Showing 69001 words to 72000 words out of 149705 words

Chapter 24 - Jalilah Book One Complete Hausa.doc

Ayusher   

28 Oct 2025

630

sannan ya fito.
Kallansa tai ta ganshi daga shi sai towel dake daure a kasa, da sauri ta juya baya tare da rufe fuskarta da tafin hannunta bai bi ta kanta ba harya saka kayansa, sannan ya dawo gaban madubi yana shafa mai, yana gamawa ya fefesa turare.
Jalila ta juyo ta kalleshi, matsowa kusa dashi ta danyi kadan tace "Yaya bakacemin komai ba."

? Bai tanka mata ba ya dau wayarsa da makullin mota ya fita, tana tsaye ya rufo kofar.
Kallan kofar tai cikin mamaki a fili tace "mekenan?"

? Takaici ne ya kamata ta zauna a bakin gadon dabas tama rasa me zata ce.

Hassan yana sauko kasa ya sa hannu ya kwankwasa kofar dakin Abba.
Bude kofar Ummy tai sannan ta kalleshi, tace "Hassan kaine?"
Ya gaisheta sannan ya kafa leka dakin yace "Abba fa?"
Tace "yanzun nan yadan fita waje gun garden waya zaiyi."
Waya? Waye ya kirashi?
Ummy ta kalleshi tace "Hassan!"
Kallanta yai fuskarsa ta fara canzawa, tace "Please Hassan ka dinga sama zuciyarka salama, ka dinga hakuri, Abbanka namiji ne yanada hakkin auran duk wacce yakeso..........."

Juyawa yai bai jira ta gama magana ba yana neman tafiya, tace "Hassan magana nake."
Ya juyo ya kalleta yace "Yahkuri Ummy abu zanyi ne cikin gaggawa."

Kamar zata sake magana sai ta fasa, ta bishi fa kallo, Allah sarki Hassan tafi kowa sanin irin kaunar da yake mata.

Garden ya nufa, Abba na tsaye yana waya ya karasa gun, kallan Abba yai kallan zargi, Abba yace "Hafiz Please ka barni tukunna."
Bai kara jiran yayi wata magana ba ya katse layin, Hassan ya kalleshi kamar zaiyi magana sai kuma ya gaisheshi.

Abba ya amsa yace "Hassan."
Kallansa yai yace "kai da wanene haka?"
Yace "business ne ba wani abun ba uban yan zargi."
Hassan ya juya kai sannan yace "me kaba iyayen Yarinyarnan a maimakon auranmu?"

Abba ya kalleshi cikin mamaki yace "Hassan menene?"

Hassan yace "bakomai, kawai dai so nake nasani, dan na tabbatar give and take kukai da rayuwar ta."
Abba yai shiru kafin can yace "Bakasanta ne ko me? Ko wani abun ne ya faru?"

Shiru yai baice komai ba, kamar kuma zai saie magana sai ya juya zai tafi, Abba ne yace "Company dinsu ne ya ke neman yin Bankrupt shine na taimaka musu."

Hassan ya kalleshi sannan yace "yarinyar fa? Have u take care of her?"
Abba yace "kamar ya kenan?"
Hassan ya kalleshi yace "Abba ina dai sone a komai zakayi ga dinga tuna wacece Ummy a garemu."

Abba ya kalleshi yace "Hassan just pray for me, wlh nikaina bansan meke damuna ba."

Hassan yai shiru yana kallansa, Abba yacigaba "yanzu zan fada mata abinda ke faruwa itama, Hassan kafi kowa sanin family na are above komai na rayuwata ciki kuwa har da ni kaina, kasan yanda zan iya sadaukar da komai saboda su, sai dai i feel like there is definitely something wrong with me, na rasa yanda zanyi in cire yarinyar daga raina, as if samin ita akai a ciki."

Hassan kallansa yake, sai dai yasan mahaifinsa tabbas wannan kalaman daga zuciyarsa suke fitowa.

Kallansa yai yace " nafahimceka sai dai bansan meyasa zuciyata take blaming dinka ba, bawai baka iso kaso kowa bane sai dai Ummy doesn't deserve this treatment."
Abba cikin takaici yace " Ba so kadai bane a raina Hassan, mata nawa nake hulda dasu? Zance ba macen da ta taba burgeni ne? No kawai na riga nasa Ummynka ne beyond every woman, sai dai wannan karan it look like obsessed, inaji kamar dolene sai na sami yarinyarnan ko ta wani hali ne."

