Showing 51001 words to 54000 words out of 149705 words

Chapter 18 - Jalilah Book One Complete Hausa.doc

Ayusher   

28 Oct 2025

614

iya kokarinta na ganin Jalila ta saki jiki da gidan.
Sagir kam baifiya ma zama ba saboda hankalinsa tashi yake inyaga Jalila.

? A hankali ta turo kofar, yana kwance a kan gado yana karatu, ta rasa mai yasa ita ko irin wayarnan taga yanayi ko yana dannata bayayi.
Shiga cikin dakin tai ta tsaya tana dan wasa da hannunta.
Bai kalleta ba bakuma tasa ran zai kalleta din, hakan yasa ta matso kusa dashi kadan.
Nan ma bai kalleta ba, daurewa tai tace "Umm Yaya!"

Bai kalleta ba yace "menene?"

Tana wasa da hannunta ta rasa mai zatace, ganin batada niyyar magana yasa ya cigaba da abinda yakeyi.

Jalila kam ganin tsayuwar bamai karewa bace gashi ita tasan zata iya fadama Sagir sai dai ta ina zata fara kebewa dashi ta sanar mai? Sannan mai zaiyi tunani? Gwara dai Hassan din tunda koma menene at least yasan wani abin na daga rayuwarta.

Ganin haka ma sai ya mike yadau waya da key din motarsa yana neman fita.

Cikin hanzari ta riko gefen rigarsa, tsayawa yai sannan ya juyo ya kalleta sannan ya kalli rigar tasa inda ta rike.
Tace "Hmm Yaya magana zamuyi."

Da kai ya mata alama da yanaji, ta sakeshi sannan ta tsaya.
Yace " in baka san me zakice ba ni zanyi gaba."

Jalila tana gani ya juya ta kara riko rigarsa da sauri, kallanta ya juyo yai sai dai yanzu yanayinsa yadan canza yace " meke nan?"
Tace "Yaya!"

Matsowa ya fara yi tana matsawa baya, tsoro ya fara ratsa mata har sai da sukaje jikin gado ta fada kan gadon, gani tai ya rufo kanta, tsoro da fargaba suka kamata, idanunta suka firfito ganin namiji akanta haka.

Idanunta ta runtse gam cikin tsoro, can taji shiru, a hankali ta bude idanunta a tsaye ta ganshi yace "2minute na baki."

Tace "Yaya......"
Yace "will you stop calling me?"

Magana nace kiyi ba kirana ba.
Ta daure tace "Yaya bansan ya zanyi ba."
Ya kalleta alamar me take nufi.

Tace "maganar Goggo."
Yace "to menene nawa a ciki?"
Tace "naam?"
Yace "menene nawa a ciki da kike fadamin?"

Shiru tai dan batasan me zata ce ba, agoggon hannunsa ya kalla yace "minutes din da na baki sun cika."

Ya juya ya fita tana kallansa, ajiyar zuciya tai tace "Jalila u are really a fool."

Shikam yana fita ya sauka kasa zai fita, Ummy ce ta leko daga daki tace "Hassan?"
Kallanta yai sannan ya matso yanasan jin menene, ta kalleshi tace "ina zaka kuma?"
Yace " fita."
Shiru tai alamar damuwa wanda yasa yace "menene?"
Tace "Hassan na rasa meke damun Abbanka."

Kallanta yai cikin kulawa, sai dai baisan ta ina zai fara jin matsalarta ba, yace " Me yayi?"

Ta girgiza kai tace "bakomai, jeka kawai amma dan Allah ka dinga zama a gida kaga Ameera tunda taje gun Aina'u bata dawo ba, Sagir kuma na rasa me yakeyi yanzu sam ya rage zaman gida, ni kuma kasan dole tadingajin nauyi na, ka taimaka ka dinga zama ko da ba lalai ka yarda kuyi hira ba at least dai zataji motsinka a kusa da ita."

Kallanta yai kawai bai amsa ba sai cewa dayai "Abban me ya miki?"
Tace "me zaimin kuwa? Kawai dai naga ne kamar akwai abinda ke damunsa" dan tasan intacemai ya canza mata gaba daya, ya daina zaman gida, ya daina zama suyi hirar business data duniya lalai tafi kowa sanin halin Hassan, abin ne ke cinta yake damunta shiyasa ma tamai magana.

? Kallansa tai tace "sai ka dawo."
Tai saurin komawa daki, haryakai jikin kofa sai naga ya juyo ya kalli sama sai kuma ya fita.

