Showing 3001 words to 6000 words out of 149705 words

Chapter 2 - Jalilah Book One Complete Hausa.doc

Ayusher   

28 Oct 2025

601

shiga aiki tana yi hawaye na zubo mata, a duk sanda aka cima Mahaifiyarta mutunci wuni take tana kuka, sai dai abin bakin cikin ba kowa bane mai cima mahaifiyar tata mutunci ba sai Mahaifinta da zuri ar sa dan kuwa zuri arsa zatace, a iya sanin rayuwarta bata taba ganin mahaifinta ya shiga bangaren Mahaifiyarta ba balle mu amala ta aure ta hadasu ba, in ta tuno irin kuncin da mahaifiyarta ta shiga a dalilin rashin so ba shakka sai taji nata ba mai zafi bane, gwara ita mahaifinta ne.

A haka har ta gama girkin, tana girkin tana gyara gidan inda ya baci, sai da ta juye musu nasu sannan ta dauko tasu samirar ta dan zuba kamar yanda aka kiyaste mata sannan ta gyara kitchen din.

Daukar na Mamar Mumy tai ta nufi sama inda take, Sallama tai sannan ta tura kofar bayan an bata izini, a zaune take sanye da glass tana karanta wata takarda, kana shiga dakin wani sanyin dadi da kamshi ne zai ratsaka, inda ake ajiye mata abinci ta ajiye sannan ta tsugunna tace  Inna barka da gida.
Bata tankata ba, inda sabo ta saba mikewa tai sannan ta nufi hanyar waje.
Muryar inna taji cikin tsantsar isarta tace  na dauka jiya ma sanar dake in kin dawo yau daga makaranta zaki kwashi wankina ki sauka dashi kasa?
Da sauri ta juyo tace  yahkuri Inna wlh na manta.
Bata kara tanka mata ba nan ta nufi inda kayan suke ta hadasu ta fito dasu.

Sauko wa tai tana kallan su Safeena da Sultan rike da littafan karatu da shigar uniform na islamiya zasu tafi.

Abinda take tsananin buri kenan a rayuwarta taga an sata a islamiyya.

Haka ta sauko ta kai wankin Inna gun Auwal dan ya kai mata sannan ta mikama Goggo abincinsu ta dawo dan gyara dakin Safeena da Sultan, tana gamawa ta koma kitchen dan daura abincin dare.

Haka rayuwar Jalila take, daga aiki sai aiki, makarantar boko kadai aka barta sai dare bayan magrib take samun zama da mahaifiyarta.

**************

_Washe gari_
Yau kam tayi sa a ba a sata yin breakfast mai wuya ba, ta samu ta biyosu Safeena, a mota dama Yasmeen ce kawai mai magana ta kula Safeena ta kula Jalila dan ita yarinya ba ruwanta.
Shi kuwa Sultan kamar baya cikin motar haka yake, earphone kawai yake sawa a kunnensa ya kwantar da kansa akan kujera har su isa.

Suna zaune ita da Zarah, duk wata hira da zata fito daga bakin Zarah na Saurayinta Nasir ne, Jalila ta juyo tace  Nikam Zarah anya Nasir na sanki kamar yanda kike sansa?
Fuska ta canza tace  wacce irin tambaya ce wannan?
Jalila xatai magana Uncle Sagir ya shigo, da sauri suka mike suka gaida shi.
Idanunsa akanta ya fara sauka, a hankali wani murmushi ya banyana a fuskarsa.
Sannan ya basu damar zama.
 Mathematics abinda ya rubuta kenan a blackboard sannan ya ruba  Quadratics Equation
Sannan ya juyo da hankalinsa kan d alibai, Jalila ta dago suka hada ido da sauri ta sunkuyar da kanta tana wata da yatsun hannunta, haka ya shiga yi musu examples.

Jefi jefi yana sauke idanunsa akanta haka itama, har ya gama period dinsa sannan ya ce a hada masa assignment din da ya bada.
Nan monitor ta mike ta hada, kallan Jalila yai yace  Habiba inasan ganinki biyoni da books din nan.
Kallansa tai sannan tai saurin cewa  Yes Sir
Tare da fitowa ta amshi littatafan.

