Showing 6001 words to 9000 words out of 149705 words

Chapter 3 - Jalilah Book One Complete Hausa.doc

Ayusher   

28 Oct 2025

603

sannan ya mike yace "Yaya kazo dan Allah ko waje ka fita kaji iskar duniya."
Bai kalleshi ba haka kuma bashi da niyyar amsamai, Sagir ganin haka yasa ya fita tare da ja mai kofar.

? Sagir yabi bayan kofar da kallo sannan yace "Allah ya yaye maka ya baka lafiya."

? Dakinsa Sagir ya shiga kallan kayan da ya cire dazu yai sannan yai murmushi ko a ya ta koma gida? Cikin nuna halin damuwa yace " ba ta dai jike ba ko?"
Kai ya girgiza yace " ya za'ai ta jike ga lemar da ya bata sannan ya tabbatar tace ai zuwa za'ai a daukesu."
Murmushi yai sannan ya dau wayarsa dayazo dayka ya sauka kasa.

? **************

? ? Jalila ce zaune tanacin abincin dare ita da Goggo, tunanin abinda ya faru dazu takeyi.
Jitai Goggo ta tabata tace " Jalila wani abun ya faru ne dazu?"
Jalila ta kalleta tace "Bakomai kawai dai ni akwai abinda na dade ina san tambayarki ne Goggo."

Goggo ta kalleta tana neman karin bayani, Jalila tace " Bawai da wani abin bafa nake san ji Goggo, kawai dai tambaya ce."
Goggo tace "Ina jinki."
Jalila tace " Ni Goggo baki da kowa ne sai Dady?"
Murmushi tai tace"Ban gane banida kowa ba sai shi? Kin tabaganin wanda bashida kowa a duniya?"
Jalila tace " To ni Goggo na kasa fahimtarki ne sam, na rasa takamaimai ke mukeyi a cikin gidan nan."
Goggo ta tsame hannunta sannan tace " Lalai Jalila, muhallin Mahaifin naki kike fadama haka?"
"Muhalli? Ai kowa yasan gidan Mumy ne ba nashi ba, sannan ni waye ma yasan ni 'yarsa? ce, ko suna a makaranta ni ansa nayi amfani da Auwal wato kakan Dady, dan kawai karma asan ni yar sace."

Goggo tace" ya isa to, ke dai ba ruwanki da wannan, mahaifinki da mahaifinki ne, sannan banaji yana da laifi a harkar nan, laifin na iyayenmu ne."
Jalila tace "Goggo dama tun can baya sanki"
Harararta tai tace"Wai yau me kikesan ji ne haka?"
Tace"ni dan Allah ki fadamin tarihinki Goggo."

Hannunta ta wanke a robar ruwan da Jalila ta kawo ta dan matsa kadan tace " sai randa hankali yazo miki."
Jalila ta dan turo baki tace "ni yau meyasa ake tacemin banda hankali?"
Goggo tace " Ce miki akai mara hankali a cikin gida?"
Tace "Safeena ce."
Goggo tace "Fada kukai kenan?"
Jalila ta hade rai tace " ni ai....."
Goggo tace "sai yaushe ne zaki dinga hakuri Jalila? Na dauka na rokeki akan kai zuciya nesa?"
Jalila ta kalleta tace "Yanzu duk hakurin da nakeyi bakya gani? Wlh a yanda nake ji da wata rana sai na fasama 'yar nan baki, kawai hakuri nake sawa a zuciyata."

Goggo tausayinta ya kamata tace"kiyi hakuri, duk tsanani yana tare da sauki, shiyasa a koda yaushe nake miki fatan miji na gari, wanda ke sanki ina tunanin hakan ne kadai zai kawo salama a zuciyata da taki."
Jalila tace "ni duk wanda zan aura sai dai in zai iya rikemin ke, dan bazan iya aure na barki ba."
Dariya Goggo tai tace "Lalai yarinta na damunki Jalila."
Haka sukai ta hira har suka kwanta.............

? *********
?

? Washegari.........

