Showing 123001 words to 126000 words out of 149705 words

Chapter 42 - Jalilah Book One Complete Hausa.doc

Ayusher   

28 Oct 2025

616

sauki haka?"

Ya sake wata dariyar, hada ido suke da wata nurse sai ya wayance ya fito daga asibitin.


?? **********


Goggo ta shiga cikin gida ta zauna, matar babban yayansu sai kallannta takeyi.

Goggo ta kalleta tace "Yaya an wuni lafiya?"
Cikin mamaki tace "Hajiya ai ban gane bane."

Goggo tace "nice Laraban Meero (haka aka dinga kiranta lokacin tana yarinta)"

Idanu ta zaro cikin mamaki tace "inalilahi wa ina ilaihi raji'un, kece?"

Nan fa ta matso ragowar matan suka baza ido, dayar matar yayan nata ma ta taho da sauri.

Maza da suka iso daga gona kowa ya shiga mamakin jin wacece.

Goggo ta kallesu bayan sun gaisa tace "Innata fa?"

Nan akai shiru kowa na kallan dan uwansa.


Jikin Goggo a sanyaye tace "batada rai?"

Babban yayansu yace "ta rasu shekara biyar da suka wuce, har ta mutu sunanki ne a bakinta."

Goggo idanunta ya ciciko, tace "Baffa fa?"

Sukace yana kwance ba lafiya yafi shekara yana fama da ciwon ko waje baya fita."

? Goggo ta kallesu nan aka shiga yi mata introducing din kowa, nan ta Nuna musu tsarabar data kawo, mamaki ne ya kamasu, ganin buhun shinkafa kwalin taliya biyu da macroni, katan din sabulun wanka guda biyar, katan din omo guda hudu, katan din sabulun wanki guda biyu, ga jarkar mangyada irin katan nan.


Nan fa aka shiga godiya da ban hakuri akan abinda aka mata, haka akai ta bata labarin yanda mahaifiyarta tai rashinta.

Goggo ta share kwallarta kafin ta shiga gun mahaifinta.

Shikam harda kukansa wajen neman yafiya agunta, yayi dana sani kara kuka ma yai a lokacin data ajiye kudi dayawa a gabansa, sannan ta fito tare da neman a rakata gidansu Abakar saboda mahaifinsa.

? Sa albarka agun Baffa har ta bar dakin, mahaifin Abakar yasha kuka daya ganta, yai ta neman yafiya shima a gunsu, ta ajiye mai kudin data kawo da katan din omo da sabulun wanka tai sallama ta fito.

Bata wani zaga gari ba saboda kafarta, sai dai dakansu mutane sukaita zuwa da wanda ya santa da wanda baisanta ba, kowa yanajin tazo kawai sai dai kaga yazo.

Haka tai ta rabasu an kudi har ta samo ta baro garin....

Zuciyarta cike da tausayi da alfahari da yanda rayuwa ta juya musu....


***********



? Yanda taga yana bacci hankali a kwance yasa ta zuba mai ido tana kallo, ko da wasa bata taba kawo rayuwarta nan gurin ba.

? Idanunta na kansa sam batasan murmushi takeyi ba, jitai ance "zan iya bude ido?"

Mamaki ne ya kamata da sauri ta dauke ido daga kansa tare da neman dankwalinta.

Ya bude idanunsa tare da sa hannunsa ta ratsinta ya sa kansa a kasan bayanta yace " angama kallan nawa?"

Tace "wai ba bacci kake ba?"

? Tai maganar tana dan juyowa kadan saboda rukun daya mata har jikinta takeji.

? Fuskarsa ya dago kamar me sanyin bacci yace " kina tashi na tashi, kawai banasan farkawa ne."

Murmushi tai tace "ga alama nan, idanka ya nuna."

Matsowa yai yasa kansa akan cinyarta yana kallanta yace "idan kara kadan?"

Yanda yai maganar ne yasata murmushi tace "a nan?"

Kai ya daga tare da rufe ido yace "kinga sai ki kalleni da kyau ba takura."


Tace "ni fa ba kallanka nai........"

Fuskarta ya nuna da yatsarsa ba tare da ya bude ido ba, tace "kasa fa?"

Bai bude ido ba yace "yau Saturday kowa na gida, Ameera ma nanan."

Tace "to........"

? Juyowa yai yasa kansa a cikinta wanda ya hanata magana, jitai har numfashinta sai daya amsa.

? Ta kalleshi idanunsa sun firfito a hankali tai murmushi.