Yana gaba tana dan binsa a baya sai jitaj yace  yau saboda in kama wata nazo da wuri sai tai sa a bata makara ba.
Tace  wata? Ni?
Ta fada tana kallansa,bai juyo ba sannan bai daina tafiya ba yace  da yau na kamata lalai da shikenan na daina amsa ko gaisuwarta.
Tace  Na daina zuwa late insha Allah, sannan jiya ma tsautsayine.
Yace  a tare zamu gama, kuna gama exams ni ma ina kammala aikina.
Murmushi tai batace komai ba.
Yace  me kikeyi tsayawa yi in an tashi daga school kullum?
Tace  Kanena nake jira a tashesu sannan a daukosu sai su biyo ta nan mu tafi.
Yace  Kannenki?
Ita kanta taji abin ban barakwai sai dai ko ma menene ai kannenta ne, tace  eh

Juyowa yai yace  a wani school suke?
Tace  Crescent International School
Kallan mamaki ya mata sai dai bai kara cewa komai ba sai juyawa dayai, yana tafiya yana mamaki, kannenta na Crescent ita kuma tana makarantar Government?

Sai data ajiye mai books din sannan ta fito, tana tafe tana mamakin tambayoyin da Uncle Sagir ya mata.

Ana tashi sun fito ita da Zarah, Zarah na ce mata ni dazu me kike nufi? Ban samu munyi magana ba........
Nasir da ta gani a tsaye ne yasa ta dakama Jalila duka a kafada tace  Jalila kinga!
Jalila ta juya ta kalli yaran dake tsaye daga gefensu tace  yayanki ne?
Yace  My Nasir ne, da alama ya gaji da missing dina ne.
Jalila ta kalli Nasir din sannan ta kalli Zarah wata dariya ta kirkiro wanda kana gani kasan ta dole ce tace  Ohh shine Ur Nasir?
Zarah ta hade rai tace  Meye hakan?
Jalila ta girgiza kai tace  Kije naga ya kura miki ido kamar zai daukeki.
Murmushi tai sannan tace  Kawata kalleni fuskata batai komai ba?
Kamar zatai kuka ta daga kai tace  Eh
Zarah ta fara tafiya cikin canza salo, Jalila kallansu kawai take cikin mamaki, wannan ai da alama makaranta ya samu da wuri amma ta tabbatar baiba Zarah shekara biyu bama, dan ma tace a level 3 yake ne amma lalai da tace sa ansu ne,lalai ansha yarinta shiyasa.

Tab itakam gaskiya bataji zata iya soyaya da sa anta, ita tafisan saurayi kamar Uncle Sagir, da sauri ta girgiza kai tace  What am I thinking? Ahhhhh lalai banida kai.


#OneLuv=ؕ?

=??? *JALILAH* =???

Written By : *AYUSHER MUHD*
Wattpad: *AyusherMohd*

*No 3*

Tana kallansu suna tafe suna rangaji irin na masoya, murmushi tai sannan ta koma gefe ta tsaya.
A hankali duk aka yoye tana tsaye, ganin rana ta fara dishashewa ne yasa ta daga kai ta kalli sama, hadari taga yana haduwa abinka da damina kan kace me gari yayi daki, da sauri ta juya ciki ganin iska mai kura tana tasowa.
Ji tai ta bugi abu, da sauri ta dago ta kalleshi.
Idanunsa na kanta, ta matsa baya da sauri cikin jin kunya, sannan tace "Sorry Sir"
Yace "anya yau sorry din nan zai karbu kuwa agurina? Da alama sai na hukunta mai laifin nan."
Kallansa tai sannan tace " Wlh ban ku........"
Yanda yake kallanta ne yasa ta kasa karasa maganar dake bakinta sannan tai saurin juyawa, dan ji take gabanta na faduwa.
Murmushi yai sannan yace "muje in kaiki gida."
Tace " Naam"
Yace "Baki ji bane ko bakya so ne? Hadari ne a garin in aka fara ruwa kina tunanin yanda zakiyi kije gida? Ko su Kannen naki ne bakyasan ki tafi ki barsu?"

