Showing 144001 words to 147000 words out of 168255 words
ne, ya rarrashe ta har ya gaji ya rabu da ita. Ita kadai ta san me ta ke ji a zuciyarta, Abdulazeez kawai ta ke son gani, da wata irin soyayyamai yawa. She only wants to see him beside her at every blink of an eye (so kawai take ta ganshi a gefenta, cikin kowanne kiftawar ido) she wants to feel herself in his arms like before,and tell him how much she love him abubuwan da ta ke ji a lokacin masu yawa ne da harshe ba zai iya bayyanawa ba. Babban tashin hankalinta ba ta san yaushe za ta ganshi ba ya ce zai zo ta ce aah ya ce su yi magana su debe wa juna kewa, shi ma ta ce aah. Har ya gaji da bibiyarta ya yi barring dinta. Me ya sa wasu lokutan mu ke yin mistakes wanda bamu daukesu komai ba, kuma ba ma sanin kuskure ne sai daga baya???
Cikin wannan halin Hafsat ta sauka a Abuja. Zuciyarta ta kara raunata da ta hango Maryam Dakata da kanta ba sako ba! Haleem ya kawo ta filin jirgin Nmadi Azikwe tana jiran isowarta kamar wadda ta dawo daga wata kasa. Ai tana isa gare ta cikin reception(she cannot control her tears). Fuskarta Mammah din ta saka cikin tafukan hannayenta tana tambayarta ko lafiya?, Kukan da ba ta san dalilinsa ba.
To ko a sake yankar tikiti a koma Jimeta ne?
Ta fada cike da damuwa.
Hafsat sai ta rungume ta cikin kuka ta ce. Ba fa Jimeta zan koma ba
Dariya ta yi ta riko hannayenta suka nufi mota, To ko in bude ciki ki koma???”
Haleem dake bayansu haushin maganganun su da shagwabar Hafsat ya ishe shi, ya karaso ya sha gabansu.
Mammah, kin san Allah yarinyar nan don ta ga ba ki da babya gabanki ne ta ke miki shagwaba, she better brings you a baby soon ko yaya Azeez ya kara aure. Yayi maza ya koma bayan Mammah.
Wata harara ta juya ta galla masa, kuma har zuciyarta zancen ya mintsine ta. Gwalo ya yi mata ta bayan Mammah wadda ta hau shi da fada tana fadin ita ba ta son expensive joke haihuwa kuma ta Allah ce. Ita ma ta faki idon Mamman ta yi masa gwalo ga hawaye shabe-shabe a idonta,maimakon ta ba shi haushi sai ta ba shi dariya. Ba zai iya tuno yanayin kwayar idanunta ba sanda ya ce “Yaya Azeez ya kara aure!.
Azumi na ta oyoyo da dawowar Hafsat, ta cika ta da abinci kala-kala. Ismael ya ce, Ina tsaraba?
Tulin kayan da Daada ta hado wa Mammah ta nuna masa. Da kanshi ya hau budewa yana ware komai gefe, akwai kindirmo sabo fari sol a cikin sabuwar farar jarka, akwai sabuwar ‘maasa da kuli’ fal a leda, su ya kinkima ya yi kitchen da su ya bar sauran tarkacen a nan, sai Azumi ce ta kauda su ta kai wa Mammah komai inda ya dace, Ismael ya ciko plate da maasa da kuli ya zo falo yana ci kenan Usman ya shigo, Shagali! Yar fillo ina nawa?
Yamutsa fuska ta yi,
Ni ba yar fillo ba ce.
Ya ce, O.k Toh Lemme say Jimeta Lady a zamanance. Yayi???.
Kafin ya rufe baki Baba Azumi ta kawo masa nasa Masan shake taf da plate.Bayan kulin ta yanka cabbage da cucumber akai. Da godiya ya karba ya ce.
Baba Azumi, Allah ya nuna min aurenki!
Me za su yi ba dariya ba har ita din. Azumi ta rangwadar da kai ta ce, Mujaddadi (Usmanu) mai babban suna, burina in ga naka kafin in ga nawa. Ya ce, Insha Allahu har liki zan miki wajen dinner.
