Showing 66001 words to 69000 words out of 149705 words

Chapter 23 - Jalilah Book One Complete Hausa.doc

Ayusher   

28 Oct 2025

612

haka bamuyi san kai ba? Ko baka ga na fara tsufa bane?"

? Idanunsa ya rufe cikin takaici yace " ya wani irin? zance kikeyi Ummy? Waye zai ga Ummy yace ta tsufa?"

Ummy tai dariyar takaici tace "ba wani kai dai sankai zakai, Hassan gashi nan na fara gani."
Yace "me?"
Tace "samun saukinka mana, rabon da kayimin magana mai tsayi haka har na manta, yau gashi nan kana min magana."

? Shiru yai kawai yana kallanta, Ummy cikin jin dadi tace "Kar kasa komai a ranka, ka manta da maganar da kukai yanzu, kayi kokari ka dawo Hassan dinka ma da, I really miss that Hassan."

? Baice komai ba sai kallanta kawai da yakeyi, Abba ne ya share kwallar data dan zubo mai, sannan yai waje da sauri.

Ummy ta kalli Hassan tace "Please ka kula da matarka, wannan shi kadai ne abinda ni nakeso, kaji?"
Hassan yai shiru, ta juya tai waje.

? Jalila na zaune a kasa a falo ta sa kanta akan gwiwowinta, gaba daya abinda ke faruwa ya sa tausayin Ummy ya sa ta zubar da kwalla, wannan wace irin macece? Ita lafiyar Hassan ce a gabanta bawai abinda taji ba?

? Tana kallan Ummy ta fita, mikewa tai ta shiga dakin, gani tai har ya tada sallah.
Nan itama ta wuce tai alwala tai sallah, ganin bashida niyar mikewa daga kan sallaya yasa ta fito daga dakin.

? Abba kam daki ya shiga ya shiga zagaye dakin cikin takaicin abinda zuciyarsa take sashi aikatawa, wani irin butulci ne hakan yake shirin yi? Ummy ce ta shigo dakin tacemai, yallabai ka fito kaci abinci, ko in kawo ma nan?"

Jiki a sanyaye yace "muje can din."

? Ya zauna akan kujera ta zubamai sannan ta turamai abincin gabansa, sannan ta juya tai daki.

Da kallo ya bita dan baisan ta ina zai fara magana ba, shi yanda takeyi kamar ma batasan me ake ciki ba shine ya kara tsoratashi, dana sani ya kara kamashi.

? Jalila kam, sai yamma liss ta samu taci abinci kadan, sam ba fuska agun Hassan, dan ko kallanta baiyi ba bare ta samu damar yi mai magana.

Haka tai tayin abinda zatai har dare, shikansa Abba har dare bai samu damar yi mata magana ba.
Bayan sallar Magrib ne Sageer zai shigo yaga motar Dady.

Nan yasa aka budemai yai parking din motarsa, Dady ya fito suka gaisa, Sageer ya jashi ciki.

Yau gidan tsit ba dadi, Hassan na daki, Jalila na falo a kan carpet a kwance tana latsa waya, Ummy na falo shi kuma Abba yana daki.

Sageer ne ya shigo ya kalli Ummy yace "Ummy dadyn Jalila me yazo."

Mikewa tai da sauri tace "ka shigar dashi falon Abba"

Nan Sageer ya shigo dashi yai bangaren Abba.

Ummy ta bude dakinsu ta kalli Abba dake zaune yayi shiru abin duniya ya dameshi tace "Abban Ameera ka fito Baban Jalila ne yazo."

Abba ya mike tare da cewa to.

Ta juya ta fita, Sageer ne ya karaso yace "Ummy na kaishi."

Tace "Sageer dan hau sama kama Jalila magana, bari na shirya abin sha."

Yace to, sannan ya hau sama har zai kwankwasa kofar yaji motsi a falon, nan ya juya ya falon, a kasa ya ganta tana ta latse latsen waya, tv din ma ba'a kunne take ba.

Kallanta ya tsaya yana yi cikin tausayawa, sai dai ya taya yayansa murna ta fara samun lafiya, sai dai shikam tausayin kansa yakeyi, anya zai iya san wata kuwa?

? Jalila ce ta juyo, ganinsa tai a tsaye ta mike zaune tana kallansa, yace "ashe kina nan?" Ya dan sosa keyarsa.

