Showing 84001 words to 87000 words out of 149705 words

Chapter 29 - Jalilah Book One Complete Hausa.doc

Ayusher   

28 Oct 2025

624

suna ciki Jalila kome Ameera ta dauko indai taga kudi sai ta maidashi, Ameera ta tsaya tace "to nidai bansan me kikeso mu siya ba, duk abinda na dauko sai ki maida." Ta karasa maganar tana kallan kwandon nasu da bakomai a ciki sai atamfa kwaya daya.
Kiran Hassan ne yasa ta kalli Jalila tace "Yaya!"
Jalila ta kalleta bayan ta amsa kiran, Ameera tace "Yaya...."
Yace "me kukeyi haryanzu? Badai shirme kuka tsaya yi ba?"
Tace "a'a Yaya, ni narasa me zamu siya ne, duk abinda na dauko sai Yaya Jalila tace wai yayi tsada sai ta maida."
Hassan ya kashe wayarsa baijira ya gama jin abinda zatace ba.
Tahowa yai ya shiga ciki, security din ya bishi da kallo yana yan kunkuni, inkasan shigowa zakai gulmar ta menene? Tun dazu ka tsaya kamar mai jira.
Hassan na shiga ya sake kiran Ameera ya tambayeta inda suke, ta sanar dashi.
Yana isowa ya bugama Jalila kallan harara sannan ya kalli Ameera yace "ina kayan da kika zaba?" Nan ta shiga daukowa tana sawa a cart din, mamaki na kara ratsata, bata dade a gidansu Aina'u ba yaushe har yayanta ya koma haka?
Jalila na tsaye tana kallansu sai zuba kaya sukeyi a cart din har sai da ya cika sannan suka nufi gun biyan kudi.
Tana can gefe suka biya kudin sannan ya kalleta ya nuna mata ledoji, matsowa tai ta dau leda biyu manya itama Ameera tadau biyu suka nufi kofar fita.
Yana kallanta da yanda ledojin suka mata nauyi dan kamar ma janta sukeyi, kallanta ya sakeyi sannan ya kalli ledar ji yake kamar yaje ya amsa sai dai inaaa bayaji zai iya yin hakan, balle agaban Ameera.
Taje kusa da motar bata kula da saman interlocks din daya dago ba, jitai tayi tintibe da sauri yasa hannu ya riko cikinta.
Ajiyar zuciya tai dan ta tsorata ga kayan da suka kara rinjayarta.
Juyowa tai ta kalleshi kawai sai tai dariya tace "yaya wlh na tsorata, har na hango kaina ya bugu da jikin motar."
Jawota yai ta mike daidai sannan ya kalli gun datai tuntube, lalai mutanen nan basuda hankali tayaya bazasu gyara gun ba? Fuska a daure ya kalleta yace "meyasa bakya kallan kasa in kina tafiya? Da bana kusa ko da banyi hanzarin kamoki ba me kike tunanin zai faru?"
Ta kalleshi jikinta yai sanyi tace "wlh ban......"
Gani tai ya wuceta rai a bace, ledar hannunta ya amsa ya sa a boot din motar sannan ya bude ciki ya shiga.
Ameera ta ajiye nata itama ta shiga baya sum sum.
Jalila ma jiki a sanyaye ta shiga, to laifinta ne? Itama ai da saninta bazata bari ta fadi haka ba.
Harya tada motar ya fito daga ciki ya nufi gun secuydin.
Kallansa yai fuskar nan a daure, security din ya kalleshi yace "Yallabai da wani abun ne?"
Shiru yai yana tunani, menene damuwarka da har kazo nan zakai fada akan su gyara gun da yarinyarcan zata fadi? Menene damuwarka Hassan.
Bai tanka mai ba ya juya, security din ya bishi da kallo yace "yau ni kuma ina na samo wannan?"Hassan ya bude motar ya shiga dya rufota da karfi yaja motar da gudu suka bar gun.