? Yau tana gama aiki ta shirya ta fito dan jiransu, dadi takeji yau ta rigasu shiryawa, yanda taga Dady ya fito da sauri ko gaisuwarta bai tsaya amsawa ba tasan lalai da matsala, mota taga ya shiga da sauri, sai ga Mumy ta taho da gudu tare da shiga gefensa itama, nan taga sun fita a guje.
Baki ta tabe tace "ko ina zasu haka oho"

? Su Safeena ne suka fito,Yasmeen na ganinta ta isa gunta da gudu tana nuna mata sabon school bag din da Dadynta ya siyo mata.
Jalila tace "inyee lalai tayi kyau."
Tafada tana kallan wata yagwalgwalaliyar jakar dake bayanta.
Mota suka shiga, Safeena ta kalli Sultan tace "Sultan kamar akwai matsala a company dinsu Dady ko?"
Sultan ya kalleta yace" ina na sani, in so kike kiji me yasa baki tambayeshi ba da zai fita?"
Haushi ne ya kamata tace " Wai kai meyasa mutum bai isa yai maganar mutunci dakai ba?"

? Tsaki tai sannan ta maida kanta kan Jalila cikin masifa tace "ke kuma uban me kike kallo?"
Jalila tace "Ba ni na kar zomon ba Hajiya."

Safeena ta kara kuluwa, da saninta tasa kafa ta tako kafar Jalila, Jalila ta kalleta.
Safeena tace " sry fa ban kula ba."
Jalila ta kalli safarta wacce ta baci sannan ta kalli Safeena tace " mantawa nai ashe idanunki basa aiki."
Ran Safeena ne ya baci tace "mene?"
Jalila ta kalli window ganin sun kusa isa, me zata gani?
Uncle Sagir ta gani yana parking din mashin dinsa, ga mamakinta murmushi ne ya bayyana a fuskarta, Safeena ce ta kalli inda take kallo nan idanunta suka sauka kan Sagir.
Idanu ta kuramai, waye wannan?
Batasan a fili ta fada ba, Jalila ta kalleta tace "Uncle dinmu ne na Math."
Safeena ta kara kallanshi sannan tace "Driver tsaya anan mana ta sauka."
Jalila ta kalleta ta tabe baki sannan ta sauka.
Muryarta yaji tace "Good Morning Uncle."
Juyowa yai ya kalleta, yanayin fuskarsa kadai zaka kalla kasan ganinta ya sashi farinciki.
Jalila ta dan matsa gunsa kadan tace "Sir nayi laifi."
Bai ce komai ba sai wani kallo da yake mata, gana kokarin b'oye abinda ke ransa, dan bai manta ita din dalibarsa bace.
Ta fara wasa da hannunta sannan tace "Lemarka jiya ta samu matsala."
Yace "ta samu matsala ko dai ba'a damu da ita ba an lalatata?"
Da sauri tace " ba haka bane, Allah iska ce ta dinga bankareta....."

? Yanayin fuskarsa ne ya canza zuwa kulawa, yace "ba dai abinda ya sameki ko? Are u okay?"
Ganin yanda ya damu da ita yasa taji ta kasa cewa komai, yanda take kallansa ne yai saurin juyawa ya kalli daliban dake ta shiga makarantar yace " Ki wuce cikin makaranta."maganar ya karasa tare da juyawa yana kallan mashin din.

? Jalila ta fara tafiya a hankali tana mamakin kulawar da yake nuna mata wanda ke kokarin sa zargin so a zuciyarta, anya kuwa? Karfa zuciyarta ta raya mata abinda ba haka ba, Uncle Sagir yafi karfinta, dan mata dayawa na sanshi, sannan da alama dan gidan wani ne duba da yanayin yanda yake zuwa wani sa'in a mota.
Wata zuciyarce ta ce mata ina ruwan so da wannan?

Juyowa tai bayan tayi tafiya mai nisa, ga mamakinta gani tai idanunsa na kanta, suna hada ido yai saurin juyawa, Jalila ta juya cikin yanayin jin kunya.


**********
A company dinsu Dady kuwa suna isa sukaga mutane ancika a waje.
Da sauri sukai parking Dady ya fito cikin tashin hankali, suna ganinshi sukayo kanshi.
Mumy na gefensa, cikin tsantsar tashin hankali yace " gaba daya kayanda muka adana sun lalace?"
Cikin damuwa yace " Muje ka gani."
Store din da suke adana dukan kayan aikin da sukeyi ya bude.
Store din acike yake da kayan ma'a dana na abinci.

Gaba daya hankalin Dady ya tashi dan kana gani kasan lalai lalata musu akai.
Juyowa yai yace " How can this happen? How......."


