Showing 66001 words to 69000 words out of 168255 words
taba ganin irin wannan masifar ba, Muazatu dai! Komai Muazatu! Tana jin ranar da suka yi aure sai ya maida ita cikinsa don so.
To ke ina ruwanki? Wani bangare na zuciyarta ya tambaya.
Zuciyarta ta bada amsa nan take.
“Ni ma mace ce, ko da baa sona ina da zuciya irin ta yaya mata tunda muna tare, har zuwa ranar da za mu rabu. Watakila ranar ne zan daina damuwa da lamarinta.
Ba ta ankara ba ta ji hawaye sun shimfido mata. Sauri ta yi ta kai daya hannun ta share su. Bacin ranta na ninkuwa, ya hana ta tafiya kuma bai fasa wayarsa ba. Kalaman da ake fada a cikin wayar ba ta taba jinsu ba. Idan ta fizge hannunta ya ce ta yi masa rashin kunya.
Sun yi a kalla mintuna biyar a haka, sannan ya yi sallama da Muazatu.
...missed you Habeeb Qalby...
... missed you more habeebty...
Ya jefa wayar kan gado ya juyo ta suka yi facing juna. Duk da babu hawaye a kan kundukukinta idanunta sun yi jazur, kuma ya gane kuka ta ke yi. Kukan farin mutum ba ya buya,gabadaya fuskarta ta kada ta yi jazur.
Ban san abin da yake yawan sanya ki kuka ba. Fitar hawaye abu ne mai matukar sauki a wurinki na fahimta, cmmon zo mu zauna, ki gaya min ni ne nake sa ki kuka, ko kina yi kawai don ki ji dadi ne?
Janyo ta yayi ya zaunar a kusa da shi, jikinsu na gugar na juna.
Shiru ta yi masa kamar ba da ita yake magana ba. Ko ransa ya baci, to wannan karon bai nuna ba, ya yi appreciating kulawar da ta nuna masa a yau, a lokacin da yake tsananin bukatar hakan. Ya tuno kukan da ta rika yi ganinsa cikin halin rashin lafiya, wannan ya nuna yana da wani matsayi ko ya ya ne a zuciyarta, wanda bai san a wane rukuni yake ba tsakanin na miji da na dan uwa. Kusa da ita ya jawo tabledin da ta dora masa abinci.
“Lets eat, mu ci tare. Na tabbata ke ma ba ki ci ba.
Girgiza kai ta yi ranta a jagule, Ni ba na jin yunwa.
“Space din cikina zai ishe mu mu biyu, ki ci. I assure you cikina zai shigo.
Murmushi ta yi ta sunkuyar da kanta, ko ba komai yayi nasara ya fiddo murmushi akan fuskartahow could this be possible? Ta fada cikin raunin murya.
A duniyar yan uwantaka everthing is possible Hafsah, just eat, muna ci muna hira.
Dauke kai ta yi cikin mamakinsa, da ma haka yake? Haka yake Hafsat, in ki ka yi laakari da yadda yake tadi da Muazatunsa ke yake yi wa (horrowface), ke da ba ya so. Ta saci kallonsa ta gefen idonta, cin kazarsa yake da forka tsanake.
Sajen fuskarsa ya kwanta a kan kyakkyawar fuskarsa sai sheki yake kamar gashin kansa. Ta yi rayuwa a cikin larabawa da turawa ba ta taba ganin wanda saje ya yi wa kyau irin Abdulazeez ba, hancinsa gwanin kyau, idonsa abin shaawa, bakinsa..... dole wannan Muazatun ta nace masa tunda ta san ya fi ta komai.
Ba ta ankara ba ya juyo sai idonsa cikin nata, ya kama kwayar idonta red-handed tana yi masa kallon kurillah na babu gaira babu dalili, kallo mai zurfi mai cike da magana wadda bakinta ba zai iya furtawa ba.
Da sauri ta sunkuyar da kanta, shi ma ya shiga kallonta. Kafin ya yi murmushi ya juya ya ci gaba da cin abincin.
