Showing 96001 words to 99000 words out of 149705 words

Chapter 33 - Jalilah Book One Complete Hausa.doc

Ayusher   

28 Oct 2025

637

da ke zuba daga kansu.
Inaji mai motar na tambayar waye ya sansu amma bakina ya kasa magana saboda numfashina da yake hawa da sauka, kaina na wani irin juyawa saboda jinin dake kwaranya.......
Kansa ya matse da karfi wanda ke mai wani irin azaba, Jalila kam hawaye duk ya gama jika mata fuska.
Matsowa tai tasa hannunta akan kafadarsa tace "Yaya?"
Hannunta ya dan ture tunda ya fara labarin sai yanzu ya juyo ya kalleta fuskarsa gaba daya ta canza, bata taba ganin Hassan haka ba, yace "Nine sanadiyar rasa rayukansu, wanda haryau kanin Abba Allah bai kara bashi haihuwa ba, wanda ranar sunan Ameera ya zama ranar rasuwar yayana, wanda nai sanadiyar mutuwar daya daga cikin farin ciki Ummy, farincikin mahaifina sannan farinciki na, bancigaba da makaranta ba saboda na dade a asibiti a kwance, sai dana samu sauki ne Abba ya kawo wani gida yana koyamin, a haka da kyar Ummy ta sani nai exam din waec daga nan ban cigaba da komai ba.
Nine sanadi, Taya zan samu farinciki a rayuwata? Taya zanyi murmushi a rayuwata, tunda abin nan ya faru har yau basusan nine sanadi ba, sai dai kowa tausayamun yake akan rashin dan uwa nane yasa ni canzawa haka? Na lalata farincikin kowa na lalata.......:"
Kansa ya kifa akan sityarin mota yanajin wani abu na ratsashi.
Ya dade a haka kafin yace " ki shiga gun mahaifiyarki, bancancanci samunki ba, bancancanci samun farinciki ba."
Shiru tai tana kallansa sai hawaye dake zubo mata wanda kamar korosu akeyi, hannu tasa ta bude kofar motar ta fita.
Idanunsa ya runtse da karfi yasan za'ai hakab sai dai zuciyarshi ce ta sake zafi dayaji ta fita, hakan shine daidai shikuma yanzu rayuwarsa sai tafi tada dan ta riga ta shiga rayuwarsa wanda yanzu ya tabbatar cireta babbar gibe ne a gareshi.
Jiyai ta sake bude motar, dagowa yai ya hade rai sannan ya kalleta.
Yanzu kam gaban mota ta bude gefensa ta bude, kallanta yai sai dai baice komai ba, Jalila ta shiga ta zauna sannan ta rufe motar, kallansa itama tai sannan tace " Inyi magana?"
Kallansa yai kallan mamaki, tace "ka fadi duk abinda ke ranka ni baka barni na fadi nawa ba."
Yace "kamar ya kenan?"
Shiru tai kafin tace " yaya kana tunanin dan Uwanka abinda yakeso kenan?"
Kallan tambaya ya mata, tace "yanzu in yasan saboda shi ka maida rayuwarka haka kana tunani zaiyi alfahari da hakan?"
Idanu ya kura mata, tace "yaya kana yaro lokacin sannan ba da saninka bane......."
Da sauri ya juya kai ya bude kofa yana neman fita, da sauri tasa hannu ta riko hannunsa.
Juyowa yai ya kalleta tace "inhar kanasan in tafi zan tafi, sai dai inhar akan dalilan nan ne hujjajun basu karbu ba."
Kallanta yakeyi, murmushi tamai tace "wace irinn rayuwa kai zuciyarka na dauke da abubuwan nan?....."
Batai auni ba ya jawo hannunta ta fada jikinsa, kankameta yai tsam, yanajin wani abu na ratsashi, duk da gabanta dake faduwa a hankali tace " meyasa kake tunanin su Ummy zasu ga laifinka akan abinda ya faru?"