Mumy ma hankalinta ya tashi ta kalli Dady tace "Yanzu ya zamuyi? Gashi zuwanka Abuja munyi signing da Al-Company zamu aika musu da kayan cikin satin nan."
Wata zuface ta karyomai yace "Muje gida mu sanar ma Inna, sai muyi tunanin mafita, dolene mu san yanda zamuyi kafin nexweek."

? Hankali a tashe suka juya gida.
Inna macece wacce tasan kan kasuwanci, dan company dinsu ya bunkasa ne harda tsananin iya kasuwancin ta, shiyasa mijinta yake girmama kalamanta sannan takeji da kanta itama.
Har Allah ya mai rasuwa, ta dade tana juya company din da kanta duk kuwa da ganin Dadyna iya nasa kokarin a karkashinta,har sai dataga girma ya kamata tana bukatar Hutu sannan tabar Dady yakejan ragama.

Inna wacce yanzu ne ta maida sunanta haka, dan da kowa Hajiya yake kiranta, yanzun ma Sultan ne ya sa mata hakan har kowa ya koma kiranta haka a gidan, amma daga ta fita sai dai kaji ana Hajiya.
Tai shiru kafin tace "nawa ne a account dinmu?"
Yace "Hajiya mun kwashe rabin kudin mun sai kayan aiki, ba nakawo miki budget din ba?"
Hannu tasa ta shafi fuskarta tace "Kudin bazasu kai musai wasu kayan ba kenan?"
Kasa yai dakai yace "Gaba dayan mun gama shirya plan dinmu banaji ko kwata zai kai."
Ta dade batace komai ba da alama nazari take kafin tace "Sai dai kenan mubi last option din da banaso."
Yace "Loan?"
Tace " dole zan duba a cikin mutanen Alhaji da nawa wanene na amana sai musan yanda zamuyi, either mu samu loan ko kuma yayi investing."

? Kai ya jinjina sannan yace "bari a kira board meeting sai a tattauna."
Tace "No ka bari sai zuwa gobe in na samu wanda zai tallafa mana."
Yace " To Hajiya."


Nan ya mike ya fita, wani karamin diary ta d'auko ta shiga duba sunaye tana auna mutane.......


#Oneluv=ؕ?

[08/10, 19:18] * +234 816 365 0557, : =??? *JALILAH* =???

Written By : *AYUSHER MUHD*
Wattpad: *AyusherMohd*

*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*
(_D home of expert and perfect writer's_=ء?)

*No 5*


?? Yau a staff room yai shiru yana tunanin yanda zaiyi, ya dade yana tunani dan baisan ma sanda wani staff yazo kusa dashi ba yace "Sagir mu mun wuce sai gobe in Allah ya kaimu."
Kallanshi yai cikin mamaki sannan ya kalli agoggon dake jikin bango, lalai har an tashi da kusan minti goma ma.
Yace "To Sai goben."
Nan ya shiga hada kayansa shima, a tsaye ya ganta a inda ta saba tsayuwa, ya dade yana kallanta sannan ya karasa kusa da ita yace "Malamar jira."
Kallansa tai sannan ta sunkuyar da kanta tana murmushi dama yanzu take tunanin bata ga fitarsa ba.
Jitai yace mata "D'an zo."ya fada tare da fara tafiya,? cikin mamaki take binsa har suka shiga wani class.
Zama yai a saman desk sannan ya mata alama data zauna daga kujerar dake gefensa kadan.
Bata musa ba ta zauna, sai daya d'an yi shiru na wasu dakiku kafin taji yace " Jalila!"

Yanda ya kira sunanta ne yasa taji wani abu yar wanda ya hanata amsawa sai kallansa datai, yana kallanta yace " labari zan baki."
Nan ma batace komai ba sai kallansa data sake yi, murmushi yai sannan yace "akwai wani sokon abokina da ya taba ganin wata yarinya tun last year, ya taho shida kanwarsa zasuje gidan yayar mahaifiyarsu, sun tafe sai kanwar tasa tace "Yaya dan Allah mu tsaya musai maganin ciwon kai, tun dazu nake kai na kemin ciwo.
Parking yai da saurin ganin chemist a tsallaken titi sannan ya fita.
An miko mishi magani kenan zai amsa ta shigo da sauri, kallo d'aya zaka mata kasan hankalinta a tashe yake, tana zuwa tace " Dan Allah maganin ciwon kafa."
Nurse din ne ya kalleta yace " Ciwon kafa wani iri?"
Tace " ban sani ba kawai kafar Goggo ce ta kumbura." Tana hawaye take mai bayani.
Wanda yazo siyar maganin ciwon kai sai duk tausayin yarinyar nan ya kamashi, zuciyarshi yaji ta shiga cikin matsananciyar damuwa na ganin yanda yarinyar nan take hawaye.
Yace "Ku kaita asibiti mana."
Bata ko kalleshi ba tace " Dan Allah nikam ka bani maganin da zai taimaka mata, banida kudi yanzu sai dari biyu, inya fi haka zan kawoma ko gobe ne."

