Showing 141001 words to 144000 words out of 149705 words

Chapter 48 - Jalilah Book One Complete Hausa.doc

Ayusher   

28 Oct 2025

621

wanda yai shiru a tsaye, tace "Sultan! Ba magana?"

Ya tsugunna kansa na kasa yace "Goggo ina wuni?"

Tai dariya tace "Haba Sultan menene hakan? Kamar wanda baka sanmu ba?"

Yai shiru kansa a kasa.
Sun danyi hira kadan kafin su taso su tafi......

***********


? Takardar gidan ya mika musu tare da sa hannu akan takardar shaida sannan suka bashi check na kudin gidan, kallan check din dake dauke da kudi zunzurutu har million 30, gidan ya kara daraja ne saboda akwai furnitures, wani irin dadi ne ya kamashi, dan shikam gani yake ya cucesu ne, ya danne farincikinshi yace "kamar yaushe zaku dawo?"

Mutumin ya kalleshi yace "eh, muna sa ran gobe dan dama iyalaina zasu baro garin Abuja ne su dawo nan."

Dady ya jinjina kai yace "bakomai ni yau zan tashi, nagode sosai."

Sukai musabaha sannan suka fito, dady cikin murna yai daki dan dama ya gama tattara kayansa, sannan ya koma ciki, wani irin ihu naji ya saki na farin ciki sannan ya kara gyara kayansa kawai ya jawo ya lodasu a mota ya ja ya fita.


Hotel kawai ya wuce ya kama katan daki suit room, ya kwanta cikin jin dadi, ya fara tunanin menene zai fi mai? Business zai fara ko kawai ya fita yawon shakatawa? Inya dawo ragowar ya nemi gida karami.

? Haka yai ta sake sake marasa ma'ana, har wani bacci mai dadi yai gaba dashi.


? Washegari yana tashi kawai ya fita yaci abinci ya siyo kayan makulashe ya dawo ya kwanta saboda yana san gobe yaje ya ciro kudin nan yasa a account dinsa.

? Ba abinda yakeyi sai dai yaci yasha ya kwanta kawai ya kunna waka yana ji.
Rayuwa ta masa dadi.


****

Yau da safe yana sallar asuba ya kasa komawa bacci saboda zumudin zuwa bank, wanka yai kawai yasa kaya ya zauna akan kujera yana kirgen lokaci, ganin lokacin baya sauri ma yasa ya fito daga hotel din ya shiga mota yaje gaban banki ya tsaya.

Karfe takwas nayi yana ganin anfara hidima yai wuf ya shige ciki.

? Sama yahau sannan yaje inda ya kamata ya mika check dinsa tare da sa hannu a aljihu irin babban alhajin nan.

Kallan check din yai ya dinga juyashi kafin ya kalleshi yai kafin yace "Alhaj wannan check din waya baka shi?"

Yai murmushi saboda ya fahimci kudin ne ya tsorata su.

Yace "Menene na tambayar abinda bai dameka ba, yi sauri ka bani inaso nai transfer dinsu bank dina ne."

? Mutumin yai shiru kafin ya fito daga inda yake yace "ina zuwa."

Bai fi minti 10 da fitaba sai gashi ya dawo shida wani, nan dayan ya kalli Dady yace "Alhaji ina ka samu wannan check din?"

Ran dady yadan baci yace "kunsan ko ni wanene kukemin wannan tambayar banzan?"

Mutumin ya kara sanyaya murya yace "ba haka bane, wannan takardar ta check ba namu bane, anyi amfani da irin namu ne anyi jabu, dan idan ka daga shi sama shida namu zakaga ba iri daya bane, sannan ko karfin takardar ma ba iri daya bane."


Dady cikin rashin fahimta yace "me kuke nufi kenan a takaici? Kunaso kucemin ba zaku bani kudi na bane ko kuma me?"

Yace "bawai zancen zamu baka ko zamu hanaka bane, zancen an cuceka an baka abu jabu mukeyi."

? Cikin tashin Dady yace "an cuceni kamar ya?"
Yace "am sorry to say amma mu ba abinda zamu iya maka, sai dai ka koma gun wanda ya baka ka nemi ya baka wani ko kuma ya maka transfer."


? Yana neman sake magana dayan ya dafashi alamar yai shiru dan ya kula Dady kamar ya gama hasala, Dady yai shiru kafin ya fito da sauri daga cikin bank din, da sauri ya fada mota sannan ya wuce gidan.

