Showing 36001 words to 39000 words out of 149705 words

Chapter 13 - Jalilah Book One Complete Hausa.doc

Ayusher   

28 Oct 2025

644

tace "tunda ance yana da matsala na tabbatar babba ne, kila fa zaikai shekara 40 ko?"

Mumy tai dariya tace "ina na sani? Sai ku bari sai ankai Amarya da daddare sai ku tambayeta."

"40?"

Gaban Jalila ne ya fadi, matsala? Meke faruwa? Duk da tasan dama bazasu taba mata auran mutunci ba amma batai tsammanin babba bane haka, da alama kenan akwai kanne dayawa tsakanin sa da Uncle?"

? A can gun d'aurin aure kuwa, Hassan dakyar ya tsaya aka d'aura auran, ana fitowa hoto d'aya ya daure akai dashi, shima wasu manyan mutanen Abba ne da bayanda zaiyi, sannan Abban na rike da hannunsa.
Ai kuwa suna gama d'auka yai wuf ya tafi.

Sagir kuwa, ba'a magana dan kuwa jiyai kamar an jefamasa katan dutse a sanda yaji sanarwar d'aurin auransu.

? Dole shi ya tsaya aka dinga gaishe gaishe dashi.

Dady sai baza ido yake yaga ango amma bai ganshi ba, Sagir dayazo suka gaisa yake tambayarsa ina Angon?
Sagir yace "Yanzun nan ya dan fita, kansa ne ke ciwo."

Hassan kuwa yana shiga cikin mota ya rufe, jiyai gumi na keto mai ta ko ina, sam hayaniyar nan tasa gaba d'aya jikinsa ya ji gaba d'aya ba dadi.

? Idanunsa ne suka canza kala, kansa ya kwantar akan kujera ya rufe idanunsa.

Firgigit ya farka dan baisan har yadan yi bacci ba, jiyai numfashinsa na neman d'aukewa, nan yasa hannunsa ya rike wuyansa yana kokarin jawo numfashinsa, gaba d'aya jikinsa ya kame, sai uban zufa dake karyomai, idanunsa sunyi jaa sosai, dakyar ya iya jawo numfashinsa.
Nan ya shiga yin numfashi akai akai.

Jinai gaba daya jikina yai sanyi, dan tabbas duk wanda yaga Hassan zai dauka ko Aljanu ne dashi ko kuma hankalinsa ba daidai yake ba, Hassan meke damunka? Abinda zuciyata ta shiga tambaya kenan? Nace masu karatu ku taimaka min.......



#OneLuv=ؕ?
[08/10, 02:15] * +234 803 222 1758, : =??? *JALILAH* =???

Written By : *AYUSHER MUHD*
Wattpad: *Ayusher Muhd*


*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*

(_D home of expert and perfect writer's_=ء?)

*No 22*


Tana zaune a d'aki wajen azahar Mumy ta fara mata knocking.
A kasan kofar take a kwance dan zazzabin dake jikinta mai zafine.
Da kyar ta iya mikewa ta bude kofar, Mumy tace "Jalila ko wanka bakiyi ba? Naga tun jiya na ajiye miki kayan da zaki saka?"
Jalila ta kalleta bakinta na rawa tace " Mumy....."
Ganin yanda idanunta keyi yasa Mumy ta riketa, jitai jikinta ya d'au zafi sosai, tace "Zazzabi kike?"

Jalila tai shiru, hannunta ta kamo tace " Muje Inna ke nemanki, in ta gama miki magana sai ki dawo ki sha magani."
Nan ta rike hannunta suka fito, kallan banza kowa yake mata dan dama duk yan uwan Mumy ne masu tayata kishi da zuga ta.
Haka suka shiga d'akin Inna.
Tana zaune tana duba abu a waya suka shiga, sai data gama sannan ta ajiye ta kalli Jalila, sannan tai dialing number a wayarta tana cewa " magana zakuyi da Goggonki, ki sanar da ita baki da lafiya shiyasa ba zakizo ba."
Kafin Jalila tai kokarin bada amsa, har Inna ta miko mata wayar sannan tasa hands free.
Muryar Sultan taji yana cewa "Inna ina Jalilan? Gani a kusa da Goggon."
Jalila ta daure tace "Sultan ni ce."
Yace "Jalila Goggo na nemanki."
Ya fada tare da mikama Goggon waya.

