Showing 36001 words to 39000 words out of 168255 words

Chapter 13 - Auren Kwangila Book 4 Hausa Novel Complete

Takori   

12 Dec 2024

305

ba, akwai kanana daidai da ita, wannan ko jambaki bai taba ganin ta shafa ba balle hoda, kullum haka ta ke a kojale, ido ko kwalli babu. Ita Mammah ke ganin ya dace ta zame masa uwargida cikon farin ciki? Mahadin rayuwa abar hutawarsa?
Ya san halin Mammah kwarai, tunda ta yi wannan furucin ba abin da zai sa/ba wanda zai sa ta canza. Sunansa sorry cikin farin cikin da ake samu a aure. Tunda ba za a aura masa wadda zuciya, ruhi da gangar jikinsa ke so ba. Sun manta da cewa kiyayyar namiji a kan mace ba karamin al’amari ba ne. Mace akewa auren dole a wanye lafiya amma ba cikakken namiji wanda ya san ‘yancinsa kamarsa ba.

Zuciyarsa ta yi duhu, idanunsa sun yi masa bakikkirin, har wani hayaki-hayaki yake gani yana fita daga idonsa, yana ji kuma yana gani wayarsa na haske da ruri da tune din Mu’azatu, ya yi ya tsinke ya sake ci gaba, amma ko dan yatsansa ya kasa motsawa. Me zai ce wa Mu’azatu? Yarinyar da ta dauki soyayyar duniya da amanar duniya ta dora a kansa? Suka gama tsara rayuwarsu yadda suke so? Ya san yadda Mu’azatu ke da kishi a kansa, ta sha gaya masa ba za ta iya sharing dinsa da kowacce mace ba, don ma in yana da burin polygamy ya rushe, za ta iya rasa ranta a kan su mallake shi ita da wata. Duk kuma ya gaya mata cewa ya amince, shi da ma a tsarin rayuwarsa mace daya ce har bayan ransa. Duk wannan ya zama tarihi kenan? Zai rasa Mu’azatu cikin dan lokaci kalilan?
Dole ya yi wani abu, dole ya yi wata hikimar ta yadda ba zai samu matsala da iyayensa ba, ba kuma zai rasa mu’azatu ba.
Mammah ba uwa ce irin sauran iyaye ba, ita ko a cikin iyaye mata ta daban ce. Ta cancanci a yi mata biyayya kowacce iri ta ke so. Zai yi kokarin kada ya bata mata, kuma shi ma ya faranta wa nasa ran ya samu abin da yake so cikin sauki.
Akwai mafita biyu da yake ganin zai gwada, in ba su yiwu ba, sai ya yi wanda zuciyarsa ta fi kwanciya da shi.
Mu’azatu ta gaya masa ko an zo neman aurensu, sai dai a yi baiko, amma biki Daddynta ya ce sai ta je ‘Law school’ ta dawo zai yarda a yi. Tana shekaarta ta karshe a jami’a yanzun haka.
A lokacin da ta fada masa yadda suka yi da Daddyn nata ya fada mata cewa shi ba zai iya jira ba, amma ya yi mata alkawarin zai barta ta je gaba da ‘Law school’ ma a gidansa in har tana so.
Yanzu zai yi amfani da wannan damar ya aiwatar da kudirinsa, yadda zai faranta wa kansa, ya kuma faranta wa iyayensa. Don ko jiya da ya tambaye ta ya suka yi da mahaifin nata a kan maganar da suka yi, saboda yana so ya turo magabatansa a yi tambaya, ta gaya masa cewa, ita ba za ta iya dosar Attorney din da wannan maganar ba, don ba zai taba amincewa ba tunda ya riga ya zartar da hakan, gara ma in shi zai je ya fadi hakan da kansa zai fi jin kunyarsa, ya yarda ko da da ta kare LLB ne.
Ya ajiye ajiyar zuciya mai nauyi, a kasalance ya mika hannu ya dauko wayarsa, ya nemo lambar da yake nema, ya yi text ya tura. Jikinsa gabadaya ya yi sanyi, ba shi da kuzari ko kankani, hango yadda zai jure rasa Mu’azatu kawai yake yi. Muguwar tsanar Addah da kyamarta nata kurdawa kowanne sako da lungu na zuciyarsa.
“Haka kawai? Why me?” Ya furta a fili.
Fitowarsa kenan daga dakin karatu, rungume da littattafai. Ya doshi hanyar fita daga cikin jami’ar Harvard, yunwa yake ji sosai. Bai dade da shiga commercial bus don ko awa gida ba ya ji alamar shigowar sako cikin wayarsa.
Zaro wayar ya yi daga aljihunsa ya duba,