Tace "Eh."
Yace "Uhmm dama Ummy ce tace nazo na fadamiki Dadynki yazo."

Kallansa tai cikin mamaki tace "Dady?"

Yace "eh, yana fallon Abba." Ya fada tare da juyawa.

Jalila ta mike gabanta na faduwa, me yazo yi? Badai wani abin bane ya samu Goggon ta?

A rikice ta shiga dakin tana neman hijab dinta, gashi a gabanta wanda ta ninke bayan tayi sallah amma tsabar hankalinta baya jikinta sam ta rasashi.

? Hassan dake zaune yana kallanta shine yace "menene?"

Matsowa kusa da shi tai kamar dama jiran kiransa takeyi, tace "Yaya! Dady ne yazo, baka tunanin ko wani abun ne ya faru da Goggona? Ko kuma wani abun suke shirin yimata?"

? Ganin yanda ta rikice ne yasa yace "Dan yazo shine kika rikice haka?"

Tace "Yaya bansan........"

Tai maganar cikin wani irin murya mai raunin gaske, da yatsarsa ya nuna mata hijab din sannan yace " a haka zaki?"

Ta kalleshi alamar rashin fahimta, yace  bazaki daidaita kanki ba?
Tsayawa tai tana ajiyar zuciya wai tana calming din kanta, baisan yanzun ma bakinsa ya motsa ba saboda yanda takeyi.

Yace  yimin magana naji.
Tace  Yaya!
Yace  sake.
Tace  Yaya.
Yace  bai yi ba.
Baki tadan turo tace  dazu amma inasan maka magana ai hade rai kayi.
Ya kalleta yace  ni yanzu inaji damuwar dake gabanki tafi tawa, ke mahaifiyarki zaki ceto wace take hannunsu, ni kuma i am confidence akan I will protect mine.

Tace  ni ma.......
Sai kuma tai shiru dan tasan she is not confident.

Yanzu ma bakinsa sai da ya sake motsawa yace  jeki, bari na jira naga yanda zakiyi.

Ta kalleshi tace  yaya zakazo?
Yace  ina kenan?
Tace  gun Dady, tsoro nakeji kar ya sani abunda banzan iya bijerewa ba.
Kafada ya daga mata alamar ba ruwansa.

Jalila tai raurau da ido tace  Yaya Please!

Samun kansa yai da kallanta cikin wani yanayi sannan yace  ki wuce kije ko?

Ta dau hijab jiki a sanyaye ta fita..........

Da kallo ya bita har ta fita daga dakin, yabi kofar da kallo.

#OneLuv=ؕ?


=??? *JALILAH* =???

Written By : *AYUSHER MUHD*
'ote me on Wattpad : *Ayusher Mohd*


? ?? *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*
? (_D home of expert and perfect writer's_=ء?)



*39*



? Fitowa tai jiki a sayaye, abin duniya duk ya dameta ga tsoron abinda zai fito daga bakin Dady da takeyi.

? Tana sauka kasa taga Ummy, Ummy ta nuna mata hanyar falo tare da mika mata tiren dake dauke da juice da cup, Jalila ta amsa tare da yin murmushin dole sannan ta nufi falon.

A gefen kofar da zata shiga da ita falon taga Sageer a tsaye, kallansa tai da idanunta wanda suka cika da taoro, yace "Jalila, menene wai?"
Kai ta girgiza mai alamar ba komai, zata shiga yankara kasa da murya yace "Jalila?"
Juyowa tai ta kalleshi, yace "Bakyasan ganin mahaifinki ne? Naga tunda na fada miki yazo naga fuskarki ta canza."

? Murmushin yake tai sannan tace " bakomai, nagode."
Kawai ta shiga, dan batasan me zatacemai ba.
Abba na falon suna ta magana ta shiga bakinta dauke da sallama.
Abba da Dady suka amsa, Dady ya kalleta cikin farin ciki yace "Jalila!"
Jalia tace "naam sannan ta karasa ta ajiye tiren a gabansa ta gaisheshi.
Abba ne ya mike yace "yanzu ba abin business kazo ba, uba ne yazo ganin yarsa, kaga bai kamata na shiga tsakani ba, later mayi magana."