? Gani yai anata sauke kaya da sauri ya karasa gun mutumin dake tsaye yana bada umarni, da gudu ya karasa inda yake yace "Malam dan Allah ina mai gidan nan?"

Mutumin cikin mamaki ya tureshi tare da cewa "Meye hakan?"

Dady a rikice yace "dan Allah mai gidan nan nake nema."

Yace "nine mai gidan kai waye?"

Dady hankali a tashe yace "bakai ba wanda na saidawa gidan shekaranjiya."


Mutumin ya tureshi da karfi har Dady ya fadi a kasa yace "kai dalla bansan hauka jiyan nan nasai gida million 50 yau kuma kazo kana tambayata maganar banza?"

Da karfi ya kira mai gadinsa yace "ya fitarmai da wannan mutumin daga gidansa.

Mai gadin ya kalleshi yace "zaka fita ko na fitar dakai?"

Dady ya mike kamar wanda zai fadi ya fita, yana fita gate ya zauna a bakin gate din..........


*******

#OneLuv=ؕ?=??? *JALILAH* =???


Written By : *AYUSHER MUHD*
Wattpad: *Ayusher Muhd*


*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*

*78*


Dady yai tsutsuru a waje har baisan sanda lokaci yai ta tafiya haka ba, mikewa yai jin cikinshi na wani irin karar yunwa, motarsa ya shiga ya zauna idanunsa sun firfito, tada motar yai ya wuce hotel din da yake ciki, yana shiga ya wuce cikin toilet ya sakarma kansa ruwa ruwa na zuba yana tunanin abinda ke faruwa, yanzu wannan uban zuzurutun kudin ya wuce kenan ko me? Gidansa fa?

Jiyai kansa yayi dumm da karfi ya saki wata irin kara na takaici ya daki bango da hannunsa, sam bai kula da jinin dake ta zubo mai ba, hucci kawai yakeyi kamar wani kumurci.

? Haka ya fito yasa doguwar riga ya bude window yana kallan gari, gaba daya kansa ya rufe yama rasa ta ina zai fara yin tunani, ga wata uwar yunwa da yakeji, mikewa yai ya dau jakarsa ya fita reception.

? Gun masu aiki a hotel din ya nufa yace "yanaso a bashi karamin daki da toilet sai a bashi ragowar kudinsa."

Nan sukacemai ai bazai yiwu ba tunda dai dama na kwana hudu ya biya kuma yanzu yayi biyu bayanda zasuyi, bakin ciki ya kara mamayeshi gashi dama ragowar na account din ya kwashe ya biya saboda yana ganin yanzu kudi sunzo masa.

? Ya baza tagumi a cikin reception yaji ance "dunoyar tama zafi ne?"

Juyowa yai ya kalleta, yarinyace wacce batafi shekara 30 ba tasha gayu nagaske, Dady ya kalleta sannan ya juya yana kallan wani gun.

? Kallansa tai sannan tace "kudi kake nema?"
Idanu ya kura mata baice komai ba, tace "ka biyoni zan baka."

Ta fada tare da ajige key din dakinta a kusa dashi sannan ta mike, ta dan matso kadan tace "1day 500k, deal?"

? Dady da sauri ya dago ya kalleta, kashenmai ido tai sannan ta mike tai ciki.

Dady ya bita da kalli sannan ya dauki key din ya mike tare da jan jakarsa, haryakai hannunsa zai murda dakin ya tuno Jalila, Safeena, Sultan da Yasmeen.

? Da sauri ya saki kofar sannan ya fara ja baya baya, yana san kudi na fitar hankali dan shi burinshi kenan ya zama babba wanda ba wanda ya isa ya rainashi, sai dai duk a cikin san kudinsa banda ta hanyar zina, in yaransa suka ganshi fa?"

Da sauri ya juya yai waje tare da yarda makullin( ina duniya zaki damu? Ace wai yanzu mace itace ke neman namiji kuma ita ke biyanshi saboda rashin hakuri da san kai da san zuciya? Allah ya mana tsari ameen)

Dady ya koma cikin dakin nan wanda yanzu gaba daya haushi yake bashi......

Haka ya gama kwanansa ya fito daga hotel din, ina zai je? Shi ba abokai ba ba wasu yan uwa ba, haka yaje ya nemi karamin hotel ya kara biyan wani kudin ya shiga, yanzu kam gaba daya ba komai a account dinsa sai dubu talatin, wanda haka yake zara yana siyan abinci.

