Showing 153001 words to 156000 words out of 168255 words
ta ce tana so. Yana fadin wannan shin last timeda zaki sha pepsi dinnan naga kina son ta, tunda kika zo kike shanta kullumbayan cutarwa suke yi. Ba don a jigace take ba har bata son magana da ta ce dashi ba gara ni ba? Kaima ka daina shan Coca-Cola duk uwarsu daya ubansu daya. Kamar ya ji ta, ko da yake Abdulazeez reads her mind easily ta dade gane hakan, wisdom dinshi har tsoro yake bata. Sai cewa yayi nasan motsin da kikeyi da baki ai, ko ni da kika ga ina shan Coca-Cola tozero sugar ce. Sukazauna a karkashin wata rumfaya jirata ta sha, sannan suka fito inda za su samu abin hawa. Da wayarsa ya yi amfani wajen samo hotel mafi kusa da kotun da zai yi abin da ya kawo shi. Ya gaya wa mai motar inda zai kaisu suka shiga suka tafi.
Karamin daki ya kama musu ciki daya (falle daya) kwana biyu, ya sa katin a kofar ta bude ya shigar da jakarsu. Ta bi shi a baya ya maida kofar ya rufe. Hafsat tsaye ta yi a jikin kofar tana kakabin yadda za ta rayu daga ita sai Abdulazeez a wannan dan karamin dakin, shi kansa gadon bai fi mutum daya ya kwanta a kanshi ba.
Da ta sani ta hakura ta zauna a NewHaven kamar yadda ya ce da farko, to in za ta canza kaya ko shi zai canza ya za a yi kenan? In za su yi wanka fa? Ta kasan ido ya dube ta yana zaune gefen gadon yana warware igiyar cambas dinsa, abinki da Lawyer nan da nan ya gano abin da ta ke tunani. Murmushi ya yi ya ci gaba da cire takalminya zare socks, sai da ya gama tsaf sannan ya dago ya dube ta a kaikaice.
Akwai wani dare da ya saura ne da Jemage bai gani ba???”
Ban gane abin da ka ce ba, waye jemage? Ta amsa innocently.
SUMAYYA ABDULQADIR TAKORI
07030137870
*Littafi na farko shine kawai free. 234 na sayarwa ne. Idan ka fidda 234 ba sai na hada ka da Allah ba zai isar min insha Allahu. Ku biya Ku karanta a nitse cikin farin ciki yafi maka kayan zunubi ranar gobe kiyama*
Mikewa ya yi ya tako har inda ta ke kyawawan tafukansa na mannnewa akan marblesya tsaya a gabanta, space din da ke tsakaninsu ba shi da tazara, hannayensa biyu ya dora a kafadunta, daya a kafadar hagu daya a ta dama. Ya rage tsawonsa suka yi kai daya sannan ya dube ta cikin idanunta da shanyayyun idanunsa,fitarnumfashinsu na sarkewa dana juna.
Da na sani Hausa na nema miki a jamia Hafsah.
Murmushi ta yi kumatunta suka lotsa sosai. Itama Hausar karantarta ake yi??
Kwarai kuwa, yadda ake karanta Geography.
Ya sa hannu ya soma warware mata lullubin dake kanta, ya saki mayafin a kasa, ya kai hannu kan hudar karan hancinta da barimar danyen gold yar kankanuwa ta dade da samun muhalli yana mai zagaye barimar da dan alinsa.Yana daga abinda yake so a kawatacciyar fuskarta maabociyar zati da kamala wannan hular hancin,sai kuma ya zarce da hannun damansa saman kanta ya shafo kwantaccen gashinta mai santsi da sheki tun daga farkonsa har karshensa.Sannan ya hada mikakken karan hancinsu wuri guda ya soma magana cikin wata irin kasalalliyar murya.
Mommanki ba ta gaya miki daga ranar da ta aura min ke mun zama sirrin juna ba? Ba ta gaya miki mun zama marufar asirin juna ba? Ba ta gaya miki mun zama abu guda ba babu sauran boye-boye ko kunya a tsakaninmu? Na dauka kunyar ta kare daga jiya Hafsah?Amma na gani cikin kwayar idanunki kina kokonton zama da ni Abdulazeez a dan tsukukun daki???”