Shiru motar tai ba wanda yake magana, sai sanyin Ac dake ratsa cikin motar.
Jalila ta kalleshi taga ba alamar wargi, tai gum.
Can ta sake kallansa nan ma taga ba alama tai gum.
Sunyi nisa sosai sai tace "Yaya kashanye yoghurt dinka?"
Bai tanka mata ba sai dai yasa hannu ya miko mata ledar, ba haka taso ba, ta daure ta sake cewa "kasan yaya sai da muka shiga cikin store din nan naji cikina yana wani kara?"
Nan ma baiko tanka mata ba, ta amshi ledar ta ajiye a kusa da ita sannan ta kalli Ameera datai shiru tana danna wayarta.
Itama jan bakinta tai bata sake cewa komai ba.
Suna isa gida Ameera ta fito da sauri saboda tsoron kar reshe ya juye da ita.
Jalila ta zauna ba alamar fita, kallanta yai yace "me kikeyi?"
Tace "Yaya kaima kasan ba kaifina bane, tuntube nai sannan wlh bawai kula bane banayi"
Yace "kinji nace wani abun?"
Tace "bakace ba amma......"
Ya katseta "sauka inkuma bazaki shiga ciki ba sai ki kulle motar inkin gama zaman."
Kallansa tai ranta yadan sosu ta fito daga ciki ta duba boot ta dauko ragowar ledojin sannan tai ciki.
Kallanta yai harta shiga ciki sannan ya dan saki huci yace " ba saboda ke raina ya baci ba saboda kaina ne."
Idanunsa yadan rufe da hannunsa kafin ya fito daga motar.
Ummy najin motsin shigowarsu ta fito daga dakinta tana cewa "Jalila kun dawo?"
Ameera ce ta taho da gudu ta rungumeta, Ummy tai dariya tace "Auta saukar yaushe?"
Ameera ta kalli Jalila tace "tare muke dasu Yaya Jalilah."
Ummy ta kalli Jalila wacce ta karaso tana cewa "da ita muka je ai Ummy."
Ameera ta kalli Ummy cikin zumudi tace "Ummy kinsan waye ya kaimu?"
Ummy ta kalleta, Ameera ta kara matsowa tace "Ummy karkiyi mamaki........."
"Hassan kun dawo?" Abinda Ummy tace ne yasa Ameera saurin boyewa abayanta, Hassan yace "eh Ummy."
sannan yace "Abba fa?"
Ta nunamai falo tana kallan Jalila wacce tana tsaye yazo ya wuce kamar baiganta ba.
Hassan ya wuce falo, Ameera ta kalli Ummy da sauri tace "Ummy kingani? Ummy yaya ne yake magana haka."
Ummy ta kalleta tace "naji hajiyar magana, akwai baki a dakinki kije ku gaisa."
Ameera tace "baki? Su waye?"
Ummy bata tanka mata ba ta matso kusa da Jalila tace "Jalila wani abun ya faru ne?"
Jalila tai yake tace "bakomai Ummy, Kinga kayan da Yaya ya sai mata."
Ummy ta kalli ledar tace "basai kin ciro ba, angode Allah ya saka masa da alkairi."
Jalila tace "Ameen."
Muryar Abba sukaji yana kiran Ummy.
Ummy ta falo, Jalila kuma ta dau leda tai dakin Ameera.
Hassan na zaune kusa da Abba ta shigo, ta zauna sannan ta kallesu tace "d'a da uba ne suke hirar yaushe gamo?"
Abba yai murmushi yace "nikaina ina jiran wannan lokaci, lokacin da Hassan zai zauna dani muyi hirar duniya."
Hassan bai tanka musu ba, Ummy tace "wani abun ya faru ne?"
Yace "a'a kawai dai sirikarsa ce ta nemi mu barta ta tafi tana kunyar zama gida daya da sirikinta da mu."Ummy tace "hakane munyi laifi da bamuyi wannan tunanin ba, sannan bamu tambayeta ra'ayinta ba."
