Showing 114001 words to 117000 words out of 149705 words

Chapter 39 - Jalilah Book One Complete Hausa.doc

Ayusher   

28 Oct 2025

631

bacci haka?"

Kallanta yai tare da ajiye littafin kan cinyarsa yace " ban fahimta ba? Baccin ne bakyasan na barki kiyi?"

Ta kalli agoggo sannan ta kara kallanshi tace "Yanzu me zancema Ummy? Kalli fa agoggo?"

? Agoggon ya kalla sannan yace "dan kin kai 11:30 kina bacci menene damuwar Ummy?"

? Ganin kamar ma bashida niyyar ganewa tace "nikam yau bansan ya zanyi ba." Tafada tana kokarin sauka.

? Kallanta yai tana dan dingisa kafa, dariyarsa ya gumtse sannan yace "me zakice ma Ummy in taga tafiyarki?"

Gabanta ne ya fadi, ta kalleshi da sauri, tace "yaya nashiga uku? Ya zanyi? Yau nikam na gama yawo."

? Kara matse dariyarsa yai sannan yace "kawai ki kwanta sai nace bakyajin dadi.

? Karasowa tai kusa dashi tace "gaskiya kam, yaya ka taimaka kacemata ina zazzabi."

Yace "karya fa kenan?"

Kallan mamaki tamai tace "yaya kaifa ka fara cewa, sannan ai ba karya bane tunda dai da gaske banajin dadin."

? Da sauri yasa hannu saman goshinta yace "daga ina ne yake miki ciwo? Nuna min?"

? Kara shagwabewa tai kamar mai neman yin kuka tace "haba yaya!"

Dariya yadanyi sannan yace "ki kwanta bari na sauka kasa."

Kwanciya tai tana cewa "yauwa Yaya."

Fuska ya hade yace "me zakimin in zan sauka na kai sakonki?"

Tace "kamar ya kenan?"
Yace "aikena zakiyi naga, to me zaki biyani?"

? Tace "oh ni yaya, yanzu kuma me kakeso?"

Yace "banasan sunan yayan nan, na rasa me yasa kika kama suna kamar ke kika rada min, komai yaya bayan ni ba yayanki bane."

? Ya mike ya fita, kasa ya sauko Ummy na zaune tana kallo, sai dai idanunta ne kawai ke kan Tv din amma batasan me ake ba, hankalinta nakan su Hassan.

Hassan taga yana saukowa, daurewa tai kamar bata damuba ta kara kallan Tv din da kyau kamar bataganshi ba.

Harsai da ya kusa saukowa sannan tace "Hassan!"

Murmushi ya mata ya matso kusa da ita yace "Ummyna an tashi lafiya?"

Tace "lafiya kalau yarona, ina Jalila? Ko tana bacci?"?
Yace "a'a."

Kallansa tai kamar zata sake tambaya, yanda tafa yayi gefe da kansa ne yasa tace "ga breakfast dinku can sai ka daukarmuku."

Yace "tam."

Kitchen din kawai ya shiga ya dauko musu tiren abincin sannan ya hau sama, yana ajiye wa ya dauko na daren ya sauko dashi.

Ummy tai murmushin jin dadi, tace "Hassan, Abbanka yace ka shirya anjima zaizo shiga Sageer kuje sallar juma'a in kuma bai gama abinda yake ba zai kiraka a waya kaje sai ku tafi."

Yace "To Ummy."

Haryadanyi gaba sai kuma yace "yarinyar nan fa?"

Tace "kwana biyu kenan banga kiranta ba."

Yai murmushi sannan ya juya ya tafi.


*********

Dady cikin bacin rai ya kalli Mumy yace "wai menene hakan?"

Kara kwantowa jikinsa tai tace "menene? Ranka ne a bace?"

Daurewa yai yace "a'a kawai banajin dadi ne."

