Showing 129001 words to 132000 words out of 168255 words

Chapter 44 - Auren Kwangila Book 4 Hausa Novel Complete

Takori   

12 Dec 2024

313

yi kuskure kuma mun gane mun yi, mun ladabtu da ladabtarwarki, muna masu farin cikin sanar da ke cewa, makamancin wannan ba zai sake faruwa ba, insha Allahu.
Shi ne har sai ka durkusa min Malam? Don Allah ka yi hakuri, abin bai yi girman haka ba, don Allah ka bar durkuson na, zan maida ita insha Allahu.
Malam ya koma ya zauna, Na gode sosai Hajiya Maryama. Ai ita kuruciya ba abin da ba ta sa wa.
A ranta ta ce, A lokacin da ya shirya kwangilarsa shekarunsa talatin da daya, shi ne za a kira wa kuruciya?
Maganar dukiyar Hafsat suka koma yi, ta ce a ci gaba da yi mata kiwo a Jimeta, kudadenta za a saya mata hannun jari ta dinga karbar share duk wata zuwa asusunta, sannan za ta saya mata motar hawa tata ta kanta.
Malam ya ce, duk yadda ta yi shi ne daidai. Ta ce, Ya kamata ku je ku ga muhallinta duk da dai an kwana biyu ba a shiga ba.
Suna haka Abdulazeez ya shigo, ya yi shirin office, kamshin daddadan turarensa ya sanyaya dakin. Yau suit din da ya sanya dark green ce haka wandonta, da farin neck tie kamar kullum. Kafin ta jefo harara ya yi maza ya durkusa ya gaishe ta, Malam kuma ya kafe ta da fararen idanunsa ya ga yadda za ta amsa don haka ta amsa kadaran-kadahan a zuciyarta tana jinjina rashin ta idon Abdulazeez da ya iya dosar Kakan Hafsat da wannan maganar. Ubangijin da ya halicce shi Ya halicce shi frank mara boye gaskiyar abu don a so shi, ko mai fuska biyu. Yadda fuskarsa ta ke sak, kamilalliya haka zuciyarsa ta ke. Ya juya ga Malam din yana masa barka da tashi ya ce,
Ya ya bakuntar birnin tarayyah? Kwana biyu ka huta zafin Yola, ko mu rike ka a nan na shekara uku?
Murmushi ya yi, ya ce, Barni in mutu a mahaifata, zafin Yola ai gyara fata yake yi ban da haka ai da ba ka gan ni haka ba.
Dariya ya yi, ya ce, Ni kuwa duk zuwana garinku bana iya kwana da riga, sannan kafin na taho bana duba madubi sabida yadda baqina da muni na yake nunkuwa.
Ni kuwa da na ce amaryarka ta Yola can za ka bar muna ita, ko ma ke ganinka a kai-akai ashe ita ma barikin za ka taho da ita?
Mammah ta dago da sauri ta dube shi, ya gintse fuska ya ce, Malam! Kada ka ballo min ruwa mana! Ka ga uwarta tana hararata, yaushe muka yi haka da kai?
Ka ji min dan albarka, ba jiya ka ce in aje maka ita sai bayan shekaru ashirin ba?
Mammah ta fiddo idanu sosai tana kallonsa. Ya dafe kai, ya ce, Malam, shekara ashirin irin ta Bahaushe nake nufi, kuma kai fa ka kawo zancenka, ka fada yadda Mammah za ta gane ba ta cika fahimtar abubuwa a yadda suke ba.
Mikewa ta yi ta bar musu dakin bayan ta yi wa Malam sallama za ta je wajen sauran baki. Da sauri Abdulazeez ya bi bayanta, a corridor din dakunan ya sha gabanta ya kamo hannunta ya marairaice idanu, Mammah ni fa ban san zancen da yake yi ba.
Kwace hannunta ta yi, Matsa ni ka ba ni hanya, a daura maka dari ma mana ya ga kana so ne.
Ya sake tare ta, shi lallai ta yarda zancen na Malam Babbah ne. ta ce, Wallahi Abdulazeez kana shiga hancina da yawa, ka kai karata ban ce maka komai ba, wani ya ce bayan Hafsat kada ka kara aure? Gashin kansa ya shafo, ya ce. Balle ma shes o.k for me, as you are o.k for Daddy.