Goggo na amsa tace "Jalila ina kika shiga?"
Jalila tace "Goggo zazzabi nakeyi shiyasa baki ganni ba."
Tace "ni ai dama cewa nai ki zauna ki huta, amma na rasa meyasa yau hankalina yake a tashe, dafatan ba abinda ya faru?"
Jalila tace "mai zai faru Goggo? Ke dai kawai kice ganina kikeso."
Goggo tai murmushi dan hankalinta ya kwanta tace "kinsha magani?"
"Eh Mumy ta kaini an banni magani."
Goggo tace "Ayya! To ki huta sosai, kar ki damu dani."
Jalila ta d'aga kai, idanunta suka ciciko a ranta tacce "Goggo ga yarki nan ana mata auran dole, auran fin karfi, auran mugunta, auran san zuciya...."

Jin shiru yasa Inna ta kashe wayar sannan ta kalli Jalila, hannunta ta kamo ta rike tace "good girl, karki damu ki kula da mijinki yanda ya kamata, muma zamu kuka da Goggonki yadda ya dace."

Jalila ta share hawayenta tace "Inna dan Allah ku kula da ita."
Inna tace " karki damu kanki, ai Goggo tamu ce, ke dai kiyi abinda muka saki."
Jalila ta d'aga kai alamar to.
Nan Mumy ta kamo hannunta suka fito.

Innata bisu da kallo, tabbas dolene su kula da Goggo sosai, saboda yanzu ne zasu kara bunkasa company ta hanyar Jalila.

Murmushi tai.........

Haka Jalila, Mumy tasata tai wanka, tasha magani, ta sa kaya sannan suka fito tare, gefe guda taja ta zauna.
Dan bata jin dadi, daga baya ma data kula hankalin kowa baya kanta ta zille tai bangarensu.

Kwanciya tai a inda Goggo take kwana, tana tuno rayuwar da sukai a cikin gidan.

Kuka ta shiga yi sosai, wanda ya kara sa mata ciwon kan dake damunta, sai yamma likis tana kokarin fita, Dady na turo kofar.
Kallanta yai jikinsa ne yai wani sanyi, yace "tundazu nake nemanki shine Mumyn Yasmeen tace kila kina nan."
Jalila ta kalleshi bata ce komai ba, kusa da ita ya zauna sannan ya kalli d'akin, yace "kina tuno rayuwa ne?"
Itadai batace komai ba, shiru ne yadan ratsa kafin yace "Jalila kiyi hakuri."
Kallansa tai cikin mamaki, yace "bazan nemi yafiya akan abubuwan dana aikata ba, domin har yanzu bana dana sanin aikata su, sannan abinda na aikata a baya sune suka sani nazama abinda na zama yanzu, sune kuma suka taimaka suka inganta rayuwar zuri'ata harda ke kanki, sai dai zan baki hakuri akan auran nan da aka miki dan kuwa na san bamu kyauta ba, sai dai ko yanzu aka dawo da hannun agoggo baya tabbas abinda zan sake yankewa kenan."

Kallansa kawai Jalila take cikin mamaki, dan ta kasa cewa komai, Dady yai shiru kafin yace "ki taso muje a shiryaki sun ce bayan isha'i zasuzo, dazu akaso kiranki nace a barki zuwa anjima."

Bata ce komai ba ta mike ta fita kawai, dan itakam bata san me zata cemai ba, tana koma tsoron kar bakincikin dake ranta yasa ta fadamai kalamai marasa dadi.

Haka ta wuce bangaren Mumy, wanka aka sata ta sakeyi tai sallah,sannan Mumy ta sata tadan ci abinci wanda cusa wa kawai tai, sannan ta bata magani, kayan da zata saka ta miko mata.

Haka Jalila ta saka kayan nan ba tare da tace kala ba.
Mumy ta mata kwalliya tai kyau sosai, turaruka ta fesa mata kala kala.
Mumy ta fita dan ance motoci sunzo.
Sagir na zaune a cikin mota gaba daya yau banda ruwa ba abinda ya shiga cikinsa, wace rayuwa zaiyi da Jalila a matsayin matar yayansa?

Gaba d'aya shikam yasan rayuwarsa ta gama hargitsewa.
Haka akai ta shiga motoci har aka fito da Jalila aka bude bayan motar da Sagir ya jawo wacce take ta Abba aka saka ta.
Kanta na kasa dan a lulube take da mayafi, tunda suka fito yake kallansu.
Jalila na zama taji yacema Mumy ina wuni?
Gabanta ne ya fadi jin muryar Uncle, shine zai ma kaita? Me yake nufi da ita?
Wani sabon takaici ne ya kara kamata, lalai yau ta tabbatar Uncle ba santa yakeyi ba.

