Showing 72001 words to 75000 words out of 149705 words

Chapter 25 - Jalilah Book One Complete Hausa.doc

Ayusher   

28 Oct 2025

656

kofar inda Goggo take a zaune.

Kallanta Goggo tai sannan ta kalli gidan zatai magana Jalila ta rungumeta ta saki wani irin kuka.

Hassan ya juyo ya kalleta, me yasa ta fita kuka ne? Shifa bayasan kukan nan.

Kallanta yai yace  kuka zaki tsaya yi ba zaki taimaka mata ku shiga ciki ba?

Ta share hawayenta tana cewa  Goggo muje.

Hassan ya fito ya wuce ciki bai jira su ba, a falo ya taradda Ummy da alama fitowarta kenan, kusa da ita yaje yace  Ummy ina Abba?
Tace  yana falon sa.

Yace  Ummy muje akwai maganar da zamuyi.

Kallansa tai cikin jin dadi tace  da alama Hassan dina yanzu bakinsa na kokarin yin magana akai akai.

Hassan ya juya ya kwankwasama Sageer kofa ya fito, yace  muje.

Nan suka shiga kofar falon Abba.
Yana zaune rike da qur ani dan suna shigowa Ummy ta dauko ta mikamai itakuma da bata sallah tadau littafin addu oi.

Shigowar su ne yasa ya kai aya sannan ya ajiye ya kallesu.

Zama sukai Abba yace  lafiya?
Ummy tace  Hassan ne zaiyi magana.

Abba ya kalleshi yace  Hassan!
Zama yai sannan ya dansa hannunsa na haggu akansa dake ciwo yace  tare nake da bakuwa.

A tare sukace  bakuwa?
Hassan yace  eh, tunani nake boys quarters din mu zansa a gyara sai na maida ita can.

Abba yace  naji ba wai wannan bace maganar, wacece bakuwar? Itace tambayarmu.

Hassan yace  mahaifiyar Jalila.

Abba cikin mamaki yace  me kake nufi? Taya zaka dauko mata a gidan mijinta da arzikinta da komai ka kawota boys quaters? 
Hassan yace  bansan ta ina zan fara bayani ba, sai dai ita zatayima Ummy kudan bata lokaci kadan, abu daya zan iya fada, wacce kuka sani a matsayin mahaifiyarta ba ita ta haifeta ba, ban kyauta ba na kawota ba da saninku ba sai dai wannan ne kadai solution din da yazomin
Ya mike saboda kansa dake ciwo ya fita.
Abba yace  meke faruwa takamaimai? Ni na kasa ganewa.

Ummy ta dafashi tace  mu jira kamar yanda yace, na tabbatar yana da dalilinsa, kasan Hassan mutum ne da baya shiga abin mutane, tunda kaga ya shiga wannan i am sure da dalili.

Sageer ta kalla wanda yai shiru yana tunani, tace Sageer taimaka muje mu shigo da ita, sai mu sata a dakin Ameera inyaso gobe sai a gyara can din.
Nan suka mike suka fita.

A waje sukaga Goggo ta tsaya tana cema Jalila,  nifa bazan shiga ba sai naji inane nan.

Jalila ta daure tace  Goggo dan Allah mu shiga wlh zan fada miki.
Goggo tace  Jalila.
Jalila ta rike hannayenta tace  Goggo gidansu mijinane.

Goggo tace  me? Miji? Miji kamar ya?

Sageer har zai fita ya tuna Goggo fa ta ganshi ta kuka san sunanshi, kallan Ummy yai yace  Ummy bari na dan shiga toilet it s urgent.

Dariya tai tace  to a fito lafiya.
Ya juya da sauri, yana cewa gwara mu mata bayani kafin ta fada cikin mutane.

Ummy tana turo kofar taji Goggo na cewa  Jalila aure kamar ya? Aure bansani ba? Auran dole aka miki?

Cikin mamaki Ummy a karasa tace  meke faruwa? Bangane aure mahaifiyarki bata sani ba, meke faruwa Jalila?

Jalila ta kalli Ummy idanunta fal tace  Ummy.

