Showing 78001 words to 81000 words out of 149705 words

Chapter 27 - Jalilah Book One Complete Hausa.doc

Ayusher   

28 Oct 2025

628

kai kadan yace "ban sani ba nima, sai dai I don't like it."

? Kallansa tai tare da neman zare hannunta daga kan kirjinsa.

Hannu yasa ya tsayar da hannu yana kallanta yace " yanzu kukan me kikeyi?"

Tace "meyasa kakesan sani?"
Yace "Hmm kawai, saboda sai naji ne zansan abinda ya dace nai."

Hannunta ta nemi janyewa tana cewa "me ya faru dakai? Duk sanda kake abin nan kamar wani abu kake tunani."

? Shiru yai bai bata amsa ba, kafin can yace " izinki nawa?"
Tace "mene?"
Yace "tambayarki nai, so nake nasan karatunki, na kula kamar bakiyi nisa ba."

Tadan sosa wuyanta da dayan hannun tace "bankai izu ko daya ba, a gida Goggo tadan koyamin na sallah."

? Idanu ya kura mata, wanda yasatai saurin juya kai yace "bakyajin zafin mahaifinki?"

? Tai shiru kafin tace "inaji, inaji sosai da har wani sa'in ganinsa ma banaso."

Yace "kenan ko me ya faru bazakiji haushi ba?"
Tace "me zakamai?"

? Mikewa yai daga kan cinyarta sannan ya saki hannunta yahau kan gado....
Da sauri ta taso tace "me zakayi?"
Yace "bakomai, fada kawai nai."

Jalila ta kalleshi alamar rashin gamsuwa.........

********

Dady kuwa yana saukowa daga gun Inna ya shiga daki kawai ya hau hada kayansa, Mumy ta shigo da sauri zatai magana taga yana hada kaya, a rikice ta rike hannunsa tace "Dear menene?"

Ture ta yai yace " menene? Da alama karshen zamana dake yazo."

Da sauri ta rungumeshi tace "menene? Kafi kowa sanin bazan iya rabuwa dakai ba, Inna ce? Itace?"

Yai shiru wai shi a dole ransa ya baci.
Da sauri ta fito ta nufi dakin Inna da gudu rai a bace.........

#OneLuv=ؕ?


=??? *JALILAH* =???

Written By : *AYUSHER MUHD*
'ote me on Wattpad : *Ayusher Mohd*


*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*
(_D home of expert and perfect writer's_=ء?)

*45*


Da karfi ta banko kofar dakin Inna, lokacin Inna na zaune tasa hannu tayi tagumi tana tunanin abinyi, yanda Mumy ta banko kofar ne yasa ta zabura ta kalleta tace "Lafiya?"

Mumy cikin bacin rai ta zauna a gaban Inna tace "Inna so kike kiyi ajalina?"

"Ajalinki kamar ya kenan?"
Tace "in ba so kike in mutu ba taya zaki nemi halakamin aure? Sanin kanki ne yanzu kinsan bazan iya rayuwar ba Abubakar ba, a da ma da 'ya'ya basu hadamu ba na kasa rabuwa dashi bare yanzu."

Inna ta katseta cikin fada tace "me ya fadamiki?"
Tace "ba damuwa ta bace da duk abinda kike tunani sai dai kiyi abinki ke kadai, dan wallahi bazan bari wani abu ya sameshi ba, in kuma so kike mu bar miki gidan to....."

Mamaki ya kama Inna ta kalleta cikin wani yanayi tace "Fatima ni kike fadama haka? Ni wacce ma sadaukar da komai dan ganin farincikin ki?"

Cikin masifa tace "kika sadaukar dame? Me kika sadaukar? Duk abinda kikeyi ba saboda kanki kikeyi ba? In har saboda nine ai da kin daraja Abakar kin bashi company din kamar........."
Marin data kifa mata ne yasa Mumy yin shiru, ta kalleta tare da rike kuncinta.

Inna ta kalli Hannunta dake rawa, dan ita kanta batasan ta mareta ba, cikin dana sani tace "Fatima......"

Mumy ta mike tsaye tana kallanta, hawaye sun cika mata ido tace " in har bakyasan in bar gidan nan ki ajiye duk abinda kike shirin yi." Ta juya tanaji tana kiranta bata amsa ba tai waje.

Inna ta bita da kallo jiki a sanyaye.....

Shikam Dady tana fita yai wata dariyar mugunta yace "Inna i am sry sai dai kin riga kin makaro akaina 'yarki da kikafiso a duniya zata iya juya miki baya."