Dariya ta yi ta somakokarin sunne kanta cikin jikinshi. Ba dama tayi magana cikin ranta sai Abdulazeez dinnan ya karanta? Bai bata damar hakan ba (buyan) ya dago fuskarta yana so su hada ido ta rufe idon da azama.Thelong eye lashes.... suka bi idon suka kwanta luf; wani abu da ya dade da lura da cewa yana tsananin fizgar zuciyarsa zuwa gare ta ya sumbaci idanunta ko bai niyya ba. Fuskarta ya saka cikin tafukansa ya ce.
Kina min wannan lumshe idon Hafsat, za ki bari in yi assignmentdinnan kuwa?
Babu kuzari a cikin muryarsa a lokacin da yake fadin hakan. Bude idanun nata ta yi da sauri. Ni fa ba lumshe ido nake ba,ido ne bana so mu hada.
Saboda me toh? Hafsah in ba ki kalle ni ba wa za ki kalla? Ko ni in ban kalle ki ba wace pretty face zan kalla haka?
Murmushi ta yi sosai da jin kalamansa. Don Allah ka je ka yi assignment dinka.Ina so ka ci maki da yawa kafi duk abokan aikin ka cinyewa.
Dariya ta ba shi sosai, wai cinyewa kamar wani abinci.Ya janyo ta sannu a hankaliya rungume tsantsan a jikinsa, ya ce. Ashe kina sona haka da yawa Hafsat? Me ya sa ba ki gaya min ba tun muna gidanmu? Saidai ki dinga ga kallon hoto na a waya a cikin duvet?
Hannuwanta ya ji ta zagaya a bayansa ta rike shi gam-gam itama. Saboda na san ba ka sona lokacin Yaya Azeez, kaga fadar ba abinda zata sauya sai ma dai ta lalata komai,kuma ko na fada babu amfani tunda sakina za ka yi ka auro Muazatu.
Lumshe idanunsa ya yi, kansa a kafadunta, idanunsa a rufe yana shakar daddadan scent din gashinta, ya ce.
Kin san wani abu?
Aah.
Ban yi wa Muazatu irin son da nake miki ba Hafsat. Ko kusa da juna basu je ba. Ni dai kawai in aure ta shine babbar damuwata, wata damuwa data tsaya ta tokare a raina. Abin da nake ji kawai shi ne sai na aure ta ne zan samu kwanciyar hankali da nutsuwa, ko hannunta ban taba shaawar in kama haka kawai ba. Hirarrakinmu babubondbabu tiesirin wanda nake ji in ina hira dake kamar zan zauce.Hirarrakinmu sun fi yawa a kan karatunta, rayuwarta da alamuranta. And I respect her Dad (ina girmama Babanta), wannan shi ne tsakanina da Muazatu Rufai which is totally opposite to your case.
Hafsat tun daga ranar da ki ka sa ni a gaba kina tambayata wai ‘sex is not allowed in Nigeria na fahimci you are very very innocent, your heart is soft and freshbabu komai a cikinta sai tarin tsabta da kuruciya. Ranar da na yi rashin lafiya ki ka kula da ni na kara fahimtar zuciyarki mai kyau ce, kuma kin san hakkin abokin zamanki duk da kuruciyarki ko da bana dadada miki. I cannont recall when I started touching you and how,but your protest....???Hummm! Ya fahimtar da ni kin kulle wani abu a ranki a kan zamanmu, kin fara sanin ciwon kanki wanda a da ba ki sani ba. Kina kullace da ni akan wasa da rayuwar ki, kuma a shirye kike da ki yi fighting dina for your rightda na danne a kan wata. Tun daga lokacin Hafsat na soma tsoronki, na fara shiga taitayi na, na kuma fara sansano wata rana na zuwa da ke din nan da nake rainawa za ki juya duniyata idan ban yi da gaske ba.
