Showing 75001 words to 78000 words out of 149705 words

Chapter 26 - Jalilah Book One Complete Hausa.doc

Ayusher   

28 Oct 2025

634

ganshi a lokacin dan har gaisheta yayi, to amma tagane tsakaninsu? Malam Sagir ashe da raban zan ganka.

Kalaman Goggo ne suka dawo mai, ajiyar zuciya yai cikin tashin hankali yace " ba zama bane ya dace dani."

Mikewa yai ta budo kofar dakinsa a hankali ha sako kai, yana leke.

Bakowa a falon, komawa yai ciki ya zauna yana tunanin abinyi, can ya daure ya fito a hankali yai falo, Ummy na zaune rike da littafin addu'oi ya shigo.

Ta kalleshi tace "Sageer fitowarka kenan, tun rana sai yamma?"

Yace "Ummy ina matar Yaya?"

Tace "Jalila? Tana BQ suna aiki, ta dage sai na taho, ya akai? Nemanta kake?"

Yai murmushin dole sannan yace "eh, bari naje can."
Ummy tace "to, amma Sagir karka tambayeta maganar mahaifiyarta, da magrib in anyi sallah za'a zauna a falon Abbanka."

Yace "to Ummy sannan yai waje.

Tana kwashe shara ya tsaya a bakin kofar yana kallanta.

Kallansa tai sannan ta matso inda yake jiki a sanyaye.

Kallan dakin yai, ya kalli Kofar Toilet inda Lantana ke wankewa.

Yace "Jalila!"

Yace "Uhmm"
Shiru suka danyi dan they are uncomfortable in suna tare ba kamar da ba.
Can ya daure yace "Goggonki, sanda mukaje asibiti....."

Sai a lokacin itama abin yazo mata, ta kalleshi da sauri tace "Ta ganka ko?"
Yace "kin manta har gaisawa munyi?"

Tai shiru tana kallansa, yace "Jalila, zaki iya mata magana? Dan banasan kowa yasan abinda ya faru a baya."

Jalila ta kalleshi tace "ince me? Ince Goggo yayan Uncle nake aure? Ko ince Goggo karki fadama kowa irin san da nakema Kanin mijina? Ko ince Goggo da naso Uncle ashe kanin mijinane?"

Yace "Jalila ya kikesan juya maganar da na fada ne? Me yasa bakya yima kalamai na kyakyasar fahimta?"

Idanunta ne suka ciciko tace "Uncle ni to ya zanyi? Me zance? Kamar yanda kake tsoron matsala ta afko a dalilinka, matsalar da zata sa hankalin iyayenka su tashi ni kaina a yanzu bana san ace nice silar wargaza farinciki Ummy da Abba, dakai kanka da yayanka, Uncle bansan....."

Kasa karasawa tai saboda kuka dake neman zuwa mata dan muryarta ta fara rawa.

Sageer yai shiru yana kallanta cikin tausayawa yace "Nafahimceki Jalila, na kuma gode da kaunar da kikema Family na, Please ko Goggonta tambayeki kawai kice mata sunane yazo daya, mu barshi kawai a haka."

Ta daga kai, kawai dan batasan itakam me zata kuma cewa ba...

Bayan sun gama aiki tai wanka a toilet din ta maida kayan jikinta ta hau sama.

Yana kwance yana bacci ta shiga a hankali ta dau kaya ta saka, sannan ta matso kusa dashi ta sa hannunta akansa, jin ba zafi yasa tai murmushi.

Da alama yau ma ciwon nasa da sauki, dan bacci yake hankalinsa a kwance.

*********
? Bayan magrib kuwa Ummy ta kalli Jalila bayan sun gama girki tace "Jalila inkin kaima Goggon ki ajiye sannan ki kaita falon Abba zamuyi magana."
Tace to, sannan ta dauki Abincin Goggo, tana shiga dakin ta zauna kusa da Goggo tare da kwanciya a kafadar ta tace "Goggona!"

Goggo ta kalleta tace " kin gama gudun?"

Jalila tace "gudun me?"
Goggo ta tureta daga kafadarta tace "kindauka bansan guduna kike ba? Kar na miki tambayoyi? Shiyasa tunda kika fita kikaki shigowa?"

Jalila ta tuntsire da dariya tace "ni? Wlh ba haka bane aiki mukeyi ne bakiga Lantana ma batanan ba?"

Goggo tace "ba wani."
Jalila fa kara kwanciya a kafadarta tace " Ummy tace inkaiki falon Abba, anan zakiji komai."

Tace "kaini dan ni kaina so nake naji."