Yanajin alamun bude kofar ya shiga kokarin zuge jaka, Mumy na shigowa ta sa hannu da karfi ta fincike jakar sannan ta rungumeshi tace "Dadyn Yasmeen me yasa baka tunani na in zaka aikata abu?"

Yace "tunanin naki ne yasani yanke wannan hukuncin, taya zan zubarma kaina mutunci? Bayan nasan ina zubar da mutunci na naki na zubar? Da ace kome zai faru zai tsaya akaina ni kadai bazai shafeki ko yaranmu ba wlh ba abinda bazan iya ba, amma ta yaya zan yarda in zubar da mutuncinki dana 'ya'yanmu."

Dagowa tai tana kallansa tace "to kamin alkawari ko me zai faru bazaka sake tunanin rabuwa dani ba."

Yace "na miki, yanzun ma ba'a san raina nake shirin tafiya ba."

Ta kara kankameshi tace "barni da Inna bazan kara bari ta wulakantamin kai ba"
Ya shafa kanta yana wani murmushin mugunta yace " taya zan yarda na zama sillan fada tsakaninki da mahaifiyarki?"

Tace " ba kaine silla ba dan dama na gaji da yanda take ma kamar wani bawanta."

Nan ya sumbaceta a kunci yace "i luv u Zarah."

Ta sakarmai murmushin so......
Nace ansha kauna=??

Inna kuwa Mumy na fita ta ture littatafan dake kan tabir din gabanta cikin takaici tace "Abakar how dare you!"

Kwafa tai tace " kana tunanin ka samu abinda kakeso? Inji wa?"

Ta sakeyin wata kwafa........

********

Zama tai a kusa dashi a kan gado yana kwance yana tunanin Zaliha, ji yake zuciyarsa kamar zata fashe da rashinta.

Ganin baimasan ta zo bane yasa tasa hannu ta tabashi.
Kallanta yai sannan ya kakaro murmushi yace "Yaushe kika shigo?"

Tace "me kake tunani?"
Kallanta yai jiki a sanyaye, murmushi tamai sannan ta kauda kai, a hankali yace "I am sry, i am really sry."

Kallansa ta sakeyi tace "me kake tunani game da mutanen nan?"

Ya mike ya zauna yace "amsar kudinmu zamuyi, inyaso company din nasu ya nukushe."

Tace "ayi haka kuwa?"

Yace " baki kula da rainin hankalin da suka mana ba? Sannan yarinyar nan da mahaifiyarta, gaba daya ba tausayi a harkarsu, Hajiya taban mamaki duk da nasan macece wace kanta yake a waye amma i didn't expect that from her."

Tace "na sani sai dai in muka duba abin ta wata fuska zamuga mu taimakonmu sukai, da farko dabadan sun yaudaremu ba da bamu san wacce zamu aurana Hassan ba, in muka duba saukin da muka dade muna nema akansa yanzu gashi abinda likitoci da dama suka kasa yi yarinyarnan a ciki wata daya ta mana, duk da bawai ya warke ne ba sai dai canjin daya samu nada yawa."

Abba yai shiru yana kallanta zuciyarshi na dana sanin abinda ya aikata mata, yace "yanzu me kike tunani?"
Tace "just live them."
Yace "kina nufin duk abinda sukai ya tashi a banza?"
Tace "ko daya sai dai ina tunanin mu barma Allah, yanda suka cutar da Jalila da mahaifiyarta Allah bazai barsu ba, mu murikesu, gatan da basu samu ba mu basu, mu jira hukunci Allah akan su."

Abba yai shiru sai kallanta kawai da yakeyi, tace "kallan fa? Shawarar batai ba?"
Yace "akoda yaushe in kina abu sai na dinga yin wani tunani, sau dayawa akance mata basukai maza zurfin tunani ba, sannan sai kaji namiji na ta aibata mace, in naji haka a koda yaushe sai insan Allah yamin baiwar da ba ko wani namiji yama ba, samunki a matsayin matata yana daya daga cikin abubuwan da nake alfahari dasu a rayuwata."

? Kallansa tai sannan tai murmushi tace " Kasan abinda yaban mamaki? Ban taba tunanin Hassan zai sauko kasa ba wlh, kasan kawai nama Jalila zancen ne amma a raina nasan bamai yiwuwa bane?"

? Abba ya kalli yanda taketa farinciki yace "ni kaina nayi mamaki, kinsan rabon da Hassan ya shigo falona kuwa harya zauna ya dade haka?"