Ummy ta kalli Goggo sannan ta kalli kafarta dake ciwo, tace  muje ciki sai muyi maganar a nutse.

Goggo bata musa ma Ummy ba suka shiga ciki.

#OneLuv=ؕ?


=??? *JALILAH* =???

Written By : *AYUSHER MUHD*
'ote me on Wattpad : *Ayusher Mohd*


? ?? *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*
? (_D home of expert and perfect writer's_=ء?)

_Should i start with sending my special greetings? Special greetings to u all my fans, thanks alot for the love and support, a sincere thanks to you all from the bottom of my heart =ؕ?Luv u all._

*42*

Ummy ta zauna akan gadon kusa da Goggo akwai abubuwan da takesan ji, sai dai ta tabbatar matarnan ba lafiya ce ta isheta ba, dan ga kafartanan.
Kallan Goggo tai tace  ki kwanta ki huta dan Allah karkiyi tunanin komai har sai hankalinki ya kwanta.

Goggo ta kalli Ummy tace  Hajiya ta ina zan kwantar da hankalina, aure? Bansani ba?
Ummy ta kalli Jalila ta mata alama da ta fita, sannan ta kalli Goggo bayan Jalilan ta fita tace  sai yanzu na fahimci me yasa yarki batada walwala duk kuwa da yanda naso ta saki jikinta da gidan nan, na fahimci an cutar dake, an munafurceki, sai dai bayanda za ai a maida hannun agoggo baya, ki nutsu ki kwantar da hankalinki, inkin huta anjima sai muyi magana, sai kiji abinda ya faru nima naji abinda ya faru, amma yanzu ko saboda  yarki da kwanciyar hankalinta kiyi hakuri, lafiyarki itace abin dubawa a wannan lokacin.

Goggo kallanta kawai take tana mamakin yanda mace mai kudi, mai aji, mai kyau haka take magana cikin sanyi da nutsuwa, da alama Matarnan macece mai tsananin imani, da kaunar jama a da sanin darajarsu.

Kasa musama Ummy tai ta daga mata kai alamar fahimta, Ummy tace  nagode, ga toilet nan in zakuyi amfani dashi. Ta fada tana kallan Lantana.

Goggo tace  Angode.
Ummy tai waje ta turo kofar.
A waje taga Jalila a tsaye, murmushi ta mata tace  me kike anan?
Jalila ta kalleta da idanunta da sukai raurau tace  Ummy kiyi hakuri, sannan nagode....



Ummy tai murmushi tace  wanda zakima godiya daban bani bace. Sannan ki barta ta huta zuwa anjima, amma meke damunta?
Tace  hawan jini da diabetes.

Ummy ta kalli kofar dakin cikin tausayawa sannan tace  shikenan mu barta ta huta.
Jalila ta daga kai alamar to sannan tai hanyar sama.

Hannu tasa tana neman bude kofar dakin, tsayawa tai tana rike da hannun kofar amma bata bude ba, tana tunanin abinda zata cemai, da wani bakin zata fara mai godiya?

A hankali tai ajiyar zuciya sannan ta tura kofar, a kwance ta ganshi kamar mai bacci, kusa dashi taje ta tsugunna tana kallansa, hawaye ne yazobo mata wanda batasan ya diga akan kuncinsa ba, a hankali ya bude idanunsa.

Kallanta yai tana share hawayenta, a hankali ya ke magana yace  Menene? Wani abun ya faru ne?
Hawayenta ta karasa gogewa da sauri sannan ta girgiza kai tace  bakomai.
Yace  and why?

Tace  bansan me zance maka bane, kawai sai naji hawaye....
Idanunsa ya lumshe kansa na sarawa yace  it looks like it s ur hobby.
Tace  kukan?
Ya lumshe ido kawai, kallansa tai sannan tace  bakajin dadi ne?
Bai tanka ba sannan bai bude ido ba, hannunta tasa a kansa wanda ke mai ciwo kamar zai tsage, jin zafi rau akan tai, da sauri ta kai hannu wuyansa, nan ma zafi a rikice tace  Yaya bakada lafiya, zazzabi ne a jikinka, jikinka zafi.

A hankali ya bude idanu yace  why? Are u worried about me?