Tunda ta ce ba za ta ci ba, bai takura ta ba. Karamin firjin cikin dakin ya mike ya nufa, gwangwanin coca-cola ya dauko ya dawo gefenta ya sake zama.Maltinar data kawo masa ya ture gefe. (Hes a Coca-Cola addict). Budewa ya yi ya sha sosai, ya rike ragowar a hannunsa.
Hafsat me ya sa sanya ki kuka? Ya tambaya (in subdued).
Shiru ta yi ba ta ba shi amsa ba, to ta ce masa me? Abubuwa da yawa suna sanya ta kuka. Tana da tausayi, tana da raunin zuciya, ba ta son ji ko ganin alamarin Muazatu, shi kuma yana yi mata abubuwa da gayya tunda ya fahimci ba ta so din. Don haka yi masa shirun shi ne abu mafi alkhairi a gare ta. Barin zancen ya yi don ya yarda ba za ta amsa ba. Wani sabon zancen ya kawo har mamakin kansa yake yi. Tana basar da shi, tana komai amma kamar dole sai an yi hirar? So yake ya debe mata damuwar da ya ganta a ciki bayan kuma shi ne sanadinta.
“Who thought you how to take care of a patient? (Wa ya koyar da ke kula da maras lafiya?)
Girgiza kai ta yi, kafin ta amsa cikin kankanuwar murya, Nobody! Wato babu kowa.
Abdulazeez ya dube ta na yan sakanni, Sagir da yarsa na kara fado masa a rai, hatta yadda ta ke basarwa haka Sagir ke basarwa in yana ba da amsa. Ajiyar zuciya ya yi yana lissafi cikin zuciyarsa.
Hafsah. Ya kira ta da bayyanannen sauti. Dagowa ta yi a hankali ta dube shi, ya fi kowa iya kiran Hafsah, yana da wani irin taushin murya da dole in yana magana ka saurare shi, balle kuma in a kotu ne, jerarrun kalaman bakinsa na da daukar hankali da kowanne harshe yake yinsu tsakanin Hausa da Turanci. Yana da lafuzza nasa na kansa masu sanya mai saurarensa nutsuwa. Sosai ta ji wata irin nutsuwa ta shige ta, ta ba shi dukkan hankalinta don da alama magana mai maana yake so su yi ba wasan da yake ta janta da shi tun dazu ba, don gusar da bacin ranta.
Kafin a yi mana aure mun zauna, mun yi maganganu masu yawa ko? Wadanda suka shafi rayuwar auren da za mu yi, da lokacin da za mu yi (terminating) auren. Na fada miki cikin zamanmu babu takura, babu munanawa juna, babu zalunci. Kowa zai yi zaman kansa ne ya ci gashin kansa. Sannan ya cika alkawarin da ya daukarwa dan uwansa. Don haka yanzu da ki ka yi waya hankalina ya gaza kwanciya, don haka nake kara rokonki ki rike amanar da ke tsakaninmu ki san abin da za ki dinga gaya wa Mammah da su Ismaeel. Ta fannina ina nan ina ta kokarin cika alkawurra na, wane alkawari ne onyour side? Sake gaya min don in tabbatar ba ki manta ba.
Ga mamakin Hafsat ba ta farin ciki da zuwan ranar rabuwar nan yanzu. Amma ta fahimci rabuwar ita ce babban abin da ya sa gaba a yanzu tunda ga shi yana kara jaddada mata. Kara sunkuyar da kai ta yi, ta soma karanto masa alkawuran wadanda suke kwance luf a cikin kanta.
Mun rabu ne ba don ba ma son juna ba, sai don kowannenmu ya kasa jure hali da dabiun dan uwansa. Haka kaddara ta tanadar mana Mommah.
Kwanciyar sautinta yake bi da tasa zuciyar. A lokacin da ta ke furta kalaman. Ta fade su ne cikin kwantaccen sauti kamar da Mammah din ta ke magana.
Je ki kwanta Hafsat, na gode da kulawarki ta yau. Allah ya ba mu alkhairi.