Hassan zaiyi magan, Ummy wacce hankalinta ya kasa kwanciya gani take kamar yanzun ma fada sukeyi yasa ta biyoshi, jin kalaman Abba ne yasa ta tsaya tana jinsu, sai dai yanzu kam idanunta ne suka zubo da kwalla, muryarta na rawa tace "it look like akwai babbar matsala a tare dakai"

A tare suka juya suka kalleta, Ummy ta karaso tace "just one month, ka bamu one month, ka daina kiranta sannan mu dukufa da addu'a musa nalamai ma su maka, in har a wata dayan nan dukda haka bakaji santa ya ragu a ranka ba ni na amince ka aureta."

Ummy!" Hassan ya fada yana kallanta, tai murmushi tace "in har a wata dayan kaima ka amince dani, karka nemeta sannan ko ta nemika ko a wayyane karka daga ko ka canza number"

Abba yace "na amince."
Hassann ya kallesu yana sanyin magana, Ummy tacee "Hassan please."

Idanunsa ya runtse, Abba yai murmushi tare da dafashi yace "Hassan bakasan dadin da nakeji ba, sauki ya fara samuwa da alama wannan auran rahama ne a gareka damu baki daya."

Hassan ya kalleshi sannan ya kalli Ummy, juyawa yai sannan yace "Shikenan Ummy tunda ke kikeso, sai dai ni ba one month ba ko shekara kikaba Abba bazan aminceba."

Ummy tai murmushi tace "nagode my eldest."

Juyawa yai yabar gun, mota ya shiga sannan ya fita daga gidan.


Jalila kam ta dade a zaune kafin ta dauko tiren abincin.

Akan dinning taga Sageer yana breakfast, da alama ma fitowarsa kenan dan tea yake hadawa.

Yana ganinta ya kura mata idanu har ta iso inda yake, gaisheshi tai, idanunsa na kanta yana nazarin fuskarta ya kasa amsa gaisuwar.

Kallansa ta sakeyi, yanzu kam ita kanta ta fahimci da abinda ke dakunsa dan duk fuskarsa ta canza,? tace "Uncle bakada lafiya ne?"

?? Flask din ya ajiye sannan ya zauna yace "a'a me kika gani?"

Tace bakomai, wuceshi tai ta ajiye tiren abincin, kallanta yai yace " Yaya fa?
Tace  ya fita.

Shiru yai sai binta da kallo da yakeyi.

Jalila ta ajiye sannan ta fara dauraye kwanukan da sukai amfani dashi.


***********

Hassan na fita ya hau titi yana tafe yana tunani, meyasa yarinyarnan bata iya fita a ransa? Ya rasa me yasa in yaji ko yaganta cikin damuwa hankalinsa baya kwanciya.

Daren jiya ya tuno wajen karfe uku da rabi, kansa dake ta sarawa ya hanashi bacci, jin kamar ana kuka da magana, mikewa yai ya kunna fitilar gefen gado.

Jalila ce da alama mafarki take, kusa da ita yaje ya zauna yana kallanta, alamar kuka takeyi tana magana kasa kasa, kunensa yasa kusa da bakinta dake motsi.
 Dady, Mumy, Inna na kuyi hakuri karku kori Goggo dan Allah, na daina, na daina......

Abinda take cewa kenan, hankalinsa da tausayinta sune suka kara ratsahi, addu oi ya mata sannan ya kamo hannunta ya rike yana kallanta.

Ya rasa me yake tunani a sanda yake kallanta, meke faruwa dashi? Is he feeling guilty? Tunda yasan dalilinsa ne yasa aka mata auran dole? Sai dai abinda yakeji ya banbanta...... ya dade sosai har sai dayaji anata kiraye kirayen sallah sannan ya mike yai alwala.

