Showing 126001 words to 129000 words out of 149705 words

Chapter 43 - Jalilah Book One Complete Hausa.doc

Ayusher   

28 Oct 2025

613

mafita, ko ta gudu?

? Sageer ne ya juyo suka hada ido, nan ya mata alama data shiga, shiga tai sannan shima ya shigo.

Haryanzu waya yakeyi sai dai yana juyowa yana kallanta ko zata nunamai wani gun.

Hannu tasa tanunamai gaban wani gida, nan ya kashe wayar yace "nan ne?"
Kai ta daga sannan ya karasa yai parking.

Gidane flat wanda a wannan lokaci zamu kirashi da rufin asiri, karami ne gidan dan daga waje ma zaka san ba wani girma ne dashi ba, sannan ba gate bane kofa ce a gidan.

Kallansa tai tace "na gode." Tasa hannu zata bude kofar.
Yace "sunana Sageer, dan naga kamar bai dace mu rabu ba wanda yasan sunan dan uwansa."

Juyowa tai ta kalleshi sannan tace "nagode."

Ta bude kofar, har ta sa kafarta bata juyo ba tace "kaji sunana a cikin chemist dincan, sunana Maimuna."

Yace "ohh haka ne ashe naji, amma ya akai na shafa'a?"

Kallansa tai sannan tadan motsa baki ta murmusa kadan sannan ta fita, tare da kara cewa Nagode.

Tana shiga ciki ta tadda Mamanta na wanke shinkafa.
Tana ganinta tace "Maimuna? Ya naga kina dingisawa? Lafiya?"

Kallansa tai kamar zatai kuka sannan ta zauna akan kujera irin ta tsugunnon nan, tace " Mama wani dan......." sai kuma tai shiru kafin tace "bigeni akai a hanya, ai nikam kafin na kara zuwa gidan yaya farida Allah sai an dade."

Maman tai dariya tace "sanda zaki dau kafa ki tafi ina ina? Tunda yanzu ake hutu ai kuma sai a hankali."

Shiru tai tana tunani, wanda ita kanta batasan tunanin me take ba, sai dai kawai ta kurawa kasa ido.


************


Sageer na juyawa yace "oh a kusa ma dasu Aunty Nana take, nan ya gangara gidan yana cewa likita ce?? Ahh ina...,? student? Kai ya jinjina yace da alama kam dan yarinyace, dariya yadanyi yace student harda nunawa irin ita likitan nan ce? Ko da yake hakan nada kyau alama ce ta nuna tanada confidence akan karatunta.

? Ganin ya wuce kofar gidab yasa yai saurin kallan koffar gidan tare da yin reverse yace "ahhh Sageer."

Yasa hannunsa acikin kansa.

Bugawa kofar yai yaga ba wanda ya bude, wayarsa ya dauko ya kira Aina'u yace "Aina kina ina ne hakan?" Tace "ni ai ina Sokoto."

Cikin mamaki yace "Sokoto? Me ya kaiki?"

Muryar yayarta yaji tace "me takeyi anan ko?"

Da sauri ya kashe wayar tare da shigewa mota yace "au ashefa acan Aunty ke aure?"

Tada motarsa yai yai gaba.


************


? Mumy ke ta kara kiran wayar dady amma yaki ua dauka, duk yanda takira kuwa ba'a dauka, kallan Safeena tai tace "Safeena inaji baya kusa ko ya bar wayar a wani gun."

Safeena tace maybe.

Sultan dake gefe yana latsa waya ne yace "yana gida har na fito."
Cikin mamaki mumy tace "bacci yake?"
Yace yana falo yana kallo.

Mumy tai ajiyar zuciya tace "maybe wayar ya barta a daki."

Har dare su safeena da Sultan suka tafi sam ba dady ba alamarsa sai kiransa take bai dauka ba.

Harta gaji ta daina.


*************


Ihun data kurmane yasani na tsorata, gani nai cikin hanzari ta nufi kitchen, wuka ta dauko ta shigo dakin cikin tashin hankali kamar mahaukaciya sabuwar kamu.

? Zaliha jikinta banda uban rawa ba abinda yakeyi, shi kansa jikinsa rawa yake kamar wanda ake kadashi.

? Zaliha ta kankame rigarsa tana ihu tace "shikenan yau ajalina yayi, uban me ya kawoka dakina?"

Hannu yasa ya tureta da karfi harta fadi yace "ki zo falo inda nake cikin wannan shigar kice bazan biyoki ba? Sannan dana biyoki ai ke kika fara rungumeni." Ya fada yana nunata sanye take da vest wanda gaba daya rabin kirjinta a waje yake da wani short knicker sanda ya matseta dam.

