Showing 120001 words to 123000 words out of 149705 words

Chapter 41 - Jalilah Book One Complete Hausa.doc

Ayusher   

28 Oct 2025

657

"lalai yaya ba kara?"
Yace "karar kenan, fadar gaskiya."

Ita kanta mamakin yanda suke hira tai har suka isa kwanar gidan, wani shago ya tsaya yace suje sudan siyo mata abinda zata kai kauye, Jalila tace "kamar me?"
Yace "ina na sani?"

Tace "nima wlh ban sani ba kaga ban taba zuwa ba."

Yace "to kawai mu bata kudin gobe in zasu tafi sa biya ita da Mamman su siya."

Tace to.
Nan suka ja mota.

? A kofar gidan sukai parking, matsowa yai gaf da ita, ta zaro ido tana kallansa cikin mamakin me yake shirin yi da yamma nan, gari da haske? Jitai yace "kin manta spots din nan?"

Kallansa tai tace "name??"
Yace "ko ayi sai a tuno?"

Da sauri tasa hannu tadan tureshi kadan tana dariya tace "ba ruwana."

Yace "au baki manta ba ashe neman magana ne."

Da sauri ta bude kofa tana dariya, ta shige ciki.

Goggo na ta kara karfafa kafarta tana ta yawo a tsakar gida, lantana na falo ana ta kallo ana yanka alayahu, Jalila ta budo kofa.

Goggo cikin mamaki ta kalleta tace "Jalila!"

Da gudu Jalila ta karasa ta rungumeta, tace "Goggona!"

Goggo ta shafa bayanta tace "haryanzu ba'a girma ba?"

Jalila ta kara kankameta tace "shine zakiyi tafiya ba rakiya."

Hassan daya shigo ya tsaya yana kallanta, Goggo tace "Hassan sai kayi hakuri wannan matar taka inta samu gu akwai sakalci da shagwaba."

Da sauri Jalila ta dago, ta kalleshi, dan batasan ya shigo ba.

Sake Goggo tai cikin kunya ta boye a bayanta.

Hassan ya karaso ciki, Goggo tace "muje falo."

Lantana tanaji alamu ta dauke kwanan alaiyahun ta shige kitchen.

Hassan ya shiga yana murmushi, Jalila na rike ta baya da rigar goggo.

Da zata zauna tasa hannu ta ture hannunta tace "to ai abarni na zauna ko?"

Jalila ta saketa tare da zama a kusa da ita.

Hassan ya kalleta yace "ikon Allah! Malama a barta ta sake mana."

Jalila ta noke kafada alamar a'a dariya ma ta bashi ya kalli Goggo sannan ya gaisheta ta amsa tana cewa "ai kanada aiki, dan wannan in ta samu guri...."

A ransa yace ai haka nake so.
Amma a fili kawai murmushi yai yace "tafiya kuma tazo."
Tace "wallahi, ai in ba zuwa nai ba hankalina bazai kwanta duka ba."

Yace "Hakane, Allah yasa a taradda alkairi."
Tace "Ameen."

Nan ta tambayi su Ummy da mutanen gidan, suka danyi hira, Jalila na makale da goggo.

Goggo ta kalleta tace "tashi ki taya lantana ayi sauri a gama abinci yaci."

Ta mike tai kitchen.

Basu dawo ba sai da sukai sallar magrib, da zasu tafi yaba Jalila kudi ta kai mata, da kyar Goggo ta amsa tanata cewa ai Ummy ta bata wasu, taira godiya kamar ranta zai fita.

Tana mamakin wadan nan mutane da halinsu, lalai haihuwa ta biya mata, ko a mafarki bata taba kawo kanta cikin wannan halin ba......


? #OneLuv=ؕ?
[1/12, 9:39 AM] Maryam: =??? *JALILAH* =???


Written By : *AYUSHER MUHD*
Wattpad: *Ayusher Muhd*


*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*


*66*

A hanya hannunta ya jawo ya rike yana tuki da daya hannun, shiru tai kawai tana tunanin yanda taji haushin mutumin nan sanda ruwa ya daketa, lalai inkaga mutum ka kalleshi, ikon Allah baya karewa a rayuwarnan.

