Showing 12001 words to 15000 words out of 149705 words

Chapter 5 - Jalilah Book One Complete Hausa.doc

Ayusher   

28 Oct 2025

604

yana nuna ya manta ne dan neman kwanciyar hankali."
? Jikin Abba ne yai wani irin sanyi tsananin tsoro ya kamashi yace "Ahmad ya zamuyi?"
Dr yadan yi shiru sannan yace "akwai solution, na farko ku yarda da abinda ya tsara na mantawa dayai, karka fadawa kowa tunda nima ban tabbatar da hakan ba, sai abu na biyu ina ganin ku nemomai mace wacce zata dinga kwana dashi tana yini dashi, in kuka samarmai mace mai hankali wacce zatasoshi a hankali mekin dake zuciyarsa zai warke, ko akwai wacce yake so?"
? Abba yace " ina ma yake kallan macen bare?"
Ahmad yace "to in wannan bazai yiwu ba sai dai in sake research in dubo wata hanya, dole dai a cikin gida maganinsa yake, sannan yana bukatar kukawar dukaninku, ta hakan ne guiltiness din dake makale a zuciyarsa sai kankare."

? Abba yai shiru kafin can yace "na fahimta sannan duk wani abu indai har bai sabama shari'a ba zan iya aikatashi indai har Hassan zai samu sauki, domin ni da matata Allah ne kadai yasan halin da muke ciki."
? Ahmad yace "Karka damu Allah na tare da mu insha Allah."

Nan sukai sallama suka fito, Ummy ce kawai a d'akin, Abba yace "Hassan fa?"
Tace yana fitowa waje yai, sai naga Sagir ya bishi.
Ya karayina Ahmad godiya sannan suka fita.

Hassan na zaune a can gefen asibitin ya kurama kasa ido yana karzar hannunsa na dama da farcen babban yatsarsa na hago, Sadiq na gefensa kadan a tsaye.

? "Inama Allah ya d'auki ransa a wannan lokacin? Babban bakin cikinsa bai wuce yanda iyayensa ke fama a kansa ba, gaba d'aya bayasan ya zama haka, sai dai ya zaiyi?"

Sagir ne ya matso da sauri ya sa hannunsa ya tare hannun damarsa yace "Yaya!"
Kallansa yai sannan ya kalli hannunsa wanda sam bai kula ba ashe ya karje hannunsa har ya fara jini.

? Hannun Sagir ya matsar sannan yace "I'm okay."

Sagir cikin tausayawa yace "muje mota gasu Ummy sun fito.


Mikewa yai suka shiga mota.

? Duk yanda Abba yai akan yai bacci ya kasa, Aina? Kai ya girgiza da sauri dan yasan halin Aunty Nana, duk da yaya take agun Mumy ya tabbatar bazata yarda a aura mata Hassan ba, balle dama ta taba cewa Ummy ya kamata akai Hassan psychiatrist.

? Ummy ce tace " abinda Dr Ahmad ya fadama ne yake damunka?"
Yace "ba abinda yacemin, baccin ne dai na kasa yi."

Bata sake cewa komai ba dan ta riga taji komai, Hassan da Sagir na fita ta je jikin kofar dan dama ta damu tasan cikaken halin da d'anta yake ciki, sai dai koda yaushe Abba bai fada mata.
Ba shakka itakam gobe zatama Aunty Nana magana akan Aina taji.


#OneLuv=ؕ?
[08/10, 19:19] * +234 816 365 0557, : =??? *JALILAH* =???

Written By : *AYUSHER MUHD*
Wattpad: *AyusherMohd*

*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*
? (_D home of expert and perfect writer's_=ء?)