? Banko kofar datai ne yasa Zaliha ta kara kwarma ihu tana kada kankameshi da neman ya taimaketa.

Tureta yai da karfi ta kuma kanta a jikin gado, kanta ya fashe, amma kuka ya hanata magana.

Tana shigowa yai toilet da gudu ya shiga ya rufe.

Kan Zaliha tai tana ihu, Zaliha ta hade hannayenta alamar roko, tana kuka tana cewa "tuba nake Aunty ko taimakeni ki yafemin, da alama na haukacene dan bana cikin hayyacina, ko kuma inaji Taura ne yamin asiri dan na tabbatar ba'a hayacina nake ba.

Sa kafa tai ta harbeta da karfi sannan ta daga wular kamar zata caka mata, sai kuma naga ta tsaya, ihu ta kara sawa ta cillar da wukar sannan ta bude wardrobe ta fara cillo mata da kayanta tace "fita dan*******>??"

Wallahi in kika kara minti biyu a gidan nan zaki fahimci ko ni wacece, sannan kayanki kawai zaki dauka wallahi ko biyar dita bazaki fita dashi ba.

Kuka Zaliha ta shiga yi tana neman Yayarta data temaka ta mata afuwa.

Haka ta kwashi kaya kadai ta fita.



***********



Kai ya girgiza mata idanunsa a rufe yace "ban yarda ba."

Murmushi tai sannan ta kwanta itama tana fuskantarsa cikin sanyin murya tace "to ni ya zanyi?"

Yace "ina na sani, ni dai asani."

Shiru tai tana tunani, wai dole sai ta sashi ya bude idansa.

Kallansa tai tana murmushi sannan ta matso da fuskarta a hankali tana kokarin kai bakinta kan goshinsa, hannu yasa ya jawota daf dashi, idanunta ta bude sosai tana kallansa, shima bude nasa idon yai yana kallanta kafin yace "a karasa."

Kallansa take gabanta na faduwa tace "mene?"

Idanunsa ne suka canza yace "abinda ake shirin min, gani nai bazan iya missing ba idona a rufe."

? Kallansa tai tana numfashi da dan sauri, tace "ba mission din ya kare ba? Tunda ka bude idon ba?"

? Kai ya girgiza yace "a ina?" Ya nuna mata bakinsa yace anan nakeso.

? Dan harararsa tai kadan sannan ta matso da fuskarta ta dora bakinta kan nasa tana neman matsawa.

? Bude bakinsa yai yasa nata a ciki, dama da alama kiris yake jira.

? Sun dade suna sumbatar juna kafin su tsaya, a hankali suka kalli juna.

Gani nai sun sa dariya a tare baki yasa ya cije lebanta, kallansa tai sannan ta kara dariya ta dan tureshi kadan tace "gaskiya yaya wannan cin zali ne."

Yace "to a rama mana in anji zafi?"

Tace "zan rama amma ba yanzu ba."

Dariya yai kafin yace "dazufa da kuna tare dasu Ummy munyi magana da Abba."

Tace "wai ka fadamai?"

Yace "sosai ma, me za'a jira?"

Tace oh yaya ba kunya, kuma me yace?"

Hassan yace "matso kiji."

Matso da kunnenta tai yakai bakinsa yace "kin tabbatar kinaso kiji?"

Ta daga kai, yace "hmm to a sakemin."

Kallansa tai tace "me kuma?"

Yace "abinda akai yanzu ni bai ishen ba."

Yanda yai maganar ne ya bata dariya tace "dan Allah ka fadamin."
Yace "sai kin biyani tukunna."

Tace "ai ko aiki sai anyi ake biya, inka fadamin zan ma."

Yace "tam na yarda."

"Dana fadamai cewa yai zai duba yaga wacce kasa ce tafi dacewa dan kinsan na fadamiki ya zauna a Egypt muma kuma haka, yanda na kula dai yafisan nan din.

Sai dai kinsan ya dago mu."
Da sauri tace "a me kuma?"

Kuncinsa ya nuna mata yace "bani half fee."

Sumbatar kuncinsa tai tace "me ya dago?"

Yace " cemin yai wai zai fadawa Ummy ba saboda mu zauna mu kadai bane mukesan tafiya."

Ido ta zaro tace "haka yace?"

Yace "eh kinga da alama ya dagomu."

Tace "kai kuma me kace?"