Haka suka shiga motar aka ja, ita kadai ke kukanta, wanda kukan ke taba cikin zuciyarsa.
Haka sukai ta tafiya har suka isa makeken gidan.

Gabanta ne ya shiga faduwa sanda akace ta fito, wai yau itace aka ma aure da wanda ko sani batai ba, ko kawayenta su Zahra basu sani ba, ko Mahaifiyarta bata sani ba.

Haka ta fito, jikinta na kara tsuma wani sabon tsoro da fargabar rayuwarta na kamata.

Sukam mutane kowa ko a jikinsa, Mumy na rike da ita suka shiga.

A gidan kuwa, Ameerra da Aina'u suna zaune a d'akinsu sunyi shiru, Ameera tace "Aina'u inaji ta iso naji guda."
Aina'u ta kalleta cikin takaici tace "Ameera me yasa iyayenmu basa duba abinda ya kamata? Kowa yasan tun ina SS1 nakesan Yaya, ni nace bandamu da matsalarsa ba tunda dai nasan ba hauka gareshi ba, me yasa ba wanda ya duba zuciyata? Ba ruwan kowa da damuwa ta?"

Ameera tai tsaki tace "nima Allah naji haushi, ita wannan din dame ta fiki daya sa su Ummy mantawa da ke?"
Aina'u tai kwafa tace "ni yau ma zan bi Umma mu tafi."
Ameera ta ce "haba dai?"
Mikewa tai ta shiga toilet dan bata san jin gudar nan."

Aunty Nana kam ta baza ido tana san ganin wacece matar Hassan, Ummy ta kalleta tace "Dan Allah karki bude mata fuska sai ta zauna."
Aunty Nana tace "ni rikota kawai zanyi bance wani abu ba."


Haka akai ta hawa sana ana ganin tsarin gidan, kowa sai ya yaba sai dai dayake bakin ciki suke.
Jalila na zaune a kasa, kanta na kasa tana hawaye.
Ummy ta d'agota tace "akaita sama.
Nan Aunty Nana ta taso da sauri ta riketa, haka ta kaita d'akinta sannan ta bude mata mayafi, shiru tai tana mamaki dan gaskiya bata taba tunani.......
Ummy ce ta dafata sannan ta rufema Jalila fuska tace " muje waje."
Fita sukai a falo, Aunty Nana ta riko Ummy tace "kun tabbatar dai yarinyar batada wata matsala ko? Ko halayen banza, kinsan wasu yaran a ido baka ganewa amma a fili sai kiga wasu iyayensu ma sun gagaresu ne."

Unmy takaici ya kamata tace " ba yanzu zaku tafi bane? Naga duk an fara watsewa."
Aunty Nana ta tabe baki tace "ba sai kin kuremu ba."
Haka ta sauko tana mamaki.

? Sagir kam yana maidasu gida yai cikin gari.


? Ummy na zaune sai kiran wayar Hassan takeyi, sai datai ringing har ta katse sau biyu sannan ya d'auka.
Ummy tace "Hassan kana ina?"
Yace "waje."
Tace "ka dawo gida dan Allah, kaga duk an watse sannan an bar yarinya ita kadai tun dazu."
Yace " to in ina nan ma me zan mata?"
Ummy tace "nidai ka dawo yanzu."
Ta katse wayar tana kallan Abba wanda ya shigo yanzu.
?? Hassan na ajiye wayar yau shiru, can ya tada motarsa ya taho gida.


? Jalila na zaune gurum ba kowa a d'akin, har ta gaji da kukan tayi shiru, sai dai fuskarta a rufe take.

Ummy ce ta fito daga daki ta shiga dakinsu Ameera ta kalleta tana assignment, tace "Ameera tashi kije gun Yayarki kafin Hassan ya dawo."
Ameera ta turo baki tace "inje in mata me?"

Ummy ta hade fuska hakan yasata mikewa ba tare da ta kara cewa komai ba.

? A zaune take akan gado Ameera ta shiga, sallamarta ta amsa.
Ameera ta shiga dakin tana cewa "ki cire mayafin kisha iska tunda ba kowa."
Jalila tace " bakomai hakan ma"

Ameera ta zauna akan kujera tana latse latse waya.

Haka suka zauna shiru kamar ba kowa a dakin.

Sai wajen karfe goma da rabi dan har Jalila ta fara gyangyadi, taji karar bude kofar dakin.