Kallanta yai yace  me kike tunani?

Tace  kawai!
Yace  ni sai yaushe za a fara mannemin kamar yanda akema Goggo?

Ta kalleshi sannan ta sunkuyar dakai tace  manne mata nake?

Yace  umm, gashi ni kuma abin birgeni yakeyi, a taimaka a faramin irin shi.

Dariya tai tana kallanshi tace  lalai yaya! Nikam bansan ya nakeyi ba.

Hade fuska yai tare da sakin ajiyar zuciya yace  ya zanyi? Da alama sai na jira.

Tace  sai ka jira me?
Kallanta yai tare da kara hade fuska yace  ya na iya?

Shiru suka danyi har sukai tafiya mai dan nisa kafin yace  Jalila haryanzu bakiyi tunanin komai akan maganar Abba ba? Yai maganar yana murza hannunta.

Ta kalleshi cikin kulawa tace  ko kara kawoshi a raina ma banyi ba, ai na fada ma duk yanda kace haka za ayi.

Iska yadan furzar kadan yace  ina san mubar gida mu zauna mu biyu amma bana sha awar barin kasata, sannan banasan tafiya nabar family na.


Shiru tadanyi kafin tace  ka duba kaga abinda ya dace, ni duk abinda ka yanke daidai ne a gurina.

Kallanta yadanyi kafin ya karkatar dakan mota kan layinsu, yace  nagode Jalila, na tabattar akan dukan lamurana yanzu am not alone.

Murmushi tamai tare da saukar da idanta kasa.

Cikin gidan suka shiga yai parking din motarsa tare da kashe ta, kallanta yai yace  muje ko?
Tace  hannuna...
Yace  au.

Sannan ya saketa, kallansa tai tace  na dauka yanzun ma cemin za ai, kin tabbatar ba ke kike san na rikeki ba?

Tai maganar yanda yake magana, girman idanunsa yadan rage yace  haka nakeyi?

Tace  eh mana.
Yace  sakemin naga?

Tai gyaran murya kadan tace  kin tabbatar ba ke kike san........
Bakinta ya sumbata tai saurin zaro ido tare da kallansa, sannan ta waiwaiga wajen window, yace  ya akai? Kunya kike?

Tace  yaya? In wani ya ganmu fa?
Yace  hmm to menene a ciki? Mukai a wajen gidan goggo ma bare cikin gida?

Da sauri tasa hannu ta toshe ma baki tace  oh ni Habiba!

Kafadarsa ya daga alamar ko a jikinsa kafin ya nunamata bakinsa da hannu.

Sakarmai baki tai ta turo bakinta tace  yaya dan Allah ka daina zancen wajen gidan Goggon nan tun kafin mu fada a inda za aji.

Yace  ahh ta ya za ace indaina zancen rana datake special a gurina?

Idanu ta kuramai kamar zatai kuka yace  kinaso na daina?
Da sauri ta daga kai alamar eh.

Yace  tam sai kin min abu goma wanda nace inaso.

Tace  abu goma?
Yace  eh! A duk lokacin danacemiki inasan abu sannan na hade hannayena haka to dole kimin, kin yarda.

Dariya tai kafin tace  lalai yaya tun daga yarintarka kakesan fanshewa, wannan fa abin yara ne.

Yace  sosai, ai dama na fada miki ki shirya, kuka kika ce kin shirya.

Tace  to naji.

Bude mota yai ya fito yana Murmushi, itama ta bude ta fito tana murmushi.

Ba kowa a falo da alama kowa yana daki, sama kawai ya wuce ita kuma tai dakin Ameera.

Kanta tasa a jikin kofar tace  Ameera!

Ameera ta taso ta bude da sauri tace  matar yaya an dawo daga hotel din?

Tace  hotel? Nan mukace zamu dama?

Ta dan daga mata gira tace  ai na gano.

Jalila ta daka mata duka tace  wallahi ke yar duniya ce, uban hotel mukaje ba hotel ba.