? Nan suka fita tare, sai data kusa kaita falon, suna tafe tare sai ga Ummy tace " Jalila barta zamu shiga tare."
Ta matso kusa da kunnenta tace "ki je ki lalabo mijinki."

Jalila ta kalleta, Ummy tai murmushi sannan ta nuna mata sama da kanta.

Jalila ta kalli saman sannan ta nufi matatakalar, anya zai fito kuwa? Gashi bashida lafiya.

Kofar dakin ta tura ta shiga, yana kan sallaya yana karatun kur'ani.

Zama tai a bakin gado tana jiransa, bai dade ba yakai ayar karshe ta cikin suratul maryam, yana neman dauko wata surar ne dan izu daya yake yi a duk tsakanin sallar magrib da isha'i tai saurin cewa "Yaya!"

Tsayawa yai bai fara wata surarba sannan bai juyo ya kalleta ba, tace "Yaya za'ayi maganar."

Ya juyo yace "magana?"
Ta kalleshi tace "maganar nan.... ba Abba yace sai anjima ba?"
Yace "and so?"

Tace "shine za'ayi yanzu ka sauko."

Yace "in me?"
Tace "ka sauko, muje tare."

Yace "kinsan me kike cewa? Nine zan sauko inje inda kowa zai zauna ayi magana?"

Kallansa tai tai raurau da ido, yace "ki tashi kije, ni ba nayi nawa part din ba? Saurab ya rage naki."

? Haryanzu kallansa take da idanun kafin tace "Yaya Please"

Juyawa yai ya bude kur'ani zai dora daga inda ya tsaya.

Da sauri ta sauko ta bayansa ta rike gefen rigarsa ta kafadarsa.

Juyowa yai yace "wai........"

Bata jira me zaice ba tace " yaya dan Allah ka taimaken, ba wai wani abu zakace ba, inka zauna agun ma ya isa."

Yace "in zauna?"

Tsugunawa tai ta gefensa tace "Dan Allah yaya."

Hade rai yai ya juya, tace "kan ne?" Ya mata shiru, tace "yahkuri yaya, na sani ina takura maka, sannan ina takura maka da neman yin depending akanka akan komai na rayuwata, kayi hakuri nasan bana kyautawa."

Ta mike tai waje, a falo ta tsaya tai ajiyar zuciya sannan tace " who do u think u are?"

A hankali ta fara sauka daga matatakar, jiki a sanyaye.

? A falo kuwa Abba da Ummy na zaune daga bangare daya, Goggo na dayan bangaren Jalila ta shigo.

Tana shigowa Sageer ya shigo, tunda ya shigo Goggo ke kallansa, inata san fuskar nan? Abba ne ya katseta da cewa "yaki saukowa?"

Ta daga kai alamar eh.
Jiki a sanyaye ta zauna a kasa kusa da Goggo.

Sageer ya zauna a kasa kusa da Abba.

Falon ya dan yi shiru kafin Abba yai gyaran murya yace "Sannu da zuwa mahaifiyar Jalila, muna baki hakuri akan abinda ya faru wanda mu kanmu bamusan takamaimai abinda ke faruwa ba, sai dai ina neman sanin dalilin dayasa ba wanda yasan da zamanki a gidan, sannan dalilin dayasa aka munafircemu mu dake akan auran nan, Jalila yar muce a yanzu shiyasa nake san sanin menene ke faruwa takamaimai."

Goggo tace "nagode da karamawa, sai dai a yanda nasan mutanen nan ba damuwa sukai damu ba ina mamakin yanda akai suka kawo Jalila cikin gidan karamci irin wannan."

Abba yai murmushi yace "mun gode da karamawa, Jalila inaso ki sanar damu abinda ke faruwa."

Jalila ta kalli Abba, ta kalli Ummy sannan ta kalli Sageer.

Ummy tace "duk wani abunda kika sani muke sanji, wannan shikadai ne abinda zaisa musan abinda ya dace muyi, kada ki munafurcemu, kada ki munafirci mahaifiyarki."

Jalila ta kalli Goggo.

Turo kofar da akai ne yasa suka kalli kofar, Hassan ne ya shigo.

Kallan Jalila yai wacce itama kallansa takeyi, a hankali wani murmushi ya bayyana a fuskarta wanda yana ganin haka ya dauke kansa daga kallanta sannan ya nufi can gefe ya zauna akan kujera shi kadai.

Goggonta kalleshi, wannan shine na dazu......


********

Inna ce ta kalli Dady tace "take all the blame."