Harara ta manna masa ta lura yau nishadi yake ji, tunda ya ci ta da yaki. Wata irin kaunarshi ke kara ratsa ta. Duk yayanta ya fi su kama da ita, hasken fata kawai ta fi shi,
Za ka ba ni hanya ko sai wani ya zo ya ganmu a nan?
Ya ce, Zan matsa, amma sai na ji yaushe ne?.
Yaushe ne me?
Za ta koma saboda tsoronki nake ji kada Malam ya tafi ki ce ba ki san zancen ba.
Dariya ce ta kamata, amma ta shanye, ko za ta maida Hafsat ai sai ta gyara ta ba haka lokaci daya ba yadda ta fahimci take-takensa, in Hafsat ta shiga hannunsa sai gyaran Allah, dole ta dasa ta a zuciyar mijinta, ya daina hango kowacce ya mace. Duk gyaran amarcin da ta yi mata ta tabbata iska ya bi. Juyawa ta yi ta koma dakin Malam yana duba wani littafi, ta ce.
Malam, ka gaya masa kada ya takura min a kan komen Hafsat, tunda na ce maka za ta koma to tabbas za ta koma, amma sai na shirya.
Malam ya ce, Abdulazeez mu kara hakuri ta yi mata lalle tukun.
Gabadaya suka bushe da dariya har ita. Ta ce, Lalle da kitso kuwa.
Ya ce, To ai ka ji, aikinsu kenan.
Mammah ta ce, Malam ko za ku je ya kai ku can gidan nasu ku gani? Wata unguwa ce nan a gabanmu Sun-City.
Girgiza kai Malam ya yi, Ba sai mun je ba. In ta haihu mun zo suna.
Duk rashin kunyarsa yanzu kam ya ji ta, ya fice da sauri ita ma ta wuce sauran dakunan. Dada ta tambayi Malam ya ta ga Hafsatu da Abdulazeez a gidan tun zuwansu ya ce gyaran gida ake musu. Mazan ma debo su aka yi daga hotel suka dawo gidan a nan suka karya kumallo. Haka wannan family suka wuni cikin aminci, suka shaku da juna cikin dan lokaci. Da Usman zai maida Dr. Bashar, Modibbo, Abdurrahman, Imamu masauki da daddare Hafsat ta bi su. Dakin da aka kama musu babba ne ciki biyu da falo, su suna ciki daya, Dr. da suke kira Abba na daya. Usman tafiya ya yi ya barsu ya ce zai dawo karfe goma ya dauke ta.
Wata irin hira aka yi yau tsakanin Hafsat da mahaifinta, da yan uwanta. Hira mai shiga rai da sanyaya zuciya. Rabin hirar labarin mahaifiyarsu suke ba ta da yadda ta kula da rayuwarsu da tattalinsu. Ta ji halin da kowannensu ya shiga ranar da suka neme ta suka rasa. Ta ji tsayin lokacin da mahaifinsu ya dauka bai kara aure ba. Rayuwarsu a hannun Dada har zuwa girmansu. Har gobe kewarta muke Gaaji (Auta), ba mu fita daga cikin kewar ba. In ji Imamu, Har gobe gani nake kamar zan rufe ido in bude in ganta ta dawo ga ki a gabanta. In ji Modibbo. Ni har gobe gani nake kamar unguwa ta tafi, ko ta je Demsawo ne ta dawo . In ji Abdurrahman.