*NO 8*

Dayake yau asabar ne takan dan samu ta koma bacci bayan sallar asuba saboda su kansu 'yan cikin gidan sai karfe 11 suke karyawa.
Tana idar da sallah tai addu'ointa ta baje akan katifa, Goggo ta kalleta tace "daga sallah sai kwanciya? Kya bari ai gari yadanyi haske ko?"
Jalila ta kara gyara kwanciyarta tace "Goggo bakiji baccin da nakeji ba wlh, nifa gani nake kamar ma baccin awa d'aya nai gaba daya."
"To wai jiya me kika tsaya kikai tayi ne har sai 11 na dare kika dawo?"
Jalila tadan tab'e baki tace "oho musu wai ko bako zasuyi ne ko me? Ni dai sunce inyi kwallima a babban falo sannan aka sani juya kujerun."
Ta mike da sauri ta zauna kamar wacce wata sabuwar gulmar tazo mata, tace "Goggo kinsan wai Inna ce da kanta take tsaye a kaina tana sani yanda zanyi?"
Goggo tace "to menene abin mamaki a ciki?"
Jalila tace "inna fa nace ba Mumy ba, Goggo bakiyi mamaki ba?"
Goggo tace "ni banga wani abu a ciki ba."
Jalila ta maida kanta ta kwanta tace "lalai nikam jiya da mamakin abin nan na kwana, na tabbatar bakon da zasuyi mai mahimmanci ne."
Goggo tace "ina miki magana ki tashi kiyi addu'oi amma ke gulma kike sonyi."
Idanunta ta rufe wai ita a dole bacci takeyi, Goggo tace "yi baccin karya da kyau."
Jalila tana jinta batai magana ba.
Batafi minti talatin da kwanciya ba sukaji ana buga musu kofa.

? Goggo ta mike da kyar saboda ciwon kafa sannan ta kashe fitilar tasu sannan tabude kofar.
Dady ta gani a tsaye tace "Ina kwana?"
Yace " Ina Jalila?"
Tace "bacci take d'anyi."
"Bacci? Batada hankali ne?"
Goggo tace "lafiya?"
D'akin ya shiga yace "KE JALILA!"

Juyi tayi dan itakam bacci take mai dadi, Dady ya kalli Goggo yace "tasheta mana."
Goggo tace "yanzu ta kwanta."
Yace "To menene damuwata a ciki?"
Goggo ta matso jiki a sanyaye tasa hannu tadan daki kafarta kadan.

? Jalila ta dan bude ido dakyar tace "Goggo dan Allah kibarni nai bacci kona awa daya ne."
Muryar Dady taji yace "kin tashi ko sai na dakeki?"
Idanunta ta bude da sauri, tace "Da Da Dy......"
Yace "will you get up"
Jalila ta mike zaune a tsorace, tace "banyi komai na Dady."
Tsananin tausayinta ya kama Goggo ace in kaga Mahaifinka tsoro kake ko kayi laifi?

?? Yace "tashi muje, Inna nemanki take."
Jalila ta mike tare da d'aukan d'ankwalinta ta sa a kanta.
Yana gaba tana binsa a baya har sukaje ba maganar data hadasu.
Tana shiga taga Inna a falo, tsugunnawa tai ta gaisheta.

Dady ya wuce daki dan bacci yakeji, Inna ta kalleta tace "na d'auka tunda jiya kinsan bako zanyi zaki zo da wuri dan tambayar abinda ya kamata, me yasa ne a koda yaushe bazaki dinga amfani da kwakwalwarki ba?"

Jalila tace " Yahkuri Inna."
Tace "taso."
Jalila ta mike sukai kitchen, kayan girki ta gani kala kala an fito dashi, Inna tace " inada bakon dazanyi wajen karfe 12 na safe, bayan kin gama yin abincin breakfast na gida sai ki shiga yin hidimar bakona."
Jalila ta kalli tulin kayan girkin tace "Inna me da me za'ai?"
Inna ta mata alama data matso, Jalila ta matsa kusa da ita, inna ta ce wannan vegetables din rabasu gida biyu zakiyi, d'aya kiyi miyar vegetables da farar shinkafa, wannan naman kazan pepper chicken zakiyi dashi.
Wannan d'ayar naman kazan sai ki raba biyu d'aya sai ki fere dankali ki hada kiyi chicken pie, d'aya kuma sai ki saka a cikin miyar vegetables din.
Ta kalli fruit din da ke gun tace " wannan kuma kiyi pineapple and coconut juice sai ki yanka ragowar kiyi fruit salad.
Tashin hankali, kallanta Jalila tai, Inna tace " ki tabbatar kinayi kina kara gyara gidan, sannan kisa turaren wuta sosai, bakon dazanyi mai mahimmanci ne a garemu.
Ki tabbatar kin kammala komai kafin lokacin.
Ta juya ta fita, Jalila ta kara kallan kayan girki sannan ta kalli agoggon dake kitchen d'in, karfe 6:40am idanunta ne suka ciciko da kwalla yanzu ia kadai akw tunanin tayi wannan uban aiki sannan ta hada da aikin gida?

