Showing 24001 words to 27000 words out of 149705 words

Chapter 9 - Jalilah Book One Complete Hausa.doc

Ayusher   

28 Oct 2025

606

kai Mahaifiyarta asibiti, sannan ki sani gobe za'a kawo lefenki da sa rana."

? Jalila kam kuka kawai takeyi, haka Dady da Mumy sukasa Goggo a mota Jalila ta shiga baya suka fita.

Asibitin Standard sukai parking, Jalila kam banda kuka ba abinda takeyi, ana shiga da Goggo nurse ta nufi office din likita dan sanar da ita halin da Goggo take ciki.

? Jalila na zaune a kasan beni kuka kawai takeyi tana addu'ar samun lafiya ga mahaifiyarta.

Dady na zaune shida Mumy, sunyi shiru suma.
Sai da suka samu da taimakon Allah numfashinta ya daidaita sannan suka shiga yi mata gwaje gwaje.

? Sai da suka gama sannan suka fito aka kira Dady.
Likitan ce kalleshi tace "wani maganin hypertension take amfani dashi?"
Yace "hypertension?"
Tace "kanaso kacemin bakusan tanada shi ba?"
Dady ya girgiza kai alamar rashin sani, tace "diabetes fa?"
Dady yai shiru nan ma.

Tace " menene tsakaninka da ita?"
Kunya tasa yace "yar uwatace."
Cikin rashin jin dadi tace "wannan wani irin abu ne? Batada miji ne? Ko kuwa neman kasheta yakeyi?"

? Dady yai shiru, tamai bayanin ciwon ta wanda ya riga ya ci jikinta sosai, tace " ta ya za'ayi ku bari diabetes har yai nisa ya ci kafarta?"
Dady yace "ai mun dauka ciwon kafa ne na girma."
Tace "ko ciwon kafa ne na girma ai kwa gwada zuwa asibiti, da kunzo da wuri ai za'a sanar daku ba shi bane." Sosai ta nuna masa laifinsu sannan ta bashi takardar magunguna tace yaje pharmacy dinsu.


? Jalila na zaune kusa da Goggo tana kuka, ko mayafi babu a jikinta dan kwalli ne kawai a kanta.

? Dady sai da ya gama biyan kudin komai sannan ya shigo dakin, Jalila ce ta kalleshi batace komai ba.
Dady yace "ya jikin nata?"
Kasa amsa mai tai dan gaba daya yau tana tir da kasancewa? uba a gareta.
Duk wani mutum mai imani bataji zai yiwa matarsa abinda dady ya ma Goggo yau.

? Dady ganin yanda Jalila ta dauke kai daga kansa yasa ya fito.
Mumy ya tadda a zaune yace " mu tafi."
Tace ya jikin nata?"
Bai bata amsa ba ya wuce mota.
Suna shiga ya kalli Mumy yace " yanzu abinda Inna tai dazu ta kyauta?"
Mumy ta riko hannunsa tace "nima banji dadi ba sai dai kafi kowa sanin duk abinda Inna takeyi tanayinsa ne saboda mu, na tabbatar ba a san ranta itama tai haka ba."

Shiru yai baice komai ba yaja motar sukai gaba.



? ******



? Ummy ce take ta buga mai kofar yanaji sai dai ya kasa mikewa ya bude, yana takure a gefen bandaki ya matse kansa da karfe, zufa nata karyomai, jikinsa sai rawa yakeyi.

? Ummy ganin ba alamar budewa yasa ta sauka kasa da sauri tana kwallama Sagir kira.
Sagir na kwance a falon kasa yasa waya a gaba sai gwada number Jalila yakeyi sai dai tai ringing har ta gaji ba'a daukaba.
Jin yanda Ummy ke kiransa yasa ya mike da sauri yana tambayarta Ummy lafiya?

Ummy a rikece ta karaso tace "Hassan."
Yana jin haka ya hau sama da gudu.
Aina'u da Ameera dake zaune suna hira suma suka taso da sauri.

? Ganin buga kofar bazata kara mai komai ba yasa ya shiga dakinsa da sauri ya dauko spire key ya bude.

? Hassan na takure jikinsa sai rawa yakeyi ga wani azabbaben ciwon kai dayake damunsa, Sagir ya karasa da sauri ya rungumeshi, Ummy kam zubewa tai a kasa tana maida nimfashi dan ta tsorata ganin yanzu abin da dan sauki zakaga in ka kwankwasa yana budewa, Aina'u da sauri ta karasa kusa da ita.

