Showing 129001 words to 132000 words out of 149705 words

Chapter 44 - Jalilah Book One Complete Hausa.doc

Ayusher   

28 Oct 2025

636

dashi.

Jan nama ta dauko ta shiga wankewa, sannan ta fara yanka albasa tana dan kankane ido.

Jin hannu ta bayanta yasa gabanta ya fadi, a tsorace ta juyo yanda ya riketa yasa tana juyowa ta juyo daf daf da fuskarshi, sumbatarta yai yace "na sauko, da me zan tayaki?"

Kallan kofa tai sannan ta kalleshi cikin mamaki tana kokarin zamewa tace "Yaya!"

Yace "da me zan tayaki?"

Tace "tayani? Yaya in wani ya ganmu fa?" Ta fada tana dan zamewa, yace "ohoo naga ke kika ce na sauko?"

Baki ta bude tace "wasa fa nake maka kaima ka sani."
Yace "wasa? To ya akai ban sani ba? Sannan banaji kema kincemin wasan nan kikeyi."

Baki ta bude tana kallansa tace "lalai yaya, me zance in su Ummy suka ganka anan?"

Yace "me zakice kuwa? Kawai mijinki ne yake taimaka miki."

Dariya tasa tace "a haka sauki fada."
Yace "a can din ma sauki zai.....yi"

Yai maganar yana kara jawota, tace "Yaya Allah kar Ummy ta fito."

Sumbatar wuyanta yai yace " wasa wasa da ke matsoraciya ce."
Tace "naji, nayi surrender, ayi hakuri, hanuna a sama."

Ta fada tana daga hannayenta.

Murmushi yai sannan ya saketa tare da bude fridge, sannan ya rufe yace "yanzu a haka zan tafi?"

Tace "hmm dan Allah yaya jeka ko falo ne,wallahi bansan ya zanyi ba in wani ya ganmu anan."

Baki ya tabe sannan yace "za'asan an koreni wallahi."

Ya juyo tare da hade fuska.
Da sauri tace "yaya?"
Tsayawa yai fuska a hade, ta matso ta dan daga kafafunta ta sumbaci kuncinsa, tace "sorry!"

Kallanta yai fuska a hade yace "wannan karan wannan bai isa ba."

Ya fita, kallansa tai tana murmushi har batasan tasa wuka a kusa da bakinta ba sai dataji warin albasa sosai yasa tai saurin sauke hannunta tana dariya.

Yaya ma yana fita yadan harari kitchen din sannan yace "chance din ramawa ya samu."

Yana kokarin bakin falon Sageer na fitowa, kallansa yai yace "Yaya? Daga ina?"

Yace "hmm na fito gaida Ummy ne naga batanan."

Sageer Yace "oh wallahi da sassafe suka fita itada Abba, sunje Bauchi, ka duba wayarka har text ta maka kai da Jalila."

Yace "Bauchi? Wani abun ya faru ne?"

Yace "wallahi ban sani ba, inaji dai zasu je gun dangin Baffanane, sannan kila akwai abin aiki da ya kaisu daga nan."

Hassan yace "Shine baka bisu ba?"

Sageer yace "kasan halinsu, in Ummy taje sai sun mata gori, gwara ni naje daga baya."

Hassan ya jinjina kai yace "Hakan yayi, kace kai kadai ne a gidan kenan?"

Yace "hmm amma nima anjiman nan zan fita zanje office din Abba akwai abinda ya sani."

Hassan a ransa yace "kenan sai mu kadai?"
Amma a fili yace "hakan yayi, ya kamata ka dinga fita ko ka samoma Ummy wata surikar tunda dai kaga ni tafiya zanyi."

Sageer yai dariya yace "kar ka damu an kusa."

Hassan yace "haba? Ka gano wata ne?"
Sageer ya matso sai tin kunnensa yace "na gano amma bansan ko inada chance ba."

Hassan yasa dariya zaiyi magana sukaji ana knocking din kofa.
Sageer ya karasa ya bude.

Mumy ce tsaye a gun, Sageer ya kalli Hassan sannan ya kalleta.

Ganin haka yasa Hassan din matsowa.

