Showing 78001 words to 81000 words out of 168255 words

Chapter 27 - Auren Kwangila Book 4 Hausa Novel Complete

Takori   

12 Dec 2024

315

yanzu ka daina sona.
Dariya ya yi wadda ta fiddo fararen hakoransa bakidayansu, Ke me ya sa ba wuya ne ki ce an daina sonki? An gaya miki ana fara son mutum don a daina ne? Youre special sis, ke da Yaya Azeez mutu-ka-raba takalmin kaza, ba yar gayu ba, ko yar sarkin Istanbul haka za ta ganku ta barku. Na tsaya miki sister, ko Mammah?
Mammah ta shimfida ledar cin abinci a tsakiyar falon gargajiyansu (African parlour) ta soma shirya plates da cokula ba ta kula shi ba. Can kuma ta ce,
In mutum ya ce shiga abin da ba ruwansa shi ne sanaarsa, ai sai kowa ya ja baki ya yi shiru ya zuba masa ido ya yi ta yi har Allah ya gajisshe shi.
Hafsa ta ce, Sosai kuwa Mammah.
Ta faki idon Mammah ta yi masa gwalo.
Abdulazeez bai kara kula su ba, wayar hannunsa yake daddannawa yana duba sakonni.
Funkason fulawa ne da sinasir da miyar agushi wada ta ji alayyahu da ganyen ugu da naman saniya, mammah ta dafo musu. Ita ta yi serving kowa. Daga Abdulazeez har Hafsat sun ji dadin abincin, sun bude ciki sosai sai ci suke don rabon kowannensu da cin kwakkwaran abinci cikin sukunin zuciya, tun fadansu. Babu wanda ya kara samun nutsuwar zuciya irin wanda ya samu a yau. Lallai UWA rahma ce, kuma komai girman Dan Adam yana bukatarta. Allah ka kara wa iyayenmu lafiya da nisan kwana mai albarka.
Mammah sarkin saido ta yi mamakin irin yadda suke ta narkar abincin nan. Ga shi da alama kowannensu ya rame idonsa ya fada, sai satar kallon junansu suke. Ko dai gaskiyar Ismael ne Hafsat ba ta girki? Amma da wuya hakan ta kasance don da ita dai ta san ba sakaran kiwo ta yi wa Addarta ba. Kusan koyaushe tare suke girki in tana gida, musamman da suka dawo Nigeria inda ba ta zuwa makaranta. Ta yi ajiyar zuciya har sai da kowa ya dago ya dube ta. Ta kudurce a ranta za ta binciki Hafsat ta tabbatar tana dafawa mijinta abinci ko ba ta dafawa.
Garin kalle-kallen Hajiya Maryam idonta ya fada kan kasaitaccen hoton Muazatu kafe a bangon gabas maso kudu na falon. Idonta ta kafa wa hoton tana son tuno inda ta san fuskar, kamar ta taba ganinta a wani wuri amma duk kokarinta ta kasa tuno inda ta gantan.
Adda wace ce wannan? Ta tambaya cikin mamaki tana mai nuna hoton da dan alinta.
A lokaci guda ita da Abdulazeez suka kai idonsu ga inda Mammah ke nunawa. Gudun jini ne ya katse a jikin Abdulazeez zuciyarsa ta yi wani irin bugu, wani rugugi ya ratsa a cikin kansa. Tun sanda ya kafa hoton don ya bakanta wa Hafsat bai kara tunanin zaman nasa kuskure ba ne, ko tunanin wani zai iya zuwa ya gani ya tambaya balle Mammah, mutum ta karshe da bai taba kawowa ba cikin masu ziyartar gidansa sabida fillancinta na alkunya.
Hafsat ya duba da sauri suka hada ido, ta yi saurin dauke kanta ganin ragaita da muzantar da ke cikin kwayar idanunsa. Saura kadan dariya ta kufce mata, amma ta hadiye.