Hassan ya kalli Ummy yace "Ummy ita so take takoma kauye nikuma ina ganin hakan ba solution bane."
Tace "mekake tunani?"
Yace "gwara a nemarmata gida anan ta zauna karami, can yayi nisa."
Murmushi tai ta kalli Abba tace "gaskiya kam yama Jalila nisa wanda zai sata damuwa."
Kare tsuke fuska yai yace "Ummy me kike....."
Katseshi tai tace " ni ba da komai nake nufi ba."
Abba ya kalleta yace "wani abun kike tunani?"
Tace "a'a shawararce naga tayi, me zai hana a gidan da ka siya kwananan wanda ke tarauni a maidata can? Naga gidan karami ne sannan ga yarinya ma mai kula da ita."
Abba ya jinjina kai yace "hakan ma shawara ce, kinga Allah ne yasa bamu sa haya ba dan har an fara tambaya, Hassan sai ka dau Jalila kunduba gidan sai a sai abunda ya kamata."
Yace "to."
Bai jira wani abu ba ya mike, yanasan yama Abba godiya sai dai bakinsa bazai iya furatawa ba, harya kai kofa ya juyo yace "Ummy na hau sama."
Tace "to Hassan."
Ya juya ya fita, Ummy ta kalli Abba tace " Ya kagani?"
Murmushi yai yace " tunda na dawo kullum Hassan sai ya bani mamaki, lalai dolene muje muyina doctor godiya ba shakka shawararsa itace babban magani a tattare dashi."
Ummy ta sake yin murmushi.....
Jalila kuwa tana shiga daki inda Goggo take ta hau nuna mata kaya, Ameera kam tana gefe tana mamaki, kenan mahaifiyarta ce ta asibitin nan? Me yasa a lokacin bata nuna mata itace mahaifiyarta ba? Goggo ta kalli Jalila tace "Jalila garin yaya kika barshi ya kwaso kaya haka? Kudi fa aka sa aka siya."
Ameera tai dariya tace "Goggo ashe ke tayo, shiyasa takasa bari na dau kaya ko daya wai tsada, sai da yaya yazo."
Goggo ta kalli Ameera tace "ke kuwa yar nan ina zan kai kayan nan?"
Jalila ta kalli Goggo wani abu ya tsirga mata na tausayi, tunda Goggo take bata saka kaya masu tsada haka ba, ba ta tana samun kaya kwatan yawan wannan ba, gaba daya kayanta......."
Idanunta ne suka ciciko ta kalli Goggo tace "yaya ya fadamin abinda kikace."
Tace "ya sanar dake?"
Jalila ta daga kai, Goggo ta riko hannunta, Ameera tai saurin fitowa daga dakin.
Goggo ta kalli Jalila tace "Jalila kiyi hakuri, nasan burinki ma shirme nasan ganin mun zauna tare bayan kinyi aure sai dai ko a da can jinki nakeyi dan bazan iya zama da sirikina ba."
Jalila ta daga kai alamar ta fahimta dan batasan tai kuka.
Goggo ta kalleta tace "shiyasa a koda yaushe ake cewa Allah ba azallumin bawansa bane, Jalila ban taba tunanin zakiyi aure cikin gata irin wannan ba, gaba daya mutanen gidan nan zuri'ace ta albarka, dolene mu gode ma Allah akan baiwar daya miki ta samun dangin miji irin wannan."
Jalila ta kalleta idanunta suka zubo da kwalla, Goggo tai murmushi tace "nikam wannan yaran kanin mijinki....."
Da sauri Jalila tace "oh Ya Sageer? Oh Goggo kinsanshi ne?"
Kallanta tai taga ba wani alama ta wani abun tace "a'a na dai ganshi a asibiti."
Jalila tace "oh haka ne."
Sundanyi hira kafin ta mike ta fito.