Cikin nutsuwa ta mike ta bar dakin, ba tare da ta sake waiwayowa ba. Insha Allahu, daga rana irin ta yau za ta koya wa zuciyarta jarumta, ta daina hango komai sai ranar rabuwa. Bacin ran da ta ke sa wa kanta a kan Muazatu aikin banza ne Abdulazeez bai fa san tana yi ba. Ya yi nisa a kan Muazatu, nisan da ko uwar da ta haife shi ba ta isa tabuka komai a kai ba balle wata ita Hafsat da bai dauke ta cikakkiyar mutum ba, face wani tsani da zai bi ya taka ya kai ga cikar burinsa.
Don haka barcinta ta yi cikin nutsuwa har da munshari. Washegari da ta yi sallar asubah ba ta koma gado ba, kicin ta fada ta shirya masa break fast mai rai da motsi. Ko kafin karfe bakwai ta shirya komai tsaf a cikin food basket don ta dade da sanin ba ya karya kumallo a gida sai ya je office.
Daki ta koma ta yi wanka, doguwar riga ta saka kirar Dammam ruwan dorawa. Ta sharce kanta ta kame da katon bound shima (yellow). Turarrukanta ta feshe jikinta da su, sannan ta fito falo.
A tsakiyar falon ta tadda shi yana shirya wasu takardu a briefcase dinsa.
Morning Suhaana. Ya fada ba tare da ya dago ya dube ta ba yana ci gaba da abin da yake yi.
Gefensa ta karasa ta russuna tana gaishe shi.
Yaya jikin naka Yaya Azeez?
Wannan karon ne ya juyo ya dube ta, ta yi wani irin kyau da (fresh) kamar jinsin Somali. Hannun damanshi ya mika mata,
Gara mu yi irin wannan gaisuwar za ta fi gamsarwa.
Kunya ta ji sosai ta sunne fuskarta cikin tafukanta tana murmushi.
Tun a Brussels Mommah ta hana ni yin hannu da maza.
Idanunsa biyu ya fiddo mata, Kuma ta ce har mijin da ta daura miki aure da shi?
Mikewa ta yi, ta nufi daki da gudunta ta rufe kofa. Ba ta taba jin kunyar Da namiji a rayuwarta irin ta yau ba. Kamar wani abu daban ya bukaci su yi ba gaisuwa ba.
Ana fadin kalmar Miji sosai a cikin magana ba tare da mace ta ji komai a kai ba. To amma gare ta yadda ya fada din da tunedin da ya yi amfani ya zo mata da sabon salo, ga wani irin launi da kwayar idanunsa ta bayar na rikida a sanda yake fadin maganar kamar ba Yayansu Azeez ba. Wani kwayan mutum guda daya da ta ke wa fassarori masu yawa a baya tun daga shekarunta na kuruciya har girma zuwa dangantakar AURE da ya hada su yanzu. Kullum kuma daga sanin da ta yi masa zuwa yau sake rikida yake yana fitar da sababbin halaye da kamanni masu ban mamaki na yau daban da na gobe da ke sanyawa ta rasa gane inda ya sa gaba.
Wato gaskiya ne da aka ce, kada ka yi judging halin mutum sai ka zauna da shi. Idan ka ce za ka yi hukunci da fassarar zuciyarka a kan mutum, za ka fadi gaibu kuma Ubangiji subhana ya hana amfani da zato, domin zunubi ne. Zaman tare shi kadai yake proving who that person is (wane ne wannan mutum din).Abdulazeez kishiyar yadda ta dauke shi yake a bangarori da dama, barshi dai da raayin rikau irin nasa, amma mutum ne mai matukar kirki, kuma mai sanin yakamata. Masanin sirrin zamantakewa. Kokari yake daga jiya zuwa yau ya sa ta sake da shi ta daina wannan dari-darin da ta ke yi da shi. Sai dai ya manta cewa, duk wani abu da aka san yana da karshe to ba za a zira jiki a cikinsa ba. In yau sun yi musabaha gobe kuma sai Yayan musabaha ko babanta?
