Showing 75001 words to 78000 words out of 168255 words

Chapter 26 - Auren Kwangila Book 4 Hausa Novel Complete

Takori   

12 Dec 2024

307

shi ne kokari na karshe da za ta yi a rayuwarta sai ta tabbatar ABDULAZEEZ ya auri MUAZATU...... sai ta tabbatar ya cika burinsa... sai ta yi hobbasar da mahaifiyarsa ba ta yi fushi da shi ba a kan hakan.
Daina mutsu-mutsun kwatar kannata ta yiganin cewa wahalar da kanta kawai take yi, bai yi mata sassaukan riko ba, bai rike tada sauki don ta kwace a sanda ta so ba, ta kwantar da kanta kawai a kirjinsa kukanta na raguwa a hankali har ta daina shi bakidaya. Hannunsa na dama ya sanya cikin yatsunta ya sarke su sosai na hagun na rungume da ita tsakiyar kirjinsa. A wannan lokacin ta tabbata da zaa tsaga jikinta ba za a samu digon jini ba ya hau ya yi sama saboda duniyar gajimaren da ta tsinci kanta. Balle kuma data tsinci tattausan bakinsa cikin nata. Dukkaninsu idanunsu sun rufe sun manta da kowanne irin nauin aure suke yi. Abin da suka sani kawai shi ne, su maaurata ne, kuma suna tsananin bukatar junansu. Alamarin ya fi karfi daga Abdulazeez a matsayinsa na namiji wanda ya kawo wadannan shekarun bai taba kusantar mace da irin wannan kusancin ba. Idanunsa sun rufe, hankalinsa ya gushe, ya soma sumbatarta da sumba mai tsayi da zurfi a duk inda bakinsa ya kai daga kan fuskarta da masangalin wuyanta, cikin wata siga mai nuna tsananin bukatar miji zuwa ga matarsa.......
Abubuwa da yawa ke yawo a kan Hafsat suna ankarar da ita rayuwar da Abdulazeez zai jefa ta idan ya samu wannan nasarar a kanta, kuma ya sallame ta kamar yadda ya kudurta; bazawara... second hand... ko mai ciki da goyo babu aure, babu martabar zama a dakin aure...... ! Sai gantali a jamia, amma ba ta da martabar da za a kira ta matar aure, ko matar Barrister Abdulazeez Hamzah Attikou!Wannan sai MUAZATU. Ita sunanta sauta ga wawa..... bazawara under twenty years!!! Don haka a take ta soma protest. Zuciyarta ba ta afu ga Abdulazeez a yau don wannan rayuwar ba ne kawai, sai don ci gaba da rayuwa tare da shi har karshen rayuwarta.
Protest ta ke sosai da dukkan karfinta da iyawarta, wanda hakan ya tayar da hankalin Abdulazeez fiye da zatonsa. Lallashi ya koma, duk da ba cikin hayyacinsa yake lallashin ba ya san kalaman sun yi tsauri a ce Suhaana yake gayawa su. Wannan jaririyar kanwar tasa da aka haifa akan idonsa ta girma a gaban mahaifiyarsa. Kalaman da yake gaya mata ta ki yarda ko kadan su yi tasiri a tare da ita, don ta amince na yaudara ne da neman cimma buri, ba ta hango komai a wannan lokacin sai zawarci babu budurci. Wani mai matar za ta aura ba ta da damar gina family nata na kanta irin na gidansu sai na gidan wasu. Ko kishiyar Muazatu ba ta isa ta zama ba sai kanwar mijinta.
Wani kuka ne ya taho tun daga kololuwar zuciyarta ta rusa masa shi tunda karfinta ya yi kadan ya raba ta da Abdulazeez a daren yau. Sosai ya tsorata da kukan mai kama da na an yanki naman jikinta, ya koma gefe ya dafe kansa a gefen gado da dukkan hannuwansa. Wannan damar ta samu ta ja duvet ta lullube jikinta tana ci gaba da gabza kuka kamar wadda aka aiko wa sakon mutuwa. Haushi da bakin ciki ne ya sanya shi maida Pajamas dinshi ya bar mata dakinta.
Da sauri ta sauko ta murza wa dakin key ta bar mukullin a jiki. Ba ta sani ba ko ta bar dakin a bude a yadda ya zuciyan nan ba dawowa zai yi ba. Shi kadai ya san cikin halin da ya kwana.
Amma ga Hafsat abin ba haka ya ke ba. Bayan ta goge ido daga kukan kwantar kan data rakito barci ta yi har da munshari da saleba, cikin mafarkinta kalaman Abdulazeez ne wadanda ya fada mata a lokacin da ya tashi daga Barrister Abdulazeez zuwa MIJIN HAFSAT! Sunan da ba za ta fada a fili kowa ya ji shi ba saboda har gobe tana tantama a kansa. Su ke nanata kansu cikin barcinta suna kara armasa mata shi.
Sosai ta makara sallar asuba don a rayuwarta ba ta taba ganin dare mai tsayin na yau ba. Wanda ta sanya shi cikin darare masu dumbin tarihi a gare ta. Wani dare daga cikin dararen da ba za ta taba mantawa da su ba. Ko da ta yi sallah ta shiga kitchen don sama musu abin da za su ci duk da ta makara, alamu ta gani na an yi girkin taliyar indomie da dafaffen kwai. Duk da lahadi ce yau ya ki zama a gidan, ba ta san inda ya tafi ba.
Yadda ta yi girkin rana haka na dare ya tadda shi a dining Abdulazeez bai taba ba, kuma ta tabbatar ya dawo gidan, don ta ji motsinsa sake fita ya yi ba tare da ya neme ta ba. Murmushi ta yi ta kwashe ta ajiye a kofar shigowa babban falonsu inda ta ke ajiyewa Danfulani abinci ya zo ya dauka da kansa.
Fushi Yaya Azeez ya ke yi da ni? Ta fada a hankali. Ya fi mini. Ta fada a fili. Wannan alamari ya fi karfina, sai Yayata abar sonka Muazatu, tunda na gane shi ne muhimmi a cikin auren ba kamar yadda na zata ba. (Its not a crime) idan akwai aure, kuma sai an kai zuciya nesa zaa iya bijirewa. Balle daga Abdulazeez din da ta yarda zuciyarta daban ta ke daukar kowanne alamarinsa.
Lumshe idonta ta yi tana tuno yadda ya ke kissing idanun kansu ba su tsira ba. Labban bakinta ta cije don ji ta yi kamar yana bayanta yana sake kissing din su.
Ya Ilahi. Suhaana ta fada a fili, tare da kwashe kwanukan daren ma ta koma kicin da su ta adana abincin a firji, ta rufo kitchen din da sauri jin horn din motarsa ya dawo gidan misalin karfe tara na dare. Gidan Barrister Sagir ya tafi, a can ya ci abincin dare, Hafsat ta jika nata ta cinye.