Tunda ta shiga daki taganshi a kwance ta fito ya dawo falo ta zauna, yunwa ce ta sata shiga dakin a hankali ta dauko tiren abinci ta fito falo taci ta zauna tana danne danne a waya, daga baya ma ta sauko kasa sukai girki ta koma gun Goggo sukai hira da Ameera.
Abincin ranarsu ma data kai taga yana kwance ta diba ta fito falo taci ta koma kasa sai da suka gama abincin dare ita da Ameera sannan ta dauko nasu ta hawo sama.
Yanzu kam a kasa ta ganshi kan sallaya yana karatu, gefe ta koma ta zauna tana sauraran kartun nashi, tana lumshe ido saboda dadi, tana bala'in sha'awar taga tana rera karatunn qur'ani haka.
Hassan na nan zaune har aka kira isha'i sannan yai sallah, itama tai.
Sai binshi take da kallo tanasan tamai magana amma ba fuska.
Mikewa tai ta zubo mai abinci tace "Yaya ka sauko kaci abinci."
Kallanta yai yace "ban dade dacin na rana ba."
Ta mike daga zaman datai a kasa ta matso kusa dashi jikin gado tace "Yaya dan Allah menene? In laifi na maka dan Allah kayi hakuri."
Idanunya kura mata, a ransa yace "me kika min? Haushin kaina nakeji da duk abinda zanyi tun dazu sai naji kina raina, haushin kaina nakeji nasan na ganki kusa dani, haushin kaina nakeji na rashin sanin abinda ke damuna a kanki."
Jalila ta kalli yanda ya kafe ta da ido kana gani kasan tunani yakeyi, tace "Yaya?"
Littafinsa ya dauka baice mata komai ba.
Tsayawa tai shiru kafin ta zauna taci abincin nasa data zuba, kadan ta iyaci dan ya mata yawa.
Har dare Hassan bai kula ta ba, itama haushi yasa ta dauke kai daga kansa tai kwanciyarta, kankace me bacci yayi gaba da ita.
Kwanciya yai ta saitinta yanda yana hangota daga kan gado, ya kura mata ido, what are u to me?
Gani yai tayi juyi ta juya mai baya.
Mikewa na ga yayi ya dau pillow dinsa ya kwanta akan kujera yanda zai ganta dan kusa da kujerar take shimfida.
Ajiyar zuciya yai ya kalli bargon data shimfida yace "wannan bazai sata ciwon baya ba? Kullum kwana a kasa? Gata ba jiki ba?"
(Nikuwa nace waye ya sata>?(?)
Ya dade a haka yana kallanta har bacci ya daukeshi.
Yauma Alhamdulila bai farka da ciwo ba, wajen asuba ya farka, da sauri ya mike yana mamakin kansa anan ya kwana? Ahh wai Hassan hankalinka daya kuwa?
Alwala yai sannan yazo kusa da ita, ya saba sa kafa ya tasheta yau sai gani nai ya sunkuyo yasa hannu yadan bugi kafadarta tare da cewa "Jalila?"
Idanu ta bude cikin bacci ta kalleshi, mikewa yai.
Ta mike itama tai alwala...........
Tunda ta tashi take jinta ba dadi, ba sabon abu bane tasan period dinta ne ya kusa, ita kuma gashi duk sanda zatai al'ada sai tasha azaba na ciwon mara, a gida Goggo sai ta sata tasha dauri, ko ta siyo panadol......
***********
Inna ce tasa aka kira mata dady, yana zama mumy ta shigo taja ta zauna.
Inna tace "Fatima meye hakan? Magana zamuyi."
Mumy tace "kome zakuyi kuyi agabana, sannan nima magana nazo fadamiki."
Inna ta kalleta tace "maganar me?"
Tace "kiba Abubakar mukamin Chairman na company ke kiyi resigning, dama ai kin dade kina cewa zaki bani ke kuma ki sauka."
Inna ta kalleta cikin tashin hankali sannan ta kalli Dady wanda shima yai alamar wai mamaki, tace "Abakar kai ka zigata?"