Jingine ta ke da kofa idanunta a rufe tana wannan tunanin. Ta tuno da abincin da ta shirya masa. Da gudu ta bude kofar ta fito ta sungumo basket din ta bi bayansa. Shi har ya isa ga motar ya bude zai shiga.
Yaya Azeez. Ta kira sunansa.
Waiwayowa ya yi ya kuma dakata da shiga motar har ta karaso. Kujerar baya ta bude ta sanya basket din, ya shiga motar ya tashe ta. Kanta ta zura ta window din side din da ya ke ta soma magana cikin sanyin muryarta.
Na san ka dade da daina tafiya da abincina ofis. Ban sani ba ko abokanka ne suka ce babu dadi? Amma yau ka yi min alfarma ka ci ko babu dadin, saboda ba ka da lafiya. Bai kamata ka zauna da yunwa bahar sai ka dawo.
Idanu ya zuba mata, ya kasa cewa komai. Ta ja da baya tana waving dinsa. Ya ja motar tare da daga mata hannu ya fita daga get din gidan nasa.
Sai zamansu ya dauki wani sabon salo mai ban shaawa. Kowanne kokari yake ya kyautatawa dan uwansa iyakar iyawarsa. Tun daga ranar Abdulazeez bai kara girki da kansa ba, girkin matarsa Hafsat yake ci safe da rana da daddare. Da safe zai tafi da shi, da rana zai turo a daukar masa, da daddare za su zauna su ci tare a dining ko a dakinsa. In ba shi da ayyuka da yawa su yi hirar mutanen gidansu ko ya ba ta labarin shariu iri-iri da suke yi a kotu.
Ya kan gaya mata cewa, rape case wato lamarin fyade ya fi yawa yanzu a kotunan Nigeria. Rannan yana bata labarin wata shariah ta fyade da suka yisai wani abu ya fado mata a rai, ta gyara zama ta hau bashi labari inda tace.
Ka ga sanda muke Brussels, akwai wani malamin mu Belgianya kan gaya mana each kind of sexual act is not a crime in their countryexcept rapeindai mutumya girma, yawuce shekara sha takwas.They teach this as sex education. Dana dawo Nigeria na kara hankali sai na fahimci cewa karya suke yi, every sexual act is prohibited, not only rape. Ba tare da kowa ya fahimtar da ni ba.
Abdulazeez rubutu yake yi, amma abin da ta ke fada sai ya dauki hankalinsa. Me ake da makarantun nasara?Hasbunallahu waniimal wakeelya ce cikin ransa. Dakatawa ya yi da rubutun ba tare da ya dago ya dube ta ba.
How do you came to know that? (Ta ya ya ki ka fahimci hakan)?
Ya tambaye ta, cikin kokarin danne kaduwarsa.
Sake gyara zama ta yi, ta soma bashi labari.
A secondary school dinmu ta ST. Barchmans College a ajinmu akwai wani yaro Bature Fayol da wata yarinya Jessica, a gaban kowa suke kissing. Ban saba ganin wannan aladar ba a inda na baro (Jeddah) don haka hankalina ya tashi na gaya class masterdinmu don ya hana su. Sai ya tara mu duka ya ce, They are not committing a crime, since its not a rape. Amma yanzu shekarunsu sun yi kadan su dinga aikata hakan su bari sai sun gama high-school. Na so in gaya wa Mommah a lokacin na ji tsoro sanin cewamuddin taji sai ta cire ni daga makarantar nikuma inason makarantar saboda na saba da ita. Amma na sa a raina abin da malamin nan ya fada ba gaskiya ba ne, wannan aiki ne na arna marassa addini. Turawa ba wani abu ba ne a wurinsu ko a hanya za ka iya ganin suna kissing, masu aure da marasa aure.
Da muka dawo Nigeria sosai na ga bambanci mai yawa. Ban ga mata na rungumar maza ba wai don ana goodbye, ban ga ana kissing a kan titi ba. Abubuwan da na saba gani duk bana ganinsu a nan. Ko masu aure ban ga suna yi ba. I then concluded that; things like that are not accepted here in Nigeria and hence, its a crime in Islam and culturedaga manya har yara, masu aure da marassa aure.