Hafsat sai ta sa kuka. Ba ta santa ba, ba ta taba ganinta ba sai a hoto! A hoton ma a dakin Dada, Mammah ba ta taba nuna mata ba sai zuwansu Jimeta, Abbah da ke kallonsu cikin tausayi da kauna bai yi magana ba sai wannan karon, ya ce, Kun sa ta a gaba don ku yi hira ne, ko don ku sanya ta kuka? Ba ku yi murna da uwar rikon da Allah ya bata ba? Ba ku yi murna da kyakkyawar rayuwar da ku ka ganta a ciki ba? Ko ku ba ku gode wa Allah da mijin nuna wa saa da ya yi mata baiwa da shi ba? Tunda nake ban taba ganin mutane masu karamcin wadanda na gani tare da ita ba. Kada ku manta fa matsayin yar aikinsu uwarta ta zauna da su, suka dauka suka rike duk da ba su da tabbacin halaccinta. Sannan ba su yi tunanin hakan ba suka aura wa gudan jininsu. A yadda alumma ta koma yanzu dan aikinka kamar ba cikakken mutum ba ne, masu kudi ba su dauki masu hidimarsu komai ba face tsumman takawarsu. Don haka kada mu kasance masu butulci ga Allah mu gode maSa a bisa wannan jarrabawa da Ya yi mana.
Usman bai dawo daukarta ba sai sha daya na dare, shi da Ismael ne. Sun yi hira da su Imamu sannan suka yi sallama suka tafi.
Suna fitowa daga mota Abdulazeez na bullowa daga guest house wajen Malam, zai shiga gida. Cikin mamaki yake dubansu su duka ukun, har suka iso inda yake tsaye. Kugunshi ya kama Ku kuma daga ina a daren nan? Yana zabga musu harara daya bayan daya har ita Hafsat din.
Ismael na son yin dariya, amma ya san bai isa ba.
Mun dauko Addah daga wajen Abbanta ne.
Da izinin wa? Ya fada yana hararar Hafsat din, rabon da ya ganta tun ranar rockview, ba ta kara yarda ko da kuskure sun hadu ba. Shi kuma ya san bai isa ya je inda ta ke ba. Haka ya yi ta daurewa yana hakurkurtar da zuciyarsa, sai kuma hidimar tafiyarshi ta kwashe kaso hamsin na lokutan da yake samu a gidan ma, ko yana nan akwai abubuwan da yake yi na cike-ciken takardu ko processing visa dinshi a system bai cika damuwa ba duk da ko me yake yi tana makale cikin zuciyarshi.Dariyar da Ismael ke yi cewa yake a ransa,
kada dai Yaya Azeez kishinmu yake yi?
Mammah ce ta ce a kai ta. In ji Usman.
Hanya ya ba su bai ce komai ba, suka wuce babu ko waiwaye. Za ta wuce ya sarko hannun ta cikin nasa, dagowa ta yi fuska a turbune. Wani irin kallo yayi matakafin yace.
Wai tsakanin ni da Mammah wa ke aurenki ne yarinyar nan?
Ta turo baki cikin kunkuni irin wanda ta saba yi masa ta ce.
“...Sai an shafa za’a ji!.Ba don ya kasance cikin masu kyakkyawan ji ba, kuma ta saba magana irin hakan in ya mata abinda bai gamsheta ba, da bazai ji ta ba.
So yake su hada ido amma ta ki, kawai sai ya finciki hannunta zuwa ciki, ta studyroom ya ratsa dasukasancewar ta cikinsa zaa iya bullewa dakunansu. Hafsat ta kalli study-roomdinnan with lingering look!Dakin daya tuna mata watarana da bazata taba mantawa a tarihinrayuwarsu ba wato ranar.... kuma dakin da aka assasa AUREN KWANGILA a cikinsa......(Wanda a yanzu ya juye ya rikide zuwa wani aure mai ban mamaki),ya bi ta can ne don kada ya hadu da kowa shiyasa bai bi ta main parlour ba zuwa inda dakunansu suke. Nashi ne a farko sannan na Ismael sai na Usman da na Haleem suna kallon nasun. Tura kofar ya yi ya fisgo ta ciki ya rufe kofar har da key. A jikin kofa ta tsaya idanunta sun raina fata, ta ce. Haba don Allah Yaya Azeez dare fa ya yi, Mammah ta san mun shigo gida tun dazu.
Wani irin kallo yake mata, wanda ya kara kada hantar cikinta. Maimaita abin da ki ka fada dazun? Tukunna ma guduna da ki ke duka a kwanakin nan na mene ne?
Hafsat ta yi shiru, ya ci gaba da matsowa gabanta. Har ya zamanto space din da ke tsakaninsu taki biyu ne kacal. Yatsunshi biyu ya sanya ya dago habarta cikin kankanuwar murya ya ce,
Hafsah!