A kofar gidansu yai horn ya shiga, Mumy da Dady na zaune a falo, Yasmeen na gefe tana shan chocolate tana wasa aka sanar dasu zuwansa.
Ba Dady kadai ba har Mumy sai da gabanta ya fadi, ta kalli Dady da sauri tace  Dadyn Yasmeen meke faruwa? Cikin rawar baki yace bansani ba nima wallahi. Yafada yana tuna kalaman Hassan badai zuwan dayace zaiyi yau ko gobe ba shine yai?

Mumy ce ta bada umarnin akan a shigo dashi, ita kuma tai sama da sauri.

Inna na zaune tana jiran Dady wanda tun jiya take sa ran ganinsa amma baizoba haryanzu.

Shigowar Mumy ne yasa ta kalli kofar ta dauka Dady ne, ganin Mumy yasa tace  ya akai kuma?

Mumy da sauri tace  Inna yaran ya dawo.

Tace  yaro? Sultan?

Da sauri tace  bashi ba, mijin Jalila.

Inna ta kalleta da sauri tace  ya dawo ina?

Mumy tace  yana gidan nan, bansan dame yazo ba.

Inna ta mike hankali a tashe tace  gidan nan?

Mumy tace  yana falo.

Inna ta dau mayafi ta fito, mumy ta biyota a baya tana cewa  Inna badai wani abun ya sake faruwa ba? Itadai Inna batace komai ba, har suka isa kasa.

Dady na kasan beni da alama jiransu yakeyi, Inna na saukowa yace  Inna.

Kallansa tai tace  badai jiyan kwafsawa kai ba?
Dady yace  kwafsawa kamar ya?

Haushi ya kamata tace  wuce muje, koma menene let s hear it together.

Nan sukai falo? Hassan na zaune akan kujera suka shigo su uku.
Kowa ya samu guri ya zauna, Hassan ya gaishesu sannan ya kalli Inna wace itama kallansa take, ya kalli Mumy da Dady wanda suma hanyace  zuwa nai mahaifin Jalila ya rakani inda mahaifiyarta take, zai sanya hannun sallamarta.

Inna ta kalleshi sannan ta kalli Dady wanda a ransa yace Oh My God! Wannan wani irin yarone? Ya gama hargitsamin plan dina.

Dasauri ya girgizama Inna kai alamar ba shi bane.
Inna ta kalli Hassan tai dariya tace  Hassan taya za a sallami mara lafiya? Bayan ba warkewa tai ba?

Yace  eh wannan damuwarmu ce, dan in aka sallameta hannuna zata koma.

Mumy d Dady da Inna a lokaci daya sukace mene?

Hassan ya kallesu yace  menene abin mamaki? Ba mahaifiyar matata bace? Banaji cikinku akwai mai hakkinta.

Inna tace  mene?
Yace  why? Bazai yiwu ba? In bazai yiwu ba bari na kira Abba na sanar dashi, ina tunanin kamar zamu amshi kudin mu.


 kudi? Hassan ya daure dan kansa wani irin sara mai yakeyi, ya mike ya kalli Dady yace  ina mota.

Ya juya ya fita alamar wai yana jiran Dady a mota.

Inna tabi kofar daya fita da kallo, sannan ta kalli Dady, takaici da bakin ciki ne suka kamata.

Dady yace  Inna ya zamuyi?

Cikin takaicinsa da bakin ciki tace  dalla wuce kaje ka rakashi, ko so kake company dinmu ya mutu?

Dady ya mike ya fita.

Inna takaici ya kamata tace  lalai ba yaran nan bane bashida hankali nice banda hankali dana kawo babban makiyi har cikin gidana da kaina......

Dady ya shiga mota Hassan yaja suka tafi.

A asibitin premier sukai parking, ya zaiyi?Gashi bayasan asibiti, gashi yabar Jalila agida sabofa bayasan su nemi wulakantata.


#Oneluv=ؕ?


=??? *JALILAH* =???

Written By : *AYUSHER MUHD*
'ote me on Wattpad : *Ayusher Mohd*


*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*
(_D home of expert and perfect writer's_=ء?)



*41*

Tsayawa yai shi bai fita daga cikin motar ba sannan baiyima Dady magana ba, Dady kam wanda yake a zaune yana nazarin yaran ya kalleshi yace  muje?