Abdulazeez gumm! Ya yi, ya ki ba ta amsa.
Haka ne ko ba haka ne ba? Ta tambayeshi curiously.
Ban sani ba Suhaana, tunda dai kin ga ni ba ni da mata. Ya amsa a gajarce, cikin son a bar zancen.
Da sauri ta ce. Ba ga ni ba?
Dariya ce ta kama shi, amma ya gintse, saboda yadda ta fadi maganar kanta tsaye kuma innocently.
Suhaanah matar wucin gadi ce ke.
Mene ne wucin gadi?
Ina nufin.......temporary.
Ok, na fahimta. Mu matan wucin-gadi ba a kiranmu matan aure?
This is beyond my knowledge Hafsa. Da na san kina da baki da Law na zabar miki.
An tabo hirar da ta ke so (karatu) tuni ta manta da waccan.Au, ba law ka zabar min ba? Mommah ta yi tsammanin hakan.
Girgiza kai ya yi, Ba law na cike miki ba, career din da ya fi dacewa da ke ne. Tashi ki je ki kwanta kin dame ni da surutu, kada gobe ki makara a kicin, kuma ki hana ni fita sai kin gama. Yau saura kadan ki sa a zane ni
Dariya ta saka ta mike tana fadin, Zan so ganinka Justice yana zane ka.
Murmushi ya yi, ya ce mata, Sai dai in tafi da ke a zane mu tare, tunda ke ki ke makarar da ni. Night!
Ya kada mata yatsu. Ya maida kai kan aikinsa lokaci zuwa lokaci yana tariyo hirarsu a ransa.
...Sex is a crime in Nigeria...all kind of sexual acts are prohibited in Islam and culture daga manya har yara, masu aure da marassa aure....... sai dariya ta kama shi ya yi murmushi, cikin ransa yana fadinIn mun rabu kin sake aure za a sha kallo a gidanku ke da future husband dinki.
A wannan dan tsukin sun zama abokan juna, ko ciwon kai ta ke sai ta gaya masa ya ba ta magani. In sharia ya yi, sai ya gaya mata yadda ta kaya. In zai shiga kotu sai ya kira ta ya gaya mata ta yi masa addua, he dont want to be a loser! In ya yi nasara sai ya gaya mata adduarta ta karbu. Ta shirya in ya dawo su je Dominicta ci Pizza ta sha ice-cream ladan adduarta. Fitarsu ta biyar kenan zuwa (Dominic) hakan ba karamin faranta ran Hafsa yake ba.
In ba ya nan tana tare da su Mammah a waya. Ko ta dauko Alqurani tayi ta tilawa da sauran littattafanta. Baba Azumi ma ta dawo daga Sokoto duk sanda Mammah ta kira ta, ko ita ta kira ta za ta hada su su sha hira. Haka kawai zai ce kada ta yi abincin dare in ya dawo za su fita su ci a Chinese restaurantko KFC. Don haka a wannan dan tsukin Hafsat ba ta da damuwa ko cikin cokali.
SUMAYYA ABDULQADIR TAKORI
07030137870
*Littafi na farko shine kawai free. 234 na sayarwa ne. Idan ka fidda 234 ba sai na hada ka da Allah ba zai isar min insha Allahu. Ku biya Ku karanta a nitse cikin farin ciki yafi maka kayan zunubi ranar gobe kiyama*
Ranar wata alhamis ya shigo mata da (past quastions and answers) na Jamb ya ce ta duba ranar asabar zai kai ta ta zana. An tura ta wata makarantar sakandire ta gwamnati a nan Abuja inda za ta zana jarrabawar.
Ta dukufa karatu ba ji ba gani duk da a wurinta da matsayinta na dalibar (ST. John Barchmans College) wannan ba wani karatu ne na a zo a gani ba.
Da yake asabar ce ba aiki, tun bakwai da rabi ta shirya ta fito tana tsumayinsa. Da ya fito ya