Idanunsa ya lumshe kawai, bayansa tadan shafa alamar lalashi tace "Yaya kaine abin tausayi ba su Husain ba, su kansu na tabbatar da zasusan abinda ka aikatawa kanka bazasuji dadi ba."
A hankali ya dagota daga jikinsa kallanta yai, ita kanta kallansa takeyi, sai dai ganin kallan da yake mata yasa ta saukar da idanunta kasa, ya rike fuskarta da hannayensa yace "Jalila kinfi kowa sanin halina, inada dizgi? Shariya? Rashin san magana? Rashin iya magana? Rashin iya hulda da mutane? Kin tabbatar zaki iya zama zama dani?"
Shiru tai tana kallansa, sai dai a wannan lokacin ta tabbatar bazata iya bijire masa ba, batada tabbas akan ko tana sanshi sai dai bazata iya musa mai ba, kai ta daga a hankali.
Kansa ya sunkuyo a hankali saitin bakinta, yakai labbansa kan nata.
Labanta ya tsotsa kadan sannan ya dago ya kalleta yace " banasan na zama nine sanadiyar ruguzamiki rayuwa."
Idanunta ta lumshe dan wani abu taji yana ratsata, a hankali ya kara kai bakinsa cikin nata, wani salo yake mata wanda yasa taji gaba daya kanta na juyawa, wani abu na ratsata har cikin kanta.
#OneLuv=ؕ?
[12/7, 9:54 PM] El-hajj: =??? *JALILAH* =???
Written By : *AYUSHER MUHD*
'?ote me on Wattpad : *Ayusher Mohd*
*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*
(_D home of expert and perfect writer's_=ء?)
Trauma is defined by the American Psychological Association (APA) as the emotional response someone has to an extremely negative event. While trauma is a normal reaction to a horrible event, the effects can be so severe that they interfere with an individual's ability to live a normal life. In a case such as this, help may be needed to treat the stress and dysfunction caused by the traumatic event and to restore the individual to a state of emotional well-being.
Some common sources of trauma include:
Rape
Domestic violence
Natural disasters
Severe illness or injury
The death of a loved one
Witnessing an act of violence e.t.c.
Idan muka duba abinda ke rubuce a sama, zai bamu damar cikaken fahimtar matsalar Hassan, Trauma na ganin mutuwar kaninsa da yake tsananin so sannan da Guilty na laifin da yake tunanin shine sanadiyar yin hakan, kafin na fara rubuta matsalolin Hassan sai danai bincike akan matsalar cutar Trauma wanda ke damunsa, na dauko bayanin sama ne saboda mu fahimci matsalarsa musan me ake nufi da wannan kalma ta Trauma, akwai mutane dayawa dake dauke da wannan matsalar sai dai bama damuwa da abinda ke damunsh saboda rashin sanin matsalarsu, wasu cikin bacci zakaga suna razana, wasu kansu ke daukar zafi, wasu duk sanda sukaga jini, duk wadannan na faruwa ne a yayin da sukai karo da wani mumunan abu wanda ya taba ayuwarsu yakan hanasu yin rayuwa yanda ya kamata.
Allah ya mana mai kyau ameen.....
*54*
A hankali ya dago ya kalleta, itama ta bude idanunta.
Kallansa tai sannan tai saurin saukar da idanunta kasa, ta zame daga jikinsa ta koma ta zauna akan kujera, karamin gyaran murya yai na burin kunya yace " zaki shiga ku gaisa da Goggo?"
Bata kalleshi ba tace "a'a."
Tada mota yai sukai gaba, shiru ne ya ratsa motar ba wanda ya sake magana.
Sunyi tafiya sosai, kafin ta daure tace " Yaushe kuma Ya Sageer din ya dawo?"