Mammah ta shigo falon tana fadin Hafsat ta je ta kwanta ta huta, kuma su daina kwarzabar mata Azumi. Baba Azumi ta ce, Jin dadina da farin cikina in gansu haka dukkaninsu a gabana muna hirarmu, ina tuno kuruciyarsu ta Jeddah da Beljiyan.Rai ne, watarana babu shi!.
SUMAYYA ABDULQADIR TAKORI
07030137870
*Littafi na farko shine kawai free. 234 na sayarwa ne. Idan ka fidda 234 ba sai na hada ka da Allah ba zai isar min insha Allahu. Ku biya Ku karanta a nitse cikin farin ciki yafi maka kayan zunubi ranar gobe kiyama*
*****
Bayan sallar isha Mammah ta tadda Hafsat a dakinta, kayanta ta ke gyarawa cikin wardrove wadanda ta dawo da su. Janye ta ke da akwatuna biyu masu matukar kyau. A tsakar dakin ta zube su ta ce ta bude ta duba wanda bai mata ba ta aje a bayar a Kano. Dinkuna ne yan uban-ubansu daga atamfa, leshi, material zuwa ready made na voils din zamani da mayafansu. Hafsat ta hau dagawa cike da shaawa ba wanda ba ta ji ba ta so ba, amma don kada ta yi hadama sai ta ce a raba biyu a bayar din. Mammah ta ce.
Dama mace tana kyautar da manyan kayan lefenta?? Cikin kayan lefen da kuka tsibe a Sun-City’ ne nasa aka dauko min na tsince manyan na bayar aka dinka miki.
Kunya ta ji, ta rage murnarta a kan kayan, ita ta manta da wasu kayan lefe. Mammah ta juya ta fita tana fadin ta je Daddy na kiranta.
Tsallake komai ta yi ta yafa yalwataccen mayafi ta nufi sassan Daddyn.
Da sallama ta shiga, Yau wace rana Daddy ba ya aiki a takardu, News yake kallo? Hafsat ta ce a zuciyarta.
Amsa sallamarta ya yi, ya kuma umarce ta da ta zo gefensa ta zauna. Abin da ya kara mata jin nauyinsa don ba za ta iya tuna rana ta karshe da ya ce ta zo kusa da shi ta zauna ba. Cikin matsanancin ladabi ta bi umarninsa, sannan ta gaishe shi. Ta lura yau Daddy cikin faraa yake sosai, ya ce, Suhaanah an gama jarabawa lafiya, sai hutu ko?
Murmushi ta yi, ta ce, Ai hutun ba yawa Daddy, har mun ci sati daya.
Gyada kai ya yi, ya ce, Mammanki ta gaya miki za ki bi mijinki ki karasa hutun tare da shi?
Da sauri ta dago sai kuma ta tuna da wa ta ke magana, ta yi maza ta sunkuyar. Mafarki ta ke ko idonta biyu? Ko dai cikin mafarkanta ne masu nuna mata Abdulazeez a dan tsukin wadanda suka zame mata jiki a yanzu? Ajiyar zuciya ta sauke a hankali, kafin ta girgiza kai ta ce masa.
Aah, ba ta yi min zancen ba.
Cikin kulawa ya ce, To sai ki je ki hada abin da za ki bukata, Im sorry you areto fly alone (ke kadai zaki tafi), na san za ki iya. A rage cost din dan rakiya, mu ma kuma za mu tafi umrah gabadaya duka a goben, amma za ki riga mu tashi. Za mu tashi Saudiyyah karfe biyu na rana, ke kuma za ki tashi zuwa America sha biyu na rana. Ungo nan. Ya miko mata passport dinta da tickets a tsakiyarsa. Jiki a sanyaye Hafsat ta karba ta yi godiya, za ta mike ya ce, Kada ki damu direct flight na nema miki har can babu (transit) kina sauka kuma zai dauke ki, ya san lokacin tasowarki da sauka. Duk da haka ki kunna wayarki da zarar kin sauka.