? Tsananin tausayinta ya kara shigarsa kallan Nurse din yai sannan yamai alama daya hada mata maganin nan masu kyau, bayan ya bata ta mai godiya ta fita.
Kallan Uncle take idanunta sun ciciko da hawaye, ba shakka daga baya tayi ta mamakin arhar maganin kenan Uncle siya mata yai? Dan ko bai fada ba tasan da kanshi yake, tunda dai na farko itace yarinyar, to in har abokinsa ne yaza'ai yabashi labari haka dala dala?
Sagir yace " tundaga wannan rana Abokin nan nawa ya shiga wani yanayi akan yarinyar nan, jefi jefi yanabi ta layin nan ko zai ganta, sai dai cikin rashin sa'a bai sake ganinta ba har sai da akai assigning dinsa zuwa inda zaiyi bautar kasar sa, duk yanda yaso ya daure akan san yarinyar nan da damuwa da ita ya kasa, shine nake so ki ban shawara me abokin nan nawa ya kamata yai? Yana tsoron kar ya bari ya huce....."

? Wata irin kunyarsa ce ta kamata, kanta na kasa tana wasa da hannunta tana murmushi.
Yace "Jalila, bakice komai ba? Ko ba kya ganin yarinyar nan zata soshi?"
D'agowa tai cikin jin kunya tace " Ta ya zatai ta......."
Yanda yake kallanta ne yasa tai saurin sa tafukan hannayenta ta rufe fuskarta cikin jin kunya."
Yace idanunsa na kanta "Ya zatai ta soshi?"
Kallansa tai da sauri tare da cewa ba haka zance ba...."
Murmushi yai sannan yace"Ya za'ai ta kasa sanshi?"
Da sauri ta mike cikin tsananin jin kunya tai hanyar waje, har taje kofa zata fita taji yace " ba kya tunanin abokin nawa yayi rashin kunya? Duba da yanayinta na dalibarsa?"
Bata juyo ba tace " Ai ba malami ne na dindindin ba sannan ko malamin ne banaji......."
Sai kuma ta kasa karasawa tana murmushi, yace "wasa wasa al'adarki ce tsayawa a tsakiyar magana, gashi nikuma zuciyata so take taji me zakice."
Cikin jin kunya ta juyo ta kalleshi sannan taj waje da sauri.

Idanunsa ya lumshe cikin wani irin jin dadi sannan yabi bayan kofar data fita da kallo.
Jalila kam tana tsaye ita kadai tana murmushi, lalai yau tana cikin jin dadi.
Ganin motarsu tayi parking ne yasa tai saurin shiga dan ta hango Uncle na tahowa, ita kuma yanzu kunyarsa takeji.
Tana shiga motar Safeena tace " Jalila ya sunan wannan malamin?"
Jalila ta hade rai tace "Wanne?"
"Wanda muka gani dazu da safe, yauwa wanda ya ajiye motar can." Ta fada tana nuna motar uncle Sagir.
Jalila ta kara hade rai tace "menene?"
Safeena tace "Meye kuwa, kawai dai burgeni yai nake tambaya."
Jalila tace "Sai ki tambayi matarsa dan ni bansani ba."
Safeena tace "Yana da mata?"
Jalila ta guntse dariyarta a ranta tace "yayarki ba insha Allah."

? *************

?? Hassan shi kadai a zaune a garden din gidansu, dan da kyar Ummy ta lalabashi ya fito, idanunsa a rufe sai dai ni kaina bansan tunanin me yake yi ba, ko kuna idanun kadai ya rufe.

? Daga bayansa yaji an rufe masa idanu, mikewa yai a zabure, Aina ta turo baki tace "Yaya!"
Kallanta yai sannan yace "Meye hakan?"
Tace "Yaya wai ni sai yaushene inka ganni zaka nuna farinciki kamar da?"
Bai tanka mata ba sai kokarin barin gun da yai,idanunta ne suka canza, tsananin tausayinsa ya kara ratsata, sai yaushene Yaya zai dawo kamar da? Tana tsaye har sai da taga ya kulle.