? Ameer ta mie da sauri tace "Yaya."
Kallanta yai sannan yai mata murmushi.
Mikewa tai ta fita, Ummy ta gani a kasan beni tace "ina ya shiga?"
Tace "dakinta."
Ummy tai ajiyar zuciya dan sai data mai magana yanzu akan lalai fa dakinta zai shiga ba nashi ba.

? Zama yai akan kujerar da Ameera ta tashi, sannan ya kalli inda take a zaune, bai damu yasan yanayinta ba, balle kamaninta.
Ita kuwa tunda taji Ameera tace "Yaya!"gabanta ke faduwa.

? Dakin ya sake yin wani shirun, jitai wuyanta yana neman sagewa.
Hassan ya kara kallanta, batada niyyar yaye mayafin ne ko me?
Ba dai aikinsa bane?
Daga inda yake yace " ki zare mayafin ki kwanta inkinyi sallah, in bakiyi ba ki tashi kiyi."

Abinda ya fada kenan, ya mike zai fita.
Har ya bude kofa zai fita sai idanunsa suka kalli ledar da Abba ya bashi.
Kara maida kofar yai ya rufe, ita kuma ta dauka ya fita ne jin rufa kofa sau biyu.
Yaye mayafin tai sannan tai wata ajiyar zuciya.

Idanunta ne ya sauka a cikin nasa, gabanta ne ya shiga faduwa, sai dai yanda yake kallanta yasa ta kasa dauke idanunta.
Kamar yasan fuskar nan, a ina?
Idanun Jalila ne suka firfito, juya baya tai da sauri.

Hassan ya matso ya d'au ledar ya mika mata.
Ganin bata ganinsa yasa ya ajiye a kasa ya juya.

Jalila tana jin ya fita ta juyo tare da ajiyar zuciya.

Hassan yayi shiru a dakinsa yana tunani, ina ya santa?
Wayar Ummy ce ta shigo, kallan wayar yai hartai ringing uku sannan ya d'aga tana neman katsewa.
Tace "kana ina?"
Yace "Ummy."
Tace "in har kanason na samu bacci ka koma gun yarinyar nan, haba Hassan taya zaka bar yarinya ita kadai bako tausayi?"

Hassan yace "Ummy kinsan fa bana iya kwana da kowa."
Bata ce komai ba ta kashe wayar.

Kansa ya dafa cikin takaicin wannan abin......


#OneLuv=ؕ?

[08/10, 02:16] * +234 803 222 1758, : =??? *JALILAH* =???

Written By : *AYUSHER MUHD*
Wattpad: *Ayusher Muhd*

_Gaisuwa Gareku 'yan Jalila Fans, nagode sosai, ba shakka ina alfahari da yanda kuka cika grp din cikin lokaci kadan.....Thanks for the love_

*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*

? (_D home of expert and perfect writer's_=ء?)

*No 23*

?? Har yasa hannu zai bude dakin nata, sai kuma naga ya maida hannunsa, komawa yai d'akinsa, yana shiga ya rufe.
Bandaki ya shiga yai wanka sannan ya kwanta.

? Jalila kuwa tayi gurum a d'aki, tana nan a zaune, da kyar ta iya tashi tai fitsarin da ya matseta.
Shiru tai tana tunanin abinda ke faruwa, Goggo!
Hawaye ne ya zubo mata, haka ta kishingida a kan gado har bacci yai gaba da ita.
? Zazzabi ne ya kara hawa mata, wajen asuba ta farka.
Haka tai ta karkarwar sanyi har aka shiga sallah, da kyar ta mike tai sallah sannan ta samu ta kara kwanciya.

?? Sai wajen karfe 10 Ummy ta turo Ameera dan kai musu abincin safe.

Yanda taga Jalila ne yasa tasan ba lafiya ba, a ranta tace ko first night din ne?
Ameera ta daure ta mika mata tiren tace "Ga breakfast dinku."

Jalila kuwa da kyar ta iya cewa "Banajin yunwa nikam."
Yanda taga Jalila tayi ne yasata saurin cewa "Lafiyarki kalau kuwa?"

Jalila tace "bana d'anjin dadi ne."
Cikin mamaki Ameera tace "ina yayan?"
Jalila ta girgiza kai alamar bata sani ba.

? Da sauri Ameera ta ajiye tiren ta sauka kasa da gudu.
Ummy na zaune akan dinning itada Sagir tana tambayarsa menene dan ta kula jiya sai dare sosai ya dawo, sannan yanzu ma taga yana kokarin fita shine ta sashi zaman cin abincin dole.
Ameera ce tazo da sauri tace "Ummy batada lafiya fa."