Ban fita daga wannan taraddadin ba na soma hada jiki da ke ba tare da zuciyata ta yi shawara da ni akan hakan ba . Hafsah ba zan iya hakan da macen da bana so ba. Inada kyama inada tsantseni.Im very sensitive and cautious ga inda zan kai hannu na balle jiki na. Your protest brought a number of sleepless nights to me!!! Ba zan iya gaya miki halin da na shiga ba saboda a lokacin na yi zargin kin fara sona kamar yadda na samu zuciyata da hakan ina karyatawa da gangan, za ki bari mu mori auren ko ya ya ne, soyayya ta sa a manta da kwangilar har sai lokacin ta ya zo. Sai kika nuna min kin san abin da ki ke yi, wanda hakan ya sa ni jin kunyarki, ya kara miki kimaa idanuna. Ya tattaro miki daraja mai yawa, na zo ina tababar yiwuwar rabuwar nan. Na shiga tsaka mai wuya, ga alkawari ga soyayyar gaskiya ta huda ni. A lokacin na yardar wa kaina na zalunce ki da wannan contract da na jefa mu a ciki, amma na rasa hanyar fita. I then concluded in fita daga sarkakiyar da na jefa kaina daga baya in dawo da ke mu gyara aurenmu ba tare da kowa ya ji ba.
Lokaci ya yi min halinsa ko in ce Allah bai barni na yi yadda na ga dama da rayuwarki ba, sai da Ya hukunta ni, Ya dandana min azabar subucewarki daga hannuna. A karo na biyu ina rokonki ki yafe mini domin hakika na zalunce mu bakidayanmu..
Dumi ya ji a bayansa wanda ba ya ko tantama hawayen Hafsat ne. ba tun yau ya lura ba abu kankani ke sanya ta kuka. Abu kankani ke karya zuciyarta. To yanzu sabida Allah cikin labarin zuciyarsa da yake ba ta me ye abin kuka? Dago ta ya yi daga jikinsa ya soma dauke mata hawayen da bakinsa.
Alfarma ta karshe da na ke nema ki yi min Suhaanahdont ever talk about Muazatu again, shes a bygone in our life,sheexists only in our past; our destiny to be tormented by.Lets create our peaceful present and abright futuretunda ita din ta zame mana ciwo. Yo ciwo mana?
Duk wani abu da zai sa ka fita hankalinka ka kasa gane abu mai kyau da mara kyau kuma ka kasa bin iyayenka akansa ai ya zama ciwo. I dont want to recall the moment I put you in trouble with your mother (bana son tuna lokacinda na sanya ki a matsala da Mamanki ) saboda hoton Muazatu a falonki. Ranar nan na ji kunyarki mai yawa na muzanta, na kirga ta cikin tarin uzururrukan da ki ke yi mun. Imsorry Hafsah once again, ni na kasa yi miki uzuri ko daya. You received a weird welcome from me.
Dariya ta yi ta zame daga jikinsa ta zauna a gefen dan tsurut din gadon don kafafunta sun gaji da tsayuwa, da alama shi Yaya Azeez tsayuwa ba ta gajiyar da shi sai kace soja. A kalla sun kwaso mintuna sittin a yadda suke. Cikin shagwabar da ba ta san ta yi ba ta ce.
Kuma sannan ka yi barringdina ba, na kasa kiranka.. na kusa mutuwa sabida damuwa da rashin jin muryarka!”.
Kusa da ita ya zo ya zauna kafada-da-kafada, ya juyo yana kallonta da kyawawan idanunsa.Fuskar sa kawai ta bayyana dadin da kalaman ta suka yi masa baka da zuci. She loves him to such an extent amma tahadiye. Ta iya controlling kanta a kullum. Hannayenta ya kama ya rike gam! Cikin nasa.
Saboda ki dandana abin da ake dandanawa in mutum na son magana da matarsa ta hana shi. A duniya ina da rival irin karatunki Hafsah? Im very-veryjealousof it. Ya fada yana kaurara very-very din wanda ya fito tun daga karkashin zuciyarsa. Hafsat me za ta yi in ba dariya ba? Ban da an an kashe deal din Muazatu kuma ta yi masa alkawarin ba za ta kara zancenta ba, da ta ce wani abu akai. Kafafunsa ya mayar kan tafukan kafarta ya sarkesu cikin na juna ya kumatake susosai da yatsunsa, ya fiddo fararen idanunsa a kanta cikin damuwa.
