Showing 48001 words to 51000 words out of 149705 words

Chapter 17 - Jalilah Book One Complete Hausa.doc

Ayusher   

28 Oct 2025

640

ta sunkuyar dakai, Mumy tace " Ga tanan mun barmuku amana."

Amana? Abinda ya darsuna zuciyar Jalila kenan, su basu riketa amana ba shine suke bada ita wai amana?
Ummy taji tace "ai Jalila diyace agurina, insha Allahu yanda zan rike dan cikina haka zan riketa."

Inna tace "mun gode sosai, Allah yabar zumunci, amma Taura fa?"
Ummy tace " yana Abuja yau dai muke sa ransa."

Sannan ta kalli Jalila tace "ki daina kuka dan Allah."
Jalila ta daga kai tana share hawayenta.

Haka suka fito Ummy ta mikoma Jalila leda tace " ki basu."
Jalila ta amsa tama Ummy godiya.

Sai da suka shiga mota sannan tamikama Mumy tace "tace gashi inji Ummy."
Inna ta kalleta tace " ki tabbatar kinji abinda na fada miki."

? Jalila batace komai ba har motarsu, ta fita daga gidan, wasu zafafan hawaye ne suka zubo mata.

Komawa cikin gida tai, wucewa dakinta tai kawai ta zauna tana kuka.
Ummy ce ta shigo dakin, itakanta Ummy tun jiya hankalinta ba'a kwance yake ba ta nemi number Abba harta gaji, yanzu kuwa bama ta shiga gaba daya.

Hannun Jalila ta kamo, tace "ya isa haka nan, insha Allahu bazakiyi dana sanin auranki cikin zuri'ata ba, Hassan na cikin wani yanayi ne sai dai ba haka Allah ya halliceshi ba, lalurace ta afkomai shekarun baya da suka wuce wanda muke addu'ar neman mai lafiya, da taimakon ki."

Jalila ta kalli Ummy, Ummy tai murmushi tace "jiya a kasa kika kwana?"
Jalila cikin mamaki tace "ya akai ki...." sai kuma tai shiru, Ummy tai murmushi tace " ya miki magana?"
Jalila tace "hmm amma baifi sau hudu ba."
Tace "Ba laifi dan banyi tunanin ma zai kula ki ba kwata kwata."

Shiru tadanyi kafin ta kara riko hannun Jalila cikin murya mai rauni da tausayi tace "Jalila ki taimakeni."
Jalila ta kalleta jiki a sanyaye, tace "Jalila ki taimakeni gun ceto Hassan daga halin da yake ciki."

Jalila tai shiru sai kallanta da takeyi, Ummy tace "Kiyi hakuri da duk abinda zai miki ma tabbatar wata rana zakiyi mamakin shi"

Jalila ta share kwallarta tace "Insha Allahu Ummy."
Ummy ta jinjina kai cikin jin dadi tace "Jalila nagode sosai, sannan karki bari ya wulakantaki, inya miki ba daidai ba ki fito ki fadamai, hakan ne zaisa ya saki jiki dake."
Jalila tai shiru, Ummy tace "Sannan inaso duk wani abu da kikeso ko ya dameki ki sanar dani, inaso mu zama daya ni dake, yanda na dauki Ameera haka na daukeki, kema inaso ki daukeni a matsayin mahaifiyarki...."

? Kalmar mahaifiya itace ta sa jikinta yin sanyi, a ranta tace Goggo kina ina????

Ummy ce ta mike sannan tace " bari naje lokacin abincin rana yayi."
Jalila ta mike da sauri tace "bari inyi abincin Ummy."

Ummy tace "ah hb? Daga yin aure sai girki?"

Jalila tace " dan Allah ki barni nayi."
Ummy tace "muje muyi tare to, dan ina tunani Abbansu yau zai dawo."

Haka suka sauko kasa abin sha'awa, sai dai zuciyar Jalila ciki take da tunani wanda take? kokarin? nemo ma kanta mafita."




#OneLuv=ؕ?

=??? *JALILAH* =???

Written By : *AYUSHER MUHD*
Wattpad: *Ayusher Muhd*


*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*

_ "There are three constants in life...change, choice and principles." -Stephen Covey_

? (_D home of expert and perfect writer's_=ء?)