Ameera tasa dariya tace  wasa nake miki wallahi, kawai so nake naga na tsokaneki.

Jalila ta harareta tace  su Ummy fa?

Tace  sun tafi daki, ya Sageer ma haka, abincin ku na kitchen.


Jalila tace  ai mun koshi amma bansan ko Yaya zai kara ba.

Ta juya tace  sai da safe.

Ta hau sama.

Hassan ya cire riga kenan tana turo kofa, kallansa tai da sauri ta nemi fita daga dakin.

Da sauri yace  Amarya ina zaki?

Ta juyo tace  na manta akwai abincin mu ne a kasa.

Takowa yai inda take kawai ya maida kofar ya rufe sannan yasa hannu ya rikota.

Tace  Yaya....Abinci....
Yace  ai kinsan a koshe muke ko?

Tace  hmm na dauka...
Saketa yai sannan ya koma ya dauko yar shara sharar shirt ya saka sannan yasa wando three quarter bata taba ganin ya kwanta a haka ba dan da doguwar riga jalabiya yake kwanciya.

Kallansa tai kallan mamaki, yace  ya akai? Kyau na miki?

Tace  nagane... sai kuma tai shiru, yace  da can ma dan karki takura ne yasa nakesa jalabiya amma dama haka nake kwanciya ta.

Jalila tace  yanzu fa?

Takowa yai kusa da ita, tadan yi baya kadan yace  yanzu na san mun zama daya ba maganar takura.

Kallansa tai kawai tai yake sannan ta zauna akan kujera.

Yace  ina kinyi sallah a gidan Goggo?
Tace  eh!
Yace  to ki taho mu kwanta dan bacci nake ji.

Tace  zan danyi tilawa ne tukunna.

Yace  okay to ki shirya ki matso sai muyi tare, ta kalleshi kafin tace  to.


Yaka ta shige cikin mayafi ta canza kaya cikin dabara sannan ta shiga toilet, pant dinta ta wanke ta shanya sannan tasa wanda ta shigo dashi daga falo.
Bazata manta ba a makaranta Zahra take bata labari haka taga yayarta nayi in tazo gida ko a gidanta.

(Mata ba wai sai kince ke bazaki iya wanka ba in dare yayi ba, ko kice inkinyi wanka ma miji zai saki ki sake wani, ko baki yi wanka ba at least change ur pant, wannan abu nada mahimmanci, Please karki sa pant tun safe har washegari yanada babbar illa.)


Jalila na fitowa ta dauko qur ani sannan ta matso kusa da gadon ta hau, sai data biyamai yamata gyara inda ya dace sannan ta rufe qur anin ta ajiye.

Jawota yai jikinsa suka kwanta, luff tai a jikinsa tanajin duminsa, a hankali taji yace  zan daure.

Dagowa tai ta kalleshi tace  da me kenan?

Kwanciyarsa ya gyara yace  ba komai.

Yanda yai maganar yasa ta murmusa.

Yace  dariya kikai?

Dagowa tai ta kalleshi tace  ni? Yaushe kenan?

Da sauri ta maida kanta jikinsa tare da jan bargo.

Shima rufa bargon yai har kansu yana cewa  inji da kunene acemin ba ai ba?

Dariya tasa tace  da gaske fa Yaya ba abinda nai......

(Jinai suna dariya nace hmm bari nai nan kafin Hassan ya fara tunanin wani abu har ya makoni......)
**************


Mumy sam ta kasa bacci daga ya dauketa take farkawa, balle dataga Inna taki farkawa, abinda likita tace mata take tunowa.

 Fatima sai dai addu a, da yardar Allah mun samu numfashinta ya dawo sai dai bamuda ikon sawa ta bude idanunta, sai dai mu dage da addu a sannan a kula da ita sosai, kar a dinga hayaniya a inda take, da alama wani abu mai tsananin mamaki ya faru da ita ne har yasa ta shiga shock haka.

Mumy ta kalli Dr hankali a tashe tace  ba wani abu da ya faru da ita.

