Showing 114001 words to 117000 words out of 168255 words

Chapter 39 - Auren Kwangila Book 4 Hausa Novel Complete

Takori   

12 Dec 2024

333

help.
Hakan ne ya sanya wata irin nutsuwa da aminci cikin zuciyarsa. Ya samu kansa da warware wa Abdulkarim Dakata komai tun haduwarsa da Muazatu, fitinannen son da ya samu zuciyarsa da yi mata rana daya bayan da in the first place mutuncin Babanta ya sa yake kula ta. Amma shi a a ransa ya san da farko ba son ta yake ba. Yanada buri mai yawa akan karatu da ya shafe masa tunanin soyayya ko yin aure a lokacin.Kuma ya sanar da Muazatu hakan amma rana daya ya samu kansa in ba aurenta yayi ba bazai taba nutsuwa ba. Kawo zancen Hafsat da Mammah ta yi masa rana daya, tunanin hanyoyin gujewa auren da ya yi ta yi ya rasa, don tsira da Muazatu. A karshe ya ga babu mafita (don Mammah ba da wasa ta dauki alamarin ba) ban da ya nemi Hafsat su yi auren a kan yarjejeniya na zaman auren shekara daya da watanni daidai da lokacin da Muazatu zata gama law-school. Ya gaya masa tubalan da aka gina yarjejeniyar akai daidai da burin kowannensu. Ya dan yi shiru, kansa na kasa (feeling guilty). Tsohonminista Abdulkarim ya saki baki, hanci da ido yana jin wauta da kuruciya zallarta hadi da shiga hurumin Ubangiji duk saboda soyayyah. Ya ce a ransato ita Muazatun da diamond aka kerata da dole sai an aure ta ko ta halin kaka? Abdulazeez ya kara sunkuyar da kansa cikin jin nauyin abin da zai fada.









SUMAYYA ABDULQADIR TAKORI
07030137870

*Littafi na farko shine kawai free. 234 na sayarwa ne. Idan ka fidda 234 ba sai na hada ka da Allah ba zai isar min insha Allahu. Ku biya Ku karanta a nitse cikin farin ciki yafi maka kayan zunubi ranar gobe kiyama*