Hannunta ta zaro daga cikin rigarsa tace " meke damunka?"
Yace "menene ma bazai damen ba? Gaba daya ba wanda yake ganina da daraja? Yaran nan bakiga yanda yaci mutunci na ba? Ita kanta yarinyar ba mutunci na take gani ba, Harta employees din company dinmu ba mutunci na suke gani ba."

Jiki a sanyaye ta kalleshi tace " ko inma transfer na share dina na company?

Ya kalleta yace "so kike Inna ta kara tsanata?"

Tace "ba sai ta sani ba, sai muyi a tsakaninmu."

Jawota yai jikinsa yace "banaso inzama silar samun matsala tsakaninki da mahaifiyarki."

Kwanciya tai a jikinsa tace "karka damu da wannan."


#OneLuv=ؕ?[1/12, 9:39 AM] Maryam: =??? *JALILAH* =???
Written By : *AYUSHER MUHD*
Wattpad: *Ayusher Muhd*
*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*
(_D home of expert and perfect writer's_=ء?)
_Where are u my beloved Wattpadians? A word can't express how much u means to me, when ever i feel down, ur comments always cheers me up.........=ؕ?=ؕ?=ؕ?=ؕ?Luv U All=ؕ?=ؕ?=ؕ?
*63*
Yana shiga daki ya kalleta, tana dukunkune cikin bargo wai a dole kar Ummy ta shigo.
Hassan ya matso kusa da ita yace "Amarya tashi ku gaisa da Ummy."
Kara dukunkunewa tai tana dagamai hannu alamar tanasan magana, guntse dariyarsa yai ya matso kusa da ita gaf da fuskarta.
Tana juyowa ta ganshi gaf da ita, idanu ta kifta tare da hadiyar yawu tace "Yaya me ka cema Ummy?"
Yace "kamar me kenan kike san ji?"
Cikin rada ta sake cewa "ba tare kuke ba?"
Yace "ni da wa kenan?"
Labanta tadan ciza kamar zatai kuka tace "Yayah Please."
Baki yadan tabe sannan ya koma kan kujera yace "Ummy wai ki tafi batasan magan........."
Ai bai karasa ba ta yaye da sauri tana cewa "Ummy wallahi ba......."
Ganin ba kowa yasa ta hadiye maganarta, kallansa tai cikin mamaki, gani tai bashida niyyar kallanta, waya yake danna wa.
Jitai kamar tasa kuka, lalai yayan nan, wato dama rashin lafiya ce ta rikeshi zolaya da tsokana ce fal cikinsa?
Gaba daya ma kamar baisan tanayi ba, haushi ya isheta ta koma ta kwanta.
Dariyarsa ya guntse sannan ya kalleta, yace "Amarya yaushe zaki bani abinci ne? So nake na shirya kafin sallar azahar."
Juyowa tai bangaren da yake, ta hade fuska wai a dole tayi fishi ta kalleshi.
Kallanta yai yace "Allah daga na irga yan mintina ba'a ban abinci ba bazanci ba."
Mamaki ya kamata tace "da gaske sai ka ki ci?"
Yace "Ko zamu gwada?"
Batasan sanda tai dariya ba, shima dariyar yai kadan a ransa yace "u smiled."
Amma a fili ido kawai ya kura mata yana kallo, yana san yarinyar nan har baisan wani irin so yake mata ba, ko dan a rayuwarsa bai taba zama da wata mace bane daga Ummy sai ita? Dan Ameera ma saboda matsalarsa basu samu sun shaku ba.
Jalila ta kwantar da kanta tana kallansa, batasan me yasa ba, tanasan taga murmushi a fuskarsa.
Ganin yanda take kallansa ne yasa ya ajiye wayar ya mike a hankali yazo inda take, tsayawa yai yana kallanta kafin yace "Kallan fa?"
Tace " kawai mamaki nakeyi ne."
Yace "mamaki na ko?"
Kai ta daga alamar eh, yace "in zan zuba mana abinci me za'a biyani dashi?"
Tace "kamar ya?"
Yace " dazu ma nace a daina cemin yaya kuma har yanzu an kasa dainawa, karfa biyan bashi ya miki yawa."