Da ma an ce in za ka gina ramin mugunta ka gina shi gajere, ba ka sani ba ko kai za ka rufta. Halacci da yawa ya yi mata a rayuwar aurensu ta tsayin watanni shidda, ko da ya bata mata alherinsa ya rinjayi kuskurensa. Ta tuno ranar da ta san ko ita wace ce a cikinsu Abdulazeez bai kyamace ta ba, ya ce da ita; ita ba shegiya ba ce da ubanta a gaban iyaye da yan uwansa. Ya ce, uwar da ta haife ta ba ta yi kama da mutuniyar banza ba. Mace ce mai cikar mutunci, mai kirkin gaske. Ya sha alwashin nemo mata uban da ya haife ta da nemo mata yan uwanta na jini ya sadar da ita gare su cikin dan lokaci kalilan.
Kafin a yi haka Abdulazeez ya yi mata alheri da kyautayi mai yawa a cikin gidan nan... she adores him much... she respectshim alot... duk wata kulawa da ya kamata a baiwa mace a gidan aure yana bata kafin suyi fada. Samunbakinta ta yi da budewa yana bai wa mahaifiyarsa amsa ba tare da ta shirya kalaman a kan harshenta kafin ta furta su ba.
Kawata ce Mammah... sunanta Faizah.
Abdulazeez ya yi baya ya lumshe idonsa yana maida numfashi, ya dauki mintuna bai bude ba. Ya yi kasa da kansa, Hajiya Maryam mamaki ya kashe ta a zaune.
Kawa Addah? Shi ne ki ka makala ta a bangon dakinki? Kullum mijinki na tozali da ita? To bakya kishin mijin ne? Da gani ma wannan ai ta girme ki kuma da kyar in ba ta da aure? Ni yaushe ma ki ka canza hali har ki ka saki jiki da kawaye? Maza-maza sauke shi tun kafin in sabar miki.
Jiki na rawa Hafsat ta mike ta hau kici-kicin sauke hoton, amma ta kasa. Mammah ta juya akalar fadanta kan Abdulazeez.
Ban so zuwa gidan nan ba, ashe rashin zuwan nawa kuskure ne babba, kana ina Addah ta yi kawance da wannan mai soyayyen idon kamar an soya gyada marau-marau ba ka tsawatar ba? Dubi kirjinta duk rabi a waje bakinta kamar na karuwai an kafe ta a falonka wai matsayin kawar matar gida, kai kuma ka bari. Za ki sauke hoton nan ko sai na kwankwatsa shi a tsakiyar dakin nan?
Hafsat ta soma hawaye, duk ta bi ta gigice, ba ta taba jin Mammah na fada haka ba. Hannunta sai rawa yake haka hoton, ga shi ta kasa cire shi. Tasowa ya yi ya iso gare ta, gabadaya jikinsa ya mutu,
Lemme help.
Ya fada mata cikin kunnuwanta da tattausan lafazi.
Zagaye ta ya yi cikin hannayensa kamar ya rungume ta, a haka ya ciro hoton ya sauke shi kasa. Mammah ta bi su da kallo, duk su biyun sun sunkuyar da kai, sai ta kasa ci gaba da fadan. Suka koma inda suka tashi suka zazzauna. Ismael ya ce,
Ni wallahi ma kamar na santa.
Abdulazeez ya galla masa harara, Mammah ma ta ce, Ah toh, ni ma kaina kallon sani nake mata. A ina ta santa? Ta jefa tambayar ga Abdulazeez.
Shiru ya yi kamar ba da shi ake ba, sai da Mammah ta kara maimaitawa. Cikin sanyin murya Hafsat ta ce, makwabciyata ce.
Tana da aure?
Girgiza kai ta yi a hankali alamar babu.
Hajiya Maryam ta ji kamar ta rufe Adda da duka don haushi, wane irin kwantaccen kai ne da ita? A yi mutum kamar sakarai bai san halin da duniya ke ciki ba sam? Ko dai ba ta kishin mijin ne? Watakila don ba sonsa ta ke ba, amma ko yaron goye ai ya san kishi. Zuciyarta ta zo wuya da yawa, in ta ci gaba da kallon Hafsat dukanta za ta yi. Mikewa ta yi tana gyara daurin zaninta da mayafi alamar tafiya.
Baba Azumi ma ta mike, Ismael tattara kwanukan nan ka kai mota, mu za mu wuce, sai gani na biyu.