Abdulazeez ya ja wani gwauron numfashi, sannan ya sauke shi a wahalce. Ya ba su tausayi sosai. Amma ba wanda ya nuna duk don su kara tsoratar da shi bisa kuskurensa. Baffah ya ce, Daddy ya kira Maryama ta hada shi da Hafsat. An yi saa suna tare ta dauko ta daga makaranta kan hanyarsu ta komawa gida. Hafsat na russuna murya tana gaishe da Baffa ya ki amsawa, ya bude mata nata rabon a kan don me bata gaya wa uwarta ba lokacin da Abdulazeez ya ce su yi yarjejeniya? Fada yake mata ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba. Fadan da bata taba zaton ya iya ba. Kullum shi mai tausasawa ne a gareta. Ya gaya mata hukuncin abin da suka aikata. Hafsat da gari banza ma kuka ta ke yi balle yau? Baffa fa! Mahaifin Daddy gabadaya. Bai bata damar cewa komai ba ya mikawa Abdulazeez wayar, Sake maimaita mata a gabana ka mayar da ita dakinta. Abdulazeez da ya hau maimaitawa sai da ya fada mata ya kai sau goma. Abdulkarim ne ya kwace wayar ya zuba masa rankwashi a tsakar ka. Ya bawa Daddy wayarsa. Adda Hafsatu ta ce, yau abin da yake so ta girka, amma wallahi ba za ta zuba masa ba. Hakuri ya dinga ba ta, amma ta kafe ba zai ci ba. Ta ce,
Ai ko don albarkacin sunana da yarinyar nan ta ci ta fi karfin kalmar saki daga bakinka. Tukunna ma wace ce Muazatun? Ku hada ku aura masa mana ya san bambancin mai suna HAFSAH da sauran sunaye?
Uncle Abdulkarim ya kwance musu labarin zuwansa neman auren Muazatu da yadda aka sallamo shi, ya ce har gobe ita yarinyar tana sonsa, mahaifinta ne ya ki, bai san dalilinsa ba, kuma ya yi gaggawar yi mata aure. Shi bai taba ganin mahaukacin so irin wannan ba, wanda Abdulazeez ke wa Muazatu, son da zai ja ka ka saba wa Ubangiji don ka faranta wa budurwa, ka gwammace bacin ran iyayenka a kan farin cikinta? Allah ya yi mana katanga da yayanmu da irin wannan son, yau da Abdulazeez ya auri yarinyar nan watakila ko gaida iyayensa sai ta ba shi izni.
Baffa ya yi tsai! Da ransa, yana sauraron labarin da Abdulkarim ke baiwa Addah. Bai ce komai ba, amma ya gane wannan yarinyar ita ce mai farautar jikan nasa. Ya kudure a ransa nemawa Abdulazeez kariya fiye da dukkan jikokinsa don shi ko yanayin aikinsa ma hatsari gare shi. Ba su baro Kano ba sai da ya sa Abdulazeez ya yi wanka da ganyen magarya har sau uku, ya ba shi rubutu kala-kala, ya ba shi adduoi da nafilolin da zai rika yi duk daren jumaa da litinin. Ya ce kuma idan ya ki yi Allah Ya isansa. Dariya ya yi, sannan ya alkawarta masa zai yi. Ya ba shi na sauran yan uwansa ya tafi musu da shi.
Tunda suka dawo gida Abuja, Mammah ta kara tsananta matakanta na tsaro a kan Hafsat da Abdulazeez, da kara toshe duk wani communication gap a tsakaninsu. Ba abin da ya dame ta da wani aurensu da aka mayar kamar ma ba ta san an yi ba, bai wani wani damu ba ya ci gaba da ayyukan gabansa cikin kwanciyar hankali. A ganinsa ba shi da damuwa yanzu a rayuwa tunda kuwa koma nisan jifa kasa zai fado,sannan hausawa suka ce wai karshen alewa kasa!.