“Tell me please. Ni da bokon nan naki wa ki ka fi so? Na san da Allah ya ba ku damar aure fiye da daya da mu biyu za ki aura ni da shiIm sure. Ya karashe kalaman da karyayyen sauti. Ta sunkuyar da kai ya dago fuskar ta. “You are to look directly into my eyes and answer me Hafsah(cikin idanuna za ki kalla ki amsa mini).
A yadda Hafsat ke jin zuciyarta tun daga lokacin da ta fara hankali a gidan Abdulazeez, ta fara bambance me zuciyarta ke ji a kansa, ta fara sanin darajar aure da martabarsa; to tun a lokacin ta riga ta mika wuya ga cewa; za ta iya hakura da komai in dai za ta tsira da shi!!! Idan ta ce komai tana nufin KOMAI!!!
Ciki kuwa har da nemo mata biological parentsdinta. Ta ji cewa za ta iya rayuwa a doron kasa ko babu kowa in dai yana tare da ita. Yau da ya yi mata wannan tambayar sai ta samu kanta da kasa cewa komai. A ganinta kalaman will not be enoughto express her inner feelings wani lokacin shiru ya fi faida a inda babu gamsasshiyar amsa.
Maimakon hakan, sai ta fada jikinsa da karfi ta wani irin cukwikwiye shi tamkar zata shige cikin tsokar jikinsa. Yana iya jin karfin matsar da ta yi masa da iyakacin karfinta kamar zata balla shi. Har sai da ta kai shi ga fadawa saman dan gadonsu akan bayansa sabida bai zata ba jinta kawai yayi. Ta bishi ta turmushe tana tumurmusa ta koina. Dariyar da bai shirya yi ba ce ta kufce masa.
Meye haka Hafsat? Karya ni zaki yi?
Nasa rukon da ya yi mata in returnya kuma jirkita ya maida ta upside-down(is beyond herwords to express the tightness). Hakannanya sanya ta yin nadamar gwada masa karfi don nuna innerexpressionsdinta. Bata da idea na yadda zata nuna din kuma tana so ya fahimta. Wani riko ne da ko jiya bai yi mata kwatankwacinsa ba. Amma can kasan zuciyarta ta sa a ranta za ta jure goman wannan a kowacce rana...... in dai hakan zai sa Abdulazeez ya rayu da ita ita kadai! Cikin kunnenta ya rada mata, a lokacin da ya dawoABDULAZEEZ dinsa maimakon mijin HAFSAH! .
“Addah Hafsatuh,kin kusa balla ni fah! Yarinyar nan karfi gareki dama??In shi ki ka aura, ai ba za ki so ki balla shi ba;Imvery surelallaba abinki za ki yi ta yi ku tsufa kuna morar juna cikin lallaba tsufanku da tsohuwar soyayyar ku.
Ta dubeshi cikin takaicin abinda yake fadidaga cikin duvet dinta data cukwikwiye ita kadai ta hana shi (dama ta saba) ta bata fuskatace.
Bokon? Bokon zan aura Yaya Azeez?”
Ya dago fuskarta cikin tafukansa yana jan tsinin karan hancin ta da yatsun sa biyu,wata halitta guda daya da tafi komai burgeshi da jan hankalinsa a fuskar matarsa Hafsat (dogon karan hancinta). Kallonta yake deeplytamkar ya hadiye ta bakidaya don SO. Cikin imitating(kwaikwayon) yanayin da ta yi maganar yace.
“To ni Abdulazeez damainada wani rival dina duniya bayan shi ne? Kar fa ki manta har kwana kike raba mana ni da shi, kada wani ya shiga na wani, ke ga mai maza biyu, in ban yi kishi da Bokon ki ba Hafsah da wa zan yi a duniya???”
Hannu ta kai ta dafe goshinta.