‘If you are free ka kira ni, za mu yi magana ta sirri, kuma very important’.
Ajiye wayar ya yi cikin aljihu, “Wallahi sai na ci abinci, kada ka fada min abin da zai kori yunwar nan da ta addabe ni”.
Sai da ya iso gidan da Daddy ya kama masa ya yi wanka, ya ci abinci. Ya sallaci la’asar, ya samu nutsuwa sannan ya zauna a ‘balcony’ ya kira Yayan nasa. ISMA’EL DAKATA ne.
“Yauwa Ishma are you o.k? Za mu iya yin maganar babu kowa tare da kai?”
Isma’eel cikin mamakin yadda husky voice din yayan nasa ta zaftare ta koma rabi, ya ce,
“I’m alone Yaya”.

Nisawa Abdul’azeez ya yi, ya sauke numfashi mai nauyi.
“Ishma, wata musiba ce ta tunkaro ni, nake so ka taimaka mini. Ni kuma na yi maka alkawarin yi maka duk abin da ka ke so a duniya, zan kuma dinga raba albashina biyu ina turo maka duk wata har ka gama karatu ka kama aiki ka tsaya da kafafunka”.
Maganganun (sounds funny) a kwakwalwar Isma’eel, daga ji ba abin alheri Yayan zai nema ba, tunda har sai ya biya shi lada. Ladan ma wai na rabin albashinsa duk wata.
“Ni kuwa me zan yi maka da har sai ka biya ni Yaya Azeez? Gaya min ko me ka ke so in yi maka, in har na alkhairi ne. Zan iya fansar da raina don in cece ka, amma wace irin musiba ce wannan da iyayenmu ba za su iya yi maka maganinta ba sai ni?”
“Su suke son jefa ni a ciki Isma’eel”.
“Subhanallahi, please Yaya, don’t say this again. Na yi amanna ba za su taba jefa ka a musiba ba, sai alkhairi ga rayuwarka. Yanzu dai me ka ke so in yi? A shirye nake da in taimaka in har abin alkhairi ne, kuma zai tafi da damuwarka, don Allah me ka ke so in yi? Wallahi ba sai ka ba ni komai ba zan yi. You sound worried. Ni ma na shiga cikin damuwa.......”
Abdul’azeez ya canza rikon wayarsa daga kunnen dama zuwa hagu, ya juya ya tabbatar babu kowa a cikin dakin, kuma babu motsin kowa daga waje.
“So nake ka bugo waya wa Mammah, ka ce mata ka dade kana son Hafsat, don Allah a ba ka aurenta, saboda ka kasa maida hankali kan karatunka saboda soyayyarta. Ka ce sonta ka ke tun tana yarinya. Ka nuna mata irin wani abu zai iya samunka din nan in ba ka samu aurenta verysoon ba, sauran kalaman ka tsara abinka, ai kai ba yaro ba ne tunda na ba ka topic din, ka gane?”
Mamaki ya gama kashe Isma’eel a tsaye. Sai da ya lalubi kujera ya zauna, “Yaya wace Hafsat din?”
“Ta gidanku mana”.
“Kana nufin Suhaana?”
“Ni wallahi sunannakin nata ba duka na rike ba, kuna kiranta da sunaye barkatai. I don’t actually know, ta wajen Mammah dai”.
“Don Allah Yaya mu yi magana ta fahimta, Hafsat-Suhaana Addar Mammah?”
A ginshire Abdul’azeez ya rausaya kai ya ce, “Eh, ita! Don na ji Baba Azumi ma ta ce mata Addar”.
Dariya ta kama Isma’eel amma ya gintse, yanzu ya gano bakin zaren duk da bai gaya masa ba. Mamakin Yayan nasa ya kama shi, amma tunda bai fito fili ya gaya masa dalilin bukatar tasa gare shi ba bari ya bi shi a hakan.
“Yaya a kan me to? A kan me zan yi hakan, a kan me zan yaudari Mammah in yi wasa da hankalinta a kan abin da ba haka yake ba a zuciyata? Yaya Hafsat mai martaba ce a wajen Mammah da mu bakidaya da muka rayu tare, muka san wace ce ita, wace irin martaba Allah ya yi mata. Kasancewarta ba jininmu ba ba ya nufin ba ma kaunarta ko don kaunar da mahaifiyarmu ke mata. Yarinya ce ta gari, amana a wajen mahaifiyarmu, ta ya ya ka ke tunanin zan iya playing game a kanta? To a kan me ma?”
Abdul’azeez ya hadiyi miyau, jin makoshinsa ya bushe kyamas da jin alamun ba zai samu nasara a plan dinsa na farko ba. Amma dai bari ya ci gaba da turzawa tunda Isma’eel dai a kasansa yake.
“A kan duk kaunar da ku ke mata, ba ta kai wadda ke tsakanina da ku ba”. Ya fada cikin kwantar da murya, jin kamar Isma’eel ya fusata.