Idanun Hafsat suka kawo ruwa, ta tabbatar ba karamin bata wa Mammah rai ta yi ba. Zuwanta gidan kenan na farko tunda ta aurar da ita, amma ba ta tsinci komai cikinsa ba sai bacin rai. A kan laifin da ba nata ba. Hasalima wanda ya yi laifin ya yi ne don ya wulakantata ya nuna mata ita ba wata tsiya ba ce a gare shi. Ga shi ta juye komai a kanta don shi ya tsira daga fushin mahaifiyarsa.
Ga mamakinta ta kasa yin nadamar abin da ta yi, gara ranta ya baci da na Abdulazeez dinta! Duk yadda ya so su hada ido don nuna mata godiyar da ke cikin idanunsa ta ki yarda. Ba ta yi don ya gode mata ba, tunaninta yanzu na yadda za ta shawo kan Mammah ne ta daina fushi da ita.
Har mota suka rako su, ta bude wa Mammah kofar mazaunin baya ta zauna, Azumi da Ismael direba na gaba. Kasa rufe murfin motar ta yi ta tsugunna a kan gwiwoyinta a kan cinyar Mommah ta soma kuka. Baba Azumi ta ce,
Me ya yi zafi Addar Mamanta? Ba za ki yi ba daidai a yi miki fada ba?
Kin san shagwababbu ba su yarda sun yi kuskure, Mammah da kin kyale mata hoton ta har Yaya Azeez ya ji yana son Faizar ya auro ta mu ga karshen kawance. Cewar Ismael.
Ciro kai ta yi fuskar nan jage-jage da hawaye ta ke harararsa. Dariya yake sosai, ya ce, Ni ki matsa in ja mota za ni zance wajen Wasilata.
Duk yadda ta so Mammah ta sakar mata fuska ta ki yin hakan, har Ismael ya ja motar Danfulani ya bude musu suka hau kwalta don barin shiyyar rukunin gidajen (Sun-City).
Shi dai Abdulazeez ba baki sai ido, hannun damansa ya sanya cikin tarin sumar kansa yana cakudawa. Daya daga cikin aladunsa in ya san yayi ba daidai ba. Yau ba don wasu dalilai masu yawa ba tsugunnawa zai yi ya goya Hafsat-Suhaana, ya kai ta har tsakiyar gadonsa. Duk da haka zai gaya mata ya gode da irin godiyar da ta dace. Su Mammah na ficewa ta yi cikin gida da sauri ko kallonsa bata yi ba. Da hoton Muazatu da suka sauke ta fara cin karo. Tsaki ta yi ta bi ta kansa da takalmi ta wuce dakinta. Ta turo kofar za ta rufe ya sa hannayensa ya tare.
Karfi ta sa wajen son rufe kofar ya nuna mata nata karfin rabin cokali ne, domin turowa daya ya yi ya shigo dakin ya maida kofar ya rufe. Jingina ta yi da kofar ta rufe idonta hawaye na zuba.
Habarta ya kama da hannun damansa ya dago fuskarta, ji yake kamar ya sanya halshensa ya dauke hawayen da ke zuba kamar an sunce famfo, wata zuciyar na hana shi. Maimakon hakan, yatsunsa biyu Hafsat ta ji a saman fuskarta suna share hawayen. Sosai ta kara tamke idonta sakamakon jin wani abu mai kama da jan wutar lantarki na bin jikinta.
Yi min komai da zuciyarki ta ga Ideserve as a punishment Suhaana, amma ki kwantar da hankalinki, ina mai tabbatar miki Mammah ba za ta iya dogon fushi da ke ba, so kawai ta ke ta nuna miki kin yi wauta, amma ba fushi ta ke da ke ba.
Magana Abdulazeez ke yi kasa-kasa, ta yadda ba don ta kasance cikin masu kyakkyawan ji ba, da ba za ta ji shi ba.