Na rantse Yaya Azeez da kai mace ne da mun shiga uku sabodamita. Oh ni Hafsatu yar Habibah jikar Hashim Babbah! Da na san abinda kashe wayar nan zai jawo min kenan da banyi shi ba. Juya mata baya yayi yana so yayi dariya. Amma ya hadiye don ya san ta tsani hakan, ta sake jawo shi da karfi ta baya jikin ta yana dan rawa.
Yaya Azeez babu wani duvet din? Na rufa da wannan amma kamar da zanin atamfa na rufa ban daina jin sanyin ba. Ta fada kamar zatayi kuka kuma sosai da gaske bilhaqqisanyin take ji,tsigar jikinta har tashi take yi duk da ta rufa din ta kuma handame abin rufar ita kadai ta hana shi.
Juyowa yayi ya kama duvet din yana kokarin janyewa ta rike gam-gam. I cant do without It, don Allah ka bar min nikadai.
Rausayar da kai yayi yana mata wani irin kallo wanda daga jiya zuwa yau ta gama sanin maanar sa tsaf!Idanunta sukayi kwalkwal amma ta riga tayi alkawarin juriya ga alamarin nan no matter what in dai zata tsira da shi!!! Ga mamakinta bayan ya raba ta da duvet din maye gurbin sa yayi a hankali in a way that is unusual to her.Hakan yasa rawar da jikin nata ke yi da tashin tsigar jikintaya ragu.
Relax Addahh,ni ba na jin sanyi,balle in kwace miki abin rufar ki. Andits not what you are anticipating Baby....
Sabuwarhanyar samar da HEAT kenan wadda tafi dukkan duvets dinki. Youhave me now......no need of your quilts daga rana irin ta yau. Ya hade bakunansu wuri guda kamar yadda ya hade jikkunansu, hannunsa cikin sumar kanta yana fadin.
Jaruma, kuma matsoraciya Hafsatu matar Barrister Abdulazeez Hamzah Atiku!.
Murmushi ta hau yi irinna karkashin zuciya. Tana mai kara nitsewa a cikin jikinsa. Wani identity data dade tana kwadaitawa zuciyarta a farke ko a mafarki. Yau gashi ya fito kai tsaye daga bakin mamallakin sa.
“The heat is unique, so its provider!
Magana take a zuci cikin lumshe idanu tana kara rungumeshi tsam, batasan cewa a fili take yi ba.Shima murmushin yayi yace mata a cikin kunnuwanta.
“TheMammahs patient is also unique too. I love herso much Hafsah! And the word LOVE is not enough!It can only make a comparison. Allah ya kara miki lafiya!!!
******
Wannan assignmentdai da kyar aka yi shisharp-sharp a washegari, sai dai su kansu sun san ba za su ci makin yadda Hafsat ta yi fata ba. In aka ce ya samu C to sunyi kokari. To duka an cinye lokacin a soyayya da wani irin honeymooning mai ban mamaki a dan tsukukun dakin (ta bakin Abdulazeez) dake cikin hoteldin WyndhamDallas Suitescikin birnin Texas. Tunda suka shigo hotel din nan sau biyu ya fita ya je kotun, daga safe zuwa yamma, ya harhada abinda ya kawo shi ya rubuta yayi typing acan.Abinci daga hotel din suke order a shigo musu da shi.
Ranar litinin suka koma NewHaven suka ci gaba da rayuwarsu mai tsafta da ban shaawa, wadda soyayya da kauna yar usulisune jigonta.Hafsat tarairayar Abdulazeez ta ke kamar ta maida shi cikin kirjinta, tareda kinkimar duk wasu bukatun rayuwarsa da dukkan iyawa da jarumtar da bai taba zato ba. Abdulazeez kula yake da Hafsat kamar yadda yake kula da bugun zuciyarsa. Duk wani abin bukatar diya mace ya kaita ya saya mata. Ya sayawa Mammah tsaraba sosai. Akwai sanda suka shiga wani shagon kayan sawa ya ga tana diban T.Shirts da Trousers masu kyau na maza tana faman gwadawa da jikinsa tana jefawa a kwando, ya ce.
Ban gaya miki bana bukata ba ne? Tsaraba kawai nace kiyi ba ruwan ki da