Tace " kasan ya sauko ya gaida baban Jalila ran nan?"

Abba yai murmushi yace "da alama yanda nai dace da mata haka Hassan yai dace, sai muyi addu'a Allah yaba Sageer mace shima ta gari."

Tace "insha Allah."


Washegari.

Dakin Sageer ta nufa tasa hannu tai knocking.

Yana kwance akan gado ya taso ya bude mata.

Kallansa tai cikin kulawa tace "Sageer lafiya? Naga baka fito ba."

Ya kalleta yace "Ummy...."

? A rikice ta kalleshi tace "menene? Bakajin dadi ne?"

Yace "a'a kawai dai..."
Tace "na kula ma gaba daya yanzu kadan canza, Sageer menene ke faruwa?"
Yace "kai Ummy wacce canzawa?"

Tura kofar tai ta shiga dakin, binta yai ciki da sauri yana cewa "Ummy."

Hannu tasa ta zuge labulen dakin ta zauna akan kujera.

Ya matso yana cewa "Ummy!!!"
Cikin shagwaba ya kirata, ta harareshi tare da hard'e hannayenta tace " In baka fadaminba ba inda zani."

Dariya ya saka sannan ya zauna a kasa kusa da ita yace "shikenan sai muyi hira."
Tace "Sageer dan Allah meke damunka? Sai yanzu na fahimta sam da yake banda nutsuwa ban kula da canzawar dakai ba."

Yace "Ummy wlh ba komai, muje na tayaki aikin kitchen kafin sirikarki ta sauko."

Kallansa tai sannan tai murmushi ta mike ta fito, yabiyo ta.

Dakin Ameera ta kalla tace "bari in nakai musu breakfast sai mu gaisa."

Shima dakin ya kalla sannan ya matso yace "Ummy me kukai da Abba akan su?"
Tace "Goggonta zata zauna anan kamar yanda Hassan yace, su kuma su suka sani."

Sageer yai murmushi zaiyi magana ya hangota a kitchen.
Tsayawa yai yana kallanta, Jalila ta juyo jin motsin mutane, kallan Ummy tai sannan ta matso fuskarta dauke da fara'a tace "Ummy ina kwana?"

Ummu ta kalleta cikin jin dadi tace "Jalila kin tashi lafiya?"
Tace "lafiya kalau Ummy."
Sannan tadan kalli Sageer a hankali tace "Ina kwana?"
Sageer yace "kin tashi lafiya?ya yaya?"
Lafiya kawai tace.
Ummy tace "Jalila naji dadin ganinki haka kamar ba abinda ya faru."

Jalila tai kasa dakai tana murmushi, a zahiri itakam ganin Goggonta yasa takejin kamar duk wani abu daga baya kenan, sannan ta rasa me yasa takejinta haka.

Sageer ya zauna a falo su kuma suka nufi kitchen, suna aiki suna yar hira, Ummy tace "Hassan abin nashi na tashi sosai yanzu?"
Jalila tace "ba sosai ba sai yai kwana biyu zuwa uku lafiya."

Ummy tai murmushin jin dadi ta kalli kular data suko dashi ta bude, kallan Jalila tai tace "jiya bakuci abinci bane?"
Tace "yayane baici ba, inaji bacci ne ya daukeshi."

Ummy tace "ba matsala tunda ya fara bude zuciyarsa nasan komai zai daidaita a hankali."

Jalila ta kalleta cikin rashin fahimta tace "bude zuciya?"

Ummy ta dauko kukar tana cewa " eh mana akanki ba."

Jalila tace "ni?" Ta fada cikin mamaki da alamar tambaya, Ummy bata tanka mata ba ta cigaba da aiki.
Jalila tai shiru tana nazarin abinda Ummy ke nufi, ba dai so take tace wai Hassan ya fara santa ba? Tab shi wannan har akwai zuciyar soyayya ma a ransa?lalai Ummy.

? Haka suka gama ta kaima Goggo ya zauna suka gaisa da dan hira, Ummy na shigowa ta mike ta dawo kitchen ta dau nasu.

Sageer na zaune kan dinning shi kadai yana cin abinci, waya yakeyi da alama da Ameera yake waya dan yana cewa "In bazata biyoki ba sai ki dawo kindai san ran monday zaku koma makaranta."

Jalila ta wuce ta hau sama, a hankali tasa hannu tadan murda kofar, tadan fara kokarin budewa a hankali.