******
Yau watan Hafsat guda da komawa makaranta, karatun session din ya kankama sosai. A watan gabadaya wani abu bai kara hada ta da Abdulazeez ba ko da gaisuwa, Mammah ta bi kowacce hanya ta sadarwa tsakaninsu ta toshe. Haka suka zauna tsayin wata biyu a gidan ba ruwan kowa da zaman dan uwansa. Idan ya taso aiki gidan yake zartowa, amma sai dai ya tsaya iya falon farko da wajen Daddy don Mammah ta hana ta fitowa ma in dai yana gidan, har sai ya gama cin abinci da hirar da suke yi tsakaninsa da Daddy da su Ismael ya bar gidan, ko giftawar Hafsat ba ya gani. Sai dai ta shige toilet ta yi kukanta mai isarta, kukan tausayin Abdulazeez dinta! Sau biyar ta ji shi a dakin Mammah ya je bata hakuri, amma ba ta tankawa. Azumi ba ta gari ta je ganin gida can Sokoto, ya tabbata da ta taimaka masa wajen tausar Mammah. Ko gaisawa za ta yi da Dr. Bashar da su Dada sai ta wayar Mammah, kuma a gabanta. Ta gama ta karbe. Time-table ta ke bi wajen kai ta makaranta, ita kanta ta gaji da wannan zirga-zirgar da ta sanya kanta babu gaira babu dalili don abu ne da bata saba ba (tukin mota), amma tsabar kada Abdulazeez ya samu damar kebewa da Hafsat ya sa ta hana Salisu kai ta da daukotan.
Ranar yau ta kasance asabar, sai suka wayi gari da bako a gidansu; Abdulazeez ne da jakunkunansa, ya bude dakinsa na samartaka na gidan ya ce Salisu ya shigar masa da jakunkunan ya shirya masa kayan a wardrove ya share masa dakin ya goge koina ya wanke masa bayi. Ismael ya shige nasa dakin wanda ke daura dana Abdulazeez din banda dariya ba abinda yake yi. Usman ya zo ya tadda shi yace.
Kana zaton Mammah za ta barshi ya zauna ne?
Ya sassauta dariyar ya ce. To ya zata yi dashi? Za ta kore shi ne shi da gidansu? Ai ni ya kyauta min, Mammah ba ta jin lallashi, an mayar da aure kuma meye na cigaba da rike masa mata?Attimes she behaves like AddaHafsatu; tough and disciplined.
Tun tashinta daga barci ta ke jin scent din Abdulazeez a gidanta. Bata kawo komai ba tunda ta san yana zuwa gidan amma ba irin wannan lokacin ba sai yamma can in ya tashi ofis. Da ta yi wanka ta shiga kitchen don ta ga me za ta dafa, shi ta gani ya jona kettle yana dafa black tea dinsa wanda shi ne abin shan sa duk wayewar garin Allah, daga shi sai threequater da farar singilet. Daga bakin kofa ta tsaya tana kallon ikon Allah. Juyowa ya yi jin alamun mutum, addua yake Allah ya sa Hafsat ce ta fito ya samu ya ganta ko daga nesa ne kafin fitowar Mammah, amma sai ya ga Mamman da kanta ba sako ba. Russunnawa ya yi ya soma gaishe ta, bata amsa ba ta wuce ciki ta kunna gass ta dora ruwa. Sai ya tuna mata da shekarun yarintarsa, haka yake ba ya son a dafa masa shayi, ya fi so ya yi shi da kansa. Hafsat ta shigo tana mutstsike idonta da alama tashinta kenan daga barci, riga da wando ne na barci farare sol a jikinta marasa kauri sosai amma ba su kama jikinta ba, kanta ba kallabi ta kame tulin gashin kanta a tsakiyar kan da black hair bound. Kwata-kwata ba ta lura da shi ba ta shigo kitchen din. Kai tsaye gefen Gass-cooker ta nufa inda Mammah ke tsaye tana cika tana batsewa, ba ta lura da yanayinta ba saboda idonta ma bai gama washewa ba.
Mammah ba ni aron waya zan kira Yaya Imamu, mafarkinsa na yi yanzun nan.
Ba tare da ta dube ta ba, ta ce.
Tana kan bed-side.