Gaba daya a dan kankanin lokacin nan har Dady ya canza.

Duk yanda ya kira Jalila kuwa bata dauka dan itakam tasan magana daya ce tsakaninsu, itakuma bazata taba taimaka mai ya kara lalacewa ba.

******

? Yanda aka bude kofar kitchen din ne yasa Ummy da Jalila suka juya da sauri dan ganin meke faruwa, Hassan kam idanunsa sun rufe da farinciki, kusa da Ummy yazo ya rike hannunta yace "Ummy na ta fito."

Tace "Visa din?"
Da sauri ya daga kai yana dariya ya kalli Jalila wacce ta juya da sauri tare da cigaba da wanke wanken da takeyi.

? Ummy ta mintsine hannunsa tace "Shine kake murna haka gaba daya kamar dama ka gaji da mu?"

Kansa yadan sosa yana dariya yace "kema Ummyna kinsan ba haka bane, murna kawai nake dai abinda ake nema an samu ba wani abu ba."

Tace "ba wani nan, bayan ga fuskarka nan ta nuna min a fili."

Yai dariya yace "dagaske?" Ya fada yana shafa fuskarsa, Ummy ta girgiza kai tace "oh ashe ni kadai ce nake tunanin rashinku."

Ta juya itama tana karasa abinda takeyi.

Hassan ya matso yace "Kai Ummy na."

Tace "Ah bari na dauko wayata." Ta juya ta fita.

Hassan na gani ta rufe kofa ya matso ya rungume Jalila yana dariya.

Tace "Oh ni yaya, dan Allah ka daina farin cikin nan haka nan, kar Ummy taji ba dadi."

? Yace " to wai ni yazanyi na daina? Nikam ki gama wannan aikin kizo mu fara hada kaya."

Jalila ta dan tureshi tace "ni dai kar Unmy ta shigo."

Ya saketa yace "ni yau ma zan sai ticket dan jibi sai tafiya, gobe na kaiki gidan Goggo sallama."

Baki ta bude tana kallansa tace "oh ni yaya."

Yace "harna fadawa Abba ma nasan yanzu shima ya fadama Ummy, kallan mamaki kawai takemai, shikam juyawa yai ya fita.

? Haka kuwa tana fitowa taji a bakin Ummy wai jibi zasu tafi, haka ya sata a daki sukahau hada kaya, itakam duk kunya ta isheta.

Washegari ya kaita gidab Goggo acan ta wuni, sunsha hira da Sultan, Goggo itakanta tayi mamakin wannan tafiyar da wuri haka, rasa mai zatace tai kawai sai dariya tai.

Ya sallami Goggo kudi mai kauri dan yasan Ummy da Abba zasu dinga kula dasu, sai dai shima yana san yai wani abin.

? Wajen magrib yazo ya dauketa ya kaita gidan Mumy wai tanasan tayima su Safeena sallama.

? Gida ne karami amma agunsu wadanda suka taso daga katan guri, dakuna biyu ne da falo da kitchen.

Mumy na ganin Jalila ga saki fara'a cikin jin dadi, Safeena ma tana toilet tanajin Mumy na kira. Sunan Jalila tai sauri ta fito tana murna, Jalila na zaune kusa da Mumy, Yasmeen na zaune a cinyarta tana bude alawoyin da Jalila ta bata, Safeena ta taho da sauri, ta rungumeta.

Mumy tace "nikam har abin yazo haka?"

Tace "wallahi gashi har mun kusa tafiya."

Jalila ta kalli Safeena tace "kin fara neman skul ne?"

Tace "wallahi maganar da muke da Mumy kenan kullum amma jiya na dameta ta kira Sani yace sai nayi Jamb.

Jalila tace "haka ne amma wacce kikeso?"

Tace "F.U.D."

Jalila tace "Allah ya taimaka ya bada Sa'a."

Tace "Ameen."

Jalila ta kalli kasan carpet wanda da alama Yasmeen abinci ta gama ci, shinkafa da wanke sukai damai da yaji, Jalila ta kurama kasan ido tana tuno lokacin da agida ake sata yin abinci kusan kala uku, kuma ko za'ai me basa cin mai da yaji sai anyi miya da nama kachha kacha.

Kallan Mumy tai tace "Mumy ya kuke da kayan abinci?"