Kallanta yai cikin mamaki yace "ban gane ba?"
Tace "kace kaine kai komai, dama matarka ce da yarka, kaga kome kai dama kaine me hakki akansu, wannan shikadaine hanyar dazamu kwaci company dinmu."

? Dady yace "ni na kasa fahimta, kenan nine na shirya duk abinda ke faruwa?"
Tace "eh ko dama nice na shirya? Ina naga matsayi? Matar data tsufa????

Dady yamata wani kallan tsantsan mamaki........


#OneLuv=ؕ?

=??? *JALILAH* =???

Written By : *AYUSHER MUHD*
'ote me on Wattpad : *Ayusher Mohd*


*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*
(_D home of expert and perfect writer's_=ء?)

*44*

? Jalila tai ajiyar zuciya sannan ta kalli Goggo tace "sanda na sameki a bangaren su Dady akwance ba lafiya........................."
Haka ta kwashe komai ta sanar dasu, gaba daya falon yayi tsiy saboda tsananin tausayin abinda kunnuwansu yakeji, Hassan na zaune ya kwantar da kansa a saman kujera, idanuwansa na lumshe kai kafe bai san me ake cewa a falon ba, sai dai gaba daya zuciyarsa a karye take da abinda kunnuwansa keji, wannan wace irin rayuwa yarinyar nan tai? Wani irin rashin imani ne hakan? Hannunsa ya matse guri guda cikin tsananin takaici.

? Jalila ta karashe maganar tana kuka tace Goggo banasan wani abu ya sameki shiyasa na kasa fadamiki, sannan suma sunce min karna sanar dake.....

Goggo tana kallanta idanuwanta na zubar da kwalla ta jawota jikinta ta rungume Jalila ta saki wani kuka mai ban tausayi, Goggo tana hawaye tana shafa bayanta tana cewa "kiyi hakuri Jalila duk nice na ja miki abinda suka miki."

Ummy ma gaba daya hankalinta ya tashi, tausayin su ya kamata.

Sageer kam ba'a magana dan baima san hawaye yana gangaromai ba, sai dayaji ruwa a kuncinsa, ya goge da sauri yana kallanta.

? Ummy ta kalli Abba wanda yai shiru yana nazarin abinda ke faruwa, kenan bayan yaga Jalila yace yanaso su bawa dansa a matsayin matar Hassan shine sukai bincike akan Hassan, da sukaji bashida lafiya shine suka hadashi da ita, to ina asalin yar tasu? Dan ya fahimci akwai wata.

Kallan Jalila yai yace "ya isa haka Jalila, su ne suke tunanin sun cutar dake suna ganin sun yaudare mu, amma ni da matata basu yaidaremu ba ko kadan dan ni dama ke nagani sannan ke kika kwantamin a rai, haka itama ke ta gani sannan ke kika kwanta mata a rai, anci mutuncin mahaifiyarki a matsayinta na wacce ta haifeki ta shayar dake sannan ta reni bai kamata ko menene ba a aura da 'ya bada sanin mahaifiyarta ba."

Ummy cikin zafin rai tace "ai muma sun ci mutuncinmu taya zasu nuna mana sune suka haifeta bayan mahaifiyarta daban, tayana dan rashin imani zasu aurar da yarinya mahaifiyarta na kwance ba lafiya? Sannan suyi amfani da rashin lafiyarta gun sata tayi abinda sukeso?"

Goggo ta share hawayenta tace " duk nice suka raina, nice suka maida abin zuba shara, nice basa ganin mutunci, nagode sosai da kaunar da kuka nuna ma yarinyar nan, ko ba'a fada ba na san akwai kulawa mai karfi datake samu a gidannan fiye da gidan da za'a kirashi da sunan gidan mahaifinta."

? Abba yai ajiyar zuciya yace "yanzu tunda nasan meke faruwa bazan barsu haka ba."

Ummy ta kalleshi da sauri tace "me zakayi?"
Ya mike cikin takaici yace "don't u understand what's happening? Sun daukemu a matsayin joke ne, kenan sun maidamu fools, duk abinda suka tsara shi muke bi."

Ummy ta kalli Hassan wanda kamar ma baisan abinda ake a falon ba, sannan ta kalli Abba tace " ni kuma ina ganin ka kyalesu kawai."

Abba yace " In mun kyalesu kina tunanin zasuyi dana sani?"

Goggo ta kallesu tace "amma dan Allah inada tambaya, me ka musu ne da harsuke tunanin ko za'a mutu sai sun kawo Jalila cikin gidan nan?"

Sageer ya kalli Abba yace "Abba ni kaina ina wannan tunanin."