Kallan mamaki ya mata kafin yace "Bismillah."

Mumy ta shigo jiki a sanyaye.

? Abinda takeyi hakan ya dace kuwa? Anya kuwa ta kyautama Abubakar?

? Zama tai a kasa sannan ta kalli Hassann da Sageer.

Hassan ya kalleta yace "lafiya?"

? Kallansa tai sannan ta hada hannayenta biyu tace "Hassan ku taimaki Inna ta da ni kaina da kuma Mijina, ku duba girman Allah. Bawai abinda muka aikata ba ku taimaki rayuwarmu."

Yanda take magana da karfi yasa Jalila lekowa.

Ganin Mumy yasa ta tsaya tana kallanta, Hassan ya kalleta sannan ya kalli inda Jalila take, Sageer ka ya kalleshi.



#OneLuv=ؕ?
[12/30/2018, 10:07 PM] El-hajj: =??? *JALILAH* =???


Written By : *AYUSHER MUHD*
Wattpad: *Ayusher Muhd*


*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*


*71*

Mumy ta kalli Hassan idanunta sun ciciko, idanunta duk sun koma kalar tausayi, ta kara daga hannunta alamar tsananin neman taimako, tama kasa magana sai hannunta kawai datake ta murzawa.
Hassan kam Jalila ya kafa ma ido yana kallanta, wacce tai tsuru tana bin Mumy da kallo.

Sageer ne ya kalleshi yanda yaga yana kallan Jalila ne yasa yace  Yaya?

Hassan ya kalli Sageer sannan ya kalli Mumy, daurewa yai yace  meke faruwa?

Mumy ta kara kallansa idanta duk ya canza zuwa tausayi, kallan inda Jalila take tai a hankali tace  Jalilah?

Jalila wacce gabanta ke ta dukan uku uku tana tsoron kar ace wani ya mutu, tsoron matsowa takeyi, Mumy ta kara cewa  Jalila!

A hankali Jalila ta fara takowa zuwa inda take, tana tafe gabanta na wani irin faduwa, kusa da Hassan ta matso ta tsaya a hankali itama tace  Mumy menene?

Mumy ta kalleta tace  Jalila ki rokarmana mijinki da mahaifinsa su taimaka su dakatar da mahaifinki.

Cikin rashin fahimta ta kalleta tace  dakatar dashi kamar ya?

Nan mumy ta kwashe abinda ke faruwa ta sanar musu sannan ta dora da cewa  bawai hanashi company din nakesan yi ba, dan ni a gurina yafi kowa dacewa daya mulki company din, sai dai ina tsananin tsoron kar san zuciya ya jefashi cikin wani halin, sannan bansan me yake kitsimawa a ransa ba, ance yanata duba takarda a gida, da farko ban kawo komai a raina ba sai dai bayan na taho ina hanya na fahimci me yake nema, takardun gidan da muke ciki yake nema, dan dama tun shekara uku da suka wuce nasa aka canza sunan gidan daga sunana zuwa nashi, saboda na kwantar mai da hankali, kenan korar mu zaiyi daga gidan, ni duk na rasa me Abubakar yake kitsimawa a kwakwalwarsa.

Hassan wanda ko kadan baiyi mamaki ba yace  yanzu halayen mijinki kike sanar mana anan? Ko kuma halin da kuke ciki ke dashi?ni na kasa fahimta.

Mumy tace  Hassan ka dubi girman Allah ka taimaka mana, na tabbatar in wani abu ya samu company din Inna wallahi mutuwa zatai.
Yace  Rai a hannun Allah yake, in lokacinta yayi banaji ke ko ni mun isa mu dakatar dashi.

Ya fada tare da juyawa ya wuce sama.

Mumy ta bishi da kallo kafin ta matso kusa da Jalila, hannunta ta riko tace  Jalila?

Jalila ta kalleta, idanunta sun ciciko itama, Mumy tace  Jalila na san bamu kyauta miki ba ko kadan, ke da mahaifiyarki, mun wulakantaku daidai wulakanci, sai dai inaso ki dubeni ta fuskar fahimta bawai dan ke akayima ba, a a ki dubeni a matsayinki na mace, ya zakiyi idan wanda kike masifar so rana daya yazo miki da mace sannan da tsohon ciki? Ya zakiyi in mijin da kike masifarso ya nemi ku barsu su zauna a muhallinki? Ya zakiyi in kikaga mijin naki baisan darajarsu ba, basu isheshi kallo ba bare ya nuna damuwarsu akansu?


