai sannan ta kalli Mumy tace  Mumy nima tafiya zamuyi da Yaya.

Cikin mamaki Mumy ta kalleta alamar rashin fahimta, Safeena cikin zumudi tace  ina zaku? Umara?

Jalila tace  a a zamu tafi Qatar ne munyi visa shekaranjiya amma bata fito ba tukunna.

Mumy jiki a sanyaye tace  me zakuje yi?

Tace  karatu zamu.

Sultan yace  haba? Kai congrats, kun samu admission ne?

Tace  wlh a a tukunna, mun dai cike, sai dai dama zamu samu, ko muna can zata fito.

Safeena tai shiru tana kallanta yanzu fa da itace take wannan rayuwar?

Jalila tai murmushi tace  bansan sanda zamu tafi ba, amma daga visa ta fito nasan ba jira.

Mumy ta jinjina kai tace  masha Allah, Allah ya bada sa a, ya karo ci gaba.

Jalila tace  ameen...
Sakon Hassan ne ya shigo,  Baby am back, ko nazo na kinkimoki?

Murmushi tai bayan ta gama karantawa sannan tace  Mumy muje.

Mumy ta mike suma suka mike suka fito, motarsa suka mufa itada Safeena da Yasmeen, Mumy kuma ta shiga motar su itada Sultan.

Tana shiga ta baza tagumi.

Jalila kam tana shiga ya kalleta sam bai kula da Safeena ba yadaiga Yasmeen a hannunta ya wani saki murmushi zaiyi magana tai saurin nunamai baya da idanta, Safeena yaga ta shigo sannan ta gaisheshi, Hassan ya kalleta ya amsa, sannan ya kalli Jalila ya dan matso saboda abin na cinsa yace  kiyi maza nima ki gaifarmin yar baby.

Harararsa tadanyi tace  zaka fara ko?

Gyara zama yai tare da gyaran murya sannan yace  me zan fara?

Jalila tace  Yasmeen ga Uncle.

Yasmeen tace  Uncle ina wuni?

Hassan yadan ja kumatunta yace  Yasmeen ko?

Kai ta daga tana murmushi, ya mika mata hannu yace  nice to meet u.

Hannu ta mikamai dan ta fahimci gaisawa zasuyi, tana dariya.

Hassan ya kalleta yace  yanzu ????      

                  ! " # $ % & ' ( ) * + , - . / 0 1 2 3 4 5 6 7 8 9 : ; < = > ? @ A B C D E F G H I J K L M N O P Q R S T U V W X Y Z [ \ ] ^ _ ` a b c d e f g h i j k l m n o p q r s t u v w x y z { | } ~  ? ina zamuyi Ranki ya dade?

Murmushi tai kafin tace zamu fara zuwa gidan Mumy ne ta debo kaya sai mukai Sultan gidan Goggo mu wuce gida.

Ya kalleta yace  To angama Hajiya.

Dariya tasa tace  Yaya?

Yace  me? Ohhh na manta ashefa ba a zama Hajiyar ba tukunna, to ko mu fara zuwa Hajj ki zama Hajiya kafin mu tafi Qatar din?

Tace  Nayi recording zan fadawa Ummy.

Safeena tai shiru tana kallansu abin sha awa, jitai idanunta na neman tara ruwa, da sauri ta maida idanunta jikin window tana kallan titi.

Yasmeen kuwa sai zolayarta yake tana dariya, Safeena kuwa tundaga gaisuwa bai kara ce mata komai ba, har suka isa gidan.

Dady na falo suka shigo, Jalila ce ta fara shiga rike da Yasmeen.

Mikewa tsaye yai yana kallanta, zaiyi magana yaga Mumy ta shigo itada Safeena.

Komawa yai ya zauna yai shiru, Jalila ta kalli gidan gaba daya ya canza a dan wannan lokacin, shikanshi dadyn duk ya wani canza, Mumy ta zuba mai ido ya kalli Yasmeen datazo gunsa da gudu ta rungumeshi, har a jikinsa sai dayaji yace  Yasmeen ya gida?

Tace  Dady ina kaje? Baka siyomin ice cream ba?

Ya dagata yana murmushi, shigowar Hassan da Sultan ne yasashi sauketa, yana kallan Hassan.