? Hannuntantasa a cikin kansa tana mamakin rayuwa yanda ta juya musu daga ita har shi.

Kamar yasan me take tunani, dan ita ta daukama ya fara bacci sai taji yace " Jalila!"

A hankali tace "Naam!"
Yace "mu bar kasar nan."

Fuskarta dauke da mamaki tace "mubar kasar nan?"

Juyowa yai saitinta yace "Uhmm, I really want to see us alone."

Tace "nan ma ai mu kadai ne."

Sai kuma can tace "kana? nufin ka yanke hukunci?"

Idanu ya lumshe mata alamar eh sannan yace "yanzun nan!"

Tace "yanzu ka yanke?"

Yace "Umm haka kawai naga barin mu nan shikadai ne zaisa mu kebe, kinga kafin mu dawo sai na fadawa Abba a nemo mana gida."

Dariya ya bata, pillow din data daura hannunta akai shita dauka ta sa a saman fuskarsa tana dariya tace " gaskiya yaya ba kunya a harkarka, saboda haka kawai kake san tafiya?"

Pillow din ya turo yasa hannunsa a saman wuyanta ya jawota daf dashi yace "bakya tausayina Jalila?"

Tace "Tausayin me kuma?"

Ya kara marairaice fuska yace "bakya tausayawa zuciyar dake san ganinsa manne da matarsa?"

Tana dariya tace "mene?"

Yace "nikam tafiya zamuyi, Allah yasa kafin mu dawo Sageer yayi aure ya tare saman."

Jalila tana dariya tace "wato shi ya zauna kai ka gudu ko?"
Yace "a'a shima yadan dana kadan sai mu gudu dukanmu."

? Jalila ta girgiza kai tana dariya tace "ni dai gaskiya so nake na sauka kasa Allah kunya nakeji aga ban sauko ba."

Ya daga ta tare da hade fuska ya koma ya kwanta akan pillow.

Hannu tasa ta taboshi tace "fishi kai?"

Ya kalleta yace "abani cin hanci na fita ko kuma inje in nemi izinin zama da matata."

? Jalila tai dariya tace "kace me?"

Yace "mu gwada mu gani?"

Da sauri ta sumbaci kuncinsa tace "inje?"

Kai ya daga mata yana murmushi.

Ta kalleshi sannan ta fita.


Tana rufe kofa ta kalli dakin sannan ta murmusa tace "Yayah!"

Sannan ta sauka.

Kunya ta kamata dataga Ameera da Ummy sun gama aikin breakfast harsuna jerawa akan dinning cikin kunya ta karasa tace "Ummy ina kwana?"

Ummy tace "Jalila kin fito? Ai da kinyi zamanki ma Ameera anjima zata kaimuku abincinku."

Jalila da sauri ta amshi kayan hannun Ummy tace "a'a Ummy."

Ameera ta guntse dariyarta.

Jalila ta shiga maka mata harara......

Bata dade da fita ba ya mike daga kan gadon ya gyara sannan ya dau wayarsa ya sauko.

Tana kokarin hawa sama ta kirashi sai gashi.

Ummy ya gaida tana amsawa Abba ya fito daga daki ya gaisheshi.


Sageer ma ya matso suka gaisa yana cewa "jiya nikam bansan sanda ka dawo ba."

Hassan ya harareshi sannan yace "Ummy nikam a sama zanyi breakfast."

Da sauri Jalila ta kalleshi.

Ya dauke idanunsa yana kallan Abba wanda ke cewa "gaskiya ne, a basu abincinsu in yaso juma'a sa dinga saukowa."

Ummy tace "kuma hakan yafi ko saboda ma Jalila bazata sake anan ba."

Hassan ya kalli Jalila yaga yanda tai tsuru tana kallansa.

Dariya ya kamashi ya guntse ya kalli Sageer yace "Malam gauro aci abinci lafiya."

Sageer yai dariya yace "gauron ma ya kusa yin zuciya ya kama nasa."


Hassan yai sama yana dariya.

Ameera ta kalli Jalila tace "Aunty Jalila ga naku nan dama Allah yaso Ummy ta ware muku."

Ta matso kusa da Kunnenta tace "oh su yaya ba kunya."

Jalila tasa kafa ta taka ta.


#OneLuv=ؕ?
[12/30/2018, 10:06 PM] El-hajj: =??? *JALILAH* =???


Written By : *AYUSHER MUHD*
Wattpad: *Ayusher Muhd*


*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*


*68*


Tana ajiye tiren abincin ya sa hannu ya jawota ta fada jikinsa, kallansa tai tace "Yaya?"

