Showing 54001 words to 57000 words out of 149705 words

Chapter 19 - Jalilah Book One Complete Hausa.doc

Ayusher   

28 Oct 2025

643

sauka, bata falon sama shiyasa ya wuce kasa.

A kitchen ya hangota, ita da Ummy da alama wanke wanke suke.
Tsayawa yai yana kallansu, bai san me take cewa ba yaga Ummy na dariya.

Matsowa yai yana san yi mata magana, kuma bazai iya ba.
Juyawa kawai yai yana neman komawa sama, Sagir yace "Yaya kaine a falo?"

Hassan ya kalleshi sannan ya juya zai hau sama, Jalila najin ance Yaya ta juyo da sauri tana hangoshi ta tsame hannunta a ruwan dauraya tai gunsa da sauri.
Ko bi takan Sagir batai ba tasha gaban Hassan tace "Yaya ina zaka?"
Kallanta yai yace " fita ma inzanyi sai an tambayen?"

Tace "au yahkuri, in fito?"

Juyawa yai ya fita waje bai bata amsa ba, da? gudu ta haura sama ta dauko hijabinta, da wayarta.
? Da gudu ta fito ta sauko, Sagir kallanta kawai yake, Ummy da mamaki ya sa ta tsaya tana kallansu, Jalila ta karaso gunta tace "Ummy zamu fita, na tafi karya fasa."

? Ummy mamaki yasa ta kasa ma magana, yau Hassan ne zai kai wani unguwa?
Kallan Sagir tai da sauri wanda yai shiru yana kallan Jalila wace yaga ko kallansa batai ba tana zumudin fita da miji.

? Ummy tace "Sagir ka ga Hassan?"
Kallanta yai ya kakaro murmushi yace "naganshi Ummy, ni kaina mamaki nake."
Ummy ta fadada murmushinta tace " Sagir da alama Hassan ya fara canzawa, ko?"
Sagir ya jinjina kai yace "sosai Ummy."

Ummy ta juya cikin tsananin farin ciki.

Jalila kam da sauri ta bude gaban mota inda yake ta shiga.

Tana hakki, Hassan ya kalleta yace "meye hakan? Gudu kikai?"

Tace " tsoro nake karkai zuciya."

Hassan ya tada mota ya ja, suna tafi motar shiru ba komai sai sanyin AC din da ya kunna, ita ta dinga nuna mai hanya da suka shiga unguwar.

Suna zuwa kofar gidan tace "nan ne, amma yaya kana tunanin zasu nuna mana inda Goggon take?"

Bai kula taba yai? horn, mai gadin gidan ya fito da sauri ya leka ganin Jalila yasa ya koma ya bude.

? Shiga sukai yai parking, sannan ya kashe motar ya kalleta yace "ki shiga."
Juyowa tai ta kalleshi tace "in shiga?"
Yace "ko ni zan shiga?"
Tace "a'a ban dai fahimceka bane, ba tare zamu ba?"
Yace " a yaushe mukai hakan dake?"

Jalila ta tsaya tana kallanshi tace "Yaya kaifa kace zaka taimaken."
Yace "a yaushe kenan?"
Jalila yanayin fuskarta ya canza tace "Amma....."
Yace " ki shiga ku gaisa, in kuka bakida niyya mu juya."

Kallansa tai tama rasa me zatace " Hassan ya dau wayarsa yana duba abu."
Idanunta ne suka ciciko ta bude motar ta fita, ta nufi gidan zuciyarta a dagule.
Amma mutumin nan anyi mara mutunci.

Shikuwa yana kallanta har ta shiga.

Dady na zaune yana hada wasu takardu yana waya ta tura kofar tare da yin sallama.

Dady ya juyo jin muryar Jalila.
A daidai lokacin Mumy ta fito ita da Yasmeen, Mumy na rike da plate dake dauke da kayan marmari.
Da yake yau asabar ba aiki.


Kallanta sukai sai suka zubo mata ido, Yasmeen ta rugo da gudu ta rungumeta tana mata oyoyo.
Jalila ta kalleta tace "My Yasmeen ya makaranta?"

Yasmeen ta rike hannunta tana zuba mata shagwaba, nan Jalila ta dauketa.