Shiru tai tana dan nazari kafin tace " Nagode da kulawa Uncle Sagir sai dai in na tafi ba tare dasu ba fada za'amin."
Kamar zai sake magana sai kuma taga ya juya ya koma ciki, tana tsaye ya fito da lema ya mika mata bai jira tace komai ba ya hau mota yai gaba.

? Da kallo ta bishi yau da mota yazo? Hmm ita kadai tasan cin zarafin da za'ama mahaifiyarta in har ta tafi.
Tana tsaye aka fara yayyafi da sauri ta bude lemarta ta shiga, kan kace me ruwa ya tsuge, ruwa ake mai karfin gaske wanda tana cikin lemar ma amma ba tsira tai ba, komawa gefe tai ta rakube.
Kamar motar zata tsaya sai taga ta yi gaba da gudu, cikin tsananin tsoro ta kalli motar tare da kwalla kara da karfi tace "Safeen ina nan fa......"
A cikin motar kuwa wanda Safeena tacema Malam Auwal da alama ta tafi ganin hadari, wanda akasan ranta ta tabbatar bata tafi ba, tsabar mugunta ce.
? Haka ta rakube dan tsoro takeji ta koma cikin makarantar ita kadai, ganin a tsayen ma tsoro ya kamata kawai ta fara tafiya tana tafe tana kuka mai sauti, sai dai kasancewar karar ruwa bai sa tasan da karfi take kukan ba.

? Yana zaune a cikin motarsa daga gefen titi wanda shi dama yafisan gurin shiru inda ba mutane, shiyasa mafi akasari zaka sameshi ne a zaune a cikin motarsa ya zuge glass kawai ya kwanta.

? Jikin motar ta tsaya da taga ruwan ya dan yi sauki duk jikinta ya jike jagaf, ga lemarma sai lankwashewa takeyi saboda iska.

? Juyawa tai ta kalli glass din motar, da yake motar mai tints ce sai ta shiga kallan kanta tana kara wani kukan,sam tunaninta bai kawo mata da wani a cikin motar ba.

? Kallanta kawai yakeyi sai sharar kuka take wiwi.
Komawa yai ya maida kansa ya rufe idanunsa kamar mai bacci.
Kara juyowa yai ya kalleta, kuka take sosai, kamar dama neman kukan takeyi, haushi duk ya isheshi kamar a kansa take kukan, kofar mazauninsa ya bude, a tsorace ta kalli motar, kallansa tai a tsorace, sannan ta kalli motar .
Kallan tsoro tamai tace "Hmm hmm."
Hannunsa ya dago ya mata alama da ta matsa daga gun, tace "Ban gane me kace ba."
Alama ya sake mata da hannunsa akan tai gaba, sannan ya maida kofarsa ya rufe, da harara tabi kofar motar sannan tace " wannan kuma wani kwarantancen dan duniyar ne? Maganarce yafi karfin yimin ko kuwa tsabar rashin mutumci ne?"

? Harara ta sake yi sannan ta juya, kallan motar ta sakeyi sannan tace "irin motar jiya"
Taja tsaki tace " da alama duk masu hawa irin motar nan basuda mutunci."
Sam ta manta da kukan da takeyi saboda masifa, tana tafe yayafi na digar mata tana yan mitocinta, sai da ta gama gajiya ligif sannan ta isa gida.

Goggo kuwa duk ta kasa zama saboda tsoro ganin yanda ake ruwa ga har yanzu bata dawo ba.
Tana shiga Goggo ta kalleta cikin tsananin tausayawa.
Jalila fadawa tai jikinta duk da jikarta ta sa kuka, idanun Goggo suka ciciko sai kanta kawai da take shafawa.
Jalila ta dago tana kuka tace ""Goggo Allah nasan da sanin Safeena, ai tasan ban taba tahowa ba."
Goggo tace "Kiyi hakuri"
Jalila tace "Goggo sai yaushe ne zaki daina cewa inyi hakuri? Gaba daya rayuwarmu ni dake a hakuri ta kare, nikam ina takaicin cewa ma Dadyne mahaifi......."
Marin da Goggo ta mata ne yasata yin shiru, kallan Goggo tai kuncinta a rike,Goggo ta kalli hannunta cikin dana sani sannan tace " taya zaki dinga kushe abinda Allah ya hada?"
Jalila tace "kiyi hakuri Goggo bazan kara ba"
Hannunta ta kamo tace " na sani, na sani sosai abinda ke ranki Jalila sai dai bayanda zamuyi da hukuncin Allah, sannan komai zaiyi ko kowa zai zageshi to lalai banda ke, domin shine silar zuwanki duniya."