*29*


?? Abba suna shigowa garin kano yacema driver dinsa su wuce gidansa na governor road, driver din yayi mamaki dan Abba ya dade bai ko leka gidan ba, ko yazoma sai dai yai abu minti kadan ya fita.
Yau kam suna isa ya shiga ciki ya kwanta a falonsa, hannunsa yasa asaman goshinsa yana tunani.

Mamman driver ya juya ya fita da mota, yana kokarin shiga layinsu shi kuma lokacin ne Hassan ya fito shima.
Ganin motar Abba yasa ya danyi parking, Maman ya bude motar da sauri ya matso jikin window din da yake zaune, Hassan ya zuge glass din sannan ya kalleshi.
Mamman ya gaisheshi, bai amsa ba yace "Ina Abban?"
Mamman yai shiru kafin yace "Yallabai na gidansa na governor road."
Kallan mamaki yamai yace " me yake acan?"
Yace "ban sani ba wlh, kawai cewa yai in kaishe."
Hassan ya tada motarsa yai gaba, direct gidan ya wuce ya shiga ciki.

? Kofar falon yai knocking sannan ya tura ta, Abba me kwanc akan doguwar kujerar dake falon, shima Abban jin motsin kofa yasa ya bude idanunsa.
Hassan na tsaye a jikin kofar yana kallansa, Abba ya kalli Hassan sannan ya mike zaune yace "Hassan?"

Hassan yana daga jikin kofar yace "me kake anan daga shigowarka gari?"

Abba yai ajiyar zuciya yace "kawai!"
Hassan yace "kawai? Taya Abba zaka taho nan bayan kasan Ummy dole tana jiranka? Ai tunda kake tafiya koda bana kula na tabbatar baka taba yin haka ba."

Abba ya mike tsaye ya tako zuwa inda yake yasa hannu daya kan kafadarsa yace " kai fa?"
Hassan yace "me?"
Abbba yace "naji ni wannan karan ne kadai na tabayin haka kaifa? Kana kula da taka matar?"

Hassan kallan mamaki yamai fuskarshi cike da mamaki yace " ban gane ba? Abba ya muna maganar Ummy kana zancen wata?"

Abba yai murmushi yace "kai namiji ne kafin d'a na yanda nima nake namiji kafin na zama mahaifinka."

Yanzu kam kallan zargi Hassan yama Abbansa yace "mekake nufi Abba?"

Abba ya girgiza kai yace "nima bansani ba, kawai dai sanar dakai nai abinda nakeji."

Hassan ya kalleshi baice komai ba, kawai ya juya zai fita.
Abba yace "sai ka maidani gida koba d'aukata kazoyi ka kaima mahaifiyarka ba? Dama kai a rayuwarka damuwarta ita kadaice abinda ka sani."

Hassan ya kalleshi kawai sannan ya juya ya shiga motar sa, zama yai yana tunanin kalaman Abba, me yake nufi? Fada sukai da Ummy? Shifa a duniya ran Ummynsa ne kadai bayasan yaga ya baci.
Yana zaune sai ga Abban ya bude motarsa ya shiga gefensa.

Hassan baice komai ba yaja suka fara tafiya..........


? Su Ummy na kitchen itada Jalila suna aiki, Ameera ta tafi gidan Aunty Nana kai sako, Ummy sai mamakin kwarewa da Jalila tai a gunki take, wanda haryasa tace mata "Jalila nayi mamakin yanda kika iya girki a shekarunki."

Jalila tai murmushi tace "ai kullum ni nake abinci a gida, daga na safe, na rana har na dare."
Ummy tace "makarantar fa?"
Jalila tace "ina zuwa."
Ummy ta kalleta cikin jindadi sannan suka cigaba, suna cikin aikin sukaji muryar Abba yace "Amarya da kanki?"

A tare suka juyo, Ummy ta kalleshi cikin kulawa sannan ta taho inda yake, Jalila kuwa sunkuyar dakai cikin kunya.

Ummy ta karaso inda yake tace "Sannu da zuwa."
Murmushi ya mata yace " yauwa."
Sannan ya juya, Jalila ce ta juyo, hada ido sukai da Hassan wanda batama san tare suka shigo ba sai yanzu, kallanta yai sannan ya dauke idonsa daga kanta.

Itakuwa kura mai ido tai zuciyarta na raya mata meke damunshi? A haka dai gashi garau sai ta tuno. Abinda yai jiya, tace da daddare kuma sai ya rikide? Ko inyai bacci?