? Sagir ya dade yana mai addu'oi samun nutsuwa sannan shima Hassan din ya fara kokarin yi a zuciyarsa.

? Ameera kam kuka kawai takeyi.

? Hassan ya kalli Sagir idansa yai ja, kallan Ummy yai da Ameera dake kuka gaba daya tausayinsu ne ya kamashi sai dai bai nuna a fuskarsa ba, mikewa yai ya zari key din motarsa zai fita.

Ummy ce ta riko hanunsa dayazo wucewa ta kusa da ita, sannan ta kalli su Ameera ta musu alama da su fita.
Suna fita ta kalleshi tace "ina zaka?"
Yace "fita kawai zanyi."
Tace "Hassan sai yaushene zaka dainafita haka kawai?"
Kallanta yai cikin takaicin rayuwarsa yace "To Ummy ya kikeso nai? Nace zan bar garin kin hanani? Sannan ba tun yanzu ba kukasan matsalata sai yaushene zaku daina damuwa in kuka gan ni cikin halin nan? Sai yaushe ne zaku cire abin a ranku ku saba da ganina haka?"

Ummy tace "taya kuwa zamu cire abin a ranmu bayan kaidin jinin mu ne? Damuwar ka itace damuwarmu? Rashin lafiyarka itace tamu?"
Cikin akaici yace "Ummy please, Please na rokeki da ki cire ni a ranki, Please ki manta dani kiyi rayuwarki yanda kikeyinta da."

? Tace " kana jin takaicin yanda nake shiga kunci saboda lalurarka?"
Kallanta yai baice komai ba, tace "in har kanaso inyi rayuwa yanda kakeso to ka amince da abinda na fada ma."

Kallanta yai yace "Ummy wai ta yaya zakuyi tunanin yimin aure cikin wannan halin? Wace macece zata iya zama dani?"
Tace " in har ka amince ai zaka ganta, zakaga wace macecen ce haka dazata iya zama dakai?"

Hassan yai shiru dan kansa har yanzu yana sarawa, yace "naji kiyi duk abinda kike ganin shine daidai."
Ya fada tare da fita daga dakin, da kallo ta bishi dashi cikin tausayawa, dan tasan halin zuciyar danta,? mutum ne mai saukin kai, sai dai tundaga faruwar al'amarin nan ya rikede ya koma haka.


? Hassan na fita ya fizge mota yai gaba.


Jalila kuwa da daddare Driver ya kawo musu abinci, ganin yunwa zataata lahani ne ya sa ta zuba abincin taci.
Goggo ce ta farka daga nannauyan maganin baccin da aka sa mata, kallan Jalila tai sannan ta kalli asibitin, a hankali ta budi baki tace "Jalila!"
Tsame hannunta tai da sauri ta isa guda da ita tace "Goggo! Kin ganeni?"
Da kyar ta mata murmushi tace "Jalila karki kuskura ki yarda da abinda Mahaifinki ke shirin yi miki."

? Jalila ta kalli kasa jiki a sanyaye sannan ta kalli Goggo tace "Goggo abinda kikesan cemin kenan daga farfadowarki?"
Goggo da kyar tace "Karki yarda Jalila, bazan kara bari su cutar dake ba ta hanyar da bazata kare ba, aure ai ba wasa bane."

Jalila tace "to bazan yarda ba yanzu dai ki kwantar da hankalinki kinji?"
Goggo ta daga kai a hankali, wani baccin ne ya kara yin gaba da ita.........



#ONELUV=ؕ?
[08/10, 02:05] * +234 803 222 1758, : =??? *JALILAH* =???

Written By : *AYUSHER MUHD*
Wattpad: *Ayusher Muhd*


*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*

? (_D home of expert and perfect writer's_=ء?)

*No 15*


? Wajen karfe 12 na dare tana zaune akan kujera a kusa da mahaifiyarta ta kwantar da kanta a kusa da ita, Goggo ce ta bude idanunta a hankali tare da kokarin yin motsi da hannunta, Jalila cr ta farka wanda dama tana rike da hannun Goggo gam.
Tace "Goggo jikin ne?"
Goggo ta girgiza kai ta mata alama data kwanta a kusa da ita sannan ta matsa mata, Jalila tace "ya za'ai in kwanta anan Goggo? Ki bari zan kwanta a kasa."