Hassan ya fito daga motar sannan ya tsaya yana kallan asibitin, babban matsalarsa bawai shigar bane, zai iya shiga reception ko gun da ba marasa lafiya kamar office, sai dai daga yayi bangaren dakuna na marasa lafiya hankalinsa yake tashi, shiyasa kwanaki yana fara hawa saman beni yaji gaba daya hankalinsa da tunaninsa na neman gushewa.

Da kyar ya daure suka nufi reception din, nan yamusu bayanin abinda sukeso, suka turasu wani office, nan ma sunyi cike cike, suka rubuta kudin da za a basu, Hassan ya biya, suna fitowa ya kalli saman benin sannan ya kalli Dady dabara ce ta fadomai yace  kaje ka sanar da ita, ka kuma nemi yafiyarta sai ku fito tare ni ina mota.

Dady ya kalleshi a ransa yace  lalai wannan yaran bashida tarbiyya, ina sirikinsa amma ya maidani dan aike? Kamar wani masinjansa, ko driver? Yana tsaye har Hassan ya fita sannan yai kwafa ya hau saman.

Goggo na zaune tana shafa mai a hannunta, yau kam jikin da sauki, lantana na tattare kwanukan da aka kawo abincin safe zata maidasu gida.

Dady ya turo kofar ba ko sallama, Goggo ta kalli kofa, ganinsa sai dayasa gabanta faduwa, ya shigo fuskar nan a hade ya tsaya yana kallan dakin, kallan Lantana yai yace  ke dan fita.

Lantana ta mike tai waje, Goggo ta kalleshi tace  ina kwana?
Dady bai amsa ba yace  hankalinki ya kwanta?
Tace  da me fa?
 A haka in aka kalli fuskarki ba wanda zaiyi tunanin zuciyarki akwai hassada, bakinciki da tsantsar munafirci.

Goggo cikin mamaki tace  me kake nufi?
Yace  sai ki taso ki zo kibi mijin yarki da kikasa ya daukeki daga gunmu.

Goggo cikin mamaki tace  mijin  yata kamar ya kenan?wace yar tawa?
Yace  ni banda lokacin munafircinki, ki taso ki fito, in kuma bazaki iyaba ki cigaba da zama.

Goggo gaba daya kanta ya daure ta kasa gane me yake nufi, kwallama Lantana kira yai yace  zo ki kwashe kayan nan an sallameta.
Goggonta mike tsaye tadan dosana kafarta tace  Wai Abubakar me kake nufi ne? Ni na rasa me yasa kullum kai burinka ka jefeni da sharri.
Cikin takaici yace  sharri? Ai kece kike bina da sharri dan na tabbatar badadan ke ba da tuni Inna ta bani company dinsu, amma saboda tana ganin naci amanarsu na kawoki, daga ke har  yarki banda bakinciki me kuke tsinanamin? Da na dauka yanzu zan moreta sai gashi yau ta wargaza komai, ni ki wuce mu tafi dan ganinki ma bakin ciki yake sani.

Goggo kallansa kawai take zuciyarta na wani irin kunna, tace  nikam menene matsayina agunka? Ma dauka ni matarka ce.

Wata irin dariya yai wanda yasa ta kallansa cikin wani yanayi, yace  mata? Wa? Kedin? Kema kinsan ni ba sa an auranki bane ko a can baya bare yanzu, ni ba wani aure ko makamancinsa tsakaninmu, ina zaune dake ne kawai saboda yarki da tazamarmin dole.

Goggo ta share kwallar ta tana neman yin magana ya fita yana cewa  kuma ki sauko yanzu.

Lantana ta shiga saukar da kaya kasa, dady ya nuna mata motar Hassan, nan aka bude boot din mota aka sasu, itakam Goggo ta dade tana kuka, nurse tazo ta kara dubata sannan ta taimaka mata ta sauk???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?o, shigowar Lantana na karashe suka sauka tare.

Tsayawa tai tana kallan motar, Hassan ya taho da sauri gunta sannan ya kalleta.
Kallansa tai cikin mamaki tace  wanene?
Hassan ya kalleta sannan yace  bari na kira kuyi magana da Jalila. Dan baisan me zaice ba.

Matsawa yai ya kira number Sageer.