Hassan ya kalleshi sannan yace  Barka dai.

Dady ya hade fuska yace  Barka dai? Wace gaisuwa ce hakan?

Hassan ya kalli Jalila ba tare da ya kara mai magans ba yace  kuyi sauri ina mota.

Ya fada tare da juyawa.

Dady ya bishi da kallan takaici, ba yanda baiyi ba akan Sageer ya barshi ya cigaba da aikinsa amma yaki, ya kuma tabbatar wannam mara mutuncin ne ya hana.

Shiga su Mumy sukai, Safeena gaisheshi kawai tai ta wuce, Sultan kam ko kallanshi baiyi ba ya wuce dakinsa, Dady ya kalleshi dan duk a yaransa yafi san Sultan.

Mumy ta shiga dakinsu, gaba daya dakin yai kacha kacha, Dady ne ya shigo ciki ya kalleta yace  yanzu ina zaku koma?

Tace  ko ina zamu koma ai ba kada ta cewa tunda ka koremu daga gidan da yake halak dinmu.

Dady yace  ku kwashe kayanku duka dan saida gidan zanyi.

Cikin mamaki ta kalleshi tace  siyarwa?

Yace  sosai, ina zan kai katan gida haka?

Haushi ya kamata tace  dan Allah Abakar ka sanar dani menene ribarka na abinda kake aikatawa?

Yai shiru yana kallanta tace  yanzu ka tabbatar min ilimi bai ratsa kaba, sannan ka tabbatarmun kai bagidaje ne, na dauka daka wulakantamu zan ganka kana rayuwa yanda ya kamata, sai dai menene hakan? Kalleka, kalli gidanka? Sannan siyarwa zakai?

Zaiyi magana tace  basai kace komai ba, tunda har mahaifiyata ta mutu baka tako ka min gaisuwa ba, ai a tunani na ko zaman kiyayya mukai dakai kaminn gaisuwar mutuwar mahaifiyata balle, ni ai yanzu ka nunamin tabbas ko da wasa baka taba sona ba.

Ta share kwallarta tana cigaba da kwashe kayanta, zuru yai ya tsaya yana kallanta fitowa tai zata dakin Safeena dan tattara kayan Yasmeen, har ta wuceshi ta tsaya tace  Ahh Sultan zai zauna a gidan Goggo saboda makarantarsa, naga kamar ya kamata ka sani.

Ta juya zata tafi, da sauri ya fizgota yace  Goggon har gida gareta?

Tace  eh sirikanta sun siya mata.

Yace  me?

Tace  sakeni dan Allah.

Yace  amma shi Sultan din bazai zauna anan ba har ya gama?

Tace  ya zauna a ina? Gidan mutumin da bai kaunarsa bai kaunar mahaifiyarsa? Ta ina ma zai zauna a wannan gidan?

Dady ya fara hucci, fizge hannunta tai ta fita, Dady yai shiru gaba daya yama rasa abinyi.


******

Jalila kuwa tana ganin sun shiga kwaso kaya ta fito inda Hassan yake, tace  Yaya muje kaga dakinmu.

Fitowa yai ya riko hannunta yace  ahh yau zanga muhallin Baby.

Tai murmushi tace  Yaya daka dan sake hannuna kar a ganmu.

Yace  to wai ni in an ganmu menene a ciki? Ahhh dana sani London nace a nemarmana dan su nasan ko me kai ba ruwann wani dakai ko a ina ne.

Jalila tace  Lalai, wato kai abu ma kake so ka dingayi a ko ina? Oh ni yays ba kunya sam.

Zaiyi magana tace  Yaya zaka saima Sultan keke?

Yace  keke?

Ta kalleshi tace  eh, a gidan Goggo zai zauna saboda exams.

Yace  ban gane ba.
Nan ta fadamai yanda sukai, hannu yasa ya shafi kanta ta baya yace  ahh baby na u are sooo kind....

Tace  kai yaya....

Tana tura kofar dan dakin yai shiru yana bin dakin da kallo, gaba daya jikinsa yayi sanyi.
Ganin yanda yake bin dakin da kalli yasa ta matso ta rungumeshi ta baya tare da kwantar da kanta a bayansa....