?? Jalila ta zauna a kasa ta baza tagumi, takaicin kanta duk ya isheta, sai yamma ta sauko.
Kofar Ummy taje ta kwankwasa, Ummy ta fito sanye da hijab da alama sallah ta idar.

Jalila tace "Ummy me za'a dafa?"
Ummy tai murmushi tace "dauko hijab dinki mu fita cefani.
Jalila cikin mamaki tace "Cefane Ummy?"
Gani tai tunda tazo gidan bata taba gani anje cefane ba masu aiki ne ke siyowa.

Ummy tacemata yi sauri.
Jalila ta juya zuwa sama, hijab dinta ta dauko sannan ta sauko.
Ummy ta daga waya tace "Dan Ummy ka iso?"
Yace eh, nan suka fita.

Sagir na tsaye jikin mota yana hangosu ya fito ya bude musu baya yanama Ummy salute.
Ta harareshi tace " Officer ka iso?"
Yace "barka da isowa."

Jalila tai dariya tana kallansu abin sha'awa, bata taba gani mace mai saukin kai kamar Ummy ba, tasan itakan Goggonta kadai ta sani sai yanzu dataga Ummy.

? Suka shiga baya dukansu, Ummy tace "Driver mu fara zuwa Wellcare.
Nan suka tafi ahanya sai hira sukeyi, Jalila kam sai dai tai murmushi sai in an tambayeta tace eh ko a'a.

? Ummy kam ta fito ne dan ta debe musu kewa da ita da Jalila, dan tasan Jalila na bukatar kulawa, ita kuma saboda gudun tunani da zargi yasa take neman abinda zai debe mata kewa.

? Haka sukaje sukai siyayya sosai, sannan suka biya shagon wayoyi, Ummy da kanta ta zaboma Jalila waya irin ta hannunta Sumsung ce Note 9.

Jalila kam gaba daya ta rasa me zatace, dan itakam batasan ta inda zata fara magana ba.
Sagir kam dadi yakeji ganin fuskar Jalila na dauke da murmushin da yake har zuciyarta bawai na iya baki ba.

?? Haka suka isa gida sannan sukai abinci ta dau nasu ta hau sama, yau kam zuciyarta ta ragu da damuwa, sannan ta kara samun karfin gwiwar yima Hassan magana.
Bayan isha'i ya dawo ta jawo mai abinci kusa dashi, Hassan ya kalleta yace "nasha yogurt, later."

Jalila ta dauke tasa a gefe, zama tai a kan gadon daga inda kafafunsa suke can karshen gado, ta mikomai wayarta.
Kallanta yai sannan ya amsa, yace "na meye?"
Tace "Ummy ce ta saimin."
Ya juyata sannan ya mika mata yace "to."
Tace "bakasa number ka ba."

Yace "me zakiyi da ita?"
Tace " In wani abin ya taso."
Ya kalleta yace "kamar me?"
Wayarta ta amsa tace "shekenan kawai kace dai bakasan sawa."

Kallanta yai yace " kawo dai."

Ta mika mai tana dan tabe baki kadan kanta a kasa, ya amsa yace "in zaki harareni ko murgudamin baki, ko tabemin baki ki tabbatar kinyishi ina kallo dan ko ban kallekiba ina sanin inkinyi hakan.

Jalila ta kalleshi tace "ni banyi komai ba."
Wayar ya mika mata yace "yi saving."
Ta amsa tasa "Yayah."
Sannan sukai dan shiru, can tace "Yaya me zanyi in taimaki Goggona?"

Kallanta yai yace "zancen dazu ne?"
Tace "eh, na gane dazu na fara ma magana ne kamar i am hopeless bansan me zanyi ba, bani kuma da plan."

Littafin sa ya dauka baice komai ba, saukowa tai kasa ta tsugunna a kusa dashi tace "Yaya dan Allah ka taimakeni."

Littafin ya ajiye yana kallanta...........


#OneLuv=ؕ?


=??? *JALILAH* =???

Written By : *AYUSHER MUHD*
'ote me on Wattpad : *Ayusher Mohd*


? ?? *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*
? (_D home of expert and perfect writer's_=ء?)


*31*



? Kallanta kawai yake baice komai ba, ta dago tace " Yaya Goggona......"
Sai ta kasa karasawa saboda kukan daya kwace mata, kallanta yake baida niyyar tanka mata, balle ya lalasheta.
Sai dai yanayin kukan da takeyi ya fahimci lalai she is desperate.
Yace "in kuka zakimin zan iya tashi in fita."