Tace "kudin da Hassan ya bamu muke cancanawa kafin mu samu a saida filin Da Inna tabarmin, sannan tanada wasu kudi a bank, sai dai su sai anyi cike ciken takardu kafin a bamu."

? Jalila tace "To Allah ya taimaka, amma Mumy tunda kinyi karatu ba gwara ki fara aiki ba ko a company din Inna ne? Inkika fara kamar abin zai kara sauki."

Cikin mamaki ta kalli Jalila tace "Oh ya akai wannan tunanin baizo min ba?"

Jalila tai dariya, Mumy tace "aikam zanyima Kanin Hassan magana, sannan ai inama da Shares din Inna."

Jalila ta kura mata ido tana kallo, shiyasa Dady ke cutanta sam bata tsayawa tai tunani? mai zurfi.

Jalila ta kalleta tace "bari na baki numbersa sai ki kirashi."

Sundanyi hira kafin Hassan ya kirata ya sanar da ita dawowarsa, fitowa tai ta shiga mota, a hanya tana bashi labarin yanda sukai.

Ya riko hannunta yace "Umm wannan babyn daga inna aka samota ne haka?"

Tai dariya tace "daga ina kuwa?"

Yai dariya zaiyi magana wayarta ta shiga kara, kallan wayar tai sannan ta katseta ta kalleshi, yace "shine?"

Tace "eh."

Yace "bakya tunanin ya kamata kiu hadu kafin ki tafi?"

? Ta kalle tace "Ai ni Dady bansan....."
Ya katseta yace "ko me zai miki, ai sallama kika mai, muje gidan ko yayane kuyi sallama mahaifine."

Jalila tai shiru batace komai ba, a kofar gidan suka tsaya saboda sunata yima mai gadin alama amma bai ko kallesu ba.

? Sai da sukai parkin ya matso yace "Daga ina?"
Hassan ya kalleshi wato har mai gadi ya canza?

Yace "kayima mai gidan magana kace Jalila nasan magana dashi."

Kamar bazaije ba sai kuma ya shiga, bai jima ba sai gashi ya dawo, ya sanar dasu cewa bai san wata Jalila ba.

Ran Jalila ya baci ta kalli Hassan idanuta suna neman tara ruwa tace "Yaya!"

Hassan ya kalli gidan sannan ya tada mota, Jalila ta kwantar da kanta a jikin window, kiran daya kara shigo mata ne yasa ta kalli wayar sannan ta kalli Hassan, ran Hassan ya baci, bai santa ba amma yasan numberta? Haushi ya kamashi ya daga wayar rai a bace, kafin Dady yace wani abu Hassan yace "baka santa ba taya kasan number ta? Inhar baka santa ba bai kamata kasan numberta ba."


Kan Dady ya fahimci abinda yake nufi har Hassan ya kashe wayar, ya kasheta ma gaba daya cikin bacin rai.

Haka suka shiga gida, Su Ummy dukansu na zaune a falo suka shigo.


? Jalila na shiga ta gaishesu da gida, Abba yace "Jalila an gaji ko?"

Tak dariya tare da maida kai kasa, yace "ya zakiyi, wannan mijin naki ya zafaffa sai kin bar kasar da wuri? Kamar wanda ake korarsa."

Hassan ya kalli Abba yace "Abba kaifa ka karfafamin gwiwa akan na tafi da wuri."

Ummy ta kalli Abba da sauri tace "dama kaine?"

Da sauri yace "ni a ina? Gani fa nai hakan yakeso sai nadan sa baki kadan dan kadan fa nabi bayan hakan."

Hassan yace "kadan? Abba kaifa ka......."

Abba ya harareshi tare damai alamar yai shiru.

Hassan yana dariya yace "Ummy na!"

Sageer yace "Ummy karki wani yarda da dadin bakin yaya, matarsa kawai ya sani."

Kunya ta kama Jalila tai kasa dakai, Amira tace "kaima Yaya Sageer ya kamata ka motsa, kaga in Aunty Jalila ta tafi gidan zaiyi shiru gwara ka kawo wata."

Sageer yai dariya tare da kallan Hassan, Hassan yace "me? Badai haryanzu baka fadama ko Abba ba?"

Sageer ya sinar dakai yana dariya, Abba yace "Sageer ni aka munafirta?"

Sageer da sauri yace "wallahi ba haka bane Abba inataso muyi maganar, kasan yanzu aikin ha karu shiyasa."