Wata irin kasala ta ji tana saukar mata, bude idonta ta yi a hankali ta dube shi. Damuwarsa kadan ce a kan abin da ya faru. Ji ta yi ya janyo ta jikinsa a hankali ya hade su sun zama mutum daya. Sosai ta ji nutsuwa na shigarta hawayen idonta na daukewa. Kamshin jikinsa na jefa ta cikin wani irin shauki mai wuyar fassarawa. Dankwalin kanta ya zame ya fadi kasa gashin kanta ya wargaje ya rufe hannayen Abdulazeez da ke zagaye da ita. Ba ta iya aune ba ta ji hannayensa cikin gashin kanta, bakinsa kuma cikin nata. Kissing dinta yake yi tun daga kololuwar zuciyarsa. Alamarin da ya jefa su cikin wani irin yanayi dukkaninsu da ba su taba ji ba a rayuwarsu. Daga can tsakiyar unguwa aka kwada kiran sallar laasar. A yau duk jarumtar Hafsat ta kasa yin protest din, ta kuma kasa yin kowanne kokari na juya wa Abdulazeez baya, ta nemi duk wani kyakkyawan tunani da ke cikin kanta ta rasa.










SUMAYYA ABDULQADIR TAKORI
07030137870

*Littafi na farko shine kawai free. 234 na sayarwa ne. Idan ka fidda 234 ba sai na hada ka da Allah ba zai isar min insha Allahu. Ku biya Ku karanta a nitse cikin farin ciki yafi maka kayan zunubi ranar gobe kiyama*

Ladanin ya ci gaba da kwada kiran sallah har tsakiyar kwanyar Hafsat. Tana cikin mutane masu matukar kiyaye lokacin sallah. Zame jikinta ta yi, an yi saa rikon da ya yi mata ba mai karfi ba ne sabida shi kansa ba shi da karfin, dukkansu zubewa sukai a kan marbleskowanne na kokawar nemo consciousness dinsa. Kafin kunya matsananciya ta zo ta lullube Hafsat, ta sanya kanta cikin kafafunta ta kasa dagowa. Abdulazeez ta ji ya kwantar da kai a bayanta ya yi shiru kamar ba ya jin kiran sallar da ake ta yi. Muskutawa ta yi cikin jin nauyi ta yi masa magana.
Yaya Azeez ana kiran sallah?
Ina ji Hafsat, na kasa tashi ne.
Ko in daga ka?.
Ya jinjina kai, dariya na son kama shiduk da halin da yake ciki,wai ta daga shi kamar wani dan ta, har yanzu bai sauke kai daga gadon bayanta ba, Its not easy daga kato iri na. Amma tunda kince zaki iya zo ki gwada. Above all (fiye da komai) a yau, kuma a yanzu, ina so in ce miki NA GODE!
Murmushi ta yi duk da ta san ba kallonta yake ba.
NAGODE din ta me ce ce?
Dagowa ya yi daga kwanciyar da ya yi a bayanta ya juyo da ita gabansa suka fuskanci juna, kwayan idanunsa ya kalmashe a cikin nata ta yadda ba za ta iya dauke su ba in ba shi ya aminta da hakan ba.
For everything!.
Ya ba ta amsa da murya mai cike da mazantaka. Tana so ta dauke idonta amma ta kasa sabida bai ba ta damar hakan ba.
Ban yi don ka gode min ba Yaya Azeez, yi wa kai ne. Amma ni ma ka yi min alfarma ka maida hoton Aunty Muazatu dakinka, tunda ban fiya shiga ba.
Abdulazeez bai taba jin ya ji nauyin mace a rayuwarsa irin wadda ya ji yau na matarsa Hafsat ba. Ko ba ta fada ba bai yi niyyar maida hoton Muazatu falo again ba don mahaifiya ba wasa ba ce. Ba ya son tuna kalaman da Mammah ta yi amfani da su a kan Muazatu wadanda sun kara farkar da shi ya san cewa akwai babban aiki a gabansa. Mammah ba za ta taba son Muazatu ba komin sauyin da lokaci zai kawo. Shi ma kuma ba zai daina sonta ba komin sauyin da lokacin zai kawo.
Babban kuskuren Abdulazeez tunda ya fara soyayya da Muazatu bai taba bai wa Allah zabi a kai ba. Abin da ya sani kawai yana sonta, dole ya samar wa zuciyarsa abin da ta ke so don bai iya jure zama loser a komai. Not even in the court of justice. In aka kada shi (wanda da wuya ake samun hakan) har ciwo yake yi. Allah ya halicce shi mutum mai nasara a dukkan abin da ya sa gaba. Yana da yakinin a gaba ma zai yi nasara, zai samu Muazatu kuma zai daidaita da mahaifiyarsa a kanta.
