Showing 108001 words to 111000 words out of 149705 words

Chapter 37 - Jalilah Book One Complete Hausa.doc

Ayusher   

28 Oct 2025

632

amsa sallamarsa ba, yasan Jalila na kasa.

Hassan na kwance yana tunanin abinda ke faruwa tsakanin Sageer da Jalila yaji shigowar mutum.

Sageer ya matso ya masa bayani, ai bai bi takan Sageer ba naga ya sauko da sauri ya dau key din mota ya fita "Ummy ina zuwa" abinda ya fada mata kenan a sanda ya ganta a zaune.



Kafin ta amsa masa yafice, tad'anji zanyi aranta, tunda yau ga Hassan zai fita harda fad'in yana zuwa, tamance shrkarun daya d'auka bai Sanar mata zai fitaba.

Sageer na saukowa yaga har ya ja motarsa ya fita, motarsa shima ya shiga yana tunani, ya bishi ne?



Can kawai yaja motar sa shima ya fita.

***********


"Alhajina kayi shiru, kobakayi murna da ganina baneba?".

Abba ya had'iyi yawu da k'yar, kafin yace, " bahaka baneba zaliha, kawai nayi mamaki. ganinkine, musamman idan anyi la'akari da safiyane, dolene kayi mamakin ganin Wanda yake Abuja a Kano a irin wannan lokacin".

Cikin salonta Na yaudara tace, "Alhajina kamanta da maganarnan ta Malam ba haushe dayace garin masoyi baya nisa........


.......baya nisa kam, balle idan kaci karo da ballagazar mace, wadda batasan muhimmancin dunk'ulalliyar zuri'a ba, narasa wane rukuni zan sakaki acikin jinsin d'an adam....."

Daga Abba har Zaliha a rikice suka juyo suna kallonsa.

Bakowa baneba face Hassan.

Yauce rana tafarko daya taba shigowa company d'in Abba ballema office d'insa, dukda yasan inda company d'in yake, amma yanzuma bisa jagorancin Sectary d'in Abba yazo, yanaji ajikinsa dama wataran sai zaliha tabiyo sawun Abba tunda batasamu yanda take soba.
Sai gashi kuwa, tunkafin ayi nisa saigata tazo d'in, hasashensa yazama gaskiya.

Bak'aramin tashin hankali Abba yashigaba, hakama Zaliha dake zaune, dan sarai tagane Hassan d'in, shine taga hotonsa a wayar Taura shida k'aninsa, tun ama hoton ta shaida wannan guy d'in bazaiyi mutunciba, balle tundaga waya dashi Taura ya dauke mata kafa.

Hassan yakatse mata tunani da fad'in "Bakiji gargad'in dana miki bane ko kuwa wanda na miki ne ya miki kadan?

Zaliha ta kalleshi idanunta suka firfito, a hankali ya fara takowa har inda take yace "zaki sauko daga inda kike zaune ko inzo in saukeki?"

Da sauri ta cire hannunta daga jikin Taura ta sauko daga kan desk din, wani kazamin kallo ya mata yace " fita fa? Zaki iyayi ko sai na jaki daga nan har waje?"

Kallan Taura tai tace "MyT?"

? Taura ya kalleta ya dake yace "ke karki kara cemin wani urT agidan uban wa na zama naki?"

Juyowa tai jiki a sanyaye ta fara takowa, kusa dashi tazo ta tsaya tana kallansa, tare da dan girgiza kirjinta.

? Tsaki yai yana kallanta yace "kina tunani wai kin cika mace a hakan?"

Tace "mene?"

Bai bata amsa ba yace "kinsan wani suna ake kiran mata irinku?"

Tace "mene?"

Nan ma bai bata amsa ba yace "kinsan a wani jere nake sa mata irinku?"

Haushi ya kamata tace "mene?"
Yace "Trash! Get out."

? Idanunta ne suka firfito fuskarta ta nuna tsananin bacin rai ta kalleshi tace "mene?"

Yace "bakyajin turanci?"

Kallansa ta sakeyi cikin wani yanayi na tsananin bacin rai, cikin mumunan bacin rai ta fito.

? A waje taga Sageer a tsaye a jikin kofa, kallansa tai yai dariya har tayi gaba yace "ke Trash kin manta jakarki."

Yafada tare da kallan jakarta dake kan desk.

Dawowa tai ko kunya ta dauka ta fita da sauri.


Sageer ya bita da kallon mugunta, ya kalli Hassan yace "kai Yaya baka zafafa ba?"