? Alamar kamawar dataji ne yasa tai saurin kallan tukunyar sannan ta cigaba da girkinta.
Shikuwa Hassan sai dayaje zai hau sama sannan ya sake juyowa ya kalleta, ya suka kare da mutanen dazu?
Tsaki yai sannan yace "meye damuwata?"
Sannan yahau sama.

? Dakinsa ya shiga kawai ya zauna akan gado.

? Ummy kuwa a daki ta kalli Abba da ya zauna akan kujera tace "gajiya ko?"
Ya kalleta yace "a gajiye nake tilis naje gidana na governor road in huta danki ya taso ni."
Tace "kamar ya?"

Ya mike yana balle botiran jikin rigarsa yana cewa " bari nai wanka."

Rigarsa ya cire ya shiga toilet da kallo ta bishi, danta? Hassan kenan dan Sagir tare suka fita da Ameera.

? A iya saninta Hassan kuma kamar abin da wuya, mikewa tai ta fito ta nufi kitchen.

Jalila ta kalla tace "ko zaki kai mai abincin safe? Banaji ya karya."
Jalila tace "Ummy azahar fa?"
Ummy tai murmushi tace "haka yake, ni kaina ina mamakin yanda yake tauyewa cikinsa hakkinsa, kamar bai san darajarsa ba."

Jalila tai shiru tana tunanin Goggonta wacce kullum take mata fada akan cin abinci, ashe ba ita kadai bace ga namijima da girmansa ana fama.

Ummy ta kalleta tace "me kike tunani?"
Jalila ta girgiza kai sannan ta nufi sama, a hankali ta tura kofar, sannan ta leko kanta.

Yana tsaye jikin madubi daga shi sai dan towel, da sauri ta maida kofar ta rufe shi kuwa yana tsaye yana kallanta.

Tana rufewa tai ajiyar zuciya tare dasa hannunta akan kirjinta tana maida numfashi, meye hakan? Taya katan namiji zai hau cire kaya haka?

Kara tura kofar tai tana tunanin ai dole ya sa riga tunda dai yaga tana neman shigowa, gani tai ba kowa a dakin, baki ta tabe sannan ta shiga ciki tana cewa dole ai yaji kunya ya shige toilet.


Motsi taji a bayanta ta juya da sauru bayanta, yanda yake dazu haka yake yana neman abu a cikin drawer, idanu ta zaro sannan tasa hannu ta rufe idanta da sauri.

Shaver zai dauka yana ganinta ya dauka yazo ya wuce kamar baisan da mutum agun ba, toilet ya bude ya shiga.

? Jin karar rufe kofa yasa ta bude idanunta a hankali sannan ta kara sakin ajiyar zuciya tana cewa "Woah! Kamar bai ganni ba?"

? Kallan kofar toilet din tai sannan ta fito, ta sanarma Ummy, suna kammala girkin Ummy ta zuba a kula ta bata tace "ki hau muku dashi sama, Jalila ta dauka ta hau sama, itakam batasan hawa saman nan kwata kwata."

? Tana shiga ta taraddashi yana ninke sallaya, ya ajiye sannan ya kwanta tare da dauko littafin da yake karantawa.

? Abincin a ajiye ta dibi nata dan kadan ta fito falo.

Yau gidan shiru kamar ba mutane, Ameera da Sagir basa nan, Ummy na daki ita da Abba shima waccan yana daki, sai ita kadai a falo.

Ummy kam ta kula mijin nata bayasan dogon magana, da alama akwai abinda ke damunsa, haka ta fito daga dakin ta zauna a falo itama.


? Da daddare kuwa banda juyi ba abinda takeyi, abinda ya faru dazu da safe shine ke damunta, taya zasu nemi ita da kanta ta wulakanta Goggonta? Matar da batasan so ba a rayuwarta? Matar da duk duniya ita kadai ke santa? Ita kadai ta damu da ita? Ita kadai ce gatanta?

Hawaye ne ya shiga zubo mata, wajen karfe daya ta mike ta zauna kawaj ta fara kuka, shikam duk abinda takeyi yan jinta, dan shi sam baya iya bacci in ana mutsu mutsu a kusa dashi.

? Jin yanda take kuka ne yasa shi mikewa zaune, fitilar gefen gado dake dakin ya kunna.

Da sauri ta koma ta kwanta tana share hawayenta.
Kallanta yai yace " inkinsan kuka zakiyi ki fitarmin daga daki, dan banga dalilin da zaisa a hanani bacci a daki na ba."