Abba ya kalli Ummy yace " kasuwanci......."

Ummy tamai alama dayai shiru, yace " yanzu ke Jalila kiyi hakuri, nasan an shiga hakkinki, sannan an shiga hakkin mahaifiyar data haifeki, kuyi hakuri wannan harda laifin mu."

? Goggo da sauri tace "ba laifinku bane, masu laifin daban, zan iya yafe duk wani abu da za'amin ko na wulakanci ko na tozarci amma bazan yafemusu ba akan abinda sukama Jalila, tayaya zasuyi amfani dani wajen ganin sun sata abinda sukeso? Yanzu da ace mugun hannu ta fada fa???? Ta fada cikin raunaniyar murya.

? Hassan ya bude idanunsa ya kalli Jalila wacce ke kuka tana zaune kusa da Goggonta.

? A hankali ya mike kawai yabi ta bayan kujera yai hanyar waje.

? Jalila ta kalleshi, shima kallanta yai sannan ya dauke idanunsa da sauri.

? Ummy ta mike tace "Hassan ya akai?"

Yace "bakomai...."
Kawai yai kofa, kallan Abba tai cikin wani yanayi, hannunta ya yadan dafa alamar ba komai.
Sannan ya kalli Goggo wacce gaba daya ita da Jalila tausayi suke bashi, yace "Sageer kai dasu Jalila ku shiga ciki, ni zanyi magana da mahaifiyar Jalila."

Sageer ya mike ya fita, Jalila ta mike ta fito.

Abba ya kalli Goggo yace " garin yaya kika bari aka maidake kamar baiwa? Ko bakida yan uwa ne?"

? Tace "inadasu sai dai a matsayin babu suke."
Ummy tace "kamar ya?"

Tace "bayan anmin auren dole da Abakar aka umarceni da karna kara tako garin sai dashi tin daga lokacin ban sake zuwa ba, dan banida darajar da zai kaini."

Ummy tace "kamar ya? Baki sake neman mahaifiyarki da yan uwanki ba?"

Tace "ina zan nemisu bayan umarni mahaifina ya bani....."
Abba yace "wani umarni ne hakan?"

Ummy tai saurin cewa "Auranki fa?" Dan ta fahimci rashin ilimin addini ne ya sa ta dauka biyayya takeyi.

Goggo tace "ban sani ba nima dan rabona dashi tun ranar da aka kaini, lokacin Allah yai dabon Jalila."

? A tare sukace "me?"
Goggo tai kasa dakai tana murmushin takaici.

Ummy tace "Goggo muje kici abinci ki kwanta."

Abba ya kalleta cikin mamaki dan akwai tambayoyin da yake san jin amsarsu.

********

Jalila na fitowa ta nufi hanyar sama, Sageer da sauri yace "Jalila!"

Tsayawa tai bata juyo ba tana share kwallarta, Sageer ya matso ya mika mata handkerchief kallansa tai kamar zata karba sai kuma naga ta fasa, kamar bazata amsa ba sai kuma ta amsa? tace "nagode." Kawai tace ta juya ta hau saman.

Tsayawa yai yana kallanta cikin tsananin tausayi, har saida tai kwana sannan ya juya zuwa dakinsa, yana shiga ya zauna a bakin gado yana tunani, haka rayuwarta take? Shiyasa ashe ake barinta a ma??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????karanta ita kadai? Shiyasa sukasata a government?

*******
Ummy ta taso tazo kusa da ita, suka fita tare, ina saurayin Jalila? Ta tabbatar Jalila.......... tunowa datai a inda tasan Sageer ne yasa ta kalli Ummy da sauri tace "ya sunan mijin Jalila?"

Ummy tace "Hassan!"

Goggo tace "wanda na gani dazu fa?"
Ummy tace "Sageer? Kaninsa ne."
Goggo tace "kaninsa?"

Ummy ta daga kai alamar eh, Goggo a ranta tace "to ko ba shi bane?"

Dakin Ameera ta kaita sannan tace "kici abinci ki kwanta, dan Allah karkiyi tunanin komai, Jalila yanzu 'yatace bazan kara bari wani abu ya sameta ba, sannan mu zamu san abinyi, ke dai ki kwantar da hankalinki ko dan lalurarki."

Goggo ta riko hannun Ummy tace "Nagode, nagode har bansan iya godiyar daya kamata nai miki ba."

Ummy tai murmushi tace "muma mungode, da kika fahimcemu, yanzu sai kisama auransu albarka."

Tace "insha Allah."

Nan ta shiga ciki.....

Ummy ta bita da kallan tausayi.