Yace "me? Bakiso na fadi haka ba?"

Tace "taya zakace haka bayan kasan yanda su Ummy kijin dadin cin abinci dakai?"

Ajiyar zuciya yai mai sauti yace " nikaina ba haka naso ba, to amma ya zanyi? Na kasa jurewa."

Tace "ka kasa jure me?"

Jawota yai ya kara rungumeta yace "nafisan na jimu shiru."

Dagowa tai ta kalleshi tace "yaya? Nikuma tsoro nake ai."

Yace "tsoron me?"

Tace "naji ance duk ma'aurata farkon aure ne kawai miji ke nuna musu so, amma da zarar sun shekara daya, biyu zuwa uku zai canza mata, wani maganar mutunci ma ba samu zatai ba."

Yanda yake jinjina kai yana tabe baki ne yasa tace " Da gaske haka ake cewa."

Ya karkata kai yace "ohhh haka ne kenan?"

Tace "mene?"
Yace "ban taba ji ba amma yanzu da kika fada da alama na fahimta."

Kallansa tai a tsorace tace "me ka fahimta?"

Dagata yai daga jikinsa ya zauna gaban abincin da ta kawo, ya nuna mata tare da cewa "matso muci abinci, yunwa nake ji."

Kallansa tai jikinta duk yai sanyi, a hankali ta matso ta zauna tace "Yaya bakace komai ba."

Yace "me kikeso nace?"

Tace "Hmm abinda ke ranka."
Yace "bakomai a raina."

Kallansa tai tace "bakomai?"
Yace "sosai, saboda labarin rayuwar wasu can daban kika bani wanda banida hadi dasu."

Tace "yaya Goggo....."
Yace "Jalila?"

Yanda ya kirata ne yasa tace "naam."
Yace "ya sunana?"
Tace "Ya..."
Yace "ba wannan ba ya sunana?"
Tace "Hassan?"
Yace "gud, mahaifinki fa?"
"Abubakar."

Yace "toh, banaso a rayuwata dake ki dinga hadashi da rayuwar wasu da kikaji ko kika gani, koda kuwa rayuwar mahaifinki ce, ni nine, sannan ke kice, bansan mace ba, ban taba magana mai tsayi da wata mace ba bayan mahaifiyata, ko Ameera kina ganin yanda muke magana, ke kadai na sani, so Please inaso ki daukeni a yanda na daukeki, nasan haryanzu baki saki jiki dani ba wanda nasan a hankali ni zan canza wannan, amma banaso ki dinga sako rayuwar wasu a cikin tamu.
Bazan miki alkawarin rashin canzawa ba ko wani abu makamancin haka, i am a human being wanda baisan ke zai faru dashi anjima ba bare gobe, amma i will try my best to love and protect you."


Kallansa kawai takeyi batasan kwalla ta tarun mata a ido ba, sai jitai ta gangaro mata, kai ta jinjina tana sharewa tace "nagode yaya, insha Allah bazan sake ba, sannan nima zanyi kokarin cire duk wata kunya dake damuna, sannan nima i will try my best to love and protect you."

Murmushi yai sannan ya miko mata hannu, itama mikomai nata hannun tai ya jawota kusa dashi, yasa kansa akan kafadarta yace "Baby yunwa, yunwa nakeji."
Murmushi tai cikin kunya tace "yanzu zakaci abinci."

Zuba musu tai a plate, chips ne da soyayyan kwan sai farfesun kaza.

? Fork ta mikamai, kai ya girgiza mata alamar a'a tace "kace yunwa kakeji?"

Yace "sosai ma." Ya karasa yana rike ciki.

Tace "to naga kaki amsa kuma?"

Yace "hannuna ciwo." Tace "hannu? Garin ya ya?" Yanda tai maganar a rikice ta kara matsowa tana duba hannunsa ne yasashi yin wani lalausan murmushi.


? Ahhhhhhh abinda taji ya fada kenan, kallansa tai rike da hannunsa tace "Ahhhhh?"
Ya daga kai yana kara bude baki, wato shine ya sa hakalinta ya tashi? Tace "ok, ta sa fork ta debo tace Ahhh

Bude bakin yai tare da rufe ido, jin shiru ne yasa ya bude idansa ya kalleta.

Gani yai tana cin abincinta tana kallansa tana danne dariyarta.

Ya kura mata ido, tace "ohh ashe fa hannun Yaya na ciwo ko?"