Ta share hawayenta tace " bansan ta inda zan fadamaka halin da Goggona take ciki ba."
Yace "ban tambayeki wannan ba, abinda kawai nakesan naji me kike tunanin yi, sannan me kikeso nayi miki?"

Ta mike da sauri tace "Yaya zaka taimakeni?"
Kallanta yai sannan ya juya kansa, shiru tai kafin tace " Bansan me zanyi ba."

Yama rasa mai zaice hakan yasa ya sa hannu zai dauki littafinsa, da sauri ta rike littafin.
Kallanta yai tace "Please!"
Yauce rana ta farko a rayuwarta da take roko da neman taimako akan 'yancinsu, aduk lokacin da aka musu abu a da sam bata kawo komai sai takaicin yanda ake wulakantasu, amma bata taba tunanin zata kwaci kanta ba, itadai kullum fatanta tai aure ta dauke Goggonta.

Hassan yace " in bakida abin cewa ki bari sai kin samu sai kimin magana, bance zan taimaka miki ba bare kisa ran zanyi, na dai ce ki fadamin ne kawai inji ko zan iya, i hate meddling in someone's life."

Bata saki littafin ba tace " Ban taba tunanin nima har akwai lokacin da zan nemi taimakonka ba, ganin halayenka, sai dai kai kadai ne a duniya a yanzu da zaka iya taimako na, Yaya dan Allah."

Yace " bai dameni ba, Ita mamar taki haryanzu suna tare da wanda ya haifeki ne?"

A ranta tace "ina laifin kace mamanki da babanki?"
Amma a fili tace "eh sai dai bansan wani irin zama ake ba wanda maganar mutunci bata hadasu."

Littafinsa ya kwace yace " to meye matsalar?"
Tace "naam?"
Yace menene matsalar ta koma gidansu mana."

Jalila ta kalleshi jiki a sanyaye, kallanta kawai yai wanda hakan ya nunamai can din ma dai ba magana.

Ya dade baice komai ba wanda har jikinta yai sanyi kafin taji yace "ki shirya gobe muje ki dubata."

Da sauri ta kalleshi sam hankalinsa baya kanta ya maidashi kan littafi, kamar bashi yai maganar ba,
Tace "Bansan asibitin da suka canza mata ba."
Bai tanka mata ba, tace "Yaya in mun dubata sai me zamuyi?"

Yace "later."
Tana shirin magana ma sai taga ya mike ya wuce toilet, ajiyar zuciya tai tace "kai wannan matarka ta shiga uku."
Sai tai shiru tace au ahh ashe fa nice ko?
(Nace kila nice.......lol)

? Mikewa tai ta fito tana cewa "da alama bai fahimci ina na nufa ba, ni ba dubata nakeso ba, darajarta nakeso su sani balle har su kara tunanin rainata."

? Haka ta fito ta sauka kasa, tana san yima Ummy saida safe.

Tasa hannu zata bude kofar taji muryar Ummy tace " wai meke damunka ne? Bansan me yasameka ba yanzu komai sai ka fara neman yin fada,? scammers ka hadu dasu ne ko me?"

Yace " ke ce yanzu bansan meke damunki ba, bansan yaushe kika fara takura haka ba, dolene sai naci abincin......?

? Jalila ta juya da sauri a ranta tana cewa " mekenan?"

Komawa tai sama da sauri, bayan sunyi sallah sannan taga yadanci abinci kadan, a ranta tace "in mace tayi ba wani abu amma namiji?"

Hassan ya hau kan gado ya zauna ya dau jornal dinsa, a ranta tace "wai baya gajiya? Daga zama da karatu sai fita?"

Wayarta ta dauka tana dan lalatsawa, lalai ta kosa gobe tayi ta nunama Goggo wayarta, amma zasu ganta kuwa? Bayan basusan sunan asibitin ba? Kallansa tai tanasan kara mai magana amma ta kasa.

? Meya faru tsakanin Ummy da Abba? Ta fada mai? Can tace "hmm wannan mutumin? Salan yace gulma naje yi?"

Kafa yasa ya tura bargon dake kan gadon zuwa kasa.
Jalila ta kalleshi, ganin ba alamar shi yayi yasa ta dauko bargon ta na neman maidawa kan gadon, yace "in kinaso kiyi amfani dashi."