Hafsat ta rasa a wane yanayi ta ke jin kanta, farin ciki ko taradaddi? A haka ta isa dakin Mammah. Daga bakin kofa ta rabe kamar mara gaskiya. Mammah ta yi kamar ba ta ganta ba, ta ci gaba da gyara kayanta cikin closet dinta. A ranta ta ce, Gulmar banza, bayan ji ta ke kamar ta goya ni.
Hafsat ta gaji da tsayuwa don kanta ta karaso ciki, a gefen gadon Mammah ta zauna ta dukar da kai. Ba ta ce mata komai ba yau za ta ga karshen fillanci. Ita da kanta shirun ya dame ta, ta motsa bakinta amma ta rasa jumlar da za ta hada wadda za ta bada maana. Tausayinta da kaunarta suka cika zuciyar Hajiya Maryam, irin macen da ta ke yi wa yayanta fata da buri kenan, mace mai kawaici, addini da alkunya. Yanzu fatanta yana kan Ismael da Usman Abdulazeez ya gama dacewa.Sai dai ga dukkan alamu burinta a kan Usman da Haleem zai cika, Ismael kam ya ce sai irin wadda yake raayi shi ba Yaya Azeez ba ne. A wannan karon ta sanya a ranta ba za ta takura wani a cikinsu ba kada a zo a samu irin matsalolin da aka samu a na farko ba don Allah ya nufa auren rayayye ba ne, kuma aka yi saa suka kaunaci abin daga baya. Da saki uku Abdulazeez ya yi kuskuren yi ba ta san ya za ta yi da kayan nadama ba, da kallon Hafsat a gabanta matsayin bazawara a shekarunta da ko ashirin ba su kai ba.
Don haka tsakaninta da yan baya addua ce da fatan alkhairi babu tursasawa. Yanzu kam hankalinta ya kwanta, zuciyarta cikin farin ciki ta ke da wannan buri da Allah ya cika mata na sanya Hafsat-Suhaana cikin ahalinta, tsatsonta, jininta, kuma uwa ga jikokinta na farko. Su Ismael su yi yadda suke so za ta bi su da addua.
Karasowa ta yi gabanta ta cire mata tagumin da ta yi. Hafsat ta dago ta dubi Mammah, sai ta ji hawaye sun ciko idanunta. Ba ta san ta ina za ta fara cewa za ta yi kewarta ba. Ji ta ke kamar yanzu ne karo na farko da za ta bar gida zuwa gidan miji kamar ba a yi hakan a baya ba, kamar ba yan satittika aka ce ta je ta yi ba! Kamar idan ta tafi ba za ta dawo ba take ji!!! Ba ta yi aune ba sai hawayen suka balle. Salati Mammah ta yi duk da a hankali ne, ta ce, Ko ba kya son zuwa ne Addah? In ba kya son zuwa babu komai, ki yi zamanki har ya dawo, amma sai dai ki tafi Kano tunda ba a yi visar Saudiyyah da ke ba, Azumi ma Sokoto za ta.
Hawayen ta share da sauri, Aa, Mommah. Murmushi ta yi, da ma tsokanarta ta ke yi don ta ji cikinta ne. Ta ce To ai kukan da ki ka zo ki ka tasa ni a gaba kina min sai ki tada min hankali, in ba hakan ba ne mene ne?
Hawayen ta ke ta gogewa da gefen mayafinta. Mommah, ina tunanin yadda zan zauna a wani wuri babu ke ne.
Dariya ta yi. Da ki ka zauna a gidanki tsayin shekara da watanni ni na taya ki zama? Ki sa a ranki kamar unguwa ki ka je ki ka dawo, za ki dora daga inda ki ka tsaya. Sai dai wannan zaman zai kasance ba irin na baya ba. Shi wannan akwai focus, kuma komai ki ka yi a cikinsa kin yi ne don neman aljannah. Wancan kuwa na sabo ne babu lada a cikinsa sai alhaki. Ku rike istigfari koyaushe ki bi mijinki ku zauna lafiya. Gidana babu space na yaji tunda wannan karon ba ni na tursasa ku zama da juna ba,don haka bazan yi tolarating kowanne nonesense daga dayanku ba. Ku yi hakuri da juna tunda kun ce kun ji kun gani kuna son zama da junanku, sai a yi zama na soyayya da amana. Tashi ki je ki hada abubuwan amfaninki. Kayan da ki ke amfani da su duk ki barsu ki yi amfani da sababbin da na baki. Mu kwana lafiya.