Yace "cewa nai Abba na gode da fahimta."


Idanu ta zaro sannan ta ceji lebanta tace "mene? abba na gode da fahimta?"

Yace "Eh, ba fahimtata yai ba?"

Haushi ya kara kamata tace "oh ni naga ta kaina, yaya so kake na daina sauka kasa."

Yace "menene? Yanzun ma laifine wai?"


Kamar zatai kuka tace "ya za'ai kacema Abba haka?"

Yace "ikon Allah to me zance?"


Mikewa tai ta zauna tare da sa kanta cikin cinyoyinta tace "shikenan nikam bansan da wani ido zan kalli Abba ba."

Hassan yace "ban gane ba, da dawani ido kike kallansa? Nifa na kasa fahimtar ma abinda kike nufi kwata kwata."

Ya fara tare da neman kamota, mikewa tai tare da cilla mai pillow ta fito falo.

Da kallo ya bita yana cewa "baki biya ragowar fee din ba."

Juyowa tai ta kalleshi sannan ta fita cikin takaici.

****************


? Wajen karfe biyu na dare hannunta ya fara motsawa, a hankali ta bude idanunta, tana kallan dakin.

A asibiti take? A hankali ta kalli Mumy dake kwance a kan kujera ta kwantar da Yasmeen a kusa da ita.

? Abubakar!!!! Kokarin zare abin dake hancinta tai, hakan yasa Mumy ta bude ido.

Ganin Inna yasa ta taso da sauri tare da kara fitilar dakin, ta matso tare da rike hannunta tace "Inna! Inna kin ganeni?"

Kai ta daga alamar eh.

Alama ta mata akan ta cire mata abin hancinta, tace "bari na kira nurse."

Inna ta rikota da sauri tare da girgiza mata kai.
Cire mata tai sannan tace "Inna bai kamata ba, gwara a cire miki."

Inna a hankali cikin wata murya numfashinta na fita sama sama tace "bacci nakeji magana daya zan miki, ki kira Sani kice ya duba yaga mai Abakar yake shiryawa, cikin mamaki tace "wani irin zance ne wannan Inna? Me yake shiryawa kuwa?"

Tana lumshe ido tace "kiyi abinda nace sannan karki kuskura ki fadawa kowa na farka koda Doctor ne balle mijinki"

Mumy zatai maga taga inna na kokarin yin numfashi da kyar, da sauri ta maida mata sannan ta kurawa Inna ido, me Inna take nufi????



#OneLuv=ؕ?
[12/30/2018, 10:07 PM] El-hajj: =??? *JALILAH* =???


Written By : *AYUSHER MUHD*
Wattpad: *Ayusher Muhd*


*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*


*70*



Mumy tai zuru tana bin Inna da kallo, me Inna take nufi da abinda ya faru a dan kankanin lokacin nan?
Shiru tai tana kallanta waya rike a hannunta, ganin hankalinta ya kasa kwanciya yasa kawai ta kara kiran Dady, har ta katse ba'a dauka ba ta sake kira, yanzun ma sai data kusa katsewa aka daga.

Hankali a tashe tace "Dadyn Yasmeen, ina ka shiga inata?

Shiru yai bai amsa mata ba, tace "kana ina? Dan Allah inkana gida kazo, Inna ce yanzu....."

Katseta yai cikin fada yace "me zaki cemin a cikin daren nan? Wai bakiga agoggo bane? Me yasa ne wai bazaku bar mutum yai bacci hankali a kwance bane?"

Tsananin mamaki ne ya kamata tace "Bakajin dadi ne?"

Dan karamin tsaki yai yace " koma ina jin dadi ko banaji inaso a sararamin haka nan, akan me za'a dinga damuna da kira ba gaira ba dalili?"
Tace "bangane mai kake........"

Jin kamar ma an riga an katse wayar ne yasa tace "Hello? Hello Dadyn Yas..."
Kallan wayar tai taga kuwa an riga an katse ta tsananin mamaki ne ya kamata, tace "lafiyarsa kalau kuwa? Ko stress ne?"

Sh????      

                  ! " # $ % & ' ( ) * + , - . / 0 1 2 3 4 5 6 7 8 9 : ; < = > ? @ A B C D E F G H I J K L M N O P Q R S T U V W X Y Z [ \ ] ^ _ ` a b c d e f g h i j k l m n o p q r s t u v w x y z { | } ~  ? iru tai tana kallan Inna, kafin ta kamo hannunta cikin tausayawa tace "Inna dan Allah ki bude idanunki, gaba daya kaina ya daure."