Da sauri ta kalleshi tace "dagaske?"
Bai tanka kata ba, ta dauka tana murmushi ta shimfida, ta hau ta luluba da bedsheet ga pillow yaukam kwanciyar ta mata dadi, wayarta ta dauko tana kara latsawa.

Haka tai ta latsa wayarta har tai bacci.

? Juyowa yai ya kalleta, gani nai ya kura mata ido daga inda yake, kamar yana nazari akan wani abu.

Can sai naga ya gyara ya kwanta, bai dade ba bacci yai gaba dashi.


? Washegari ma Alhamdulila anyi sa'a abin nasa bai tashi ba, bayan yayi alwala yasa kafa ya dan buge ta dan dama haka yake tashinta.

Idanu ta bude ta kalleshi, kallanta yai sannan ya mata alama data mike, Jalila ta tashi ta dauke da bargon daga gun, ga fili nan a dakin amma shidai anan yake sallah.

Toilet ta shiga shi kuma ya tada sallah.

Sai wajen karfe 7 ta tashi ta kasa ma baccin saboda ta matsu ya tashi su tafi gun Goggo, saukowa kasa tai dan fara aikin abinci saboda yana tashi itakuma ta gama komai sai tafiya.

? Ganin dakin Ameera tai a bude, a ranta tace "ta dawo ne?"
Dakin ta nufa ta kara tura kofar, me zata gani?
Ummy ta gani a kwance tana barci.

Meke faruwa?
Badai fadan da sukai jiya bane haryakaisu ga haka?

Gyara kofar tai ta juya a hankali tabar gun ta nufi kitchen.

Aikin breakfast take amma sam hankalinta nakan Ummy, ta rasa meyasa batasan wani abun ya bata mata rai sam.

Tana aiki har masu aikin gidan suka zo, suna fara kwankwasawa ta fita da sauri ta bude musu kofar, bataso a tashi Ummy.
Gaisheta sukai sannan suka fara aikin shara da gyare gyare, saboda girman kasan.

Sagir ne ya fito ya hangota a kitchen tana ta aiki, tsayawa yai yana kallanta inama matarsa ce? Da yanzu zuwa zaiyi kawai ta bayanta ya rungumeta.

Da sauri ya fara a'uziyya saboda neman tsari daga shaidan, komawa ciki yai da sauri ya zauna a gefen gado sannan ya kwantar da kansa kan pillow.

Ummy kam sai wajen takwas da kwata ta farka, kallan agoggo tai cikin mamaki, wani irin bacci tai haka? Shiru tai tana tunanin abinda ya faru itada Abba a daren jiya.

? Bayan ya dawo tanemi ya fito falo yaci abinci, tunda haka suka saba.
Kallanta yai yace mata "bayajin yunwa."
Tai murmushi tare da ajiye jakarsa tace "haka ka koshi a waje ne da alama."

Ganin sun saba irin wannan abin bata daukeshi a komai ba, sai cewa?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? yai ban gane na ci a waje ba? Me kike nufi? Gun wata naje ta bani ko me?
Mamaki ya kama Ummy tace "meye hakan? Ai kafi kowa sanin ba hakan nake nufi ba."

Ai kuwa ya kara hawa wai ta rainashi, nan ya fara masifa ta inda yake shiga bata nan yake shiga ba.

Haushi yasa ta fito tabar mai dakin, ajiyar zuciya tai sannan ta mike, ta fito falo.

Tayi mamakin ganin masu aikin har sun gama shara suna mopping.
Can tai tunanin Sagir, murmushi tai sannan ta nufi kitchen.

Jalila ta hango tana aiki, da sauri ta karasa tace "Jalila?"
Jalila ta juyo tace "Ummy ina kwana?"

Ummy tace "Jalila? Yaushe kika tashi haka?"
Jalila tai murmushi tace "kije ki zauna Ummy na kusa gamawa ma."

? Tace " banyarda ba bari naje na dawo dai."
Ta juya ta nufi dakinta.

? Shikansa bai samu barcin arziki ba, dan bayan ta tafi abin duniya ya dameshi, ya rasa mai yasa yake saurin hawa akan kome ta masa wanda ya tabbatar basai wani abin bane, ya rasa meke damun zuciyarsa da yanzu duk abinda Ummy tai matar da yake ganin kimmarta a rayuwarsa bata birgeshi yanzu.
Zaliha.......
Duk sanda wannan sunan yazomai saurin mikewa yake yana girgiza kai, bai isa ba, ta ina zai fara yima Ummy butulci? Yasan bazata taba hanashi aure ba dan macece mai class da sanin rayuwa wacce sam batasan fada balle musu, to amma yarinya sa'ar danta? How can he?