Yace "Sageer? Bayan abin ya faru ne hankalin su Abba ya tashi shine suka nemi alfarma akan a dawo dashi, ko hankalina dana Ummy zai kwanta, dakyar dai suka amince."
Ta dan kalleshi tace " Yaya na kasa fahimtar abu daya, me yasa kafi damuwa da Ummy kadai? Dan na kula yanda ka damu da Ummy baka damu da Abba ba."
Kallanta yai sannan yace "haka kike gani?"
Tace "bani kadai ba hakan ne ma."
Shiru yai har kamar bazaiyi magana ba sai yace " Abba a koda yaushe in na ganshi nakanji tsananin tausayinsa, nine sillar rasa dansa da kuma dan kaninsa sai dai yanda yake nunamin so shine ke damuna, i have to be cold to him saboda ya rage damuwa dani, dan ban cancanci kaunar da yakemin ba, inasan ya rage san da yakemin ne saboda ko daga baya inyasan abinda ya faru bazai dameshi ba."
Jalila ta kalleshi kawai sai jitai tayi dariya, kallan mamaki ya mata yace "dariyar menene?"
Tace "yaya, wallahi rashin sakarma mutane fuska da zama cikin mutane yasa gaba daya tunaninka daban ne, kana tunanin wai abinda kakemai na zafi zafi shine sai sa ya rage sanka? Ko ya rage damuwa dakai?"-
Hassan ya kalleta cikin mamaki, tace "ashe ma gwara ni."
Fuska ya hade yace "gwara ke me?"
Tace shikenan.
Shiru yai baice komai ba ta kara cewa "tab lalai yau naji abinda ban taba ji ba."
Harararta ta yai yace "zaki cigaba ko?"
Ta rufe bakinta tace "bance komai ba."
Haka suka isa gida, suna isa suka shiga ciki, Abba na kallansu ta glass din falonsa, murmushi yai na jin dadi tare da godiya ga Allah.Suna shiga daki ta shiga toilet tai wanka saboda fashin sallah da takeyi, sannan ta fito ta dau bargo zata shimfida, kallanta yai yana zaune akan gadon yace "ki dawo nan ki kwanta yau ma a kasa zan kwana."
Tace " a'a ka kwanta."
Kallanta yai tace "in na kwana yau gobe ma anan zan kwana."
Yace "sanda na matsu da gadon sai na tureki na kwanta."
Tadan hade rai kadan tace "bari na dau hijabina na tafi gidan Goggo kafin ma a tureni inji ciwo."
Murmushi yai yace " wannan dai neman magana kike, matar dana kaiki har kofar gidan kikace bazaki iya rabuwa dani ba?"
Baki ta bude cikin mamaki tace "a yaushe akai hakan?"
Yace "musawa zakiyi kenan?"
Ta matso kan gadon wai ita a dole an ba ta mata rai ta kwanta tare da juya baya tace " wallahi na kula duk abinda banceba sai acemin nace."
Kallan bayanta yai ya tuno abinda ya faru a mota, kallanta yai yace "to ko mu sanar da Goggo laifin da mukai?"
Juyowa tai ta kalleshi tace "laifin me?"
Yace "na fitsarar da mukai......"
Da sauri ta mike tasa hannu ta toshemai baki tace "yayah."
Kallanta yai sannan ya zare mata hannun data rufemai baki yace "yanzu yanda kika hau kaina me kike nufi?"
Da sauri taja baya tace "wai ni yaya....."
Yace "wai a yaushe na zama yayanki ne?"
Baki ta turo tace "to ni me kakeso nacema?"
Yace "oho amma ni bansan yayan nan."
Tace " to naji ka daina tsokanata."
Fuska ya hade yace "a yaushe na tsokaneki? Bakiyi rashin kunyar bane? Ko yanzu baki hau kaina ba?"
Tace "kaine fa ka jawoni kamin kiss sannan yanzu bafa kanka na hau ba."
Kansa ya juyar gefe yace "ni? Kin tabbatar bake kika fara ba?"