Sageer na daki lokacin da Hassan ya kirashi, yayi mamakin kiransa ya amsa da sauri yana cewa  yaya lafiya?
Hassan yace  Sageer ina Jalila?
Yace  tana sama dazu ta hau.
Hassan yace  please ka dan kai mata waya.

Yace to sannan ya mike ya fito.

Jalila tafito daga wanka kenan ta zura wata doguwar rigar atamfa, dan dama kwalliya bata dameta ba saboda ba barinta ake tana yi ba, sannan bama wani iyawa tai ba, balle hankalinta ma ba a kwance yake ba bare tai tunanin yi.
Mai kawai ta shafa ta dan shafa hoda tasa turare, dan kwalimta kawai ta yafa akanta, ta zauna kenan ta dau wayarta taji knocking.

Mikewa tai ta bude.

Ganin Uncle ne yasa ta tsaya tana kallansa, shima kallanta yai sannan ya mika mata waya yace  Yaya ne.
Amsa tai bata rufe kofar ba ta juya zuwa ciki tana cewa  Yaya!

Yace  yauwa. Tana jiran ya sake magana kawai taji sallamar Goggo, jikinta na rawa cikin rawar baki tace  Goggo.
Goggo tace  jalila?

Jalila hawaye ya zubo mata tace  Goggo kina ina?
Tace  gani a kasan asibitin ance wai wani ne ya zo daukana shikuma naga bansanshi ba, shine ya kiraki, kinsanshi ne?

Jalila tana kuka tace  ki biyoshi Goggo, ke kadai ce?
Tace  a a mahaifinki nanan.
Jalila tace  Goggo dan Allah karki nuna bakinsanshi ba, ki bishi zai kawoki inda nake.

Cikin mamaki Goggo tace  inda kike? Kedin bakya gida?
Jalila tace  inkinzo zan sanar dake komai.

Goggo tace to, sannan ta kalli Hassan ta mikamai waya, baice ma Jalila komai ba kawai ya katse wayar.

Jalila ta juyo inda Sageer yake tana hawaye, tace  Uncle!

Shikam hankalinsa ya tashi ganin tana kuka yace  menene? Wani abun ya faru ne?

Gani yai tana dariya tana kuka, tace  Uncle, Yaya ya daukomin Goggona.

Tsayawa yai sai dai yanzu baisan me zai kwatanta abinda yakeji ba, yai murmushi yace  duk da bansan meke faruwa ba, it look like abin farinciki ne, sannan alama ce ta shakuwa na shiga tsakaninku, tunda gashi har yasan abinda ba wanda ya sani, sannan lafiyarsa ma nasan samun kusanci dake ne yasa, uhm congratulation, Allah ya barku tare.

Ya juya jiki a sanyaye da kallo ta bishi zuciyarta na tausayamai, ta tabbatar Uncle na santa sosai bawai ya rabu da ita bane dan kansa sai dai zumunci da kaunar da ke tsakanin shi da yayansa.
Hawayenta ta share sannan ta zauna abakin gadon tana tunanin me zata ce ma Goggo?

Hassan kam Goggo na shiga mota ya kalli Dady yace  Allah yasa akwai kudi a jikinka
Dady yace  babu, menene?

Hassan ya sa hannu a aljihu ya dauko 1000 yace gashi ka hau mota dan gida zan wuce daga nan.

Dady yace  mene? Kai ni na haifi Jalila fa, bawai dan aikin gidansu bane, wai me yasa......
Ganin Hassan yai ya shiga mota kamar ma badashi yake ba yaja yayi gaba, ran Dady a bace yabi motar da kallo.

Hassan kam jan motar yai sukai gaba, Goggo da Jalila na baya, suna fara tafiya Goggo tace  meke faruwa? Ya akai Jalila tabar gida?

Hassan ya dan shafi kansa dake ciwo yace  Jalila zata miki bayani, zaifi cancanta ta miki bayani da kanta.

Goggo tai shiru tana addu a aranta, Allah yasa Jalila ba wani mugun abu ta fada ba, sai dai kallan Hassan yasa wannan ya tafi daga ranta.

Kallan tangamemen gate din da aka bude yasa Goggo ta kara cewa  tana cikin nan?

Yace  eh.

Kallan gida take har yai parking, da gudu Jalila wacce ke tsaye a waje ta taho bude

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login