Anan ta dan kwantar da kanta har safiya tai, sallah tai sannan ta gyarama Yasmeen kwanciya ta dau wayar Inna ta kira Sani.

Yana ganin kiran ko gama ringing din farko baiyi ba ya daga tare da cewa "Hajiya? Lafiya kuwa inata kira wayarki a kashe."

Mumy tace "Sani ina kwana? Fatima ce."

Yanayin maganarsa ne ya canza yace "Ina kwana ranki ya dade."
Tace "me kake neman Inna ka fada mata?"

Yace "a'a bakomai, bata kusa ne?"

Mumy tace "tana kusa sai dai bazata iya ko magana ba, menene? Ka sanar dani."

Yai shiru tare da jan numfashi kafin yace " Hajiya muna cikin matsala, dan tabbas yau akwai gagarumar matsala dazata afku a company dinmu."

Gabanta ne ya fadi kila hakan ne yasa hankalin mijinta ya tashi, jiki a sanyaye tace "meke faruwa?"

Yai shiru kafin yace "Hajiya ina tsoron sanar dake domin abin ya shafeki."

"Ni kuma? Ta yaya? Ni yanzu kiranka nai akan Inna ta bani sallahu gunka, ban fahimci kuma abin ya shafeni ba."

Shiru yai har saida ta sakemai magana sannan yace "Hajiya mijinki....."

Sai kuma yai shiru, tace "Abubakar? Me ya sameshi?"

Yace "ba wani abin bane ya sameshi."
Ajiyar zuciya tai dan hankalinta yadan kwanta tace "to menene?"

Iska yadan firzar kadan kafin yace "Kwace matsayin Hajiya zaiyi a gobe dan har ya zauna da Board members."

Cikin rashin fahimta tace "ban gane kwace matsayin Inna ba, ta yaya? A kuma wani dalili? Bayan dama matsayin nashine nan gaba?"

Yai shiru kafin yace "Ranki ya dade ki taimaka ki duba abinda yake a lulube da bargo, ki daina kallan abinda zuciyarki kesan gani, please ki duba reality."

Tace "bangane ba."

Cikin takaici yace "in bakiyi wasa ba san da kikema mijinki shine dalilin da zai halaka komai na rayuwarki, bakisan wanene mijinki ba, mutum ne dabaisan komai ba sai kansa, masan komai game dashi saboda Hajiya tasa inyi following dinsa dan ganin me yake aikatawa."

Cikin tashin hankali tace "ni kasa na rasa me ma kake nufi da kalamanka."

Yace "ba sai kin gane ba a wannan lokacin, saboda munacin crisis din da muke bukatar mafita cikin gaggawa, Anjima karfe 10 za'a sauke Inna daga matsayinta a bashi, bawai bashin bane matsala shi din ne matsala, dolene kizo ki kwace company din da mahaifinki da mahaifiyarki suka sha wahala gun ginashi."

Hawaye ne ya cika a idanunta fal, tace "yanzu me ya kamata muyi? Sai dai inaji kamar ina betraying din mijina akan san zuciyata."

Ya runtse ido yace "dan Allah na rokeki da Allah ki tashi daga baccin da kikeyi, ki duba sosai kiga wanene ke betraying din wani tsakanin ke dashi, sannan ki duba mahaifiyarki da mahaifinki."

Mumy tai shiru kafin tace "yanzu me ya kamata muyi?"

Yace "dolene a cikin dayan biyu mu zabi daya, ko dai kiyi amfani da shares dinki ki ja ra'ayin directors din, ko kuma mu nemi wanda yai investing a company din ya baki matsayin."

Shiru tai tana tunani kafin tace "plan din farko ama cireshi dan na riga na bashi shares dina, plan na biyu kuma da matsala saboda investors din gidan mijin yarsa ne."

Inalilahi wa ina ilaihi raji'un Sani ya hau fada kafin yace "ki taimaka ki hadani da Hajiya muyi magana ma tabbatar ita zatasan yanda za'ai."

Mumy ta share kwallarta tace "Inna tana asibiti ba lafiya."

Sani ya runtse ido yace "shikenan magana ta kare,haka Allah yai, ya jikin nata?"

Mumy tace "gatanan dai a kwance."

Yace "shikenan sai nazo dubata, da alama ba sai nake company din bama."