Dr tace  bazai yiwu ba, dan alama ce ta taji wani abu wanda ya girgizata har ya santa cikin wannan halin, karfa ki manta bawai faduwa tai ba ko kuma dama batada lafiya ne.

Mumy tai shiru tana kallan Inna, a hankali ta goge hawayenta.

Jitai an dafata ta baya, juyowa tai ta kalleshi hawaye suka zubo mata.

Dady ya tsugunna tare da rungumota jikinsa, yana shafa bayanta alamar lalashi.

Itakam kuka kawai takeyi.

Washe gari suna zaune a asibiti wajen karfr hudu na yamma, Sultan ne ya fara shigowa.

Ajiye basket din da suka kawo kato dauke da kuloli kala kala yai sannan yace  Mumy!

Kallansa tai tace  Sultan Yasmeen fa?

Yace  tana tare da Dady.

Bude kofar da akai ne yasa ta kalli kofar.

Safeena ce ta shigo da gudu ta karaso ta rungumeta kam, atare suka sa kuka, tare da kankame juna.

Mumy ta dagota tace  Safeena? Jiya fa mukai waya.

Tace  Mumy dama na riga ma na sai ticket lokaci, da bakice na taho ba da wani gun zanyi.

Mumy tasa hannu akan fuskarta tace  ya naga kin rame?

Safeena ta share kwallarta tace  Mumy ya ji?????
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
 kin Inna?

Tace  gatanan sai addu a Safeena na ma rasa ya zanyi.

Sultan dake tsaye ya juya kansa saboda hawayenn da suka zubomai......


**************


Ihun da ake yi ana bin motar da gudu ne yasa na ruga da gudu nima dan ganin meke faruwa, kauye ne sosai dan haryanzu mota ba shiga take kauyen ba sai da dalili, dan basuda mutane masu mota.

Goggo ta kurama kauyen ido itakam bataga wani canji ba da aka samu, yana nan kamar yanda ta barshi, duk tsawon shekarun nan kuwa.

Tuno rayuwar datai a kauyen mara galihu ne yasa ta yin shiru tana bin yaran dake bin motar da kallo.

Ita da kanta ta dinga nuna layin, har suka je.

Katon gida ne na gaske amma fa ba katon da kuke zato ba, kato na yawa nake nufi.

Duk wanda zaiyi aure a cikin gidan yake zama.

Mata gasunan kacha kacha, yara kusa kamar kaje wani taron.

Ganin mota ta tsaya a kofar gidan wasu da ke cikin masu bin motar wadanda suka kasance a gidan suke suka kwalkwala da gudu gidan dan sanar musu.

Kankace me sai ga mata manya ana leka katanga dan ganin abinda ke faruwa, yara maza kuwa har sun gangara gona da gudu wasu sunyi majalisa dan kiran iyayensu maza dan suzo suga abinda ke faruwa a garin nasu.

Abba mota ya bada makekiya mai masifar kyau motar da ko a birni inkaga mutum da ita to fa lalai ya isa ne, shikansa Abba ba hawanta yakeyi sosai sai inza ai abu mahimmi yake hawanta.


Goggo ta kalli matan dake ta lekowa ta katanga duk bata sansu ha sai guda biyu wandanda suka kasance matan yayanta maza ne.

Mamman ya juyo yace  nan ne ko?

Tace  eh nan ne, sannu da kokari mungode fa.

Yace  karki damu Hajiya, ki shiga kiyi abinda zakiyi a nutse inyaso da yamma sai mu koma.

Tace  har yamma? Kai kuma fa?

Yace  karki damu dani, zan gangara garin misau na samu abinci naci na jira ku, in kun gama sai ki kirani.

Tace  to, ta mikamai wayar tace  samana lambarka ko?

Ya amsa ya saka, yai saving sannan ya nuna mata taba Lanta tace Lantana ki kalla yanda ko na kasa ganewa zaki nunamin, tace  to.

Ta amsa ta gani sannan ta bata.



*************

Baki a sake ya tsaya yana kallan titi, me ya gani yanzu? Anya kuwa ba gizo idanunsa suke masa ba? Yanzun nan Yasmeen ke damunsa akan ice cream sun fito shiyana tunanin yanda zaiyi ya kwaci matsayin da yakeso a company dinsu, ya tsaya a gun bada hannu kawai yaga daga gefensa wata katuwar mota.