Da sauri tace  sosai ma, ka tashi muje asibiti. Ta fada tare da mikewa tana kokarin dagashi, hannu tasa ta riko hannunsa tana neman dagashi.

Jawo hannunta yai, ta fada jikinsa, shiru ne ya ratsa dakin, ita kuma zuciyarta na harbawa da sauri da sauri, a hankali ta kalleshi, idanuwansa a rufe suke, sai cewa yai  sai yaushe za a daga ni?
Ta kalleshi ta kalli kanta data danneshi, neman dagawa tai sai taji hannunsa na rike da ita gam.

Tace  to ai.....
Idanu ya bude a hankali ya kalleta, a hankali tai kasa da idanunta.
Saketa yai ta mike ta zauna a gun, bata tashi ba tace  Yaya dan Allah muje asibiti.
Yace  bana zuwa asibiti, sannan ni nasan jikina kawai nayi abinda bansaba bane shiyasa, karki damu.

Idanu ta kuramai bayan ya maida idanunsa ya rufe, a hankali tana kallansa tace  Yaya nagode, ban taba tunanin wannan ranar ba.

Bai tanka mata ba, idanunta ne suka ciciko tace  Kayi hakuri Yaya nagode sosai har bansan ta ina zan fara ba.
Yace  hakurin me?
A ranta tace  da na dauka kai mutum ne mara tausayi da mutunci.

A fili tace  for everything.

Idanunsa ya bude a hankali sannan ya kalleta, itama kallansa takeyi, sai dai da sauri ta maida idanunta gefe.

Yana kallanta yace  ya zakiyi?
Tace  name?

Idanunsa na kanta tana kallansa taga ita yake kallo ta dauke idanta da sauri, yace  ya zakiyi insu Ummy sun tambayeki?

Tace  bansan ya zanyi ba, wata zuciyar na sanar dani in fadi komai, wata kuma na tunanin abinda zai faru da Dady dan na tabbatar Inna bazata barshi ba.

Kamar bazaiyi magana ba, dan harta mike zata nemomai maganin zazzabi ragowar tata wanda takaima Ummy taji muryarsa yace  kiyi abinda ya kwanta miki a rai.

Juyowa tai ta kalleshi tace  In na tuno abinda yama Goggo tundaga haduwarsu zuwa yanzu, sai naji kome zai sameshi bazan damu ba sai dai bansan meke damuna ba, I wish nima inada dauriyar zuciya ko rabin taka ce.

Alama yamata da hannu akan ta matso, matsowa tai gunsa, ya mata alama data kara matsowa, nan ma ta matso takai kunnenta saitin bakinsa, a hankali yace  in fada miki sirrin?
Kai ta daga da sauri, yace  kisa Goggonki a saman komai.

Abinda ya fada kenan yai shiru tare da juya mata baya ya rufe idanunsa, tsayawa tai tana kallansa me yake nufi? Tace  yaya!

Shiru yai baice komai ba, itama shiru tai tana tunanin me yake nufi.
Ta dade a tsaye kafin ta daukon mai maganin, ta dauko ruwa a karamin fridge din dake dakin, tazo kusa dashi tace  Yaya tashi kasha magani.

Bai bude idanunsa ba, ganin bashi da alama ne yasa ne ta kara cewa  Yaya Please, ko in fadama Ummy?
Idanunsa ya bude yace  wato kina neman kiyi amfani da weakness dina ko?

Dariya tai tace  inkaki tashi yanzu sai na sanarma Ummy.

Yace  eh lalai kinga gadon bacci na...

Ta kuntse dariyarta tana nunamai gadan da yake kwance akai, harararta yai sannan ya mike zaune ya fizgi ruwan hannunta ya mikamata dayan hannun ta. Zubamai maganin tana dariya.

Sha yai sannan ya kwanta.


**********

Ummy na shiga falon Abba ya kalleta yace  meke faruwa? Nifa na kasa gane abinda ke faruwa.
Tace  ni kaina bansani ba sai dai na tabbatar Hassan yasan me yakeyi, kafi kowa sanin halinsa a da can inyai abu ma to akwai dalili, daga baya kuma da matsala ta faru gaba daya ma yadaina shiga rayuwar kowa inba tasa ba, kaga yanzu dayai abin nan kasan zuciyata dadi takeji dan na fara ganin Hassan dina na da na shirin dawowa.