Da sauri Dady ya kalleta yace "Menene hakan? Ce miki nai inasan shugabanci na company din? Meyasa kike neman sa Inna taga kamar nine nake saki abu? Banasan irin wannan abun."
Mumy ta kalleshi tace "Dadyn Yasmeen."
Ya hade rai yace "Taya zaki yanke hukunci ba tare da kin sanar dani ba?"
Tace "gani nai...."
Inna ta kalleshi lalai yaran nan me? Ce miki akai inasan shugabanci?????
Tai wani murmushin takaici.......
#Oneluv=ؕ?
[12/7, 9:53 PM] El-hajj: =??? *JALILAH* =???
Written By : *AYUSHER MUHD*
'?ote me on Wattpad : *Ayusher Mohd*
*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*
(_D home of expert and perfect writer's_=ء?)
*48*
Ummy ce ta kalli Jalila tace "Jalila lafiya? Naga tau kamar bakyajin dadi?"
Tace "lafiya ta kalau Ummy."
Ummu tace "da ina tunanin ko in dau Goggo da Ameera muje dakanmu mu siyo kayan gidan muje a saka, kamar zaifi dan nasan halin Hassan bazai shiga gun kayan ba, kinga kuma ke kadai abin bazai yiwu ba, sai da babba."
Jalila tace "to Ummy."
Ummy tace "ko kinfiso kije da kanki? Ko mu tafi tare?"
Da sauri tace "a'a wlh Ummy hakan yafi, ni me na sani a wannan harkar?"
Ummy tai murmushi ita kuma bataso subar Hassan shikadai dan Abba ya fita duba wani aiki.
Jalila tace "me za'a dafa da rana?"
Ummy tace "komai ma duk abinda miki."
Jalila tai murmushi sannan tace "to Ummy nagode Allah ya saka da alkairi."
Ummy ta kalleta cikin kulawa tace "Hassan fa?"
Jalila tace "yana daki."
Ummy tace "nasan yana daki ai haryanzu bai sauko ba?"
Jalila tace "Ummy kema harkin gane? Ni na rasa me namai."
Ummy ta guntse dariyar dake neman zuwa mata tace " da alama dai kin mai babban laifi tunda har nima na gane."
Jalila tai ajiyar zuciya tace "na kasa gane me namai, kuma shima ya ki fadamin."
Ameera da ta fito tasa dariya tace " ba kunya?"
Jalila ta kalleta sannan tai saurin mikewa, sai yanzu ta fahimci bai dace ba.
Ummy tasa hannu ta rikota ta makama Ameera harara tace "to uwar sa ido, menene damuwarki? Ni bana sirikanta da ita 'ya ta ce."
Ameera ta kara yin dariya tace "hmm nayi shiru ai."
Ummy ta kalleta tace "kicema Goggo ta shirya zamuje wani guri."
Ameera tace "ina zaku bani?"
"Ko shirya dake zamuje kema, in muka sai kayan farko sai ke da Lantana da Goggo akaiku gidan ni da Sageer sai mu karasa siyan abinda ya kamata."
Ameera tace to, tai ciki da sauri.
Haka suka shirya Jalila na kusa da Goggonta, Goggo sai tambayarta take wai ina zasu? Itakam Jalila cewa kawai take nima ban sani ba Goggo.
Haka suka fito Sageer ya daukesu a mota, Jalila ta baishi da kallo duk ya canza da dai ba haka tasan Uncle ba, mutum ne faran faran dasan tsokana, yanzu kuwa ya rage sannan duk yadan rame.
Tana tsaye har motar tasu ta bar gidan sannan ta dawo ciki.
A falon kasa tadan kwanta dan mararta ciwo take mata daurewa kawai takeyi, mikewa tai can ta hau sama dan tana san shiga toilet.
Hannu tasa ta bude kofar dakin dakin ta shiga, yana zaune a kasa yana cin abinci da alama baima dade da tashi ba.