Dady ya mike yana godiya har ya fita, kallan Jalila yai wacce ke tsugunne a inda ta ajiye juice din, Dady yace "zauna mana."

Ta gyara zamanta tana kallansa, gabanta sai faduwa yake.

Dady ya zauna sannan ya kalleta yace "hmm ya gidan?"
Tace "lafiya, wani abun ne ya samu Goggona?"

Yace "wani abun? Kamar me kenan?"
Tai shiru ta kasa magana, yace "dan uba yazo ganin yarsa sai ya zama sai akwai matsala?"

Jalila ta kalleshi tace "a'a ba haka bane."

Yace "Jalila ni mahaifinki ne, ki daina dararewa da ni."

Ta kalleshi kawai bata ce komai ba.

Matsowa ya danyi kusa da ita yace "jalila magana nakesan muyi."
Kallansa tai cikin tsoro, yace "Nikam ya kukai da mijin naki?"
Tace "wani mijin?"
Yace "wanda kukazo tare mana, badai wani abun kika fadamai ba ko? Naga kamar baiji dadi ba ranar."

Jalila ta kalleshi gabanta na faduwa ta kasa magana, Dady yace "amma yasan Goggo ce ta haifeki ko?"
Jalila ta daga kai alamar eh, Dady yace "ya fadama wani ne?"

Tace "ban gane ba?"
Yace "ya fadama wani kamar mai gidan nan cewar Goggo ce ta haifeki?"
Jalila tai shiru, yace "ba dai duk wani sirri na gida kin fadamai ba?"

Jalila ta kalleshi yanzun ma batace komai ba, ya kalleta ransa a bace, badai duk wahalar da wulakancin da ya hadiye ba lokaci daya wannan yarinyar zata zo ta ruguzamai? Dan ya tabbatar in har Taura ya kwace kudin daya basu tabbas Inna korar sa zatasa ayi daga company din.

Kallan Jalila yai rai a bace yace "Wai Habiba ba magana nake miki ba? Sai dai ki kalleni? Ko kema munafircin uwar taki zaki koya?"

? Jalila cikin tsoro ta kalleshi, hannunya daga a zuciye zai kai mata mari.
Jiyai ance " da alama sararka kenan?"

Juyowa tai da sauri ya kalli mai maganar, Jalila ma kallansa tai kawai sai ji tai hawaye sun zubo mata.
Karasowa yai cikin tafiyarsa ta isa sannan ya kalleta yace " tashi."

Mikewa tai tana kallansa, yace "bakiji me nacemiki ba ne da zaki zo?"

Tace "me kace?"
Yace  sau nawa zan ce miki ki canza tone in zakiyi magana? Meyasa bakyayi da confidence?

Kallan juna sukai, hawaye ya gangaro mata, juyawa yai ya kalli Dady wanda yai tsuru tsuru.

Hassan ya kalleshi yace  gobe zanzo muje dakai asibiti inda aka kwantar da mahaifiyarta, a gabanka zakasa hannun sallama mu amsheta.
Dady yace  me kake nufi?

Yace  abinda zuciyarka ta baka, u don t deserve to be a father nor a husband.

Kallan Jalila yai yace  wuce mu tafi.

Kallan Dady tai gabanta na ci gaba da faduwa, Hassan ya kalleta ya mata alama data fara fita, nan ta fita tana waiyaye.

Tana fitowa daga bangaren falon taga Sageer a tsaye a jikin bango.
Yana ganin ta fito ya matso da sauri yace  Jalila
Hawayenta ta share sannan ta kalleshi, yace  menene?

Kallansa tai kamar zatai magana sai kuma ta fasa ta juya tai gaba, Sageer yace  Akwai abinda ya faru ko? Naga yaya ya shiga kuma shi bai fito ba.

Juyowa tai ta kalleshi sannan ta juya kawai ta hau sama da gudu.

A falo kuwa

Hassan ya kalli Dady yace  me ka samu, na saida yarka dakai?
Dady yace  me kake nufi?
Hassan yace  yanda kai da manyanka iyayen gidannka kuke nunawa, kunayi ne kamar kun samu wani abu sosai wanda yasa kuka bada yarku.