“Haka ne Yaya, to amma a kan me zan yi karyar ina son nata? Ni ban taba sonta ba! So na soyayyar aure, amma ina mata dukkanin kaunar da Yaya ke wa kanwarsa. Har tsarkin kashi na yi wa Suhaana, ban taba yi mata wani kallo bayan wanda nake yi wa Halim ba. Sannan ba zan iya wasa da hankalin Mammah har haka ba, me ta yi mana da ta cancanci haka? Ka yi hakuri Yaya, ba zan iya ba. Kuma kaima na rokeka ka bari, ka yi mata abin da ta yi maka umarni da kyakkyawar zuciya, kar ka sake tunanin yi mata (trick). Yaya, Allah yana kallonka, duniya da kyale-kyalen cikinta aikin banza ne. Mammah ita ce kofar shigarka aljanna, matsayin da Allah ya ba ta a gare ka ya wuce duk yadda ka ke zato. Na yi maka alkawarin wannan maganar da muka yi ni da kai an barta a nan, ba za ta taba fita daga bakina ba. Mu wuni lafiya”. Ya kashe wayarsa.
Duba wayarsa ya yi sosai, yana mamaki. Shi Ishma ya kashe wa waya???
“Ba dole ya kashe maka waya ba, tunda ka kawo raini ga mahaifiyarsa?”
Zuciyarsa ta yi hanzarin halarto masa da amsa, “Da kyar ma in girmanka bai zube a idanunsa ba!”. Ta kara ankarar da shi.
Jikinsa ya yi matukar sanyi, kansa ya yi masa nauyi. Babu nasara a ‘plan 1’, bari Allah ya kai mu gobe ya aiwatar da ‘plan 2’. In shi ma babu nasara sai ya amince da babban, wanda zuciyarsa ta fi kwanciya da shi. So, ya rufe masa ido, ta yadda har ya kasa ganin muhimmancin nasihohin kanin bayansa Ismael.
Washegari ya kira tsohon minista, kawun mahaifinsa Abdulkarim Dakata. Ya gaya masa yana son ganinsa, ya ba shi lokaci ya tadda shi a gida ko ofis (yana aiki da ofishin jam’iyyar NPC a yanzu, a matsayin mataimakin shugaban jam’iyyah). Akwai shakuwa ta musamman a tsakaninsu. Abdulkarim na son Abdul’azeez kamar ko ma fiye da yadda yake son su Farhan. Ya zabi ya same shi a office.
Don haka washegari, kwana biyu kenan da yin maganar da iyayensa, a gobe ne za su zauna da shi don jin abin da ya yanke. Ya wani rame tun daga jiki har fuska a kwana biyu kacal saboda daura wa kansa masifar da Allah bai dora masa ba. Mammah na kallon duk motsinsa a kwanaki biyun nan tana shan mamaki, anya yarinyar nan da iyayenta haka suka kyale Abdul’azeez? Ko dama shiyasa suke bashi abinci? Uban wa ma ce ya aike shi cin abincinsu? Wannan wace irin masifa ce? A ce wai ita Abdul’azeez ke jayayya da ita a kan mace? To su zuba ita da shi ta ga iya gudun ruwansa dan halas ka fasa!
Sun kulle kansu a office shi da tsohon Sanata kuma tsohon minista, kawu ga mahaifinsa. Ya kwashe komai ya gaya masa tun haduwarsa da Mu’azatu a (Law school) da hidimar abincinsa da ta rika yi ita da iyayenta har ya gama. Da alkawuran da kakkarfar soyayyar da ke tsakaninsu. Da kuma abin da iyayensa suka bijiro da shi shekaran jiya na auren Addah. Da amsarsa da suke jira a gobe.
Sosai Abdulkarim ya tsaya ya saurare shi da kunnuwan basira, kafin ya hadiye fushinsa ya soma zubo masa wasu irin tambayoyi da duk hikimarsa ta lauya bai san yadda zai yi ya amsa masa su ba.
“Yanzu me ka ke so in yi?”
Ya yi shiru, gabansa ya soma faduwa ganin yadda yanayin kawun Baban nasa ya canza gabadaya. Abdulkarim kuwa cikin mamaki yake, wai ashe sun haifi wani Da cikin zuri’ar Abdullahi Dakata da za su yi wa umarni ya tsallake ya yi gaba yana neman hanyar kubucewa daga yi musu biyayya a kan wata aba soyayyar banza? Akwai dan da suka so, suka wahala a kanshi irin Abdul’azeez? Akwai dan da tsohon Ambassadaya nuna wa soyayya a zuci da fili irin Abdul’azeez? Yanzu Abdul’azeez ya yi girman da ya yi ilmin neman hanyar kubucewa umarninsa? Yake ganin ya fi su sanin abinda ya dace da shi da wanda bai daceda shi ba? Shin uwa irin Maryam ta cancanci ‘ya’yan da ta wahalta wa haka su ki yi mata biyayya a girmansu?