Abba yai murmushi yace  na fahimta sannan nasan wanene Hassan, sannan ni koma menene ya faru ba wani abun dan ni dama ita na gani sannan ni ita na zaba, ko da a lokacin zasu nunamin wata ba lalai zuciyata ta amince da ita ba.

Ummy tai murmushi itama tace  maybe suna tunanin sun cuceta ne da alama sunyi bincike akan Hassan..........

Karar wayar hannunta ne yasa ta kalleshi, kashe kiran tai sannan ta kalleshi, yace  Sim dina na wayarki ne?
Tace  eh, da na cire sai kuma nai tunani kar san zuciyata yasa wasu dasuke nemanka ko na taimako ko na aiki suyi ta nemanka, shiyasa nasa Sim din a wayata.

Shiru yai tare da maida kansa gefe can yace  Kiyi hakuri.
Tace  kadaina fadar haka, kaddara ce ta zo mana, sai dai mu roki Allah akan ya taimakemu yasa mu wuce kaddarar nan.

Abba yai shiru bai sake cewa komai ba......


*********

A can gidan Inna kuwa, Dady cikin takaici ya dawo gida, bakin cikinsa ko waya bai fita da itaba bare yasa a zo a daukeshi, rabansa da taxi haryamanta amma haka yahau ransa a bace.

Yana isa gida ya wuce daki cikin zafin rai, Mumy dake kitchen tana bada umarnin abincin da za ai ta taho da sauri ta shiga ciki.

A tsaye ta ganshi tace  Abban Yasmeen lafiya?

Juyowa yai rai a bace yace  kinsan yaran nan...... sai kuma yai kwafa.

Ta matso da sauri tace  ya kukai? Yadauke Goggon Jalilan?

Yace  ya dauketa mana, yaran nan yana abu kamar shine gaba dani, kinga yanda yake wulakantani, amatsayina na uban matarsa?

Mumy tai shiru can tace  nikaina yaran nan yaban tsoro, wai garin yaya kukaba Jalila yaran nan? Bakusanshi ba? Na dauka kunyi bincike.

Cikin masifa yace  bincike? Abinda Inna ke bada umarni mu ina mukaga ta cewa?

Mumy tai tsaki tace  ai gashi nan ta ja mana masifa, ita kanta yanzu abun ya dameta, gashinan abinda take tunanin samu ma ba samu zatai ba, wanda take dashi ma yana neman wargajewa.

Dady yace  wai yaran nan ni zai kalla yacemin wai inada kudi a jikin? Sannan ya mikon wai 1000 wai na hau mota shi bazai kaini ba?

Mumy tace  mene?
Yai kwafa cikin takaici yace  ni nama rasa ma me zance, kamar ni????

Mumy ta rungumeshi tace  cool down Dadyn Yasmeen, zamu san mafita, bari Mu sanar ma Inna.

Yai tsaki cikin takaici, tace  Safeena ta kira, ta isa Paris lafiya.

Yace  Wai paris taje dama?
Tace  eh can Inna tasa a nemar mata skul.

Yai shiru baice komai ba....

Inna gaba daya tunda Hassan ya fita ta kasa tsaye t kasa zaune gaba daya ta kasa samo mafita, cikin takaici ta kira Sani tacimai mutunci akan kin yimata binciken daya kamata akan Hassan kawai yacemata bashida lafiya alhalin bai bincika wani irin ciwo na kwakwalwa yake ba....


************

Kuka Zaliha take sosai tana cema Yayarta ita wlh kome zata yi tayi amma itafa kawai ta aura mata Taura in ba haka ba wlh barin gidan zatai ta shiga duniya...

Hankalin yayarta ya tashi tace  kar ta damu dan dole zata koma Niger.


#OneLuv=ؕ?


=??? *JALILAH* =???

Written By : *AYUSHER MUHD*
'ote me on Wattpad : *Ayusher Mohd*


? ?? *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*
? (_D home of expert and perfect writer's_=ء?)