SUMAYYA ABDULQADIR TAKORI
07030137870

*Littafi na farko shine kawai free. 234 na sayarwa ne. Idan ka fidda 234 ba sai na hada ka da Allah ba zai isar min insha Allahu. Ku biya Ku karanta a nitse cikin farin ciki yafi maka kayan zunubi ranar gobe kiyama*

Daki ta shige da gudu ta rufe kofarta. Ba ta kara fitowa ba sai washegari bayan ta idar da sallar asubah ta fito kitchen don hada masa abincin kari da zai fita shi, tunda ranar (office) ce.
Da wuri ya shirya don ya ba ta haushi, duk saurin da ta yi ta gama tana fitowa daga kitchen din ta ga ficewarsa daga falon. Da sauri ta koma kitchen ta dauko basket din, amma tana fitowa yana yin reverse zai fice daga gidan ga Danfulani ya wangale masa get. Yana hango fitowarta ta madubin motar har tana tuntube don sauri, ya fizgi motar da gudu ya fice daga gidan. Allah ne ya so ta kananan duwatsu ne shimfide da harabar gidan bakidaya, la-shakka da ta sha kura.
Kasa daurewa ta yi sai da ta yi hawaye, sabon salon da zamansu ya dauka ke nan. A ganinta laifin da ta yi bai yi kamarin da zai yi wannan fushin ba. A kan gaskiyarta ta ke. Yaushe ta tashi daga matar wucin-gadi zuwa parmanent wife? A cikin ajandarsu babu auratayya. Ba kowa ya fahimtar da ita wannan shi ne aure ba, shekarunta da kwakwalwarta ne. Abin da ta ke ji a kan Abdulazeez ma zuciyarta na son fahimtar da ita maanarsa da gangan ta ke kin karba. Idan wannan alamari da Abdulazeez ya bijiro a gare ta shi ne aure, hakika auren abu ne mai matukar nauyi kwarai, kuma zai iya ruguza duk wasu tubala da suka gina auren nasu a kai, tunda ba zaa fara don a daina ba. Ga shi ta sha alwashin taimakawa Abdulazeez ya samu abin da yake so ya cika burin rayuwarsa.