Ta bude fararen idanunta tarrr! Ta dube shi, da wani irin kallon so da ya tsirga har babban yatsar kafarsa wanda ita bata san ta yi ba. Umarni ne na zuciyarta kawai zuwa idanunsa. Da azama ya rungume ta, ya soma magana cikin kunnenta da sauti mafi tsananin taushi da ya mallaka.
Kin ce in shafa in ji ko? Ni da Mammah wa ke aurenki?Ok Hafsat lets find out......”.
Dago kantayayi daga rungumar da yayi mataya sanya fuskarta cikin tafukansa ya somasumbatarta cikin wata irin siga (wani abu data lura ya fi kwarewa a kai muddin ya samu damar hakan tun a gidansu wato sumba. Ta fahimci wannan shine abinda cikin kowanne hali yake ciki (bacin rai ko akasinsa) baya iya fasawa a kantawato dai baya gajiya da sumbatarta). A yanzun kuma yana yi ne cikin yanayin da ke nuna tsananin kewar ta da yayi, da matukar son sa da hakan. A wannan lokacin ita kanta Hafsat bata da banbanci da shi na jin cewa tayi kewar tasa don dai ita mace ce, kuma maabociyar kawaici da alkunya.
Saidai ita ta san bata wannan fannin kadai tayi kewar Abdulazeez ba. Ita in general komai da ya dangance shi take kewar;fadansu, jayayyar su, kalamansa, murmushinsa da komai nasa... Daga shi har Hafsat sun fita a duniyar su sun afka wata sabuwar duniyarda dawowa daga cikinta abu ne da zaidauke su lokaci.
“.....Ina son in nuna miki bambancina da ita ne, da abin da ta ke sanyawa kina missing...!!!.
Abin da ta iya fahimta kawai kenan cikin tarin tausasan kalamansa cikinkunnuwanta.Hafsatta fahimci abin da Abdulazeez ke kokarin yi nextshi ne raba ta da sittirun jikinta. Idan hakan ta faru kuma bata san me zai biyo baya ba; bata san iya ina alamarin zai tsaya ba. Ta tuna a inda suke, a gidan waye, kuma a tsakanin wadanda za ta kwana. Wani karfin zuciya ne ya zo mata ba don ta cancanci mallakarsa ba, sai don tunanin rashin dacewar abin da suke shirin yi cikin gidannan ya rinjayi halin da ta tsinci kanta. Daman kuma a tsaye suke don haka ta tattara dukkan karfin da ya saura mata ta tura shi baya ya fada gadonsa. Ta yi mamaki da ta ji kamar ta hankade karamin yaro, ba wani sauran karfi a tare da shi.
Da azama ta isa ga kofa ta murza key din ta fice. Sai da ta tabbatar she is safe sannan ta tsaya jikin hudar kofar ta ce, Imsorry Yaya Azeez!. Ta gyara tsayuwarta, ta yi lullubinta sannan ta daidaita numfashinta, ta lallaba kamar mara gaskiya ta shige ciki.
Cikin saa ba ta gamu da kowa ba, ta murda kofar dakinta a hankali ta shige. Dada ta kashe fitila sai jan rago ta ke (munshari). Hamdala ta yi ta fada bandaki don ta yi wanka. Amma me?
Ba ta son ta wanke scent din Abdulazeez daga jikinta, wani kamshi da ta fi so fiye da kowanne a rayuwarta. Fasa cire kayan tayi. Tajingina da kofar bandakin ta lumshe idonta komai da ya faru a yan daqiqan da suka gabata ta ke tunowa daki-daki tana sakin murmushi. “...Ina so in nuna miki bambancina da ita ne, da abinda ta ke sawa kina missing....!!!. Ta tuno kalamansa,wadanda suka sanya ta kara zurfafa murmushinta kamar wata sabuwar mentally retarded.Wato ta fahimci wani aji na musamman Abdulazeez ya gina, ya dauki Mammah ya ajiye ta cikimai kama dana kishiyar sa. Kai Yayan Haleem sai a barshi.