Goggo tace "kwanta anan mmagana zamuyi."
Jalila ta mike ta kwanta akan karamin gadon wanda ya musu kadan, Goggo ta rike hannunta tace "Jalila duk abinda zai faru karki yarda da abinda mahaifinki ke shirin yi miki, daga shi har zuri'arsa, kinada wanda kikeso dan haka ni mahaifiyarki na baki shawarar bin zuciyarki."

Jalila cikin sanyin murya tace "Goggo me yasa muke zaune a cikin mutanen da basa kaunarmu?basu damu da rayuwarmu ba?"

Goggo idanunta suka canza kala zuwa damuwa da bakin ciki tace" Sunana kamar yanda kika sani Khadija, amma Kubra ake cemin, muna zaune a can wani kauye mai suna Chabai wanda yake karkashin karamar hukumar Misau a gariin bauchi.

Kasancewar karamin kauye ne sannan haka al'ada ta saba yarinya tun tana tsuma ake mata miji, haka zata taso har lokacin da zata isa aure a aura mata shi.
Mahaifiyata itace mace ta uku a cikin matan mahaifina, sannan itace ta tsakiya, 'ya'yan gidanmu mu 23 ne, nice ta 5 sannan ta biyu a gun mahaifiyata, a ranar da ake radamin suna a ranar ne Mai garin mu wanda ya kasance mahaifin Habubakar yamai kamu na.

Na taso mace marasan hayaniya dan a garin yara sa'anina har tsiya sukemin saboda asaranci irin nawa da rashin iya fada, Habubakar kuwa mutun ne dan gayu wanda tunda ya tasa yake bin yan garinmu Misau, Lagos da kano in zasu tafi rani.
Ko sau daya bamu taba kebancewa da sunan saurayi da budurwa ba saboda shi gani yake yafi karfina, sannan sam baima fiya zama a garin ba.
Ya yawan kasuwancinsa ne ya hadu da wani babban mutum mai kudi a garin kano, wanda suke safarar kayan abinci.
Habubakar nada kokari da himmar yin aiki shiyasa mutumin ya amince dashi sannan yasan harkar gona sosai, ganin yana moruwa da Habubakar ne yasa mutumin ya nemi shawararsa akan sa shi yayi karatu, haka Habubakar ya shiga makaranta ba tare da ya sanar a gida ba, a aji hudu aka sashi saboda girmansa, ya dage sosai saboda shi mutum ne mai tsananin buri da san ya zama wani abun, haka ya share sama da shekara 8 a garinkano yana harkokin karatunsa da taimakon Uban gidansa.
Sam ba abinda ya dameshi da tushensa inda iyayensa suke.
Ni kuwa a lokacin sa'anina duk sunyi aure dan alokacin shekarata 15 duk inda naji tsiya akemin akan nayi kwantai, hakan yasa ko fita nadainayi, sannan Innata ta ma daina bani talla dan haushi ma takeji itama akan kullum ta bani tallan kunu kwantai yakeyi.

Shi kuwa Habubakar ya zama dan gayu yana ta hidimominsa, alokacin ne kuma Mumy taji kaunar Habubakar ma ratsata saboda duk wani abu datake so kafin ta nema zakaga ya mata shi, wanda shi a gunsa ba wai so bane tsabar neman gun zama ne a gidan.
Mumy wanda asalin sunanta Fatima ta bayanna ma Habubakar san da take mai,ba wani kokonto ya amince da ita saboda a lokacin ne ya tabbatar da arzikinsa ya tabbata.
Haka ya dinga nuna mata tsantsar kauna ba tare da sanin iyayenta ba, Fatima tayi zurfi a kaunar Abbakar wanda ya canzama kansa suna zuwa na gayu.
Hajiya Zinaru wacce take mahaifiyarta ta mata hadin aure da dan uwanta, sai dai Fatima ta sanar dashi bata san sa ita Abubakar take so kuma zata aura.