Jitai an jawo kofar da karfi har ya hado da ita data rike kofar, ta taho ciki da dan gudu ga tire a hannunta.

Da sauri ya rike tiren yana kallanta.
Daidaita tsayuwarta tai sannan tace "yaya irin wannan fizgar kofar fa?"

Yace "ke kuma irin wannan bude kofar fa? Kamar wata munafuka? Ko laifi kikai?"yai maganar da alamar tuhuma.

Da sauri ta ajiye abin hannunta tace "laifin me? Ni wlh ba laifin danai."

Baisan yanzu ma bakinsa yadan motsa ba yace " kin tabbatar?" Ya fada tare da matsowa.

Da sauri tai baya tana cewa "ni wlh banyi komai ba, kawai dan na murdo kofa a hankali."

? Yadan kalli idanunta yace "why do i have this kind of feeling?"

Tace "ikon Allah, dama dai fada kakesan yi, daga shigowata?"

? Ya zauna akan gado yana cewa " ramawa nai."
Tace "me nai da zaka rama?"

Bai tanka taba ya dau littafinsa tare da gyara zama, ido ta kuramai a ranta tace "so? Hahh lalai Ummy wannan mutumin nan?"

? Bai kalleta ba yace "kallan fa?"

Ta dauke idanta da sauri tace "sauko kaci abinci."

Yace "banaci."
Tace "bakaci jiya da daddare fa?"
Yace "shiyasa ai bazanci yanzun ba."
Tace "ban gane ba???"
Ya shareta.

Ta matso tana neman amsar littafinta, wani kallo ya mata yace "littafin kike san amsa ko rikeni kike sanyi?"

Da sauri ta matsa baya tace "rike ka kamar ya?"

Yace "kamar yanda kika saba."

Mamaki ne ya kamata tace "kaima ai kana rike ni."
Wai meke damun mutan nan? Jiya da daddare kamar bashi ba.

Kallanta yai kamar bazai yi magana ba sai jitai yace "inma na rikeki ai ke matatace."

Mamaki me ya kamata ta saki baki tana kallan ikon Allah, shikuwa kamar baiyi maganar ba ya cigaba da karatunsa.

Tace "dan Allah ka sauko kaci abinci."
Yace "Allah bazan ci ba."
Tace "bangane hakan ba."

Mikewa ma taga yayi ya ajiye littafib ya nufi toilet, mamaki ne ya kamata ta bishi da kallo.
Haryaje zai shiga toilet sai taji yace "inkin gama ki shirya muje a siyoma Goggo kayan dakinta da abin bukata." Ya shiga ciki yana cewa jiya dana jira kizo muci ai shareni kikai kema kiji ko da dadi......

Duk da taji dadin abinda yace sai dai wulakancin daya mata yasa tama rasa abinyi.

? Da kyar tasha ruwan tea, duk kuwa da tanajin yunwa amma takaici ya hanata, wai Allah bazanci ba, kalmar nan ta bata haushi.

? Tana nan a zaune ya fito daga wanka daure da towel, da sauri ta juya baya.

Ko kallan inda take baiyi ba ya fara shiryawa.

? Yana gamawa ya dau key yace "ina jiranki a mota."yai waje.

Da kallo ta bishi tai tunanin jiya bayan ya warke, kamar ba shiba yana mata magana a hankali, to yanzu me ya sameshi kuma? Ramawa? Me tamai?

Haka ta mike tai wanka duk ranta ba dadi, ta fito tana kokarin sa bra a saman towel din jikinta ya turo kofar.

? Idanunsa ne ya sauka a kanta, zaro ido tai tana kallansa, da sauri tasa hannu ta rufe kirjinta.

Ganinsa tai ha fara matsowa inda take, idanu ta runtse tana tsoron abinda zai biyo baya, sai dayazo daf da ita har tana jiyo numfashinsa yasa hannu cikin wardrobe ya dauko abu, kallanta yai yace "Wallet."
Ya fada tare da nuna mata wallet din, ya juya ya futa.

Wani nanauyan numfashi ta saki........


#OneLuv=ؕ?


=??? *JALILAH* =???

Written By : *AYUSHER MUHD*
'ote me on Wattpad : *Ayusher Mohd*


? ?? *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*
? (_D home of expert and perfect writer's_=ء?)

*46*

? Hassan na saukowa kasa ya nufi hanyar fita da sauri "Hassan!" Juyowa yai da sauri kamar mara gaskiya ya kalleta.