*43*

Inna tana zaune tananin mafita Mumy ta banko kofa da sauri, Inna ta kalleta tace "naga sanda hankali zai ratsaki ki daina buga kofa haka, yarki ta kai a mata aure amma haryanzu inkina wani abu kamar karamar yarinya."

Mumy ta zauna da sauri tace "ni Inna ki bar fadanki zuwa anjima yanzu akwai matsala."
Gaban Inna ne ya fadi ta kalleta tace "Abakar ya dawone?"

"Ya dawo sai dai yaran ya dauke Goggo"
Inna tai shiru hankalinta ya tashi, ta kalli Mumy tace "yanzu kenan da alama sunsan komai ko?"

Mumy tace "me zai hana? Shiyasa Inna ni dama na kasa gane dalilinki na......."
Wani kallo data mata ne yasata yin shiru, Inna tace "kinsan menene yake bakantamin rai?" Bata jira amsartaba tace " rashin wayau da auna tunaninki, daga ni har mahaifinki munada saurin tunani da kwakwalwa amma ke ni bansan ina kika dauko ba, da farko kince yaran ubanki zaki aura yaran da ko A bai sani ba lokacin, dole da ganin bamuda wani da bayan ke yasa muka jure, sannan kikasan wannan yaran ya munafirceki ashe har aure gareshi, amma tsabar rashin kwakwalwa kika dage ke sai shi, sannan abin bakin ciki duk yanda nai dake akan kiyi aiki a company din da muka gina nida mahaifinki amma kinki, kin dage sai dai mijinki yai, sannan yanzu kice me?"

Mumy tai kasa dakai sannan tace "Inna wai dan Allah sai yaushe ne zaki amince da Abakar daro bisa dari? Mutumin nan na miki ladabi wanda ko ni bana miki, sannan ya a sona san da ba wanda yakemin irinshi..."

Inna tai tsaki tace "ni tashi ki bani guri nasan mafitar data dace damu dan zamanki anan bakomai yake karamin ba sai bakin ciki."

Mumy ta mike tai waje rai a bace....

Inna tai shiru tana tunani kafin ta dau waya ta kira Abakar.
Yana zaune a falo Mumy na gefensa itada Yasmeen, Sultan na daki yana ganin kiranta gabansa ya fadi ya kalli Mumy yace da alama Inna tagama shawara.

Mumy tace "muje tare."
Yace "karki damu ki zauna bari naje."
Nan ya mike yai sama.........


**********

Inna ta tashi tayi wanka, Ummy ta kawo mata kayanta tace ta saka, dan itakam ta kula kayan dake jikinta da wanda aka dauko a leda san ba magana, itada Jalila ne sukaje BQ dan ganin yanayin gun.

Jalila ta kalli Ummy tace "Ummy kije ciki zan gyara."

Ummy tai murmushi tace "Jalila ko dai ince masu aiki gidannan sundinga kwana ne?"

Jalila tace "saboda me?"
Tace "da alama aikin gidan ya karu, sannan zai yi yawa, tunda akwai bangarensu ina tunani gwara mu tambayesu, in zasu dinga kwana to, in kuma bazasuyi ba kinga sai mu samo wasu."

Jalila tai shiru can tace " Ummy gani, ga Lantana ina tunanin ba wani abu."

Ummy tai murmushi tace "baki fahimceni ba kenan."
Jalila ta mata kallo mai alamar tambaya tace "ban....."

Ummy tai dan dariya tace "so nake kibama Hassan kulawa 80% dan na kula ina hanaki kula dashi."
Jalila da sauri ta juya tana tattare kaya dan kunya, Ummy ta sake dariya tace "ko nayi sankai?"

Jalila tace "a'a kawai ta cigaba da aikinta.

Ummy ta kalleta tana murmushi, Lantana ta kira suka gyara gun, Ummy tace "gobe sai a siyo gado da kayan bukata a sa a ciki, wai gadan ciki ya tsufa, da Jalila zatai magana Ummy ta harareta wanda yasata yin shiru.


Sageer kuwa a daki hankalinsa duk ya tashi tabbas Goggonta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login