Jalila tai shiru tana kallanta, Mumy tashare kwallarta tace  Nasani bazaki fahimceni ba, na kuma san ban kyauta muku ba daga ke har Goggonki ko da Abakar bai nuna damuwarshi akanku ba ni kuma baikamata na maidaku kamar masu aiki ba, sai dai Jalila ki dubeni a matsayin ba kowa ba, dan Allag ki ceshi mai neman bukata, Jalila Inna tana cikin wani mawuyacin hali.

Jalila tai shiru tama rasa me zatace muryar Sageer taji yace  Please in kin gama ki fita.

Shima ya wuce ciki dan shikam gani yake ko kadan basu cancanci a taimaka musu ba.

Mumy ta kalli Jalila ta kamo hannunta tace  Jalila!

Jalila ta daure tace  Mumy zan shiga ciki. Ta karasa tana dan zare hannunta.

Jalila ta juya zata tafi,muryar mumy taji  Safeena ta dawo.

Cikin mamaki Jalila ta juyo ta kalleta tace  ta dawo daga Abujan?
Mumy ta girgiza kai tace  ba abuja taje ba, fita da ita abroad mukai karatu sai dai alhakinki ne inaga yasa gashi ta dawo ba karatun ba kuma jin dadin, ta fita a banza mun kashe kudi a banza sannan me makon ta dawo cikin farinciki ta dawo cikin kunci.

Jalila tai shiru tana kallan Mumy, kafin Mumy tace  kinga yanda rayuwa take Jalila, a da bamu daukeki a komai ba, yar mu kawai muka sani yanzu gashi kece a matsayin komai, ki duba darajar da Allah ya baki, ki rokarmana Sirikinki da mijinki su taimaka mana.

Jalila tai shiru, sai dai ya zatayi? Ko da ace naman jikinta suka dinga yanka, yan uwanta ne, duk duniya batada kamar Safeena, Sultan da Yasmeen, dan jini ba wasa bane.

Yanda Mumy ke kara rokarta ne yasa tace  bari na mai magana, sai dai ko da wasa Mumy karkisa ran zasuyi abinda kikeso, ni dai zan yi iya nawa ne, ba kuma dan kowa zanyi ba sai dan Allah da darajar yan uwantaka.

Mumy ta hau gyada kai tana cewa  nagode Jalila, nagode.

Jalila ta shiga kitchen ta rage gas sosai sannan ta fito tai sama, Mumy ta bita da kallo, rayuwa kenan, wai su da sunyi tunanin cutar da ita sukai, sun killace tasu, sai gashi ashe daukakata sukai, hawaye ne ya kara taruwar mata sai yanzu hankalinta kadan kadan yake kai mata manufar Abakar, yanzu kam ta fara tantama ma in har yana santa.

Jalila ce ta tura kofar dakin, yanna zaune yana latsa waya ta shigo, kusa da kafarsa ta zauna dan yadan jasu sama.

Sa kanta tai saman gwiwoyinsa, ta dan karkato da kanta gefen da wayar take tace  Yaya! Shine ka gudu ka barni?

Kallanta yai tare da ajiye wayar yace  Bansan me zance miki bane, shiyasa na taho.

Ta dan rufe baki kadan kafin tace  me zaka cemin kamar me?
Yace  mahaifinki ne, me zance?

Kanta ta kwantar akan gwiwar tasa kafin tace  mahaifina ne sai dai tunda nake dashi Yaya ban taba zama dashi munyi maganar mutunci ba, duk maganar da zata fito daga bakinsa zakaji san zuciya ne da tsantsan san kai.

Hassan yai shiru yana mata kallan tausayi, murmushi tai kafin tace  sai dai Yaya duk yanda naso na gane na kasa fahimta.

Ya mata kallan rashin fahimta, tace  wani irin uba ne Dady? Yaya duk yanda naso na kasa gane wa.