Mumy tai shiru hakan yasa yace "sai anjima."
Ya kashe wayar, Mumy ta dafa kanta dake sarawa, agoggo ta kalla karfe bakwai da rabi na safe, wayar Abubakar ta sake kira, bayan tayi kira biyu ma sai ma taji an kashe wayar gaba daya, shiru tai tana kallan wayar sannan ta kalli Inna, tunowa ta dingayi da kalaman Inna daya bayan daya tun kafin auranta da Abubakar yanda ta dinga neman hanata suna fada akan itafa sai shi, to itakam ai haryanzu tana sansa kuma ta tabbatar akwai wani misunderstanding ne a tsankaninsu dan Abubakar bazai mata haka ba, da kwacewa yakesan yi da ai tuntuni halayensa dake boye sun fito.

Lalai ko saboda Inna tasan ba hakan bane gaskiya dolene ta binciko gaskiyar al'amari ko kuma kila dai da akwai wani abun.
Sai dai ta ina? Taya zai nemi taje gidansu Jalila?

Inna ta kalla wace ke kwance, yanda mahaifiyarta da mahaifinta suke kaunar company din yanda sukasha wahala gun kula dashi.


Idanu ta runtse tana tunani, hawaye ne suka sake zubo mata, kukan Yasmeen ne ya dawo da ita hankalinta, mikewa tai da sauri tazo ta dauketa tace "Yasmeen ganinan."

Yasmeen ta rungumeta sannan ta fara neman komawa bacci.

Tana komawa Mumy ta kwantar da ita sannan tadau waya ta kira Safeena, tana dagawa tace "Mumy lafiya da safan nan?"
Mumy tace "dubamin ko Dadynku na nan."

Nan ta mike tai dakinsu wayar na kunnenta tana cewa "Mumy nikam meke damun Dady wai?"

Tace "me kika gani?"

Tace jiya sai barbaza takardu yake a daki na shiga kamar yana neman wani abun, sannan da na fito kai plate kitchen najishi yana waya yana cewa "nagode yallabai bazan manta da hallacin da akamin ba, kn dai na zama chairman i will definitely fulfil your wishes."

Cikin tsananin mamaki Mumy tace "meyake nema?"

Safeena tace "bansani ba."
Ta karasa maganar tana knocking, jin ba amsa yasa ta tura kofar dakin, bakowa a ciki tace "Mumy ya fita."

Mumy tace "shikenan kidanzo asibiti inasan fita ne."
Tace "okay bari nai wanka dan naga har ma angama break din da za'a kawo."

Mumy ta kashe wayar tare dayin shiru tana tunani, me yake nema? Sannan wanene yallabai?

Ganin batada mafita yasa ta mike tana zarya a tsakiyar dakin.
Safeena na shigowa ta zari mayafinta tace mata ina zuwa.

Fita tai ta hau motar da aka kawo Safeena dan daka drivern ya shigo duba Inna, tace mai gidan Jalila.

************

? Hannunsa yasa a cikin kasan rigarta tasa hannu ta rike hannunsa tare da cewa "Yayah?"
Yace "wai abin haryanzu bai wuce ba?"

Tace "menene bai wuce ba?"
Yace "gashinan gaba daya sai wani mazewa kikeyi, kindai san na fiki iya hade fuska ko?"

Ta kalleshi tare da cewa "nifa ba hade fuska nake ba."
"Ohh tafiya ne bakyasan yi dani ko me?"

Tace "Allah ba haka bane Yaya kawai dai bansan yanda zan sauka kasa bane, nasan yanzu Abba ya fadawa Ummy."

Yace "ikon Allah! To sai me? Ai ko bai fadaba ni zan fadamata."

Cikin shagwaba tace "haba yaya?"

Yace "to naji bazan fadaba, Abban ya fada mata shikenan?"
Ta kalleshi kamar zatai kuka, da alama Yaya bazai gane ba, agoggo ta kalla tace "oh ya kamata na sauka kasa fa."

Ta fada tana neman saukar da kafarta daga kan gado, Yaya ya jawota tare da cewa "yanzun ma fitar za'ai a barni?"

Cikin zolaya tace "ko zamu tare? Sai ka tayani?"
Ganin yanda ya tsaya yana kallanta yasa tai dariya tare da rufamai bargo ta mikomai littafi tace "malam mai karatu ai karatu dayawa."

Ta mike ta fita tana dariya, Yaya kam birgeshi tai, gani nai ya mike ya zura doguwar riga kawai ya sauka.

Jalila kam sam batai tunanin zai kawo wani abun a ransa ba, kitchen ta nufa, yau kam tai sa'a Ummy bata fito ba, dadi ne ya kamata ta wuce kitchen tare da tunanin abinda za'ai breakfast

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login