*****
Kwanaki sun shura ana wani irin zama mara dadi tsakanin Abdulazeez Dakata da matarsa Hafsat-Suhaana. Shi yake fushi da ita ba ita ke fushi da shi ba, fushin da in zaa daura masa wuka a makoshi a tambaye shi dalilinsa ba zai iya fada ba. Hafsat ta fi shi gaskiya in gaskiyar yake so. He attempted to cross the limit, ita kuma ta ankarar da shi. Me ye laifinta fisabilillahi? Ya daina cin abinci da ita, ya daina hira da ita. Ya daina zaman gidan.
Shakuwarsu da Sagir da iyalinsa ta karu a dalilin yawan zuwa gidan da yake yi yanzu don debe kewa, ko gidan iyayensa. A ganinsa janyewa Hafsat shi zai ceto shi daga katoton ramin da zuciyarsa ke son jefa shi, ramin da in ya kuskura ya fada sai ya yi tsalle dubu bai iya fitowa daga cikinsa ba.
Dole ya lallashi Muazatunsa suka shirya domin ya yarda har da nisa da ita cikin dalilan shakuwarsa da Hafsat, shakuwar da ba za ta haifar da Da mai ido ba, sai tarin nadama.
Sau-tari ya kan samu kansa cikin zurfi a tunani, Hafsat matarsa ce da addini ya halasta mishi iyaye da duniya bakidaya suka shaida. Yana da damar kusantarta no matter what, rashin samun damar hakan na iya jefa shi cikin wani hali a yanzu da yake tsananin bukatar mace a tare da shi. Ya ture komai ya karbi hakkinsa, shi ya ga abin da ya gani, ba yarinya ce kankanuwa ba irin daukar da yake yi mata. Ko protest din da ta yi masa ya nuna Hafsat na da wayonta, ta san abin da ta ke hangowa a cikin aurensu duk da tana da feeling a kansa wanda in ya yi rantsuwa ba zai yi kaffara a kan hakan ba. Tana da wani feeling na daban a kansa a yanzu bayan aurensu da zamansu tare na tsayin watanni, zuciyarsa ce ke karyatawa da gangan. Da hujjar cewa; yarinya ce, shekarunta ba su kai ta bambance da abin da zuciyarta ke so ba, sai wanda aka karkatata a kai.

(Anya kuwa Abdulazeez?).