Ta saki baki tace "yaya tanan ka bulo? Su biyu fa kenan kana min haka."
Murmushi ya sake yi.
Da sauri tace "yaya kayi murmushi wlh."
Shiru yai yana kallanta sai dai yanayin fuskarsa ya canza yace "Jalila!"
Gyara zama tai a hankali tace "naam."
Yace "nagode."
Kallansa tai cikin mamaki, yace "zan sanar ma Abba komai, ko tsanata zaiyi ko hukuntani zaiyi zan dau komai, nagode da kika budemin zuciyata kika nunamin rayuwar daya kamata nai."
Kallan rashin fahimta tamai tace "ni?"
Yace "kin tabbatar zaki jure ganina a kasa?"
Tace "kamar ya?"
Yace "duk girman gadon nan sai na sauka?"
Tace "tare zamu kwana?"
Yace "ba haka kikeso ba dama?"
Tace "yaushe nace?"
Yai ajiyar zuciya yace "yanzu abinda na gani kenan kin fada a fuskarku."
Tai tagumi tace "oh ni."
Kwanciya yai ya dau littafinsa yace "ba abinda zan miki in ma shi kike tunani, tunda dai har kikai fitsara a gidan goggo ai kwana tare ba zai zama issue ba."
Jalila tai dariya tace "wallahi yaya na fahimci kawai so kake kai ta zolaya ta."
Bai amsa mata ba ya fara karatu, kwanciya tai daga can karshe tace "wai yaya mai kake karantawa haka kullum?"
Yace "kawai karantawa nake nai ta tisawa ina san dauke tunani daga raina."
Shiru tai tana kallansa, yace "inkingama kallan nawa sai kiyi bacci."
Da sauri ta rufe idanunta a haka har bacci ya dauketa.
Bargo ya ware ya luluba mata sannan ya kura mata ido yana kallo, Jalila! Jalila! Nagode da amincewa da kikai dani.
Murmushi ne ya sake bayyana a fuskarsa, sannan yai shiru yana tunanin Abba da Ummy dasu Sageer, gobe zai sanar dasu komai ya kuma nemi yafiyarsu, kome zasumai gani yake zai dauka tunda tana tare dashi.
Sai can ya kwanta yai bacci, bacci mai dadi yai wanda shikansa bai sani ba,bai farka ba sai biyar saura, wanda raban dayai irin baccin nan ya dade, addu'oi yai tayi da neman yafiya har gari yai haske kafin ya dawo ya kwanta, yaso tashinta tayi karatu amma yabarya saboda ganin yanda take bacci.
*********
Wajen karfe 9 suna aiki da Ummy a kitchen akai sallama, Sageer dake kallo a falo ya bude kofar, mamaki ne ya kamashi ganin Inna da Mumy.
Inna tace "Taura harya fita?"
Ya daure ya gaisheta kafin yace "yana nan."
Tace "ko zaka sanar dashi?"
Muryar Ummy yaji tace "Sageer wanene?"
Sageer yace " Matar gidansu baban Jalila ce."
Ummy tace "matar me?"
Yana kallansu yace "kishiyar Goggo."
Ummy tace oh Sageer akwai tsiya, kallan Jalila tai wacce tai tsuru tsuru, Ummy ta dafata tace "kin manta a inda kike ne?"
Kallan Ummy tai sannan tai murmushi tare da girgiza kai.
Ummy tace "shigo dasu mana." Sannan ta wanke hannu ta fito, a falo suka zauna.
Ummy ta karaso suka gaisa duk jikinsu a sanyaye.
Inna ta daure tace "Hajiya dan Allah a mana magana da Taura."
Ummy ta kalli Sageer tace "Sageer kira Abbanka."
Mikewa yai ya nufi falonsa.
Aiki yakeyi sanda ya shiga nan ya sanar dashi, Abba yace yana zuwa.