Dady ya kalleshi yace  Hassan ta ya zaka ce haka? Kana so kace rashin so ne yasa muka aurar da ita?
Yace  sosai, inba rashin so ba kun taba tambayar ya mijin nata yake? Wasu halaye gareshi? Me nene aikinsa? Ya mu amalarsa da jama a take? Duk kunyi wannan tambayar? A matsayinka na uban yarinya?

Dady ya kalleshi yace  Inna tayi bincike ita ce tasan mahai.......
Ya katseshi rai a bace  wacece ita? Menene matsayinta agun Jalila?

Dady yace  bangane ba?
Hassan yamai wani kallo yace  karka manta gobe zanzo in banzo ba jibi zanzo, in kuma har kukai tunanin yin abinda bai kamata ba, zan baku mamaki.
Ya juya bai jira mai zai ce ba ya fita.


Dady haka ya fito gaba daya kansa yayi nauyi, Sageer ne kawai a falon yamai sallama ya fita, yana cemai ya gaida Taura.


Mota ya shiga yai gaba.

Sai daya je kofar gida sannan yai parking a gefen mota ya kashe motar ya fito yana tunanin abinda zai fi mai mahimmanci, danshi rayuwarsa itace gaba da komai, mai zaiyi dan cigaban sa?


Hassan kam yana haura beni kansa na wani juyawa da kyar ya kai kansa daki yana shiga ya kwanta.

Jalila na falo tana ganinsa ta taso dan dama ta kasa ko zama ne.
Yana shiga a shiga dakin itama, akwance ta ganshi akan gado, taje kusa dashi tana san mai magana sai dai ganin idanunsa a rufe tasan bayasan magana, balle ya juya mata baya.

Ta dan dade a tsaye kafin ta fito.

Karfe tara tai shimfida ta kwanta, shikam tunda yai sallah ya sake kwanciya bai sake ko motsawa ba balle ta samu damar magana.

Shikam takaicin abinda ke faruwa a gidansu ne yake damunshi, meke damun Abba? Meyasa ita wannan rayuwarta take a cude? Meyasa abubuwa ke faruwa haka? Yau ce rana ta farko dayai fada da magana mai tsayi haka, gaba daya kansa wani irin sarawa hakeyi, ya dade sosai kafin bacci ya daukeshi.

Jalila kam ta dade a kwance kamar tana bacci, me suka fada da bata nan? Taya uba wanda ya haifeta zai dinga mata haka? Hawayenta ta share data tuno rayuwar da mahaifiyarta tai, lalai bazata bari Goggo ta cigaba da zama dasu ba.

Juyawa tai saitin da Hassan yake, ta haska wayarta, ganinsa tai a dukunkune ta mike ta dan rage A.C din dakin sannan ta matso inda yake, kansa baya kan pillow din, in dagashi? Ganin yanda ya kwanta a takure.

Hannu tasa a hankali ta daga kansa ta daura akan pillow din sannan ta juya ta kwanta.

Shikam tana tabashi yaji ta, har sai data kwanta idanunsa na bude juyawa yai shima saitin da take kwance, duk da ta kashe hasken dakin ba ganinta yakeyi ba, sai dai ya samu kansa da tsurawa gun ido kafin ya maida idanunsa ya rufe.


*************

A kasa kuwa, Ummy ce tasa kayan baccinta ta sa hijab tana neman fita daga dakin.
Abba ya kalleta yace  ina zaki?

Tace  Dakin Ameera, ni kam kamar munyi kuskure da mun sani dakin can mun gyarashi.

Kallanta yai yanda take mai magana kamar bawani abu na sabani a tsakaninsu.

Abba ya kalleta zaiyi magana wayarsa tai kara.

Kallansa tai tace anama waya, ta juya ta fita.

Zaliha ce, kashe wayar yai gaba daya sannan ya mike ya fito daga dakin.

Dakin Ameera ya shiga, Ummy tana kade gadon ya bude kofar, kallansa tai tace  ya akai? Ko akwai abinda kakeso?

Abba ya kalleta sannan ya shigo ciki ya zauna akan gadon yace  Kinsan gwara kiyi fada?
Tace  fada kamar yaya?

Yace  wannan abinda kikeyi it really scared me, gwara ki nunamin ranki ya baci in ma hakuri ne na baki.