Jalila kam kamar zata shiga ciki sai kuma ta fasa, zama tai a falo kawai tana kuka ko kwanwutar bata kunna ba.

? Shima zama yai a kasa ya kwanatar da kansa akan kujerar dakin, wace irin rayuwa yarinyar nan tai? Amma duk da haka akwai laifinsa a ciki, ya tabbatar dabadan shi ba da baza'a mata auran dole haka ba, wadan nan tunani sune suke tayimai zirya a ransa, tarinta yaji hakan yasa ya kalli kofar falon.

? Mikewa naga yayi ya jingina kansa da jikin kofar, sheshekar kukanta yaji wanda yasashi rufe ido cikin tausayawa.

Jin kukan yake har zuciyarsa, a hankali ya bude kofar.

? Dayake makunin fitilar falon a kusa da kofar take kawai sai ya kunna ta.

Haske ne ya baibaye falon, da sauri ta dago.

? Jingina kansa yai da jikin kkatangar falon yana kallanta tare da sa hannunsa na hagu cikin aljihunsa.

? Kallansa itama takeyi, sun dade a haka kafin ta sauke idanunta kasa.

Yace " yau ma hobby din naki ya motsa ne?"

Ta kalleshi da idanunta da suka sha kuka, yace "a rana kuka nawa kikeyi?"

? Baki tadan motsa tanasan magana, yace " in zakiyi kuka kiyi a gurin daba kowa, dan ni ba hobby dina bane sauraransa."

? Ya juya bai rufe kofar ba ya zauna akan kujera, me yasa yace haka? Shi dayaje dan ya lalasheta?

? Mikewa yai yai sallar Isha'i, ganin batada niyyar shigowa yasa yaki mikewa daga kan sallayar, yana jiranta.

? Kofar yake lekawa, yaga ba alama.

? Pillow ya janyo yasa kansa akai yana kallan kofar.

? Abincin su ya kalla, bataci abinci ba, shiru yai yana tunanin shigowarta.

? Yana nan a kwance har karfe 10, baisan sanda bacci yai gaba dashi ba.

Jalila kam bayan ya juya kawai ta kwanta akan kujerar tana yan mitoci, kasan baka damu da hawayena ba me yasa dazu kazo? Nikam Yaya me yasa baya magana mai sanyi? Tadan turo baki ta kwanta tana tunanin rayuwarsu.


? Batasan bacci ya dauketa ba, sai karfe 11 ta farka, batai isha'i ba ya akai bacci ya dauketa?

Da sauri ta sauko daga kan kujera ta nufi dakin, a kwance ta ganshi a kasa, batai mamaki ba dan taga yanayi, kawai ta wuce toilet.

Tai alwala tazo tai sallah, jitai cikinta na karar yunwa, ta zo ta bude abinci zataci, gani tai ba alamar taba abincin, baici abincin dare ba kenan?

Kadan ta zuba a plate ta faraci.

Lomarta uku taji kakarinsa, wani sankamewa yakeyi, da sauri ta ajiye abincin ta matso inda yake.

? Gaba daya ya sai juye juye yake, yana girgiza kai alamar a'a, ga zufa tanata keto mai.

? Hannunsa ta riko tana tabashi, Yayah! Yayah!
Gaba daya ba alamun yanajinta, kansa ta kwantar a kan cinyarya dan murkususun dayake yasa kansa ya sauka daga kan pillow din, tasa hannu ta rike kansa dayan hannun kuma tasa a saman kirjinsa tana dan tabashi tare da kiran sunansa.

? Can kuma sai tadanyi kulhuwalahu da falaq da Nasi sai tadan tofa mai.

? A hankali taji ya daina motsumutson.

Idanunta na kansa ya ciciko saboda da tausayinsa, wannan wani irin abu ne ke damunshi? Me ya sameshi? abaya?

A hankali ya bude idanunsa, daidai lokacin kwalarta ta zubo ta zubu saiti idanunsa, wanda yana rufe ido ta zubo a bayan idansa.

? Idanunsa ya sake budewa ya kalleta, dayan hannun data rike kansa dashi ta saki ta share hawayenta sannan ta kalleshi tace "Yayah!"

Idanunsa ya lumshe yana kallanta kamar yanda take kallansa cikin sansanyiyar murya mai kamma da rada yace "sai yaushe ne zaki daina saurin kuka?"

Tace " kukan ne bakaso nayi?" Itama a hankali tai maganar tana kallansa.

Mamaki ne ya kamata dataga ya daga kai alamar eh, tace "meyasa?"
Ya dan girgiza

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login