? Jitai ance "me kikeyi banji kin fara ba?"
Lekowa tai ta ga Inna a digirgire a zaune a falon kusa da kitchen.
Nan ta bude fridge ta d'auko kayan cikin da Mumy tace farfesunshi zata musu da soyayyiyar doya dakwai.

? Yau kam gun gajiya ba'a cewa komai a gun Jalila, dan dama tun datashiga Ss1 aka sakar mata girkin gida gaba d'aya, a da tare sukeyi da Mumy, ashe batasan training ake mata ba, data shiga Ss1 kuwa sai dai ta zauna a kitchen din tana cewa tai kaza tai kaza, wanda a yanzu indai abinci ne ko snacks ko abinsha sai dai in wanda bai fito ba, amma ba wanda ba'a sata yi ba.

Haka ta shiga aiki kamar mahaukaciya, duk mai tausayi inya ganta saiya tausaya mata.



*************


A hankali Ummy ta tura kofar d akin, a kwance taganshi a kasan d akin daga can gefen gado, yana kwance akan sallaya yana bacci, takan rasa inda zata sa kanta a koda yaushe in taganshi a kwance akasa, abinda ke damunta shine inhar bacci dare zaiyi bazaki taba ganinsa akan gado ba, sannan a kasan ma kwanciya kawai yake, amma in gari ya waye sai kiga ya kwanta akan gado.

Kusa dashi ta karasa ta dauko karamin bedsheets a gefen gadonsa sannan ta lulubamai, jiki a sanyaye ta juya ta fita.
Tana rufe kofar yana bude idanunsa, kofar ya kalla dan tun da ta shigo ya farka, idanunsa ne suka canza launi a hankali ya maidasu ya rufe saboda tsananin tausayin da yakeji na mahaifiyarsa.

Mikewa yai ya hau kan gado yai wata kwanciya a dukunkune, a hankali idanunsa suka zubo da wasu zafaffan hawaye.

Ummy tana fita ta sauka kasa, kitchen ta shiga inda Ameera da Aina u suke girkin abincin safe.
Tace  wannan jagwalgwalo har mun gaji da jiransa, sai kace wanda ake mana abincin arziki.
Ameera tace  Ummy kin dage sai munyi girki da weekend kinga kuwa kome muka dafa sai kuyi hakuri kuci.

Ummy tace  ai na gama kula dake sam bakyasan yin girki, yanzu kuwa kinjama kanki duk asabar da lahadi ke zaki dinga yin girkin safe.

Ameera tace  Shikenan Ummy sai mudingacin Indomie.
Aina tai dariya tace  Lalai Ameera, Abban zaki ba indomie?

Ummy ta juya tana murmushi, falo ta zauna sannan ta d au waya ta kira Aunty Nana.
Bayan sun gama gaisawa tace  muna nan da Aina u munatashan hutu.
Aunty Nana tace  ai gwara datazo dan nasan yanzu Ameera tafi kowa jin dadi.
Ummy tai murmushi.
Aunty Nana tace  Ya jikin Hassan?
Tace  dama saboda shi na kiraki
Aunty Nana tai shiru tana sauraranta.
Ummy tace  Me kike tunanin akan yi masa aure?

Aunty Nana tace  Aure? Wace irin magana kike yi Hafsa? Wa kike tunanin zai aureshi? Karfa san kanku ya muku yawa.

Ummy mamaki ya kamata tace  ban gane san kai ba? Sai kace wani mahaukaci ko mai lalura mara warkewa ko fa nakasar jiki?
Aunty Nana tace  Ni dai dan bakwasan gaskiya ne, amma na tabbatar Hassan nada matsalar kwakwalwa, kardai ku aura masa yarinya yazo yana neman kasheta.