Ya kara hade rai yana harararta, tace sorry na mantane yanzu ahhhh

Fizge fork din hannunta yai yace "banaso."


Murmushi tai sannan ta sa hanunsa cikin nata tace "bakaso?"

Yanda tai maganar tare da langwabar dakai ne yasa ta kashe mai jiki, ita kanta batasan me ya sameta take wannan sakalcin ba, ko d yake dama can Jalila sakaliyace agun Goggonta.

Yace "inaso."
Yanda yai maganarne ya bata dariya ta maze tace "to In baka?"

Ganin kamar zolayarsa take tasa ya zare hannunsa yace "nama daina cin abincin tare, a samun nawa."

Ya juya baya tare da jan tiren gabansa.

Dariya tai sannan ta kwantar da kanta a bayansa tace "dani yaya?"

? Idanu ya runtse dan bazai iya jurewa ba, juyowa yai ya kalleta yace "Jalila? Wato kin gama sanin lago na da alama."

Tai dariya tace "Allah yanzu zan baka Ahhh."

Bude bakin yai fuskarsa a daure ta samai tana dariya.

Kare hade rai yai yana taunawa.


************


Wani irin ihu ya saki a cikin motarsa na tsantsan farinciki, dan sai da ya zoge duka glass din motar sannan ya saki ihun tare da cewa "Kai Chairman Abubakar."

Idanu ya lumshe can ya hango sunansa a rubuce a jikin kofar office dinsa ansa *Chairman Abubakar*

Dariya ya saki tare da cewa "kai mutumin."
Tunowa yai yanda members na board din suka aminta dashi da kuma yimai alkawarin bashi matsayin Inna a jibi, zasuje company din da kansu suyi convincing din directors na cikin company din."
Wata muguwar dariya ya saki yace "kai ba sauki, kamar na janyo jibin nan haka nake ji.

Kamar ya kamata na nemi gida, dan na tabbatar matarnan tana farkawa zata nemi korata daga gidanta tunda company din na kwace.

Can kuma yace "to in ta koreni yar ta fa? Jikokinta fa?"

Dariya yai na jin dadi tare da cewa Ranka ya dade
Ina zaka?

Dariya yai sannan ya tada mota, mai makon yaje asibiti kamar yanda ya kamata kawai ya wuce gida ya shiga daki ya kwanta yana latsa waya cikin nishadi mara misaltuwa.


**************


? Cikin takaici ta wanka mata mari tace "Zaliha ba kiji me nace miki bane?"

Kallanta tai shekeke tare da sa hannunta akan kuncinta tace "shine kika mareni?"

Tace "na mareki din, dan ina yayarki sai akace duk abinda kikeso a duniya sai na miki?"

Zaliha ta kumburo fuska tace "magana daya ce na miki in har kina so in cigaba da samo miki alhazawa muna amshe kudinsu, ki tabbatar kin kamomin akalar Babban yaran Taura, dan sai na kwanta dashi na nuna masa ya kwanta da trash sannan hankalina zai dawo jikina, ba sai lalai na aureshi ba."


Aunty haushi ya kara kamata tace "dalla ni rufemin baki da zancen yaran nan, sai ki dinga wani nunawa kamar fansa zaki dauka akansa alhalin ni na fahimci so kike kawai ki ganki dashi, kudi nawa kikasa muka kashe akan yaran nan da mahaifinsa? Duk abinda muka tara kinsa ya kare a shirmen banza, maza nawa ne ke sanki? Dolene sai shi? Ko dolene sai ubansa?"


Ihu tasa mata tare da cillar da pillow din dake kan kujera kasa tace "ni dai sai shi, na kuma fada miki."

Hannu tasa ta kara kifa mata wani marin tace "duk kinsa kudina ya kare akan yaran can da ubansa, bazan iya ba, ki tattara ki koma gida inyaso sai in dauko Sariha ta zo ta zauna, dama ita ta fiki san ta taho sannan na tabbatar ita bazata dinga bijeremin ba."

Ta juya tai gaba rai a bace, ihu Zaliha ta saka cikin wani irin murya tace "Aunty Aunty!"

Tanajinta ta rufo kofar falon ta fita.

"Inkoma kasarmu? A ta ina? Kasar da bakomai a cikinta sai wahala? Ni?"


(Hala ni=??)


**************

Yanda motar gabansa ta taka burki ne yasa shima ya taka, a tsorace ya dago ya kalli motar dake gaban nasa, ganin ya fita yasashi shima ya fito daga motarsa ya nufi gaban motar.