#OneLuv=ؕ?=??? *JALILAH* =???


Written By : *AYUSHER MUHD*
Wattpad: *Ayusher Muhd*


*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*

*77*


Hannu yasa ya juyo da ita saitinsa sannan ya rike hannunta, janta yai zuwa katifar dakin, kwantawa yai sannan ya miko mata hannu, murmushi ta sakar masa sannan ta kwanta kusa dashi itama, jawota yai ya rungume ta ajikinsa sannan ya shafa bayanta yace "Yau na kwanta a inda Baby take kwanciya shekara da shekaru."

Jalila ta dago da fuskarta ta kalleshi tace " katifarka duk tayi kura ka kwanta."

Yace "katifar da kika sha kwanciya akai ko me tai ai banaji zan kasa kwanciya."

Jalila ta kankance ido tana kallansa, yace "wannan kallan fa? Ko kin dauka karya nake?"

Tace "ah haba wani karya kuma kawai dai ina tunanin da Yayan nan lafiyarsa kalau, yan mata nawa zaiso kafin ni? yan mata nawa ne zasu soshi kafin ni?"

Yatsa yasa ya dungure mata kai yace "wadannan tunanikan naki sai nadau mataki babba akansu."

Tai dariya zatai magana yace "badai a kasan ranki kina farin ciki da rashin lafiyar danai ba ko?"

Da sauri tace "ni? Inji wa?"

Hannunta ya riko ya matse yace "fadamin gaskiya....:"

Dariya ta dinga kyalkyalawa saboda yanda ya mata rikon tana cewa "yaya wallahi da zafi...."

Ganin yanda take dariya sosai yasashi a wani farin ciki, can yace "Jalila."

Ta kalleshi bayan ta daina dariyar, yace "Shigowata dakin nan sai na fara tunanin kamar ban kyauta miki ba, zan daukeki daga inda zakiga Goggonki saboda wasu burika nawa, nasan ci gaba da karatu da kuma san kadaicewa."

Kallansa kawai takeyi fuskarta dauke da murmushi, kara kwantar da kanta tai a jikinta tace "ka manta me nace ma tun farko?"

Yai shiru yana saurarenta, tace "ko ka manta nacema duk abinda ka tsara daidai ne a gurina?"

Ta dago ta kalleshi sannan tace "Goggo ma dinga yin waya, sannan kaima ai is not easy ka rabu da su Ummy da su Abba."

Shiru yai kafin yace "nifa kinsan me na miki?"

Tace a'a yace " course daya na cike mana fa ni dake."

Dariyarta ta kunshe tace "shiyasa a sanda Abba ke tambayata wani course nakeso kaketa shashantar da zancen?"

Hassan yai dariya yace "eh mana, nafiso mu shiga tare mu fito tare, sannan kinga in muka tashi aiki muyi a company din Abba a tare."

Jalila tace "Hmm wannan wayan yayi."

Yace "ai dama yayi sosai ma."

Jalila tai dariya kawai......

Su Mumy na gama hada kaya suka fito suka shiga motarsu, ita kuma da Hassan sukadau Sultan, Hassan yaba Mumy kudi suka fito, dady na tsaye zuru yana kallansu, Yasmeen sai kuka take ita gun Dady takeso.

Shikam Dady haushi ne ya isheshi har dakin Sultan ya shiga dan suyi magana amma Sultan yaki kulashi.
Haka ya fito rai a bace.

? Mumy kam shiru tai kawai a cikin mota gaba daya ta kasa ko furta kalma daya, itakam Safeena kanta ta kwantar akan kujera kawai.


**************

Sun isa gidan Goggo, Sultan ya tsaya a jikin kofar shiga falon, Hassan ya sa hannu a kafadarsa ya jashi ciki, Goggo tana ganinsu ta mike cikin jin dadi, Jalila kam da sauri aka wuce aka fada jikin Goggo.

Goggo tasa hannu ta tureta tace "ko kunya ma bakyaji mutum inya girma ai yasan ya girma."

Ta koma gefe tare da turo baki, Goggo ta kalli Hassan tace "Yasu Ummy?"

Yace "suna lafiya."

Ta kalli Sultan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login