Sosai ya boye fushinsa, yake kallonsa da idanun rahma. Cikin kwanciyar hankali yake magana.
“Na ce me ka ke so in yi?” Ya sake yin shiru duk plans din da ya tsaro ya kasa furta ko daya. Wani irin kwarjini kawun Daddyn ya yi masa.
Abdulkarim ya jeho masa tambaya ta biyu, ganin ya kasa amsa masa ta farko.
“Abincin da gidan su yarinyar suka ba ka na shekara daya kai ka roke su? Ko ko ba ka da kudin sayen abinci da hakan zai sanya auren diyarsu ya zama dole? Ita Maryam abincin shekara nawa ta ba ka?”
Shiru Abdul’azeez ya yi yana da na sainin kawo kansa kotun shiga ba biya, fita da Allah ya isa.
“Mu ture ta maganar abinci, wata nawa ta dauke ka cikin wahala da kaka-ni-ka-yi a karkashin mahaifarta? Ka san me ta jure a yayin fitowarka duniya? Wace irin dawainiya ta yi da kashi da fitsarinka? Me ta yi ta koya maka zama, rarrafe da tafiya a kan doron kasa? Wane irin jele ta yi zuwa asibiti a duk lokacin da ba ka lafiya? Bari in gaya maka abin da ba ka sani ba, ka kasance yaro mai yawan zubar da jini ta hanci (Nasal bleeding) wato ‘habo’, Maryam kullum tana asibiti don nema maka waraka. A duk sanda ka ke wannan ‘nasal bleeding’ din Maryam kuka ta ke yi tana share maka a gaban kowa da mayafinta da dankwalinta, don haka ina tunasar da kai da kakkausar murya da ka shiga hankalinka.
Ka ba ni mamaki Abdul’azeez yanda ban taba zato ba, a tunanina duk cikin yaranmu babu mai hankalinka da kaifin basirarka, kullum kwatance nake wa su Sha’aban da kai ina cewa su yi koyi da kai, tukunna ma wai shin ni don Allah don Annabi da ka zo wajena ka gaya min, a matsayin ka kawo karar iyayenka,saboda Allah me ka ke so in yi maka a kan wannan umarnin da suka yi maka?Suke so ka rufa musu asiri ka yi musu biyayya kan abinda suke so?”
Zufa ya rika sharewa irin wadda ta rika addabarsa a lokacin da yake gaban iyayen nasa suka yi masa nasu umarnin na auren Suhaana, yanzun ma da wannan masifaffen Kawun ya tsatstsare shi da manyanidonsayana jiran amsar bakinsa ita ta rika tsattsafo masa ta kowacce mabubbugar gumi ta jikinsa. Da ya sani da bai zo ba!Ya dauki lamarin da zafi fiye da iyayensa ma. Shi bai taba sanin Minister Abdulkarim ya iya fada haka ba, ga kisan mummuke mai kashe gwiwoyin mutum. Abdulkarim Dakata ya katse tunaninsa da lallashi.
“Yi wa Allah ka gaya min me ka ke so in yi a kai Abdul’azeez, na yi kuskure da na tari hanzarinka, bayanin bakinka kawai na ji ban tsaya na ji role din da ka ke so in taka a kai ba”.
Abdul’azeez ya dan nisa cikin jin sassauci.
“Ba burina in ki yi wa Mammah biyayya ba Uncle, amma ni ma ta duba hanzarina”. Ya fada cikin yankewar buri da sagewar gwiwa.
“Mene ne hanzarin naka?”
“Ta bar ni in auri Mu’azatu, ta ba wa Usman yarinyar in Isma’el baya so, shi ma danta ne. Kuma ya fi daidai da ita, bai girmeta da yawa ba, ba ta isa aure ba, ta yi kankanta da yawa, sannan ba ta da asali, har gobe ba’a san ubanta ba. Wannan abun shi ya fi damuna, kyankyaminta nake yi Kawu, kamar yadda nake kyamatar zina”.
Abdulkarim ya yi shiru. Hanzarin nasa ya dan taba shi. Da gaske ba su san ubanta ba, ba su san asalinta ba. Wannan abin dubawa ne, to amma su suka raine ta, sun san halinta sun san komai nata. Maryam ita ce uwa mafi kusanci da ita, inda tana da wata illa ko wani gibi ba za ta ce sai ya aura ba, if she is harmful ba za ta so hada jini da ita ba duk son da ta ke mata. Babu yadda za a yi a ce ta fi sonta a kansa. Ya san halin Prof. Bai da takurawa ‘ya’yansa, idan Abdul’azeez ya ce bai so ba zai taba takura masa ba, amma Maryam kaifi daya ce. Asali da dangi abin dubawa ne a aure tabbas. Amma nasa case din akwai bambaci tunda iyayensa su suka raine ta. Ya nisa a hankali cikin sassauci.
SUMAYYA ABDULQADIR TAKORI
07030137870