Tace "a'a ni bari na zuba da kaina, me yai zafi?"
Ta fada tana neman mikewa, hannu yasa ya maidata yana murmushi yace "just joking, amma na yanzu."
Bargon ya yaye ya miko mata hannu, kallansa tai ya mata alama data kama hannunsa, nan tasa hannu ta rikeshi, a hankali ya taimaka mata ta sauka, gun da suke cin abinci ya karasa da ita sannan ya zaunar, shima ya zauna.Kular ta bude, plantain ne aka soya aka dora soyayyan wainar kwai a sama, dayan kular kuma anyi potato ball, sai farfesun naman rago.
Zubawa tai a plate, sannan ta matso mus da plate din tsakiya, kallanta kawai yakeyi har ta gama sannan yai bismillah ya fara ci.
Itama ta fara ci, sunyi shiru suna cin abinci sai dai kallon juna da sukeyi jefi jefi, in suka hada ido kuma sai su saki murmushi a tare.
Ya kalleta yace "kin samo sunan da zaki fada min?"
Tace "wlh ni yaya......"
Kallan daya mata ne yasa tai shiru tana cewa "oh ni..."
Jitai yace "me kike cema Sageer?"
Kallansa tai kawai tasa dariya, tace "oh ni, shi fa uncle din mu ne dama haka muke cemai."
Bai kara magana ba ya cigaba da cin abincinsa, sai dai yanzu ya daina kallanta.
Har suka gama cin abinci, ya mike yace "bari nai wanka."
Ta daga kai alamar to, ya wuce toilet.
Murmushi ta bishi dashi sannan ta hada kwanukan, mikewa tai ta gyara gadon sannan ta dan kara kimtsa dakin, kofar ya turo hangota yai tana gyara gun kujera tare da maida littafin dayai amfani dashi, a hankali ya tako inda take, ita kuma jin motsin kofa yasa tace "yaya ka fito?"
Sam batai tunanin yazo inda take ba, ta sukunya tana ajiye littafin taji ya sanya hannayensa ya zagayo cikinta, tsayawa tai cak dan batai zaton jinsa haka ba, a hankali ta juyo ta kalleshi sumbatar bakinta yai kadan sannan yace " kinasan kari ne?"
Tace "karin me?"
Kara sumbatarta yai yace "yanzu fa?"
Kallansa tai kamar zatai magana sai kuma tai dariya, ya matso saitin kunnenta yace "Jalila bansan meke damuna ba?"
Dagowa tai, ya juyo da ita saitinsa, tace " bakajin dadi ne?"
Yace "ko kadan kawai sai nake jina kamar ba ni ba."
Tace "jikin naka ne?"
Ya zare hannunsa daga kugunta ya sa akan fuskarta yace "ko kadan kawai dai haka nakejina, da alama shekarun dana samu a dukunkune sune nakesan na fanshe."
Murmushi tai har hakoranta suka fito tace " haka ake so ka fanshe duka, tun daga yarintar ka data rike zuwa yanzu....."
Yanda yake kallanta ne yasa tai kasa da idanunta tana murmushi gaba daya yaya yasa tana neman cire kunyarta.
Saketa yai yace "kin tabbatar zaki jure ko?"
Tace "zan jure."
Juyawa yai yana sa kaya, ta juya tare da zama kan kujera, shadda ya dauko sabuwa, cikin wanda Abba ke yawan dinkamai baya sawa, duk sanda Abba zai dinkama Sageer manyan kaya sai ya dinka masa, sannan dama ko kananan ma shi yake siyo masa.
Yayi kyau kamar ba shi ba, ya dauko hula ya saka, ya karasa gaban madubi ya sa turare tare da sa agoggo, Jalila ta zuba mai ido ta cikin madubi, kallanta yai tai saurin dauke idanta, takalmi ya dauko yazo kusa da ita, hannu yasa ya dau wayarsa tare da nuna mata sannan ya dau key yai hanyar waje.
Sai dayaje kofa yace "na tafi."