Ummy tace "wa? Jalila?"
Sagir ne ya mike da sauri, a rikice ya haura saman.
Tana kwance sharkab a kasa hankalinsa yayai mugun tashi, har yakai hannu zai dagota sai ya fasa, da sauri ya fito yana yina Ummy magana da karfi.
Ummy kizo, Ummy.
Ummy da itama take ta sauri ta shigo d'akin hankalinta a tashe.
A kasa suka ganta.

Ummy ta rungumota jikinta, zafin da jikinta ya dauka ne yasa hankalinta ya tashi.
Ta kalli Sagir rai a bace tace "buga mai kofa."
Sagir ya mike ya nufi dakin Hassan.

Yana kwance akan sallaya yanajin lecture na Sheik Ahmad Deedat, jin knocking yasa ya mike ya bude kofar.
Sagir ya kalleshi yace "kazo."
Haka kawai yace ya juya, bai musa ba yabi bayan Sagir, gani yai ya shiga d'akin sa na da.
A bakin kofar ya tsaya, Jalila ya gani a kwance a jikin Ummy.

? "Ummy!"
Kallansa tai rai a bace tace "Hassan me kenan?"
Yace "me ya faru?"
Sagir ta kalla, tace "Sagir muje akaita asibiti."
Sagir da sauri yai waje, duk ya rikice, gani yake kamar duk laifinsa ne.
Ummce y ta kalleshi tace "ni zan kaita mota?"
Karasowa yai ya d'agata.
Jin an d'agata yasa ta bude ido a hankali, kallansa kawai tai sannan ta maida idan ta rufe dan wani irin jiri take ji.

Shikam fuskar nan a hade ya ajiye ta a bayan mota.
Ummy ce ta fito itada Ameera ta kalli Sagir tace "Sagir ku kaita asibitin, sai muje ya ake ciki."
Yace to, sannan ya shiga mota.

Ko kallan Hassan batai ba ta juya ciki.
Sagir ya kalleshi yace "Yaya mu tafi?"
Yace "kuje ni banasan asibiti ka sani, amma me ya sameta?"

Ameera tace "Yaya aikai za'a......"
Kallan daya mata ne yasa ta guntse maganar ta, juyawa yai kawai yai ciki.
Sagir ya kalli Jalila dake cikin mota, shiga motar yai yaja suka fara tafiya.
Ameera tace "muje Standard tunda yafi kusa."
Bai musa ba ya wuce, Ameera ta kalleshi tace "Yaya menene? Naga hankalinka a tashe."
Kai ya girgiza kawai baice komai ba.
Shiru sukai har suka isa asibitin.
Ameera ce ta kamata suka shiga ciki.

Sagir yaje a ciro musu file, yace Ameera ta zaunar da Jalila.
Jalila ta kalli Ameera tace "Dan Allah zan hau sama."
Ameera cikin mamaki tace "me zakiyi?"
Jalila tana numfashi sama sama tace "Dan Allah ki rakani."
Ganin yanda ta damu yasa ta rike hannuunta suka hau sama.
Suna zuwa kusa da dakin Goggo, Jalila ta zare hannunta daga cikin na Ameera sannan ta tura kofar d'akin.

? Goggo na kwance tana bacci, Jalila ta shiga.
Ameera cikin mamaki itama ta shiga d'akin ta tsaya a jikin kofa.
Jalila ta karasa kusa da gadon Goggo sannan ta riko hannunta.
Wasu hawayene suka taho mata, Goggo ta bude idanunta jin an riketa, kallan mamaki tama Jalila tace "Jalila kece?"
Jalila tace "in ba ni ba wacece Goggo na?"
Goggo tai dariya tace "wato dana ce ki zauna a gida ki huta kasa zama kikai ko?"

Tace "ina zan iya zama banganki ba?"
Goggo ta kara riko hannunta da sauri ta mike zaune sannan tasa hannunta a goshinta tace "Jalila! Bakida hankali ne? Kina irin wannan zazzabin kika fito?"

Jalila tai murmushin yake tace "karki damu Goggo ba wani wahala yake ban ba."
Goggo tace "ga wanda bai kalleki ba kenan, duk kin rame a dan kwana biyun da ban ganki ba?"

Jalila tai kasa da kanta.
Ameera ta kalla sannan ta kalli Jalila, tace "wannan fa?"

Ameera ta matso ta gaisheta sannan tace "

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login