Daga karshe dole ta yi wankan don ta san in bata yi ba bazata iya barci ba sabida dawainiyar jamaa data sha yau.Ko da ta yi nafilolin da ta saba ta hau gado, kasa baccin ta yi. Yau ne ranar da ta yi dakacen kwace wayarta da Mammah ta yi. Muryarsa kawai ta ke so ta ji, da halin da yake ciki. Ji ta yi kamar ta yi kuka saboda tausayinsa, amma can a karkashin zuciyarta ana gaya mata hakan da ta yi shi ne daidai, su maza babu ruwansu ita kadai za ta kwana a ciki. Ta tuno halin da ta kasance a ciki ranar da suka je Rockview ko ruwan sha da kyar yake wucewa a makogaronta a gidannan sabida kunyar Mammah.
Ta dauki kwanaki ba ta iya hada ido da ita. Balle yau a cikin gidanta? Ta sani ko ya yi fushi zai huce, duk da ta san fushinsa a kan irin haka ba mai sauki ba ne. Ta tuno sanda suka yi irin haka a gidansu ba ta ji da dadi ba na kwanaki masu yawa. Muguwar gaba ya kulla da ita sai ranar da Allah ya kawo Mammah gidan suka shirya dole.Abdulazeez bai iya fushi ba, kuma in ya tashi yi mara dalili yake yinsa wanda kuma in an bi salsala shi ne at fault.
Da kyar bacci barawo ya iya sace ta. Zuciyarta fal da so da kaunar mijinta, wanda watanni goma sha shidda irin wadannan a baya ba ta taba tsammanin wai wata rana irin haka na zuwa da za ta so shi ba. Bata taba daga ido tayi masa wani kallo bayan na Yayansu ba; Yayan ma irin wanda baa so! Wanda da da hali da an canza shi daga yayan cikin Mammah!Ba ta san ma mene ne son ba, amma yau a kansa ta koye shi ba tare da wani ya koyar da ita ba. Shi kansa bata zaton ya taba attemptingyin wani abu da gangan ba don ta so shi! Bai taba yin wani abu da sunan ya ja hankalinta kansa ba. Ta so shi ne don radin kanta bisa umarnin zuciya, ruhi da gangar jiki. Don haka ta rattaba soyayyah a matsayin wani abu da turawa suka kira naturalisticphonemenon; wani alamari da ke faruwa bisa kudurar Ubangiji, da hikimarSa. Wanda karfinsa tamkar chemistrydin gravity.
*****
Washegari mutanen Jimeta suka yi harama aka yi sallama cike da begen juna. Sun tafi tare da Ismael da Usman wadanda za su yi musu jagora zuwa gidan Malam Abdullahi Dakata. Su Inna Hafsatu tuni sun san da zuwansu, don haka tarba aka yi musu ta girma, irin wadda wannan family suka gada, su din maabota karamci ne kwansu da kwarkwatarsu. Sai suka samu iyalin Hashim Babba Jimeta suma da nasu nauin karamcin. Godiya ce dai da adduaoin alkhairi suke ta yi babu iyaka duk a kan rikon Hafsat da inganta rayuwarta da suka yi, suna rokon Allah subhana ya saka musu da mafificin alherinSa.












SUMAYYA ABDULQADIR TAKORI
07030137870

*Littafi na farko shine kawai free. 234 na sayarwa ne. Idan ka fidda 234 ba sai na hada ka da Allah ba zai isar min insha Allahu. Ku biya Ku karanta a nitse cikin farin ciki yafi maka kayan zunubi ranar gobe kiyama*

Sun so su wuce Jimeta a ranar yamma ta yi, dole sai da suka kwana. Kasancewar gidan babban gida mai sassa daban-daban ya kwashe su tsaf, maza sun kwana a dakunan maza, haka mata. Washegari asubanci suka yi suka koma Jimeta. Su Ismael suka juyo Abuja dauke da sakonnin Mammah daga jamaar gidan da abubuwan da Inna Hafsatu ta saba aika mata wanda ke musu wuyar samu a Abuja. Duk da ma dai lokacin zuwansu Kanon ya kusa, suna zuwa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login