Wani lallausan murmushi ta sakar mai sannan ta daga kai alamar to, ya fita tare da turo kofar, idanu ta lumshe tana tuno daren jiya, lalai itakam bata taba kawo wannan yanayin ba, kwanciya tai kan kujerar tare da lumshe idanunta.
Knocking din data jine yasa ta bude idanunta, tare da kokarin mekewa, Ummy ce ta turo kofar tana cewa "ba sai kin taso ba Jalila."
Ganin Ummy ce yasa cikin hanzari ta mike tana neman tahowa gunta, azabar dataji ne saboda saurin datai yasa tadan tsaya sannan tadan cigaba da takowa a hankali.Ummy tana kallanta ta fahimci lalai danta ya girma, tana karasowa kusa da Jalila kawai ta rungume Jalila.
Cikin mamaki Jalila tai tsuru tana san sanin meke faruwa, Ummy tace "Allah ya miki albarka ya kareki daga sharri duk wani wanda yake nemanki da sharri, ya sa aljanna ta zama itace makomarki, ta sa ki gama da duniya lafiya."
Jalila a hankali tace "Ameen."
Ummy ta saketa sannan ta jawo hannunta suka zauna a bakin gado, tace "kin dan shiga ruwan zafi ne?"
Cikin rashin fahimta tace "ruwan zafi?"
Tace "zaki iya saukowa? Muje kasa?"
Jalila tace "eh."
Ummy tace "dauko kayan da zaki saka sai muje kasa."
Mikewa tai ta bude drawer kawai kayan dake sama tasa hannu ta jawo, Ummy tai murmushi tace "Jalila atamfar ya dinkinta yake?"
Tace "wlh ban sani ba Ummy, na daiga shine a sama."
Ummy ta mike tazo ta bude kayan, maidasu tai ta cigaba da dubawa, sai datazo kan wani material mai masifar kyau, jikinsa kamar lace yake sai dai ba kafe bane, ita tasiyoshi da kanta sanda ake hada lefe.
Budeshi tai taga dinkin kuwa yayi kyau riga da skirt ne.
Ta ajiye sannan tace "muje?"
Jalila tace to, Ummy tace "dauko inners."
Kunya ta kama Jalila ta zaro ta cusashi tsakiyar kaya, Ummy tace "mu tafi to."
Nan suka sauko Ummy na rike da hannunta.
Da yake toilet din sama bashida bath hub kawai gun shower ne aka killaceshi shi yasa ta sauko da ita.
Dakin Ameera ta kaita sannan ta shiga toilet ta kunna ruwan zafi, sannan ta toshe makwararar ta fito, zama tai kusa da Jalila wacce ita gaba daya ta kasa gane me Ummy ke nufi, ba dai tasan wani abun ya faru ba? Ko da yake bata fada ba ta ya zata sani?
(Nace uhm yaro man kaza>?#?)
Fita Ummy tai bata dade ba ta shigo rike da kofi, na baza ido ina san ganin menene a ciki, mikama Jalila tai tace "sha."
Jalila ba musu ta amsa ta kafa kai ta shanye, sannan ta mikama Ummy kofin, Ummy ta kalleta tace "Munyi waya da Goggonki tace "tanaso tadan je kauye taga gida."
Jalila tace "jiya munyi waya amma bata fadamun ba."
Ummy tai dan dariya kafin tace "batasan ne kece sai kin bita."
Jalila tace "Amma Ummy ba tare ya kamata muje ba?"
Tace "tunda dai ita kadai take san zuwa yanzu sai ki barta taje inyaso ke daga baya sai kije ko da Hassan ne ko kuma ku koma tare."
Jalila ta daga kai alamar to, sannan tace "yaushe zata?"
Ummy tace "gobe da safe, nasa Sageer ya tura Mamman driver da mota sai suje tare."
Jalila tace "to Ummy Allah ya kaimu, mungode sosai."
Ummy tace "muma mun gode, ta shiga toilet, sai dataga ruwan yayi kusan rabi sannan ta kashe ta taba ruwan, jun zafi sosai yasa ta????