Yarinyace wacce da kadan tafi Ameera kana kallan yanda gwiwarta ke jiki da gwiwar hannunta zakasan bige ta akai tadan fadi, kokarin mikewa ta shiga yi saboda yanda zanin jikinta ya kwaye, ga mutane harsun fara taruwa.

Juyawa yai zai koma mota yaji muryar mai motar na cewa "ungo! Dan ma tabbatar saboda ki samu kudi kika fadomin kan titi haka, ba tin yau ba dama mukasan irinku."

Juyowa yai cikin mamaki ya kalli mutumin sannan ya kalli yarinyar, wacce ko kallansa batai ba kafarta kawai take dingisawa tana neman wucewa.

? Ya sha gabanta yace "ungo tun kafin ki ha kin masifa, ko?"

Juyowa tai ta kalleshi, kamar zatai magana sai suka hada ido, rike da hannun mutumin wanda yake rike da dubu daya yai.

Ya kalleta sannan ya kalleshi yace "in zakai wulakanci sai kayi dakyau, sannan ita data fado dan ta samu kudi kana tunanin 1000 ya isheta?"


Ranta ya kara baci ta kalleshi sannan ta fara tafiyarta, itakam yau da alama batai addu'a ba ta fito daga gida...


Murya a zafafe yace "kai kuma waye?"

Nunamai motarsa yai sannan ya nuna kansa alamar mai motar ne.

***********

#Oneluv=ؕ?
[12/30/2018, 10:07 PM] El-hajj: =??? *JALILAH* =???


Written By : *AYUSHER MUHD*
Wattpad: *Ayusher Muhd*


*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*


*69*


Hannunsa ya warbar ganin yanda yarinyar ke dingisawa tana kokarin barin gurin, tausayinta ne ya kara kamashi ya koma motarsa da sauri ya hau ya tadata, gani yai tana kokarin yin wata kwana da sauri yaja motar zuwa inda take, tana shiga kwanar shi kuma yana saurin ratsa gun, horn ya mata, tsayawa tai tare da kallan motar, ganin layin bawai mai girma sosai bane yasa ta matsa tana tunanin duk gurin nan ya mai kadan?

? Ta gefenta ya matso sannan ya zuge daya glass din motar saitinta yace "are u okay?"

Kallansa tai yanzu kam ta ganeshi, kai ta dagamai alamar eh sannan ta fara neman juyawa.

"shigo na karasa dake."

Kallan mamaki tamai tace "ina?"

Yace "yace bakya tunanin ya kamata kije chemist?"

Shiru tai tana kallansa kafin tace "nagode na kusa isa gida."

Ya kalleta yace "ina ne gidan? Dan da alama nidin ne bakyasan na kaiki kikacemin kinzo gida."

? Hannu ta daga ta nuna mai karshen layin kawai tace anan daga can.

Yace "anan? Daga can? Wannan wani irin kwatanceni?"
Sannan bakiga zaninki ya samu matsala ba? Ba wai saboda wani abu ba ki duba yanayinki kizo na karasa dake."

Kamar zatai magana sai kuma naga ta kalli jikinta, kafin a hankali tasa hannu ta bude motar, shiga tai ta zauna tare da yin shiru.

? Yace "mu mike?"
Kai tadaga mai kawai, nan ya mike layin, yace "sai ina?"
Tace "hagu zamuyi."

Yana juyawa ya ga wani chemist, kallanta yai sannan ya gangara yai parking yace "muje."

Kallan chemist din tai tace "ba sai munje ba inmunje gida zan gyara dakaina."

Yai murmushi yace "Sry likita amma yanzu kam sai munje."

Haka ta fito suka shiga, mai chemist din na ganinta yace "Maimuna kece?"

Kai kawai ta daga sannan ta kalleshi tace "Kairiyya fa?"

Yace "tana ciki."

Kallan Sageer tai tace "da ka barni anan ma in nagama sai na wuce gida."

Yace "shiga ki gama ina jiranki."

Mai chemist din ne yai dariya yace "wooo Maimuna yau kece da saurayi, lalai yau akwai abin mamaki."

Kallansa kawai tai ta shiga ciki, ganin mutum na jiranta yasa ta azalzala Kairiya ta mata dressing din da sauri ta fito, dan itakam nauyi ya daura mata na jiranta dayai.

Tana fitowa ta ganshi a tsaye a jikin mota da alama waya yakeyi, tsayawa tai tana tunanin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login