Alokacin ne akan san da soyayyar dake tsakaninsu, duk yanda Zinaru tai ta rabasu abin yaci tura, shi kuwa Abbakar ya dinga riricema Fatima akan kaunar da yake mata.
Fatima taki ci taki sha ita fa sai Abbakar, mahaifinta shikam dama yana so, Zinaru kuwa ganin abin na Fatima yayi nisa dolene ta amince amma da sharadin dolene ya zauna dasu sannan ya cigaba da karatunsa, sannan duk abinda ta unarceshi dolene yayi.
Abbakar hankalinsa ya kwanta dan yanzu yasan tabbas ya zama wani abun, Mahaifin Fatima ne yace yaje gida ya sanar ma iyayensa.
Sam Abbakar baiso ba danshi babu komawa kauyensu a tsarinsa.
Haka ya shirya ba'a san ransa ba yace zai taho, key din motarta Fatima ta bashi tace yaje da ita dan ya dawo da wuri.
A yanzu shekaruna 18 duk garin har iyayena sun gallabeni gashi mahaifin Habubakar yaki yarda a hadani da wani, a lokacin akwai wani babban mutun wanda yakeda mata biyu dayaso ya aureni amma yaki.
Haka rayuwata ta koma cikin tsangwama da wulakanci a garin, kuka kuwa nayishi har ba iyaka.
Kwatsam ranar mahaifina ya shigo cikin farinciki yake cewa Habubakar ya dawo.
Sam ko mikewa banyiba daga aikin da nakeyi saboda ni maganar mutunci ma bata taba hadamu ba.
Randa Ya isa gidansu mahaifinsa ya haushi da fada ta ko ina bai ma jira maganarsa ba, sannan yace a ranar zai daura mana aure.
Ran Habubakar ya baci sosai yace shi ba wanda ya isa ya aura mai yar kauye, haka aka turo gidanmu akan washegari da azahar za'a daura auranmu.
Bakin ciki yasa Habubakar ya fita can bayan gari gidan wani tsohon abokinsa inda suke zama da yaje ya aika a kirani.
Da kamar bazanje ba tsautsayi yasa na fita, haka yaran dan aiken ya kaini har gidan.

Tsayawa nai a waje saboda bansan dakin ba.
Habubakar ya bude kofar yasa hannu ya fizgoni ciki, ba abinda yacemin sai gefe daya koma ya cigaba da cin abinsa yana dadana waya.
Na gaji da tsayuwa haka Yasa nace zan tafi.
Mikewa yai yazo kusa dani yace " ni kike jira na aureki? Na miki kala da dan garin nan? Ko mijin wata kuchaka kamarki?"
Nace "naji koma menene ni ba damuwa amma kabarni na fita."
Dariya yai sannan ya sa abu ya rufe kofar ya koma yai zamansa.
Kafafuwana har suka gaji suka fara rawa saboda tsayuwa, nan fara kokarin bude kofar ji nai an fizgemin hijab dina ta baya an yar a kasa, tsoro yasa na fara kuka ina matsawa.
Dariya yamin sannan ya koma ya zauna, baifi minti biyu da zama ba mukaji ana buga kofa da karfi, muryar mahaifina da mahaifinsa mukaji suna cewa Habubakar ka bude kofar nan ko kuwa?
Mamaki ne ya kamani da naga ya cire rigarsa ya bar vest sannan ya taso ya bude kofar.
Yana budewa ya koma gefen kafita yana cewa Baffa kayi hakuri.
Nikam hawaye na nacigaba dayi, ganin abinda ke faruwa yana zuwamin a baibai.
Mahaifina na zuwa ya kwadamin mari ya fara makamin kafa, nan na hau kuka sosai.
Mahaifinsa ma ya hau dukanshi, yan kauyenmu na waje suna gulma.
Kuka kuwa kamar zan mutu haka na dinga yinshi.
Kallansa nai nace "Habubakar ka hadamusu gaskiya ni wlh ba abinda nai."
Mamaki ne ya kamani da naga ya min dariya ta kasa, anan ne na fahimci shiri ne nashi.
Nan na shiga yin kuka, shikuwa ya dauka in yai haka mahaifina zaisa a hanashi ni, baisan suma duk sun gaji dani ba, haka suka dauramana aure bayan sallar asuba wanda tunda muke a kauyen ranarce ana ta farko da aka taba yiwa mace aure da asubahi.
Ranar dukan da na sha ba'a magana, Habubakar kam bakin ciki kamar ya kasheshi.
Yaso guduwa da asuba amma yaji an rufe kofarsa, haka yana ji yana gani aka hanashi fita.
A ranar da rana aka kawoni ba tare da wasu kayan daki ba, kuka kuwa nayishi kamar in kashe kaina.
Shikuwa bakin cikin an hadamu daki daya yasa ya huce a kaina wai ai ni matarsa ce.
Wannan ita kadaice ranar da wani abu ya shiga tsakanina dashi, sannan itace ranar da aka samu cikin ki.