Kallan motar yai saboda kyan datamai, daidai lokacin da aka dan zuge glass din baya kadan, hakan kuma yayi daidai da bada hannun da akai, sai dai ana zuge glass din nan ya hango wata mace kai kama da Goggo, bai kara kare mata kallo ba motar tai gaba.

Kansa ya girgiza da sauri tare da cewa  lalai na fara haukacewa.

Yasmeen tasa kuka kallanta yai yace  menene kuma?

Ice cream dinta daya zube ta nunamai tana kuka tare da bua kafa, haushi ya kamashi yace  dan ya zube shine zaki dinga kuka haka?

Ganin yanda yake mata fada abinda bai taba yi ba yasa ta sa kuka sosai.

Yanda yaga ana kallansa ne yasa yai saurin daukanta yana cewa  sry muje a siyo wani, shikenan?

Kwanciya tai a jikinsa tare da ajiyar zuciya.

A ransa yace  yara duk an batasu da sakalci.

(Nace kuma>???)



#OneLuv=ؕ?[12/30/2018, 9:50 PM] El-hajj: =??? *JALILAH* =???


Written By : *AYUSHER MUHD*
Wattpad: *Ayusher Muhd*


*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*


*67*


? Dady yana tuki yana tunani harya isa asibitin, Mumy na zaune akan kujera kusa da Safeena tanata tambayarta rayuwar datai,? jefi jefi Mumy na share hawayenta dan tausayin yarta, tace "kiyi hakuri Safeena, ni a guna gata muka miki, sai dai daga baya na gane ba gata muka miki ba."


Safeena tana kuka tace "yanzu Mumy ina Jalilan?"

Mumy ta kalleta tare dayin ajiyar zuciya na takaici tace "Jalila tafi karfin mu, tafi karfinki, yanzu tana wani matsayin da muke neman alfarma da taimako a gurin ta."

Safeena cikin mamaki tace "ban gane ba Mumy?"

Shigowar Dady ne ya hana mumy bada amsa, Yasmeen ta rugo gun Safeena da gudu tare da fadawa jikinta, Safeena ta kankameta tana hawaye.

Dady ta kalla sannan ta mike tazo kusa dashi ta rungume shi tana kuka.

? A hankali ya dagata sannan yace "Saukar yaushe?"

Tace "dazu na iso shine akace su Mumy nanan muka taho da Sultan."

Ya kalli Mumy sannan yace "ya mai jikin?"

Kai kawai ta girgiza alamar ba labari.
Ya kalli Safeena yace "ki huta zanje na dawo."

Ya janyeta ya fita waje, yana fita ya tsaya a jikin katangar dakin yai shiru, ba dai yanzu opportunity bane ya bude mai bai sani ba? Kila Allah ne ya dubi zuciyarsa da yanda yai musu wahala ko shiyasa Allah ya kwantar da ita dan ya samu abinda yake so? Lalai yanzu kam ya gama sanin Allah ne yake sanshi da rahama.
Da sauri ya dau waya ya kira babban board director na company dinsu.

Yana dagawa yace "Abakar ne."

Cikin mamaki yace "Abubakar kana lfy?"

"Lfy kalau dama kira nai na fadama Hajiya ba lfy she is unconscious."

Fuskarsa dauke da mamaki yace "Subhanallah garin ya ya?"
Cikin muryar damuwa yace " wlh sai Allah, muna asibiti."

Yace "ba kanta, gashi munada meeting jibi monday."

Yace "bansan nima ya za'ai ba."
"Tunda kaine sirikinta sannan next in line ai kawai sai kai kazo."

Yace "ta inaxan zo, kamar bai kamata ba."
"Bai kamata ba kamar ya? Dama Hajiya ai ta girma akan running din company yaci ace tun yaushe tayi resigning, sai mun ganka."

Kafin Dady yai magana ya kashe.

Dady yai dariya yace "ikon Allah! Cikin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login