Tace  munyi fada dakai ne?
Kallanta yai, tace  kai da Hassan ne kukai fada akai na wanda ni banaso, sai dai ya zanyi? Banaso naga kuna irin wannan akaina, tunda nake dakai na taba hanaka aure?

Yace  kece kuwa kike da yanda zakiyi tunda akanki akeyi, ke kadaice kike da dama hana fadan, sannan maganar aure nasan tunda nake dake ban taba sha awar kawo wata mace gidana ba, yanzun ma ni kaina bansan meke damuna ba.

Ummy ta kalleshi tace  saboda kanasan ta shine ka hauni da fada waccan zuwa akan zaka koma Abuja, sannan yanzu kace bakasan meke damunka ba? Ni mubar wannan maganar, ni matsalata da damuwa ta akan Hassan ne, dan Allah ka daina barin yana sanin abinda ke faruwa a tsakaninmu, kafi kowa sanin halinsa in har yasan ina cikin damuwa, banaso Sageer ko Ameera ma susan wannan maganar, na rokeka da Allah, in aure zakayi kayi, wannan ra ayinka ne sannan rayuwarka ce amma Please karka bari yarana su shiga wani hali a dalilin abinda kakeso.

Abba ya runtse idanu cikin takaicin abinda ya dade yana ginawa, wato farin cikin gidansa na neman wargajewa a dalilinsa.

Ummy ya kalla cikin wani yanayi na tausayawa sannan yace  Maimuna ina cikin wani hali........

Yanda yai maganar ne yasa ta tsaya tana kallansa sai dai tausayinsa ne ya kamata, dan bazata taba manta irin wannan muryar ba daya zo mata da ita a can baya shekaru masu yawa, a lokacin kalmar nan sai data sata kuka mai yawa, yanzun ma hannunta tasa akan nashi sannan ta zauna a gefensa tace  In kanasan ta ka aureta, in dai shine matsalar, ni zanma Hassan magana, sai dai kafi kowa sanin baka isa ka zaunar da ita a gidan nan ba, in har baso kake danka ya mata illa ba.

Kallanta yai cikin rauni yace  ba santa ne matsala ba, ni gaba daya abinda ke damuna ne matsala, n rasa a yaushe na fara santa, a yaushe naji in banganta ba bazan iya rayuwa ba, na rasa a yaushene na fara amsa mata akan duk abinda tazomin dashi.


Ummy ta kalleshi cikin mamaki tace  me kake mufi?

Ya kalleta yace  kizo mu kwanta, banajin dadin abinda mukeyi, me kike tunanin zai faru in Hassan ya ganki anan? D a nane sai dai duk duniya nafi shakkarsa akan kowa, sannan shikuma indai akanki ne ba abinda bazai yi ba.

Ummy bata musa ba ta mike sukai daki, kwanciya sukai, tace  baka fadamin matsalar ba.

Yace  gobe zan gaya miki mike faruwa wanda na kasa ganeshi.

Ummy tace  Allah yaa kaimu.

Nan sukai bacci............

Sageer kam gaba daya ya kasa bacci, daga bayama mikewa yai ya zauna akan gado ya kunna fitila yana tunani, anya bashine sillar komai ba?

Gaba daya tausayin Jalila ya hanashi rintsawa......
******

A can gidan Inna kuwa, Inna sai kiran wayar Dady take bai dauka ba, yana kallan kiranta yaki dauka, sai data kira sau hudu sannan ya daga yace  gashinan zuwa.

Ajiye wayar yai ya koma mota, dan ya gama tunanin mafitarsa, yasan kuma yanda zai buloma abinda ke faruwa dashi..........



#OneLuv=ؕ?


=??? *JALILAH* =???

Written By : *AYUSHER MUHD*
'ote me on Wattpad : *Ayusher Mohd*


? ?? *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*
? (_D home of expert and perfect writer's_=ء?)



*40*

Washegari......


Jujuya cokali kawai takeyi a cikin cup din tea din, jefi jefi tana kallansa ta kasan ido tanasan mai magana, shikuma yana zaune a kasan yanacin abincinsa kamar ba wani abu dake damunsa.

Can dai ta tattaro dauriyarta tace "hmm yaya nace......"
Kallan daya mata ne yasa ta maida bakinta ta rufe tare da kallan cup din ta cigaba da juya cokalin.

? Yana gama ci ya mike ya shiga toilet, wanka yai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login