Tana shigowa ya kalleta, itama kallansa tai ta tsaya sannan tace "Yaya ka tashi?"
"Umm, dazu." Ya fada idansa na kanta, ta dan tsaya kafin tace "hmm su Ummy sun fita tare da su Goggo."
Yace "okay."
Tadanyi shiru kadan sannan tace " duk tare suka fita."
Yace "nagane, kina nufin daga ni sai ke kenan ko?"
Tace "hmm can gidan zasu."
Yace "duk na fahimta."
Juyawa tai ta nufi toilet kafin ta kara juyowa tace "Yaya!"
Ya kalleta tace "abincin bai huce ba?"
Yace "me kikesan ji? Da alama wadannan maganganun naki akwai abinda kike san ji."
Tace "bakomai." Ta shige toilet.
Da kallo ya bita ya dade kafin yacigaba da cin abincin.
Tana fitowa yana gama cin abincinsa, tadan tsaya a jikin kofar saboda ciwon da mararta yakeyi gashi daga bayanta yake tahowa.Da kyar ta taka ta zauna akan kujera tadan tukunkune.
Mikewa yai daga kasa ya juyo ya kalleta, bai kawo komai a ransa ba ya dauka dai kwanciyar tai ko toilet din data shiga ne ya sa ta.
Komawa yai ya zauna ya dau littafi, dan nishin datai kadan ne yasa ya juyo da sauri ya kalleta.
Yace "Jalila!"
Dagowa tai ta kalleshi a hankali tace "naam."
Ganin haka yasa ya sauko da sauri yazo kusa da ita inda take a kwance, kusa da inda kanta yake ya zauna sannan yasa hannu ya dagota.
Kallanta yai itama ta kalleshi yace "menene?"
Tace "bakomai yaya..."
Yace "menene kikeyi to hakan?"
Tace "me nayi?"
Idanu ya kara kura mata sannan yace "menene? Karkisa na sake tambayarki."
Ta kalleshi tace "marata"
Yace "ciwo?"
Ta daga kai alamar eh.
Yace "kinayi ne ko yau ne kika fara?"
Tace "inayi dama."
Shiru yai yana kallanta yace " menstrual pain?"
Kallansa tai sannan ta saukar da idanta kasa.
Yace "ko muje asibiti?"
Tace "a'a yaya zai daina zuwa dare."
Idanunta tadan runtse dan abin karuwa yake yi.
Sa hannu yai ya dagota ya kawota jikin gado yace "kwanta."
Kallansa tai sannan ta kwanta.
Zama yai kusa da ita yana kallanta, ita kuma idanuwanta a runtse suke tasa hannunta kan kasan cikinta.
Wayarsa ya dauko ya shiga google ya rubuta how to relieve menstrual pain.
Nan ya shiga dubawa, kallanta yai sa hannu ya gyara mata kwanciyarta zuwa rubda ciki.
Juyowa tai ta kalleshi yace "menene?"
Kai ya girgiza alamar ba komai sannan ta gyara kwanciyarta.
Shiru yai yana tunani, massage lower back and abdomen? Ta ina zai iya?
Mikewa yai tsaye da sauri ya koma kan kujera ya zauna dan jin yanda zuciyarsa ke bugawa da sauri.
Jalila kam abin ne ya kara motsawa juyawa tai ta kara dukunkunewa tana dan nishi kadan.
Kallanta yakeyi sai dai hankalinsa duk ya tashi.
Ya mike ya taso kusa da ita ya gyara mata kwanciyarta zuwa na dazu, idanunta ne suka ciciko ta kalleshi tace "yaya hakan bayamin dadi."
Yace "na sani daurewa zakiyi."
Tace to sannan ta gyara kanta tana runtse ido.
Jitai hannunsa akan kasan bayanta inda yake mata ciwo, kallansa tai, ya kalleta shima fuska a hade yace " ki kwanta ba wani

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login