Dady ya kalleta yace "Jalila! Kece?"

Mumy ma tace "Jalila shigo mana."
Jalila ta shigo jiki a darare ta zauna a kasa, tana gaidasu.

Mumy ta amsa sannan tace "banyi tunanin ganinki ba daga aure."
Jalila ta kalleta sannan tai kasa dakai ita duk ta rasama me tazo yi.

Knocking din kofa sukaji, Dady ya kalleta yace " bake kadai bace?"
Kallan kofar tai da sauri tana cewa "eh tare muke."

Mamaki tai dataga Dady ya mike da sauri yana kallan Mumy yace "yi maza kinsanar ma Inna."
Mumy tai sama da gudu.

Jalila ta tsaya kallan ikon Allah, Dady ya bude mai kofa.
Hassan ya kalleshi sannan yace "sannu."
Dady ya washe baki yace "shigo mana."
Hassan ya shigo tare da zama akan kujera.

Dady ha zauna a dayar kujerar yana cewa "ai bamu san tare kuke ba, ke kam Jalila bakyaji akan me da kika shigo baki sanar mana ba?"
Hassan ya kalleshi sannan ya kalli sama wanda yaji alamar saukowar mutane.

Matan biyu daya gani a gidan su yau ma su ya gani.
Kallan Dady yai yace " tanata damuwa akan rashin lafiyar mahaifiyarta shiyasa nace bari muzu."

Turus Inna da Mumy sukai akan kasan beni, Jalila ma da sauri ta kalleshi, Dady yace "naam? Me kake nufi?"

Hassan ya zubawa su Inna ido yace " Jalila a ina Goggon take? Dan nasan bata cikin su."
Ya fada yana nuna su Mumy da kai.

Inna wace ranta yakai koluwa gun baci, ta kalli Jalila tana jiran me zatace, Jalila kuwa tayi mamakin kalamansa dan bata taba tunanin haka zai bulo musu gatse gatse ba.

Hassan ya kallesu yace " Ina wuni?"

Inna bakinta na dan rawa tace "Lafiya."
Hassan ya mike ya kalli Dady yace " dan Allah a ina take? Ina sauri ne."

Dady baki na rawa ya kalli Mumy da Inna yace "tana primer."
Yace "wani dakin?"
Dady ya kalli Mumy yace "wani dakin ne ma?"
Tace "hmm...."
Hassan ya kalli Jalila yace "muje ko?."

Jalila tai sakato tana kallan ikon Allah.
Ganin yana neman fita yasa ta mike da sauri kar a rufeta da duka tai waje.

Suna shiga mota ya ja yai gaba.

Jalila ta zubamai ido tana nazari akansa, can tasa wata dariya tace "Yaya kaga idon Inna kuwa?"
Kallanta yai yace "wacee hakan?"

Jalila tace "kaka ta? Ahh ba kakata ba kakar su Yasmeen."

Hassan bai kula ta ba ya juya yana tuki, ita kuwa in ta tuno yanda sukai sai ta kara sa dariya.
A haka har suka isa, suna shiga ya nemi a duba musu sunan Goggo.

Nan wata nurse ta wuce dan nuna musu dakin, Hassan ya kalleta yace "ina mota."
Da sauri ta riko rigarsa ta kasa tace "mota?"
Kallanta yai, tace "dan Allah kuje ka gaidata. Batasan anmin aure ba fa?" Ta fada tare da canza fuska xuwa tausayi......


#Oneluv=ؕ?

=??? *JALILAH* =???

Written By : *AYUSHER MUHD*
'ote me on Wattpad : *Ayusher Mohd*


? ?? *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*
? (_D home of expert and perfect writer's_=ء?)


*33*


Hassan ya kara kallanta yace  kina nufin in shiga ciki?
Ta daga kai, ya kara kallan asibitin, batasan nan ma dakyar ya shigo ba?
Jalila ta kalleshi tace  Yaya!

Kallanta yai sannan ya fizge rigarsa ya juya.
Binshi tai har jikin motar ta tsaya a jikin kofar inda yake tace  Dan Allah yaya kazo muje.
Kallanta yai yace  wai meke damunki? Ana abu dole ne?