Juyawar nan da za ta yi da zummar fita sai ta yi arba da Dan Ambassador Hamzah Atiku, tsaye yake jikin kitchen-cabinet ya harde hannayensa a kirji. Lumsassun idanun dake dimauta ta ke kallonta admiringly daga can kasan idanun. Zuciyarta ta ji ta harba da karfi.Yaushe rabon duniya da ayyaraye! Yaya Azeez ashe tana da rabon sake ganinsa nan kusa??? Watanni biyu masu kama da two decades. Hajiya Maryam haushi ya ishe ta ganin sun manta da ita a wurin ta tsaya ta ki ficewa, sai kallon juna suke yi da wani irin yanayi cikin kwayan idanunsu.The excessive emotions for seeing each other continue to linger in their eyes(shaukin su na ganin juna ya cigaba datsayuwa na lokaci mai tsaho cikin idanunsu). Wani uban dundu ta zuba mata sauran kadan ta fada kansa. Da sauri ya taro ta, ita kuma sai ta yi maza ta zame saboda kunyar da ta kamata. Mammah ta dube shi ta ce fitar min daga kitchen, in ji dai nan din ba gidanka ba ne? Me ma ya kawo ka da sassafen nan?
Sunkuyar da kai ya yi yana shafa kansa. Mammah ai na dawo nan, the house is very wide for me (gidan yayimin fadi da yawa).
Hafsat ta dafe bakin ta da hannayenta biyu ganin yadda Mammah ta fusata, cikin damuwa kuma a marairaice ta ce.
Mammah we didnt talk, ni ban san ma yana kitchen din ba da ban shigo ba. Ki yi hakuri.
Shi kuma ya ce. Ni ruwan zafi nake dafawa. Allah Mammah I didnt give her a second look, ki yi hakuri.
Ya juye tea dinsa a mug (kofin tangaran mai zurfi) ya zuba zuma kadan a ciki ya fita. Hafsat ta ja gefe tana jin wani irin radadi a zuciyarta. Mutum da gatanshi ya koma kamar wani maraya a gidan ubansa! Shayin ma ba zaa bashi ba sai ya dafa da kansa. Da kuka wiwi ta bar kitchen din. Hajiya Maryam ta bi ta da kallo bakinta a bude, sai kuma ta girgiza kai ta yi murmushi ta juya ta ci gaba da abin da ta ke yi.
Ta yi rub-da-ciki tsakiyar gadonta tana kuka ta ji an murda kofar dakinta da alamar shigowar mutum, a zatonta Mammah ce ta biyo bayanta don ta lallashe ta tasan bata iya jure ganin ta cikin bacin rai, don haka ko dagowa ta ki yi. A kan bed-side drawer na gadonta ya zauna kafarsa ta dama na bisa gadon daya na kasa.
Tashi ki sha tea.
Muryar Abdulazeez ta ji kamar a cikin mafarki. A firgice ta dago da hawayenta shabe-shabe suka hada ido. Hankalinsa kwance yake, da alama yanzu kam ba shi da damuwa. Waiwayawa ta yi bakin kofa a kidime kuma ta juyo ta dube shi a rikice. Na shiga uku! Ta furta a fili muryarta na rawa har ta so ta bashi dariya, mug cupdin hannunsa ya mika mata har ya sha rabin shayin. Karbi, ko sai na baki a baki?
Harara ta maka masa tamkar idanun zasu fadokasa.
Da kai ka ke ba ni shayi?
Girarsa ya daga mata. Just taste it, mine is special....just beyond comment(ki dandana ki ji, nawa na musamman ne, fiye da yadda zaki iya sharhi.
Mikewa ta yi tsakiyar gadon ta dirgo da sauri, gara ta fice daga dakin nan in ba haka bata lura bashi da matsala in Mammah ta sanya ta a turmi ta kirba tunda shi yana da Muazatu. Ita kuwa ba ta da mai damuwa da ita ta wannan fannin wanda zai tsaya ya lallasheta in ta sha dukan. Kafin ta kai kofar Abdulazeez ya riga ta, ya kuma murza key din da ke jiki. Hannu ta dora a ka za ta zuba ihuya toshe mata baki da hannun daman sa ya janyo ta tana tirjewa har gefen gadonta. A jikinsa ya zaunar da ita, ya dauko shayin ya kai bakinta. Turewa ta yida karfi tana kokarin mikewa har da zabura,da haka duk suka zubar da ragowar shayin a jikkunansu. Ga shayin da sauran zafin sa sosai amma ba ta wannan take ba. Ta yi wuf ta mike jin Mammah na buga mata kofa, iyakar rikicewa Hafsat ta rikice, iyakar rudewa ta gama rudewa, tashin hankali baro-baro ya bayyana a fuskarta. Ta soma kyarma daga tsaye tana masa kallon ka cuce ni. Murmushin mugunta ya yi mata ya karasa a nitse ya bude kofar.