Ita dai Hafsat tunda ta samu kalamanta suka jefa shi a tunani ta sulale ta yi bandaki. Sanda ta fito babu shi a dakin, sai kamshin turarensa. Ajiyar zuciya ta yi ta matsa gefen ibadarta ta tayar da sallah.
Bayan ta idar da sallah ta yi nafilfilinta sunkuyawa ta yi ta fada a tunani, abin da ya faru tsakaninsu yan mintuna kalilan ta ke tunawa da shauki mai yawa.Fondest thought! Wato tunani mafi soyuwa a zuciya. Ko ba a gaya mata ba, wannan shi ne romance na tsakanin miji da mata da a shekarunta da rayuwar da ta yi ta tsayin lokaci a cikin masu jajayen kunnuwa ya kamata a ce ta sani. To amma ai kuma masoya ke yinsa kuma ba ya faruwa sai da soyayya. Wannan na nufin..... wannan na nufin... tsakaninta da Abdulazeez Dakata akwai SOYAYYAH???
Tambaya ce da ta yi tsananin zurfi a kwakwalwarta har barin kanta ya soma ciwo. Wata murya ce daga can kasan ranta ta ke cautioning din ta.
Ki yi a hankali Hafsat! Be very careful!! Wannan rayuwar da Abdulazeez ya soma jefa ki a ciki kuma zuciyarki da gangar jikinki suka karbe ta da hannu bibbiyuwill ruin your entire future.tunda ya ce MATAR WUCIN-GADI ce ke, wani abu da Hausawa ke kira dandani haukaci, ya maida ke emotional, kuma ya yi dumping dinki ya dauki wadda yake yi wa so na hakika. Da ma dai a ce zai dauke ki da irin matsayin da zuciyarki ta dauke shi a yanzu ne, amma ki ja babban layi a kan wannan alamarin kowa ya tsaya a limit dinsa har zuwa karshen tafiyar.
Wani karfin zuciya ne ya shigi Hafsa a wannan lokacin. Ta yarda gaskiya ce zallah super ego side dinta ke gaya mata psychologically. Ta ci gaba da karfafawa kanta gwiwa da cewa, gara Abdulazeez ya yi ta fushi da ita, amma za ta tserar da martabarta no matter what! Yana son kansa da yawa duk da akwai adalci a cikin (selfishness) dinsa. Ya kamata ita ma ta so kanta, ta tanadarwa mai sonta na hakika abin da zai yi alfahari da ita. Wanda ba komai ba ne sai cikakkiyar Addah Hafsatu...... Haka kawai ta ji kuka ya zo mata, wanda ba na komai ba ne sai na tausayin kanta.
A masallacin unguwarsu irin fadan da Abdulazeez ke yi wa kansa kenan. To amma ya ya zai yi ne? Shi kansa yana mamakin alamarinsa da Hafsat, yadda yake zama ba shi ba muddin za su kadaice. Yana bukatar amini da zai gaya wa damuwarsa, ya ba shi shawara. Sai dai kuma Allah ya halicce shi wani mutum mai son rike duk wani sirri da ya shafi iyalinsa. Hatta Muazatu ba ta san tsakaninsa da Hafsat ba. A tunaninta rayuwa suke kamar kowadanne maaurata in ta yi laakari da yadda ta kusa rasa shi a kan kalamanta a kan aurensa. Gabadaya manyan abokansa Abdallah, Taufeeq, Esq Ahmad and co. Kalamansu na alkhairi ne a kan Hafsat tun lokacin aurensu. Yarinyar da komai nata da kamalarta sun kayatar da kowannensu, duk da sun lura kamar Abdulazeez ba ya sonta. Ba tare ya yi karatu da su ba, wajen aiki ne ya hada su, don haka ba su da labarin Muazatu kowani abu da ya shafe ta. Abdallah ya taba gaya masa ko bai son yarinyar nan wani lokaci zai zo da zai so ta, ko da zai mata kishiya. A lokacin ya ce da shi, Allah ya kiyashe ni zama da mata biyu. Kuma haka yake har kokon ransa.
Bai taba mafarkin zama da mace sama da daya ba a burikan rayuwarsa. Yana kuma rokon Allah kada ya jarabce shi. Ga shi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login