Yana kallanta ta shigo ko kallansa batai ba ta shiga toilet, can ta fito ta bude wardrobe ta dau abu zata fita.
Yace "Hajiya! Ina tunanin zuwa Bauchi gobe."

Tace "Adawo lafiya."
Ta fita.

Adawo lafiya?
Ita kuwa tana fita tai kitchen gun Jalila, tare suka karasa aikin.
Jalila tace "Ummy bari na hau sama."
Ta fada tare da saurin yin saman.

Hassan ya farka ta turo kofar dakin, kallansa tai tace "ina kwana?"
Bai amsa ba, tace "bari na shirya."

Ya daga kai alamar to, juyawa tai tadau towel tai cikin bandakin sanye da kayan jikinta.


#OneLuv=ؕ?


=??? *JALILAH* =???

Written By : *AYUSHER MUHD*
'ote me on Wattpad : *Ayusher Mohd*


? ?? *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*
? (_D home of expert and perfect writer's_=ء?)


*32*


? Kallansa tai bayan ta fito cikin zumudi tace "Yaya na fito ka shiga wanka."
Yace "in nayi wanka me zan miki? Ko dama ke kike sani yin wanka?"

A ranta tace "hmm wannan mutumin?"
Amma a fili tace " a'a gani nai zamu fita."
Yace "zuwa inafa?" Ya fada yana gyara gadan daya kwanta dan shi kam badai gyara muhalinsa ba."
Jalila da sauri ta fara tayashi ta dayan bangaren tana cewa "jiya fa kace yau zamu."
Yace "yau din ta kare ne?"


Baki tadan turo mai mutumin nan yake da ita?
Hassan ya matso kusa da inda take a tsaye, hannu yasa ta bayanta ya dauko wani littafi sannan ya koma kan kujera ya zauna.
Jalila ta tsaka sakato tana kallan ikon Allah, amma mutumin nan....
Cikin takaici ta fita waje tana wata irin tafiya, bugo kofar tai sannan tabi kofar da kallo, dama ita tasan ba lalai ya taimaketa ba.
Da alama Uncle kawai zata fadama, haka ta zauna a kujera ta kuna Tv.
Shikuwa tunda ta fara cika tana batsewa yake kallanta ta gefe ido, da ta fara wata irin tafiya kuwa tsayawa yai yana kallanta harya banko kofar.
Mai zan gani? Hassan naga ya murmusa sannan ya girgiza kai.
Shikansa bai fahimci murmushin yai ba saboda rabansa dayai murmushi ko dariya har ya manta.
Amma tabas yau kam da saninsa ya kular da ita, dan ya fahimci wani sabon zumudi da takeyi.

Ajiye littafin yai sannan ya mike ya shiga toilet, yana fitowa ya dauko jeans da shirt yana shirin sawa, baisan msi ya tuna ba sai naga ya cire ya dauko farin yadi mai shara shara ya sa.
Bayasa hula dan haka ko dubata ma baiyi ba.
Zama yai ya bude tiren data ajiye.
Kallan plate biyun dake gun yai, kenan bataci abinci ba?

A falo taji yunwa ta kamata ta turo kofar daki fuskarta a hade, kallanta yai sannan ya dauke kai kamar bai ganta ba.
Ganinsa a gaban abinci yasa ta tsaya turus tana kallansa.

Kallanta yai yace " Kin fasa zuwa ne?"
Da sauri tace "zamu?"
Kallan abinci yai sannan ya kalleta, da sauri ta matso tana dariya, duk yanda taso ta boye farin cikinta ta kasa.

Shikam ya hade rai yana kallan ikon Allah, shi ta fara zubama sannan ta zuba nata.
Dan kadan taci ta fara neman mikewa, kallansa tai taga shima kallanta yai fuskarsa a daure.
Da sauri ta koma ta zauna tana kara cin abincin.

Yana mikewa kuwa itama ta mike, gani tai ya koma ya zauna akan gado.
Tace "Yaya na......"
Kasa karasawa tai sai ta wayance tace "Yaya naga bakasha tea din ba, ko na kawoma ruwa?"

Yace "later."
Juyawa tai ta fita, kallanta yai sannan ya mike ya dau key din mota ya dau wayarsa.

? Sannan ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login