Fuskarsa ya sa ko kusa da tata, yace  wanda baisan baiwar da Allah ya mai ba?

Tace  baiwa?
Kiss ya mata yace  baiwar yarinya kamarki mana.

Idanu ta kankance tana kallansa kafin tace  ahh yaya.

Murmushi yai kafin yace  yau kinsan mu biyu ne a gidan nan?

Murmushi tai sannan tace  kafin mu zama mu biyu kadan taimakamin kadan.

Name? Tayaki breakfast din zanyi? Ya fada yana dan kamo gefen cikinta.

Dariya tasa tace  kai Yaya!

Yace  ba su bane?

Tace  ka taimakeni kar Dady zuciyarshi tai nisan da bazata taba waiwaye ba.
Yace  kamar ya?

Tace  banaso mahaifina idanunsa ya rufe, ina tsoron halin da zai afka, baya tunanin komai sai kansa, shiyasa nakeso a dakatar dashi haka daga kan san kansa da yakeyi, ya fahimci yanada responsibility s da kuma abinda yafi shikansa daraja.

Yace  yanzu me kikeso ayi a tsayar dashi?

Tace  dan Allah ka taimaki Mumy, hakkinsu ne company din nan, mahaifinta da mahaifiyarta sune sukasha wahala gun ginashi, taya Dady zai zo lokaci daya ya nemi kwacewa? Bayan na tabbatar da yayi hakuri Mumy yanda take sanshi da kanta ma zata bashi, kaga alama ce ta san zuciyata da tsantsar burin rayuwa ne yake damunsa, wanda ya rufemai ido daga taimakon da aka mai, yake ganin kamar komai ya cancanta ne shiyasa ake mai?

Hassan ya sa hannunsa yaja kumatunta kamar wata baby sannan yace  ohhh wannan babyn da alama ta mike tsaye.

Bai saki kumcin nata ba ta shiga kokarin magana tana cewa  Yaya Please!

Dariya yai yanda tai maganar yace  to ni kinsan bansan kan harkar ba, ta ina zan taimaka miki?
Tace  muje mumy sai tama bayani, lokaci yana kurewa.

Yace  Hmm umm. Cikin shagwaba yai tasa dariya tace  da alama in an gama wannan zan kara nema amin abin nan.

Fuska ya hade yace  haka kawai ina murna zamu zauna mu biyu yanzu kuma kinzo da wani zance daban?

Tace  sry yaya.


Ajiyar zuciya yai sannan yai gaba.

Da kallo ta bishi sannan tai murmushi, bin bayansa tai.

Kasa suka sauko Mumy nata amsa waya tanata magana da Sani.

Tana ganinsu ta kashe wayar tare da gyara zama.

Hassan ya sauko kofar Sageer ya nufa tare da yima knocking.
Sageer da ya bude kofar ya kalleshi.

Hassan yace mai  Sageer dan fito plx.

Fitowa yai tare da rufe kofar.

Jalila kam na saukowa kitchen ta nufa kawai ta cigaba da harkarta.

Duk da hankalinta nakan abinda ke faruwa a falo sai dai ta sa wa ranta abu daya, duk abinda Hassan ya yanke kawai yayi, dan bazata tilastamai akan abinda bayaso ba.

Mumy ce ta kalli Hassan wanda yacemata  fado abinda kikeso ayi muji.

Nan Mumy tamai bayani kamar yanda Sani ya mata, tace  duk yanzu kudin dake running a company din 80% kudin Mahaifinku ne, hakan yasa kuna da hujjar kwatar company din kuba wanda kukeso in har bamu biyaku kudin da kuke bin mu ba.

Sageer yace  amma contract din ai kamar lokacin biyan nada tsayi.

Tace  eh, sai dai nunawa zamuyi kamar abin yazo.

Hassan yace  nuna wa zamuyi? Har a yaushe muka zama mu?

Mumy tace  bada wani abun na fada ba, kuyi hakuri dan Allah.

Hassan ya kalleta sannan yace  na kasa fahimtar wani abu, in an amshi company daga hannun mijinki wa kikeso a ba?