Hassan yace "kaima ka zafaffa ai wai ke Trash...."

Abba ne ya hade fuska yana kallansu yace " wato dai kune masu kula dani ko? Sai a fadamin wanene ma ya samar daku?"

Hassan ya kalli Sageer, da sauri Sageer ya juya kai yace "Abba na manta inada appointment" dariya suka saka a tare hardashi Abban, Abba yace "amma yanzu ai bazata sake dawowa ba ko? Sageer yace "inta dawoma tana da mai maganinta....

? Suka kara yin dariya.....

Abba yace kuyi alwala muje masallaci sallar la'asar tare.

? Hassan ya kalleshi, Abba yace "let us try kaji?"

Ya daga kai alamar to.

Haka suka yi alwala suka zauna a office din Abba macema Sageer ya daure ya fara aiki anan, Hassan na taya Abba har la'asar ta karasa, Abba ya kalli Hassan yace "muje?"

Atare suka fito su uku abin sha'awa, basuga motar Zaliha ba agun da alama ta bar gun.

Masallacin suka nufa, tsayawa yai yana kallan yanda mutane ke ta shiga ciki, ya kalli Abba.

Abba yasa hannu ya riko hannunsa sannan ya riko hannun Sageer yace "gamunan mu uku, ka cire komai a ranka kawai kasa a ranka gun bautawa Allah zaka, sannan gamu a kusa dakai."

Hassan yai murmushi suka nufi masallacin, daurewa kawai yake dan zuciyarsa sai bugawa take da sauri da sauri.


? A bakin kofar suka tsaya sukai addu'a sannan suka shiga.

? Haka suka shiga, suna shiga ciki suka hau jam'i a tsakiya suka sakashi, liman yaja sallah.

? Suna idarwa Abba ya kalleshi, wasu zafaffan kwalla ne suka shiga neman zubomai a lokacin daya daga hannu yana rokon Allah, yaushe rabo? Addu'a ya shiga yi har bai san sanda hawaye ya zubo mai ba.

Sageer ma sai daya zubo da kwalla saboda tsananin tausayi.

? Ya dade yanata addu'oi kafin su fito, dan sukan shi suka tsaya jira, dukansu sai tausayinsa yakeyi.

^**********

Dady ne ya kalli kofar gidan, kwanansa biyu kenan yana zuwa yana komawa dan shifa gaskiya ya kasa sa kafa cikin gidan, ko dai wayau zaiyi ya fara zuwa gidan da Goggo take? Ita yasan mai sauki ce inyaso sai tazo nan da kanta ta basu hakuri.....


? Juyawa yai da motar kamar zai koma sai ga motarsu Abba.

? Kallansu yai sun shiga ciki, sun hada ido da Hassan amma sai ya dauke kai, da kallan takaici ya bishi yace "wannan dan iskan yaran....."

Suna shiga shima ya shiga da motarsa.

? Su Abba na fitowa shima ya fito da sauri yace "Ranka ya dade!"

Abba ya juyo ya kalleshi, murmushi yai yace "Ah Alhaji kai ne?"

Dady ya matso yana kallan Sageer da Hassan da sukai kamar basu ganshi ba.

? Hassan ya kalleshi bayan ya karaso yace "Ina wuni?"

Dady ya washe baki yace "Hassan an wuni lafiya?"


? Hassan yace "lafiya."

Ya wuce ciki, Sageer ma yace "Ina Wuni?"

Nan ma yace "malam Sageer ko?"

Sageer yace "eh."

Ciki yai Abba yace "bismillah!"

Nan suka shiga ciki...........


? Falonsa ya kaishi ya zauna sai wani washe baki yakeyi, yana cewa "wlh na dade inasan nazo."

Abba ya kalleshi baice komai ba.....

Shiru sukai dan Abba kam shikanshi haushinshi yakeji, ai koda laifin su Inna da Mumy to tabbas laifinsa yafi yawa, dan a matsayin sa na uba, miji abinda ya aikata shi kansa yayi alawadar dashi, tun ma daga auran mahaifiyar Jalila zuwa zaman da sukai......

Dady ya kalli Abba jiki a sanyaye yace "Ranka ya dade nace........"


? Abba ya kalleshi, Dady yanda yaga ya kalleshi ya daure yadanyi shiru......



**********

Hassan na shiga ya kalli kitchen, Ameera ce ta fito rike da kofi tana shan abu, tana ganinshi ta matso tace "Yaya."