Tace "Na daina Goggo kiyi hakuri."
Goggo tai murmushi tace " yi maza ki cire kayanki."
Mikewa tai ta shiga dan dakinsu.

Tana cire kaya tai sallah sannan ta mike tace "Goggo bari naje"
Goggo tace abinci fa? Naga da safe ma a tsatsaye kikaci, shiyasa kullum gakinan kamar a hure.
Tace " Goggo in na dawo naci" tace ban yarda ba sai dai ki tafi dashi can kici, ina zaki jira sai wajen magrib kici abinci?
Jalila tai murmushi sannan tace " to in na gama ma rana zam deba inci a namu."
Goggo tace "kin tabbatar?"
Tace eh karki damu Goggo na

Tana isa ta tadda Safeena a falo tana kallo, wata banzar harara ta maka mata sannan tace " da kuka taho kuka barni sai kuma gashi mai rai da lafiya yayo gida da kansa."
Safeena tace " au da gaske kina can dama? Ni danaga ana zabga ruwa sai naga ina mai hankali zai tsaya a cikin ruwan nan?"
Jalila tace " mai hankali kikace ai ni kuwa ina na ganshi?"
Ta karasa maganar tana harararta, jitai ance " Uban wa ya baki damar cimata mutunci?"
Gabanta ne yai wani irin faduwa, duk gidan ba wanda take tsananin tsoron ya mata fada irin Inna, a tsorace ta kalleta idanunta sun firfito, bakinta ne ya shiga rawa tace "In nn nna......"
Kallanta tai sannan ta kalli Safeena tace " ke kuma Jalila matsayinku daya da zaki dinga zama tana fada miki kalamai irin haka?"
Jalila ta hadiyi wani miyau me daci tace " in na bahaka bane......."
"Dake nake magana?"
Jalila gabanta sai faduwa yakeyi.
Sultan ne ya fito daga kitchen rike da jarkar ruwa na faro yace " Inna ita Safeenar itace da laifi bai kamata ku dinga yanke hukunci ba tare da bincike ba."

Kallansa tai tace " Sultan shiga daki"
Baice komai ba ya wuce ciki, Jalila kuwa kamar wacce aka tsunduma a wani ruwan haka takeji, muryar Dady ne ya ratsa falon wanda maganganu Inna ne suka sa shi fitowa, da sauri yace "Hajiya ki mata afuwa ni zan hukuntata da kaina."
Kallansa tai a wulakance tace " kai har wani hukunci zaka iya? Ka saisaita yarinyarka in ba haka ba daga ita har uwarta zasu bar gidan nan, karka kuskura ka manta gida da dukiyar wanene kake mora daga kai har su."
Mumy ce ta rike hannunta tace " Kiyi hakuri ki bari dan Allah."
Ta fada tare da jan hannun ta zuwa dakinta.
Suna shiga tace "Inna sai yaushene zaki daina disga Abakar cikin yaransa? Karfa ki manta 'ya'yansa sunanan kuma suna jin zafin abin."
Kallanta tai tace " ke meyasa bakida hankaline? Kin nace sai kin aureshi dake da mahaifinki, bakya tunanin wannan cin mutuncin da nakemai shine dalilin da yasa yake nuna miki kulawa haka?"

? Tace " Wlh Inna ke kike ganin haka Abbakar na sona kamar yanda nake sansa, dan Allah ki daina wulakantashi."
Ta karasa maganar cikin lalashi.

A falo kuwa Dady a zuciye ya sa hannu ya fizgo Jalila ya kaita kitchen, cikin fada yace " sai yaushe ne zakiyi hankali kisan darajarsu Safeenan kikeci ke da uwarki?"
Kallansa tai cikin rawar baki tace " Dady itace........"
Cikin tsawa yace " so kike in fasa miki baki? Ko me ta miki bazaki hakura ba? Shashashar banza to wlh ki bala'in shiga hankalinki in har kinaso mahaifiyarki dake ku zauna a gidan nan."
Yana gama magana yai falo, yana shigowa Safeena taje da gudu da rungumeshi.