Tace  ni kaina bawai so nake ba, saboda koda wasa ban taba burin mulkar company din nan ba, ni kaina shi nakeso aba sai dai bata wannan hanyar ba.

Hassan ya mata wani kallo dan shikam ya dai jitane.

Yace  Sageer ya kake gani?

Sageer yace  bari na kira Abba muyi discussing.
Ya fada tareda mikewa.
Ganin za a barsu su biyu yasa ya mike ya shiga kitchen.

Ta banyanta ya tsaya tana soya yankanken kayan miya akan frying pan.

Tana ganinshi ta juyo tana kallanshi.

Karasowa yai ya sa hannunsa ya zagayo da ita ta cikinta ya kwantar da kansa a kafadarta yace  kallanfa?

Tace  ya kukai?

Yace  kawai dai.

Murmushi tai kafin tace  Thanks alot Yaya.

Yace  banasan wani thanks kawai zanbi bashi ne dan sai an biyani.

Murmushi ta sakeyi tace  da alama bashin nan nawa karuwa yakeyi dayawa.

Sumbatar wuyanta yai yace  da alama zamu dan barki a gida ke kadai na dan wata awa daya.

Kai ta daga alamar gamsuwa ba tare da ta tambayeshi ba.

Saketa yai sannan ya wuce sama, wanka yai yasa kananan kaya sannan ya sauko, Sageer ya tarar a falon Abba yana rike d wasu takardu yana kuma waya.

Yana ganin Hassan yamai alama dayazo, nan sukai magana su biyu kafin su fito falo.

A tare suka fita, Mumy ta shiga motarta suma suka shiga motar Sageer.

Suna shiga Hassan yace  haka Abba yace?

Sageer ya shiga yimai bayani, Hassan ya jinjina kai alamar gamsuwa yace  shikenan.


*************

Ba wani kato bane main branch din nasu, sai dai dayake ajiyar kayan abinci sukeyi daga baya akwai wani tangamemen fili da akai gini inda ake aikin a ciki.

Sani na ganinta ya taso da sauridan dama yana zaune a waje yana jiranta, tanna karasowa ya matso da sauri yace  sun shiga cikin meeting din kamar minti 5 da suka wuce.


Mumy ta matso ta sanarma Hassan.

Dakin babban taro na hadaka suka nufa, suna zuwa Sani yasa aka bude dakin.

A lokacin kuwa Dady ne tsaye yana bada speech dinsa na yanda company dinsu wai ke cikin matsalar da suke san akawo mafita dan a kwatota daga ciki, Babban director din yace  Bravo! Gaskiya duk company din nan ba wanda yake sanshi da kula dashi kamar kai, shiyasa nazo da babban shawara akan sauke Hajiya wacce girma ya kamata yasa take neglecting din aiyukanta, a baka kai sirikinta wanda ka sadaukar da komai naka akan company din mu.


Muryar Sani sukaji yace  Investors din da suka taimaki company dinmu sunzo.

Kowa kallan su ya juyo yai, Mumy ta zubama Dady ido wanda gaba daya shima idanunsa na kanta.

Hassan ya matso inda Dady yake yace  will you please get down?

Dady ya kalleshi zuciyarsa gaba daya ta rage bugawa yanda ya kamata, Hassan ya kalli Sageer yamai alama dakai akan ya matso.

Sageer ya kalli Dady wanda yake saukowa kamar wanda bashida ragowar laka a jikinsa.


Sageer ya fara bayani kamar yanda Abba yamai.
Takarda ya zaro ya daga sama yace  wannan shine contract din da mukai da company dinku akan za a biyamu 50% na kudinmu a kwana uku da suka wuce.
A cikin wannan contract din munyi bayani time da kuma kudin da za a fara biyanmu.
Sai dai jiya mun nemi Chaiwoman din company din me makon ta bamu sai ma taki daukan wayarmu, wannan dalilin ne yasa muka sauko kasan contract din wanda yace  in har ba a biyamu kudin mu akan lokaci ba rabin company din zai dawo namu.


Nan fa kowa ya fara kananan maganganu, Sageer ya kallesu yace  saboda haka daga rana tayau zan zama nine shugaban company din nan har zuwa ranar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login