!
"
#
$
%
&
'
(
)
*
+
,
-
.
/
0
1
2
3
4
5
6
7
8
9
:
;
<
=
>
?
@
A
B
C
D
E
F
G
H
I
J
K
L
M
N
O
P
Q
R
S
T
U
V
W
X
Y
Z
[
\
]
^
_
`
a
b
c
d
e
f
g
h
i
j
k
l
m
n
o
p
q
r
s
t
u
v
w
x
y
z
{
|
}
~

?
kunna na sanyi.
Sai data tabbatar komai yayi sannan ta fito ta kalleta tace "ki shiga cikin ruwan ko zuwa minti 20 ne zakiji dadi inkin fito."
Yanzu kam Jalila ta fara fahimta, da sauri ta sunkuyar da kai cikin kunya, Ummy ta juya ta fita.
Jalila kunya ta rufeta da kyar ta mike a shiga.
Yanda Ummy tace tayi haka tayi.
Ta dade a ciki kafin ta cire tai wanka.
Taji dadin jikinta sosai, kaya ta saka ta shafa mai da powder sai turare kawai ta fito falo.
****************
Zaliha ce ta shiga wurgi da kayan dake cikin wardrobe dinta tana wani irin ihu, Auntyn ta ta matso tana cewa "Zaliha menene hakan wai? Tunda kika dawo daga kano gaba daya kin koma kamar wata wacce bata cikin hayyacinta, wani abun ya faru ne wai?
Kayan kawai take zubarwa tana ihu, ganin abin yaki karewa yasa ta matso kusa da ita ta rike hannayenta, ta girgizata tace "Zaliha wai meke damunki? Gaba daya kin canza, ko abincin kirki ba ci kike ba, wai menene ke faruwa? Kin ki fadamin sai ihu kawai kike."
Ture Aunty nata tai ta fada kan gado tace "me? In amince duk abinda nakeso zan samu? Kinsan me aka kirani dashi? Ko bacci nakeyi in na tuno abinda akamin sai dai na farka, ko abinci nasa abakina ina tunowa sai naji bazan ita taunawa ba."
Tace "to me aka kiraki dashi?"
Kara watso wasu kayan tai wanda suka rage a ciki ta sa wani ihu na bakin ciki......
Mamaki da tsoro ne suka hanata magana, tana kallan yanda take ihu daga baya ta tsugunna kawai tasa kuka.........
**********
Yana isa yai parking ya fito da sauri dan ganin motarsu na kokarin fita, wayarsa ya dauko da sauri ya kira number Abba, Abba ya daga yana kallan Sageer.
Hassan yace "Abba gani nazo, naga kamar zaku fita."
Ya kalli Sageer ya fadamai, nan Sageer ya juya kan motar, a tsaye suka ganshi, suna karasowa kawai ya shiga bayan motar.
Abba yace "motar taka fa?"
Yace "in mun dawo sai in biyoka sai na dauka, ko na turo mamman."
Abba yace "okay, dan daga masallaci gida zamy muyi lunch."
Sageer ne ya juyo ya kalleshi yace "Yaya barka da isowa."
Hassan ya kalleshi cikin tsantsar kulawa yace "ya? Ko na anshi tukin ne?"
Sageer yai dariya yace "yaya ka manta? Na rigaka fa iya mota, kai da sai da daga tasa ka gaji da zaman daki kasa Mamman ya koya ma."
Hassan ya harareshi yace "amma dai daga nan har......"
Abba yai dariya yace "ba wani har..... shi dai mutun tunda an wuceshi shine yake neman waskewa."
Hassan yace "bakomai tunda hademin kai za'ai zan sanar ma Ummy na nima."
Sageer yai dariya yace "wai yaya wallahi Allah ne kawai ya tsare da katon Mama Boy za'ai."
A tare suka sa dariya da Abba, Abba yana cewa "sosai ma."
Hassan yace "to duk kowa ya gama nima zan fanshe."
Haka sukai ta yan tsokana kana ganinsu kaga mutanen dake cikin tsantsar farin ciki, bazaka taba tunanin wani ba dan wani bane a cikinsu.....
(Ni kaina da badan Hassan ya sanar ma Jalila ba ko da wasa ban taba kawo hakan ba.....)
#OneLuv=ؕ?
[1/12, 9:39 AM] Maryam: =??? *JALILAH* =???