Karasowa yai inda take sannan ya gaisheta, fuskarta dauke da murmushi tace "fita zakai?"
Yace "eh ni da...." sai kuma yai shiru, murmushi ta sakeyi tace "ya zaka fita baka gaida sirikarka ba?"
Yace "sirika?"
Nunamai dakin Ameera tai da hannu, Hassan ya kalleta alamar rashin fahimta, tace "badai bazaka ba?"

Kallan dakin ya kuma yi sannan taga ya nufi dakin, da kallo ta bishi cikin jin dadi.

Hassan ya kwankwasa kofar dakin, daga ciki Lantana ta mike ta bude.

Tsayawa yai yana tunanin me ma zaice inya shiga?
Goggo dake zaune a kasan carpet tana ganin shine ta mike tace "Hassan? Shigo mana."

Shigowa yai ya zauna daga gefe yace "Ina kwana?" Kansa na kasa.

Goggo tace "ka tashi lafiya? Ya dawainiya da mu?"

Hassan yai shiru dan bai san me zaice ba, Goggo tadanyi shiru haryana shirin mikewa.
Tace "Hassan."

Komawa yai ya zauna tare da kallanta, Goggo tace "in ba damuwa magana nakeso muyi."

Yace " ba komai, menene?"

Tadanyi shiru kafin tace "da farko dai nasan kafi karfin Jalila, saboda ita ba gata gareta ba, ba kudi gareta ba sannan ba 'yan uwa dake santa take dashi ba, yarinyar tasha wahala agidan mahaifinta wanda har bata iya cewa ko kawo kawarta da sunan gidansu, tunda nake da ita bata taba kawo kawa ba, bata taba zuwa gidan kawa ba, nasan bawai dan batada shi bane sai dan tana gudun wulakancin dazai biyo baya, dan Allah Hassan ga amanar yarinya ta nan, ka taimakeni kamar yanda Allah ya taimakeka ya baka iyaye na gari ya baka duk wani abu da ya dace ka kularminn da ita, ba marainiya bace sai dai tafi wasu marayun rashin gata, dan garasu a kalla sun san mahaifinsu ba rai gareshi ba akanta, wacce tana ganinsa sai dai yafi karfinta."

Tai shiru kafin ta daura da cewa "nagode sosai da kaunar da kuka nuna mata, da kuma kaunar da kuka nunamin sai dai kuyi hakuri bazan iya zama a gidan 'yata ba."

? Cikin mamaki Hassan ya kalleta yace "meyasa?"
Tace " taya zan iya zama a gidan ku? Bayan kudin sirikainane? Wani irin zama zamuyi?"

Hassan yace "wlh bakomai."
Tace "nafi kowa sanin ba komai, dan kaunar da kuka nunamin a kwana dayan nan yasa na fahimci hakan, sai dai kuyi hakuri bazan iya zama a gida daya da sirikaina da yata ba, abinda yasa ban fadama kowa ba sai kai bakomai bane sai dan kaidin kaine ka kawoni gidan sannan inaso inbaka girmanka na mijin 'yata tilo."

Hassan yai shiru dan baisan me zai kuma cewa ba Goggo tai murmushi tace " ka sanar dasu ra'ayina, zan koma inda na fito."

Yace "ina kenan?Goggo?"
Tace "karka damu kauye nake nufi bawai gidan Babanta ba."

Hassan yai shiru yana nazari, jiyai tace "jeka dama abinda zan fadama kenan kar na tsayar dakai, zuwa anjima ko gobe zan tafi in Allah ya kaimu."

? Hassan yai shiru kafin ya mike ya fito, mota ya shiga yana nazarin kalamanta, bazai takura akan ta zauna ba dan hakan ita kuma zai iya zama takura ne a gareta sai dai ya kula ganin mahaifiyarta shine zaifi sata farinciki........
Kofar da aka bude ne yasa ya kalli kofar, shigowa tai ta zauna.

? Yauce rana ta farko data taba saka doguwar rigar abaya, shima a cikin kayan lefenta yake ta dade tanasan ta saka amma kunya ta hanata, yau ma daurewa tai ta saka, dankwali baki ta daura a ciki ta yafa dankwalin abayar.

? Tana shigowa idanunsa suka kalli kirjinta, da sauri ya dauke ido daga kanta, meye hakan? Abinda zuciyarsa ta tambayeshi kenan.

Tada mota yai baice komai ba, itama tai shiru ranta a bace wai ita a dole ya bata mata rai, bazanci ba, kalmar nan ta bata haushi.
Ina zaije? Bayan Goggon tace bazata zauna ba? Sai dai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login