Haka akai ta tsokana Ummy na hira tana kuma kukulla abubuwan data shiryama Jalila wanda zata tagi dashi.

*********

Dady kam gaba daya yau ta karemai dan kudin daya biya na hotel din ya kare kuma bashida wani, shiyasa yake ta neman Jalila akan ta taimaka mai, cikin lota ya fito ya shiga yana ta nemanta jin ma wayar a kashe daga baya yasa ya cilar da wayar tasa cikin takaici.

? Kwanciya yai a cikin motar sannan ya dauko wayarsa yana duba sunaye ko akwai wanda zai iya kira, sai dai kaf wayarsa ba wasu mutane, daga su Mumy sai 'ya'yanta sai Jalila, sai number Inna sai kuma harkokinsu na business.

Bakinsa ya ciza cikin bakin ciki yace "duk kun lalatamin rayuwa, na dage ina muku bauta amma karshe ku hanani abinda na dace dashi? Gyara kwanciyarsa yai tare da kallan cikin motar, wai shine ke kwana a mota? Lalai dole ya nemo mafita, zaije ya samu Jalila gobe har kasa zai tsugunna ya nemi yafiyar Hassan da Mahaifinsa, ya tabbatar intaga halin da yake ciki zata tausaya masa.


**********

Hannu yasa ya jawota yace "me kuma kikeyi?"

Tace "bakomai, so nake kawai na karasa hada kayan nan."

Yace "Yanzu ina toilet wani abu ya fadomin, anya Dadynki bai saida gidan nan ba?"

Tace "ah haba? Ya saidashi ya koma ina? Sannan gidanda ba nashi ba? Taya zai saida musu abinda ba nashi ba?"

Hassan ya ajiyaf zuciya yace "kuma haka ne."

Tace "Bansan dai mai ke damunsa ba, na kasa gane dalilin kiran nawa."

Hassan yai shiru shima yana tunani.


? Bayan sun kwanta wajen karfe shadaya hankalinsa ya kasa kwanciya, mikewa yai ya dau wayar Jalila ya fito falo.

Kunnata yai sannan ya kira wayar Dady, Ringing uku ya dauka da sauri yace "Jalila?"

Hassan cikin mamaki yace "dazu da mukazo gidanka me yasa ka kore mu?"

Jin murtar Hassan yasa yadan yi dum....
Sai dai jin kalamansa yasa yace "gidana???"



#OneLove=ؕ?=??? *JALILAH* =???


Written By : *AYUSHER MUHD*
Wattpad: *Ayusher Muhd*

_Gareku duk mai kaunar littafin nan, ina tsananin godiya akan yanda kuka nuna kaunarku ga littafin nam, nagode kwarai da gaske>?p?>?p?OneLuv=ؕ?_


*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*

*79*

Dady yai shiru har saida Hassan yace "dazu."

Dady ya hadiye wani abu na bakin ciki yama kasa magana.

Hassan yace "kana ina?" Dan ya fahimci da matsala.

Dady yace "inzo ne?"

Hassan yace "eh in zaka iya, sai na sameka a waje."

Da sauri dady yace "to."

Mamaki ya kama Hassan ya bi wayar da kallo kafin yakoma ya zauna yai shiru yana tunanin rashin adalcin da akama Jalila da mahaifiyarta, da rashin adalcin dayama Mumy da 'ya'yanta.

Wayarce tai ringing kamar zata katse kafin ya daga, Muryar dady taji akan wai yana waje.

Hassan ya sauko a hankali ya fita waje.

Dady na tsaye a wajen gate, yana ganin Hassan ya taho da sauri, Hassan ya bishi da kalli duk ya wani mole ya canza, kayan jikinsa duk sunyi datti.

Dady ya matso da sauri yace "Ina wuni?"

Cikin mamaki Hassan ya kalleshi yace "Ina wuni?"

Dady ya kalleshi sannan yadan sosa kai yace "Hassan ina Jalilan?"

Hassan ya hade fuska tamau yace "menene dalilin korarmu dakai da mukaje gidanka?"

Dady ha kalleshi jiki a sanyaye sannan yace "Gidan ba nawa bane yanzu."

Hassan ya kalleshi wato tunaninsa ya tabbata, Dady yace "wasu mugaye na hadu dasu suka kwace gidan ba tare da na samu kudina ba."

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login