Tace  i am really scared
Kallanta ya sakeyi, tace  bansan a wani hali zan sameta ba, bansan me zance mata ba in ta tambayeni, Yaya dan Allah kazo muje.

Oh God! Wannan wace irin yarinya ce? Yace  to in naje ta tambayeki wanene ni me zaki ce?

Kallansa tai sannan tai shiru, yace  ki je ki fito in kuma in barki anan ne sai ki zauna sai dare.

Jalila ta kalleshi tace  zan zauna anan din.
Yace  ur choice.
Sannan ya kalleta yace zan rufe kofa.

Jiki a sanyaye ta matsa daga jikin motar, ya ja yai gaba, ta glass din mota ya hangota tana tsaye inda ya barta.

Bazai iya shiga ciki ba dan shikadai yasan memory din da yake dawomai in ya shiga cikin asibiti gun marasa lafiya.

Jalila ta juya jiki a sanyaye, tana shiga nurse din ta tareta tace  ina yayan naki?
Jalila ta kalleta tace  a ina Goggon take?
Nan tai gaba Jalila ta bita a baya.

Goggo na zaune akan gado, ba laifi kafar tata ta samu sauki sosai, tana shiga tai gunta da gudu ta rungumeta ta saki wani irin kuka.
Ita ma Goggon kuka ta saka, sun dade a haka kafin Goggon ta daure tace  Jalila ina kika shiga?

Jalila ta dago ta zauna kusa da ita tace Goggo na.
Goggo tasa hannu ta share mata kwalla tace  kukan ya isa hakanan, me ya faru? Ko jikin naki ne?

Jalila ta kalleta tana girgiza kai tace  ba komai Goggo na, ya jikin naki?

Goggo ta kalleta kallon tuhuma tace  Jalila kin tabbatar? Dan nikam tsoron mutanen nan nakeyi.

Hassan har ya fara tafiya naga yayi kwana da motarsa ya dawo asibitin, bude kofar motarsa yai ya fito sannan ya nufi asibitin.
Nurse din tana ganinshi ta taho inda yake, tace  ka dawo?

Hassan yace tana ina? Nan Nurse din ta fara tafiya yana binta a baya.

Suna taka steps din gaba daya kawai takawa yake, suna zuwa second floor yaji kansa ya fara juyawa, da sauri ya rike bango, sannan ya tsaya ya rike gefen zuciyarsa.

Wani irin numfashi yake fitarwa, juyawa yai da sauri ya sauka kasa, nurse din ta juyo kawai taga bayanan.

Hassan ya sauka da sauri ya shiga mota ya ja ya rufe ya fita da gudu.

Sai da yai nisa sannan yai parkin ya kifa kansa akan sityarin motar yana maida numfashi.

Jalila tai murmushi tace  Allah Goggo ba komai, kawai dai ina bakin cikin laifin dana miki ne.
Goggo tace  laifi?
Jalila ta kwantar da kanta akan cinyarta tace  ni dai ki yafemin Goggo na.
Goggo ta shafi kanta tace  ba abinda kika min Jalila, na tabbatar ko da kin min ba daidai ba sai dai a rashin saninki ko kuma tirsasaki akai, kawai dai inaso kisan ke kadai ce dani a duniya

Jalila ta share kwallar data gangaro mata tace  tsoron sanar dake nakeyi.

Goggo tace  ko menene ki fadamin.
Jalila tai shiru can tace  zan fada miki amma sai kin warke an sallameki.
Goggo tai murmushi tace  shikenan, da alama akan Sagir ne.

Jalila tai murmushin yake batace komai ba.

Haka ta zauna makale da Goggonta, Lantana na gefe tana kallansu gwanin sha awa.


*************

Su Hassan na fita Inna ta matso kusa da Dady ta daga hannu ta sharara mai wani wawan mari, da sauri ya kalleta dan sam baiyi zatan abinda zatamai ba kenan.

Mumy ta matso da sauri ta tsaya agan Inna tace  Inna menene hakan?
Inna cikin takaici tace  Uban wa yace ka fadi inda take?
Dady ya kalleta ransa a bace takaicinsa agaban Yasmeen dan wulakanci.