Kallanta yai yace "baki tafi islamiya ba?"

Tace "ai yau alhamis."

Yace "okay."
Ya wuce sama, da sauri ta koma kitchen ta taba Jalila tace "Aunty mai sanyin ya dawo...."

Jalila ta juyo ta taka kafarta, Ameera ta saki yar kara Jalila tace "bari na fadamai wai mai sanyi."


Ameera tace "wayyo Allah na ki rufamun asiri."

Jalila tana dariya ta fito, da sauri ta hau sama tana murmushi, ina yaje dazu?

Tana shiga ta taraddashi yana cire kaya, da sauri ta juya baya tana cewa "yaya ashe ka dawo."

Yana cire kayan amma kallanta yakeyi, yace "nemana kike?"

Juyowa tai ta manta sam da abinda yakeyi tace " naga......."

Ganin ya cire rigar tasa gaba daya tai sauri sake juyawa, murmushi yai yana kallanta, Jalila menene tsakaninki da Sageer? Me ya faru a baya? Anya ya dace nama Sageer haka?

Tambayoyin da yakeji kamar ya yimata kenan, ta juyo ita kuka da sauri tace "Yaya kasan me?"

Kallanta yai, ta kara kallan jikinsa da sauri ta sa hannu ta rufe fuskarta.

Murmushi yai sannan yace "ki hadiye maganarku tunda kunyata kikeyi, in kuma so kike in matso to."

Tace "ka matso ina?"

Takowa yai yazo inda take, idanu ta bude da sauri, ya sa hannu ya lankayo cikinta yace " haka kikeso?"


Idanu ta zaro tana kallansa tace "yaya wlh ni......."

Shiru yai yanayin fuskarsa ne ya dan canza, murmushi yai sannan ya saketa yace "Mahaifinki fa yazo."

Tace "yaushe?"

Yace " yanzu ya shigo, da alama yazo ganin yar sa ne."

Tace "hmm yadai zo abinda yazo yi, ko an turoshi."

Hassan ya kalleta kamar zaiyi magana sai ya fasa, cikin toilet ya shiga ya rifo kofar.

Da kallo ta bishi tare da yin ajiyar zuciya.....
Itakam batasan ya akai take tsananin san ganinta da Hassan haka ba, lalai yanzu ta fahimci kaunarshi ta fara yin nisa a ranta.

Dolene ta je gun Goggo ta fada mata dan itakam yanzu tanajin Hassan har ranta...........


?

#OneLuv=ؕ?
[12/7, 10:12 PM] El-hajj: *_=???JALILAH!!=???_*

Written By : *AYUSHER MUHD*
'ote me on wattpad : *Ayusher Mohd*


*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
? (_D home of expert and perfect writer's_=ء?)

_Wannan shafin sadaukarwa ce gareku yan Sparkling Son Sorians=ؖ? ina godiya da kaunar da kukema min da littafin nan=ؕ?Luv u all....._


*60*


Juyowa tai ta fito daga dakin fuskarta dauke da murmushi.

Shikuwa Hassan a toilet ruwa mai dumi ya sakar ma kansa yana ta zuba a jikinsa, Jalilah! Sageer! Wani irin so Sageer yakema JalilahA? Wani irin so Jalila takema Sageer? Abinda yaketamai yawo kenan a kwakwalwar kansa, duk yanda ruwan ke zuba a jikinshi baiyi tunanin lafiyarsa Wba.
I jm. J
Ya dade a haka kafin ya saba jikinsa ya fito, ya zura doguwar riga jallabiya ya zauna akan kujera yana tunane tunane.

Jalia kam tana sauka Ummy ta fito daga falon cxAbban nc, kallanta tai tace  kun gaisa Wn

Tace  da wa?
Ummy tace  mahaifin.......
Yanayin fuskarta ne ya canza wanda yasa Ummy kallanta tace  ki shiga yana ciki. Jalila tace to sannan ta nufi ciki.

Abba kuwa a falo ya hade fuska yana sauraren Dady dakemai zancen banza, ya cika yayi fam.

Dady kuwa tsabar hauka baima kula ba ya dauka fahimtarsa Abba yakeyi.

Ya kara kallan Abba yace  gaba daya haka rayuwata take a cikin wannan gidan nasu, komai sai abinda suka tsara, basu dauke da girma ba duk kuwa da nine mahaifin yaran.