Shi da kansa ya soma saukowa daga dokin fushin nasa ba tare da kowa ya lallashe shi ba. Ganin halin da fushin nasa ya jefa Hafsat. Ta shiga cikin matsananciyar damuwa da rashin walwala, in bai yi kuskure ba zai ce har ramewa ta yi jiya da ya saci kallonta tana gyaran falon, a lokacin yana zaune tsakiyar 3-seater ya mike kafafunsa da system a kan cinyarsa yana duba wani aiki. Amma duk da haka ya sa a ransa zai rage kusancinsu don tserar da kwangilarsa. Daga jibi Alhamis zai soma azumin tadauwai don samun lafiyarsa.
Washegari suka wayi gari da baki na ba-zata. Mammah da Baba Azumi, Ismael ya tuko su ya kawo su. Shi bai fito ba ma. Fitowarsa daga wanka kenan Danfulani ya kira shi ya sanar da shi, wai suna da baki ga su zaune a cikin mota sun ce daga Asokoro ne. Bai tsaya goge ruwan jikinsa ba ya sanya kaya, bakin wandon Jeans da shudiyar T.Shirt yar gidan Nordstrom. A gurguje ya fito don ya san babu wasu da ya sani a Asokoro sai iyayensa.
Ilai-kuwa, Mammah da mai aikinta Azumi da kaninsa Ismael ke fitowa daga mota.
Mammah!
Ya fada cikin bayanannen farin ciki.
Karasawa ya yi da sauri, shi ba abin ya rungume ta ba ta ce ya yi girma, shi kuma a yau ban da rungumar bai san me zai yi mata don nuna mata jin dadinsa ba da tako kafarta muhallinsu.
Hannayenta biyu ya kama, You arehighly welcome to our home Mammah.
Murmushi ta yi ta kwace hannunta tayi gaba, ya russuna ya gaida Azumi, ya ba wa Ismael hannu, ya karbi handbag din Mammah ya shige cikin gidan da sauri yana kwala wa Hafsat kira, Hafsa! Hafsa!!
Mammah ta ce, Wannan kira haka ai sai ka ba ta tsoro. In ka kyale ta har dakin zan isko ta.
Kwance ta ke lamo a cikin quilt kasancewarta mai yawan son dumi ko da gari babu zafi, kanta a kan filo ta cure gashin kanta a gefe, kwance ta ke kawai ko wanka ta kasa tashi ta yi saboda nauyin zuciya. Ba tunanin kowa ta ke ba sai na Abdulazeez din da ya hana zuciyarta zama lafiya a duk kwanakin nan, da tunanin hanyar da za ta bi ya daina fushi da ita. Kamar daga sama ta ji yana kwala mata kira da wata murya kamar ba tasa ba. Kasa amsawa ta yi, amma ta mike zaune cikin faduwar gaba. Sai ga shi ya shigo dakin, da sauri ya iso gare ta, har gadon ya isko ta ya zauna a bakin gadon. Hannunsa daya ya nutsa cikin sumar kansa ya iko hannunta da dayan ya dube ta cikin ido.
Mammah ce. Don Allah Hafsat ki rufa min asiri, mu koma shirinmu na dade da hucewa wallahi.
Yadda ya marairaice yana mata maganar ya yi balain ba ta dariya. Sosai ta dake ta dauke idonta daga kansa jin wani abu na fizgar zuciyarta daga cikin kwayan idanunsa. Ta rasa dalilin da ba ta iya jure kallon idanun Abdulazeez masu dauke da wani maganadisu da ba ta taba ganinshi a idon kowa ba. Hannayenta biyu ya kamo ya matse su sosai cikin nasa.
Kina jina Hafsa? Don Allah ki manta komai, babu lokacin magana save it, za mu yi ta in sun tafi. Duk wani punishment ki tanadar min zan dauka, amma ki saki ranki don Allah.
Daga kanta ta yi alamar ta ji, kuma ta amince. Sai jin sallamar Mammah sukai a bakin kofa, da sauri Hafsat ta janye hannayenta daga cikin nasa.
Mammah ta yi kamar ba ta gani ba.
Ba dai sai yanzu ki ka tashi daga barci ba?
Saukowa ta yi daga gadon da gudu ta yi kan Mammah ta rungume ta kankam. Abdulazeez ya ce, Ba ta jin dadi ne. Tun jiya ta ke fama da zazzabi, amma na ji yanzu ya sauka.
Ni ki cika ni kada ki kada ni.
Da kyar Mammah ta samu Hafsat ta cika ta suka zauna tare. Dakin ta ke bi da kallo, komai tsaf a gyare ban da gadon.
Ta ce, Zazzabi? Ba sai a je asibiti ba? Ana raina zazzabi ne?