Written By : *AYUSHER MUHD*
Wattpad: *Ayusher Muhd*


*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*


? (_D home of expert and perfect writer's_=ء?)

_Gaisuwa gareku yan Maryam Salisu Maidala, Hausa Novels Room, Unity Girls 2011, Mamu Novella da Billy Giro Novel...._


*64*

Yanda ake ta shiga cikin masallacin ga wasu sunata sa sallaya a waje, wasu akan tabarma, wasu kuwa ma a haka suke tsayawa, anata huduba,Hassan ya kurawa mutanen ido zuciyarsa na wani irin bugawa, Abba ya sa hannu ya riko hannunsa, sannan ya kallu Sageer yace "muje?"
Sageer ya daga kai tare da cewa "Yaya yau sai mu rubuta ta cikin tarihi."

Hassan yai murmushin yake, haka Abba ya rikeshi, Sageer na rike da babbar sallayarsu, masallacin ya cika dan haka daga baya ya shimfida musu sallayar, Hassan zuciyarsa na ta sake rauni, yana neman yafiya gun Allah akan rashin ziyarta dakinsa dayai na shekaru haka masu tsayin gaske.

Haka suka je suka zauna sunajin huduba, a hankali wasu zafafan kwalla suka gangaroma Hassan, dan a iya tsawon hankalinsa zaice bai taba jin huduba haka ba sai dai dayake yanajin na saudiya a waya amma bai taba ji zahiri haka ba, Abba ma ji yai gaba daya jikinsa yayi sanyi, hannu Sageer ya sa ya dafa kafadar Hassan.
Hassan ya kalleshi cikin wani yanayi na jin dadi da tausayawa, ji yai ya fara yi masa addu'a a ransa "Allah ka kare wannan yaran, ka biyamai bukatunsa na alkairi, ka kareshi daga sharrin masu sharri, ka bashi mace ta gari wacce zata so shi ta kuma kaunaceshi fiye da tunanin mai tunani."

Ganin yanda yake kallansa yasa Sageer yace "yaya."

Hassan ya maida kansa kasa kawai baice komai ba, har lokacin sallah yai sukai sallah sannan suka shiga mota.

Abba yace "yanzu mu wuce gida? Ko da wani abun?"

Hassan ya kalli Sageer yace "kanada abinyi? Ni dai gidan nan nafi san zuwa."

? Abba yace "gida kafisan zuwa ko gun matarka?"

Hassan ya kalli Sageer, shikam dariya yai yace "da alama Abba ka gano yaya, dan na kula ya gama matowa."

? Ganin yanda Sageer yai ne yasashi yin murmushi kadan yace "Abba ba haka kakeso ba dama?"

Da sauri Abba yace "ka gama magana dan kuwa hakan shine buri na."

Nan Hassan ya tada mota dan dama yanzu shi ya karbi tukin, Yace "Sageer kai fa? Har yanzu ba labari?"

Abba yace "ni kaina na matsu inji labari, ya? Haryanzu dai?? Gashi har zaka fara aiki."

Sageer yace "in nayi auren ina zan sata?"

Da sauri Hassan yace "Sama, dan ni......."
Yanda Abba ke kallansa ne yasa yai shiru tare da waskewa yace "ni sai in

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login