Mikewa Ummy tai idanunta suka canza tace  mene?
Aunty Nana tace  Hafsa......
Kashe wayarta Ummy tai sannan tai shiru tana kara maimaita kalaman Aunty Nana a ranta.
Aunty Nana irin matan nan ne da duk abinda ya fito musu a baki fada suke ba tare da sunyi nazari. Da yaya zaka fuskanci kalamansu ba.

Ummy ta shiga d aki jiki a sanyaye, Abba ya gama shiryawa yana fesa turare ta shigo, yanda yaga ta zauna akan gado yasa ya juyo yace  Lafiya?
Kallansa tai tace  Alhaji ya zamuyi da Hassan?

Ajiye kwalbar turaren yai yace  keda Yaya Nana ce?

Kallansa tai cikin mamaki tace  ya akai ka sani?
Yace  me yasa haryanzu bakisan kanki ba? In dai har naganki a wannan yanayi to nasan matsalar Hassan ne ke damunki, to in har naga yanayin ya hada da dan baccin rai to inba Aunty Nana ba waye? Ni dai nasan ba ni bane, sannan Sagir banaji ya taba bata miki ran da har zaki shiga cikin wani hali, ita kuwa Ameera yarinta ce a kanta.

Ummy ta kalleshi tace  jiya naji yanda kukai da Dr Ahmad, shiyasa......
Yace  kike tunanin hadashi da Aina u?

Tai shiru, kusa da ita ya zauna yace  Hafsa!
Kallansa tai yace  shi aure da kike gani nufine na Allah, sannan wani baya auran matar wani, Allah ne kadai yasan abinda ya shirya akan rayuwar yaran nan, mudai abinda zamumai kawai shine mu dinga mai addu a kamar yanda muka saba.

Kai ta jinjina alamar gamsuws sannan tace  yanzu zaka wuce ne? Naga bakai break ba.
Yace  In naje naci acan, dan nasan thnda dai gida ta gayyacen ta shiryamin abinci, sannan ba dadi taga naje banci ba, kuma kinsan halina inhar naci abinci yanzu 11 banaji akwai abinda zan iya ci nan da awa d aya.

Tace  Hakane, kai kadai zaka ne?
Yace  a a da ina tunanin tafiya da Sagir to kuma ina tunanin kar taji nauyin fadar bukatun ta a gabansa, shiyasa zan tafi daga ni sai Ibrahim.

Tace  to sai kun dawo.

Ya dau hularsa ya saka sannan suka fito tare.
Sagir na falo ana masu Ameera tsiya akan sun gaji da jiran abincin safe ya hangosu, mikewa yai yana dariya yace  Ummy zaku fita yawon shakatawa ne?
Harararsa tai tace  a haka ake fita ba ko mayafi?
Yace  ai ba komai tunda mota zaki shiga.

Abba ya kalleshi yace  Wato Sagir in baka zolayi mahaifiyarka ba na kula sam bakajin dadi.
Keyarsa ya sosa yana murmushi yace  Abba kasan nafisan kullum naga tana murmushi ne.

Ummy ta kalleshi tace  Muje muga masu abinci tunda Abbanka ya mana yajin aiki yau.

A tare suka fara takawa suna hira, Abba ya bisu da kalli cikin jin dadi sannan ya juya ya fita.


************

Jalila anci uban aiki duk tai wujiga wujiga ga ko abinci ba wanda ya damu taci, sai data gama jera komai sannan ta fito, bangarensu ta nufa cikin tsantsar gajiya.
Goggo na zaune hankalinta duk yana kofa tana jiran yar tata ta shigo, ko abincin ma ta kasa ci, Jalila na shigo ta zube tare da kwanciya akan cinyarta.
Goggo tace  zauna ki danci abinci.
Da kyar ta mike ta sha shayi da bread sannan ta fara kokarin kwanciya, Goggo tace  Jalila kidan jira ya tsirga miki.

Tace  Goggo wlh nikadai nasan me nakeji.
Tafada tare da kwantawa.


Abba ya iso batare da shan wahala ba, saboda kowa yasan Hajiya, Sun shiga babban falo inda ake sauke manyan baki.

Dady ne ya fara tarbarsu, ya zauna suka gaisa, sannan mumy ta shigo.
Bayan sun gaisa ne sai Hajiya ta shigo.