Ta kafe Abdulazeez da ido. Sunkuyar da kai ya yi don gudun haduwar kwayar idanunsu. Ya san halinta sarai, kallo daya za ta yi masa ta karanto karya, ko gaskiya a kalamansa. Ba shi kadai ba har sauran yayanta.
Hafsat tuni ta yi kitchen ta soma tattaro abin saukar baki, kusan duk abin motsa baki da lemukan da suke da su a firji ta kwaso, Ismael na tsokanarta, Baba Azumi na tare mata.
Su matar gida manya, sai dai kuma babu wanka babu kwalliya.
Baba Azumi ta ce, Eh din, ta dai fi budurwarka mai kama da shamuwa da wasu kafafunta a bubbude kamar tayar mota, ko ba ta yi wanka da kwalliyar ba.
Dariya ya yi, ya ce, Wallahi Wasila ta fi Adda kyau, ga gayu, ga class, amma wannan tsami gayen sai Yaya ya hada da hakuri don bana jin ko girki ta iya.
Kumburi sosai ta yi tana hararar Ismael, Mammah da Abdulazeez suka fito.
Mommah, kin ga Illaila ko? Wai ni ce tsami-gaye?
Mammah ta ce, Ba dole ya ce miki tsami-gaye ba? Karfe goma na safe amma ba ki wanka ba, ba ki dafa wa mijinki abin kari ba, ba ki gyara gadonki ba balle ki yi masa kwalliya.
Kamar za ta fashe da kuka ta ce, Wallahi Mammah ina yi yau ne kawai.
Abdulazeez ya harari Ismael kasa-kasa. Mammah na fa gaya miki ba ta jin dadi.
Kana kare ta ne kawai amma ba zan yi miki uzuri ba Addah, shi ya sa ban gaya muku zan zo ba, zuwana na farko ga yadda na tadda ke.
Hafsat ta soma kuka kamar ta ce da Mammah in ta dafa abincin ba ya ci, ya daina kula ta dalilin hautsinewarta kenan, ta tuna rokon da ya yi mata yanzun nan na ta rufa masa asiri. Amma Abdulazeez ya cuce ta. Duk yadda ta ke hana idonta barci ta hada masa (verities) na abinci mai rai da motsi kullum sai dai ta zubar, ko ta bai wa maigadi, yadda ta ke kalkale gidan nan da kwalliyar da ta ke dandasawa ko kallo ba ta ishe shi ba yau daya sun tashi a banza! Ganin tana kuka zuciyar Hajiya Maryam ta tabu.
Abdulazeez cikin damuwa ya ce, Ishma, me ya sa ba ka iya wasa ba ne? Ni na ce da kai ba ta girki?
Ismael fa ba ya gajiya da tsokana, sai dai in bai ga abin fada ba, ya ce,
To Yaya a zubo mana man tunda an dafa?
Mammah ta janyo Hafsat jikinta.
Rabu da Ismael Addah, ni na dafo mana abincin saboda bana so ki sha wahala.
Ta dubi Baba Azumi, Karbi mukullin boot a shigo da coolers din nan gabadaya.
Ismaeel ya yi mata gwalo ya mike suka fita shi da Baba Azumi. Ta sake bara baki tana kuka, wai ya yi mata gwalo. Abdulazeez abin ya ba shi dariya, ya ce, Me ya sa ki ka zo da shi ne Mammah? Da Usman ki ka dauko.
Ka san Usman da gudu a titi, ni kuma bana son gudu shi ya sa na dauko shi. Na manta takura miki zai yi Addah.
Allah ba zan je gidansa ba, kuma ba zan je bikinsa ba. In ji Hafsat. Karaf! A kunnensa yana shigowa dauke da food-warmers din Mammah masu kyau,ya ajiyesu tsakiyar falon ya ce,
Ai gara kada ki zo din, balle ki koya wa Wasilata kazanta, rashin girki da rashin gyara.
Abdulazeez ya dau filon kujera ya jefa shi da shi. Filon ya cafe da hannayensa yana fadin, In ba za ki koyi gayu ba na rantse sai na yi wa Yaya budurwa yar gayu ko cikin kannenWasila.
Sosai Abdulazeez ya fusata, ya ce, Fita daga gidan nan Ismael, tunda babu gadonka a cikinsa.
Hannayensa biyu ya hada irin na rokon afuwa yana kallon Hafsat, Im so sorry uwargidan Ya Azeez. Amma kafata kafar uwata.
Mammah ta girgiza kai, Ni ma ba za mu jera ba, tunda kana fatan a yi wa Addata kishiya.
Na tuba na bi Allah na bi ku dukkanku. Baba Azumi ki gaya musu wasa nake, amma ai ita Adda ta sani ko a cikin kanne ita ta musamman din Illaila ce.
Zumburo masa baki Hafsat ta yi, Aah,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login