Jalila ta dan turo baki wasu hawayen suka zubo mata, Hassan ya kashe fitilar sannan ya kwanta, mikewa tai tana neman fita, dayake dakin duhu ai kuwa ta bugu da jikin gado.

Da karfi tace wayyo!
Iska ya firzar sannan ya zauna ya kara kunna fitilar dakin, yace "meye......."


Ganin yanda ta rike kafarta ne tana kuka yasa ya kalli gun, karamin dan yatsanta ta buga gashi hargun ya daga yana jini sosai.
Dama me neman kuka, ganin ya taso inda take kawai ta kara sa kuka.

? Bai kulata ba sai hannunta daya riko ya zaunar akan gado, tissue ya warwaro dayawa ya rufe gun ciwon idanunsa suka canza zuwa jaa.

Daga bayama gani tai ya runtse idan nasa kamar bayasan ganin jinin.

? Kallanta yai sannan yace " rike."
Rikewa tai tana kuka, mikewa yai ya juya ma inda take baya, sannan ya dan dafa kansa.

? Kwalin tissue din ya miko mata ta amsa tana kuka, yace "will u please keep quiet?"

Hadiye kukan nata tai tana kallan bayansa.
Juyowa yai inda take cikin zafin rai yace "are u a fool?"
Shiru tai tana kallansa, hannu yasa ya dagota ya rike kafadunta da karfinsa ya matso cikin zafin rai yace " me yasa sanda suke miki zancen banza baki basu amsa ba? Me yasa sanda suke neman sa ki abinda zai saki kuka baki sanar dasu abinda ke ranki ba? Nine marainin wayanki? Zakizo ki sani a gaba kina min kukan banza?"

? Idanun Jalila ne suka firfito gabanta sai faduwa yake da sauri da sauri saboda tsananin tsoronsa da ya shegeta, bare yanda ya matso daf da ita haka ba namijim daya taba mata haka, ga idanunsa sun canza, ga yanda yake mata fada, jitai gaba daya ta rasa abin cewa.

Ya turata kan gado cikin takaici yace " kinsan ma'anar uwa kuwa? Ko dabansan meye hadinki dasu ba, kada ki kuskura ki dauki uwa a bakin wasa, no matter how they threatened u , don't u ever try that."

Ya juya zaiyi falo, gaba daya zuwan yarinyarnan yasa ana sashi magana mai tsayi haka, wanda rabon daya yita har ya manta.

Harya kai kofa tana kuka tace " kana tunanin nima asan raina akemin haka?"
Tsayawa yai amma bai juyo ba, tana kuka tace "batada lafiya, batada lafiya sosai Yaya!"

Ta kara sa kuka, juyowa yai ya kalleta, kuka take sosai wanda haryasa hannu zai bude kofar yasa ya fasa.

Komawa yai ya zauna a kan gadon sannan yace "zan kwanta."
Mikewa tai ta sa tissue din a dustbin sannan ta koma kasa ta kwanta tana share hawaye.
Kashe wutar yai dakin yai duhu sai sanyi dake kara ratsa dakin, dukansu idanunsu biyo sai juyi kawai da takeyi.
Shikuma yana kwance rigingine.

Can ta daure tace "yaya ya akai ka sani?"

Bai kula ta ba hakan yasa tai shiru, can tace " bansan yazanyi ba, Goggo na sun dauketa daga asibitin da aka kaita, bansan abinda zasu aikata ba inhar banyi abinda suke so ba."

? Yanzun ma bai kula ta ba, sai dai a yanzu ya fahimci da mahaifiyarta ake sata abinda akaso, wanda yauce rana ta farko tun bayan faruwar abinda ya sameshi yauce rana ta farko daya fara tunanin yanasan jin dalilin abinda bai shafeshi ba, yanasan sanin me zata aikata akan abinda baishafeshi ba.



#OneLuv=ؕ?


=??? *JALILAH* =???

Written By : *AYUSHER MUHD*
Wattpad: *Ayusher Muhd*


*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*

_ "Sometime you will never know the value of a moment untill it becomes a memory" Dr Seuss_

? (_D home of expert and perfect writer's_=ء?)


*30*


?? Wajen sallar asuba tana bacci taji kakkari, idanunta ta bude a tsorace sannan ta mike tana neman fitilar jikin gado dan ta kunna, ji tai ta fada kan mutum a rikice tasa hanny ta taba shi.
Kan fuskarsa ta taba, hannu yasa ya riko hannunta da karfi yana wani abu.
Idanunta ne suka firfito saboda tsananin tsoro jikinta ya fara kyarma, da kyar takai dayan hannun nata ta samu ta kunna fitilar.