Jalila kam aikinta ta cigaba, tanaji harsanda Abba ya shigo.
Inna ta gaidashi kamar irin itace karama, Mumy ma ta gaisheshi.
Zama yai yace "lafiya? Da safen nan?"
Inna ta murmusa tace "dama munzo ne muyi bayani."
Yace "bayani?"
Tace "munsan kunsan komai akan abinda muka aikata."
Yace "sai akai yaya?"
Tace "laifinane, sai dai ina baka hakuri, muci darajar marigayi karka kwace kudinka."
Abba ya kalleta kamar zaiyi magana sai yace "Sageer yima yayanka magana."
Inna najin haka gabanta ya fadi, ita kanta Mumy hankalinta ya tashi tace "ai ba sai yazo ba, hakuri mukazo badawa."
Abba yace "na sani kuma na fahimta, matarsa ce wacce kuka wahalar kuka nemi tozartawa, hakkinsane ya yafe muku ko yaki, sannan ita yarinyar ita zaku ba hakuri ba ni ba, idan har yarinyar da mijinta sun yafe muku banaji ni inada matsala."
A ran Inna tace nasan Jalila batada matsala, babbar matsalar yaran nan......
***********
Kallansa tai tace "me kake nufi RAM?
Yace "haba Safeena ke sai yaushe ne zaki bar gidadanci? Baki kula duk mutane ba wanda yakesan harka dake ba saboda kauyancin da kike nunawa?"
Shiru tai tana kallansa kafin tace "To ya kakeso nayi wai?"
Yace "ki tashi dalla ki canza wannan shirmen na jikinki kisa wando da riga ki bar ragowar a hannuna, ni zan maidake fitaciya a skul din nan."
Kallansa tai cikin gamsuwa sannan ta kike........
#OneLuv=ؕ?
[12/7, 9:55 PM] El-hajj: =??? *JALILAH* =???
Written By : *AYUSHER MUHD*
'?ote me on Wattpad : *Ayusher Mohd*
*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*
(_D home of expert and perfect writer's_=ء?)
*55*
Sageer ne yamai knocking, yana zaune a kasan carpet yayi shiru yana nazarin dayake damunsa.
Mikewa yai da sauri yace "shigo mana."
Sageer ne ya shigo ya kalleshi yace "yaya ashe ka tashi?"
Yace "na tashi tun dazu, inzo ne?"
Mamaki ne ya kama Sageer ya girgiza kai yana murmushi yace "baki kayi."
Cikin alamar mamaki yace "baki?"
Yace "eh daga gidan su Jalila."
Da sauri yace "Goggo ce?" A ransa yana fatan badai ta gansu ba? Da sauri yace inta ganmu sai tazo? Shikanshi ya fahimci wannan bai bada ma'ana ba, kafin yai magana Sageer yace "matar gidansu babanta ce da yarta."
Cikin rashin fahimta yace "bangane hausar ba."
Sageer zai sake magana Hassan ya kalleshi, bai san sanda ya sa dariya ba yace "Tab amma lalai Sageer matar gidansu babanta?"
Mamaki ne ya kama Sageer yaya ne anya kuwa?
Hassan ya fahimci yanayin da Sageer ya shiga sai ya dan hade rai kadan ya matso kusa dashi kafadarsa ya dafa, yace "Me kake tunani?"
Sageer yai murmushi yace "kawai ina mamaki ne, banaji tunda nake na taba ganin kana dariya haka ba."
Yace "ni kaina na dade banyi dariya haka ba, kai ne yanda kai maganar ne banma san sanda dariya ta zomin ba."
Sageer ya kura mai ido cikin jin dadi, yana hamdala aransa.
Hassan ya juyarmai da kansa gefe yace " muje."
Murmushi Sageer yai sannan suka fito, tare suka sauko.
Ummy tana zaune a falo ta hangosu, tunda suka taho ta zuba musu ido cikin jin dadin ganinsu tare, karasowa sukai Hassan ya hade fuska gam, ya zauna daga kusa da Ummy.