Ya kara neman marairaicewa zai kara wani rainin hankalin Ummy ta shigo falon dauke da ruwa da juice.
Wannan dalilin ne yasa ta yin shiru, tana kallan yanayin Abba ta fahimci baya jin dadin hirar, sai tai sa a kuwa tana fitowa sai ga Jalila.


Dady ya kalleshi ya sake marairaicewa yace  a koda yaushe sai sun yanke hukunci nake sani, sannan ban isa na kawo nawa uzurin........


Sallamar Jalila ce ta katseshi, haushi ya kara kamashi.

Abba kam yana ganin Jalila ya mike tsaye yace  bari na barku ku tattauna.
Dady ya mike da sauri yana cewa  Danka ya dade......
Ai Abba bai jira cigabansa ba yai waje, yana fita yaja wani dogon tsaki ya kalli Ummy yace  wlh dabadan mahaifin Jalila bane da wlh mutumun nan... sai kuma yai kwafa.

Ummy tai daria tace  ni ina kallanka nasan ha labari.
Ya kalli kofar yace  mutum na kara banzatar da kansa da wulakanta kansa saboda abin duniya?

Dady kallan Jalila yai bayan ta shigo ta tsugunnadaga can bakin kofa.

Yace  Jalila! Ya da zama daga nan? Nine fa mahaifinki, yanzu in wani ya shigo ya ganmu ai dauka zaiyi wani abin nake miki, taso dan Allah.

Kallan mamaki tamai, sannan ta mike ta taso, zaka tai daga gefensa kadan matso da jikinsa inda take, yace  Jalilah!

Dagowa tai ta kalleshi sannan ta gaisheshi, ya amsa fuska a sake kamar wanda akayima wani gagarumin albishir, Dady ya kara sakin fuska yace  ya jikin Goggon taki?

Kallansa ta sakeyi tace  da sauki.

Yace  Jalilah!
Ta kalleshi sai dai fuskarta ba a sake ba, tace  naam

Yace  Jalila ni mahaifinki ne wanda nine na haifeki, nafi kowa sanin zafinki da darajarki, koda duk mutanen duniya zasu kike wallahi ni bazan taba gudarki ba.

Jalila batasan sanda ta juyo ta kalleshi ba cikin mamaki take kallansa.

Dady yace  ki dainamin kallan tantama sai dai nidin da gaske nine na haifeki, jinin jikinki daga jikina yake, amma nikam Jalilah kinji wani abu na harkar company dinmu a nan gidan?

Yanzu kam zargin da take ta gama tabbatarma kanta, ta daure tace  kamar name kenan?

Dady ko kunya yace  dama inata tunani ne ko da yanda za ai tunda dai yanzu kudin sirikanki ne gaba daya yanzu yake tafiya da company din me zai hana ki taimaka ki sanar dasu a bani company din, ni nafi kowa sanin darajarsa, lokacin kankani zan maida musu kudin su, na tabbatar bazan taba basu kunya ba.

Jalila kallan mamaki kawai takemai, baijira tama kaiwa kwakwalwarta amsar da zata fadamai ba taji yace  Jalila har zuciyata banasan rabuwa da mahaifiyarki, in har suka takura sai na bar musu gidan kawai, muzo muyi rayuwarmu daga ni sai mahaifiyarki, sai ke inkinzo.

Jalila yanzu kam ta kai matuka gun tunzura wato itace kuka mai dadin hawa kenan itada mahaifiyarta, shiyasa yazo mata da wannan zancen?


Ta kalleshi ta tuno kalaman Hassan tace  Dama ko da wasa nasan wallahi Dady bazaka taba zuwa saboda ni ba, ko goggo.

Ya kalleta yace  bangane ba?

Tace  yanzu Dady wani mahaifine zaiyiwa matarsa haka? Wani mahaifine zai nemi saida yar sa amma daga baya ya dawo ya nemi kara saida nasa mutunci?

Cikin tsananin bacin rai yace  Jalilah? Bakida hankali? Ni kike.......... sai kuma ya canza tone din maganarsa yace  Nine na haifeki ba wani ba, nine jininki.

Hawaye ne ya zubo mata tace  jini? Dady sai yanzu kasan jini? Sanda ni da mahaifiyata muke kuntata muke neman tallafinka, Da????? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? 
dy kana ina? Kana ina lokacin da.........

Hawayene yacikarfinta, ta kasa karasawa, Dady ya turzuko yace  bakin ciki kikemin? Bakin ciki kikeyi zaki taimakeni?

Jalila ta kalleshi cikin takaici tace  bakin ciki kamar ya?

Yace  inba bakin ciki ki...........