Inna ta goge wata kwalla wacce ta zubo mata, tace haka aka sashi dole ya tafi dani, naje gida sallama sai mahaifina cemin yai duk randa na tako garin nan ba tare da Habubakar ba bazai taba yafemin ba, ya kuma fadi haka ne har bayan ransa.
Innata ma ta kara jaddadamin hakan, haka aka sani a motarshi a dole yaja muka tafi.
A hanya sai wayarsa yakeyi da Fatima, yana gamawa ya hau ni da masifa akan shi a duniya ba abinda ya sani sai kansa, sannan duk abinda zai aikata sai dai yai abinda yasan zai amfaneshe.

Haka ya kaini can wata unguwa wanda ya kamamin gidan haya daki daya ya sani, sannan ya bani kudi.
Tundaga ranar ban kara sashi a idona ba sai dai lokaci lokaci wani yaro yana kawomin kudi wanda nake sana'a.
Shikuwa sunyi auransu da matarsa suna shan soyayyarsu.
Gidan hayar kullum habaici sukemin akan cikin shege ne a jikina.
Cikina ya kai kusan wata bakwai abin duniya ya dameni, sai ranar kwatsam Habubakar yazo.
Baiyi mamakin ganina da ciki ba, sai dai baice min komai ba ya ajiye abinda ya kawo ya fita.
Ashe gidansu yaje ya sanarma mahaifin Fatima hadin auran dolen da akamai da cikin da nake dashi, ya karasa maganar yana kuka yana cewa shi in har Fatima tace ya sakeni to ba wani kokonto zau sakeni ne.
Mahaifinta yace a'a sannan ya sanar dashi ya daukoni ya dawo dani boys Quaters.
Fatima tasha bori balle da taji inada ciki wanda itama a lokacin tanada ciki.
Haka ya sata a daki ya dinga lallabata har ta yarda sannan ya mata alkawarin bazai kara shiga dakina da sunan tarayyar aure ba.
Zinaru kuwa tasha mita sai dai ba yanda zatai saboda umarnine na mijinta.

Wannan shine dalilina na komawa gidan, mahaifinta shine ya sa miki suna Jalila bayan an sa miki asalin sunan mahaifin Habubakar.....

Kuka ne ya ci karfin Jalila wacce bakin ciki da takaici sukama yawa............


Goggo tace "Jalila bana ganin laifin mahaifinki domin tun farko ya nuna bayaso, iyayena sune basu damu da rayuwata ba...
Jalila cikin kuka tace "kowa nada laifi Goggo ta ya za'a maida rayuwarki kamar rayuwar dabba?ta ya ta ya............
Kuka ne yaci karfinta wanda ya hanata magana...


#Oneluv=ؕ?
[08/10, 02:07] * +234 803 222 1758, : =??? *JALILAH* =???

Written By : *AYUSHER MUHD*
Wattpad: *Ayusher Muhd*


*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*

(_D home of expert and perfect writer's_=ء?)

*No 16*

Kallansa Inna tai sannan ta zare tabaron dake manne a fuskarta, ta ajiye magazine din da take dubawa tace "Me kace?"
Abubakar ya kalleta cikin jin shakarta yace "Inna abinda akai dazu bai daceba, bana tunanin ya kamata a sa rayuwar mahaifiyarta a tsakiya saboda neman abinda mukeso."
Inna tai murmushi sannan tace " a yau ne ka fara damuwa da yar taka? Ko kuwa yau ne kake neman kula da matarka?"
Yace "Inna kinsan ba haka nake nufiba."
Tace "ya isheni haka nan, sannan daga wannan lokacin ba ruwanka akan duk abinda na sharada akan harkar bikin nan, na dauka kaine ka sanar damu da matar da abinda ke cikinta duk baka sansu? Na dauka kaine ka nuna mana Fatima da 'ya'yanta ne kadai abinda kake so?"
Yace "Inna......"
Tace "ya isheni haka nan."

Mumy cikin rashin jin dadi tace "Inna me yasa kike san canza maganar mutunci zuwa rashinsa? Kinfi kowa sanin Abban Yasmin ba haka yake nufi ba, ko ni banji dadin abinda kika aikata ba dazu, yanzu da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login