Mumy ta kalleta tace  Ta ya bazai fada ba bayan yaran yasan komai, da alama Jalila ta gama sanar dashi duk abinda ke faruwa?

Inna cikin kunar rai ta zauna akan kujera tace  Akace bashi da hankali?

Mumy ta zauna kusa da ita tace  dama
Bakiyi bincike ba?

Inna tai shiru kafin tace  muna cikin tashin hankali, idanun yaran nan ba tsoro ko fargaba a ciki sannan da alama baya ragama wanda ya tabashi, me kuke tunanin zai faru in yasan abinda akama matarsa? Sannan canjen da mukai muka bashi Jalila a maimakon Safeena?

Mumy ta kalli Dady tace  Dadyn Yasmeen!

Dady ya kalli Inna wacce ke kallansa yace  hakan bazai faru ba, ni da kaina zan sanar da ita karta kuskura ta sanar dashi komai, kuskuren sanar dashi Mahaifiyarta datai ya isa.

Inna ta jinjina kai tace  u have to take care of her, in ba haka ba ni zan bulo mata ta bayan gida, zan sata dana sanin da bata gaba yi ba daga ita har uwarta.

Dady yace  insha Allahu baza a sake ba.
Mikewa tai ta hau sama.

Tana tafiya ya mike a zuciyd ya shiga dakinsu.


Mumy ta bishi da sauri tare da rungumeshi ta baya tace  Darling.
Hannunsa ya zare yace  meye hakan? Kina abu kamar yarinya?

Ta kara kankameshi tace  Dadyn Yasmeen am sry.......

Kallanta yai kamar zaiyi fada, da sauri ta sumbaceshi...........

*************

Ummy ce ta kalleshi tace  ina zakaje da har kake san in wakilceka akan taron da yake da mahimmanci?

Yace  Abuja zan koma dan akwai abu mai mahimmanci da nake sanyi.

Ummy ta kalleshi tace  yafi wannan mahimmanci?
Abba yai shiru yana duba abu a computer sa.

Ummy tace  ni na kasa gane abinda bazaka iya fadamin ba
Cikin zafin rai yace  wai meke damunki ne? Dolene ko wani abu na rayuwarta sai na sanar miki?

Da karfi ya budo kofar wanda ya sa suka kalli kofar a tare, kallan Abba ya shiga yi idanunsa sun canza sosai.

Yanda yake kallan Abban ne yasa Ummy ta matso da sauri ta sa hannu ta riko hannunsa tace  Hassan meye hakan? Taya zaka banko kofa haka bako sallama?

Idanunsa na kan Abba haryanzu wanda gaba daya Abba ya gama shan jinin jikinsa.
Hassan ya daure yace  mekenan?

Ummy tace  mekenan kamar ya?

Hassan bai kalli Ummy ba idanunsa nakan Abba yace  me Ummy tai da har kake mata fada haka?

Ummy tasa hannu da karfi ta turashi waje sannan ta fito itama, ta rufo kofar sannan ta kalleshi tace  muje.
Ta fada tana jan hannunsa, dakyar ya hau saman sannan ya kalleta cikin takaici yace  Ummy me kika mai yake fada haka?

Tace  ba abinda yamin nice namai lefi shiyasa yakemin fada akan abinda nai.

Kallan ta yai dan shikam bai yarda ba, to ko laifin ma tamai taya zai hauta da fada haka? Ummy ta kalleshi tace  Ina Jalilan?

Yace  Ummy kin tabbatar ba abinda ya miki?
Tace  sau nawa kake so na fada ne? Ina tambayarka Jalila, badai ajiye ta kai a hanya ba?

Yace  Tana nan, kawai ya wuce dakinsa.
Zama yai a bakin gado yana tunani, dolene ko wani abu na rayuwata sai na sanar miki?
Kallaman Abba ne ya sake dawo mai, meke faruwa?

Ummy tana sauka ta koma dakin, Abba ya kalleta yace  me kika cemai? Tace  kome nacemai bana tunanin nima ya zama dole in sanar dakai.

Abba ya matso kusa da ita yace  Ciwon sa fa? Ya tashi?

Ummy ta kalleshi tace  kaje ka duba.
Ta matsa daga kusa dashi.