Hafsat na shirya kayanta cikin babbar jaka tana hawaye. Haka kawai maganganun Mammah ke shawagi a kanta. Wadanda ke nufin wannan karon za su yi zama ne ita da Abdulazeez irin na kowadanne maaurata babu interference na iyaye. An ce kuma cikin zaman aure akwai kalubale mai yawa wanda duk son da ake wa juna sai an yi hakuri. Daya zai iya bata wa daya rai kuma dole ya yi hakuri. Ga Abdulazeez mutum mai wuyar shaani, abu kadan zai nuna ransa ya baci. Tana rokon Allah ya ba ta nasara cikin zama da shi ya dinga sassauta zuciyarsa a kanta.
Salisu direban Daddy shi ya kwashi dukkan jamaar gidan da kayayyakinsu a washegari zuwa filin jirgin saman Nmadi Azikwe. Ismael da Usman ne suka yi ta yi mata shige da fice na awo da immigrationcheck har ta shiga jirgi da kayanta bayan sun yi bankwana da juna.Ba ta dade da shiga jirgi ba su ma aka fara screening din kayansu. A kan idonsu jirginta ya keta hazo ya lula cikin sararin samaniya.
A lokacin ne Daddy ya fiddo waya ya kira Abdulazeez ya gaya masa tasowar Hafsat da lokacin da za ta sauka. Yadda ta ji maganar bagatatan haka shima ya ji. Amma ya yi kokari ainun ya rike kansa da reaction dinsa, ta yadda Daddyn bai gane yadda ya karbi zancen ba. Ya ce masa dai insha Allah zai je ya dauke ta a kan lokaci, sannan ya kara da godiya. Daddy ya juya ya ce da matarsa.
Kamar bai yi murna ba!.
Mammah ta ce.
Itama ai ba ta yi murnar ba, har da kuka, Oho su suka sani!.
******
HADUWAR AMARYAR DA ANGON!
Jirgin Egypt Air ya sauke Hafsat-Suhaanah a birnin NewHaven din Connecticut da misalin karfe bakwai na dare agogon kasar Amurka. Jamiar da Abdulazeez ya zo, wato (YALE UNIVERSITY) tana cikin New-Haven din jihar Connecticut. A sannu ta biyo bayan jerin gwanon fasinjojin da ke saukowa daga matattakalar jirgi rataye da jakarta louisVuitton a kafadarta ta dama. Bakar abaya ce a jikinta ta nade kanta da dan mayafinta. Fuskarta ce kawai a waje, ta yi fayau sabida baccin da ta sha a jirgi. Takalmin kafarta mai tsayin dunduniya ne siririya wadda ta daure igiyoyinsa a idon sawunta. Saukarta a sararin airport din Bradely International Airport ya tuna mata da abubuwa da dama; rayuwarsu a Belgium da kewayenta, bambancin ba mai yawa ba ne da nan.Amma in ka dubi tsakiyar idanunta za ka hango yar kankanuwar damuwa makale cikin kyawawan idanunta wadanda bacci ya canza musu launi.
Shin Abdulazeez ya san da zuwanta? In ya sani da yardarsa aka turo ta? Shin wace irin tarba za ta samu daga gare shi? Ta yi masa wani alkawari mai girma da yau ce ranar cika shi Alkawarin cewa duk ranar da suka hadu; babu kunya a tsakaninsu..... And It will be a day in history! Yau ga ranar ta zo, amma ta zo a wani irin jirkice; Abdulazeez din yana fushi da ita.