Sai daya gaishe da Abba ya gaisheta sannan ya kallesu ya gaishesu a wani irin yanayi da inhar kana gurin sai ka dara.
Sageer ya juya kai yana guntse dariyarsa, Inna ta amsa cikin fara'a tace " sannu Malam Hassan, ina Jalilan tamu?"
Bai amsa mata ba yace "Abba ance inzo nayi baki."
Abba yace "bakin a sunan naka ne amma gun matarka sukazo."
Hassan ya juya bai ganta ba, Ummy tamai alama da tana kitchen, kallansu yai yace "ayya, wani abun ne ya faru?"
Inna ganin yanda yai magana yasa hankalinta yadan kwanta tace "Hassan nasan zakuyi tunanin cutarku mukai muka yaudareku sai dai maganar gaskiya ba haka bane, duk laifin nan nawa ne, ganin yanda Taura ya taimakemu ne yasa nai zauna nai tunani, Safeena bata dace da sirikar Taura ba, yarinyace mai san jikinta, gashi bata iya ko girki ba, ni kuma ina tun.........."
Hassan ne ya katseta yace "Tambaya nai kawai wani abun ne?"
Inna ta kalleshi, Mumy tai murmushi tace "ba wani abun bane, ita Inna tana tunanin bata kyauta ba gun yaudarar da muka muku shine mukazo neman yafiya, da neman taimako akan karku kwace kudinku."
Hassan ya kalli Abba yace " kudi na Abba ne ra'ayinsa ne ya kwace ko ya barku, ita kuma Jalila da mahaifiyarta da kukama laifi su zaku nemi yafiya agunsu ba mu ba, sannan na tabbatar wannan neman yafiyar bawai anzo yinshi bane saboda zuciya ta saduda anzo ne saboda ana san duniya."
Ya kalli Abba bai jira amsarsu ba yace "Kafin su nemi yafiya a gunka ina tunanin me zai hana a kudinmu na company dinsu mu sai share dashi? Kaga muma ya zamana munada iko akan su, saboda ni gaba daya mutanen nan basumin ba."
Ummy ce tai saurin tabashi, ya kalli su Inna ya kalli Mumy sannan ya kalli Abba yace " duk wani tunani da kukeyi akan mutanen nan sun wuce nan, ku duba abinda sukama Goggo da Jalila."Inna tace "munsani abinda muka aikata bai dace ba."
Hassan yace " Ina shi mutumin yake?"
Mumy tace "mutumin wa kenan?"
Sageer yace "mahaifinta? Bashine ya dace ya fara zuwa ba?"
Mumy tai saurin cewa "yayi tafiya ne."
Hassan yace " ohhh!"
Inna ta kasa dakai tace "na sani mu masu laifine agareku sosai, sai dai ya zamuyi? Shi mahaifinta bai taba nuna ya damu da ita ba, bai taba nuna mana damuwarsa akan matar data haifeta ba, sai dai yana neman yanzu na sakar mai ma company din, to ni ina tunanin kudinka dake ciki......."
Abba yai shiru yana kallan Inna wato a wayau tana nunamai ba fa sune masu laifi ba tsohon tane, ai in suka fahimci hakan sa dau mataki akanshi.
Sageer ya kalli Abba yace "dama ai duk mai laifin mahaifinta ne."
Abba yai shiru yana kallanta, tana ci gaba da bayani, akan yanda Dady ya banzatar da Jalila da Goggo.
Hassan kam mikewa yai ya bar falon.
Me Ummy zata gani? Gani tai ya nufi kitchen mamaki ne ya kamata sai dai wani farinciki ne ya shiga ratsata.
Cikin kitchen din ya shiga, tana vegetables a tukunya ya shiga.
A bakin kofa ya tsaya yana kallanta, juyawa kawai take amma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login