Abba yai shiru yana tunani sannan ya koma ya zauna agefen gado.

***********

Bayan magrib yana zaune yana karatu, naga ya rufe littafin ya sauko zuwa mota.

Kallo daya zakamai ka fahimci yana cikin bacin rai tsantsa.

A asibitin yai parking sannan ya fito, duk yanda yaso ya duba Nurse din a reception din bai ganta ba.

Kawai komawa yai mota ya zauna, ya kwantar da kansa akan kujera.

Jalila kam sunata hira da Goggo taga isha i tayi.
Wayarta ta dauko tana dubawa ko zai kirata, ta ina zai kirata? Bayan bashi da numberta? Itama haka.

Ajiyar zuciya tai sannan ta ajiye wayar.

Goggo ta dau wayar tana kara kallo tace  gaskiya wayar nan tayi kyau ta birgeni, mahaifiyar Sagir ce?

Tace  Hmm.
Goggo tai murmushi tace  karki damu ina warkewa zansa ya turo ai auran.

Wani film akeyi a tv dake dakin, saurayin ta na waje yana ta jiranta ita kuma bata sani ba tana cikin gida suna ta hirar su
Mikewa tai ta dau hijab dinta tace  Goggo ina zuwa.

Ta fito, tana tafe tana cewa kai inaa.... ta ya zai zauna jirana? Au ko bai san inda nake ba na tabbatar zai sa a nemi ni.

Tana fitowa kawai ta hango motarsa, mamakinne ya kamata ta karaso gun motar a ranta tana cewa  kai.... ba shi bane, kanta tasa tana leka motar.

Hassan na kwance ya bude idanunsa, gani yai ana leko cikin motar, tunda akwai haske fitulun waje.

Hassan ya zuge glass din motar yace  meye hakan?
Tace  kai!!!! Kaine da gaske, me kake anan?

Yace  me nake kuwa, bakisan wannan shine hubby dina ba?
Tace  zama a mota?

Bai tanka mata ba yace  muje?

Tace  bari nama Goggo salama, Yaya bazaka shiga ba?

Kansa ya kawar gefe.

Ta fita ta ma su Goggon salama, goggo ta bita da kallo tana tunanin tabbas akwai wani abun, Jalila bazata taba zuwa ta tafi a aranar ba.

Jalila ta shiga mota ya tada suka fara tafiya, yanda taga yanayin fuskarsa ne yasa tai shiru dan taga ba alamar wasa.

Can ta kasa daurewa tace  Yaya nagode.

Bai kalleta ba yace  4 wat?
Tace  taimakon da kamin.

Shiru sukai sai tafiya kawai da yakeyi, can tai murmushi cikin sanyin murya tace  at first tsoronka nakeyi, later sai na fara fahimtar ka, yau kuma na ga wani side naka na daban.

Hassan bai kulata ba sai da aka dade yace  kina tunanin adan karamin kwanakin da mukai ne kike tunanin kin fara sanina?

Tai murmushi tace  a a bansanka ba, sai dai na fahimci abu daya.
Juyowa yai ya kalleta, yana jiran abinda zatace.

A ranta tace u are kind, amma a fili dariya tai tace  na fahimci kana matukar san Ummynka.

Kansa ya dauke daga inda take ya cigaba da tukinsa.

Tana san sanar dashi matsalar Ummy sai dai tana tsoro.......


#Oneluv=ؕ?


=??? *JALILAH* =???

Written By : *AYUSHER MUHD*
'ote me on Wattpad : *Ayusher Mohd*


*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*
(_D home of expert and perfect writer's_=ء?)


*34*


Yana tafe yana tunanin kalaman Abba har suka iso gida, parking yai sannan ya maida kansa ya kwantar a jikin motar.

Jalila ta fita daga cikin motar, sannan ta juyo ta kalleshi, ganinsa tai bashida alamar ma fita.
Komawa tai cikin motar ta zauna tace "Yaya! Bazaka shiga ba?"

Bai kalleta ba bashi kuma da alamar bata amsa, Jalila ta kalleshi tace "Yaya?"
Idanunsa ya bude ya kalleta yace "Nikam bakinki baya shiru ne?"

Kallansa tai ta rufe bakinta da labanta,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login