A yayin da tata zuciyar ke cike taf da alamura masu wuyar fassaruwa;so much love, so much affection, so much devotion, so much emotion, so much respect for him and so much many more things!!!Ina ma ana dawo da hannun agogo baya? Da ta yi rewinding ta goge duk wani laifi da Abdulazeez ke ganin ta yi masa! Bata yi da gangan don ta bata mishi rai ba. Bata dauki hakan laifi bane sai da ya nuna bacin rai akai. Ina ma ya kasance cikin mutane masu saurin yi wa abokan rayuwarsu uzuri kamar yadda kullum ita ta ke yi masa? Da Allah kadai ya san muhimmancin ranar yau a gare su.
Duk da dare ne amma koina haske yake da fitilu masu tsananin haske wadanda ko allurarka ce ta fadi za ka duka ka dauki abarka ba da wuya ba. Kanta tsaye ta ke tafiya janye da jakarta bayan ta dauko ta daga kayan da jirgi ya sauke. Kujerun da matafiya ke zama don jiran masu daukarsu ko hutawa ta nufa ta zauna da jakarta a gabanta. Alal hakika ta gaji tibis, kwanciya kawai ta ke son yi a lallausar katifa, ba ta tare da yunwa don ta ci abinci a jirgi, abincin ma na mukami domin kuwa a first class seats ta zo. Tunanin ta inda za ta ga Abdulazeez ta ke yi cikin dubban mutanen nan farare, jajaye da bakake. In bata yi kuskure ba tace har da shudaye da koraye. Ta tuna Daddy ya ce ta kunna wayarta. Tana laluben wayar cikin jakarta ta ji an zauna a gefenta. Kafin ta dago Creed Aventus ya ziyarci hancinta da karfinsa. Kafin ta farfado ta ji muryarsa mai amo da karsashi (husky) cikin kunnuwanta.A yayin da ya rankwafo sosai daidai kunnen nata har tana jin sanyin numfashinsa.
Welcome to New Haven!!!”.
Abinda Ya rada mata kenan. Muryar ta kara gardi da dadin sauraro fiye da koyaushe. Ko kuwa ita kadai ta ji hakan? Bazata iya cewa ba! Lumshe idanunta ta yi, kafin a hankali ta bude su tarr a kanshi. Dauke kansa ya yi ya dubi wani gefen daban, We can go (zamu iya tafiya).
Wani irin kallo ta bi shi da shi kasa-kasa, zuciyarta na melting. Ya kara tsawo fiyeda wanda ta san shi da shi, ya yi wani irin freshya saje da black-Americansdin da ke giftawa jefi-jefi. Sai dai kuma ya yi musu zarrah kasancewar shi akwai hasken addinin musulunci a tare da shi da cikar zati da kamala. Wadanda suka samar da wani irin kwarjini a tareda shi. Sanye yake da dogon wando da riga Long-sleeved(Burberry Hartford) ruwan makuba. In ta ce;he is handsome is not enough to convey thehandsomeness, ta san hakan tun tana karama da ta ke ganinsa a gidansu a Jeddah. Ta kuma sha fadin hakan a zuciyarta cewa ya fi duk yan gidan kyau mai daukar hankali, sai dai kuma duk sun fi shi kirki. Har gobe hakan ne a wurinta, sun fi shi saukin kai da dadin muamala, ya fi su Psychological Charisma.
A haka ta mike cikin sanyin jiki, za ta ja jakarta ya sanya hannu ya dauka, suka jera zuwa harabar airport din inda motocin haya suke jiran fasinja. Tun kamin su karasa wani siririn bature ya iso gare su ya karbi trolley din daga hannunsa yana tambayarsu inda za su je. Hannunta ya kama ya rike cikin nasa suka shiga farar taxi din mai matukar lafiya da sabunta. Sai da suka fara tafiya Abdulazeez ya ce da shi.
NewHaven Towers!.
NewHaven TOWERS, gidan bene ne mai kunshe da gidaje masu yawa(apartments)da mafi yawan daliban Yale ke zama, ana kiran daliban Yale University da (Yalies).Apartmentsdin ba iri daya ba ne, ya danganta da yadda ka ke so, single room, onebedroom, two bedrooms ko three bedrooms. Suffofin New Haven TOWERS sun hada da proximity ga jamiar Yale, wuraren siyayya, wuraren cin abinci, libraries, museums, parks da duk