**************

?? Yana shigowa cikin gidan ya tadda mahaifinsa a zaune a falo, karasawa yai ya gaidashi sannan ya fara kokarin mikewa.

Mahaifinsa yace "Hassan!"
Komawa yai ya zauna tare da kallansa, Abba yai ajiyar zuciya sannan yace " Baka manta badai karshen satin nan zamu koma asibiti ko?"
Hassan ya kalleshi yace "Abba please ka hakura
Abba cikin kulawa yace " Ka taba ganin inda uba ya hakura da dansa? Karka damu insha Allah da yardar Allah wannan matsala taka zata warware sannan zaka samu sauki cikin yardar Allah."
Kallan mahaifinsa kawai yake shidai sun kasa fahimtarsa, mikewa yai baice komai ba zaiyi gaba.
Kaninsa ne ya dafashi yace " Yaya kace Ameen mana ko hankalin Abban zai kwanta?"
Ummy ya kalla wacce ke tsaye ita da Ameerah yai shiru sannan a hankali yadan motsa baki yace Ameeen.
Murmushi sukai dukansu m, Sagir ya dafashi yace " Ko kai fa Yaya."
Hannunsa yasa ya ture nashi daga kafadarsa yai wuce, Ummy tabi bayansa da kallo sannan ta kalli Ameera.
Kai Ameera ta daga sannan tai kitchen.
Faten dankali wanda Ummy ta masa ta zubo a plate sannan ta dau spoon ta fito, sama ta hau sannan ta shiga dakinsa.
Yana zaune a kasa kan carpet ta shiga.
Gabansa ta ajiye abincin sannan ta ce "Yaya abinci."
Kallanta yai yace " BAna......"
Tace " Na sani yaya baka jin yunwa dama ko da yaushe zancen kenan, sai dai Yaya ka ci ko dan Ummy ta samu sukuni a ranta."
? Yace "Naji zanci, ke kuma fita."
Ta mike tace " to"
Waje tai sannan ta turomai kofar.


#OneLuv=ؕ?

=??? *JALILAH* =???

Written By : *AYUSHER MUHD*
Wattpad: *AyusherMohd*

_Gaisuwa mai yawa tare da fatan alkairi a koda yaushe gareki Aunty na ta kaina.....Aunty Goggo Allah ya kareki ya ja da ranki=?
? much luv Sister_

? ? ? ? ?? *No 4*


?? Da kyar ya tura abincin sannan ya mike ya shiga bandaki, wanka yai tare da dauro alwala.
Jalabiya ya zura ya tada sallah, ya dade sosai akan sallayar yana mika rokonsa gurin Allah sannan ya kwanta a kasa, a takure ya kwanta , sam baisan sanda bacci yai gaba dashi ba.
Ummy ce ta leko ta ganshi yana bacci, kusa dashi taje ta zauna tana kallansa cikin tsantsar so da kulawa da kuma tausayi, jan numfashi tai sannan ta mike ta dau tiren abincin da yaci tai waje.

? Gab da magrib yana bacci yaji kamar ana shakemai wuya, wani irin mumunan mafarki yakeyi wanda ya shiga sandarewa yana kankake jikinsa, idanunsa a runtse sai wani irin zufa da yake kwaranya daga jikinsa, numfashinsa ne ya shiga hawa da sauka, shure shure ya shiga yi saboda tsananin azabar da yake fuskanta.

? Har zai shiga dakinsa yaji alamar m??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????otsin Hassan, da sauri Sagir ya tura kofar, ganin Hassan a kankame yasa yai saurin shiga dakin, tabashi yai yana cewa Hassan! Yaya!
? A firgice ya bude idanunsa tare da jan wani irin numfashi, Sagir ya dagashi zaune yace "in kawo ma ruwa?"

? Hassan ya daga kai, da sauri ya mike ya dauko mai ruwa,? amsa yai ya lafa bakinsa, sai dayasha sosai sannan ya kalli Sagir ya mikamai jarkar.
Sagir ya amsa sannan yace "akwai abinda kake bukata?"
Kai ya girgiza alamar a'a.
Cikin tausayawa Sagir ya kalleshi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login