*Littafi na farko shine kawai free. 234 na sayarwa ne. Idan ka fidda 234 ba sai na hada ka da Allah ba zai isar min insha Allahu. Ku biya Ku karanta a nitse cikin farin ciki yafi maka kayan zunubi ranar gobe kiyama*

AUREN KWANGILA 1

Page8


“Na fahimce ka Abdul’azeez, amma kada ka manta iyayenka su suka raine ta, in tana da wata illa sun fi ka sani. Sannan Ubangiji ba ruwansa da kana da hujja, biyayya ya ce dole ka yi musu, ka na so ko ba ka so. Don haka ka watsar da komai ka yi musu biyayya na tabbatar maka ba za ka yi da na sani ba. Za ka ga da kyau a rayuwa.
Kada ma ka sake kawo zancen Usman ko Isma’el, sun fi ka sanin da zamansu suka ce kai suke so ka aura. Abdul’azeez ni gani nake wani gata ne Maryam ke son yi maka, kasancewarka mafi soyuwa a zuciyarta, kuma tana ganin ta isa da kai. Idan ta ba ka amana za ka rike, idan ta yi umarni za ka yi biyayyah, haba Abdul’azeez kada ka watsa mata kasa a ido, ake dauko Da daga gidan marayu a aura balle wadda mahaifiyarka ta raina tun cikin jinin haihuwa? Me ye amfanin karatunka na lauya in ba za ka yi amfani da shi wajen binciken abin da ya shige maka duhu ba? Za ka iya bin diddigi ka nemo mahaifin yarinyar nan daga inda mahaifiyarta ta shigo hannunku. Bayan wannan sai me ye matsalarka da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login