Bakin ciki take maka, ko dole ne dan ka haifeta sai ya zama dolene duk wani abu daka zarta mata sai ta bishi?

Juyowa yai da sauri, saboda muryar dayaji, a tsorace ya mike tsaye ya kalleshi.

Hassan wanda har ya zauna yai tunanin kamar ya dace yazo ya gaida shi, yana tsaye Dady ya fara mata zancen karshe da amsar data bashi, dan dama yana fitowa daga wanka riga ya zura kawai ya sauko.


Dady ya kalleshi yace  Hassan ba.......
Hassan yai saurin cewa  bansan me ka ke nema a gunta ba, na dauka bayan neman saida ita dakai bakada idan neman wani abu daga gunta, amma yanzu na gane duk ba haka bane, tun farko zuciyarka dama ba komai a ciki sai tsantsar san kai, in ba kanka ba banaji akwai abinda kakeso a ciki.

Dady ya fara kokarin yin magana, Hassan ya matso ya kama hannun Jalila yabar falon da ita.

Dady ya tsaya sakato, cikin kunar rai.


Hassan kam janta kawau yakeyi, ya matse mata hannu har sai da suka shiga daki, ransa ya gama baci ya kalleta yace  sau nawa zance ki zama mai confidence?

Kanta ta karkatar tana kallansa, a hankali ta saki murmushi tare dacewa  Kasan dazu harda hawaye na? Amma kana zuwa falon naji sun dauke.

Kallanta ya sakeyi fuskarsa a hade yace  ina tambayarki abu daban kina ban wata amsar.

Tace  Yaya, me yasa inkaga ana wulakantani baka iyayin shirun? Ko wanene kuwa?

Kallanta yai kamar zaiyi magana sai ya saketa, juyawa yai zai fita ma daga dakin.

Da sauri ta riko hannunsa daya saketa dashi, tsayawa yai sai dai bai juyoba tace  Yaya.

Juyowa yai yanzu ya kalleta idanunsa sunyi jaa, Jalila ya zanyi da kaunarki? Menene tsakaninki da Sageer?

Kallansa tai tace  me kake tunani?

Kallanta yai sannan ya girgiza kansa alamar a a, zame hannunsa yai ya juya ciki me makon ya fita, jitai yace  yau munje masallaci da Abba.

Cikin tsananin zumudi ta matso kusa dashi, shi kuma baisani ba ya juyo tare da takowa, bugar kirjinsa tai tsayawa sukai a haka, a hankali ta dago ta kalleshi, idanunta sun canza.

Shima kallanta yai cikin wani yanayi, murmushi ta sakar mai sannan tace  dan Allah? Tayaya?

Idanu kawai ya kura mata kafin yace  tare da Abba da Sageer.

Cikin jin dadi batasan sanda tasa hannu ta zagayo dashi ta cikinsa ba ta rungumeshi, tace  naji dadi yaya Alhamdulila.
Wani abu ne ya shiga ratsashi kafin yace  Jalilah?

Yanda ya kira sunan nata ne yasa gabanta faduwa.
yace  menene ya faru tsakaninki da Sageer a baya?

Gabanta ne ya fadi da sauri ta sakeshi tare da kallansa, zuciyarta na bugawa da sauri da sauri.

Tace  naam?

Kallanta yai yana shirin yin magana...........
Www

#OneLuv=ؕ?
[12/7, 10:12 PM] El-hajj: *_=???JALILAH!!=???_*

Written By : *AYUSHER MUHD*
'ote me on wattpad : *Ayusher Mohd*


*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
? (_D home of expert and perfect writer's_=ء?)

_Ga taku na musamman 'yan JALILAH NOVEL, D QUEEN BEE & AYUSHER FANS CLUB._
_Wannan shafin sadaukarwace gareku gaba daya, ina godiya sosai da kauna=ؕ?OneLuv_



*61*


? Kallansa tai cikin tsananin tsoro idanunta suka firfito cikin tsananin mamaki, daurewa tai tace "Yaya......."

Kallanta yai bakinsa na san magana amma ya kasa, idanu kawai ya kura mata, sai dai shikam a gunsa yaga rashin gaskiya karara a bayanne a fuskarta, murmushi yai wanda gaba daya inka shakeshi bazai ce ya iya irinshi ba, sannan bazaice ma yasan manufarsa ba.

? Juyawa yai kawai ya koma hanyar waje, Jalila kam gaba daya ta kasa furta komai, saboda tambayar tazo

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login