Taura yana ganinta ya mike, sai data zauna sannan ya gaidata.

Mumy ta mike ta fito, d akin Safeena ta shiga taga bata nan, na ta fito ta bude dakin Sultan, yana zaune akan computer da alama game yakeyi. Tace  Safeena fa?

Yace  Safeena? Ba jiya take cewa akwai inda zasuba yau da friends dinta? Inaji sun tafi ai.
Mumy tace  dama yau ne? Ni na dauka sai gobe ai, to kai taso ku gaisa da bakon.
Mikewa yai ya fito, yana gaishesu ya koma d aki.

Mumy tace  Inna bata nan kinsan tace yau akwai inda zasuje.
Inna ta kalli Taura tace babbar yarinyar bata nan sun fita.
Yace  bakomai Hajiya,ni ai ban masan kinada jika babba haka ba. Yana nufin Sultan.
Tai murmushi tace  Sultan ai na biyu ne, babbar mace ce ajinta shida a secondary.
Yace  Masha Allah, Allah ya raya.
Tace  Ameen.

Sun d an bar musu falon na sama da minti talatin saboda su ci abinci.

Sai da suka gama sannan Inna da Dady suka shiga.
Sun d anyi shiru kafin Inna tace  Taura kayi hakuri rashin nemanka danai har sai damatsala ta tasomin.
Yace bakomai Hajiya.
Tace  Taura muna cikin matsala wanda company dinku ke neman fuskantar durkushewa...........
Nan ta zayyane masa duk yanda matsalolin ke faruwa,shima Dady na kara mai jawabi.
Sai da sukka gama, Ta daura da cewa  shine nake neman taimakon ka.

Taura yai shiru kafin can yace  ba matsala indai, sai dai nima sai kun bani zuwa gobe na duba yanayin abin sannan sai musan yanda za ai.

Taji dadi sosai, dady yace  mungode kwarai.
Taura ya dau takardar ya shiga kara dubawa, yana nazari, kudi sukeso sosai dole dai ya nutsu kafin yasan abinyi, dan business ne.

Inna ta kara godiya, Dady ma haka.

Bayan sun gama ne suka mike dan tafiya.

Jalila bayan tayi wanka Goggo ta bata mafici dan takai makotansu akwai wata tsohuwa agidan da ta sa a mata.

A gun ajiye motoci ta hango su a tsaye, da alama bakon ne, ta gabansu dole zata wuce shiyasa tana zuwa inda suke ta tsugunna har kasa ta gaishesu.

Kallanta Taura yai ya kura mata ido, har ibrahim ya amsa gaisuwar shi bai ce komai ba.

Ta kara kallan Taura wanda kallan da yake mata yasata yin kasa dakai tace  Ina wuni?
Taura yace lafiya kalau, kece babbar yarinyar gidan?
Cikin halin ko in kula tace  Eh!
Yace  Masha Allah, aji shida akace kike ko?
Takara cewa eh.
Yace  Alhamdulila.

Mikewa tai tace  Sai anjima.
Taura yasa hannu a aljihu ya zaro dubu biyar, yace  gashi!
Idanu ta zaro tai saurin cewa  A a kabarshi nagode.
Kallanta yai sannan yai murmushi yace  kyauta na miki fa?
Tace  wlh ka barshi, na gode.

Kai ya daga sannan ya bita da kallo, Ibrahim ya kalla bayan sun shiga mota, yace  me zakace game da yarinyar nan?
Ibrahim yace  ban fahimceka ba.
Taura yai murmushi sannan yace a ransa Alhamdulila ala kuli hal......


#Oneluv=ؕ?
, : =??? *JALILAH* =???

Written By : *AYUSHER MUHD*
Wattpad: *AyusherMohd*

*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*
(_D home of expert and perfect writer's_=ء?)

*NO 9*


Taura yayi shiru a d aki yana nazari, Ummy ce ta turo kofar tare da sallama.
Bai jita ba dan ya nustu sosai, kusa dashi ta tsaya tace  Lafiya?
Kallanta yai sannan yadan murmusa yace  tsi wlh hankalina ya tafi tunani ne.
Tace  abinda kajeyi bai yiwu bane?
Yace  Hafsa dan zauna.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login