? Yanda yake yi da jikinsa ne yasa ma ta kasa kokarin kwace hannunta, gaba daya tsoro ya gama kasheta.
Tai tsuru tsuru da ido tana tabashi da dayan hannu tana cewa "Yaya! Yaya!"

? ? Hannunta ya saki ya sa a wuyansa kamar me shirin shake kansa, Jalila cikin tsoro ta rike hannu tana kiransa.
Bakinta rawa kawai yake gun kiran sunan nasa, idanunta sun ciciko batama san sanda hawaye ya fara zubomata ba saboda tsoro.


? Yau abin yafi na jiya shiyasa hankalinta ya tashi gashi su biyu a daki, kuka kawai take tana jinigashi.
Sai dan karatun data iya datake yi, idanunta ta rufe kawai dan batasan ganinsa a haka gaba daya ya canz kamar mahaukaci ko mai farfadiya ko mai aljanu.

? Kuka take tana kiransa wani sain tai karatun idanunta gam, har batasan abin ya lafa ya bude idanunsa ba.
Addu'oi yai sannan ya kalleta, tausayinta ne ya kamashi, yarinya karama a maidata mai jinya? Hannunta da take tabashi dan ya tashi ya rike.

Idanunta ta bude a hankali a tsorace, ta kalleshi.
Yace "kukan meye hakan?"

Bakinta na rawa tace "Yaya?"
Yace "mutuwa akai?"
Kai ta girgiza, yace "to meye hakan?"

Tana kuka tace "bakomai."
Yace " meyasa baki nemi sanin wanda za'a baki ba?"
Tace "kamar ya?"
Yace "bakida 'yanci ne? Ko tsabar biyayya ce tasa? Ni naji inada lalura wanda ban isa in zabi matar da nake so ba, kefa?"

Tace "nima."
Nima? Ta share hawayenta da dayan hannu? "ni Goggo batamasan nayi aure ba."
Abinda ta fada kenan a ranta batasan a fili tai ba sai jitai yace " Goggo?"

Kallansa tai sannan ta kakaro murmushi tace " hannuna."
Sakar mata hannu yai sannan ya mike zaune yana kallan agoggo, mikewa yai ya nufi toilet ba tare da ya sake kallanta ba.

Kallansa tai a ranta tace " ikon Allah, wato wani sa'in sai kaga Allah ya baka komai sai ya hanaka wani abun, kalli yanda ake sanshi a gidan nan, batasan ba kodan bashi da lafiya ne amma kaf gidan nan yanda suke mai sai kasan sanda sukemai daban ne, wanda ko kwana daya ko wuni mutum yai dasu zai fahimci hakan.

Mikewa tai bayan ya fito tai alwala, kafin ta fito ya tada sallar ta fita falo tai sallarta sannan ta kwanta akan kujera, yau kam baccin bai dauketa da wuri ba tayi luff akan kujera tana jin kira'ar qur'ani mai dadin gaske wanda ta tabbatar radio ne yake aiki, tanasan taga tana karatun qur'ani ko ba kamar haka ba amma dai taga ta iyashi, in sultan na karatu a gida ji take inama itace.

A haka har bacci yai gaba da ita.

? Hassan kam ya dade akan sallaya kafin ya kwanta.

? ***********
_Bayan kwana hudu._

? Goggo ce ta kalli lantana tace "Lantana Jalila bataso ba da ina barci?
Lantana tace "eh."
Goggo tai shiru "yau kwanana hudu kenan a sabon asibitin nan amma banga Jalila ba wanda na tabbata indai har da lafiyarta bazata taba iya kwanakin nan haka batazo ba, sannan ba wanda take gani abinci kawai suke aiko mata, bayan sanda zasu canza mata asibiti sai da suka sanar da ita Jalila nacan ma tana jiranta.

Meke faruwa? Anya ba wani abun sukama Jalilanta ba kuwa? Wannan tunanin ne yasa hankalinta ya tashi, har jininta ya sake hawa, matar da ake tunanin sallamarta nanda kwana biyu.

Goggo kira kawai take a kira mata Jalila.

*******
Itakam Jalila kalaman Hassan sune sukai ta mata yawo.
Gashi hankalinta ya kasa nutsuwa saboda rashin Goggonta, duk da yanda Ummy ke

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login