Hajiya Maryam ta bi shi da kallo, sannan ta shigo ciki sosai ta dubi Hafsat wadda ke tsaye fararen kayanta jike tsamo-tsamo da bakin shayi. Ido ta dan kafa mata, Hafsat ta rasa me za ta ce mata, kafin ta tattaro kalaman kare kanta Mammah ta juya ta bar musu dakin. Kuka ta saka ta yi kanshi da duka, tana isowa bata ankara da ya bude hannuwa bata fada ciki dawata itin azama ya rungume ta. Ya wani irin lumshe ido kamar bazai bude ba. Kokawar kwace kanta ta koma maimakon dukan huce haushin data yi niyya, cikin hakanya samu saar cafko bakinta ya soma kissin cikin wata irin siga mai nuna tsananinkewarsa da kishirwarsa da hakan, alamarin da ya tafiyar da ragowar kuzarin ta gabadaya jikinta ya saki bakidaya. Sai da ya tabbatar ba ta da sauran karfin fada da shi sannan ya saketa ya ja da baya ya zauna a dandaryar kasa ya rufe idanunsa yana maida numfashi, kallo daya zaka yi masa ka tabbatar ya shiga damuwar da bai taba shiga a rayuwarsa ba,cikindusashshiyar muryayace.
Hafsah ya ki ke so in yi mata? Ba ta jin lallashi ko kadan, ba ta jin ban hakuri, zuciyarta kamar ta dutse.I can handle her(zan iya da ita) ki daina damun kanki. Mammah ta sanni ni ma na santa, daga ni har itaba mai iya canza wani, don haka ki koma gefe kawai kiyi kallo.
Ta koma gefen gadonta ta zauna ta dafe gefen kanta dake balain sara mata. Kawai sai ta sa kuka ta kifa kai cikin cinyoyinta. Gefenta ya dawo ya zauna ta yi saurin matsawa.
Wallahi ita nake so sau dubu ba kai ba, kuma wallahi na fi ka saninta, har yaushe ka zauna da ita? Kullum gudunta ka ke, sai yanzu rana tsaka bayan ka gama wulakanta ni ka zo ka ce za ka shiga tsakaninmu? Ka tafi ka auri Muazatunka tunda tace bazata hakura ba ka kyale ni da Mammah nah.
Babu damuwa ko kadan a tattare da shi ya ce. Duk na ji, kuma na yarda kin fi ni saninta.Amma maganar na wulakanta ki ni ban santa ba.Idan kuma akwai wata rana da hakan ta faru a zamanmu ki gaya min ita, na yi kuskure na yi saki, kuma na ce na mayar a gaban kowa in ga wanda ya isa ya ce bai maidu ba. Sannan ta wani bangaren I might not call it a mistake; da yardarki aka yi shi (sakin) saboda ba ki san daraja ta ba, kin fi son boko a kaina.
Na ba ki bokonki nace ki tsufa kina yi karewa, yanzu kuma ki fi kowa daukar zafi wai an sake ki? To an sake kin, kuma an ce an mayar da ke sau sabain in kin isa ki ce babu auren kwata-kwata damuwar ki ce. Na ba ki minti talatin ki yi wanka ki yi min kwalliya, you are looking shabby, ki sama min abin da zan citunda kin zubar min da tea kuma Mammanki ba bani za ta yi ba tunda Azumi ba ta nan.
Ya mike ya yi ficewarsa ya barta nan a zaune kamar an kafe ta. Ashe gaskiya ne da ta ke ji ana fadinwai maza ba su da kunya? Sai dai wasu daga cikin kalamansa sun tsaya mata a rai, ta nutsu tana analysing(duba su filla-filla) tana dora su a sikeli na hankali da adalci.... Ba ta san darajarsa ba! She is afterstudies morethan the marriage itself. Da yardarta aka yi saki, aka yi contract, aka shirya komai aka tsara shi daidai da burin kowannensu. Kamata ya yi yanzun da ya yi nadama ya yi damarar gyara kuskurensa ta ba shi goyon baya su hadu su gyara kuskurensu tare, su nemi afuwar iyayensu game da yaudarar da suka yi musu a sirrance hadi da yafiyar Allah na saba masa da suka yi da gangan. Adashin karkacewa daga umarnin Ubangiji da suka yi ne saboda son zuciyoyinsu suke kwasa gabadayansu a yanzu. Ko wannan soyayyar dake cin zukatansu azaba ce mai zaman kanta. Sannan takunkumin Mammah ma kadai punishment ne mai cin zuciya. To amma anya zabar farin cikinsu ita da shi a kan biyayyar Mammah abu ne da ya kamata daga gare ta?Butulcewa umarnin ta wani abu ne da ya kamata ta aikata cikin hankalin ta? Ta tabbata ta kuma amince duk abin da Mammah ke yi tana yi ne don ta daidaita rayuwarta, tana yi ne for her own well-being da kwato mata darajarta. Tana yi ne don ta samu eternalfarin cikin aure da rayuwa mai inganci har karshen rayuwar ta.
Hakika takasance mai matukar rauni kwarai a kan Abdulazeez da soyayyar sa. Kada ta manta Mammah ta yi musu aure cikin mutunci, ta so su zauna da juna cikin aminci su kaunaci juna da zuciya daya, amma suka hadu ita da shi suka yaudare ta,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login