Tahowa tai daga gun jiki a sayaye, tana tura kofa taji ance "WAH!"
Idanu ta runtse dan ta tsorata, dariya taji an kwashe mata dashi, ta bude idanunta cikin shagwaba tace "Ya Sagir!"
Yace "Matsoraciya!"
Tace "Naji din na tabbatar ko kaine sai ka tsorata."
A tare suka nufi cikin falon suna tafe suna hira, Ummy tace "Haba Aina, an shigo da trolly banga mai trolly din ba."
Tace "Ummy Yaya na hango shine naje mu gaisa."
Ummy tace "kece ashe kika koroshi daga inda yake"
Kusa da Ummyn taje tare da zama a kasa tace "Ummy ina wuni?"
Ummy ta amsa sannan Aina tace "Ya jikin Yayan?"
"Jiki Alhamdulila zance kenan? Sai fatan Allah ya yayemai larurar nan."
Tausayin Ummy ne ya kama Sagir, kusa da ita ya zauna yace "Ummy d'anki yayi girlfriend"
Kallansa tai tace "Haba?"
Aina ta tabe baki tace " da alama yarinyar bata da taste."
Harararta yai tare da maka mata pillow yace " uwar sanjin gulma sai kije can ki shiga da kayanki kafin Ameera ta dawo."

Ta tabe baki sannan ta mike tare da jan Trolly dinta.

Ummy cikin zumudi tace "a ina take Sagir?"
Yace "Makarantarmu."
Tace "students ce?"
Kai ya daga yana murmushi.
Ummy tace "bani labari."
Dariya yai sannan ya mike yace "Ummy ba yanzu ba."
Tace "bama nasan ji."
Nan yai sama yana cewa "zama na musamman zamuyi ai Ummy na."

Da kallo ta bishi tana murmushi azuciyarta tace"Allah ya kawo randa zanga Hassan na walwala kamar haka, Allah ya kawo sanda zaimin zancen mace."

? ***********

? Inna ta dade tana nazari kafin ta zagaye sunan mutane hudu a cikin dan littafin nata.
Nan ta kira Sani wanda ya kasance Secretary dinta ne a lokacin da take ganiyarta, bayan sun gaisa tace "Nikam ya labarin Alh Ayuba?"
Yace "Alh Ayuba ai yana England tun shekaru hudu da suka wuce shi da iyalansa."
Tai shiru sannan tai cancel din sunan sa tace " Alh Muhammad fa?"
Yace "Hajiya kin manta shine na baki labari an rufe company dinsu?"
Tace "Oh na manta." Nan tai canceling din sunansa tace "Alh Abdullahi Taura fa?"
Sai daya danyi nazari yace " eh shi yana nan garin Kano, sai dai yayi retire daga managern banki ya fada kasuwanci."
Tace "kasuwancin kamar ya yake?"
Dariya yai yace "Kasuwanci mai karfi, dan yanada company na motoci, yanada gidan mai sannan yanada store a nan garin."
? Murmushi tai tace "bashida wani issue na matsala ko personal life dinsa?"
Sani yadan yi shiru yace "Ba komai a iya sanina na dai san akwai yaransa uku, sai dai akwai kananan maganganu akan babban dansa wanda inaji kamar akwai wata matsala da yake fama dashi, sai dai su suna kokarin boyewa."

? Ba tare da wani dogon nazari ba tace "yauwa na gode, yanzu ka bincika ka samomin number dinsa, cikin gaggawa."

Yace "To Hajiya!"

Harzata tambayeshi mutum na karshe da take tunani sai ta fasa dan dama tafisa ran mutane ukun.


? Mikewa tai ta shiga dan xagaye d'akin nata tana tuanani, tabbas tanajin ba matsala dan kuwa tasan Taura akwai mutunci sai dai tasan harka ta business bani in baka ne."

Ta tabbatar in ta nemi taimako dole sai ya nemi wani abu itama daga bangarensu, waya ta daga ta kira Dady tace "Abakar ya situation din directors dinmu?"
Yace "Hajiya abin dai ba dadi, duk an rasa mafita"
Batace komai ba ta katse wayar, hoton mijinta wanda sukai ita

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login